Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

A sanyaye ta kalli Ameer ta jinjina kanta ta ce

"Toh mu gwada koh?" Ta sake tambayarsa. Sai ya jinjina kai yana murmushi.

"Kin ga idan ba su ɗauke mu ba ma ai dai mun ga gidan nasu mun yi musu wayo." Ya ƙare yana dariya. Ita ma er ƙaramar dariyar ta yi tana sake kallan gidan a karo na biyu.

Sai da gari ya sake yin nisa sannan Daneen ta amince Ameer ya je ya ƙwanƙwasa gidan nan. Shi ko tsoro ma ba ya ji, ita ya bar ta da faɗuwar gaba. Shiru babu alamar za a buɗe. Ya juya ya kalli Daneen, kafin ya ce komai ta ce a hankali

"Ko dai ba gida ba ne?"

"A'ah fa gida ne ke kam." Ya ba ta amsa cike da tabbatarwa kamar da gasken ya sani. Be jira ta sake cewa komai ba ya juya ya cigaba da ƙwanƙwasawa. Babu daɗe wa suka ji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar. Kallan juna suka yi shi da ita, Ameer ya yi murmushi kawai, ba tare da sun ce komai ba suka maida duban su kan wadda ta zo ta buɗe ƙofar. Tun daga sama har ƙasa take kallan su, kamar wadda ta ga baƙin halittu. Tana sanye cikin wata doguwar rigar da ba ta kai ƙasa ba. Hannunta ɗore a kan gate ɗin tana cigaba da kallan su.

"Lafiya?" Ta faɗa kai tsaye tana jefa musu wani kallo. Kallan juna Daneen da Ameer suka sake yi kafin Daneen ta buɗe baki a nutse ta ce

"Aiki muka zo nema, ko kuna da buƙata." Har za ta buɗe baki ta ce ba sa buƙata, sai kuma ta yi shiru. Ta sake kallan Daneen a karo na barkatai kafin ta ce

"Ku shigo." Ta yi maganar tana ba su hanya. Babu musu suka sanya ƙafafunsu zuwa cikin , gaba ɗaya idanunsu a kan cikin gidan, suna kallan irin zubin da aka yi masa, tamkar ba a duniya mutum yake ba. Gaba matar ta yi, ya yin da suka cigaba da bin bayanta.

"Ka sanar wa da Auntyyy ta yi baƙi." Ta faɗa lokacin da suke dab da wuce wani da ke zaune a kan kujera yana danna waya.

"Auntyyy, kin yi baƙi." Wani gabjejen mutum da muryarsa ta fi kama da ta er budurwa ya faɗa yana kallan matar da ke zaune a kan kujera. Sanye cikin doguwar rigar wani material, a ƙalla a shekaru ta ba wa 50 baya. Fuskar nan ta yi ɗau ta yi jajir da farin bature. Sai dai wani sashe na fuskarta duk ya yi baƙi-baƙi, musamman ma daga gefen idanunta. Kanta ɗaure da ture kaga tsiya, ta baza uban ƙananun kitson da suka zuba har gadon bayanta. Kujerun da ke gefen ta kuwa wasu manyan alhazai ne su biyu, da ke sanye cikin shadda ɗinkin babbar riga. Kowanne da ka gan shi ka san kuɗi ya zauna masa babu wai.

"A shigar mini da su ɗaki, ka dai san ina tattauna wa ne mai muhimmanci. Zan ƙaraso daga zarar na gama." Ta ƙare maganar tana wani karairaya kamar wata yarinya er shekara 20.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 12

Kallan juna Daneen da Ameer suka yi, lokacin da suke ƙoƙarin zama a ƙasan kujerar ɗakin da aka shigar da su. Babu wanda ya ce da su ko uffan, haka aka fice aka bar su ciki su kaɗai. A karo na barkatai suka sake kallan junansu kafin Ameer ya ce

"Adda kar fa mu je en yankan kai ne." Ya faɗa yana sakin jakar hannunsa idanunsa sun yi tsilli-tsilli. Wani yawu da ya tsaya wa Daneen a maƙogwaro ta haɗiye tana sake bin ɗakin da kallo ta ce a sanyaye

"Toh mu jira dai mu gani." Ta faɗa tana gyara zaman ta. Cikin ranta tana fatan Allah Ya sa ba gidan en yankan kai suka kawo kansu ba.

Bayan wajen minti 30 suna zaune cikin ɗakin amma shiru babu wanda ya leƙo. Zuwa lokacin sun fara ruɗewa.

"Ni dai wallahi ki tashi mu tafi, hmm uhmm." Ameer ya faɗa yana girgiza kai. Ita ma a ɓangaren ta hakan take saƙa wa a ranta, su tashi su fice daga gidan, don da alama ma waɗanda suka kawo su sun manta da rayuwarsu. Tun da ga shi tun da suka tafi ba su sake bi ta kansu ba. Kafin wani a cikin su ya sake cewa komai, sai ga motsi an shigo cikin ɗakin. A tare suka ɗaga ido suka kalli matar da ta shigo. Wannan matar ce ta ɗazun da ke zaune da wasu maza. Cikin shigar ɗazun dai take, da alama ta gama da waɗancan ɗin shi ne tayo nan. Tun da ta shigo idanunta ke kansu, har ta ƙarasa ta nemi waje ta zauna tana cigaba da bin su da kallo.

"Ina wuni?" Suka haɗa baki wajen faɗar hakan. Sai da ta ɗan yi jimm kafin ta ce

"Lafiya, ku ne baƙin nawa?" Ta faɗa tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta sake ganin gaba ɗaya yanayin Daneen, zubin halittarta da komai na jikinta. Jinjina kai suka yi kafin Daneen ta ce cikin siririyar muryarta

"Eh."

"Kuka ce aiki kuke nema?" Ta ƙare tana jin wani murmushi na taho mata.

"Eh." Daneen ta sake amsa wa a wannan karon ma. Jinjina kai Auntyy ta shiga yi kana ta ce

"Toh, kun samu." Cikin wani irin farin ciki suka ɗaga kai suka kalle ta. Ta sake jinjina kai sannan ta ce

"Ƙwarai kuwa. Abin da nake buƙata kawai sirri, da kuma haɗin kai. Ba na son taurin kai ko kaɗan. Yin sa kan sa na kori mutum na har abada. Idan dai har kun amince shi kenan, maganar kuɗi kuma za ku iya samun sa duk ranar da kuka yi aiki. Ke aikin ki ya fi yawa, saboda haka da ke zan fara." Ba tare da kawo komai a kan zancen ta ba Daneen ta ce

"In Sha Allah ba za ki yi kuka da mu ba."

"Haka nake so." Aunty ta faɗa, kafin ta ɗan ɗaga murya ta ce

"Shanawa zo ka shigar mini da yarinyar nan ciki." Shiru ne ya wanzu a wajen, zuwa can wannan mutumin na ɗazu ya shigo cikin ɗakin. Cikin muryarsa ta mata ya ce

"Aunty ga ni. Ina yarinyar?" Ya faɗa yana jefa idanunsa da yake ta wani fari da su cikin ɗakin.

"Tashi ki bi shi, zai kai ki inda za ki yi wanka ki shirya." Kallan Ameer da shi ma ita yake kalla Daneen ta yi, kafin ta maida duban ta kan Aunty a sukwane ta ce

"Wannan ƙanina ne." Ta faɗa tana nuna shi.

"Kar ki damu, zai zauna a ɓangaren maza ne. Ki je ki yi wanka ki shirya ke dai, shi ma zai je ya gyara jikinsa." Jin abin da ta faɗa ya sanya ta ji daɗi. Ta miƙe tana ɗaukar jakarta. Da sauri Aunty ta ce

"A'ah ajiye ta, akwai komai na buƙata a ciki." Babu musu ta ajiye ta, ta kalli Ameer ta ce

"Bari na je, ka je ka shirya kai ma ka ji? Sai mu fara aikin da wuri ka ga gidan na da girma." Ta faɗa ƙasa-ƙasa. Jinjina kai Ameer ya yi. Daneen ta bi bayan mutumin nan. Tafiya suka soma yi, suna tafiya yana karairaye karairayensa, shi a lallai dole mace. Ita dai sai taɓe ɗan mitsitsin bakinta take saboda haushi da ya ba ta. A haka har suka ƙarasa wani ɗaki. Tsaya wa ya yi a wajen, ya dakata ya yi knocking na ƙofar, zuwa can aka zo aka buɗe. Wata dattijuwar mata ce da a ƙalla za ta yi shekaru 40 ko da wani abun. Tana sanye cikin riga da zani da ɗan'kwali irin na da ɗin nan.

"Toh ke ga baƙuwa nan kin samu. Na san Aunty ta gama miki bayani." Jinjina kai matar ta yi kafin ta kalli Daneen ta ce

"Shigo." Haka nan kawai ta ji ƙirjinta ya buga, har sai da ta kira sunan Allah, kafin ta soma taka wa. Ta saka ƙafarta cikin ɗakin. Daga haka shanawa ya juya, ya yin da matar ta rufe ƙofar bayan Daneen ta shige cikin ɗakin. Kallan ta matar ta shiga yi kamar wadda ta ga sabuwar halitta, sosai ya yaba da kyawun Daneen matuƙa. Don kuwa idan ban da kayan da suke jikinta, a kallan farko idan ka yi wa fuskarta za ka iya kiran ta da er'india, saboda tsananin kyan da Allah Ya ba ta irin mai ɗaukar hankalin nan. Babu abin da ma ya fi tashin kai a kan fuskarta irin cat eyes ɗinta, masu wani irin shape na musamman.

"Mu je ciki banɗakin na ciki." Ta faɗa tana nuna wa Daneen ciki. Kallan inda ta nuna ɗin ta yi, kafin ta ce

"Toh." Ta yi maganar a sanyaye. Sai da matar ta ƙarasa ta haɗa wa Daneen komai da ta san za ta buƙata na wanka kafin ta fito. Daneen ta ƙarasa ciki tana kallan irin tsarin da aka yi wa banɗakin kamar ba banɗaki ba. Don sau dubu ya fi ɗakin da suke kwana a ƙauyen su. Jinjina kai ta yi tana ƙarasawa ciki. Ta fi minti nawa tana tunanin ta inda za ta fara, kafin zuwa can ta yi ƙarfin halin soma wankan a sanyaye. Ta ɗauki wajen minti 30 kafin ta soma ƙoƙarin fito wa, ta mugun jin daɗin jikinta. Har wani sassanyan murmushi ke tashi daga kyakkyawar fuskarta ta fito.

"Mu je in wanke miki kai." Matar nan ta faɗa tana kallan ta. Ita ma kallan ta Daneen ta yi kafin ta juya a hankali ta koma cikin banɗakin. Haka tana ji tana gani, ta buɗe kanta a gaban matar, ta shiga wanke mata sassalkan gashin kanta da ya fi kama da wanda ya jiƙu da tsadaddun maya-mayai. Yadda yake a kwance, a miƙe sai ka ɗauka wani shahararren gyara take masa na fitar hankali. Hakan ne ya sa ba su daɗe ba ta wanke mata kan da ruwa kafin suka fito. Ita ta taimaka mata ta gyara mata kan tsaff ta tufke mata shi da wani ribbon, ya kuwa zuba har gadon bayanta. Tana gama wa kuwa Daneen ta ɗauki ɗankwalin da ta cire ta lulluɓe kanta, don ta riga ta saba idan dai har ba a gaban Innarsu ba ko Ameer ba ta taɓa iya buɗe kanta. Sai ga shi yau wata ce ma ta wanke mata.

"Kar ki mayar da kayan nan, ki bari yanzu zan kawo miki wasu." Matar ta faɗa tana ƙoƙarin juya wa. Bin ta da kallo Daneen ta yi, ba don ba don ba da sai ta ce matar nan ta fiya iyayi. Dan dai kawai babba ce. Ta gyara zama tana cuno bakinta fuskar nan a haɗe.


***
Ta kai wajen mintina goma tana juya wayar a hannunta, ta rasa ta ina za ta fara. Number Abdoul ta daɗe cikin wayarta, ji take kamar ta kira su gaisa ko ta ɗan samu sassaucin abin da take ji a cikin zuciyarta. Sai dai da ta kai hannu za ta kira, sai ta fasa. Ba ta so ta yi wani abu ba tare da sanin Yah Tareeq ba.

"Sultanah." Ta jiyo muryar Maami ta ambata daga gefen ta. Da sauri ta ɗaga kai ta kalli Maamin, don kwata-kwata ba ta ji zuwan ta wajen ba. Tsaya wa ta yi tana kallan ta na tsawon sakanni, kafin ta gyara tsayuwarta.

"Ba ni wayarki na gani." Maami ta faɗa cikin tsare gida tana kallan Sultanah. Jikin Sultanah a matuƙar sanyaye ta miƙa wa Maamin wayar idanunta a kan fuskarta. Daidai lokacin da wayar Maamin ta shiga ruri, ta kalli mai kiran ta, kafin ta maida duban ta kan Sultanah ta ce

"Kar na ji kar na gani Sultanah." Ta faɗa tana miƙa mata wayar. Jinjina kai ta yi da sauri, tana saka hannu ta karɓi wayar. Maami ta yi cikin ɗaki tana amsa wayarta, ya yin da Sultanah ta bi ta da kallo. Ita gaba ɗaya ta kasa fahimtar Maamin a kwana biyun nan. Gaba ɗaya ta kasa gane dalilin da ya sa ta saka mata idanu a kwanakin nan, bayan hakan ba ɗabi'arta ba ce. Yah Tareeq ya fi kowa saka wa rayuwarsu ido ita da er'uwarta, sai dai ga shi cikin kwanaki kaɗan gaba ɗaya Maamin ta bi ta sauya, ta tsiro da wani nau'i na takura, wanda kwata-kwata ba ta saba da shi ba. Ta sake rungume wayar cikin tafin hannunta tana rasa ta inda za ta fara. Gaba ɗaya zuciyarta a dame take, ta rasa yadda za ta yi. Ko ishashshen bacci ba ta samu a kwana biyun nan.


***
"Yah Tareeq don Allah ina son mu yi wata magana." Shi ne saƙon da ya gani a saman wayarsa bayan ya kunna ta. Cikin mamaki ya ɗan ƙanƙantar da kyawawan ƙwayar idanunsa yana kallan number da ta turo saƙon. Maimaita saƙon ya sake yi kafin kai tsaye ya danna kiran number Sultanah yana miƙe wa tsaye. Ya riga ya san idan har irin haka ta faru, toh tabbas wani babban abu ne. Kwata-kwata ba shi da wasa a kan duk wani abu da ya shafi ƙannensa. Sanin hakan ne ma ya sa ko da wani abu ne ya faru, shi suke fara samu da maganar, ko da wata matsala ce shi suke sanarwa. Shi kuma ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya magance musu ita da taimakon Ubangiji. Tun da kuma ya ga Sultanahn ba ta kira shi kai tsaye ko ta masa magana da baki ba, ya san tabbas wani abun ne.

"Sultanah." Ya ambata lokacin da ya fara taka wa kamar mai shirin fita daga office ɗin.

"Na'am Yah Tareeq." Ta faɗa a sanyaye.

"Ba ki da lafiya ne?" Ya tambaya a nutse, kamar wanda ba ya so a ji abin da ya faɗa. Girgiza kai ta yi kamar yana kusa da ita kafin ta ce

"A'ah lafiya ta ƙalau."

"Ohk, kina gida?"

"Eh, ina nan." Ta ba shi amsa tana tashi zaune daga kwancen da take.

"Toh mu haɗu palourn Dadaji." Ya faɗa, sanin da ya yi ta ji shi ne ya sa kafin ta kai ga amsa wa ya tura wayar cikin aljihunsa ba tare da ya kashe ba ya fice daga office ɗin.

***
A ɗaya ɓangaren kuwa tana nan zaune bayan wajen minti 10 sai ga matar ta dawo hannunta ɗauke da wasu kaya cikin leda. Ta ƙarasa inda ta bar Daneen da kalle-kallen tsarin da aka yi wa ɗakin ta ajje kayan kafin ta ce

"Ga shi nan ki saka, zan jira ki a palour. Kar ki daɗe."

"Tohm." Ta faɗa a ranta tana tunanin irin wannan iyayin. Don kawai za su yi musu aikin wanke-wanke da shara har sai sun yi wanka, har da wani wanke kai da wasu kaya. Ita ba ta san haka en birnin suke da fi'ili ba. Matar ba ta sake cewa komai ba ta fice daga ɗakin. Daneen ta bi ledar da kallo, kamar ba za ta taɓa ba. Sai kuma ta janyo ta, ta shiga fidda kayan da ke ciki. Rigar da ta soma gani ta ɗaga tana kalla. Rigar ta fi kama da irin ta arnan nan, domin kuwa idan mutum ya saka, wuyansa duk a waje yake. Don kuwa har rabin ƙirjinsa kan iya fito wa. Ta jinjina kai tana cigaba da kallan rigar.

"Chaɓɓ! Wace er iska? Wallahi ba zan saka ba." Ta faɗa tana hararar kayan. Abin da ta ji ya faɗo daga cikin rigar shi ne ya sanya ta kai idanunta ƙasa. Ta ajiye rigar hannunta, tana kai hannu ta ɗauki abin da ya faɗi ɗin. Da mamaki take bin abin da ta gani a hannunta. Idan dai har idanunta ba su yi ƙarya ba, sharbale ce take gani. Ta kai hannu ta toshe bakinta cike da mamaki. Ita duk sai ta ji kunya ma ta kama ta. Duk da tun a ƙauyensu Inna ta siya mata half vest amma ai ba ta kai ta saka sharbale ba, dududu ma nawa take? Ina ƙudan yake ballantana romonsa? Jefa ta kan gadon gefen ta ta yi tana faɗi a fili

"Babba da ita amma ga wani iskanci." Ta ƙare maganar tana harara tamkar idanunta za su faɗo.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 13

Ta kai wajen mintina goma zaune a gefen gadon tana ta saƙe-saƙe. Tana kuma cigaba da kallan cikin ɗakin. Sai ji ta yi an taɓa ƙofar ɗakin. Da sauri ta ɗaga idanunta ta kalli mai shigowar. Matar ɗazun nan ce dai, tun da ta shigo take kallan ta, har ta ƙaraso. Da mamaki shimfiɗe a kan fuskarta ta ce

"Me kike jira har yanzu ba ki shirya ba?" Ta tambaya tana sauke idanunta a kan kayan da ta ba ta. Ita ma Daneen kayan ta kalla kafin ta maida duban ta kan matar ta ce bayan ta girgiza kai.

"Ba zan iya sakawa ba." Sake kallan kayan matar ta yi, kana ta sake maida duban ta kan Daneen ta ce

"Ba su yi miki bayanin abin da za ki yi cikin gidan nan ba?" Ta tambaya a mamakance. Ba don ta fahimci abin da matar ke nufi ba ta girgiza kai. Matar ta shiga jinjina kai na tsawon sakanni, kafin ta juya ta fice daga ɗakin. Daneen ta bi ta da kallo tana mamakin wane irin gida ne wannan suka kawo kansu? Ko kuwa dama haka en birnin suke? Haka suke saka kaya waɗanda marabar su da babu duk ɗaya ne? Ita dai ba zuwa ta taɓa yi ba, ballantana ta san haka ɗin ne ko ba haka ba. Tana nan zaune bayan shuɗewar wasu mintuna, haka nan ita dai ta kasa samun sukuni da zaman. Ban da bugun zuciyar da ya ɗan yi sanyi yanzu da take ji. Sai kuma yadda kusan rabin hankalinta na kan ɗan'uwanta. Ɗaga dogwayen lashes ɗinta ta yi ta kalli ƙofar ɗakin jin da ta yi an turo. Maimakon ɗazu, yanzu su biyu suka shigo da Aunty. Kallan ta Aunty take yi tun daga ƙasa har sama. Wato duk yadda ake so yarinyar nan ta kai. Ta riga ta san tabbas yau kuɗin da za ta samu suna da yawa. Kyau Allah Ya ba wa yarinyar. Gashi tamkar er india. Duk da yadda take babu wayewa, hakan bai hana kana mata kallo ɗaya ka gano tsantsar tsagoron kyawun komai da Allah Ya ba ta ba. Duk kuwa da ƙananan shekarunta hakan bai hana fitowar dirinta ba. Ita har tunani take idan da ta fi haka girma da ya za ta gan ta? Murmushi ne ya suɓuce mata a kan fuska, lokacin da ta ƙarasa dab da Daneen. Gabanta ya yanke ya faɗi, ta ɗan lumshe kyawawan fararen idanunta da babu kwalli cikinsu.

"Ga waɗannan kayan maza ki saka ana jiran mu." Aunty ta faɗa tana watsa mata wani sassanyan murmushi. Ba ta san lokacin da ajiyar zuciya ta ƙwace mata ba, ta saka hannu ta karɓi kayan, ba tare da ta ce komai ba ta shiga duba su. Kaya ne irin na mutane masu mutunci, riga da skirt. Sai a lokacin ta ji hankalinta ya kwanta. 'Wato kenan wannan ta fi waccan matar hankali' Ta raya hakan a cikin zuciyarta. A fili kuma sai ta ce

"Toh." Daga haka ta juya banɗaki don sakawa. Har matar nan na ƙoƙarin dakatar da ita, Aunty ta yi azamar dakatar da ita ta ce

"Rabu da ita, bi ta a hankali, yarinya ce." Jinjina kai matar ta yi ba tare da ta ce komai ba.

"Ki kawo mini ita palourn ƙasa ina jiran ku yanzun." In ji Aunty.

"In Sha Allah Rankiyadaɗe." Ta amsa da hakan cike da girmamawa. Daga haka Aunty ta fice daga ɗakin. Babu daɗewa Daneen ta fito daga banɗakin sanye cikin kayan da suka matuƙar karɓi halittar jikinta. Sai jan rigar jikinta take tamkar wadda ta ɗage mata. Duk sai take jin ta a takure, duk da kayan ba kama ta suka yi ba. Sai dai duk da haka sai ta tsinci kanta gefe guda tana jin daɗi. A rayuwarta tana son sabon kaya, shi ya sa duk lokacin da Inna-wuro ta siya musu sabon kaya farin cikinsu na ranar daban yake. A hankali ta ɗaga idanunta ta kalli matar da ita ma ita take kalla, daidai lokacin da ta ce

"Yawwah, mu je koh?" Ta faɗa tana murmushin da ya sa Daneen sake kallan ta. Don za ta iya cewa wannan shi ne karon farko da ta ga murmushinta tun shigowar ta ɗakin. Ɗaukar mayafin da ke ajje Daneen ta yi, ta lulluɓa kamar yadda suka saba a ƙauyensu, idan sun tashi saka mayafi musamman da sallah. Ba tare da ta ce komai ba ta bi bayan matar suka soma tafiya. Tafiya mai ɗan tsayi suka yi, kafin suka isa wani ƙaton palour. Kai tsaye matar ta afka ciki, har lokacin Daneen na bayanta suka shige cikin ɗakin. Ƙaton palour ne irin sosai ɗin nan. Aunty na zaune daga gefe can kan wata kujera. Ya yin da wasu maza su huɗu ke zaune kowa a kan kujera mabambanta.

"Hajiya ga ta." Matar nan ta faɗa kanta a ƙasa. Ba kuma ta jira amsar Aunty ba ta fice daga ɗakin. Neman waje Daneen ta yi ta zauna tana jin yadda ƙirjinta ke bugawa. Kafin ta kai ga cewa komai Aunty ta dubi waɗannan gabza-gabzan manyan mutanen da ke zaune gaban ta. Waɗanda a shekaru a ƙalla gaba ɗayan su za su ba wa 40 baya.

"Ga haja nan fa, kai tsaye ku faɗi farashi ba sai an ɓata lokaci ba. Kun san sabgogi sun yi mini yawa." Ta faɗa tana murmushi. Ita dai Daneen ta yi ƙwam, don kwata-kwata ba ta fahimci inda zancen Auntyn ya dosa ba. Amma haka nan kawai kamar ɗazun ta kasa sukuni. Ta ma rasa wanne irin aiki aka ɗauke su ne ita kam. Gaba ɗaya zuba wa Daneen ido suka yi na tsawon mintuna. Kowanne na kallan duk wata halitta ta jikinta da za su iya hasashe, tun da tana lulluɓe ne cikin mayafi. Wani daga cikinsu ya gyara zama, yana murmushi ya ce

"Na karɓa a 500k." Duk tunaninsa za su bar masa ita ne, su ce ta yi ƙanƙanta. Don shi ƙanƙantarta ya soma gani, ya kuma san dukkansu ma za su gan ta. Kuma idan aka yi sa'a ya same ta tabbas zai huta da kyau, don shi kaɗai ya san abin da ya hango. Sai dai tun kafin ya ajiye zancen nasa, wanda ya fi kusa da shi ya ce

"Na ƙara 200k a kai." Cike da mamaki ya kalle shi yana ji tamkar ya miƙe ya masa duka, sai dai maganar da ya ji daga ɗaya gefen nasa ita ce ta sanya shi juya wa jiki a sanyaye.

"Na karɓa a 900k."

"Na cike ya zama 1million." Ya yi ƙarfin halin faɗa don so yake ba sai an ja da nisa ba kawai su bar masa yarinyar ya tafi da ita ƙasar da zai tafi su shana a can. Haka suka dinga yi, kamar waɗanda ke siyan kaya. Idan wannan ya ji wani ya kere su, sai wannan ya ƙara kuɗi masu yawa. Har zuwa lokacin da duk suka yi shiru bayan da ɗaya daga cikinsu ya faɗi kuɗin da ya kere su matuƙa. Abin ya ba wa Aunty nishaɗi, don haka ba ta so aka tsaya a iya nan ba. Ta so sun cigaba da tayawa kuɗin da za ta samu su yi ta hauhuwa. Amma duk da haka, yau ɗin ta samu kuɗi masu yawa ta dalilin Daneen.

"Kar ku damu za a kawo wasu kayan ko zuwa gobe ne." Aunty ta faɗa tana kallan waɗanda suka miƙe. Ɗaya ne kawai ya iya amsa mata, ya yin da ragowar ficewa kawai suka yi. Wanda ya yi nasarar biyan kuɗin da suka shallake na kowa ya ce

"Sai haƙuri fa, kara wa da ni sai an shirya." Ya ƙare yana murmushi. Ita dai Daneen gaba ɗaya duk wani ruwan kanta ya tsotse, jikinta ya yi sanyi, ya yin da duk wasu abubuwa da ke faruwa cikin ɗakin ke sake ruɗa ta, suke kuma tunkuɗa kwanyarta cikin tunanuka barkatai. 'Anya kuwa?' Ta tambayi kanta tana jin yadda zuciyarta ke bugawa kamar za ta faso ƙirjinta. Ita dai ta ji suna maganar kaya, haja, amma kuma ba ta ga wasu kaya a wajen ba. Hasalima idan maganar kaya za su yi, ba ta ga amfanin wanzuwarta a wajen ba.

"Za ki ji Alert yanzu, abin da ya rage kawai ki ba ni yarinya." Murmushi Aunty ta yi

Please Login or Register in order to submit comment