Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba ta ƙara mintuna masu yawa cikin ɗakin ba, ta fice ta bar shi tsaye cike da saƙe-saƙe.


.. "Yah Tareeq ka yi haƙuri, ban san wane irin kallo za ka mini ba, ban kuma san wane irin hukunci za ka yi mini ba, idan na sanar da kai cewa na kamu da soyayyar abokinka Abdoul. Ka yi haƙuri Yaya." Hidaya da ta karanta saƙon da Sultanah ta gama rubutawa ta tura.

"Wallahi Hidaya ina tsoron fushin Yah Tareeq." Sultanah ta faɗa kamar za ta yi kuka.

"Ke ki dena jin tsoro, ina tare da ke fa." Hidaya ta faɗa tana riƙo hannun Sultanah, duk da ita kanta tana jin tsoron, amma don ta ba wa 'yar'uwarta ƙwarin gwuiwa ya sa ba ta nuna ba. Ganin alamar blue tick da suka yi ne ya sanya kusan a tare suka gyara zama. Sultanah ta haɗiye wani yawu da ƙyar tana jin yadda bugun zuciyarta ke ƙaruwa. Ba ta san yadda za ta yi da zuciyarta ba, ba ta san lokacin da ta faɗa ƙaunar Abdoul ba. Farga kawai ta yi dumu-dumu cikin wata matsananiyar ƙaunarsa irin mara adadi ɗin nan. Tun tana ganin za ta iya jurewa har ta kasa, don kuwa yanzu haka ita kaɗai ta san irin zafin da zuciyarta take yi, na rashin isar da saƙon zuciyarta gare shi, har zuwa wannan lokacin. Ta san halin yayansu, shi ɗin mai damuwa da damuwarsu ne, sai dai ba ta sani ba, ko a wannan karon ma ze bi bayanta ne bayan ta sanar da shi tana ƙaunar abokinsa. Ba ta sani ba ko ma hukunci ne ze biyo baya.

"Har yanzu fa be yi reply ba Hidaya." Sultanah ta faɗa ganin da ta yi bayan wajen minti 5 da ganin saƙon da Tareeq ya yi amma har yanzun be yi reply ba.

"Ze yi ne Sulty, mu ƙara lokaci." Hidaya ta faɗa a sanyaye, saboda yadda ta ji gaba ɗaya ɗan ƙwarin gwuiwar da ta yi nasarar haɗa shi yana ƙoƙarin zagwanyewa.


A ɓangaren Tareeq kuwa ya karanta saƙon nan ya fi sau uku. Daga ƙarshe dai sai ya sake dubawa don tabbatarwa da gasken Sultanah ɗin ce ta turo masa saƙon. 'Tabbas ita ce' Ya tabbatar wa da kansa hakan yana sake kallan saƙon. Shiru ya yi na tsawon lokaci, tabbas abin ya matuƙar ba shi mamaki, ya kuma ɗaure masa kai. Be taɓa tunanin ƙanwar tasa za ta iya yin hakan ba, har kuma ta sanar da shi. Sai dai kuma da ya nutsa tunaninsa sai ya ga abin da Sultanah ta yi kamar shi ne daidai. A matsayinsa na yayanta mai ƙoƙarin samar mata mafita a kowanne yanayi ne, shi ya kamata ta sanar wa da abin da ke faruwa. Abu na biyu kuma shi ɗin aminin Abdoul ne, wanda ze iya amfani da kasancewar hakan wajen samar wa 'yar'uwarsa mafita. Sauka ya yi daga Whatsapp ɗin kai tsaye ya nemo number Abdoul ya kira. Ringing 1_2 ya ɗauka, kafin Tareeq ɗin ya ce komai Abdoul ya ce

"Barka Aboki."

"Yawwah, kana lafiya?" Tareeq ya faɗa hannunsa na kan goshinsa yana ɗan murzawa.

"Alhamdulillahi. Ya ake ciki?" In ji Abdoul.

"Kana gida ne?"

"A'ah, yanzu na ɗan fita ne karɓo saƙo." Sai da Tareeq ya ɗan gyara zaman sa sannan ya ce

"Ohk, gobe za ku shigo ai?" Murmushi Abdoul ya yi kana ya ce

"Eh mana, da wuri ma kuwa In Sha Allah."

"Allah Ya nuna mana, akwai wata muhimmiyar magana da nake so mu yi da kai."

"Ikon Allah! Wacce magana ce wannan?" Abdoul ya faɗa cike da mamaki. Ɗan murmushi ne ya wanzu a kan laɓɓan Tareeq kafin ya ce

"Kai dai za mu haɗu."

"Malam ka sanar da ni kawai please."

"Sai kuma ka yi ai." Tareeq ya faɗa cikin basarwa.

"Kai fa dama ɗan rainin hankali ne wallahi.." Abdoul ya dakata daga haka, kafin ya yi ƙwafa kana ya ɗora da faɗin

"Amma ya na iya.. Allah Ya kai mu." Murmushi mai sauti Tareeq ya yi kana ya amsa da "Ameen." a nutse. Daga haka suka yi sallama.


**
Washe gari sosai gidan ya tashi da karɓar 'yan'uwa na kusa. Waɗanda ke ta shirye-shiryen dawowar Alhaji Alhassan Dikko. Jawahir da ba su kwana a gidan ba, da sassafe suka diro gidan don tarbar Abeeyn. Tun safe duk suna sashen Dada ji, Maama, Hidaya, Sultanah, Jawahir da Mamanta. Maamin Sultanah ce kaɗai tun wayewar garin kwata-kwata ba ta shigo ba. Duk kuwa da cewa ayyukan da ake gabatarwa sun fi yawa a sashen Dada ji ɗin kamar yadda aka saba. Duk kuma da cewa ta san duk en gidan suna sashen nata, hakan be sanya ta zuwa ba. Tana can sashenta tana shirya wa mijinta abubuwa na musamman. Babu kuma daɗewa ƙawarta, aminiyarta Hajiya Zulaiha ta iso gidan. Mata ga Aminin Abeey, kuma mahaifiya ga Abdoul Aminin Tareeq. Su biyu suka iso gidan, Abdoul ya wuce sashen Tareeq, ya yin da Umma ta wuce kai tsaye sashen Maami.

Da sallama ya shiga palourn, idanunsa a kan Tareeq da ya kwantar da kansa a kan kujera idanunsa a lumshe. Ya ɗora hannunsa ɗaya a kan fuskarsa, wanda hakan ya yi nasarar kare idonsa guda ɗaya. Sai da Abdoul ya ƙarasa ya zauna a gefen sa ya ce cike da mamaki

"Tareeq." Da sauri Tareeq ya buɗe idanunsa, don kwata-kwata be ji shigowar Abdoul ba. Idanunsa da suka ɗan janye saboda daɗewar da suka yi a lumshe ya sauke a kan Abdoul. Ya ja wani nannauyan numfashi da ya fito daga ƙirjinsa a takure kafin ya ce

"Yaushe ka shigo?"

"Bayan ka yi nisa a tunanin." Tareeq ya faɗa yana karantar yanayinsa. Iska kaɗan Tareeq ya fesar daga bakinsa kafin ya gyara zamansa, ba tare da ya ce komai ba, har lokacin da Tareeq ya ce

"Anya kuwa lafiya Aboki?" Ya faɗa yana sake karantar yanayinsa. Cikin basarwa Tareeq ya ce

"Lafiya mana, wani abu?" Ya ƙare har lokacin dai cikin basarwa.

"Ko dai har yanzu maganar Diyana ne?" Be san lokacin da tsaki ya suɓuce masa ba.

"Me kake so na ce maka ka yadda na daɗe da cire Diyana a babin rayuwata? Allah ɗaya ne koh? Toh ina rantse maka da shi, ko kaɗan babu damuwar Diyana a tattare da ni. Ina ga zuwa yanzu ya kamata ka amince da ni." Numfashi Abdoul ya sauke kana ya ce

"Shi kenan, amma tabbas idan babu wannan akwai wani abu da kake ɓoye mini." Da sauri Tareeq ya girgiza kai. Ba tare da ya kalli Abdoul ba ya ce

"Kar ka damu kanka, babu wani abu."

"Amm.." Abdoul ya buɗe baki ya fara magana Tareeq ya yi saurin katse shi da faɗin

"Maganarmu.." Girgiza kai Abdoul ya yi, jin yadda ya basar da zancen. A ransa yana saƙa tabbas ko ma mene ne, idan ta yi tsami ze ji. Idan dai har abin da ya kamata ya sani ne, toh ya san Tareeq ɗin ze sanar da shi ko ba yanzu ba. Hakan ne ya sanya shi faɗin

"Ina jin ka." Gyara zama Tareeq ya yi, sai dai kafin ya ce komai wayarsa ta soma ƙara. Ya janyo ta yana kallan mai kiran nasa.

"Yaya wai ka fito muna palourn Dada ji." Hidaya ta faɗa, bayan Tareeq ya amsa wayar.

"Ohk." Ya amsa da hakan, yana mayar da kallan sa kan Abdoul ya ce

"Tashi mu je, Abeey na dab da iso wa." Ya faɗa yana miƙewa. Be jira Abdoul ya ce komai ba ya shige bedroom ɗinsa. Bayan shuɗewar wasu mintuna ya fito, suka fice daga sashen gaba ɗaya.


... A ɓangaren Daneen kuwa, da mayafin da ke jikinta ta yi amfani wajen nannaɗe fiye da rabin jikinta. Ta kifa kanta a kan gwuiwarta tana lumshe idanunta. Kewar mahaifiyarta take matuƙa gaya, kewarta ce ke ratsa duk wata gaɓa ta jikinta. Yanzu ko tana ina?Tana can tana tunanin suna zaune a ƙauyensu suna jiran ta? Tana can ita ma duk inda take hankalinta yana kansu, kamar yadda nasu hankalin ke kanta? A nutse ta sake lumshe idanunta tana jin yadda wani bacci ke ƙoƙarin fizgarta. Haka ta yakice shi, don duk wani hankalinta yana kan Ameer. Ta kwashe fiye da awa ɗaya tana ta saka ran jin muryar Ameer ya yi mata magana, amma shiru. Tun tana cigaba da kwanciya har ta gaji ta tashi zaune, ta shiga rarraba manyan idanunta da suka ɗan faɗa, cikin rashin sanin abin yi. Wasa wasa, har bayan wajen awa uku, babu Ameer babu alamarsa. Har ba ta san lokacin da ta miƙe a kan ƙafafunta ba, duk da jikinta da babu ƙwari hakan be dame ta ba, burin ta kawai ta san yadda za ta yi ta je ta nemo inda Ameer ya yi, ya bar ta a nan tana ta jiransa. Har ta soma takawa don barin wajen, kamar wadda aka tsikara kuma sai ta dakata. Ta sake kallan inda take tsaye, sai ta mayar da ƙafarta baya. Gaba ɗaya tunaninta ya tafi kan Ameer, idan kuma har ta bar wajen nan, kai tsaye ba ta san inda za ta nufa ba. Bayan kuma ya faɗa ya sake jaddada mata da kar ta je ko'ina komai daɗewar da ze yi ta jira shi. Idan ta bar wajen kuma shi ya dawo be gan ta ba fa? Daga nan me zai faru? Cikin sauri ta shiga girgiza kanta kamar wadda ke magana da wani. Cikin matuƙar sanyin jiki ta koma da baya ta zauna inda ta tashi. Tana nan zaune har ta ji an soma kiraye-kirayen Sallahr Azahar, amma babu Ameer babu dalilinsa. Gaba ɗaya wani tunaninta ya tafi kan inda ya tsaya. Haka zalika tambayar da ke ta mata yawo a cikin kwanya ita ce 'Ina ya tsaya? Me ya sa har yanzu bai dawo ba?' Cikin sakannin da ba su wuce biyu ba, ta ji bugun zuciyarta ya ƙaru, nan take jikinta ya ɗauki rawa, fararen idanunta tuni suka soma sauya kala, cikin sakanni ƙalilan, hawaye suka taru. Kawai sai ta shiga juye-juye, cikin rashin sanin abin yi, sai ka ce wadda aka cewa idan ta juya ɗin za ta hango shi. Duk kuma lokacin da ta kalli mutanen da ke kaikawo a wajen, sai ta ga kamar za ta hango Ameer ɗin a cikinsu, babu kuma abin da take ji, sai ƙarin faɗuwar gaba, da bugun zuciya.


A yi manage da wannan, In Sha Allah gobe ma za ku samu Update.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 16

Kamar idanunta za su faɗo, haka take ci gaba da kallon hanyar da ta ga Ameer ya bi. Zuwa can dai ta miƙe a kan ƙafafunta, ba ta kuma san yadda za ta iya ci gaba da zama a wajen ba, bayan takamaimai ba ta san inda ɗan'uwanta yake ba. Ga shi kuma har an idar da Sallahr Azahar. Sai dai miƙewar da ta yi ya yi daidai da lokacin da muryar Ameer ta daki dodon kunnenta.

"Adda." Ai ba ta san lokacin da ta juya da sauri ba. Take idanunta suka sauka a kan Ameer. Wani murmushi mai haɗe da ƙwalla suka wanzu lokaci guda a kan fuskarta. Idan ta ce tana farin ciki ma ɓata baki ne, don kuwa fuskarta kawai za ka kalla ka fahimci tsananin farin cikin da ta tsinci kanta a ciki bayan ganin Ameer.

"Ameer ina ka je?" Ta yi tambayar da ke ta ci gaba da yi mata lugude a ka. Murmushi ne ya suɓuce masa kafin ya ce

"Aiki na samo Adda, kina zaune zan din ga yin aiki muna samun kuɗi. Mu samu na cin abinci da komai ma, har kuma mu tara na koma wa ƙauyenmu." Ya ƙare yana murmushin dai. Wani sabon murmushin ne ya sake ƙwace mata, ta ce

"Da gaske?" Jinjina kai ya yi kafin ya ce

"Ehh, amma dai ki zauna ki fara cin abinci yanzu. Ya jikin naki?" Sai da ta harare shi kafin ta ce

"Bayan duk ka gama tsoratar da ni."

"Wallahi Adda ina can ina tunanin kar ganin na daɗe ki ce za ki je ki nemo ni, in zo kuma ban gan ki ba in shiga 3." Ya ƙare fuska a marairaice. Har ba ta san lokacin da dariya ta suɓuce mata ba.

"Mu je mu samu ruwa mu yi sallah tukunna." Ta faɗa. Be musa mata ba, ya amsa da "Toh."


... Tun daga farkon layin idan ka kalla za ka fahimci lallai wani gagarumin al'amari ke faruwa. Saboda yadda motoci ke ta kai-kawo cikin layin, 'yan sanda na ta zagaye, haka zalika mutane na ta kai da kawowa. Kowa ka kalli fuskarsa cikin annushuwa yake, wanda hakan ze alamta maka cewa ko ma mene ne abin da ke faruwa abin farin ciki ne. Tahowar wata ƙatuwar hamshaƙiyar mota da kallo ɗaya za ka mata ka san kuɗinta ba na wasa ba ne, shi ne abin da ya sa masu gadin gidan wangale ƙatuwar ƙofar gidan tun kafin motar ta ƙaraso. Tuni kyakykyawan dattijon mutumin da ke sanye cikin farar shaddar da ta matuƙar yi masa kyau, ta kuma sake bayyana kwarjininsa da kamalarsa ya gyara zamansa. Tun kafin ya ce komai, drivern ya yi hanzarin wangale glasses ɗin motar. Wanda hakan ya ba wa mutanen da ke tsaye suna jiran zuwan Alhajin nasu damar soma ganinsa. Cikin lokaci ƙanƙani fuskarsa ta cika da annuri, ya yi amfani da hannunsa wajen ɗaga musu hannu fuskarsa na cigaba da nuni da yadda ya yi farin cikin ganin su. Alhaji Alhassan Dikko kenan, mutum mai matuƙar kima da mutunci a idon jama'a, mutum mai matuƙar taimako da jiki da dukiyar da Allah Ya ba shi. Mai kirki, mai matuƙar kula da buƙatun mabuƙata, maƙotansa da kuma mutanen gari. Wanda hakan ya saya masa soyayyar mutane da dama, ya kuma ƙara masa kimar da tun tale-tale yake da ita. Har sai da suka dangana da cikin gidan sannan mutane suka haƙura. Daga haka aka rufe gate ɗin bayan motocin da ke bin bayan ta Alhaji Alhassan su ma sun shige cikin gidan. Shi har ya riga ya saba, duk lokacin da ya yi tafiya irin wannan haka mutane ke masa duk ranar da ze sauka a ƙasar. Don kuwa ƙarya ne mutum ya ce be yi kewarsa a en kwanakin da ya yi ba ya ƙasar ba. Saboda yadda ya kasance mutum mai matuƙar kula da duk wanda ke kusa da shi. Duk da kafin ya tafi yana ɗora wani a kan abubuwan da yake yi, amma duk abin da ze yi, ba ze kai wanda yake yi ba. Shi ya sa idan yana nan abubuwa da dama suka kasance na daban, suke kuma tafiya a tsari.

Ko a cikin gida ma hakan ce ta kasance, mutanen da ke zaune cikin gidan tuni suka fara zuwa suna kwasar gaisuwa, kamar kodayaushe fuskarsa cike da annuri yake amsa musu. Kai tsaye sashensa ya wuce kamar yadda ya saba, sashen nasa na nan a gyare tsaff-tsaff kamar yadda ya tsammata. A gaggauce ya watsa ruwa a jikinsa kana ya sake shiryawa cikin babbar rigar shadda ita ma fara. Kai tsaye ya wuce sashen Dada ji da gaba ɗaya iyalan nasa ke jiran sa a can ɗin. Ai kuwa cikin matuƙar farin ciki dukka suka tarbe shi lokacin da ya iso. Kowa ka kalli fuskarsa ka san tabbas yana cikin farin ciki. Sai da ya shafe wajen mintina goma, sannan Maami ta iso, ita da Mom Abdoul, ba ta yi tsammanin kai tsaye nan ɗin ze wuto ba. Shi ya sa ta din ga tsumayin ganin inda ze nufa, sai dai shirun da ta ji ne ya tabbatar mata da tabbas nan ɗin ya nufo. Wannan ne dalilin da ya sa ta ɗebo 'yan matan ƙafafunta ta taho, duk da ta so tare suka shigo. Dan da ta san ma ba zai shiga sashenta ba, tun a harabar gidan za ta je ta tarbe shi don su shiga sashen Dadan a tare. Ko minti 5 ba su yi da zama ba, bayan sun yi wa Abeey barka da zuwa, Amininsa Alhaji Bashir ya iso gidan, mahaifi ga Abdoul. Sosai farin cikin Abeey ya daɗu. Bayan kwanaki masu yawa, yau ga shi tare da iyalansa, ga kuma abokinsa ƙwalli ɗaya takk da yake da shi tun yarinta shi ma. Wannan dalilin ne ya ƙara ƙawata zaman nasu. Nan aka shiga hirar yaushe gamo. Kafin zuwa can aka nufi ɗakin da ya kasance na cin abinci, nan cikin sashen Dada ji. Sultanah, Hidaya da Jawahir su ne suka kwaso komai daga kitchen ɗin Dada ji suka jere shi kan dinning ɗin. Abubuwa ne kala-kala masu aji, waɗanda aka yi abubuwan da Abeeyn ya fi so a rayuwarsa. Baƙin-ciki kamar ya kashe Maami, da ta tuna abincinta na can jibge yana jiran Abeeyn. Kenan idan ya zauna ya ci abincin a nan, ita kuma nata ya za ta yi da shi? Ita fa dama wannan tsohuwar tana matuƙar shige mata hanci da ƙudundune, tana yawan kawo mata cikas a cikin al'amuranta.
A kusa da Dada ji ya zauna, don babu ƙarya ya yi kewar mahaifiyar tasa. 'Yan matan ba su zauna ba, sai da suka yi serving na kowa kafin suka ja kujera suka zauna. Duk yadda Sultanah ke ƙoƙarin ta jure, ba ta din ga satar kallon Abdoul ba, hakan ya gagara, ta kasa daurewa. Don haka a ɗan fuzge ta din ga satar kallon shi, cike da fatan kar ya kama ta, ko kuma Yah Tareeq ya gan ta, ya tuna be yi mata faɗa a kan abin da ta yi ba. Don kuwa tun da ta ga ya kalli saƙon be ce komai ba, ta san tabbas wani abun yake shiryawa, dalilin kenan da ya sa take jin jikinta a matuƙar sanyaye. Ita dai Jawahir sai sakin murmushi take yi, saboda yadda Ummanta ta sanar da ita Maama ta tabbatar mata da za ta isar wa da Abeey maganarta ita da Tareeq. Ita kuma dama ba ta da wani buri illa na mallakar Tareeq ɗin. Ba tun yau ba, kyawunsa ke matuƙar kashe ta, tana ƙaunarsa ainun, tana matuƙar son kallon kyakkyawar fuskarsa, da kuma irin ƙirar da Allah Ya ba shi. Sai bayan sun gama cin abincin sannan suka koma palourn Dada ji, nan aka cigaba da hira sosai. Sai dai idan dai har abin ya shafi Maama, toh ba za ka ji Maami ta ce komai ba. Don ita hirar ta ta fi kasancewa ne tsakaninta da Hajiya Zulai, da kuma Alhaji Bashir. Duk abin da take Dada ji na lura da ita, ta yi dai kamar ba ta gani ba ne. Don ita kam har ta gaji da yi mata magana a kan halayenta. Maamin wata irin mata ce da lokuta da dama ka kan kasa gane kanta. Ban da haka idan hali mai kyau ne Maama ta fi ta. Amma kuma ita burin ta kawai kowa ya yi harkarsa, ba ta son wani abu ya haɗa ta da abokiyar zaman nata kwata-kwata. Sai ka ce masu zaman gaba, wanda ita Dada ji ba za ta ɗauki hakan ba. Duk da hakan ya fi saka wa su zauna lafiya, amma kuma babu yadda za a yi su zauna babu magana, bayan suna zaune ne cikin gida ɗaya, ƙarƙashin mutum ɗaya. Kuma hakan ya samo asali ne, tun wani ɗan tashin hankali da ya faru tsakanin su, Dada ji ɗin da kanta ta shirya al'amarin, ta ce babu ruwan kowa da kowa. Shi kenan Maami ta riƙe wannan maganar, a cewar ta ai an ce da ita babu ita babu Maama. Ya yin da ta ɓangaren Maama, duk wani abu da ya shafi Maami babu ruwanta da shi, amma tabbas idan suka haɗu za ta mata sallama, da sauran su. Girgiza kai Dada ji ta yi. 'Mace sai ka ce mai zuciyar kafirai, kina abu tamkar ƙaramar yarinya. Toh ai ga mijin naku nan ya dawo, sai ki ci gaba da gaba da abokiyar zaman naki' Ta raya hakan a ranta.

Kallon Tareeq Abeey ya yi da ya miƙe yana gyara tsayuwarsa hannunsa ɗauke da waya.

"A'ah, Tareeq ina za ka je ne?" Ɗan murmushi ya yi a kan laɓɓansa kafin ya ƙarasa gaban Abeeyn ya tsuguna a gefen kujerar da yake kai ya ce a nutse

"Abeey, ina buƙatar fita ta gaggawa." Daga haka suka ɗan yi magana ta tsawon mintina biyu a hankali, wanda babu wanda ze ce ya ji abin da suka faɗa. Kallan Tareeq Abeey ya yi, kana ya ce

"Ubangiji Allah Ya tsare, zuwa gobe ma samu mu tattauna." Abeey ya faɗa yana ɗan kafe shi da idanunsa, saboda tabbatar da abin da idanun nasa ke ganar masa a fuskar ɗan nasa.

"Ameen Abeey." Ya faɗa yana miƙewa. Sallama ya yi da duka mutanen ɗakin kafin ya fice. Kai tsaye sashensa ya wuce, ya ɗauki abin da ze ɗauka ya fice daga gidan. Ba shi ya dawo cikin gidan ba, sai bayan ƙarfe 12pm. Don haka ruwa kawai ya watsa ya kwanta don yadda idanunsa ke buƙatar bacci.


... "Idan da zaɓi za ka ba ni, toh tabbas zan nemi soyayyar Hidaya ne, saboda Sultanah mahaifiyarta duk da kasancewarta aminiyar Ummeey ina shakkar ta wallahi." Abdoul ya ƙare yana shafa kansa. Dariya Tareeq ya yi jin abin da ya faɗa. Ya ja siririn tsaki kafin ya ce

"Amma dai ka ba ni kunya Abdoul.. Amma dai ba wannan ba, ni nan ni ne amininka, kuma ina mai ba ka shawara da ka nemi Sultanah saboda ta fi Hidaya sauƙin kai. Abeey dai shi zai aurar da Sultanah ba Maami ba, idan kuma ba shi ba ni ne. Don haka kar ka ji komai, duk da ma Maami na da kirki wani lokacin, amma fa idan ka fahimce ta." Jinjina kai Abdoul ya yi irin a yatsinen nan, cike kuma da rainin hankali ya ce

"Ehh, haka fa." Wani murmushi Tareeq ya saki ba tare da ya ba wa yanayin Abdoul ɗin muhimmanci ba ya ce

"Uhmm." Gyara zama Abdoul ya yi, bayan ya sauke ajiyar zuciya ya ce

"Ka tabbatar?" Jinjina masa kai Tareeq ya yi ba tare da ya ce komai ba. Don haka Abdoul ya ce

"Shi kenan, zan gwada.. Allah Ya ba ni sa'a." Ya ƙare irin a marairaicen nan. Cike da jin daɗin yadda burin ƙanwar tasa ke neman cika ya janyo wayarsa cikin basarwa ya ce

"Bari na soma sanar da ita, don ta fi ɗaukar abin da muhimmanci." Da sauri Abdoul ya riƙo hannunsa yana girgiza kai ya ce

"A'ah kar ka kira ta, kar ya zamana hakan ya koma tirsasawa, gwara ka bar ni da kaina na yi mata magana, na san duk wani abu da ke ranta za ta fito ta faɗa mini ba tare da wani shakku ko tsoro ba, tun da ba zan nuna mata ta hanyarka na biyo ba." Sauke ajiyar zuciya Tareeq ya yi, irin 'Shi kenan toh' ɗin nan, kafin ya ce

"Allah Ubangiji Ya tabbatar da alkhairi. Amma tsaya ka tabbatar ba karɓar tayin nan ka yi saboda mutuncinmu ba? Za ka so ƙanwata kamar yadda nake fatan ita ma za ta so ka? Ka san ba na son a wulaƙanta mini er'uwa." Dariya sosai Abdoul ya yi, kana bayan ya dena ya soma faɗin

"Tareeq manta wane ne kai kake a wajena, ka manta duk wani abu da ya shafe ka dole ne a wajena na so shi? Toh ka manta da wannan son, ba irin shi zan yi wa Sultanah ba, nata na daban ne, matuƙar dai ta amince da ƙudurin da zan je mata da shi." Wani irin sanyi ne ya ji yana ratsa shi, ya lumshe kyawawan idanunsa yana jin har cikin zuciyarsa farin ciki mara misaltuwa. Wato har abada ba zai daina alfahari da kasancewar Abdoul amininsa ba. Fata yake hakan ya zama silar farin cikin er'uwarsa na har abada. Yana fatan hakan ya zama dalilin sake ɗorewar zumuncinsu da su Abdoul na har abada. Yana fatan wannan abu ya zama ɗaya daga cikin abin da zai zama cikin tarihin gidan Iyalan Dikko na sama-sama.


.. Washe gari ma suna tashi da safe a wajen da suka kwana jiya, Ameer ya yi sallama da Daneen ya tafi inda ya sami aikin. Ita kuma ta ci gaba da zama a wajen, saboda gurin ya fi security, kuma babu mutane da yawa, can kuwa maza ne kawai,

Please Login or Register in order to submit comment