Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yunƙurin dukan Inna-wuron ne.

"Toh yanzu da kika ɗauko ƙafa kika dawo gida, ba ma ke kaɗai ba har waccan yarinyar da ke bayanki, da kuma abin da ke cikinki kina nufin mu za mu din ga ciyar da ku? Toh wallahi kin yaudari kanki. Shigo idan zaman gidan kike so ga ki ga shi, amma fa tabbas ki sani za ki yaba wa aya zaƙinta."

"Ki yi haƙuri Uwar gida." Baffa ya faɗa ƙasa-ƙasa ko hakan ze sa Dadan ta sakko daga fushin da take. Sai dai cikin ɗaga murya ta ce

"Da Allah ni ƙyale ni, ka rabu da ni in ji da abin da ke damu na. Idan ba haka ba daga kai har 'yar taka zan haɗa in ci wa mutunci wallahil azeem. Don na ga kai ma ka fara canja hali, za kuma mu haɗu da kai." Bin ta Baffa ya yi da sauri yana ba ta haƙuri, sai ka ce yaron da ya yi wa uwarsa laifi yake so ta haƙura. Ita kuma ko kallan inda yake ba ta yi ba ta wuce ɗaki, ya bi bayanta ba tare da ya sake bin inda Inna-wuro take da kallo ba. Runtse idanunta Inna-wuro ta yi, tana jin yadda tausayin kanta, da na mahaifinta na kama ta. Ta ɗaga ƙafafunta da suka sage, tana jin yadda Daneen ke mutsu-mutsu a gadon bayanta, wanda hakan ke alamta mata farkawar da ta yi. Ƙarasawa ta yi cikin ɗakinta da ya canja. Ta ɗan gyara a gurguje ta sauko da Daneen, kafin ta nemi waje ta zauna. Gaba ɗaya yinin ranar babu wanda ya sake kula ta, daga Dadar har Baffan. Sai ita ma ta kama kanta ta yi shiru cikin ɗakin tana tunanin yadda rayuwarta da ta 'ya'yanta za su kasance cikin gidan.


... Karɓe kwanon da ke hannun Baffa, Dada ta yi da sauri tana faɗin

"Wallahi ba za ta ci ba, ba ka isa ba. Ƙatuwa da ita da 'ya har da cikin wani a ce mu za mu din ga ciyar da ita? Toh wallahi ba a gidan nan ba. Waye ya hana ta zaman aure? Idan da ita wata ƙatuwar mai hankali ce komai yake mata ai zauna wa za ta yi. Amma da yake shashasha ce duk irin arziƙin da ke gidan Alhaji Baita sai da ta yi abin da ya sa ya sako ta. Toh wallahi ko dai ta fidda miji ta yi aure ko kuma takura da gallazawa yanzu ta fara ganin su cikin gidan nan." Shiru Baffa ya yi jikinsa a sanyaye don be yi tunanin Dadar za ta gan shi lokacin da ya kawo wa Inna-wuro abincinsa ba. Ya haɗiye shakkarta da yake ji ya ce a hankali

"Don Allah ko don shayarwar da take ki bar ta ta ci abincin nan don Allah."

"Na ce ba za ta ci ba." Ta faɗa tana shirin barin wajen, bayan ta makawa Inna-wuro wata uwar harara.

"Toh ko yaya ne a din ga ba ta. Tun da dai kin ga yanzu ba ta damar yin aure har sai ta haihu, daga nan duk abin da kike so sai a yi." Baffa ya faɗa yana kallanta cike da fatan ta amsa roƙonsa. Wani kallo ta ƙarasa juyowa ta watsa masa, mamakinsa na kama ta. Lallai dole ne ta tashi tsaye a kan mutumin nan.

"Malam..?" Ta ƙarasa ambatar sunan nasa da alamar tambaya.

"Ki yi haƙuri." Ya yi saurin faɗin hakan yana shirin juyawa jiki a sanyaye da irin kallan da ta masa. Kafin ya kai ga wuce wa Dada ta ce

"Shi kenan. Na yarda da abin da ka faɗa, amma fa tabbas sau ɗaya zan din ga ba ta abinci, zuwa lokacin da za ta haihu. Daga nan ko dai ta fidda miji, ko kuma ta koma ciyar da kanta, ko kuma gaba ɗaya ma ta bar gidan." Ba ta jira wani daga cikin su ya ce komai ba ta bar wajen, ta bar su da bin ta da idanu.

"Na gode sosai Baffa." Inna-wuro ta faɗa da sanyayyiyar muryarta, a ranta tana addu'ar Allah Ya sake dawo mata da Baffanta daidai ko ta ji sauƙin rayuwarta cikin gidan.

Haka rayuwar Inna-wuro ta cigaba da tafiya ita da ɗiyarta. Baƙin cikin yau daban na gobe daban. Ko da wani lokacin Baffa ya yi niyyar taimaka mata ko kallanta da idon rahama sai Dada ta san yadda ta yi ta hana hakan faruwa. Shi kuma da ta yi magana shi kenan yake shiga taitayinsa. Sai dai zuwa lokacin Dada tana yarda ta ba ta abinci sau ɗaya a rana, daga nan kuma ko kallan inda take ba za ta sake yi ba. Wani lokacin sai dai a ɓoye Baffa ya kawo mata nasa. I zuwa lokacin kuwa ta soma ramewa, musamman da ya kasance ga shayarwa da take, ga kuma cikin jikinta. Sosai abubuwan suka haɗe mata, cikin lokaci ƙanƙani ta soma sauyawa daga ainahin Inna-wuronta, ga babu isasshen abinci, ga babu laifi cikin na matuƙar ba ta wahala, lokaci guda kuma ga Daneen da ke fama da rashin lafiya, duk ta bi ta rame saboda haƙori da ya saka ta gaba. Wannan ya taka muhimmiyar rawa wajen sake taɓarɓarewar lamarin Inna-wuron, ta zama abar tausayi. Idan ka yi mata kallo ɗaya ita da Daneen sai sun ba ka tausayi, musamman ma dai ita da duk ta bi ta lalace tamkar ba a gidan mahaifinta take ba.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 04

__ Babu wani sauyi da ya samu har zuwa lokacin da ta haife abin da ke cikinta, a cikin gida kamar yadda ta haifi Daneen cikin sauƙi da rangwamin Ubangiji. Sai dai wannan karon namiji Allah Ya ba ta, kyakykyawa mai kama da 'yar'uwarsa. Lokacin da ta haihu shekarar Daneen ɗaya, don haka ta yaye ta a wannan lokacin. Ko arba'in ba ta kai ga yi ba, ta ga zama cikin gidan nan haka kawai ba zai yi mata ba. Idan ba haka ba, ba jaririnta ba, ba Daneen ba, ita kanta yunwa za ta mata lahani. Dalili kenan da ya sa ta tattara duk wani abu da ta mallaka ta siyar, ta siyar da saniyar da Allah Ya taimake ta Dada ba ta ƙwace ta yi rara-gefe da ita ba. Kasancewar ba a gidan take kiwon ta ba. Da wannan kuɗaɗen ta haɗa ta soma siyar da abinci da fura da nono a cikin kasuwar ƙauyen nasu. Yaro ta samu shi ne wanda yake taya ta ayyuka saboda kula da 'ya'yanta. Wannan sana'ar, ba ƙaramin taimaka mata ta yi ba, domin kuwa za ta samu ta ci abinci, Daneen ma ta ci, sannan kuma jaririnta da ya ci suna Ameer ma ya samu ya ci.


.. "Ni fa na faɗa maka ba zai yiwu ba. Ta yaya za a yi a ce ƙatuwar mata har da 'ya'ya biyu a ce a gida za ta din ga zama. Daga wannan layin sai wancan layin. Fisabillahi a haka za a rayu? Haka za mu cigaba da zuba mata idanu ta yi ta zama babu aure?" Ta jiyo muryar Dada daga tsakar gida, daidai lokacin da take shayar da Ameer, ya yin da Daneen ke kwance a kan cinyarta. Runtse idanunta ta yi, ita kam ta rasa me Dada take nufi da ita. Duk salon rashin ƙaunarta ne yake cigaba da fito wa kusufa-kusufa haka? Ta nuna ba za ta ciyar da ita ba, ta yi haƙuri ta zauna. Yanzu kuma tana ciyar da kanta ma ba ta tsira ba? Wannan wace irin rayuwa ce. Sai dai cikin sakannin da ba su wuce biyar ba, ta buɗe idanunta lokacin da ta jiyo muryar Baffa na faɗin

"Ba kuma zai yiwu ba gaskiya sai dai ki yi haƙuri. Tun da dai sana'a take don ta ciyar da kanta da 'ya'yanta ba za mu hana ta ba gaskiya." Ya faɗa ba tare da ya kalli Dadan ba, duk da yadda yake jin wata irin shakkar ta. Amma ya danne, ya cije ya faɗi abin da ke masa yawo a zuciya. Lumshe idanunta Inna-wuro ta yi tana jin wani irin sanyi na ratsa ta. Wasu hawaye masu ɗumi suka zubo a kan kuncinta.

"Ya Allah Ka ƙara dawo da hankalin Baffana kaina. Ka kare shi daga sharrin wannan matar." Ta faɗa a hankali, har lokacin idanunta na a rufe. Buɗe idanunta ta yi lokacin da ya sauka a kan Daneen da ke ta kallon ta, zuwa lokacin uwar ramar da ta yi duk ta yi nata wajen. Sai ta sakar mata murmushi tana kamo kumatunta ta ja.

Zaro idanu Dada ta yi zuciyarta na bugawa, cikin matuƙar tsoro ta ce bakinta har rawa yake

"Umar.." Ta ambata tana kallansa, kafin ya ce komai ta sake faɗin

"Ni kake faɗa wa haka?" Ta faɗa har lokacin bugun zuciyarta bai koma daidai ba.

"Toh ai gaskiya ce." Ya faɗa yana juya wa ya bar ta a wajen tsaye kamar wadda aka dasa. Ta kai wajen minti 5 tsaye a wajen ba tare da ta motsa ba. Gaba ɗaya ƙwaƙwalwarta ta toshe, kanta ya kulle. Mai take ganin yana shirin faruwa? Lallai ta yi mugun sake. A daren Dada ta fice daga gidan zuwa gidan wata 'yar'uwarta. Kuka kawai ta fashe da shi tana faɗin

"Ni kam na shiga uku Hanne, ki taimaka mini kafin rayuwa ta juya mini baya. Umar ya fara juya mini baya." A ranar suka saɓi jiki zuwa wajen Malamin da ya saba musu aiki faka-faka.



_BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYAR_


A cikin shekarun nan abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa har da sauyawar Dada kaɗan, saboda wani dalili da ita kaɗai ta bar wa kanta sani. Duk da shekarun da suka tafi, hakan be sa ta watsar da makamanta ba, ko don yadda girma ke ƙara kama su. Domin kuwa daga zarar ta ga Baffa ya soma ɗan sassautawa, yana ja da abin da ta faɗa za ta yi saurin koma wa wajen malaminta ya yi mata aiki a kansa. Kai daga ƙarshe ma sai ta nemi a yi mata aikin da har abada ba za ta sake dawo ba. Nan da nan Malamin ya nemi da ta kawo kuɗaɗe masu yawa, ta kuwa siyar da saniyarta ta biya kuɗin aikin, domin kuwa abin da take ƙoƙarin aikatawa ta san zai kawo mata ninkin ba ninkin kuɗin Saniyar da ta kashe. Daga nan kuwa al'amarin Baffa ya sake rikicewa fiye da da, ya zama shi ma ya koma muzgunawa Inna-wuro a cikin gidan nan. Kwata-kwata babu sauƙi ita kam a kowanne ɓangare sai a wajen Allah. Sai kuma idan ta kalli 'ya'yanta da take fata nan gaba su zame mata sanyin idaniya, kamar yadda tun yanzun su kaɗai take kalla ta ji daɗi. Daneen da Ameer sun taso ne tamkar 'yan biyu. Don kuwa tun da Ameer ya fara girma sai da ya kamo Daneen, sai ya zamana idan ma ba ka sani ba kana kallan su za ka kira su da 'yan biyu, saboda tsananin kamar da suke, uwa uba kuma kansu ɗaya. A tare suka taso da wata irin muguwar shaƙuwa, da tsananin soyayyar junansu. Ɗaya ba ya son abu ya samu ɗaya. Idan ɗaya ba shi da lafiya ba za ka taɓa gane waye bai da lafiya ba, saboda gaba ɗaya haɗuwa suke su yi jinyar tare. Wanda hakan ba ƙaramin tada wa da Inna-wuro hankali yake ba. Ta rasa inda za ta jefa kanta, har sai mara lafiyar ya warke kafin take samun nutsuwar zuciya, ita da mai taya jinyar. Har zuwa lokacin tana siyar da abinci kala-kala, har ma da wasu abubuwan buƙata. Da wannan sana'ar ta yi amfani wajen saka 'ya'yanta a makarantar da ke nan bakin kasuwar da take siyar da abinci. Nan suke zuwa su same ta idan an tashi kafin idan ta gama abin da take su tafi gida. Da daddare kuma su je makarantar dare, wadda take babu nisa daga gidansu. Duk wannan abubuwan har zuwa lokacin Dada ba ta canja ba. Sai dai wasu abubuwan sun ɗan yi sauƙi saboda gajiya. Uwa uba kuma da ya kasance watarana ma idan ta ga Inna-wuron da safe sai dare sannan za ta kuma sanya ta a ido. Dalili kenan da ya sa ta ɗan yi sanyi tana jira lokacin da Malam ya ce mata ta jira ya yi. Sai dai kuma maimakon haka sai ta ɗauki rabin tsanar da ta yi wa Inna-wuro ta maida ta kan Daneen da kuma Ameer, ba su da damar su fito tsakar gidan yin wasa, ko wani abun sai ta hantare su. Har gwara ma Baffa, duk da shi ma ba ya wani kula su, amma dai ba ya hantarar su kamar yadda Dada take.

Da ma kuma tun da suka taso suka fara wayo suka fahimci ko ma wace ce Dada ba ta ƙaunar su, don su ɗin yara ne masu matuƙar wayo. Don akwai ranar da suna kasuwa siyar da abinci, Ameer ya kalli Inna-wuro ya ce

"Inna.."

"Na'am Ameer." Inna-wuro ta faɗa bayan ta juyo ta kalle shi da murmushi ɗauke a kan fuskarta.

"Wai me ya sa Dada ba ta sonmu?" Ya yi tambayar da ta sanya Inna-wuro janye murmushin fuskarta.

"Ameer?" Ta yi ƙarfin halin faɗar hakan fuskarta a haɗe. Ba ta taɓa zata ba, ba ta taɓa kawo wa tun a yanzu za su fahimci cewa Dadar ba ta ƙaunar su ne ba. Sai dai ga shi sun shammace ta. Kafin ya ce komai ta ɗora da faɗin

"Waye ya ce maka ba ta son ku?" Ta tambaya a sanyaye. Ɗan ƙaramin bakinsa ya buɗe ze yi magana, sai kuma ya juya ya kalli Daneen da ke zaune suna kallan juna. Dara-daran idanunta farare ƙall ta ɗaga ta zuba wa Ameer ɗin su tana jira ta ji me ze ce. Ganin yana shirin buɗe baki ya yi magana ya sanya ta soma girgiza masa kanta, ƙasa-ƙasa da siririyar muryarta mai daɗin saurara take faɗin

"Inna ba ni ce ba."

"Adda Neen." Ya faɗa yana nuna ta, lokacin da ya turo bakinsa. Don babu yadda ze yi, ba ya so Innar ta kama shi da laifi kwata-kwata musamman da ya ga ranta ya ɓaci. Sai dai in da a waje ne, ko ma wane irin laifi Adda Neen ɗin tasa za ta yi ya gwammace ya ɗauki laifin. Shi ya sa sau da dama ko a makaranta sai dai a yi faɗa da shi ba dai da Daneen ba. Don kuwa zama yake tamkar shi ne yayan ita kuma ƙanwar. Maida duban ta Inna-wuro ta yi kan Daneen da ta yi rau-rau da idanunta kamar me shirin saka kuka, ta buɗe baki za ta yi magana Daneen ta ɗaga yatsanta guda ɗaya ta kai saitin bakinta tana faɗin

"Inna na rantse ba haka ba ne." Dariya ta ba ta, don haka ta sanya hannu ta janye hannun tana faɗin

"Ya isa haka, kar na sake jin wani a cikin ku ya ce haka. Dada tana son ku sosai Uhmm?" Jinjina kai kawai suka yi suna murmushi.

"Ya yi kyau. Abin da nake so da ku kawai ku dage ku yi karatu, ina so ku zama wasu, ku zama waɗanda kullum zan din ga alfahari da su."

"Inna da ma muna ƙoƙari ai ko?" Ameer ya faɗa yana murmushi.

"Kuma dai na fi Ameer ƙoƙari." Daneen ta faɗa tana rausayar da kai, sassanyan murmushi na fita daga kyakykyawar fuskarta.

Haka suke yini cikin farin ciki idan suna tare, sai dai daga zarar sun koma gida sai farin cikin ya gushe, musamman idan halin Dadan ya motsa. Haka za su yi gum a ɗaki ta yi ta jarabarta ita kaɗai. Idan Inna-wuro ta tanka ta ce za ta mata rashin kunya. Idan kuma ta yi shiru ta ce ta maida ta mahaukaciya tana magana ta mata shiru. Wannan dalilin ne yake sanya Inna-wuro kasa sanin takamaimai abin da za ta yi. Sai kawai ta haɗa kan 'ya'yanta ta rungume cikin rashin sanin abin yi.

Wannan kenan.



*** *** ***

__ Ƙaton palour ne da ya amsa sunansa palour. Haɗaɗɗe, me ɗauke da zafafan kujeru masu ɗaukar hankali, kyau da nutsuwa. Ƙatuwar T.V ɗin da ke gefe, inda take zaune a tsare babu hayaniya ce ke ta aiki. Sai dai ga dukkan alamu babu wanda ya damu da abin da ake haska wa a ciki. Wata dattijuwar mata ce zaune a kan ɗaya daga cikin lausasan kujerun da ke zagaye da ɗakin, ƙafarta ajje a kan wani tattausan pillow, wata matashiyar budurwa na matsa mata ƙafar. Can gefe kuma wata kyakykyawar mata ce zaune, sanye cikin atamfa doguwar riga ɗinkin kaftan, ta yi ɗauri wanda ya dace da shekarunta. Har bayan wajen mintuna biyar babu wanda ya ce ko uffan. Zuwa can wata matashiyar budurwa ta shigo cikin ɗakin da sallama ɗauke a bakinta. Hannunta ɗauke da tsadaddiyar wayarta, tana sanye cikin wata doguwar riga da ta matuƙar karɓar jikinta. Neman waje ta yi ta zauna gefen wannan dattijuwar fuska a narke tana kallanta. Girgiza kai dattijuwar ta yi kafin ta ce

"Toh.. za a yaudare ni ne?" Ta ƙare tana taɓe baki. Turo baki matashiyar ta yi kafin ta ce

"Babu wata yaudara fa Dadaji. Allah kuwa magana na zo mu yi da ke mai muhimmanci." Jin hakan ya sanya wadda ke yi wa dattijuwar tausa miƙewa, don ba hurumin su ba ne jin wata maganar da ta shafi 'yan gidan. Don haka ta ce cikin girmamawa.

"Rankiyadaɗe bari na je." Amsa mata Dadaji ta yi tana maida dubanta kan Hidaya ta ce

"Me kuma ya faru?"

"Dadaji har zuwa yanzu fa Yah Tareeq bai fito ba. Na yi wa Maama magana ta ce na bar shi zuwa an jima, na kikkira wayarsa ya ƙi daga wa kuma Aminu ya tabbatar mini da ya ga shigowarsa cikin gidan nan, ni kuma na kasa haƙuri."

"Oh ni 'yar nan. Toh ni kuma meye nawa a ciki Hidaya? Ke ɗin da kuke ɗasawa ma da shi bai ɗaga kiranki ba me zan yi masa? Da ma ya aka cika ballantana kuma wani abu ya faru? Ni kam ban san me zan masa ba kuma." Dadaji ta faɗa.

"Kai don Allah.. Wallahi dai ya kamata a tausaya wa Yaya.. Ni fa ina tsoro wallahi, kin dai san shi da saka abu a rai. Maama don Allah ki saka baki kin ji?" Ta ƙare maganar tana juyawa ta kalli ɗayar matar da ke cikin ɗakin.

"Hidaya na faɗa miki ki bar shi yana buƙatar kaɗaici koh?" Maama ta faɗa tana kallan Hidayar.

"Ah toh." Dadaji ta faɗa tana jinjina kai. Jiki a sanyaye Hidaya ta ce

"Tohm." Daga haka ta miƙe ta wuce ɗakinta, har lokacin tana sake kiran number Yayan nata amma be ɗaga ba.


... Bayan tsawon mintuna masu yawa da ya kwashe a toilet ɗin, inda ya sakar wa kansa ruwa me sanyi. Ɗaure da towel a ƙugunsa ya fito daga toilet ɗin. Nannaɗaɗɗen gashin kansa jiƙe sharkaf da ruwan da ya daɗe a cikinsa. Farar fatarsa ita ce ta tona asirin baƙar gargasar da ke jikin gaɓɓai da yawa na jikinsa. Musamman ma dai ƙirjinsa zuwa kan hannunsa, wadda duk da yadda take a jiƙe hakan be hana ta miƙewa ba. Be yi tunanin duk daɗewar da ya yi cikin ruwan nan zai cigaba da jin ɓacin rai ba. Sai dai yadda zuciyarsa ke tafasa, tana sake yin zafi ya sa hatta numfashinsa yake fita da sauri. Tsigar jikinsa har lokacin ta ƙi dena tashi, wadda ita ta taimaka wa gargasar jikinsa wajen ƙin lafe wa a kan faffaɗan ƙirjinsa. Cikin takun nutsuwa ya ƙarasa bakin mirror ya tsaya, daidai lokacin da kyakykyawar fuskarsa ma'abociyar wani sassanyan kyau ta bayyana. Kyakykyawa ne na gani na faɗa, irin kyan nan me ruɗar da duk wanda ya yi tozali da shi. Fari irin farin nan me mugun kyau, wanda ƙasumbar da ke zaune ras a kan fuskarsa ta ƙara ƙawata kyawunsa da kuma farin nasa. Wasu idanu ne da shi na musamman, farare masu ɗauke da baƙa wuluk ɗin ƙwayar ido. Ɗan ƙaramin baki ne da shi tamkar wata mace, ja kamar wanda ke shafa wani abun. Yadda kwantacciyar ƙasumbar fuskarsa ta zagaye fuskarsa har tana ƙoƙarin rufe mitsitsin kyakykyawan laɓɓansa. Hannunsa ya kai ya ɗan shafa saman girarsa idanunsa a lumshe yana ɗan fidda numfashi a hankali ko zai samu ɓacin ran da yake ji ya tafi, ya manta da abin da ya faru, ya ɗauka ya jefa shi cikin kwandon sharan abubuwa mara sa amfani, amma ya kasa, ya kasa kwata-kwata. Daidai lokacin wayarsa da ke yashe a kan gado ta ɗauki ƙara. Be ko motsa ba, ballanta ya yi yunƙurin ɗaukar wayar. Wani kiran ne ya sake shigo wa bayan wancan ya tsinke. Duk da ba a ɗaga ba, hakan be sa an dena kira ba, ya lumshe idanunsa yana jan ƙaramin tsaki, sabon ɓacin rai na taso masa. A nutse ya juya ya ƙarasa kan gadon ya ɗauki wayar, yana shirin kashe ta gaba ɗaya sabon kira ya sake shigo wa. Ya dafe kansa da yatsu biyu kafin ya kalli me kiran nasa. Sauke ajiyar zuciya ya yi har lokacin kyawawan idanunsa ɗore a kan wayar. Dab da za ta tsinke ya ɗauka. Daga can ɓangaren aka ce

"Tareeq.. Me ya sa za ka yi haka ne?" Ya faɗa a gajiye. Maida wayar ya yi ya riƙe da ɗayan hannunsa kafin ya gyara tsayuwarsa, kafin ya kai ga cewa komai aka sake faɗin

"Don Allah ka fito. Wallahi ka ɗaga mini hankali." Ya faɗa dan ya san halin abokin nasa da saka abu a zuciya, ƙaramin abu ma idan ya saka a zuciyarsa an banu, ballantana wannan lamari da dukkanin su babu wanda ya taɓa tunanin hakan za ta iya faruwa.

"Abdoul don Allah ka ƙyale ni, zuciyata na buƙatar hutu, idan har ba so kuke ta tarwatse ba." Ya ƙarasa maganar a gajiye, yana fesar da wani huci da ya fito tun daga ƙasan zuciyarsa.


*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 05

__ "Tareeq!" Abdoul ya faɗa bayan ya sauke ajiyar zuciya. Bai ce komai ba sai ajiye wayar da ya yi, ya koma ya zauna a gefen gadon hannunsa ɗaya cikin sumar kansa, idanunsa a lumshe, zuciyarsa na sake cunkushe wa waje ɗaya.

A ɗaya ɓangaren kuwa kallan Abdoul Maama ta yi ta ce

"Ya katse ne?" Ta tambaya tana kallan sa. Gyara zaman wayar ya yi a hannunsa kafin ya jinjina kai, a nutse ya buɗe baki ya ce

"Ehh, amma dai sauƙin ta ɗaya yana cikin gidan nan." Ajiyar zuciya Maama ta sauke kana ta ce

"Ku bar shi, kar wanda ya sake kiran sa don Allah, ni da kaina zan je na same shi zuwa gobe, na san kafin nan In Sha Allah zuciyarsa ta yi sanyi."

"Toh shi kenan." Abdoul ya amsa da hakan. Daga haka ya yi sallama da su ya fice daga ɗakin.


... Tura ƙofar ɗakin ta yi, cikin sa'a kuwa sai gashi ta buɗe. Ta sauke ajiyar zuciya tana saka kanta cikin ɗakin da sallama ɗauke a bakinta. Yana zaune a kan haɗaɗɗiyar kujerar da ke cikin palourn, sanye cikin ƙananan kaya da suka matuƙar yi wa jikinsa kyau. Laptop ce gabansa yana dannawa cikin ƙwarewa, gaba ɗaya fararen idanunsa na kai, da alama wani aikin yake mai matuƙar muhimmanci. Duk da kusan duk hankalinsa na kan laptop ɗin, hakan be hana shi jin lokacin da aka turo ƙofar ba. Ya ɗaga manyan fararen idanunsa ya kalli ƙofar a nutse. Daidai lokacin da Hidaya ta ƙarasa shigowa cikin ɗakin, kamar koyaushe babu abin da ke tashi sai sassanyan ƙamshin jikinsa da kuma na cikin ɗakin. Wanda suka cakuɗu suke bayar da ƙamshi me daɗin gaske. Rufe laptop ɗin ya yi kafin sassanyan murmushin da ya ƙawata fuskarsa ya bayyana a kan laɓɓansa. Sai dai yadda tsagoron kyawunsa ya sake bayyana, ga duk wanda ya kalle shi zai so a ce ya zauna a hakan ne ko da yaushe. Ita ma murmushin Hidaya ta yi tana ƙarasawa ta nemi gefensa ta zauna ta ce a narke

"Kai

Please Login or Register in order to submit comment