Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi tamkar yana gabanta, sai kuma ta buɗe baki a hankali ta ce

"Ehh."

"Madallah, kamar yadda na faɗa miki ki yi takatsantsan da wayar nan. Zan din ga kiran ki a kai a kai. Yanzu ma kuma na kira ne don na sanar da ke, kar ki ce za ki din ga zama cikin ɗaki, a'ah.. ki din ga ƙirƙiro duk wani abin da zai sa ki din ga ganar mana takun Tareeq. Duk wani takunsa ya kasance kina sane da shi, kina kuma sanar mini, ta hakan ne kawai zai sa mu cimma abin da muke so."

"Tohm." Ta amsa masa bayan ta gama jin bayanin nasa.

"Ya yi kyau." Ya faɗa daga can ɓangaren, daidai lokacin da ta sauke wayar daga kunnenta. Ta yi shiru kamar mai tunani, sai kuma ta sake sauke ajiyar zuciya, kai tsaye ta wuce banɗakin. Sakin baki ta yi tana kallon banɗakin da ya gaji da haɗuwa tamkar ba banɗaki ba. Kai idan ba don ta fara wayewa ba, da yau ne farkon zuwanta garin nan cewa za ta yi ba banɗaki ba ne. Don kuwa tsaff za ta samu wajen kwanciya, tsaff za ta iya yin shimfiɗa ta kwanta abin ta ba tare da ta san cikin banɗaki take ba. Haka dai tana ta kalle-kallenta da mamakin yadda masu ginin gidan 'yan birnin nan ke zama su tsara ko'ina, ciki kuma har da toilet. Ita dai ruwa ta tara a bokiti ta yi wankanta kamar yadda ta saba a gida. Zuwa can ta fito bayan ta mayar da hijab ɗin jikinta. Doguwar rigar abaya ta tarar a kan gadon, ta ɗauka tana kallon ta. Sai kawai ta zumbula ta, ba ta bi ta kan mayafin ba, ta mayar da hijab ɗin. Sai ta cusa wayar cikin kayan da ta cire, ta ninke su waje guda. A ɗakin ta ci gaba da zama, wani sashe na zuciyarta na faɗa mata ta fita, saboda ta din ga ganin motsin Tareeq, ya yin da wani sashen ke raya mata da kar ta yi gaggawa. Yau ne ranar ta farko cikin gidan, don haka ta bari zuwa gobe sai ta fara aiwatar da abin da ya kawo ta.

... Washegari da safe tun da suka fita ba ta sake jin motsin su ba. Saboda sun san da baƙunta, nan suka ajje mata abin karyawa, suka kuma bar ta ta sake sakewa ita ɗaya kafin baƙuntar ta sake ta. Ba ta san me za ta faɗa wa Yohana ba idan ya kira ya tambaye ta yadda ake ciki ba. Don haka kawai ta miƙe, gwara a yi komai da wurwuri, ko zuciyarta ita ma za ta samu sassaucin abin da take ji. Cike da takatsantsan take takawa, tana yi tana duba gefen ta don kar ta haɗu da wata. Cikin sa'a kuwa har ta fito palourn Maama ba ta ga kowa ba. Don haka a gaggauce ta fice daga palourn. Daidai lokacin da shi kuma yake ƙoƙarin wucewa. Da sauri ya yi baya, saboda yadda ya lura sam ba ta san da tahowar wani ba. Cike da mamaki yake bin ta da kallo. Rashin tsammanin ganinsa ya sanya ta ji ƙirjinta ya wani irin bugawa. Sai ta runtse idanunta da sauri ko za ta samu ta ji nutsuwa ta zuwar mata.

"Ina so.. ne na je na.. gaisar da Kaka." Ta faɗa cikin inda inda. Shiru Tareeq ya yi yana kallon Daneen na tsawon sakanni, kafin ya ɗauke kyawawan idanunsa daga kanta. Ba tare da ya nuna ya ji abin da ta faɗa ba ya ce

"Kin tashi lafiya? Ya jikin naki?" Runtse idanunta Daneen ta sake yi a karo na biyu, ta tsani ta ji ya yi mata wannan tambayar, kai gaba ɗaya ma ba ta son wata magana ta haɗa ta da shi. Ji take kamar kar ta amsa, ji take kamar ta yi wucewarta ba tare da ta tanka masa ba. Sai dai kuma ta san hakan ka iya zama abu na farko da zai kawo cikas na zamanta cikin gidan. Ta san hakan ka iya janyo zargi a wajen kowa ma ba shi kaɗai ba. Don haka cikin dakiya ta furta

"Alhamdulillah."

"Ma Sha Allah, Allah Ya ƙara afuwa. Hope dai kin ji daɗin gidan namu?" Ya faɗa ba tare da shi kansa ya yi tsammanin hakan ne zai fito daga bakinsa ba. Don tabbas da wani ɗan gidan nasu na wajen shi kansa sai ya yi mamaki. Ko da yake magana fa ake a kan wanda ta ba shi ƙoda. Shi ma kansa hakan ya ɗauka a matsayin dalilin da ya sa yake son jin lafiyarta a ko da yaushe. A yanzu kam har cikin zuciyarta shiru ta yi niyyar yi, ta damƙe hannunta ɗaya da ke cikin ɗayan. Da ƙyar, kamar wadda aka yi wa dole ta ce

"Ehh."

"Madallah." Ya faɗa, daga haka bai sake cewa komai ba ya wuce parking space a gaggauce. Ɗaga idanunta da har kalarsu ta sauya ta yi ta bi shi da kallo, zuciyarta ban da harbawa babu abin da take yi. Tana kallon yadda yake ɗan waige-waige lokaci zuwa lokaci. 'Duk wasu alamomi sun nuna ba ya son kowa ya lura da fitar tasa, wata ƙila ma wajen fasiƙancin zai nufa, shi ya sa ba ya so a sani.' Ta raya hakan a ranta, daidai lokacin da Ameer ya faɗo mata cikin rai. Ta yi yaƙe tana fesar da iska daga bakinta, don hana kukan da ta ji ya taho mata fitowa. Kawai sai ta juya da sauri ta koma cikin ɗakin da aka sauke ta.


... "Huh Hidaya Yah Abdoul ne, wallahi Yah Abdoul ne Hidaya. Ina zan saka kaina don daɗi, karanta ki gani fa, neman amincewa ta yake a kan soyayyarsa. Ina zan saka kaina don daɗi Sisi?" Sultanah ta faɗa lokacin da Hidaya ke a jikinta ta ruƙunƙume ta kamar za ta ɓalla ta. Dariya mai suna dariya Hidaya take yi, don babu ƙarya ta taya 'yar'uwarta murna ainun.

"Na gani Sisi, Alhamdulillah, Alhamdulillah Alhamdulillah." Hidaya ta faɗa tana murmushi. Sai a lokacin sannan suka koma suka zauna. Daneen da ke gefe kwance kamar mai bacci tana jin duk abin da suke cewa. Sai dai ba za ka taɓa zata ba, duk da kwanciyar da ta yi ba irin ta bacci ba ce, amma za ka yi tsammanin baccin ne ya kwashe ta ba tare da ta sani ba.

"Mu tashi Daneen ta ci abinci tun kafin Maama ta shigo ta ci mana mutunci." Hidaya ta faɗa tana kallan Daneen. Girgiza kai Sultanah ta yi kafin ta ce

"A'ah, bar ta ta yi baccin, idan ta tashi sai ta ci. Yanzu dai mu yi magana a kan abin farin cikin da ya same mu. Ya kike gani? In faɗa wa Maami?" Waro ido Hidaya ta yi ta karɓi wayar hannun Sultanah ta ce

"Hajjaju, ki ba shi amsa tukunna. Maami kuma ba yanzu ba gaskiya, mu bari sai komai ya kankama tukunna." Ta ƙare tana murmushi. Jinjina kai Sultanah ta yi kafin ta ce a sanyaye.

"Ga shi dai cikin farin ciki nake ji na Sisi, amma ban san me ya sa nake jin wata irin faɗuwar gaba ba. Na kasa gane dalili." Murmushi Hidaya ta yi tana kamo hannun 'yar'uwar tata ta ce

"Cikin farin ciki kike jin ki fa Sulty, ina da tabbacin hakan na da nasaba da farin cikin. So ki kwantar da hankalinki, burin ki ya kusa cika In Sha Allah. Yah Abdoul zai so ki fiye da yadda kike son shi."

"Ina fatan hakan." Sultanah ta faɗa a sanyaye.

"Ya kamata mu je gidan Umma, kin san dai halinta da na Jawahir ɗin kanta. Biki yana ta matsowa." Ajiyar zuciya Sultanah ta sauke kafin ta ce

"Wato Hidaya mu sake gode wa Allah da Ya ba mu ɗan'uwa irin Yah Tareeq wallahi, har abada zan ci gaba da alfahari da shi, ki ga dai yadda silar sa nake ta farin ciki. Bikinsa kuma nan da sati biyu, ai dole ne mu tashi tsaye. Daɗin abin kuma Jawahir ce matar. Allah dai Ya tabbatar da alkhairinsa." Taɓe baki Hidaya ta yi kafin ta ce

"Ameen dai, duk da dai ni wallahi ban wani so haɗin nan ba." Duka Sultanah ta kai mata a kan yatsun hannunta ta ce

"Ke Sisi."

"Yoh Allah kuwa." Motsin da Daneen ta yi ne ya sanya Hidaya kallon ta. Ta dubi Sultanah ta ce

"Kin ga kar mu tashi baiwar Allah, zo mu fita mu ba ta waje." Ta faɗa tana jan hannun Sultanah. Babu musu Sultanah ta miƙe a nutse suka fice daga ɗakin. Wani irin gumi ke tsatstsafowa Daneen tun da ta ji abin da suke faɗa. Ta kai wajen mintina goma tana sake tauna maganganun nasu, kafin ta miƙe ta ɗauko wayar nan daga inda ta ɓoye ta. Hannunta har karkarwa yake yi, lokacin da ta ke nemo number Yohana cikin karambani. Sai kuwa ga shi ta gano ta, ta danna masa kira tana jin wani irin zafin zuciya. Idan har Tareeq ɗin ya yi aure ya bar ta cikin gidan me kenan?

"Daneen." Ya ambata tun kafin ta ce komai. Ba tare da ta amsa kiran sunanta da ya yi ba, ta soma faɗin

"Yanzun nan na ji ƙannensa na faɗin aurensa nan da sati biyu. Na rasa me ma zan ce ne ni kam." Cikin wani irin tashin hankali Yohana ya miƙe tsaye, idanunsa har wani ƙanƙancewa suke yi. Ya kai wajen mintina biyu bai ce komai ba, kafin daga baya ya buɗe bakinsa ya ce

"Ya zama dole mu tashi tsaye.. Kamar yadda yake, har yanzu babu abin da ya canja a ƙudirinmu, sai dai a yanzu sati biyu ne da mu ni da ke. A cikin kuma sati biyun ne za mu yi duk abin da ya kamata. Ki shiga cikin jerin abubuwan da suke kan wayar, za ki ga Whatsapp, ki shiga ciki zan tura miki wasu hotuna, ki duba ki karanta da kyau. Zan yi miki bayanin komai ta can. Abin da kawai nake so na tunasar da ke, dole sai kin dage, sai kin cije, kin saka wa kan ki jarumta. Kin ji kowacce kasada ce za ki iya don samun damar cika burina, da kuma naki. Hakan ma ya yi daidai, ko babu komai idan muka san muna da ƙayyadaddun kwanaki, za mu fi yin aikin da sauri. Ki ajje wayar yanzun nan ki shiga abin da na faɗa miki." Daga haka ya yi mata bayanin yadda za ta hau online ɗin yana jiran ta.

"Kar ki manta sati biyu ne kawai da mu." Ya sake maimaita mata kafin ta katse wayar. Tamkar yana gabanta ta jinjina kai, tana jin ko ma wacce irin kasada ce za ta yi domin cikar burinsa, daga nan kuma ya samu ya shigar mata da Tareeq ɗin ƙara, a ƙwatar wa Ameer haƙƙinsa.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 25

Kamar yadda ya kwatanta mata haka ta yi, kamar wadda ya koyawa ga ta ga shi, sai ga shi har ta gane duk abin da ya koya matan. Maganarsa ce kaɗai cikin Whatsapp ɗin, don haka kawai sai ta taɓa sunan nasa da ya yi saving da YOHANA B. Tarin messages ne, duka daga shi ɗaya. Har bayan ta shiga ma wasu ba su daina shigowa ba. Tsayawa kawai ta yi tana kallon ikon Allah. Duk da ya yi mata bayanin komai, amma a wannan karon kuma ba ta san mai za ta yi ba. Amma dai sai ta shiga karanta saƙonnin da suke a rubuce ɗaya bayan ɗaya. Daidai lokacin da wayar ta soma ƙara kenan. Yanzun ma dai shi ke kira, don haka ta ɗaga tana kara wa a kunnenta.

"Kina ji na?" Shi ne abin da ya faɗa. Ta jinjina kai tamkar tana gabansa. Sai kuma tunawa da ta yi ba ya ganin ta ya sanya ta buɗe bakinta ta ce

"Ehh.." Nan da nan ya shiga yi mata bayani tamkar ɗazun. Ta yi shiru tana saurara, da kiyaye duk abin da yake faɗa mata. Wajen mintina 20, sannan suka yi sallama. Sai a lokacin ta koma cikin Whatsapp ɗin suka ci gaba da magana ta nan. Ƙura wa wayar idanu ta yi tana kallon takardun da ya turo mata. Ta iya karatu daidai gwargwado, saboda haka ta shiga karanta duk abin da ta gani rubuce a jikin takardar. Wasu abubuwan ta fahimci me ake nufi, ya yin da wasu suka yi mata tsaurin fahimta. Hakan ne ya sa maimakon ta fahimci abin da take karantawa, sai ya zamana kawai karantawar take yi ba tare da tana fahimtar komai ba. Don inda ba ta fahimta ba, ya fi inda ta fahimta sau fiye da biyar. Taɓe baki ta yi, tana mamakin dalilinsa na son nemo masa irin takardun.

"Ashe ma shi duk a kan takarda yake wannan abin." Ta raya hakan cikin zuciyarta tana ɗan juya manyan idanunta. Shiru kuma ta yi na tsawon mintuna, kafin murmushin gefen baki ya ɗan bayyana a kan laɓɓanta, murmushin da yanzun ya maye gurbin murmushinta tun bayan mutuwar Ameer. Ba ta taɓa tunanin bayan ganin gawar ɗan'uwanta za ta iya ci gaba da walwala ko murmushi ko da kuwa na yaƙe ne ba. Ba ta taɓa tunanin idan Ameer ya rasu za ta iya ci gaba da rayuwa ba. Sai ga shi ta iya rayuwar, har ma ga shi tana iya murmushi. Ta ɗan lumshe idanunta da lokaci ɗaya kalarsu ta sauya daga fari zuwa ja.

"Toh ko dai ya yi haka ne duk saboda ni?" Ta sake raya hakan a ranta. Cikin ƙanƙanin lokaci ta ji tabbas haka ne, idan ma ba haka ba ne, toh ko ma waɗanne irin takardu ne suna da muhimmanci, duk da ita ba ta ga wani muhimmancinsu ba. Don haka ko ma mene ne za ta yi yadda za ta yi ta ɗakko masa takardun. 'Don dai takarda?' ta furta hakan a kan laɓɓanta. Lokaci guda tana lumshe idanunta. A ranta tana sake jinjina kirki irin na Yohanah. Gefe guda kuma tana tuna yadda daga zarar ta ɗakko masa takardun, nan ba da daɗewa ba za ta ga Tareeq a gaban kotu. Asirinsa ya tonu a idon duniya. Sannan kuma a yanke masa hukunci.


... "Ba kwa jan yarinyar nan a jiki, shi ya sa kullum take zaune ita ɗaya. Kada dai shiririta ta mantar da ku alkairinta gare ku." Maama ta faɗa tana kallon Hidaya da Sultanah. Tareeq da ke zaune ya kalle su a ɗan fuzge kafin ya ci gaba da danna wayarsa. Ita kanta Maama da take zaune ba ta yi tunanin yana da abin da zai ce ba, sai lokacin da ta ji ya buɗe baki ya ce

"Kuma ina yawan ba su amanarta ba." Ya faɗa ba tare da ya kalle su ba.

"Yah Tareeq Allah kuwa muna kula da ita. Yanzu haka ma barin ta muka yi ta yi bacci." Hidaya ta faɗa bayan ta karyar da kanta gefe.

"Ke Sultanah maza je kira mini yarinyar nan." Da "Toh." Sultanah ta amsa tana miƙewa. Kai tsaye ta wuce ɗakinsu. Cigaba da zama suka yi cikin ɗakin, lokaci zuwa lokaci Maama kan jefo wata maganar, shi ko Hidaya wani ya amsa ta. Har zuwa lokacin da Sultanah da Daneen suka shigo ɗakin, Daneen na sanye cikin hijab ɗinta kamar koyaushe. Don ko a cikin gidan ma da aka tashi yi mata siyayyar kaya, har hijabi suka kawo mata da yawa. Ba ta sani ba ko gani suka yi tana son shi ko haka nan ne kawai, ita dai ba ta sani ba. A hankali take takawa cikin ɗakin, kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki. Abin da ya ƙara wa tafiyar armashi kenan, sai ta zama kamar tana tafiyar ƙasaita ne. Ƙasan kujerar da Maama ke kai ta nema ta zauna, a nutse ta ce

"Barka da rana."

"Barka ka dai, ya jikin naki?" In ji Maama.

"Alhamdulillah." Daneen ta faɗa har lokacin a sanyaye. Tun kafin ta iso cikin ɗakin ta tabbatar da wanzuwarsa ciki. Sai kuma da ta yo kusa-kusa, sai ta ji duk ya cika ɗakin. Sai dai kuma gefe guda, ita kaɗai ta san abin da take ji. Ta kuma saka ranta ba za ta gaishe shi ba. Akan me ye ma za ta gaishe shi? Waye shi ɗin? Mutumin da ya yi sanadiyar mutuwar Ameer shi za ta gaisar? Lallai kuwa da ta cika cikakkiyar mara lafiya.

"Toh Alhamdulillahi, Allah Ya ƙara afuwa. Sannu kin ji Daneen?" Maama ta faɗa tana murmushi. Ita ma ɗan murmushin ta ƙaƙalo tana gyara zamanta. Kamar ya ce mata ya jiki, ko kuma dai wani abun, sai kawai ta gintse, duk da ya san da wanzuwarta cikin ɗakin, amma bai nuna ba. Don kuwa ci gaba ya yi da danna wayarsa kamar bai san ta shigo ba. Tun da har ba ta san ta gaida babba ba, bari ya kama kansa, ko ita ma ta saita nata. Dakatawa kuma ya yi da danna wayar, ya ɗan yi shiru sai dai har lokacin idanunsa na kan wayar ne. Amma kuma idan ya yi hakan ya yi daidai? Yarinyar da ta ba shi ƙoda ba tare da wani dalili ba fa? Ya ɗan runtse idanunsa hannunsa a kan goshinsa yana murzawa.

"Na bar muku sashena a buɗe, wata a cikin ku ta ɗan je ta gyara mini. Zan ɗan fita ne." Da mamaki Maama ta kalle shi ta ce

"Unguwa kuma Tareeq? Ina za ka je?" Sai da ya ɗan gyara zamansa sannan ya sanar da ita inda zai je. Ta yi masa addu'ar Allah Ya tsare, ƙannensa na amsawa da Ameen sannan ya fice daga ɗakin. Ta lumshe idanunta tana jin wani irin daɗi na ratsa ta, 'Sashensa a buɗe?' Ta sake tuna hakan cikin zuciyarta tana ji kamar ta tashi ta taka rawa. Ba ita ta bar palourn ba sai da Maama za ta wuce ɗaki ta ɗan yi bacci. Ta yi sallama da Maaman, don dama ɗazun su Hidaya sun fita. Daga haka Maama ta wuce daƙinta, ya yin da Daneen ta wuce nasu ɗakin. Babu ɓata lokaci ta kira Yohana ta sanar da shi abin da ke faruwa. Ya yi shiru yana saurarar ta har ta gama, sannan ya ce yana murmushin da har a cikin muryarsa kana iya ji.

"Da gaske?"

"Ehh.." Ta amsa masa a taƙaice, kamar yadda ya taƙaita tambayar tasa.

"Yanzun nan zai fita? Yawwa toh ki yi amfani da wannan damar wajen shiga sashen nasa, kar ki yi sanya. Na san ba yanzu zai dawo ba. Don haka ki yi abin da na sanar da ke. Sannan kuma tsaya, ki sake tabbatar mini da yanzun zai fita." Ba tare da kawo komai ba ta jinjina kai, kafin ta buɗe baki ta ce

"Eh, yanzun nan ya fita."

"Toh shi kenan zan ajje waya. Ki yi duk abin da ya dace ina jiran kiran ki."


.... A fuzge ya kalli wayarsa da ta shiga ringing. Ya ɗauke kai yana maida hankalinsa kan driving ɗin da yake, Abdoul da ke gefensa ya kalli mai kiran. 'Jawahir' Shi ne abin da ya bayyana a kai.

"Ba za ka ɗaga ba ne?" Abdoul ya faɗa yana kallonsa. Lumshe manyan idanunsa ya yi kafin ya ci gaba da driving, kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya sanya hannunsa ya ɗauki wayar. Bai kai ga ɗagawa ba ya ce

"Haka na faɗa maka?" Ya faɗa bayan ya juya ya jefa masa harara. Murmushi kawai Abdoul ya yi, saboda ganin da ya yi ya kara wayar a kunnensa, alamar ya ɗaga. Ajiyar zuciya Jawahir ta sauke kafin ta ce

"Har na cire ran ba za ka ɗauka ba wallahi."

"Saboda haka ne halina?" Ya faɗa cikin basarwa, lokaci ɗaya yana sauya hannun da ya riƙe wayar da ɗayan hannun. Duk sai ta dabirce, ba wai don wani abu ba, sai don yadda ya yi magana ya dake ta, har sai da ta ji wani yarr.

"A'ah.. fa.. ba haka.. nake nufi ba." Ɗa. Jinjina kai kawai ya yi a hankali kafin ya ce

"Toh yanzu dai ya aka yi? Ina driving ne." Ya yi maganar a haɗe.

"A'ah babu komai, kira na yi kawai na ji muryarka, sannan na sanar da kai yadda na yi kewar ganin kyakykyawar fuskarka." Ta ƙare maganar tana ɗan sauke numfashi gami da murmushi. Ɗan sauke wayar ya yi daga kunnensa, yana jin waɗannan kalmomin nata sun daɗe da ginsarsa. Ko ba ma haka ba, ya daɗe da daina jin wasu abubuwa da suka shafi soyayya za su birge shi. Sai dai kuma ita burinta kullum ta faɗi yadda take ƙaunar ganin kyakykyawar fuskarsa, abin da ba ya so kenan, amma ta kasa ganewa.

"Toh ya yi, zan samu na shigo." Ya faɗa kamar a gajiye. Murmushi ta yi tana faɗin

"Yawwah sai ka zo Habiby." Daga haka ya sauke wayar ya ci gaba da driving ɗin da yake.

"Aboki Allah Ya sa sau kana son Jawahir." Abdoul ya faɗa yana kafe shida idanunsa, kamar mau son gano gaskiyar abin da zai faɗa. Tareeq bai kalle shi ba, illa ci gaba da abin da yake yi da ya yi. Bayan shuɗewar minti ɗaya, wanda sai ka ɗauka ba zai amsa ba ne sannan ya ce bayan ya sauke gajeriyar ajiyar zuciya

"Idan dai har na aure ta zan koyi sonta. Abin da na sani kenan." Ya yi maganar kamar ya gama kenan, sai dai kafin Abdoul ya ce komai ya cigaba da faɗin

"Amma idan dai har halayenta sun yi mini." Da mamaki Abdoul ya kalle shi cikin rashin fahimta ya ce

"Ban gane ba? Idan kuma halayen nata ba su yi maka ba fa?"

"Za ma su yi mini, tun da har na amince da ita yanzun." Jinjina kai Abdoul ya yi yana murmushi kafin ya ce

"Toh Allah Ya tabbatar da alkhairi. Ameen." Ya yi addu'a da amsar duka a tare, don ya san halin mutumin nasa ba lallai ya amsa ba. Ko zai amsa ma sai dai ya amsa a zuciya, wanda shi ba zai gane ya amsa ɗin ba.

"Sauke ni nan Tareeq." Abdoul ya faɗa yana kallon inda suke ƙoƙarin wucewa. Babu musu Tareeq ya gangara gefen titi ya tsaya. Suka yi sallama da Abdoul sannan ya tashi motar ya bar wajen.


Sanye cikin hijab ɗinta take ci gaba da tafiya, ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ba ta waige-waige saboda kar a gano ta. Dab da za ta isa sashensa, ta yi kiciɓus da Sultanah da riƙe da waya a hannunta. Dakatawa ta yi tana jin zuciyarta na harbawa, ita ma Sultanah dakatawa ta yi tana kallon ta da murmushi a kan fuskarta ta ce

"A'ah, Daneen.. me ya fito da ke?" Wani daƙiƙin murmushi Daneen ta ƙaƙalo tamkar za ta fashe da kuka.

"Ko kin gaji da zaman cikin ne?" Sultanah ta katse ta da faɗin hakan a daidai lokacin da take tsaka da lalubo abin da za ta faɗa. Har wata ajiyar zuciya ce ta suɓuce mata, sai kawai ta shiga jinjina kai tana murmushi.

"Allah Sarki mu je in taka miki." Lokaci guda gaba ɗaya murmushin ya ɗauke. Ta yi maganar tana soma takawa. Kamar ta rusa ihu haka ta ji, sai dai babu yadda ta iya, haka ta bi bayanta suka soma tafiya. Tun kafin su yi nisa, wayar Sultanah ta shiga ƙara. Daneen ba ta ji abin da aka faɗa daga can ɓangaren ba, ta dai ji Sultanah ta ce a sanyaye

"Toh Maami." Daga haka ta sauke wayar daga kunnenta. Ta kalli Daneen a nutse ta ce

"Ki ƙarasa kawai 'yar'uwa, bari na je ciki, Maami na kira na."

"Tohm." Daneen ta faɗa tana jin wani irin farin ciki na mamaye ta. Sai dai ba ta nuna a kan fuskarta ba, saboda yadda take ji a ranta ya zama dole ta saita kanta, ta sauya takunta, idan ba haka ba a ramfo ta. Sai da ta daina gano Sultanah sannan ta ci gaba da tafiya, addu'a take a ranta kada Allah Ya sa ta sake haɗuwa da kowa har ta je inda za ta je. Addu'ar tata kuwa ta karɓu, don har ta ƙarasa inda yake da tabbacin nan ne sashen Tareeq ba ta haɗu da kowa ba. A wannan lokacin ma sai da ta ɗan tsaya ta dudduba, ta ga babu kowa sannan ta wuce cike da sassarfa, har tana ji kamar za ta kifa. Wata kasalalliyar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta buɗe idanunta da ke a

Please Login or Register in order to submit comment