Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta yi ba ta da ra'ayi a kai. Don ita dai haka kawai ta ji haɗin bai kwanta mata ba. Musamman kuma da ta san halin Tareeq ɗin. Ga kuma abin da ya faru.

"Amma me ya sa ba ki samu Yayanki ko Dadaji kin mata maganar ba?" Murmushi Momy ta yi kafin ta ce

"Ke fa ke ce mahaifiyar Tareeq. Ke kika fi dacewa na fara tuntuɓa da wannan maganar. Idan har ke kika fara masa maganar zai fi ɗaukar ta da muhimmanci. Kin fi kowa sanin halin ɗanki shi ne dalili."

"Toh shi kenan, Ubangiji Ya zaɓa abin da ya fi zama alkhairi."

"Ameeeeen.." Momy ta faɗa tana jan Ameen ɗin cikin farin ciki.


... A nutse ta ƙarasa fitowa daga cikin ɗakin jikinta a matuƙar sanyaye. Don haka kawai ta ƙi jinin kiran Dada, domin da wuya idan na alkhairi ne. Ƙarasawa ta yi ta nemi waje ta zauna cikin ladabi ta ce

"Dada ga ni." Ƙarasa abin da take Dada ta yi, kafin ta dawo ta nemi waje ta zauna gefen Baffa ta ce

"Toh ke sai ki fara shiri, domin kuwa mun yi miki miji. Miji ya zo, Baffanki ya gan shi ya masa, ni ma kuma na gan shi ya yi mini. Don haka gobe zai zo ki je ku gaisa. Ba wani da yawa za a saka ba, cikin ƙanƙanin lokaci za a yi komai a gama." Dada ta faɗa maganar tamkar da ita mutumin da ya zo suka yi magana. Tun lokacin da Dada ta ambaci miji ta ji zuciyarta ta buga. Ba ta tsaya ba, sai cigaba da bugawa da ta yi. Ta runtse idanunta tana tuna lokacin da suka gabatar mata da Alhaji Baita a matsayin mijin da za ta aura. Daga zuwa siyar nono. Ba tare da sanin waye shi ba. Mene ne asalinsa, su waye iyayensa duk ba su sani ba. Haka kawai suka ɗauke ta suka ba shi don kawai ya yi musu ɓarin kuɗi. Toh idan kuma shi ma wannan ɗin halinsa ɗaya da Alhaji Baitan fa? Abin da ya fara zuwa kwanyarta kenan, tana jin wani sabon tashin hankalin na ziyartar ta. Duk wani tunaninta, burinta, da duk wani fatanta ba ya wuce a kan inganta rayuwar 'ya'yanta. Toh idan dai har suka ce ta yi aure yaya rayuwar 'ya'yanta za ta kasance? Ko kuwa wanda suka sake zaɓar mata a karo na biyu zai yarda ya riƙe 'ya'yanta? Tunanin nata ya katse ne, lokacin da hayaniyar da ake a waje take sake kusanto gidansu.

"Ɓarawo, Ɓarawo.." Shi ne abin da kafatanin mutanen ke faɗa cikin ɗaga murya. Haka nan kawai ta ji ƙirjinta ya sake bugawa a karo na barkatai. Daidai lokacin da aka soma buga ƙofar gidan da ƙarfi, wanda ke bugawa ɗin yana faɗin

"Ina mutanen gidan suke ne? Ku fito tun kafin in ba wa mutane umarnin shigowa su muku rashin mutunci wallahi. Ku fito na ce.." Ya ƙare maganar yana sake dukan ƙofar kamar wanda ze jijjige ta. Kusan a tare dukansu suka miƙe. Daneen ma da ke cikin ɗaki ta yo tsakar gidan babu shiri. Gaba ɗaya suka nufi ƙofar gidan don ganin abin da ke faruwa, ko kuma ma ya farun..

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 07

__ Dandazon mutanen da ta gani a ƙofar gidan nasu, shi ne abin da ya sake tsinkar mata da gaba. Ta runtse idanunta tana ambaton sunan Allah, lokaci ɗaya tana buɗe idanun, a daidai lokacin da ta sauke idanunta a kan Habule da ke riƙe da kwalar rigar Ameer. Ya cukwuikuye ta kamar wanda ke shirin zame ta daga jikinsa.

"Ɓarawo." Kunnenta ya sake tsinto mata wannan kalmar.

"Ya isa haka.." Mutumin da ke riƙe da kwalar rigar Ameer ya faɗa bayan ya yi amfani da hannunsa wajen alamta musu abin da ya faɗa. Kamar dama shi ya saka su, sai kuwa suka yi shiru.

"Ameer." Daneen ta faɗa idanunta da take suka sauya a kan Ameer, ban da lugude babu abin da zuciyarta take.

"Na shiga 3 ni Hanne.. Me kuma ya faru?" Dada ta faɗa har da dafe ƙirji kamar gaske.

"Na san zuwa yanzu kun fahimci abin da ya faru. Yaron nan ya yi mini satar zogale. Ni kuma wallahi ba zan haƙura ba, don haka zuwa na yi a biya ni kuɗin abin da ya tsinkar mini." Habule ya faɗa yana gyara tsayuwarsa. Tun da suka zo wajen kwata-kwata Ameer ya kasa ko da ɗaga idanunsa ne ballantana ya kalli mutanen da ke tsaye a wajen. Shi kaɗai ya san yadda kalaman da ake faɗa suke sukar zuciyarsa. Ya rasa abin da ze yi, ya rasa ya ze yi. Be san cewa mutane da dama ƙiris suke jira a kansu ba sai yanzu, sai da abin nan ya faru.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Ameer! Yanzu nan sai da ka nuna halinka a waje? Sata da farar ranar nan? Oh jama'a.. Jinin Hadeeza sun shiga 3." Dada ta yi maganar tana tafa hannu. Babu shiri Ameer ya ɗaga idanunsa ya kalli Dada, cike da mamakin maganganun da suke fito wa a bakinta. Cikin sauri kuma sai ya mayar da idanunsa kan Inna-wuro da ta runtse idanunta cikin rashin sanin abin yi. Girgiza kai ya shiga yi tamkar tana kallansa

"A'ah Inna, kar ki yarda da abin da suke faɗa, wallahi ban yi masa sata ba. Ɗansa ne ya ce mini in je in tsinka tun da ban samu na siyarwa ba. Inna kar ki yarda, wallahi ban yi masa sata ba Inna." Ya ƙare maganar gwanin ban tausayi. Shi gaba ɗaya abin da mutanen ke masa be dugunzuma masa hankali ba kamar tsoron ka da Innarsa ta yarda da abin da suke faɗa.

"Dallah rufe mana baki ɓarawon banza ɓarawon wofi." Wani da ke gefen Habule ya faɗa yana tunkuɗa masa ƙeya. Ya tafi kamar ze kifa kafin ya dawo a kan ƙafafunsa. I zuwa lokacin zuciyarsa ta yi taurin da yake ganin ba ze iya jure wannan cin mutuncin ba. Wani irin zafi zuciyarsa take masa, ji yake kamar ya fasa ihu ko ze ji sauƙin abin da yake ji. Don haka a fusace ya juya ya cakumi wuyan wanda ya tura shi yanzun. Cikin ƙanƙanin lokaci maganar mutane ta soma tashi a wajen, kowa da abin da yake faɗa. Tuni ya ƙwace jikinsa daga hannun Habule. Kamar yadda ya cakumi wuyansa, haka shi ma wancan ɗin ya cakuma, suna shirin soma faɗan ya ji an riƙo hannunsa. Cakk ya dakata, ya ɗaga idanunsa ya sauke a kan fuskar Inna da ta riƙe hannunsa. Ta girgiza masa kai a sanyaye, muryarta ma a sanyaye ta furta

"Rabu da shi.. Allah zai saka maka." Ta ƙare maganar tana jan hannunsa. Babu musu ya sake shi, har lokacin yana jin yadda zuciyarsa ke cigaba da wani irin zafi, gefe guda kuma wani rauni ne a cikinta. Ganin da Habule ya yi Inna-wuro ta ja hannun ɗanta ya sanya shi saurin faɗin

"Ina za ku je ba tare da kun.."

"Daneen ɗakko kuɗi ki ba shi." Maganar Inna-wuron ta katse masa maganar da ya soma. Ya ja ƙwafa yana faɗin

"Ah toh." Kusan a tare suka shige gidan su ukun, har lokacin Inna-wuro na riƙe da hannun Ameer.

"Don Allah ka yi haƙuri, ka san halin 'ya'yan yanzu.. Ka yi haƙuri amma tabbas zan tsawatar masa, ta yadda ba zai sake marmarin ɗaukar abin wani ba." Maganar Dada kenan, wadda ta sauka a kunnen Daneen lokacin da ta fito daga cikin gida, hannunta ɗauke da kuɗi ta miƙa wa Habule, ba ta jira ya ce komai ba ta koma cikin gidan tana cigaba da tariyar kalaman Dadan.

"Babu komai." Habule ya faɗa lokacin da yake ƙirga kuɗin hannunsa.

"Ka yi haƙuri." Baffa da tun ɗazun be ce komai ba ya faɗa yana kallan Habulen. Jinjina kai Habule ya yi yana kallan mutanen da suka biyo shi ya ce

"Ku wuce mu je." Duk sai suka ɗunguna suka bi bayansa. Dada da Baffa suka bi bayansu da kallo har sai da suka ɓace musu da gani. Ƙwafa Dada ta ja ba tare da ta ce komai ba ta shige cikin gida, babu daɗe wa Baffa ma ya bi bayanta zuwa ciki.

A ɗaya ɓangaren kuwa, a sukwane Daneen ta nemi gefen Ameer ta zauna, yana zaune kansa ɗore a kan gwuiwarsa. A hankali ta kai hannunta ta dafa kafaɗarsa, cikin sanyi ta ce

"Ɗan'uwa." Runtse idanunsa ya yi kafin ya buɗe, ya ɗago a hankali ya kalli Daneen. Girgiza mata kai ya shiga yi yana jin yadda zuciyarsa ke karyewa.

"Adda wallahi ba sata na yi masa ba." Ya ƙare yana riƙo hannunta. Idanunta da suka cika taff da hawaye ta lumshe tana buɗe wa a lokaci guda. Sai ta shiga jinjina kai tana riƙe hannunsa sosai.

"Na sani Ameer.. Inna ma ta sani, ka dena damun kanka."

"Amma kin ji abin da Dada ta faɗa koh? Tun da nake na taɓa sata a rayuwata ne? Me ya sa ne muke rayuwa a cikin gidan nan Adda? Babu wanda ke sonmu fa sai mu kanmu. Ni ba ɓarawo ba ne Adda. Wallahi ba ɓarawo ba ne ni." Ya ƙare yana fashe wa da kuka. Sai a lokacin kukan da ita kanta Daneen ɗin ke riƙe wa ya fito fili, ta ja Ameer jikinta ta rungume ita ma tana fashe wa da kukan.

"Ya isa haka Ameer.. Ya isa haka.." Ta yi ƙarfin halin faɗa. Cigaba da girgiza kai ya yi, don tabbas abin da ya faru ya masa zafi, kukan da yake shi ne kaɗai zai sanyaya masa zuciya. Ita ma Daneen ɗin ba ta hana shi ba, ta bar shi ya yi kukan, dan ta san hakan zai taimaka wajen rage raɗaɗin da yake ji a zuciyarsa.

"Ku dena kuka In Sha Allah, Allah zai kawo mana mafita nan ba da daɗewa ba." Inna ta faɗa tana haɗa su su duka ta rungume. Ba ta so ta bar wata alama da zai sa su fahimci ita ma tana cikin damuwar. Sai dai za ta iya cewa abin da take ji cikin zuciyarta ya fi wanda suke ji. Ita kaɗai ta san abin da take ji a duk lokacin da kalmar 'ɓarawo' ta faɗo mata cikin rai. Mummunar kalmar da aka jefi ɗanta da shi. Mummunar kalmar da mutane da dama suka kira ɗanta da shi. Kawai sai ta runtse idanunta tana jin yadda Ameer yake sauke ajiyar zuciya cikin ƙunar rai. Lallai yau ɗin tabbas abin ya taɓa zuciyar Ameer, tun da har yake kuka, duk kuwa da ƙarfin zuciya irin nasa duk da ƙananun shekarunsa.

Ranar dai haka suka wuni babu walwala. Cikin sa'a kuma ita ma Dada sai ba ta kula su ba. Ta cigaba da harkokinta daga tsakar gida zuwa cikin ɗaki.

Washegari da ta kasance babu makaranta bin Innar suka yi kasuwa. Ba su suka dawo gidan ba sai da yamma. Har kuma zuwa lokacin Ameer be koma daidai ba. Daneen da Inna-wuro ke ta ƙoƙari wajen ganin sun kwashe damuwar da ya ɗora wa kansa.


... "Kin sanar da shi kin amince?" Tambayar da Dada ta jefa mata kenan tun kafin ta ida shigo wa soron gidan. Gaba ɗaya sai ta ji jikinta ya yi sanyi, ta girgiza kai kafin ta ce

"Na sanar da shi zan yi shawara, sannan kuma na nemi zaɓin Ubangiji." Inna-wuro ta faɗa a sanyaye, cike da fatan Dadan ta amince da hakan, ko dan kasancewar yanzu ba kamar da ba ne. Tun da yanzu da hankalinta ba kamar da ba.

"Toh ki koma ki sanar da shi kin amince.. don wallahi ba shawararki muke nema ba, umarni ne muke ba ki. Ki koma ki sanar da shi kin amince, ko kuma yau ɗin nan wallahi ki ga abin da zan muku cikin gidan nan, babu ruwa na da wasu 'ya'ya da kika tara wallahi ci miki mutunci zan yi." Dada da ke dab da soro ta faɗa tana maka mata harara. Girgiza kai Inna-wuro ta yi ta ce a sanyaye

"Dada.."

"Ka saka baki Malam.. Wallahi ba kirki ne da ni ba, ka da ki ɓarar mana da wannan damar." Dada ta faɗa tana kallan Baffa da ke zaune a tsakar gidan. Ɗaga idanunsa ya yi ya kalli Inna-wuro ya ce

"Kin ga maza koma ki sanar da shi kin amince. Mun riga mun zaɓa miki shi, babu buƙatar wani tunani kuma." Duk da yadda zuciyarta ke bugawa hakan be hana ta juya wa ba, ƙafarta har wani rawa take lokacin da ta bi umarnin mahaifinta wajen koma wa wajen mutumin. Har ya shiga cikin motar ya tayar da ita, ya hangi Inna-wuro da ta fito. Sai ya kashe motar cike da mamakin abin da ya fito da ita bayan sun yi sallama. Kai tsaye inda take tsaye ya nufa yana kallan ta.

"Ina so mu yi wata magana." Inna-wuro ta faɗa jikinta a matuƙar sanyaye. Ita kam ta rasa wannan wace kalar rayuwa ce. Ta rasa mafita a rayuwarta. Tana so ta inganta rayuwar 'ya'yanta, sai dai da alama Dada tana so ta yi mata cikas. Maimakon a ce yanzu haka maganar auren 'yarta ake, amma wai nata ake. Ba ta san dalilin Dada na saka mata ido ba. Ba ta san me ye ƙudurin Dada a kanta na son sai ta yi aure ba.

"Ikon Allah! Ina sauraron ki." Alhaji Abubakar ya faɗa yana gyara tsayuwarsa. Sauke numfashi Inna-wuro ta yi tana tunanin ta inda za ta fara. Sai dai kawai ta yi ƙundunbala wajen soma faɗin

"Ina da 'ya'ya guda biyu.. Ina neman alfarmar idan dai har za ka aure ni ka bar ni na taho da su. Ni ba zan ɗora maka komai ba. Ni zan din ga musu komai da ake buƙata, ni dai buri na kawai ka amince na zo da su gidanka." Cikin matuƙar farin ciki ya ce

"Kina nufin idan dai har na amince da hakan kin amince za ki aure ni?" Runtse idanunta Inna-wuro ta yi, kafin ta shiga jinjina kanta a sanyaye. Murmushi ya yi, har cikin ransa yana jin daɗi. Ya buɗe baki a nutse ya soma faɗin

"Ni da ba ki guje ni ba duk da ina da 'ya'ya, kika kuma amince za ki kula da su, mai zai hana ni ma na kula da naki? Idan dai har kin amince da aure na, ni mai iya haɗa 'ya'yana da naki ne na kula da su In Sha Allah." Wani irin sanyi ta ji yana ratsa zuciyarta. Farin cikin da ta daɗe ba ta tsinci kanta a ciki ba yau ta ji shi. Har ba ta san lokacin da wani irin sassanyan murmushi ya suɓuce a kan fuskarta ba. A kan laɓɓanta ta furta

"Alhamdulillah." Ta buɗe idanunta a nutse ta kalli Alhaji Abubakar ta ce muryarta na bayyanar da farin cikin da take ciki

"Na amince. Allah Ya tabbatar da abin da yake alkhairi a gare mu." Ta ƙare maganar tana lumshe idanunta, a ranta tana fata hakan ya zame mata alkhairi, kamar yadda take fata. Ko ma wane irin hali ne da Alhaji Abubakar ɗin, idan dai har tana tare da 'ya'yanta za ta ji sauƙi. Ta kuma san In Sha Allah Allah zai taimake ta, ya taimaka mata wajen kula da rayuwar 'ya'yanta.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 08

Kusan a tare suka sauko daga cikin motar. Dukkansu fuskarsu ɗauke da annurin da ke bayyana farin cikin da suke ciki. Hidaya ce, sanye cikin doguwar rigar da ta matuƙar amsar jikinta, ta kuma haska kyakkyawar farar fuskarta mai kama da Tareeq. Gefen ta wata budurwar ce, wadda a kallan farko za ka iya kiran su da sa'anni. Ko ma kai tsaye ka kira Hidaya da babba saboda yadda ta fi Sultanah cika ido. Sai dai a zahiri Sultanah ta ba wa Hidaya kusan shekaru biyu ne, wanda a ido ba za ka taɓa faɗa ba idan dai har ba faɗa maka aka yi ba. Uwa uwa kuma yadda suke abubuwan su tare, suke komai tare, kai tsaye idan ba ka kira su da tagwaye ba, za ka kira su da sa'annin da suka fito daga gida ɗaya.

"Na yi matuƙar kewar gida." Sultanah ta faɗa tana murmushi. Ita ma Hidaya murmushin ta yi kafin ta ce

"Ki bari kawai Sisi, shi kansa gidan ya yi kewar ki." Ta ƙare dimple ɗin da ke gefen kumatunta na lotsawa. Daidai lokacin da wata babbar mace sanye cikin wata hamshaƙiyar atamfa ɗinkin bubu ta fito daga cikin motar da su Hidaya suka fito daga cikin ta. Kunnen ta kare da waya tana amsa wa. Idanunta saye cikin glass, hannunta kuma ɗauke da jakar da ke ɗore a tsintsiyar hannunta. Ba tare da ta dubi inda 'yan matan ke tsaye ba, kai tsaye ta wuce sashenta tana cigaba da amsa wayar.

"Sultanah bari na je, ki fara zuwa ki huta yanzun dai." Hidaya ta faɗa tana kallan Sultanah. Girgiza kai ta yi kafin ta ce

"A'ah ni kam.. Sai na fara zuwa na gaishe da Dadaji, tun da dai yanzu haka Abeey ba ya cikin gidan nan." Dariya Hidaya ta yi kana ta ce

"Toh shi kenan mu je." Daga haka suka maida akalarsu zuwa sashen kakar tasu. Daidai lokacin da Tareeq da Abokinsa Abdoul suke dab da ƙaraso wa wajen. Ƙirjin Sultanah ya buga, ta runtse idanunta tana ambaton sunan Allah. Daidai lokacin da suka ƙaraso.

"Yah Tareeq." Hidaya ta faɗa kyakkyawan murmushin nan da ke ƙara wa fuskarta kyau kamar koyaushe yana kan fuskarta.

"Da alama shi kaɗai kika gani?" Abdoul ya faɗa yana kallan Hidaya, lokaci ɗaya yana ɗage girarsa. Dariya kawai ta yi tana gaishe da Abdoul ɗin.

"Yah Tareeq barka da wannan lokacin." Sultanah ta faɗa tana jin kewar yayan nata.

"Barka sweetsis.. Kin dawo lafiya?" Jinjina kai ta yi kafin ta ce

"Eh, na yi kewar ka sosai." Ta faɗa kawai, dan ta so ba a gaban abokinsa ba ne, da hugging nasa za ta yi. Sassanyan murmushi ne ya tashi a kan fuskarsa kana ya amsa da

"Missed you more Sulty." Sai a lokacin sannan ta maida duban ta kan Abdoul ta gaida shi. Tun da ta masa kallo ɗaya ba ta sake bari ta kalle shi ba. Don kwata-kwata ba ta iya jure kallan nasa. Daga haka ba su ƙara mintuna masu yawa ba, Sultanah da Hidaya suka yi sashen Dadaji, ya yin da Tareeq da Abdoul suka wuce.

Tun kafin su ƙarasa shiga ta tafi a guje tana faɗin

"Dadaji tawa." Ta faɗa tana rungume tsohuwar da ke zaune a kan lallausan carpet ɗin da ke malale a tsakiyar ɗakin.

"Oh ni ɗiyar babana, yau ga Sultanah na neman karya ni." Ta ƙare tana yamutsa fuska.

"Kai Dada tsananin kewar ki da na yi ne fa." Sultanah ta ƙare tana turo baki.

"Eh dole ai ki yi kewa ta mana.. Ke ni ba wannan ba, tun da dai yanzu Allah Ya dawo mini da ke lafiya, maza tashi ki shiga kitchen."

"Kai Dadaji daga dawowa ta?" Ta ƙare tana waro ido. Taɓe baki Dadaji ta yi ba tare da ta ce komai ba. Sultanah ta sake faɗin

"Ga Hidaya nan da babu gajiyar komai a tare da ita."

"Ni! Raba ni da wannan malalaciyar." Dadaji ta ƙare tana auna wa Hidaya harara. Dariya Hidaya ta yi tana faɗin

"Toh shi kenan ki bari Sulty ta shiga tsakaninmu. Ni dai babu ruwa na." Ta ƙare tana gyara zamanta. Dariya Sultanah har ma da Dadajin suka yi jin abin da Hidaya ta faɗa.


... A ɗaya ɓangaren kuwa cikin ƙanƙanin lokaci aka tsaida ranar auren Inna-wuro da Alhaji Abubakar. Babu daɗewa Inna-wuro ta sanar da su Daneen canjin da suke ƙoƙarin samu, na barin ƙauyen gaba ɗaya zuwa can wani waje su rayu. Farin ciki kamar su taka rawa haka suka ji. Ko babu komai za su rabu da Dada. Matar da zuwa yanzun suka sake fahimtar kwata-kwata ba ta ƙaunar su, ba ta son duk wani abu da ya shafe su. Musamman ma dai Ameer da tun da abin nan ya faru ya ɗauki gaba da Dadan. Sai da Inna-wuro ta fahimci abin da ke faruwa sannan ta tsawatar masa. Shi ne ya sassauta saboda gudun ɓacin ran Innar tasu.


A ƙofar gidan ya yi parking na matarsa, kamar kodayaushe sanye cikin shadda ɗinkin babbar riga. Bai kai minti 3 da tsayuwa ba, Baffa ya fito daga cikin gidan.

"Ƙaraso ciki mana, ai yanzu ka tashi daga ɓako ka zama ɗan gida. Kwana nawa ne ya rage?" Baffa ya ƙare maganar yana murmushi. Shi ma murmushin Alhaji Abubakar ya yi kafin ya gaishe da Baffan cikin girmamawa. Ya amsa yana yin gaba don ba wa Alhaji Abubakar damar shiga gidan. Babu musu ya bi bayansa, cikin ransa yana saƙa lallai ko ma mene ne dalilin kiran nan nasa yana da matuƙar muhimmanci, tun da har aka umarce shi da shiga cikin gidan. A soro suka dakata, Baffa ya nuna masa wata tabarma ya ce

"Bismillah." Babu musu Alhaji Abubakar ya tuɓe takalmansa, ya nemi waje ya zauna bayan ya tattare babbar rigarsa. Baffa da takaimaimai bai san dalilin kiransa ba ya shiga gidan don kiran Dada. Tun kafin ya ƙaraso ta ce

"Mu je, ai na shirya ma." Ta faɗa tana gyara zaman gyalen da ta yafa a kanta, sai dai gaba ɗaya ta kwashe shi zuwa kan kafaɗarta, har rigar jikinta ana gani. Babu musu ya juya, ya bi bayanta, don har ta riga shi fita.

Da mamaki shimfiɗe a kan fuskar Alhaji Abubakar yake kallan Dada, ƙwarai da gaske ya yi mamakin ganin ita ke son magana da shi. Duk da tun bayan da ya ya soma zuwa wajen Inna-wuro ya soma fahimtar halayenta. Amma duk da haka bai yi ƙasa a gwuiwa ba wajen gaishe ta cikin girmamawa.

"A'ah lafiya ƙalau Alhamdulillahi. Wallahi mun gode Allah." Ta faɗa tana gyara zama. Kafin ya ce komai ta cigaba da faɗin

"Dama abin da ya sa na kira ka.. Ba wata doguwar magana ba ce. Magana ce a kan 'ya'yan Inna-wuro da na ji ka ce za ka riƙe. Toh ka san yanzu yadda rayuwar nan ta sauya, 'yan gulma sun yi yawa. Sai a dinga gulmar ko ma dai mata biyu ka aura ne ba ɗaya ba. Toh saboda gudun hakan ya sa na ce bari na faɗa maka.. Idan har niyyar kula da su ka yi, ni ɗin nan kakarsu ce, zan iya kula da su fiye da yadda kake tunani. Idan ya so duk wata sai ka dinga yo aiken abin da za a kula da su. Ai hakan ba wani abu ba ne." Ta ƙare tana dariya gami da gyara zama. Shiru Alhaji Abubakar ya yi na tsawon wasu sakanni yana nazarin maganganun Dadar. Kafin can ya ce, bayan ya sauke ajiyar zuciya

"Babu komai Baba. Ni ma ina da 'yan matan har guda biyu, shi ya sa ma nake so na haɗa su waje ɗaya. Hakan ba abin damuwa ba ne. Zan kula da su idan babu damuwa."

"Toh! Ikon Allah!" Dada ta faɗa a wani sheƙe tana kallan Alhaji Abubakar. Ji take kamar ta tashi ta rufe shi ta tsinannan duka ko ta ji daɗi. Sai dai kafin ta ida tsara abin da ke cikin ranta ta jiyo muryarsa yana faɗin

"Ga wannan.. Na gode sosai Allah Ya saka da alkhairi." Ya yi maganar bayan ya ajje kuɗi a gaban Dadan. Don ba tun yanzu ba ya fuskance ta, ya kuma fahimci me ye damuwarta. Sai kuwa ta fashe da murmushi tana riƙo kuɗin lokaci ɗaya tana furta

"Duka dai? Kai dai ba ka gajiya." Ta ƙare tana murmushi. Shi dai be sake cewa komai ba ya miƙe ya saka takalmansa. Ya yi sallama da Baffa ya fice daga gidan, a ransa yana cigaba da bitar kalaman Dada.

Babu jimawa lokacin da aka saka na biki ya zo. Ranar wata juma'a aka ɗaura auren Inna-wuro da Alhaji Abubakar. Tuni dama Inna-wuro ta ajiye sana'ar nan tata. Musamman da ya kasance a lokacin tana da kuɗin da za su yi amfani da shi wajen harkokin yau da kullum. Ga kuma Alhaji Abubakar da shi ma ba ya barin ta haka, duk da yadda take nuna ba ta so. Amma sai ya nuna mata tamkar yadda ya yi alƙawarin kula da 'ya'yanta to zai fara ne tun yanzu. Ita dai Inna-wuro sai dai ta runtse idanunta tana gode wa Sarki

Please Login or Register in order to submit comment