Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ta ƙare cikin ɗaga murya tana kallon Likitan. Kafin ba tare da ta bi ta kansa ba, ta saka hannu ta yaye lulluɓin da ya yi masa, ya zamana tana iya kallon fuskar Ameer, ta ce tana bubbuga fuskar tasa.

"Ameer ka tashi ka ƙaryata abin da mutumin nan yake faɗa, ka tashi ka yi mini magana Ameer. Ameer don Allah kar ka tafi ka bar ni, kar ka yi mini haka Ameer. Ya ya zan yi da rayuwata idan ya zama babu kai? Mai zan koma na cewa Inna idan ka yi mini haka? Don Allah idan wasa kake yi ka tashi Ameer. Me ya sa zuciyarka ba ta da juriya ne Ameer, me ya sa ka koyi rashin juriya bayan a da kai ne me juriyar. Yanzu ni za ka yi wa haka Ameer? Tafiya ka yi ka bar ni a wannan duniyar Ameer?" Daneen ta faɗa cikin gigitaccen kuka tana girgiza kanta. Idanunta har wani hazo-hazo take gani saboda tsabar kuka.

"Ka tashi Ameer, ni ce fa nake ce maka ka tashi, wai so kake su sake ce mini ka mutu? Ameer me ya sa za ka yi mini haka?" Ta ƙare maganar tana kifa kanta a ƙirjin Ameer, ta shiga girgiza kanta tana fidda wani irin sautin kukan da ke fitowa tun daga can ƙarƙashin zuciyarta. Hannu Hidaya ta kai ta riƙo Daneen, duk da yadda ta kasa ko gezau ne ta ƙi ɗaga jikin Ameer, hakan bai hana Hidaya yin iya ƙoƙarinta ba wajen ɗago ta. Sai kuwa ta faɗa jikinta tana fashewa da sabon kuka, mai tsuma zuciyar mai sauraro. Kuka take irin kukan nan da ke fita haɗe da zafin da ɗan adam ke ji a cikin zuciyarsa.

"Kin ga ya ƙi kula ni koh? Ya ƙi yi mini magana don in yarda da abin da wancan mutumin ya faɗa. Me ya sa Ameer zai mutu ya bar ni? Bai san yadda nake ƙaunarsa ba ne?" I zuwa lokacin Hidaya kasa jurewa ta yi, kawai ita ma sai ta fashe da kukan tana saka hannunta ta dafe kan Daneen da ke kan kafaɗarta. Wani irin tausayin Daneen ɗin na ci gaba da ratsa ta. Nauyin da ta ji ne a jikinta ya sanya ta kai hannunta ta goge hawayen kan fuskarta, daidai lokacin da Sultanah ke faɗin

"Hidaya kamar ta suma fa?" Ta ƙare maganar kamar mai tambaya. Likitan da kansa ya yi kiran nurses aka zo aka fitar da Daneen ɗin da ta fice a hayyacinta gaba ɗaya daga cikin ɗakin. Duka suka bi ta da kallo ba tare da kowa ya ce komai ba.


Lokacin da su Maama suka ji labarin rasuwar Ameer ba ƙaramin tashi hankalinsu ya yi ba. Kusan gaba ɗaya suka ɗauki salati, cike da tausayin Daneen ɗin da wasu daga cikinsu ke kallon ta tamkar 'yar'uwarsu, tun lokacin da ta sadaukar da wani abu daga jikinta zuwa Tareeq.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Tareeq ya faɗa yana runtse idanunsa. Haƙiƙa tabbas ya ji mutuwar yaron, duk da bai taɓa ganinsa ba sai labarinsa. Ita kanta wadda ta ba shi ƙodar har yanzu bai taɓa ganinta ba, duk da yadda yake so ya haɗu da ita ya ga wace ce ita, sannan kuma ya yi mata godiya a bisa wannan sadaukarwar da ta yi. Sai ga shi lokaci guda ana faɗin ɗan'uwan nata da take komai saboda shi ya rasu.

"Ubangiji Allah Ya gafarta masa." Ya faɗa yana jin har zuciyarsa babu daɗi.

"Ameen Ya Rabbi. Allah Sarki yarinyar nan, wallahi tausayi take ba ni, tana matuƙar ƙaunar yaron, ko awa ɗaya ka zauna da ita sai ka fahimci irin ƙaunar da take wa yaron. Ashe ɗazun sallama ta je su yi, kai ya ilahil alameen ka gafarta wa yaron nan, wai ƙaramin yaro da ciwon zuciya." Dada ji ta faɗa jiki a sanyaye.

"Ciwon zuciya?" Tareeq ya faɗa cike da mamaki. Jinjina kai Dada ji ta yi kafin ta ce

"Wallahi kuwa, ai a kan hakan ma aka yi masa aiki. Ashe ashe ma ba zama zai yi ba."

"Ikon Allah! Allah Ya gafarta masa." Tareeq ya faɗa shi ma jikin nasa a sanyaye.


Hidaya ce take zaune a ɗakin da Daneen ke kwance, ta kwashi fiye da awa uku kafin ta farka.

"Ameer." Nan ma da abin da ta farka kenan. A kan laɓɓanta Hidaya ta furta

"Ya Allah." Tana miƙewa ta ƙarasa kan gadon.

"Me nake a nan? Ina ɗan'uwana yake?" Ta faɗa a zabure tana kallon gefe da gefen ta.

"Ki yi haƙuri ki zauna Daneen, don Allah ki yi haƙuri." Girgiza kai Daneen ta shiga yi, daidai lokacin da wasu sabbin hawaye suka fara zubowa sharr sharr a kan kuncinta.

"Shi kenan Ameer ɗina, zuciyata zafi take yi mini, ina jin tamkar za ta fito daga ƙirjina, ta ya ya zan iya jure rashin ɗan'uwana rabin jikina? Wai Ameer ne ya rasu? Ameer fa, ya rasu? Ya tafi kenan ya bar ni? Ba zan sake ganinsa ba, ba zan sake jin maganarsa ba? Ba za mu sake zuwa makaranta tare ba? Ba za mu sake fita kasuwa tare ba? Dada ba za ta sake saka mu aiki tare ba? Ba za mu sake yi wa Innarmu aiki tare ba? Ba zan sake ganinsa yana dariya ba? Ba zai sake zama kusa da ni yana ba ni labari ba, ba zai sake ɗora kansa a kan kafaɗata ya yi kuka ba, ya sanar da ni matsalarsa, ya kira ni Addarsa. Ashe ɗumbin ƙaunar da nake masa ta ƙanƙanin lokaci ce, ashe ba za mu daɗe da shi ba? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Ya Allah Ka sassauta mini abin da nake ji, zuciyata za ta iya tarwatsewa. Wayyo Ameer ɗina." Ta ƙare maganar lokacin da wani sabon kuka ya ƙwace mata. Jikin Hidaya ne ya ƙara yin sanyi, ta shiga share hawaye saboda yadda maganganun Daneen ɗin suka sake jefa ta cikin tausayinta matuƙa.

"Ki yi haƙuri." Shi ne abin da ta iya faɗa a sanyaye. Daidai lokacin da Likitan ya ƙaraso cikin ɗakin, ba tare da ya ce komai ba, ya ƙarasa haɗa allurar hannunsa. Ya yi wa Hidaya alama da kansa, miƙewa ta yi ta ƙarasa inda Daneen take ta riƙe ta, da taimakonta ya yi wa Daneen wadda ke shirin soma magana allura. Wani irin runtse idanunta ta yi na tsawon sakanni, maganar da ta kasa fitowa kenan. Kawai sai ta koma ta kwanta a kan gadon numfashinta na fita da sauri da sauri, A hankali ta ji wani irin bacci na fizgarta, lokaci guda tasirin baccin ya yi nasarar danne duk wani abu da take ji, don haka cikin ƙanƙanin lokaci wani irin nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita. Kusan a tare Doctor Adam da Hidaya suka sauke ajiyar zuciya, ya kalli Hidaya ya ce

"Na yi mata allurar bacci don tana buƙatar ƙwaƙwalwarta ta huta, idan ba haka ba za a iya samun matsala. Ki kula da ita."

"In Sha Allah." Hidaya ta faɗa tana jinjina kai. Daga haka ya fice daga ɗakin, ya yin da ta ci gaba da zama idanunta a kan Daneen ɗin cike da matsanancin tausayinta.

... "Daneen." Hidaya ta faɗa da sauri tana ƙarasawa inda Daneen ɗin ke tsaye, bakin ƙofa tana ƙoƙarin fita daga ɗakin.

"Ina za ki je?"

"Wajen Ameer." Ta ba ta amsar tana kallon ta.

"Ya Ilahy." Hidaya ta faɗa tana dafe goshinta.

"Ina so ne kawai in sake kallon fuskarsa, duk da na san ba magana zai yi mini ba." Sai a lokacin sannan Hidaya ta sauke ajiyar zuciya jin abin da Daneen ɗin ta faɗa.

"Amma dai ya kamata ki je ki ɗan huta tukunna."

"Uhmm.. uhmm." Ta faɗa tana girgiza kai, ta lumshe idanunta tana jin yadda kanta ke juyawa kamar zai rikito ƙasa. Ganin haka ne ya sa Hidaya ta bi bayanta. Har ɗakin da Ameer ke ciki Daneen ta shiga, sai dai ga mamakinta babu kowa a ciki, ta ƙarasa tana sake duddubawa hankali a tashe.

"Ina suka kai mini ɗan'uwana?" Ta tambaya a razane, lokacin da ƙwalla ta kawo idanunta.

"Bari na kira miki Likita." Hidaya ta faɗa tana ficewa daga ɗakin. Bin ta da kallo kawai Daneen ta yi kamar wata doluwa, har zuwa bayan wasu mintina Doctor Adam ya shigo cikin ɗakin. Muryarta har rawa take lokacin da ta furta

"Ina Ameer? Ina ɗan'uwana yake?"

"Ɗan'uwanki Yohanah ya karɓi gawarsa. Mun yi duk wasu abu da ya kamata lokacin kina bacci, ba zai yiwu kuma a jira ki ba saboda ba bacci ne mai ƙarewa da wuri ba, shi ya sa ma ya karɓe shi kawai." Wani irin bugawa da zuciyarta ta yi, shi ne ya sanya ta saurin kai hannunta kan ƙirjinta tana lumshe ido, kawai sai ta koma ta yi yaɓar a kan gadon, daidai lokacin da wani irin jiri ya soma ƙoƙarin kayar da ita, duk kuwa da a zaune take.

"Thank god, zo ka yi magana da ita." Doctor Adam ya faɗa yana kallon Yohanah da ya shigo cikin ɗakin. Babu ɓata lokaci kuma ya fice bayan sun gaisa da Yohanah.

"Daneen." Yohanah ya faɗa yana ƙarasawa inda Daneen take, sai a lokacin ta iya ɗaga idanunta da suka yi mata wani irin nauyi ta kalle shi, tun kafin ya ce komai ta ce

"Ina ka kai mini ƙanina?" Sai sa ya fesar da iska daga bakinsa sannan ya ce

"An binne shi." Amsawar da ciwonta ya yi, shi ne ya tuna mata akwai ɗanyen aikin da ba a daɗe da yi mata shi ba. Ta runtse idanunta tana girgiza kai. Kafin a hankali ta ɗaga su ta kalle shi, muryarta na karkarwa ta ce

"Ameer musulmi ne, kai kuma ba musulmi ba ne." Girgiza kai Yohanah ya yi kafin ya ce

"Kar ki damu, wajen wani maƙocina na kai shi, shi ya yi masa komai na musulmai." Kukan da take ta ƙoƙarin dannewa shi ne ya ƙwace mata, ta zube a wajen tana soma raira shi. Shi kenan Ameer ya tafi ya bar ta, shi kenan da gaske ita da Ameer sai dai a lahira. Kwata-kwata ta kasa cewa komai, sai kukan da take gaba ɗaya jikinta na wani irin rawa.

"And har Alhaji Dikko ma ya samu damar halartar jana'izar." Ya ƙara mata bayani a kai, don cire shakkun da ya gani a tare da ita lokacin da yake magana. Cakk kukan da take ya tsaya, ƙirjinta ya buga a lokaci guda, hawayen da suke sintiri a kan kuncinta suka dakata. Har ba ta san lokacin da ta miƙe a kan ƙafafunta ba, tana kallon Yohana ta ce cikin dakushashshiyar muryarta.

"Waye Alhaji Dikko?" Da mamaki Yohana ke kallon Daneen, ganin da gasken ƙarin bayani take nema ya sanya shi faɗin

"Mahaifin wanda kika ba wa ƙodarki.." Cikin wani irin tashin hankali, ruɗu ta ƙarasa kusa da Yohana, tana kallon cikin idanunsa ta furta

"Ɗansa na ba wa ƙoda?" Ta tambaya a gigice. Jinjina mata kai ya yi alamar tabbatarwa. Ta runtse idanunta, tana buɗewa lokaci guda a kan Yohanah.

"Shin ka san kuwa dalilin mutuwar Ameer?" Nan ta shiga sanar da shi abin da ya faru da Ameer, da kuma ambatar ɗan gidan Alhaji Dikko da Ameer ya yi, kafin ta ɗora da faɗin

"Yanzu kuma kana mini wata magana da na kasa fahimtar ta. Me kake so ka faɗa mini? Me kake so ka ce mini? Faɗa mini tun kafin zuciyata ta buga, ƙaryata abin da zuciyata ke hasaso mini don Allah kar ka ce na ɗauki wani sashe na jikina na sadaukar da shi ga wanda ya zama silar mutuwar ɗan'uwana." Ta ƙare maganar jajayen idanunta da suka kumbura sosai kamar mai ciwon ido a kansa. Sai da Yohanah ya lumshe idanunsa, ya dafe ƙirjinsa yana sauke ajiyar zuciya, saboda shock ɗin da abin da ke fito wa daga bakin Daneen ya shigar da shi, kafin ya soma faɗin.

"Alhaji Dikko dai ɗaya ne cikin garin nan, wanda kowa ya san shi. Kuma ɗa namiji ɗaya gare shi, shi ne kuma wanda kika ba wa ƙodarki." Yohana ya ƙare maganar yana gyara tsayuwarsa, idanunsa a kan Daneen.


Ameer! Ya Allah 😭
Ina miƙa saƙon ta'aziyyata zuwa gare ku, Allah Ya ji ƙan Ameer. A yi haƙuri da abin da aka gani, kar a cinye ni ɗanya. 😂 Dama haka rayuwar take, dukkanmu abin da muke jira kenan, sai dai fatan Allah Ya sa mu cika da kyau da imani.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 22

Wani irin dumm ta ji kunnenta ya yi, jirin da ta ji yana neman kada ta ya sanya ta saurin yin baya ta zube a kan ƙafafunta. Idanunta a rufe suke lokacin da take sake jiyo kalaman Yohana a cikin kunnuwanta, tamkar wanda ke maimaita mata su. Kallon gefen sa Yohana ya yi ko zai samu ruwa ya ba ta ta sha, ko ta ɗan ji sassaucin zafin da ko ba a faɗa ba ya san abin da take ji kenan. Musamman kuma da saboda tsabar ruɗewa hawaye ko kaɗan ya ƙi sauka a kan fuskarta.

"Bari na samo miki ruwa." Ya faɗa yana ƙoƙarin ficewa daga ɗakin. Da sauri ta girgiza kai, lokaci ɗaya tana buɗe idanunta da suka sake haɗewa suka yi wani irin mahaukacin ja. Ta kafe shi da su tamkar mai neman ƙarin bayani. Fahimtar abin da take nufi ne ya sanya shi jinjina kai, kafin ya ɗora da

"Abin da na faɗa haka yake. Amma ki kwantar da hankalin ki, komai zai zo cikin sauƙi." Cikin wani irin zafin nama ta miƙe tsaye a kan ƙafafunta da suke rawa, amma ba ta damu da hakan ba, tsananin tashin hankalin da take jinta a ciki ya sanya duk wani abu da take ji ba ta damuwa da shi. Wani irin huci take fitarwa, gudun numfashinta ya ƙara sauri, ya yin da zuciya da komai nata suka ƙeƙashe.

"In kwantar da hankalina kake faɗa mini? Shin ka manta abin da ya faru ne? In ɗauki ƙodata in sadaukar da ita gurin wanda ya zama sanadin mutuwar ɗan'uwana sannan ka zo kana ce mini in kwantar da hankalina? In kwantar da hankalina ta ya ya? Ta ya ya zuciyata za ta sami sukuni, bayan ƙodata na can jikin makashin ɗan'uwana? Ta ya ya zan kwantar da hankalina bayan wanda ya yi silar mutuwar Ameer na ci gaba da rayuwa ne a dalilin taimakon da na masa. Hasbunallahu wa ni'imal wakeel." Ta faɗa tana dafe kanta da duka hannayenta biyu saboda wani irin juyawa da yake mata. Iska Yohanah ya fesar daga bakinsa, ya jinjina kai kafin ya sauke ajiyar zuciya, cikin kwantar da murya, saboda yadda ya ga yanayin Daneen ɗin ya sauya cikin ƙanƙanin lokaci ya ce

"Nemi waje ki zauna." Idanunta ta ɗaga ta watsa masa, ya dafe goshinsa kafin ya ce

"Ki zauna ki ji abin da zan faɗa miki." Nan ma dai ba ta motsa ba, bai kuma ga alamar za ta zauna ba. Don haka sai ya ƙarasa kusa da ita, a hankali ya soma faɗin

"Ban yi niyyar sanar da ke komai a yanzu ba. Sai dai bisa ga dukkan alamu ƙudirinmu zai iya zama iri ɗaya. Shin kin shirya ɗaukar wa ɗan'uwanki fansa? Idan ehh ne amsar, toh ki zauna mu yi magana." Tun da ya fara maganar take kallon shi har ya dakata. Ta runtse idanunta tana jin yadda kwata-kwata numfashinta ya ƙi saituwa. Tunanin ɗan'uwa rabin jikinta ya tokare mata komai, uwa uba kuma wannan mummunan al'amarin da ya faru, ta rasa inda za ta saka kanta ta ji daɗi. Kukan da take ta ɗan ji sanyi a ranta yanzu ta kasa, ta kasa kwata-kwata, ban da wani irin abu da ya tokare mata ƙirji ya hana ta sakat, babu abin da take ji. Ajiyar zuciya Yohana ya sauke a karo na barkatai lokacin da ya ga Daneen ta zauna, ta shiga jinjina kanta kafin a fili ta ce da dashashshiyar muryarta.

"Zan iya komai saboda ɗan'uwana. Ƙalilan abu ne ba zan iya ba.." Kafin ya ji ta ambaci abin da ba za ta iya ɗin ba, ya katse ta ta hanyar fara faɗin

"Kar ki damu, ki yi shiru kawai ki saurare ni." Ya ɗan dakata a nan kafin ya ci ga da faɗin

"Wato a zahirin gaskiya, ni ɗin nan da kika gani, ban saka hannuna dumu-dumu cikin sha'aninki da ɗan'uwanki haka kawai ba, sai saboda wata manufa. Manufar kuma ba komai ba ce, yanzu za ki ji ta. Na kawo ki asibitin nan ne saboda ki bayar da ƙodarki ga Tareeq, wanda na samu labarin rashin lafiyarsa a wajen wani abokina da yake bibiyar mana rayuwarsa. Na sanar da ke su ne za su biya kuɗin aikin, saboda kar ki saka wani abin a ranki, ina tsoro kar ki saka shakku a kaina, har idan an zo gaɓar da nake so in faɗi ba tare da na yi nasara ba. Sai dai a zahirin gaskiya ba su ne suka biya kuɗin aikin Ameer ba, ni ni ne nan na biya kuɗin, ya yin da su kuma aka sanar da su kin bayar da ƙodarki ne kyauta ga ɗansu ba tare da kina buƙatar ko sisinsu ba. Na san za ki yi mamakin dalilin da ya sa na yi hakan, toh ba komai ba ne face saboda sanin halin Alhaji Dikko da na yi. Idan dai har daga ƙarshe ya fahimci wace ce ke, zai iya ɗaukarki zuwa cikin gidansa, a matsayin wadda kika ba wa shalelen ɗansa ƙoda ba tare da buƙatar ko sisin kwabo ba. Ni kuma dama abin da nake so kenan. Na san idan dai har na ce ki je ki ba su ƙoda a baki kuɗi, daga baya ko da wani abu ya faru, ba lallai su kalle ki ba, tun da zai iya yiwuwa ma daga lokacin da suka ba ki kuɗin ƙodarki shi kenan sun gama da ke. Ko kuma ma ba lallai su haɗu da ke ba, ƙila a yi komai ta hannun likita. Ni ɗin nan da kike gani, fansa nake so na ɗauka a kan Tareeq, shi ya sa na so amfani da ke wajen tura ki cikin gidansu, aikina ba mai wahala ba ne, zan iya cewa naki ma ya fi shi wahala. Idan dai har ki amince sai na sanar da ke abin da za ki yi mini. Sai dai abu ɗaya nake so ki tuna shi ne, ke ɗin kin sani ba kowa ba ce, ba za ki iya yin shari'a da ɗan gidan Alhaji Dikko ba, saboda ba wannan karon ne farko da wasu da dama suka yi yunƙurin yin hakan ba. Ki sani idan dai har kika amince kika aiwatar da abin da zan sanar da ke, toh ki kwantar da hankalinki, ni da kaina zan yi amfani da duk wata dukiya da nake ita, in taimaka miki wajen shigar da Tareeq ƙara, kuma ba zan haƙura ba har sai an ƙwato wa ɗan uwanki haƙƙinsa. Amma fa duk hakan ba za ta yiwu ba, sai kin san yadda kika yi kika shiga gidan na Alhaji Dikko, kika yi duk abin da zan faɗa miki. Daga nan sai ki koma wajen mahaifiyarki ku taho a fara shari'ar mutuwar Ameer. Dukkanmu abu ɗaya ne a ranmu, FANSA! Saboda haka za mu haɗa hannu mu yi aiki tare." Shiru Daneen ta yi na tsawon mintuna bayan da ta gama jin maganganun Yohana. Maganganun da suka shigar da ita cikin duniyar tunani, haɗa su take sake yi waje ɗaya tana ci gaba da fahimtarsu. Zuwa can ta sauke ajiyar zuciya tana kai hannunta saitin zuciyarta da ke ci gaba da bugawa ta dafe.

"Ki yi magana please." Ya faɗa yana kallan ta, a ransa yana fatan Allah dai Ya sa ba ƙin amincewa za ta yi ba. Ba tare da ta damu ta ji dalilin Yohanah na ɗaukar fansa a wajen Tareeq ba, ita dai kawai tun da ta san za ta ɗauki fansa ne a kan ɗan'uwanta shi kenan. Don haka ta buɗe bakinta da ya yi mata nauyi ta ce

"Na amince!" Ta faɗa don tabbas duk wasu abubuwa da Yohanah ɗin ya faɗa ya yi mata. Ta kuma amince da shi ɗari bisa ɗari. Wata gauruwar ajiyar zuciya ya sauke kamin ya ce

"Za ki iya zuwa ki huta, za mu ƙarasa maganar." Miƙewa ta yi ba tare da ta ce komai ba, duk da yadda ta ji jiri na shirin mayar da ita, hakan bai sanya ta komawa ta zauna ba, ta soma takawa a hankali tana runtse idanunta lokaci bayan lokaci.

"Amma kar ki sake ki sanar da su kina da iyaye a can wani waje. Ka da ki sake ki nuna musu kina da iyaye, na sake maimaita miki. Idan har da gaske a kan ɗaukar fansar ɗan'uwanki za ki je gidan yi, toh kar ki sake su san da wannan maganar. Ki bari tukunna sai bayan komai ya kammala sai ki koma wajen mahaifiyarki da zancen mutuwar Ameer, sai dai kuma tare da kyakykyawan labarin kin ɗauki fansa a kan wanda ya yi sanadin mutuwar ɗan'uwan naki." Maganganun Yohana suka daki dodon kunnenta. Ta ɗan dakata kaɗan, amma ba tare da ta juyo ba. Kenan hakan na nufin za ta ci gaba da zama tare da su ba tare da ta koma wajen Innarta ba? Ko da yake lokaci ne ƙanƙani, daga zarar ta samo wa Yohana abin da yake so, shi kenan Tareeq ya shiga hannu, kamar yadda ya sanar da ita, ta kuma san lokacin ne hukuma za ta ƙwatar wa Ameer haƙƙinsa. Don haka kawai ta jinjina kai, a kan laɓɓanta ta furta.

"Toh." Wanda ita kanta ba ta da tabbacin ya ji ta ko bai ji ta ba, don ita kanta ba ta ji sautin maganar tata ta fita ba. Tamkar wata er maye haka ta ci gaba da takawa don isa ɗakin da aka kwantar da ita. Duk kuwa da irin yadda jiri ke ci gaba da kwasarta, yana ƙoƙarin kifar da ita hakan bai sanya ta dakatawa ba. Gaba ɗaya zuciyarta ta bushe, ta ƙeƙashe, Fansar nan dai ita kaɗai ke yawo a cikin zuciya, ruhi da ƙwaƙwalwarta.

Numfashi Yohana ya fesar lokacin da ta ida ficewa daga cikin ɗakin, ya fito da wayarsa yana sake fesar da iska daga bakinsa, har lokacin idanunsa a kan wayar.

"Kai baba shege ne wallahi, ka fiya takura. Toh yanzu ga shi garin abin da na yi da kake ta kushewa ya janyo mana wata hanyar mafi dacewa. Ga shi nan yanzu mafita ta same mu cikin sauƙi. Ya kamata ka sara mini, don wallahi kaina na wuta, ka jira ni gani nan zuwa, idan na zo zan yi maka bayani." Daga haka ya katse wayar yana miƙewa, ba tare da ya bi ta kan kowa ba ya fice daga asibitin.


... Sun fi awa cikin asibitin, amma ta kasa matsa wa ko nan da can ne daga kusa da Tareeq ɗin. Duk da wanzuwar Maama, Ummanta har ma da Abeey hakan bai dame ta ba.

"Ya kamata fa a yi maganar auren yaran nan Yaya." Umman Jawahir ta faɗa daga inda take zaune tana kallon Jawahir. Shi ma Abeey kallon su ya yi kafin ya ce

"Kar ki damu, daga zarar yaron nan ya samu lafiya, za mu yi magana da mahaifin Jawahir a tsayar da ko sati ɗaya ne. Ban ga amfanin ɓata lokacin ba, saboda haka ku ma ku fara shiri." Cikin wani irin farin ciki Umman Jawahir ta ce

"Alhamdulillahi, Allah Ya ƙara girma Yaya, Ya kuma tabbatar mana da alkhairinsa." Murmushi ya yi kafin ya amsa da

"Ameen." Daidai lokacin da Dada ji ta shigo cikin ɗakin, Maama da ba ta daɗe da fita ba na bin bayanta. Ta nemi waje ta zauna lokaci ɗaya tana amsa sannu da zuwan da suke mata.

"Alhassan har yanzu fa sau ɗaya matarka ta zo duba yaron nan." Dada ji ta faɗa tana kallon Abeey. Sai da ya ɗaga kai ya kalle ta sannan ya ce bayan ya sauke numfashi kaɗan

"Ki bar ni da ita Dada ji, babu damuwa." Girgiza kai ta yi ta ce

"A'ah, kar ka yi mata komai. Na tambaya ne dai in ji ko ba ka sani ba, toh amma tun da ka sani ɗin bar ta. Ta ci gaba da duk abin da ta ga shi ne daidai, babu damuwa." Dada ji ta ƙare maganar tana irin murmushin nan na

Please Login or Register in order to submit comment