Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ina zan fara ba." Sultanah ta faɗa jikinta a matuƙar sanyaye. Gyara zama Hidaya ta yi kafin ta ce

"Kin ga ki fara ko ta ina ne. Na ƙagu na ji me ke damun ki, tun da kuka dawo gida dama na fahimci tabbas akwai abin da ke damun ki." Shiru Sultanah ta yi tana kallan Hidaya ba tare da ta tanka ba. Hidaya ta kamo hannunta ta jinjina mata kai don ba ta ƙwarin gwuiwa.

"Ki sanar da ni." Ta faɗa har lokacin tana kallan ta. Ajiyar zuciya ta sauke, ta lumshe idanunta kana ta buɗe bakinta ta ce a hankali

"Er'uwa ban san yadda za ki ɗauki zancen ba ke kanki, ballantana kuma har in yi wa Yah Tareeq maganar. Amma tabbas na tsinci kaina dumu-dumu cikin ƙaunar Yah Abdoul." Ta ƙare maganar tana jin yadda mikin da ke cikin zuciyarta ke famuwa. Hannunta Hidaya ta zare daga cikin na Sultanah tana kallan ta sosai cike da matuƙar mamaki.

"Yah Abdoul kuma Sultanah?" Jinjina kai Sultanah ta yi a sanyaye, tana jin duk wani ƙwarin gwuiwarta na zagwanyewa, ganin tilon er'uwarta da take saka rai a kanta tana neman watsa mata ƙasa a ido.

"Kar ki zama mutum ta farko da za ki fara ganin laifi na Hidaya don Allah." Sultanah ta faɗa tana kamo hannun Hidaya. Murmushi Hidaya ta yi don saboda kar ta zubar wa da er'uwar tata ɗan ƙwarin gwuiwar da take da shi ta ce

"Ba watsa miki ƙasa a ido zan yi ba Sultanah. Kawai dai abin ne na ji shi tamkar a mafarki, na kuma yi matuƙar mamaki. Amma In Sha Allah zan taya ki da addu'a idan rabon ki ne shi ɗin Ubangiji Ya juyo miki da hankalinsa tun kafin ki sanar da shi. Don ban san ta yadda za mu sanar wa da Yah Tareeq kina ƙaunar Abokinsa ba." Ajiyar zuciya Sultanah ta sauke kafin ta ce

"Ni ma abin da nake tunani kenan Hidaya. Ina tsoron Yah Tareeq ya ji zancen nan, amma ban san yadda zan yi ba. Abin yana damu na matuƙa a cikin zuciyata."

"Ki yi haƙuri Sisi, In Sha Allah komai zai zo da sauƙi."

"Ke! Maganar wa na ji kuna yi?" Maami da ta fito daga cikin ɗaki yanzun ta faɗa tana kallan su, tana sanye cikin doguwar rigar atamfa. Tsananin kamar da suke da Sultanah shi ne zai bayyana maka mahaifiyarta ce. Gaba ɗaya ɗaga kai suka yi suka kalle ta a tsarge. Da sauri Sultanah ta shiga girgiza kai

"Babu komai Maami."

"Anya kuwa?" Ta sake faɗa tana kafe Sultanah da ido, kamar mai son gano gaskiyar abin da take faɗa a kan fuskarta.

"Ehh Maami." Hidaya ta faɗa. Jinjina kai kawai Maamin ta yi, tana wuce wa kitchen ɗin da dama abin da ya fito da ita kenan. Wata gauruwar ajiyar zuciya Sultanah ta sauke kafin ta ce

"Na gode wa Allah." Ta faɗa tana dafe ƙirjinta. Bin ta da kallo Hidaya ta yi, tana mamakin yadda ruɗewar Sultanahn ta yi yawa. Sai dai sanin halin Maamin ya sanya ta girgiza kai kawai.


***
Ɗaga kansa ya yi ya kalli wanda ya shigo office ɗin, ya amsa sallamar yana maida dubansa kan takardun, ba tare da ya kalli abin da ke rubuce a cikin su ba ya haɗa su waje guda. Ƙarasawa Abdoul ya yi ya nemi waje ya zauna shi ma hannunsa ɗauke da wasu takardun.

"Ga waɗannan takardun, duk dai cikin na Diyana ne." Abdoul ya faɗa yana miƙa masa takardun. Ba tare da ya ce komai ba, ya karɓa ya haɗa su waje ɗaya. Ba dan ba dan ba, yanzun nan zai saka wani ya ƙoma masa takardun, sai dai ko ma mene ne, ba ya so komai da ya shafe shi ya fita waje. Don haka bayan ya gama haɗa su waje ɗaya, sai ya nemi waje ya killace su. Sai a lokacin ya mayar da duban sa kan Abdoul ya ce

"Ya ake ciki?"

"Na tura maka komai ta E-mail naka, ka bincika bayanin komai na ciki." Jinjina kai Tareeq ya yi kafin ya ja laptop ɗin da ke gabansa ya shiga dannawa cike da ƙware wa. Kyawawan idanunsa na bin duk wani rubutu da ke bayyana a kan fuskar laptop ɗin, kai ka ce haddace kowacce kalma yake yi, saboda yadda yake bin su cike da takatsantsan da son tabbatar da duk abin da ya gani gaskiya ne.


***
Sosai dare ya sake tsalawa har lokacin suna tafiya, wani lokacin idan sun gaji su nemi waje su zauna. Wani lokacin kuma su cigaba tafiya. Sai dai har zuwa lokacin ba su san takamaimai inda za su je ba. Kuɗin da ya rage a hannunsu dududu bai fi na abincin da za su ci ba, ballantana su yi tunanin komawa ƙauyensu, tun da dai wannan gari Allah Ya masa faɗin da sanin inda Innarsu take kamar ba mai yiwuwa ba ne. I zuwa lokacin ban da kukan tsuntsaye, da motsin ƙalilan ɗin ababen hawa babu abin da kake iya ji. Tsoro da fargaba tuni sun cika zuciyoyin Daneen da Ameer. Musamman ma dai Daneen da ke cigaba da raba ido kamar munafuka.

"Adda wai tafiya za mu yi ta yi, ba za mu nemi inda za mu kwana ba." Ameer ya faɗa yana dakatawa.

"Toh Ameer a ina za mu kwana? Ni na rasa ma mai zance wallahi."

"Kawai mu nemi wani wajen wallahi, kin ga fa titin babu kowa yanzu. Idan ya so gobe sai mu nemi mafita." Cikin na'am da zancen Ameer ɗin Daneen ta gyara zaman jakarta, suka cigaba da tafiya suna kalle-kalle, ko za su samu inda za su yar da haƙarƙarinsu. Lumshe idanu kawai Daneen ke yi, saboda baccin da ke ta kawo mata hari, dalili kenan da ya sanya manyan idanunta suka ɗan taasa kamar waɗanda suke ciwo.

"Bacci kike ji ko Adda?" Ameer ya faɗa cike da kulawa. Jinjina kai ta yi tana kai hannunta saitin bakinta lokacin da ta yi hamma. Ta ɗan runtse idanunta tana sake buɗe su, daidai lokacin da ta jiyo muryar Ameer na faɗin

"Laa Adda kin ga wani waje can wallahi ki zo mu je. Za mu iya kwana abin mu." Ya faɗa yana jin yadda farin ciki ke mamaye ilahirin jikinsa. Inda yake nuna wa ta bi da kallo. Trader ce irin ta mai shayi. Wadda da alama mai ita ba ya zama, ko kuma wani dalili ya hana shi zama yau ɗin. Saboda yadda masu shayi kan kai wa dare, bai ci a ce har ya tashi i yanzu ba. Juya wa Daneen ta yi ta kalli titin da motoci ke cigaba da wuce wa. Kafin ta dawo da dubanta kan trader. Kawai sai ta ji jikinta ya sake yin sanyi. Tabbas da ta san ba za su haɗu da Innarsu ba, ba za ta taɓa yarda su fito daga gida ba ko me Dada za ta musu. Ba ta taɓa tunanin akwai gari mai girman da za a ce kowacce unguwa akwai nasu mai unguwar ba sai yanzu. Ba ta taɓa tunanin ƙaddarar rayuwa kan iya jefo su har suna shirin kwana a kan titi ba. Shin me ya sa ta biye wa Ameer suka fito daga ƙauyensu zuwa wannan garin mai girman da da alama ya ninka ƙauyensu sau babu adadi. Shin me ya sa suka yi wannan gangancin na biyo Innarsu ba tare da sun san takamaimai inda take ba.

"Ki zo mu ƙarasa." Ameer ya faɗa yana jan hannun Daneen, ganin da ya yi da alama ta yi nisa a tunanin da ta tafi. Babu musu ta bi bayansa. Shi ya fara yin gaba, ya yin da ta bi bayansa. Har ciki suka shiga kasancewar babu ƙofa. Sai dai wajen irin keɓantaccen nan ne. Don haka ko da suna ciki babu wanda zai iya ganin su. Karɓar jakar hannunta Ameer ya yi, ya ajje ta gefe, ya sanya hannunsa ya ɗakko rigunansa guda biyu ya shimfiɗa, kana ya kalli Daneen ya ce

"Adda taho ki kwanta." Ya yi maganar lokacin da yake gyara zaman jakarta don ta ji daɗin yin pillow da ita. Kallan Ameer ɗin Daneen ta yi, ba ta san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba. Ƙaunar Ameer a gare ta yawa gare ta, haka zalika ƙaunar ta gare shi tana da yawa. Don ji take tamkar ta fi ƙaunarsa ma a kan yadda take ƙaunar kanta.

"Kai fa?" Ta tambaya tana kallan sa.

"Ki fara kwanciya, ni ma zan kwanta." Ƙarasawa ta yi ta kwanta, zuciyarta cike fall da tunane-tunane. Sai dai abin da ya fi tsaya mata a rai, shi ne yadda za su samu kuɗin motar da za ta maida su ƙauyensu. Sai a lokacin sannan Ameer ya nemi waje shi ma ya yi shimfiɗa ya kwanta.

Sosai dare ya cigaba da tafiya, gari na sake yin shiru, ƙarar kukan tsuntsaye na daɗuwa. Sautin ababen hawa na raguwa. Har zuwa lokacin da motsin su ya ɗauke kwata-kwata.

"Baba yau fa so nake na afa aji garau ɗin nan da yawa, don wallahi so nake na haura hazo na yi ta shawagi ni ɗaya." Sautin da ke fita a daddaƙire, cikin irin muryar en shaye-shaye ta doki dodon kunnen Daneen da baccin nata kwata-kwata bai yi nisa ba.

"Kar ka damu. Ni kaina yau ɗin nan so nake na yi mugun cajin da na daɗe ban yi ba." Wanda suke tare ya faɗa. Lokacin da suke ƙara kusantar trader. Kai tsaye can suka nufa, suka nemi waje suka zauna. Cikin ƙanƙanin lokaci suka baje kayan harkarsu. A hankali Daneen ta tashi zaune, tana jin yadda zuciyarta ke buga wa tamkar za ta faso ƙirjinta. Ta lalubi fuskar Ameer ta taɓa, ta ji bacci yake. Sai ta ɗauke hannun nata tana koma wa ta zauna a kan shimfiɗarta, bugun zuciyarta har wani sauti yake bayar wa 'dif, dif, dif' saboda tsananin tsoron da take ji.

"Kai.. Ni fa kamar motsi nake ji a cikin abar nan." Ɗaya daga cikin su ya faɗa yana ɗan waigawa. Buɗe idanunta Daneen ta yi jin abin da ya faɗa, daidai lokacin da wasu hawaye suka samu damar zubo wa a kan kuncinta lokaci guda.

"Kai ni ma fa kamar na ji. Waye a nan?" Ya faɗa a ɗan tsawace yana kallan cikin trader. Runtse idanunta Daneen ta yi tana karanto duk wata addu'a da ta zo ranta, lokaci ɗaya tana haɗe jikinta waje ɗaya, kanta ɗore a kan cinyarta, zuciyarta na wani irin harbawa, tsoron da tun da uwarta ta haife ta ba ta taɓa jin sa ba na cigaba shigar ta.

"Ya kamata mu duba fa." Ɗayan ya faɗa yana miƙe wa. Shi ma miƙe wa ɗayan ya yi suka shiga takawa zuwa inda su Daneen suke. I zuwa lokacin zuciyar Daneen bugawa ne kaɗai ya rage ba ta yi ba. Kawai sai ta cigaba da addu'a tana miƙa wa Allah lamarinta kawai. Don ba ta san kuma abin da ya kamata ta yi ba bayan wannan.

"Kai! Wallahi kamar mace nake hange a ciki fa. Kar dai a ce yau rabon farka wata yarinya ne ya fito da mu." Wanda da alama ya fi ɗayan tantiranci ya faɗa yana dariya, lokaci ɗaya yana kallan Daneen, hannunsa a kan haɓarsa yana shafawa.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 11

"Ke don tantiranci ma kawo kanki kika yi? Lallai abin zai bayar da citta." Ya ƙare lokacin da ya ida ƙarasa tura kansa cikin wajen da su Daneen suke. Har kuma lokacin shu'uman idanunsa na kanta, yana bin ta da wani kallo kamar tsohon maye. Cikin saurin da ba ta san tana da shi ba, ta miƙe daidai lokacin da ta ida buɗe kumburarrun idanunta a kansa.

"Me ye haka kuma? Ina kike ƙoƙarin zuwa? Maada ƙaraso da gulafarka ciki mana." Shi dai wanda ya soma magana tun farko ya sake faɗa. Kamar cikin mafarki Ameer ya soma jiyo maganganu ƙasa-ƙasa. Babu shiri ya buɗe idanunsa da ke ɗauke da bacci. A kan Daneen ya sauke su lokacin da take zube a kan ƙafafunta, kyawawan idanunta sharkaf hawaye. Tun da Inna-wuro ta haife ta, ba ta taɓa tsintar kanta cikin tashin hankali irin wannan ba.

"Don girman Allah kar ku yi mana komai, ku bar mu mu tafi don Allah. Wallahi ba za mu sake zuwa wajen nan ba, don Allah." Ta ƙare hannayenta biyu a haɗe waje guda. Dariya Maada ya sheƙe da ita, yana kallan Dawa kafin ya ce

"Kaa ji me take cewa fa." Ya faɗa yana nuna Daneen da yatsan hannunsa. A tare suka sheƙe da wata sabuwar dariyar suna kallon Daneen da har lokacin take zaune a kan gwuiwoyinta.

"Bari ka gani." Dawa ya faɗa yana soma sassauta ɗaurin tazugen wandon da ke jikinsa.

"Adda." Ameer ya faɗa yana miƙe wa lokacin da ya gama fahimtar maza har biyu sun shigo cikin trader yana bacci. Ga kuma abubuwan da ya ji suna faɗa. Abin da ya tayar masa da hankali kenan, ya kamo hannun Daneen ya riƙe gam cikin nasa, kafin ya maida dubansa kan su ya ce

"Don Allah ku yi haƙuri." Da mamaki Dawa ya ɗaga ido ya kalli Ameer, don kwata-kwata bai lura da wanzuwarsa cikin wajen ba sai da ya yi magana.

"Maada yi mini waje da wannan wawan, kai ma ka ɗan ba mu waje, idan na gama sai ka shigo ka ɗora." Tun kafin ya ida maganar, Maada ya ƙarasa ya cafki hannun Ameer da niyyar fidda shi daga cikin trader. Ganin da Ameer ya yi da gaske so suke su fitar shi, ya bar su kenan tare da Addarsa? Hakan ne ya sanya shi sake riƙe hannun Daneen gam-gam cikin nasa, ita ma hakan ce ta faru. Duk da yadda ilahirin jikinta ke ɓari, sai ka ce wadda zazzaɓi ke shirin rufe wa, ko kuma ya rufe ɗin ma. Gaba ɗaya ta rikirkice, ta ruɗe, ta rasa abin da ya kamata ta yi. Sai dai har lokacin ba ta dena ambatar sunan Allah cikin ranta ba. Ganin da Maada ya yi Ameer zai ɓata masa lokaci ne ya sanya shi saka hannunsa gaba ɗaya ya soma ƙoƙarin saɓa shi a kafaɗa.

"Ka sake ni, ka sake ni malam. Ka sake ni." Shi ne abin da Ameer ke ta faɗa yana ciccije wa, yana kuma sake riƙe hannun Daneen da ke cigaba da riƙe na shi. Duk inda Maada ya ja shi sai Daneen ta bi shi, don haka kawai ya saɓe shi gaba ɗaya. Daidai lokacin da hannun Ameer da na Daneen ya rabu, ta buɗe duk wata murya da take da ita ta yi wata ƙara, da tunani tare da fatan wani ya ji ya zo ya taimaka musu.

"Ka sake ni, kar ku cutar mini da Addatah. Kar cutar mini da Addatah, kar ku taɓa mini ita. Ka sake ni." Ameer ya cigaba da faɗa lokacin da yake kafaɗar mutumin, yana dukansa da duk wani ƙarfi da ya san yana da shi. Amma ko bi ta kansa bai yi ba, sai cigaba da tafiya da ya yi da shi.

"Toh ke sai ki haƙura ai mu sarara." Dawa ya faɗa yana kallan Daneen da ke kuka kamar ranta zai fita. Tana kuma ƙoƙarin bin inda su Maada suka yi don fice wa daga wajen, amma Dawa ya ƙi ba ta dama. Ganin da ya yi idan ya cigaba da biye mata za ta ɓata masa lokaci ya sanya shi yin kanta gadan-gadan yana ƙarasa zame tazugen wandonsa gaba ɗaya. Wata ƙarar Daneen ta saki cikin dashashshiyar muryarta. I zuwa lokacin ji take zuciyarta na dab da fito wa daga ƙirjinta.

"Wallahi kika sake yi mini wannan ihun za ki ga yadda zan wulaƙantaki cikin daren nan." Dawa ya faɗa a fusace, don tsoro yake ji kar garin ihun nan nata ta tona musu asiri tun kafin su shana. Kwalar rigarsa da ya ji an kama babu zato babu tsammani, ita ce ta sanya shi dakatawa cike da mamaki. Ya san babu yadda za a yi Maada ya yi masa haka, shi ya sa ya yi mamaki, sai ya ɗaga kai ya kalli wanda ke riƙe da kwalar rigar tasa har lokacin. A cikin idanunsa ya sauke nasa idanun. Cike da mamaki ya gyara tsayuwarsa

"Waye kai?" Ya faɗa cikin ƙarfin hali. Murmushin takaici Tareeq ya yi kafin bai ce komai ba ya ja Dawa ta hanyar jan kwalar rigarsa zuwa waje.

"Malam me ye haka ne?" Ya faɗa cikin muryar nan tasa da ta jiƙu da shaye-shaye. Karo na farko da ya buɗe baki, bayan ya kalli Abdoul da ke tsaye a wajen ya ce

"Ba shi ɗaya ba ne, ina iya jin sautin murya daga baya. Taimaka ka taso ƙeyar kowaye mu miƙa su." Iya abin da ya faɗa kenan, har lokacin bai saki Dawa da ke cigaba da kallan sa ba. Amsa wa Abdoul ya yi yana yin gaba. Daidai lokacin da Dawa ya soma faɗin

"Ka san wani abu Boss? Ka yi haƙuri ka rufa mana asiri kar ka miƙa mu wajen kwalawa. Wallahi tallahi babu abin da na yi wa yarinyar mutane. Dama razanarwa ce kawai ehh ka gane ai. Ban da haka babu wani abu. Ba na son haɗuwa ta da kwalawa ko kaɗan, muna da case da su dama. Ka yi haƙuri ka mini afuwa ka bar ni na je, ba ma za ka sake gani na a arear nan ba." Ya ƙarasa maganar daidai lokacin da Abdoul suka ƙaraso da su Maada da Ameer. A guje Ameer ya ƙarasa ya rungume Daneen, a ruɗe yana faɗin

"Babu abin da ya same ki ko Adda? Babu abin da ya same ki?" Ya faɗa shi kansa jikinsa ko'ina rawa yake. Rungume shi ta yi, ko ta ji sauƙin abin da take ji cikin zuciyarta. Ta shiga jinjina kai har lokacin hawaye ba su dena sintiri a kan fuskarta ba.

"Taso mu tafi Adda, ba za mu sake kwana a wajen nan ba. Taso mu tafi." Ameer ya faɗa bayan ya miƙe, yana riƙo hannunta. Ita ma miƙewar ta yi, tana saka hannunta ta goge gefen fuskarta.

"Ki dena kukan toh kin ji?" Ameer ya faɗa cike da kulawa. Jinjina kai ta yi tana jin zuciyarta na sake karye wa. Sai dai ba ta bari hawayen sun zubo ba. Ta saka hannu ta ɗauki jakarta, shi ma tasa ya ɗauka bayan ya tura kayansa ciki kafin suka fito. Suna tsaye su biyu, Tareeq na daga baya, ya yin da Abdoul ke gaba. Da alama dama inda suke ya nufo. Ɗaga ido suka yi suka kalle su kafin suka ɗauke.

"Ina za ku je?" Abdoul ya tambaya yana kallan su sosai don fahimtar su. Shiru suka yi kamar masu tunani. Kafin Daneen ta gama tsara abin da za ta faɗa Ameer ya ce

"Gida."

"Kuna da gida mai ya kawo ku nan?" A wannan karon Tareeq ne ya yi maganar yana kallan su sosai, duk da ba ya iya ganin takamaimai ya fuskarsu take, saboda ƙarancin hasken da aka samu a wajen yanzu ba kamar ɗazu ba.

"Wuce wa muka zo yi. Mun je unguwa shi ne muka yi dare." Ameer ya sake faɗa. Cigaba da kallan sa Tareeq kawai ya yi, sai dai bai ce komai ba.

"Ko ma ina ne kuka je ku dena kai wa dare haka, kuna ganin gari ya yi shiru haka, babu kowa. Ga ɓata gari sun yi yawa. Yanzu ga shi kuna gani ba don Allah Ya taƙaita ba, da sai dai Allah Ya tsare. Ku din ga kula, kai wa dare a waje ba na 'ya mace ba ne." Abdoul ya faɗa. Jinjina kai kawai suke yi kamar wasu ƙadangaru, ita dai Daneen ko ɗaga ido ta kasa yi ballantana ta kalle su. Sai a lokacin Tareeq ya gyara tsayuwarsa, ya kalli Abdoul ya ce

"Ka ɗauke su ka kai su gida please, na kira Nuhu yana jira na." Ya ƙare yana kallan Abdoul, kafin a karo na barkatai ya sake kallan Ameer. Sai dai har lokacin bai sake ce masa komai ba, suka yi sallama da Abdoul ya wuce.

"Ku wuce in kai ku gida." Abdoul ya faɗa yana kallan su. Babu musu suka yi gaba, kamar da gasken suna da gida. Har inda motarsa take suka ƙarasa, ya buɗe musu suka shiga, kafin ya tayar da motar. Shiru kawai Daneen da Ameer suka yi jin yadda motar ke tafiya tamkar ba a kan titi ba. Ameer ya kalli gefen su, don sake tabbatar da da gaske a kan titi suke tafiya ba wani wajen ba.

"Mai ya sa ba ka bari mun ce masa ba mu da gida ba, ka sani ko ya samar mana aikin da za mu yi mu samu kuɗin da za mu koma ƙauyenmu." Daneen ta faɗa ƙasa-ƙasa tana kallan Ameer.

"A'ah.."

"Wacce unguwar ce?" Abdoul ya katse wa Ameer maganar da ya fara. Sai kuma idanunsu ya yi tsilli-tsilli, suka kalli juna cikin rashin sanin abin yi.

"A kan titin nan ne ai." Daneen ta yi ƙundunbalar faɗin hakan jikinta a matuƙar sanyaye. Cigaba da driving ɗin ya yi har zuwa lokacin da Daneen ta sake yin ƙarfin halin faɗin

"Ya isa haka, nan ne." Ta faɗa ƙirjinta na wani irin bugawa. Sauka ya yi daga kan titin, kafin ya ce

"Bari na ƙarasar da ku." Ya faɗa yana shiga cikin layin da ta nuna masa. Daga ita har Ameer sai da cikinsu ya ɗuri ruwa. Amma haka suka yi shiru, suka cigaba da rarraba ido kamar shege a rabon gado.

"Ya isa haka, mun gode." Daneen ta faɗa cikin sanyin muryar nan tata da ta sake yin sanyi matuƙa. Jinjina kai ya yi yana tsaida motar, suka sauka bayan sun yi masa godiya sosai.

"Babu komai." Ya faɗa yana murmushi.

"Allah Ya saka da alkhairi." Daneen ta sake faɗa a karo na barkatai. A wannan karon murmushi kawai ya yi, ba tare da ya ce komai ba. Ya bi su da kallo lokacin da suka shige wani waje da ke nuni da gidan da suka nufa nan suke ƙoƙarin shiga. Sai a lokacin ya tayar da motarsa ya bar wajen.

Ajiyar zuciya Ameer ya sauke kafin ya ce

"Addaneen."

"Na'am." Ta faɗa tana kallan sa.

"Allah Ya taimake mu, amma yanzu ya za mu yi?" Ya tambaya a dame. Kallan inda suke ta yi na tsawon sakanni, kafin ta ce

"Kawai mu zauna a nan zuwa gobe mu nemi aikin da za mu samu kuɗin koma wa gida. Ni ba na son garin nan, kwata-kwata bai yi mini ba. Ba na son shi." Daneen ta ƙarasa maganar tana lumshe kyawawan idanunta. Kallan jar fuskarta da ko'ina na jikinta ya yi jajir Ameer ya yi kana ya ce

"Ni ma haka, ba na so. Ina so mu koma ƙauyenmu kafin Inna ta dawo. Na yi kewar ta, ina so in gan ta." Ba ta san lokacin da murmushi ya ƙwace mata ba. Ta nemi waje ta tsuguna, tana tunanin ta inda za su fara.

Cikin ikon Allah tun da suka zauna a wajen, babu wanda ya fito daga cikin gidan da suke zaune a ƙofarsa, ko kuma wani ya zo wuce wa. Musamman da yake gidan ba a waje yake sosai ba, an yi wasu en dabaru wajen kare shi. Hakan ne ya sa suka zauna a nutse, sai dai fa bacci babu shi babu alamar sa. Suna nan zaune har aka kira sallahr Asuba. Ameer ne ya samo musu famfo suka je suka yi alwala, suka dawo suka yi sallah a wajen, kafin suka cigaba da zama. Lokacin da gari ya ida buɗe wa, sosai Daneen ta shiga buɗe idanunta tana kallan irin gidajen da ke zagaye da su. Gidaje ne waɗanda ba ta taɓa tunanin akwai su a gaske ba. Gidaje ne maka-maka, haɗaɗɗu na gani na faɗa, waɗanda ba ta taɓa ganin irin su ba.

"Kin ga wancan Adda." Ameer ya faɗa yana nuna mata wani gidan da shi ma ya gaji da haɗu wa.

"Kuma gidan ne fa da gaske koh?" Ta tambayi Ameer a sakarce. Sai da juya ya kalli bayansu kafin ya ce

"Toh mu gwada buga wannan mana sai mu tabbatar." Riƙo hannunsa ta yi da sauri tana girgiza kai

"A'ah babu ruwa na wallahi."

"Ba sai mu ce aiki muke nema ba, idan za su ba mu kin ga ai sai mu yi mu samu kuɗi." Ya ƙare maganar yana murmushi. Shiru Daneen ta yi kamar me tunanin wani abu, kafin ta sake ɗaga kai ta kalli gidan.

Please Login or Register in order to submit comment