Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗaya, zuciyarta fall tunanin shin su waɗannan ɗin su waye su?

"Ina wuni?" Ta yi ƙarfin halin faɗa a hankali.

"Alhamdulillahi, ya jikin ƙanin naki?" Maama ta faɗa.

"Alhamdulillahi." Ita ma Daneen ta ba ta amsa a sanyaye. Hidaya da ke gefen Maama ta ce

"Wai ita ce za ta ba wa Yah Tareeq ɗin ƙoda?" Jinjina kai Maama ta yi tana murmushi. Cikin matuƙar farin ciki Hidaya ta miƙe ta koma kusa da Daneen, tana jin wata irin ƙaunarta lokaci guda. Tun shigowar ta take yaba irin kyawun da Allah Ya ba ta, sai dai da yake ba ta san wace ce ba ya sanya ta kama kanta.

"Amma na ji daɗi, Allah Ya ba ki abin da kike nema duniya da lahiya, Allah Ya biya miki buƙatunki na alkhairi."

"Ameen." Sultanah ta amsa addu'o'in Hidaya tana murmushi.

"Ya sunanki?" Hidaya ta faɗa tana kallon Daneen da murmushi a kan fuskarta. Sai da ta ɗaga kyawawan idanunta da suka ƙanƙance sannan ta ce

"Daneen."

"Woww, suna mai daɗi. Sannu Daneen." In ji Hidaya tana murmushi. Godiya sosai suka ci gaba da yi wa Daneen, suna kuma yi wa Ameer addu'a. Abin da ya matuƙar faranta ranta kenan.

"Sultanah ku je gida tare da ita ta samu ta yi wanka ta yi bacci ta huta kafin goben da za a yi aikin." Maama ta faɗa bayan ta miƙe tsaye. Da sauri Daneen ta kalli Maama tana girgiza kai. Tana kai wa ƙarshen maganarta ta soma faɗi cikin sanyayyiyar muryarta.

"A'ah, ba zan iya tafiya in bar ƙanina ba. Ki yi mini afuwa don Allah ba zan iya ba." Kallon ta su duka suke yi, abin bai ba su mamaki ba, don duk tana hakan ne a kan ɗan'uwanta. Su ma kuma sun san me ake nufi da ɗan'uwa.

"Shi kenan, ki je zuwa an jima sai ku dawo idan kin huta." Kamar za ta fasa kuka haka ta ji. Tabbas matar ta yi mata kwarjini amma duk da haka ba ta ji ko nan da can za ta iya matsawa daga asibitin, bayan Ameer na ciki a kwance. Don haka cikin girmamawa ta ce

"Don Allah ki yi haƙuri ki bar ni wajen ɗan'uwana." Ta faɗa lokacin da ƙwalla ta cika cikin idanunta. Cike da tausayawa Maama ta ce

"Babu damuwa. Allah Ya ƙara lafiya, Ya kuma saka miki da alkhairi." Wata ƙatuwar ajiyar zuciya Daneen ta sauke, tana jin wani sanyi na ratsa ta. Haƙiƙa ta ji daɗin kai ƙarshen maganar da matar ta yi, don da ta ci gaba da cewa ta je ɗin ba ta tunanin za ta iya ci gaba da yi mata musu. A sanyaye ta amsa da

"Ameen." Daga haka suka yi sallama da Daneen suka fice daga ɗakin. Ita ma ba ta ƙara wasu mintina ba ta fice zuwa inda take zaune ɗazun.

Washegari ita ce ranar da za a yi wa Daneen aikin cire ƙoda, ya yin da za a yi wa Tareeq na dashen ƙodar. A kuma safiyar ranar ne Yohanah ya je ya biya duk kuɗaɗen da ake buƙata na aikin da za a yi wa Ameer. Cike da mamaki Likitan ke kallon sa, ya ce har lokacin ya kasa dena tantamar anya kuwa Yohanahn kafiri ne da gaske?

"Amma me zai hana ka nuna fuskarka wajen Alhaji Alhassan. Alkhairinka yawa gare shi wajen iyalinsa." Murmushi Yohanah ya yi kafin ya ce

"Babu damuwa, ina yin komai ne saboda Allah, kuma ba na so ya sani. Akwai dalilin yin hakan, ina so ne na rama abin da ya yi mini. Kamar yadda yake taimakawa mutane a bayan ido, shi ya sa nake so na rama masa ba tare da ya sani ba." Jinjina kai Likitan ya yi, bayan ya sauke ajiyar zuciya ya ce

"Duk da haka, ko da sau ɗaya ne ka bari ya ganka ya gode maka. Ka samo wadda za ta ba wa ɗansa ƙoda. Duk da a matuƙar buƙatar kuɗi take, hakan bai sa ka bar ta da shi ba. Ka kuma ƙi barin Alhaji Dikko ya biya kuɗin aikin a matsayin kuɗin ƙodar yarinya, shi ma ka ɗauke masa. Kuma duk da haka ba ka so ya sani, bayan kai ɗin na daban ne, mai ɗumbin alkhairi a gare shi." Kafin Yohanah ya ce komai wayarsa ta shiga ringing, ya kalli mai kiran nasa, kawai sai ya tura ta cikin aljihunsa kafin ya ɗaga idanunsa ya maida su kan Likitan ya ce

"Please doctor a yi abin da na ce. Ita yarinyar babu damuwa za ta iya haɗuwa da shi, amma ni babu buƙatar hakan kamar yadda na faɗa maka." Yohana ya ƙare maganar yana sakin wani murmushi, lokaci ɗaya yana kai hannunsa guda ɗaya ya shafa haɓarsa har lokacin idanunsa a kan Likitan.


#YOHANAH
#KIDNEY
#DANEEN
#TAREEQ
#AMEER

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 20

Jinjina kai Likitan ya yi kafin ya ce

"Shi kenan, Allah Ya saka maka da alkhairi. A madadin Alhaji Dikko, ina sake miƙa godiya gare ka." Ba tare da Yohana ya amsa ba ya miƙa wa Likitan hannu har lokacin fuskarsa da murmushi suka gaisa. Daga haka ya yi waje, Likitan ya bi shi da kallo yana ci gaba da mamakin kyawawan halaye irin nasa.

Cikin nasara, ikon Allah da kuma tarin addu'o'i daga bakunan iyalan Dikko aka yi wa Daneen da kuma Tareeq aiki.


.. "Sannu yaron nan." Dada ji ta faɗa tana kallan Tareeq cike da tausayawa. Jinjina kai ya yi daga inda yake kwance, yana sake lumshe idanunsa. Shafa goshinsa Maama ta yi tana jin wani irin tausayin ɗan nata, saboda sanin halinsa da ta yi, idan dai har ka ga ciwo ya kayar da shi, toh da gasken ciwon nan ya shahara. Ba ta ce komai ba, sai neman waje da ta yi ta zauna, daidai lokacin da aka turo ƙofar ɗakin. Sultanah, Abdoul da Hidaya, su ne suka shigo. Idanunsa a kan Abdoul ya sauka, cike da mamakin yadda suka shigo tare da su Sultanah. 'Ko dai har abin nasu ya ɗore haka?' Ya raya hakan a ransa, yana fatan a ce da gasken haka ne.

"Tare kuke ne?" Dada ji ta yi tambayar tana kallon Abdoul, tambayar da take ta masa yawo cikin kai. Don haka sai ya maida duban sa kan Abdoul don jin amsar da zai bayar, cike da fatan Allah Ya sa burin ƙanwarsa ya cika.

"A'ah, a cikin asibitin muka haɗu." Ya ba wa Dada ji amsar cikin girmamawa.

"Ayyah." Ta yi maganar a taƙaice. Daga haka ya gaishe ta, kafin ya gaisa da Maama. Sai kuma ya ƙarasa inda abokinsa yake.

"Sannu! Ya ƙarfin jiki?" Ya tambaya cikin kulawa. Sai da Tareeq ya lumshe idanunsa kafin ya ce

"Alhamdulillahi."

"Allah Ya ƙara sauƙi, sannu." Yanzu kam jinjina kai kawai ya yi yana sake lumshe idanunsa don so yake ya ɗan sake runtsawa, don jin sa yake tamkar an canja ji. Wani daban yake ji tun bayan da aka yi aikin. Sai dai shi a karan kansa ya matuƙar jin daɗin jikinsa, wanda ya yi kwana da kwanaki rabon da ya ji irin hakan. Su ma Hidaya da Sultanah gaishe da yayan nasu suka yi. Zuwa can Abdoul ya ce

"Maama zan so na ga wadda ta sadaukar da ƙodarta a kan Tareeq ɗinmu, ko don in yi mata godiya." Da sauri Dada ji ta kalle shi ta ce bayan ta soma tafa hannunta.

"Kaa ga aikin shiririta, daga zuwa ɗazu tana bacci babu wanda ya sake komawa. Ke maza ku tashi mu je wajen baiwar Allah ɗin can." Ta ƙare maganar tana miƙewa tsaye. Babu musu dukkansu suka miƙe. Maama ta kalli Tareeq, ganin da alama kamar bacci ya ɗauke shi ne ya sanya ta bin bayan su Dada ji da suka yi waje.

"Allah kuwa Yah Tareeq yana jin jiki, wallahi duk jikina a sanyaye yake." Hidaya ta faɗa a marairaice, tana hango fuskar yayanta da ta ɗan sauya, kamar ba shi ba.

"Wallahi ke kam.." Ita ma Sultanahn ta faɗa a sanyaye.

Hidaya ce a gaba, don haka ita ce ta yi amfani da hannunta wajen tura ƙofar ɗakin. Sultanah, Maama da Dada ji suka bi bayanta. Sai Abdoul da ke a ƙarshe, wanda sai da Maama ta ce ya shigo sannan ya bi bayan su. Gaba ɗayansu idanunsu na kan gadon. Tana kwance har zuwa lokacin tana bacci, duk da yadda take bacci hakan bai hana bayyana yadda idanunta suka ɓurma suka yi ciki ba.

"Allah Sarki baiwar Allah." Dada ji ta faɗa tana kallan innocent face ɗin Daneen, wadda yarintarta ta gama bayyana ko daga kallan fuskarta. Tun kafin su kai ga zama, Daneen ta wani irin zabura daga baccin da take, a firgice ta furta bayan ta tashi daga kwanciyar da take.

"Ameer!" Gaba ɗaya idanunsu sai suka sake koma wa kanta. Tarr ta buɗe idanunta cikin ɗakin, sai ta shiga rarraba manyan idanun nata, tana kallon duk mutanen da ke ciki.

"Ameer." Ta sake faɗa a kan laɓɓanta har lokacin ba ta daina kallon su ba. Hidaya ce ta tashi ta ƙarasa inda take, ta nemi waje ta zauna kafin ta kalli Daneen da ke takure waje ɗaya ta ce

"Sannu." Kamar sai da ta ce sannun sannan ta tuna abin da ya faru, saboda yadda ta kai hannunta ƙirjinta ta dafe. A hankali ta buɗe baki ta ce

"Tohm."

"Ya jikin?" Sake dafe saitin ƙirjinta ta yi tana sauke wani numfashi kamar wadda ta yi tsere, ba tare da ta ba wa tambayar Hidayan muhimmanci ba ta ce

"Ƙanina.."

"Hidaya taimaka mata ta gyara jikinta, sai ta je ta ga ƙanin nata." Maama ta faɗa. Da "Toh." Hidaya ta amsa, kafin ta miƙe tana kallon Daneen ta ce

"Mu je koh?" Babu musu Daneen ta soma ƙoƙarin saukowa daga kan gadon. Da sauri Hidaya ta riƙo ta saboda ganin yadda ta yi ta koma baya da sauri.

"Sannu." Ta sake furtawa cike da tausayin Daneen ɗin. Kusan a tare duk 'yan ɗakin suka sake faɗin "Sannu." Ya yin da Abdoul ya ɗora da faɗin

"Bari na je waje Maama, zuwa an jima sai na shigo." Babu musu ta amsa da "Toh." Daga haka Abdoul ya saka kai ya fice daga ɗakin, Sultanah ta bi shi da kallo tana murmushi.

Hidaya ce ta taimaka wa Daneen sosai wajen yin komai, don har cikin ranta tausayi take ba ta. Sun kwashe fiye da rabin awa kafin suka dawo ɗakin. Nan ma dai ta taimaka mata ta sake kwanciya, saboda yadda ta fi jin daɗinta. Don ita kanta ji take kamar ba ita ba. Wajen da aka mata aikin kuwa babu laifi yana mata ciwo, amma dai ita wannan ɗin bai ɗaɗata da ƙasa sosai ba, duk kuwa da cewar ba zafi ne normal ba, tana jin zafin har cikin jikinta, amma kuma ba ta ɗauka hakan da muhimmanci ba. Don gani take duk wani zafi da za ta ji, toh zai biyo bayan zafin da take ji na ganin ɗan'uwanta cikin halin ciwon da sanadiyyar wasu suka jefa shi. Sai a lokacin sannan suka gaisa, dukkansu suna yi mata ya jiki.

"Alhamdulillahi." Shi ne abin da take amsawa da shi kawai, don ita dai gaba ɗaya hankalinta yana kan Ameer.

"Mun gode sosai, Allah Ya saka miki da alkhairi, Allah Ya biya miki buƙatunki na alkhairi, Allah Ya ba wa ɗan'uwanki lafiya." Dada ji ta faɗa tana jin har cikin ranta abin da yarinyar ta yi musu yana ɗaya daga cikin alfarmomi masu matuƙar muhimmancin da har abada ba su taɓa mantawa da shi ba. Ba kuma za su taɓa iya biyanta abin da ta musu ba.

"Ameen, ina so na ga ƙanina." Ta faɗa a narke tana kallon Dada ji. Ajiyar zuciya Dada ji ta sauke tana kallon Maama ta ce

"Anya kuwa za su bar ta ta fita?" Kallon ta Maama ta yi kana ta ce

"Hakan ba damuwa ba ne, amma kuma ai jikinta za a duba. Ki bari idan kin ɗan ƙara jin dama-dama ko zuwa gobe ne sai ki je ki gan shi." Maama ta ƙare maganar tana kallon Daneen. Runtse idanunta Daneen ta yi tana jin yadda take bugun zuciyarta ya ƙaru. Ta yaya ma za ta iya haƙura ba tare da ta ga ɗan'uwanta ba? Ba ta san lokacin da ta miƙe ba, duk da yadda wajen ciwonta ya amsa, amma hakan bai dame ta ba. Sai dai ta runtse idanunta na tsawon sakanni kafin ta buɗe. Ta ce muryarta na karkarwa.

"Don Allah ki bar ni na je na gan shi kin ji? Zan iya tafiya, zan iya komai ma kin gani?" Ta yi maganar tana soma miƙewa tsaye. Da sauri Hidaya da Sultanah suka miƙe, suka riƙo ta.

"Maama don Allah ki bar ta ta je, tana so ta gan shi ne." Hidaya ta faɗa fuskarta a narke tana kallon Maama.

"Toh shi kenan, ku je ke da Sultanah ku raka ta. But u should go and ask doctor Adam, za ta iya fita?" Jinjina kai Hidaya ta yi tana sakin Daneen a hankali ta fice daga ɗakin. Daidai lokacin da wayar Maama ta yi ƙara. Ta kalli mai kiran kafin ta ɗaga. Sai da suka gaisa kafin daga can ɓangaren Umman Jawahir ta ce

"Ya mai jikin?"

"Alhamdulillah, jiki da sauƙi." In ji Maama.

"Wallahi na ƙagu mu dawo in ga jikin yarona. Kin ga musamman ma dai Jawahir duk ta bi ta ɗaga hankalinta. Tun da aka kwantar da shi a asibitin nan ta ɗauki damuwa ta ɗora wa kanta, yanzu haka ma kin ganta kuka take, don Abbanta ya ce ba gobe za mu taho ba." Murmushi Maama ta yi, a ranta tana ji idan Allah Ya yarda yaronta ya samu mace mai sonsa tsakani da Allah kenan.

"Ayyah Allah Sarki Jawahir. Ai babu komai me ye na damuwar? Jikin nasa kuma da sauƙi ai, ki ƙara rarrashinta."

"Ni ma haka nake faɗa mata. Kin ji koh Jawahir?" Umma ta ƙare maganar tana kallon Jawahir da ke gefen ta.

"Yawwah." Maama ta faɗa.

"Toh Allah Ya ƙara afuwa. Kuma In Sha Allah muna dawowa nan za mu taho babu ɓata lokaci."

"Allah Ya yarda." Daga haka suka yi sallama. Ba ta daɗe da ajiye wayar ba Hidaya ta dawo cikin ɗakin. Ita da Sultanah suka taimaka wa Daneen wajen kai ta ɗakin da Ameer yake. A bakin ƙofar suka bar ta.

"Bari mu jira ki a nan." Hidaya ta ƙare maganar tana sakin murmushi. Ita ma murmushin ta ƙaƙalo kafin ta jinjina kai. Daidai lokacin da Yohanah ya fito daga cikin ɗakin, yana shirin rufe ƙofar ya ga Daneen. Sai ya saki murmushi yana faɗin

"Ke ce?" Jinjina kai Daneen ta yi hannunta dafe da gefenta don ta fi jin daɗin tsayuwar.

"Ki ƙara gode wa Allah, saboda da alama an yi aikin nan cikin nasara. Ameer na dab da samun lafiya." Ba ta san lokacin da wani murmushi ya suɓuce mata ba, sam sai ta kasa amsa wa Yohanah maganarsa, ban da ƙarasawa ciki da ta yi don ta gane wa idanunta. Shi ma bai damu da amsar tata ba ya wuce ta gaban su Hidaya da babu wadda ta kalle shi har ya bar wajen.

Cike da sassarfa take ƙarasa wa cikin ɗakin idanunta a kan Ameer da idanunsa ke a lumshe.

"Ameer." Ta faɗa tun kafin ta ida ƙarasawa inda yake. Kamar a mafarki ya ji muryar 'yar'uwarsa, don bai taɓa tunanin zai sake buɗe idanu ya ga wani ɗan'adam ba, a lokacin da za a masa aiki. Sai ga shi da alama an gama masa aikin, ga shi kuma zai ƙara ganin 'yar'uwarsa. Abin da dai bai sani ba kawai shi ne, shin zai sake ganin Inna-wuro?

"Ameer." Daneen ta sake faɗa tana riƙo hannayensa. Wasu irin ƙwalla ne suka sakko daga cikin idanunsa zuwa kan kuncinsa.

"Addatah." Ya faɗa muryarsa a wani irin cunkushe.

"Na'am Ameer, ka warke koh?" Ta tambaya tana jin wani irin farin ciki na ziyartar ta. Murmushin yaƙe Ameer ya yi kafin ya ce

"Ba na tunanin har abada zan warke Addaneen. Ina ji a jikina kamar ba zan ƙara ganin Innarmu ba, duk da yadda nake son ganinta. Na so a ce na ga babanmu kafin na tafi na bar ki Addatah. Ban san zuwanmu garin nan shi ne silar rugujewar farin cikinmu ba, da ban matsa mun taho ba. Ban san neman kuɗin koma wa ƙauyenmu zai sake zama wani ɓangare na wargajewar farin cikinmu ba, da ban nema ba. Na yi nadama matuƙa, na janyo wa kaina. Kalli yadda mutanen nan suka lalata mini rayuwa, zuciyata kuma rauninta na da yawa shi ya sa ta kasa daurewa. Adda kin san su ɗin su waye?" Kallon sa kawai take yi tun da ya soma magana har ya dakata, ji take gaba ɗaya maganganun kamar ba na Ameer ba, kamar ba Ameer ɗinta ƙaninta mai tarin ƙuruciya da shiririta ba. Sai ta ji maganganun da suke fitowa daga bakinsa tamkar wanda wani babba yake yin su. 'Shin me yake shirin faruwa?' Ta tambayi kanta tana maida dubanta kan Ameer.

"Ni na faɗa maka ina buƙatar sanin su waye su Ameer? Wanne irin maganganu ne suke fito wa daga bakinka Ameer? Ba ka da hankali ashe dama?" Ta faɗa tana jin yadda ilahirin jikinta ke karkarwa tamkar mazari. Girgiza kai Ameer ya yi, ya yi nasarar kamo hannun Daneen cikin nasa ya ce

"Ban sani ba ko Allah zai sa ki samu dama ki shigar da su ƙara Addah, ban sani ba ko bayan raina za ki buƙaci sanin sunan mutanen da suka datse mana farin cikinmu, suka yi mana katangar ƙarfe da rayuwarmu mai daɗi, suka kuma zamo sanadiyyar rabuwarki da ɗan'uwanki." Wani mari Daneen ta kai wa Ameer a gigice tana jin yadda jikinta ke ci gaba da ɗaukar rawa. Tuni idanunta sun soma zubar da hawaye. Jin maganganun Ameer ɗin take har cikin kowacce gaɓa ta jikinta.

"Ameer ba ka da hankali? Ba ka da hankali ashe dama? Ashe ba ka sona Ameer? Ashe ka tsane ni Ameer ban sani ba? Wasu irin maganganu kake faɗa haka mara sa daɗin ji? Toh ko dai so kake zuciyata ta tarwatse?" Ta tambaya cikin kuka tana kallon yadda ya runtse idanunsa. Duk da yadda ya ji zafin marin, amma hakan bai sa ya ji ya karaya ba. Shi kaɗai ya san me yake ji yanzu haka a cikin gaba ɗaya jikinsa, wasu abubuwa yake ji waɗanda ko za a kashe shi ba zai iya kwatanta su ba. Hannunsa ya saka da iya ƙarfin da yake da shi ya janyo Daneen ɗin, idanunsa a lumshe ya saka bakinsa saitin kunnenta ya soma faɗi a wahalce, sannan kuma a rarrabe, a kuma hankali.

"Ki yi haƙuri Adda, ko da za ki buƙaci sanin su waye su.." Sai ya dakata a nan yana sake riƙe hannun Daneen da masifar gaske.

"Ki fara shari'a da yaron gidan Alhaji Dikko, shi ne shugaba kuma ogan duk waɗanda suka yi amfani da.." Maganar da ta kasa fita kenan, saboda wani yunƙuri da ya yi. Cikin second ɗaya ya saki hannun Daneen, wanda hakan ya tilasta mata saurin kallon fuskarsa. Numfashinsa ne yake fita da wani irin sauri, tuni idanunsa suka soma ƙaƙƙafewa, ya yin da ya fara wata irin shaƙuwa. Wani mahaukacin karkarwa da jikinta ke yi shi ne ya sanya ta runtse idanunta. Ta buɗe su a kan Ameer da ta ga yana wasu abubuwa waɗanda ba ta taɓa ganin irin su ba. Don haka ta yi saurin riƙo shi tana faɗin

"Ameer." Ta faɗa da ƙarfin gaske, tana ci gaba da kallon yadda yake kokawa da numfashinsa. Kwata-kwata tunaninta bai kawo mata ta je ta kira likita ba, don saboda tsananin ruɗewa, kawai kiran sunansa take. Sai zuwa can da ta ga dai babu sauƙi sai a wajen Allah, hakan ne ya sanya ta sakinsa, ta sake sauke luhu-luhun jajayen idanunta a tsakiyar kyakykyawar fuskar Ameer daidai lokacin da ya ja wata ƙatuwar ajiyar zuciya, ta juya don zuwa kiran Likita. Sai dai a maimakon ɗazu da sautin fitar numfashin Ameer ya cika dodon kunnenta, sai ta ji shiru. Cakk ta dakata tana buɗe idanunta da har wani rufewa suke don kansu saboda tsabar kukan da suka sha har suka gaji. Fata take a ce numfashin nasa ne ya daidaita, ya kuma daina duk wasu abubuwa da ta ga yana yi waɗanda ba ta taɓa gani ba. Sai dai wata daƙiƙiyar faɗuwar gaba da ta ji ita ce ta sanya ta sake runtse idanunta na tsawon sakanni, kafin ta buɗe a hankali ta juya idanunta a kan gadon da Ameer ke kai.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 21

Ƙura masa kumburarrun idanunta ta yi tana kallon yadda gaba ɗaya ya wani miƙe a kan gadon, gaba ɗaya sautin nan nasa da take jiyo wa ta daina ji kwata-kwata. Maimakon ta ji farin cikin fahimtar numfashinsa ya daidaita, sai ta ji wata irin faɗuwar gaba ta ziyarce ta, wadda ta sanya ta saurin runtse idanunta. A hankali ta shiga taka wa zuwa kan gadon, har lokacin idanunta a kan Ameer. Hannunta duka biyun ta saka ta riƙo fuskarsa, a sanyaye ta furta

"Ameer." Ta ƙare sunan da ya gama fita da sautin bugawar zuciyarta. Shiru babu amsa. Ba tare da kawo komai cikin ranta ba ta sake kiran sunansa a karo na biyu, nan ma dai shiru, bai kuma motsa ba, haka zalika bai kalle ta ba. Cikin ƙanƙanin lokaci jikinta ya ɗauki rawa. Ta sake yin amfani da duka hannayenta biyu wajen riƙo shi, ta shiga jijjiga shi a haukace tana faɗin

"Ameer ka tashi, Ameer ka tashi mana. Meye haka kake yi Ameer? Ameer.." Ta ƙare maganar cikin ɗaga murya. Dalili kenan da ya sa Hidaya da Sultanah da ke waje saurin shigo wa cikin ɗakin. Ko sanin sun wanzu cikin ɗakin ba ta yi ba, a haukace ta ci gaba da faɗin

"Ameer ka tashi mana Ameer ka tashi don girman Allah." Ta faɗa muryarta na wani irin sarƙewa. A tsorace suke kallon abin da ke faruwa tsakanin Daneen da Ameer, gaba ɗaya tashin hankali ne ya bayyana a kan fuskarsu. Sultanah ta kalli Hidaya, murya can ƙasa ta ce

"Sisi je ki kira Likita." Sai da Hidaya ta lumshe idanunta tana jin wani irin tausayin Daneen ɗin na kama ta kafin ta fice daga ɗakin. Babu daɗewa suka shigo tare da Likitan, har kuma zuwa lokacin Daneen ba ta haƙura ba, ci gaba take da jijjiga Ameer tana kiran ya tashi, ya buɗe idanunsa. Hidaya ce ta ƙarasa ta riƙo Daneen tana faɗin

"Bari Likita ya duba shi." Hannu Daneen ta saka tana shirin ƙwace jikinta a lokaci ɗaya tana furta

"Kin gan shi fa ba ya motsi." Ta ƙare tana nuna Ameer ɗin da hannunta ke wani irin karkarwa. Riƙe ta sosai Hidaya ta yi tana faɗin

"Ehh, ki bari ya duba shi." Ta faɗa cikin rarrashi tana rungumo Daneen ɗin. Tun kafin ta kai ta jikinta take iya jiyo sautin bugun zuciyarta da yake fita da wani mahaukacin gudu. Gaba ɗayansu ƙura wa Likitan idanu suka yi, suna kallon lokacin da ya fara gwada Ameer. Daneen ta kafe shi da jajayen idanunta tana jira ta ji abin da zai faɗa. Zuwa can sai ta ga ya zame abin da ya saka a kunnensa, ya kuma ja zanin da ke a iya cinyar Ameer ya rufe masa fuska, ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa, kafin ya juyo a sanyaye idanunsa a kan Daneen da ita ma shi take kalla tamkar idanunta za su faɗo.

"Ameer ba ya tare da mu, Ki yi haƙuri Allah Ya karɓi abinsa." Ya faɗa a sanyaye, don shi kansa ya matuƙar gigita da mutuwar Ameer ɗin, saboda yadda bayan an gama masa aikin ya gwada masa komai ya ga normal, kuma suke saka masa ran samun lafiya da yardar Ubangiji cikin ƙanƙanin lokaci, sai ga shi cikin awannin da ba su da yawa Allah Ya karɓi abinsa. Kwata-kwata ma ba ta ji abin da ya faɗa ba, saboda yadda hankalinta ya koma kan Ameer da ta ga Likitan ya lulluɓe.

"Me ya sa za ka rufe shi? Kar ya kasa shaƙar iska." Daneen ta faɗa bayan ta yi nasarar fusge hannunta daga cikin na Hidaya, ta ƙarasa tana ƙoƙarin buɗe Ameer.

"Ki yi haƙuri Ameer ya koma wajen mahalliccinsa." Likitan ya faɗa don ya ga alama ba ta fahimce shi ba.

"Ƙarya kake yi Ameer ɗina bai mutu ba, Ameer bai mutu ba, Ameer ba zai taɓa iya tafiya ya bar ni ba."

Please Login or Register in order to submit comment