Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gefen baki.

"Ai Dada ji da kin bar Yaya ya yi mata ko ma mene ne, ban da iskanci kuna cikin gari ɗaya, gida ɗaya a ce wai sau ɗaya ta zo ta duba Tareeq duk uban jikin da yake sha? Mu kan mu da ba ma garin gaba ɗaya hankalinmu na nan, ba shi ne dalilin da ya sa muka dawo yau ba. Ai da ba yau za mu dawo ba. Amma ita ki ga abin da take fa."

"Ummu Kulsum ki yi shiru ki bar mutum da halinsa, akwai ranar ƙin dillanci." Dada ta katse ta da faɗin hakan. Jijjiga kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.


... Tun da ta shigo Hidaya ke kallon ta. Ta tashi da sauri don ta taimaka mata saboda yadda ta ga tana tafiya tana wani rangaji, sai Daneen ta yi amfani da hannunta wajen dakatar da ita kafin a fili ta furta can ciki.

"Zan iya." Hidaya ba ta takura mata ba, ta koma ta nemi waje ta zauna, ya yin da ita kuma Daneen ta ƙarasa kan gadon ta kifa kanta a kan gwuiwarta ta runtse idanunta. Sai a lokacin sannan ta ji wannan abin da ya tokare mata ƙirji ya soma warwarewa, lokacin da wasu hawaye suka taru a cikin idanunta, kafin ka ce mene wannan sun soma sintiri a kan kuncinta. Wasu zafafan hawaye ne, da suke sakkowa da zafin su, wanda kuma ba na komai ba ne sai na nadama, takaici, da kuma baƙin cikin ba da ƙodarta ga mugu, azzalumi, wanda ba ya tsoron Allah!!

"Yah Tareeq!" Hidaya ta faɗa tana miƙewa bayan ta amsa sallamarsa.

"Wai da kanka?" Ta ambata tana kallonsa murmushi fall kan fuskarta. Shi ma murmushin ya ɗan yi kafin ya jinjina kai kawai.

"Alhamdulillahi, sannu, ka ƙaraso Yaya." Babu musu ya ƙarasa shigewa cikin ɗakin a nutse cike kuma da takatsantsan. Ya nemi waje ya zauna kan wata kujera, idanunsa a kan Daneen da ake iya jiyo sautin shashsheƙarta. Sai da ya ɗaga kai ya kalli Hidaya kafin ya ce bayan ya ɗan ƙanƙantar da kyawawan idanunsa.

"Subhanallahi! Har yanzu ba ta bar kukan ba?" Sai da Hidaya ta rausayar da kanta kafin ta ce

"Wallahi kuwa, na rasa yadda zan yi." Hannu ya saka ya ɗan murza goshinsa, har ga Allah ya ji mutuwar yaron nan, ba kuma zai so a ce wadda ta zama silar ci gaba da rayuwarsa tana zaune cikin wannan halin ba. Don haka cikin muryarsa mai daɗin saurara ya ce

"Sannu.."

"Daneen.. Yah Tareeq.." Hidaya ta faɗa tana murmushi.

"Ohh.." ya faɗa yana ɗage girarsa ɗaya. Kamar daga sama ta ji sunan Tareeq da Hidaya ta ambata, sunan da tun da Yohana ya sanar da ita shi ne ɗan gidan Alhaji Yohana ta ji ta tsani jin sunan, ballantana kuma a kai ga ganin mamallakin sunan da ba ta taɓa ganinsa ba. Sai dai tarin abin da ya bar mata danƙare a cikin zuciya na da yawa. Har ba ta san lokacin da ta ɗaga jajayen idanunta ta sauke su a kan Tareeq ba. Karo na farko da ta fara ganin kyakykyawar fuskar Tareeq, wadda a gare ta baƙa ƙirin ce, fuska mafi muni a rayuwarta, fuskar mutumin da ya zamo silar wargajewar farin cikinta. Shi ma wannan ne karo na farko da ya soma ganinta. Idanunta cikin nasa suka faɗa, saboda yadda ta ɗago ba tare da ta shirya ba. Duk da tsananin tasirin da idanun Tareeq ke da shi, hakan bai sanya ta ko da ƙoƙarin janyewa ba ne, sai ma ci gaba da jefa masa wani mummunan kallo da ta yi, tana jin yadda zuciyarta ke ci gaba da zafi, wata uwar wutar fansa na sake ruruwa a ƙirjinta. Cikin basarwa, duk da yadda ya tsargu da irin kallon da take bin sa da shi, sai dai ƙaryar mutum ya fahimci hakan, ya ɗan gyara zamansa kaɗan kana ya ce

"Ya ƙarin haƙuri? Ki yi haƙuri Allah Ya gafarta masa, Ya sa can ta fiye masa nan. Ke kuma Allah Ya saka miki da alkhairi. Na gode sosai, na kuma yaba da ƙoƙarinki." Runtse idanunta Daneen ta yi tana jin yadda kalamansa ke ratsa kunnuwanta, jin tasirin su take tamkar ana soka mata mashi a ƙirji. Jin su take kamar yana watsa mata ruwan zafi tafasasshe.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 23

Har kusan bayan minti ɗaya da gama maganar ba ta ce komai ba. Shi ma kuma bai damu ba, don ko shi wani lokacin ya kan tsinci kansa cikin rashin son yin magana. Musamman ita kuma da take cikin wannan hali, dole ne ya yi mata uzuri. A nutse cike kuma da takatsantsan ya miƙe tsaye ba tare da ya sake kallon inda Daneen take ba ya dubi Hidaya, kafin ya ce komai ta ce

"Yaya sai haƙuri, mutuwar ta taɓa ta sosai wallahi. Tun kuma da aka ce an fitar da gawarsa daga cikin asibitin nan abin ya sake yin gaba. Ka ga duk ta takura kanta, tun ɗazu ba ta umm ba ta umm umm. Kawai dai a takure take." Ta ƙare maganar a dame. Ɗan lumshe idanunsa ya yi, yana buɗe su lokaci guda. A nutse ya ɗan juya ya kalli Daneen kafin ya juyo bayan ya ɗan sauke numfashi. Sai da ya kai hannunsa saitin ƙirjinsa kafin ya ce

"Allah ne Ya sa zan rayu, amma ta sanadin yarinyar nan, saboda haka ki kula da ita tamkar yadda za ki kula da kanki Hidaya. Ko da yaushe ki din ga tuna akwai muhimmiyar tsokarta a jikina, wadda nake tsaye a nan saboda ita." Murmushi Hidaya ta yi, saboda yadda ta ji matuƙar daɗin yadda ya nuna damuwa da kulawa a kan yarinyar da bai taɓa ganinta ba sai yanzun.

"In Sha Allah Yah Tareeq. Ko ba ka faɗa ba wannan ya zame mini dole." Jinjina kai ya yi yana ƙoƙarin ficewa daga ɗakin, Hidaya ta yi saurin faɗin

"Bari na taka maka." Daga haka suka jera suka fice daga ɗakin.

Tun lokacin da ta ji wannan kalaman nasa ta ji wasu irin hawaye sun tarar mata cikin idanu, sai dai ga mamakinta wannan raunanniyar zuciyar tata, sai ta neme ta ta rasa, kawai dai wani irin zafi take ji da kuma raɗaɗi mara misaltuwa. Maganganun nasa sun matuƙar ɓata mata rai, wato nuna wa yake shi ɗin mutumin kirki ne. Abin da ya fi komai tsaya mata a rai, shi ne maimaita yana rayuwa ne ta dalilinta. Idan ta tuna ta sadaukar da ƙodarta ga mutumin da ya zama silar mutuwar Ameer ɗinta, ji take gaba ɗaya ta tsani kanta, ji take da tana da hannun dawo da agogo baya, da ta dawo da shi, ta ƙi ba shi ƙodarta.
Tana nan zaune har zuwa lokacin da Hidaya da Sultanah suka shigo. Ko ɗaga kanta ba ta yi ta kalle su ba, don gaba ɗaya ba ta ƙaunar ganin su. Duk da yadda zuciyarta ke raya mata ba su san waye ɗan'uwansu ba, amma yau dole ta bi abin da wani sashe na zuciyarta ke raya mata. Ci gaba da kaɗaicewa ita ɗaya shi ne mafita. Su ma ba su takura mata ba, suka ci gaba da zama kawai.


Bayan kwana bakwai.
Abubuwa da dama sun faru a cikin kwana bakwai, ciki kuwa har da ci gaba da kula da lafiyar Tareeq da kuma Daneen. Ta kowanne ɓangare Alhamdulillah ana samun ci gaba. Sai dai Daneen da kullum tamkar ana ƙara mata kewar Ameer ne. Duk lokacin da kewar ta tashi, sai dai ta zauna ta yi kukanta ta gode wa Allah. Don ma dai in da aka samu sauƙi, tana jin sassauci idan ta tuna abin da ya ci gaba da zaunar da ita cikin asibitin. Duk da ba ta da tabbacin idan ta koma ƙauyensu za ta tarar da Innarsu, amma dai tabbas daga zarar komai ya kammala can ɗin za ta nufa.
Kullum sai Tareeq ya zo duba ta, ta ɓangaren ta ban da wutar fansa da ke ci gaba da ruruwa a cikin zuciyarta babu abin da zuwansa ke haifar wa sai hakan. Dalili kenan da ya sa ta ga alamun zai shigo za ta fake da bacci ko dai wani abun, wanda zai sa ba za ta haɗa ido da shi ba, saboda yadda take jin wata irin tsanarsa a can ƙarƙashin zuciyarta. Ta ɓangaren sa kuwa, samunta tana bacci ko wani abun bai taɓa damunsa ba. A wajensa ma ya fi son hakan, ko babu komai za ta sake warwarewa sosai. Ya kuma san a cikin kwanakin dole ne ta ci gaba da kewar ɗan'uwanta. A lokacin ne kuma aka sallame su su duka, da niyyar za su din ga dawowa ana duba su lokaci zuwa lokaci.

... "Doctor Adam ya sanar da ni Yohana ɗan'uwanki ne wanda kike da shi shi kaɗai yanzu bayan ɗan'uwanki da kika rasa. Sai dai yau kuma na ji wani batu daban, ya ya abin yake kenan?" Abeey da ke zaune kan kujera ya faɗa yana kallan Daneen da ta yi shiru ita ma tana zaune, kanta na kallon ƙasa. Sai da ta runtse idanunta sannan ta buɗe, ta tuna maganar da suka gama da Yohana yanzu, inda yake jaddada mata kada ta manta, kada ta taɓa ambatar tana da iyaye, idan har da gaske tana son ɗaukar fansar ɗan'uwanta. Don haka ta ɗan sauke numfashi kafin ta soma faɗin

"A wajen kishiyar kakarmu muke, wadda ta haifi Innarmu, ita ce ba ta sonmu, kullum cikin muzguna mana take. Ameer da kansa ya ce mu gudu mu bar mata gidan kafin ta ƙara yi mana wani abun. Shi ne ma dalilin da ya sa muka baro ƙauyenmu. Muna so ne mu gina rayuwarmu kafin mu koma mata." Jinjina kai Abeey ya shiga yi kana ya ce

"Iyayenku fa..?" Wani irin bugawa ƙirjin Daneen ya yi, sam-sam ƙarya ba halinta ba ne, ba ta saba yi ba kwata-kwata, shi ya sa take ta kame-kame. Yanzu kuma ga shi ya yi mata tambayar da ba ta tunanin za ta iya amsa ta. Ta ya ya za ta buɗi baki ta kashe iyayenta? Innarta fa?

"Ayyah, ba dai sun mutu ba?" Ta jiyo muryar Abeeyn kamar ya san me take tunani. Jiki a saluɓe ta ɗaga kai ba tare da ta kalle shi ba, don gani take kamar idan ta ɗaga kai ta kalle shi zai karanto ƙaryar da ta masa.

"Ya Salaam.. Allah Ya gafarta musu, Ya sa sun huta." Ba ta iya amsawa ba, sai shi ya amsa abarsa da kansa. Bai kuma damu da hakan ba, don ya san wataƙila ta tuna da iyayen nata ne. Don haka ya gyara zamansa kafin ya ce

"Ki kwantar da hankalinki, In Sha Allah daga yau kin zama ɗiyata. Zan ɗauke ki na tafi da ke gidana a matsayin 'yata albarkacin wannan alfarmar da kika yi wa shalelena. Za ki rayu a gidana ba a matsayin wata daban ba, a'ah kamar yadda na faɗa miki daga yau ke ɗin 'yata ce. Zuwa nan gaba kaɗan, In Sha Allah ni da kaina zan kai ki ki ziyarci ita kakar taki, ba kuma da niyyar in mayar mata da ke ba. A'ah, zan kai ki ne kawai ku gaisa, don za ki zauna tare da ni ne In Sha Allah har Allah Ya kawo miki mijin aure." Ɗaga raunanan idanunta Daneen ta yi ta kalli Abeey cike da mamakin jin abin dake fito wa daga bakinsa. Lallai wannan mutumin akwai karamci. Duk wasu alamomi kuma sun nuna bai san waye ɗansa ba, bai san abubuwan da yake aikatawa a ɓoye ba. Sai da ta harhaɗa kalmomin da za ta faɗa sannan ta buɗe baki da ƙyar ta furta

"Na gode sosai, Allah Ya saka da alkhairi." Cike da yabawa da hankalin 'yar ƙaramar yarinya mai juriya ya ce

"Allah Ya yi miki albarka, Ameen." Daga haka ya miƙe tsaye yana gyara zaman babbar rigarsa. Kafin ya kai ga ci gaba da tafiya ya ce

"Ki shirya duk abin da kike buƙata, za a shigo a ɗauka, sai ki fito da su Hidaya mu wuce."

"Tom." Nan ma ta faɗa a sanyaye. Sai da ya fice daga ɗakin sannan ta miƙe tsaye, idanunta a lumshe take hango yadda za ta kasance cikin gidan na Alhaji Dikko, da niyyar ɗaukar fansa. Kamar daga sama ta jiyo jagwalgwalalliyar hausarsa lokacin da yake faɗin

"Na gode wa Allah." Dalili kenan da ya sanya ta buɗe idanunta da sauri ta sauke a kansa. Hannunsa ya zura a aljihu ya fito da wata babbar waya ya miƙa mata. Bin wayar ta yi da kallo, kafin ta ɗaga kai ta kalle shi. Ya jinjina kai yana nuna wayar da bakinsa.

"Karɓi ki ji mana." Ya faɗa a ɗan dame. Hannunta ta saka ta karɓi wayar, daidai lokacin da ya soma faɗin.

"Ki riƙe wayar nan, zan din ga kiran ki a cikinta lokaci zuwa lokaci. Ki kasance ko da yaushe kina kusa da ita, kar ki yi nisa da ita, saboda yadda zan din ga jin duk abubuwan da suke faruwa. Kar ki yi wasa don Allah. Kusanci kawai nake so ki samu da 'yan gidan, daga nan zan sanar da ke abin da za ki yi mini." Jinjina kai Daneen ta yi, kafin da muryarta da har lokacin ba ta koma ainahin tata ba ta ce

"Ban iya amfani da ita ba."

"Riƙe, zan sanar da ke yadda za ki yi amfani da komai. Na saita miki komai, idan kuma na kira, za ki ga wajen accept nan za ki danna." Jinjina kai dai Daneen ta kuma yi ba tare da ta ce komai ba. Ya juya baya da sauri jin kamar motsi.

"Bari na tafi, don Allah ki yi komai cikin takatsantsan, don kada a fahimci abin da ya kai ki cikin gidan." Daga haka bai jira ta ce komai ba ya fice daga ɗakin. Wayar hannunta ta bi da kallo na tsawon sakanni, kafin ta juya ta ta shiga kallon bayanta, sai kuma ta matsa ta ja wasu kaya da ta ga Hidaya ta haɗa ɗazun, wanda da alama nata ne ta jefa wayar ciki, bayan ta nannaɗe cikin wani ɗan kwali.

Lokacin da Abeey ya sanar wa da Dada ji hukuncin da ya yanke a kan Daneen, murmushi ta yi ta ce

"Haba kai kuwa Alhassan, kana tsammanin zan ce ban amince ba? Ni kuwa da wace irin uwa ce? Yarinyar da ta ɗauki ƙodarta ta ba wa Tareeq don ka ce za ka ɗauke ta cikin gidanka sai in hana?" Ta dakata a nan tana girgiza kai, kafin ta ci gaba da faɗin

"Ina maraba da ita ɗari bisa ɗari. Allah Ya sa zaman ta alkhairi ne a cikinmu."

"Ameen." Ya amsa yana murmushi.

Duka a harabar ƙaton haɗaɗɗen asibitin suka haɗu, sai a lokacin Daneen ta nutsu tana ƙarewa wannan waje da ake kira da wai asibiti, wannan kyakykyawan waje kallo. A mota suka ɗunguma, inda driver ke jan su. Dab da za su fita daga asibitin ta ji wani irin hawaye masu zafin gaske sun sauka a kan kuncinta. Sun shigo tare da Ameer, sai ga shi ta fita ita kaɗai ba tare da Ameer ba. Lamarin da tun da take ba ta taɓa zata ba. Ba ta taɓa tsammanin akwai ranar da za ta zo su rabu da Ameer ba, rabuwa ma irin ta har abada. Wani sabon miki ne yau ɗin ya tayar mata a zuciya, kewar ɗan'uwanta ta dawo mata sabuwa. Don haka ta shiga rera shi, tana ji ina ma ina ma a ce mafarki ne take yi, ko kuma wani wajen Ameer ɗin ya tafi zai dawo su ci gaba da rayuwarsu. Har suka isa gidan na Alhaji Dikko ba ta daina kukan da yau ɗin ya dawo mata sabo ba. Tun kafin su sauka, masu aiki suka ƙaraso suka soma kwasar kaya suna shigar da su cikin gidan. Ko samun nutsuwar kallan irin ɓarin kuɗin da aka yi a ginin gidan ba ta tsaya yi ba, don gaba ɗaya hankalinta ba ya wajen.

"Sultanah ku je da ita ɓangaren ku." Abeey ya faɗa yana kallan su.

"Toh." Sultanah da Hidaya suka amsa kusan a tare. Sai a lokacin suka kalli Daneen, wadda duk suna sane da ita, sun ƙyale ta ne ta yi kukan, don sun san dole ɗan'uwanta ta tuna shi ya sa take kuka.

"Su kai ta ɓangaren su kuma kamar ya ya?" Maami da ke ƙarasowa wajen ta faɗa tana bin Daneen da wani irin kallo, tamkar ita ce mai gidan. Da mamaki Abeey ya kalle ta ya ce

"Asma'u.." Ya ambata yana kallon ta da matuƙar mamaki shimfiɗe a kan fuskarsa. Sai da ta girgiza kai sannan ta ce

"A'ah, ai wai tambaya ce." Girgiza kai Abeey ya yi ba tare da ya ce komai ba, ya ja siririn tsaki yana barin wajen.

"Toh ita ce yarinyar da ta ba wa Magaji ƙodarta." Muryar Dada ji ta katse mata saƙe-saƙen da take a zuciyarta. Ta san da biyu ta faɗi hakan, don ta san ba ta ƙaunar ta ji ta kira Tareeq ɗin da Magaji. Abin da ba ta iya ɓoyewa kenan har a kan fuskarta. Sai da ta ɗauke kai tana kai wa iska harara, ba tare da ta bari kowa ya ganta ba sannan ta ce

"Amma don kawai ta ba wa Tareeq ƙoda, hakan ba shi ke nuna za a shigo mana da ita har cikin gida ba tare da mun san wace ce ita ba."

"Aou kawai ne ma Asma'u? Ehh lallai.." Dada ji ta faɗa tana jinjina kai. Ɗauke kai ta yi tana jefa wa Sultanah da ke ta narke fuska, tana yi mata alamun ta bari don Allah harara. Ita kuwa ko a jikinta, don ita dai haka nan kawai tun kallo ɗaya da ta yi wa yarinyar ta ji kwata-kwata ba ta kwanta mata ba.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 24

Murmushin yaƙe Tareeq ya yi, wanda ya tsaya iya kan laɓɓansa. Ya girgiza kai, mamakin halin Maamin na kama shi. Ta yadda ita kwata-kwata ba ta iya ɓoye abu, sai ta amayar da abin da ke ranta sannan take samun nutsuwa. Har Dada ji ta buɗe baki za ta sake yin magana, sai kuma ta fasa, ta juya ta kalli su Hidaya ta ce

"Ke Hidaya ku wuce da ita sashenku. Zuwa an jima idan Allah Ya kai mu za mu haɗu." Babu musu Hidaya ta amsa da "Toh." Daneen da ta fahimci da ita ake, sai ta bi bayan su Hidaya.

"Ki huta lafiya Dada ji, bari na raka Tareeq sashensa." Maama ta faɗa ba tare da ta kalli inda Maami take ba. Murmushi Dada ji ta yi kana ta ce

"Tareeq ɗan gatan Maama. Allah Ya ƙara lafiya." Ta haɗe maganar lokaci ɗaya. Ɗan lumshe idanunsa Tareeq ya yi kafin ya yi murmushi ba tare da ya ce komai ba. Dada ji ta wuce sashenta, ya yin da Maama da Tareeq suka wuce sashen nasa. Da kanta ta buɗe ko'ina. Tamkar suna cikin gidan, babu wani abu na datti, ko kuma wanda zai nuna an daɗe ba a shiga ɗakin ba. Saboda kullum duk da ba ya cikin gidan, sai Hidaya ko Sultanah, ɗaya daga cikinsu ta zo ta gyara ɗakin. Har bedroom ta kai shi, sai da ya nemi waje ya zauna sannan ta ce

"Ka samu ka yi wanka, ka yi bacci ka huta sosai yau ɗin nan." Ta faɗa don ta san halinsa sarai. Jinjina kai ya yi yana ɗan murza goshinsa ya ce

"In Sha Allah Maama." Murmushi ta yi, tana jin farin cikin yadda ta ga jikin yaron nata ya yi matuƙar kyau, wanda hakan ke nuna yadda ya samu lafiya. Sai da ta miƙe sannan ta ce

"Bari na wuce."

"Toh Maama." Daga haka ta fice daga ɗakin. Sai da ya tabbatar ta fice daga sashen sannan ya sauke ajiyar zuciya, ya dawo da dubansa cikin ɗakin, idanunsa a kan laptop ɗinsa da ke ajje gefe guda. Ya ɗan fesar da iska daga cikin bakinsa kafin ya miƙe. Kai tsaye toilet ya faɗa, ya yi wankan da ya kwana biyu bai yi irinsa ba da ruwa mai matuƙar ɗumi. Ya kwashe kusan awa guda sannan ya fito, yana jin iska na ratsa ko wacce kafar gashi ta jikinsa. Kai tsaye gaban mirror ya nufa, ya shiga taje kwantacciyar sumar kansa. Ya taje ta tsaff, sannan ya shafe jikinsa da turarukansa masu matuƙar daɗin shaƙa. Cikin wata doguwar rigar jallabiyya ya shirya, wadda kalarta ta karɓi kalar fatarsa. Tattausar fatar jikinsa ban da sheƙi babu abin da take yi. Key ya ɗauka ya ƙarasa ya kulle ƙofar gaba ɗaya, sai ya bar key ɗin ma a jiki. Kai tsaye ya wuce kan gadonsa, ya zauna. Ƙafarsa ɗaya na tankwashe a kan gadon, ya yin da ya saukar da guda ɗaya ƙasa. Ya saka hannunsa ya ja laptop ɗin da ke ajiye ya kunna ta. Kamar yadda ya tsammata ayyuka ya tarar jingim a gabansa. Ya lumshe idanunsa yana tunanin ta ina zai fara. Ɗaya bayan ɗaya ya din ga bin komai da ya kamata ya duba. Har zuwa bayan wani lokaci. Ya fito da wayarsa da tun da ya kwanta a asibiti bai sake bi ta kanta ba ya kunna. Tun kafin ya kai ga buɗe ta kira ya shigo cikin wayar. Ya fesar da zazzafar iska daga bakinsa yana kallan mai kiran nasa. A nutse ya amsa wayar, ya shafe wajen rabin awa suna magana kafin ya katse, ya kira wata number. Daga can ɓangaren aka ce bayan sun gaisa

"Yallaɓai za ka iya shigowa kuwa? Abubuwa da yawa suna jiran ka." Sai da ya ɗan yi jimm kafin ya ce

"Zan yi ƙoƙarin shigowa, ni kaina na yi kewar komai, ba kuma na son abubuwa su haɗe mini, saboda haka zan shigo gobe idan Allah Ya kai mu, ka tura mini duk wani abu da ya kamata na sani kafin na zo." Daga haka ba su daɗe ba ya katse wayar. Haka ya din ga yin waya a daren kusufa-kusufa. Daga wannan sai wannan, wani su daɗe suna wayar, wani kuma ba sa wuce mintina kaɗan. Ranar dai gaba ɗaya haka ta ƙare ba tare da ya rintsa ba. Domin kuwa bayan ya gama abin da zai yi, sai yi shiga yin sallolin da ya saba duk dare, bayan ya idar kuma ya shiga muraja'ar Al Kur'ani.

... Tun da suka shigo ɗakin take kallon sa, ita dai i zuwa yanzu ta daina mamakin irin waɗannan tanƙama tanƙaman ɗakunan na alfarma. Wani irin ƙaton ɗaki ne da ya ji kaya masu kyau matuƙa. Komai a wataye yake ba tare da takura ba, abubuwa kala-kala masu ƙawata ɗaki duk ɗakin ya ji su. Komai biyu ne cikin ɗakin, wanda hakan ke nuna kowa na da mallakinsa. Ta ɗaga kai a hankali tana kallon wani waje da tabbas ya fi yi mata kama da banɗaki, don i zuwa yanzu ta soma fahimtar abubuwa da yawa tun bayan shigowar su cikin garin Kano.

"Ki shiga ki yi wanka." Ta jiyo muryar Hidaya. Da sauri ta kalle ta, sai kuma ta jinjina kai tana ƙaƙalo murmushi. Kawai sai ta yi gaba, wannan ledar da take ta fata a ce an shigo da ita ta hanga, don haka kai tsaye can ta nufa don ɗauke wayar da Yohana ya ba ta.

"Akwai komai na buƙata a ciki, bari mu je mu dawo." Hidaya ta sake faɗa. Sai da ta lumshe idanunta tana jin daɗin hakan, sannan ta ce bayan ta juyo

"Tohm." Daga haka suka fice daga ɗakin a tare. Sauke ajiyar zuciya ta yi, kai tsaye ta nufi jakar nan, ta yi saurin ciro wayar ta riƙe a hannunta. Juya ta ta shiga yi, don kamar yadda ta faɗa masa kwata-kwata ba ta san yadda za ta yi amfani da ita ba. Kamar jira yake, sai ta ji hannunta yana girgiɗi, ta yi saurin kallon wayar ganin dalilin girgiɗin hannun nata daga wayar ne. Sai ta ga number na yawo a kan wayar. Ƙura wa wayar idanu ta yi kamar mai jiran wani abu, sai kuma ta kai hannunta, tana tuna abin da ya faɗa mata. Don haka ta danna 'Accept' tana kara wa a kunnenta.

"Daneen." Ta ji an ambata daga can ɓangaren.

"Na'am." Ta ambata tana gyara tsayuwarta, don ko ba a faɗa ba, ta san shi ne.

"Kun isa gidan?" Ya tambaya. Jinjina kai ta

Please Login or Register in order to submit comment