Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za ta ce ga takamaimai abin da ya kawo su ba, tun da ya zo gidan kuma bai tambayi lafiyar ɗiyarsa ba, ballantana ta ce ko ya kawo su ne domin a duba lafiyarta.

"Ki fito mana, a'ah.." Ya sake faɗa. Hannu ta saka ta buɗe motar ta fito, tana cigaba da kallan cikin asibitin. Be ce da ita komai ba sai gaba da ya yi, babu ɓata lokaci ta bi bayansa. Kai tsaye ɗakin likitan suka shiga, bayan doguwar gaisawar da suka yi da Alhaji Baita, wanda hakan ke nuna sabon da ke tsakaninsu.

"Matata ce wannan, kamar yadda aka saba nake so a yi mata. Idan da akwai maganin da za a ba ta kwata-kwata ta dena haihuwa a ba ta don Allah." Cikin wata irin ruɗewa Inna-wuro ta kalli Alhaji Baita, zuciyarta na wani irin bugu da ya wuce na ƙa'ida. Girgiza kanta ta soma yi tana jin yadda tarin ƙwalla ta cika idanunta. Ilahirin jikinta na rawa kamar mazari, cikin karyayyiyar muryarta da ke rawa saboda tsabagen ruɗewa ta ce

"A'ah don Allah kar ka mini haka, kar ka cuci rayuwata, kar ka zama sanadin katsewar farin cikina, ina son na haihu, ina son ganin 'ya'yana ko da guda nawa Allah zai ba ni ina son su. Don girman Allah kar ka yi mini haka." Ta ƙare lokacin da wasu kyawawan hawaye suka sauka a kan fuskarta.

"Ni kuma ba na so, ba na so kwata-kwata. Ke kan ki kuma kin san ba don ki haihu na aure ki ba. Kar kuma ki yi tunanin don kin ce in ƙyale ki hakan na nufin zan ƙyale ki ko na datse alaƙar da ke tsakaninmu. A'ah zama da ni yanzu kika fara, domin iyayenki sun riga sun ba ni ke halak malak, don haka dole ki zaɓi mafita ɗaya. Ko dai ki zaɓi a cire mahaifar gaba ɗaya, ko kuma ki yi planning na shekaru, wanda za ki din ga sake wa daga zarar lokacin lalacewarsa ya yi." Alhaji Baita ya faɗa yana kallon cikin idanun Inna-wuro. Shiru doctor ya yi yana saurarar duk abin da ke gudana. Lallai Alhaji Baita shege ne, kuɗi kuma kan su shegu ne, tun da ga shi mata kala-kala na yarda su zauna ƙarƙashin Alhaji Baitan duk da yadda yake yadda ya ga dama da su. Kanta ta ji yana wani irin juya mata, tana tsoro kar ta je ta amince da abin da ya faɗa a yi mata abin da ya buƙata tun da farko. Idanunta da ke a rufe ta buɗe a kan fuskar Alhaji Baitan. Ta riga ta san ba ta da wani 'yanci na neman saki a wajen Alhaji Baitan, tun da iyayenta suka riga suka mallaka masa ita, duk da ba ta son sa, kuɗin da ya din ga musu ɓarinsa ne ya sa suka ba shi ita. Ta buɗe bakinta da ya yi mata nauyi da ƙyar ta furta

"Na amince."

"Likita na shekara biyar nake so, kar a yi na ƙasa da haka. Shekarun na cika kuma za mu dawo" Alhaji Baita ya faɗa yana kallan Likitan. Hannunsa da ya haɗe waje ɗaya ya raba su kafin ya ce

"Kar ka damu Yallaɓai. Ka bar komai a hannuna, ba za ka yi dana sani ba."

"Godiya nake Doctor." Alhaji Baita ya faɗa yana murmushi.


.. Har dare ya yi bai nemi ya ga ɗiyar da aka haifa masa ba. Tana zaune cikin ɗakin ta fito daga wanka ya shigo ɗakin, ƙarasowa ya yi yana kallanta lokacin da take ɗaure da towel. Ya lumshe idanunsa kafin ya ce

"Ki ɗauki yarinyar ki miƙa ta sashen 'yan aiki su kula da ita zuwa safiya. Sai ki taho sashena ina jiran ki." Da matuƙar mamaki ta ɗaga kai ta kalle shi, bakinta har rawa yake lokacin da ta furta

"Watanta biyu ne fa..?"

"Ko yau kika haife ta.." Ya ba ta amsar cikin rashin kulawa. Kafin ta kai ga cewa komai ya ce

"Ina buƙatar ki, ki same ni a ɗakina. Ba na son ɓata lokaci." Daga haka ya juya yana shirin ficewa, jin ba ta ce komai ba ya sanya shi dakatawa, ya juya ya kalle ta kafin ya ce

"Kin ji koh?" Jinjina kai ta yi kafin ta lumshe Idanunta daidai lokacin da ya fice daga ɗakin. Ta kai wajen minti 10 a cikin ɗakin tana tunanin abin da ya kamata, kafin ta share hawayen fuskarta ta ja Daneen a jikinta ta rungume, kusan mintuna 2 kafin ta sauke ta, ta shayar da ita na tsawon mintuna masu yawa kana ta miƙe ta fice daga ɗakin. Kai tsaye sashen 'yan aikin ta nufa, zuciyarta cunkushe da tunane-tunane kala-kala. Shin idan ta yi hakan ta yi wa yarinyarta adalci kuwa? Da wannan tunanin haka ta ƙarasa, ta samu Atika da ta yarda da ita sosai ta miƙa mata yarinyar.

"Ki kula mini da ita don Allah. Idan ta farka ki ba ta ruwa ta sha In Sha Allah za ta koma bacci. Zuwa safiya zan zo na karɓe ta." Yadda take maganar a hankali kamar wadda ke shirin yin kuka ya sanya Atika faɗin

"Rankiyadaɗe lafiya kuwa?" Ta tambaya tana karɓar fidar da Inna-wuron ta miƙa mata. Murmushin yaƙe ta yi kafin tace

"Lafiya ƙalau. Ki kula mini da yarinya."

"In Sha Allah Hajjaju kar ki damu." Ba ta iya sake cewa komai ba ta fice daga sashen gaba ɗaya. Kai tsaye sashen Alhaji Baita ta nufa, gaba ɗaya zuciyarta a cunkushe, jikinta kuma a matuƙar sanyaye. Tana shigowa ya miƙe ya rungumo ta fuskarsa ɗauke da murmushin da rabon da ta ta gan shi a kan fuskarsa tun bayan da ya fahimci tana da cikin Daneen. Ƙarasawa ya yi da ita a jikinsa zuwa kan gadon. Kamar koyaushe cikin ƙanƙanin lokaci ya shiga fiddo da zilamarsa a kanta a fili. Duk wata kewar jikinta da ya yi na tsayin kwanaki sai da ya fanshe a daren.

"Shi ya sa kullum nake ƙara jin son ki a cikin zuciyata Fatima." Ya ƙare maganar yana shafa doguwar baƙar sumar kanta da ke kwance kamar wadda ke saka wa relaxer. Wasu hawaye masu ɗumi ne suka samu damar sakkowa zuwa kan fuskarta, waɗannan kalaman da ya faɗa babu abin da suka haifar mata sai raunin zuciya da sake kashe mata jiki. Shin kowacce mace haka take fuskanta a gidan aurenta? Shin da ma aure ana yin shi don wannan abun ne ko kuwa dai ita nata kalar auren ne daban da na mutane? Ba ta taɓa samun farin ciki, ba ta ganin murmushinsa idan ba a kan wani abu da ya shafi jikinta ba.


... Sam ta kasa zaune, ta kasa tsaye. Daga ta je can sai ta dawo nan. Ban da bugawa babu abin da zuciyarta ke yi. Kanta gaba ɗaya ya kulle, tsoro da fargaba take ji matuƙa. Idan dai har ba kuskure ta yi ba, tun da ta dawo daga gida haihuwar Daneen ba ta sake ganin baƙon watanta ba. Duk kuma wasu alamomi da ta ji farkon cikin Daneen shi take ji a yanzu. 'Kar dai abin da take tunani shi ne?' Ta tambayi kanta tana jin sabuwar faɗuwar gaba na ziyartar ta. A hankali ta kai idanunta kan Daneen da ke kwance kan gado tana ta wasa, don yanzu ta sake wayo sosai, ta yi ɓul-ɓul abin ta. Tausayinta ya kama ta, kawai sai ta ji ƙwalla ta taru a idanunta. Daidai lokacin da Alhaji Baita ya shigo ɗakin. Ta yi saurin ɗauke ƙwallar tana juyawa da sauri ta kalle shi.

"Me kike yi ne har yanzu ina jiran ki ba ki ƙaraso ba? Ko kin manta yau kwanan ki ne?" Ya tambaya ba tare da ya damu da yanayin da ya gan ta ba. Girgiza kai ta yi kafin ta ce

"A'ah, Daneen ke kuka na tsaya rarrashin ta." Ta yi maganar idanunta a kan Daneen.

"Toh ki yi da jiki." Ya ƙare maganar yana fice wa daga cikin ɗakin. Ta bi shi da kallo kamar me son gano wani abun. Sai da ya ida ficewa kafin ta dawo da duban ta kan Daneen. Tun dawowar ta gidan har zuwa yau ɗin nan bai taɓa kula ko tambayar lafiyar Daneen ba, bai taɓa jin yaya ta kwana ko yaya ta tashi ba. Bai taɓa damuwa da ya ɗauke ta ba, ko da hakan zai janyo ƙauna ta shiga tsakanin su ba. Shi dai kawai abin da ya sani, tun da ba ya son cikin, ko da ta haihu ma ba ya ƙaunar abin da ta haifa ɗin. Tun da da ma kamar yadda yake faɗa, be aure ta ba ne don ta haihu. Sai da ta tabbatar ta ƙoshi sosai kafin ta ɗauke ta kamar yadda aka saba ta kai ta wajen Atika kafin ta wuce ɗakin Alhaji Baita.


.. Su uku ne zaune a kan dinning suna break, Alhaji Baita, Hajiya Amina sai Inna-wuro da ke zaune, ita ba cin abincin take ba, sai dai ta riƙe cokali ne kawai tana caccakawa cikin abincin. Hira Alhaji Baita da Hajiya Amina (Abokiyar zaman ta) suke, sam hankalinta ba ya wajen. Ƙoƙari kawai take ta iya tare kanta, ta riƙe kanta kar wannan ƙamshin abincin da ke tashi ya sanya ta yin amai. Wani yamutsawa da 'ya'yan cikinta suka yi, shi ne ya sanya ta jefar da cokalin hannunta. Ta guntse bakinta tana jan wata ajiyar zuciya, duk don kar ta yi abin da take ta gudu, ko don gudun tonuwar abin da ta riga da ta tabbatar da lallai tabbas shi ne. Sai dai ina kwata-kwata ta kasa, cikin sauri ta miƙe ta nufi toilet ɗin da ke cikin palourn ta shiga kwara amai kamar za ta amayar da kayan cikinta. Cikin sauri Hajiya Amina ta ajje cokalin hannunta, ya yin da Alhaji Baita har bai san lokacin da cokalin hannunsa ya suɓuce ba. Cikin tashin hankali suka bi ta da kallo, sai dai babu wanda ya iya furta komai. Har bayan wajen minti 5 sannan Inna-wuro ta fito daga banɗakin cikin mutuwar jiki, ba tare da ta kalli inda suke ba, ta fara ƙoƙarin komawa ɗakinta cike da fatan kar ya yi mata magana. Sai dai tun kafin ta yi taku 5 ta jiyo muryarsa cikin kaushi yana faɗin

"Ke!" Dakatawa ta yi jikinta na ɗaukar rawa, ta runtse idanunta daidai lokacin da ta sake jiyo muryarsa yana faɗin

"Kar ki sake ki je ko'ina, ƙaraso wajen nan tun kafin raina ya ɓaci na yi miki abin da ba za ki taɓa mantawa ba." Cike da sassarfa ta juya akalarta zuwa inda suke. Tun kafin ta ƙaraso ta jiyo muryarsa da ke ɗauke da zallar tuhuma ya ce

"Me ye ma'anar wannan aman da kika yi? Me kike nufi? Ciki ne da ke?" Ya yi tambayar duka a jere. Kasa ɗaga ido ta yi ta kalle shi, ballantana ta ce wani abu. Ta rasa me za ta ce, ta rasa ya za ta yi, gaba ɗaya kanta a kulle yake.

"Tambayarki nake ciki ne da ke?" Ya yi maganar yanzu a tsawace. Runtse idanunta ta yi tana jin yadda ta ji muryar tasa har cikin kanta. Ta buɗe baki da niyyar yin magana, ya katse ta da faɗin

"Kar ki sake ki faɗa mini ba daidai ba, sanar da ni abin da ke faruwa da gaske. Ciki ne da ke?" Jijjjiga kai ta shiga yi tamkar wata ƙadangaruwa, har lokacin kuma ba ta kalle shi ba.

"La ha ila ha illal lahu.." Hajiya ta soma faɗa tana tafa hannu. Shi kuwa Alhaji Baita shiru ya yi don gaba ɗaya kansa ya kulle, ya ma rasa me ya kamata ya yi. Ciki? Ciki ne da Fatiman? Abin da yake ta masa yawo a ƙwaƙwalwarsa kenan. Ya sauke wani zazzafan numfashi yana tunanin ta ina zai fara? Tabbas yana ƙaunar Fatima, uwa uba kuma jikinta. Kaff matansa, da duk irin aure-auren da yake har yanzu bai samu irin Fatima ba. Duk kuwa da ta haihu, amma kullum jin ta yake kamar sabuwa. Sai dai duk da haka ba ya tunanin ze iya zama da ita. Don yana da tabbacin idan dai har ya cigaba da zama da ita, toh kowacce shekara sai ta haihu. Be san yawan adadin shekarun da za su ɗauka tare ba tare da ya gaji da ita ba, kenan 'ya'ya nawa za ta haifa? Ya kuma san ko me ze yi ba za ta yarda a yanke mahaifarta ba, don kuwa ya kwana da sanin ko kaɗan dukiyarsa ba ta gaban ta.

"Ciki kika sake yi?" Tambayar da ke ta masa yawo a ƙwaƙwalwa, ta samu damar fitowa kan laɓɓansa yana kallan Inna-wuro. Da mamaki ta ɗaga jajayen idanunta tana kallansa, kafin ta kai ga cewa komai Hajiya Amina ta ce

"Toh ai Alhaji ina ganin kamar laifinka ne, garin yaya ka bar ta ta shigo cikin gidan nan da mahaifa? Ka san fa 'yan ƙauye da ma akwai zilama." Be bi ta kan abin da Hajiya Amina ta faɗa ba, duk da ta wani ɓangaren maganar tata ta shige shi, amma kuma tun da mai afkuwa ta afku zancen yaushe kuma?

"Wai ba kafin mu shigo gidan nan sai da na kai ki asibiti aka tabbatar mini an tsayar da haihuwar ba? wace irin zulamammiya ce ke? Duk da planning ɗin da kika yi amma sai da kika ɗauki ciki?" Alhaji Baita ya ƙarasa maganar yana jin yadda zuciyarsa ke tururi, tarin baƙin ciki da ɓacin rai na sake tunzura fusatacciyar zuciyarsa.

"Ka yi haƙuri Alhaji." Hajiya Amina ta faɗa cikin salo na kwantar da murya.

"Kin ga maza je ki tattara kayanki ki bar mini gida, ki ɗauki abin da kika haifa, da wannan cikin da ke jikinki ki fice a gidan nan. Wallahi ba zan iya cigaba da zama da ke ba. Idan na ce duk macen da na aura za ta haihu, 'ya'ya nawa zan tara kenan? Ni ba don ki haihu na auro ki ba. Na auro ki ne don ina son zama da ke ke kaɗai, amma saboda ƙauyanci da gidadanci cikin watannin da za a ƙirga su a hannu har kin yi ciki biyu? Ba zan iya ba. Ki je na sake ki saki uku, na kuma yafe abin da kika haifa da kuma wanda za ki haifa nan gaba. Ki je ki riƙe kayanki ba na so, ke kar ma ki taɓa tunanin suna da uba. Kar kuma ki taɓa nuna musu suna da uba. Ki manta cewar ba ke kaɗai kika haife su ba, na yafe har gaban abada. Ke ke kaɗai kika haife su. Saboda haka ke da kika haifa ke kaɗai suke da. Na bar miki su halak malak."

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 03

__ Idanunta a runtse suke tun daga lokacin da ya fara magana har ya kai ƙarshe. Duk yadda ilahirin jikinta ke rawa hakan be sanya ta yi yunƙurin nema wa kanta waje ta zauna ba. Kalaman Alhaji Baita ne kawai ke cigaba da yi mata amsa-kuwwa cikin kunnenta. A hankali wasu hawaye masu ɗumi suka gangaro daga cikin Idanunta da har lokacin suke a rufe. Cikin ƙanƙanin lokaci bugun zuciyarta ya ƙaru fiye da farkon lokacin da ya fara magana.

"Ki bar wajen nan." Ya faɗa a zafafe yana nuna mata hanya, ba tare da ya kalle ta ba. Don ba ya so ya kalle ta ɗin ka da wani abu ya ɗarsu a ransa, har ya saka ya yi nadamar abin da ya aikata. Ya riga ya tabbatar wa kansa daga yau Fatiman ba tasa ba ce, komai nata ya zama ba nasa ba. Saboda haka kamar yadda ya yanke alaƙarsa da ita har abada ba ya so ya sake kallon fuskarta, jikinta ko kuma ma duk wani abu da ya dangance ta. Maganar da ya yi ita ce ta sake tuna mata da zafafan kalaman da suka yi nasarar jefa zuciyarta cikin wani irin yanayi mara misaltuwa. A hankali ta ɗaga ƙafafunta da suka mata nauyi ta soma takawa don barin wajen, daidai lokacin da ta buɗe idanunta da suka rine suka yi jajir, hawaye sun cika sun tumbatsa cikin idanun, wanda hakan ya sanya take ganin dishi-dishi. Bugu da ƙari kuma maganganun nasa da suka sanya jinta da ganinta ya ɗauke na wucin gadi. Babu abin da ke cigaba da zama daram a ƙwaƙwalwarta, suka fi kuma kowaɗanne kalmomi maimaita kan su sai

"Ke da kika haife su ke kaɗai suke da. Na bar miki su halak malak."

Da ƙyar ta iya kai kanta ɗaki, sai a lokacin zuciyarta da ke cunkushe, ta ba ta damar fashewa da wani irin kuka me cin rai. Kukan da ke fito wa tun daga ƙasan zuciyarta, me zafi wanda ke taimakawa wajen rage raɗaɗin da zuciyarta ke ciki. Ta kwashe fiye da rabin awa tana kukan, ta kasa hana kanta dena wa. Ba sakin da Alhaji Baita ya yi mata ne ya fi damunta ba, face yadda ya nuna ba ya son abin da ta haifa, da wanda za ta haifa nan gaba, wanda ke cikinta a yanzun. Shin ya rayuwar 'ya'yanta za ta kasance idan suka taso suka gane waye mahaifinsu? Wane hali za su tsinci kansu duk lokacin da suka ji labarin mahaifinsu ba ya son su tun samun cikinsu har haihuwarsu? Har ma an saki mahaifiyarsu ne saboda haihuwarsu? Haihuwar da wasu suke ƙarar da dukiyarsu da duk abin da suka mallaka don su samu. Haihuwar da a kanta wasu suke fitowa daga gidajensu. Lallai Allah mai mabambantan halittu, masu kuma mabambantan halayyya. Wani numfashi ta ja tana runtse idanunta, kafin ta miƙe ta ƙarasa inda Daneen take, ta ɗauke ta ta saɓa a baya. Hijab kawai ta ɗauka, ta ɗauki kuɗin da ta san ze kai ta gida, bayan nan ba ta taɓa komai da ke cikin gidan ba. Don kuwa ba ta buƙatar komai da ya dangance shi kuma. Kai tsaye ficewa ta yi daga ɗakin. Dab da za ta gifta inda suke zaune, Alhaji Baita ya saka hannu cikin aljihunsa ya fito da kuɗi, ya jefa mata ƙasan ƙafarta daidai lokacin da ya ce

"Ki yi kuɗin mota."

Ba ta yi niyyar tankawa ba, sai dai yadda zuciyarta ke bugawa, tana ƙara zafafa da wannan cin mutuncin da ya mata ya sa ta ji ba za ta iya ba. Shirun da za ta yi tamkar nuni ne da ta ji haushin fitar ta daga gidan, wanda ta san tabbas hakan ze yi masa daɗi, ba ma shi kaɗai ba har Hajiya Amina. Sai dai tana dakatawa da niyyar juyawa ta yi masa magana, zuciyarta ta ƙeƙashe, tarin takaici ya cika zuciyarta. Ba ta jin tun da take a rayuwarta akwai fuskar da ba ta ƙaunar sake gani kamar ta Alhaji Baita. Kamar yadda ya ce babu shi babu ita, babu kuma shi babu 'ya'yansa, toh har abada sun rabu ɗin kenan. Daga haka ta gewaye kuɗin ta fice daga ɗakin ba tare da ta sake ko da waiwayowa ba ne.

... A ƙofar gidansu ta tsaya tana kallan ƙofar gidan kamar wadda ta fara ganinsa yau. Ta yi shiru tana cigaba da kalla zuciyarta na harbawa. Tunanin abin da ke cikin gidan take, tunanin da wane ido za ta kalle su ta sanar da su Alhaji Baita ya sake ta take. Sai dai ko ma mene ne zai biyo baya ta shirya karɓarsa. Tun da ba ta da inda ya wuce mata nan ɗin. Tuna hakan ya sanya ta ɗaga ƙafafunta ta jefa cikin gidan nasu, da sallama ɗauke a bakinta ta shiga gidan.

"A'uzubillahi minash shaiɗanir rajim." Shi ne abin da Dada ta ambata ƙirjinta na bugawa tana kallan Inna-wuro. Dakatawa Inna-wuro ta yi, jin da ta yi tun a lokacin gaba ɗaya ƙwarin gwuiwar da ta ji kafin ta shigo gidan yana rugujewa yana yin nasa wajen. Tun kafin ta ƙara taku ɗaya Dada ta matso tana faɗin

"Me ya dawo da ke gida kuma? Me kika zo yi mana a gida?" Buɗe baki ta yi jiki a matuƙar sanyaye ta ce

"Dada.."

"Kar ki sake ki ƙara kiran sunana. Daga ganin idanunki akwai abin da kika shuka, faɗa mini me ya faru. Me ya dawo da ke gida?" Girgiza kanta ta soma yi, daidai lokacin da wasu sabbin hawayen suka sake cika idanunta taff, ta buɗe baki kamar me koyon magana ta ce

"Ya.. sake.. ni."

Salati da sallallamin da Dada ta soma yi shi ne ya fito da Baffa daga ɗaki, ya ƙaraso yana faɗin

"Lafiya kuwa Uwar gida?" Ya ƙarasa maganar daidai lokacin da idanunsa suka sauka a kan Inna-wuro, da zuwa lokacin hawaye har sun jiƙa fuskarta.

"Inna-wuro?" Ya ambata yana kafe ta da idanunsa. Ɗaga jajayen idanunta ta yi ta kalli Baffan, daidai lokacin da Dada ta fashe da kuka.

"Subhanallahi me ya faru?" Baffa ya tambaya yana kallan Dada.

"Tambayi 'yarka, tambayi 'yarka kai kam. So take ta kashe ni wallahi" Shi ne abin da take maimaitawa cikin tsananin ƙunar zuciya. Juyawa ya yi ya kalli Inna-wuro, ya buɗe baki da niyyar tambayar ta, Dada ta ji ba za ta iya tsayawa har sai ta faɗa da bakinta ba. Don haka ta buɗe bakinta ta ce

"Alhaji Baita ya sake ta, ya sake ta. Mu kuma shi kenan mun shiga uku."

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Baffa ya ambata yana kallan Inna-wuro da ta kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ne. Idanunta na kallan ƙasa cikin rashin sanin abin yi. Kamar wadda aka tsikara Dada ta miƙe ta dawo gaban Inna-wuro, ta goge hawayen fuskarta sannan ta ce

"Saki nawa ya miki?" Ta tambaya cikin tsananin tashin hankalin da ba ta ji makamancinsa lokacin da Inna-wuron ta ce an sake ta ba.

"Ɗaya ya miki koh?" Dadan ta sake ambata kafin Inna-wuron ta kai ga cewa komai. Cike da tsoron jin abin da zai fito daga bakinta. Shiru Inna-wuro ta yi tana tunanin ta inda za ta fara, sai dai kuma tana tsoro kar Dadan ta kawo mata duka, saboda wani irin kallo da take bin ta da shi.

"Saki uku." Ta faɗa jikinta na ƙarasa mutuwa gaba ɗaya. Ta riga ta saddaƙar yau ɗin Allah ne kaɗai ze raba ta da Dadan. Sai dai Dada kasa cewa komai ta yi, ban da komawa da ta yi baya ta yi zaman ɗabaro ta yi shiru, ban da bugawa babu abin da zuciyarta take, ta kuma kasa furta komai.

"Inna-wuro ashe ba ki da hankali? Me kika yi wa mijinki ya sake ki?"

"Baffa babu abin da na masa.. Wallahi ban masa komai ba Baffa." Ta ƙare maganar tana kuka jajayen idanunta a kan Baffa. Cike da fatan yau ɗaya ya ji tausayin ta, ko da kafaɗarsa ne ya ba ta ta ɗora ta yi kuka ko da za ta ji sassaucin abin da take ji a cikin zuciyarta.

"Ƙarya kike munafuka, ƙarya kike yi. Yo ko yankar namanki yake ai kya zauna. Uban me bakinki yake lokacin da kika ji yana ƙoƙarin ambatar sakin, mai ya hana ki saurin katse shi ba tare da ya ƙarasa ba. Ashe mahaukaciya ce ke Inna-wuro ban sani ba? Ashe bayan kanki da kike yi wa baƙin ciki har mu kike yi wa? Wallahi ko ki faɗa mini dalilin da ya sa ya sako ki ko in miki shegen duka yanzun nan. Ki buɗe baki ki mini magana kafin na ci ubanki." Duk da zagin ta da ta yi hakan be sanya Baffa ko da kallan ta ne ba, ballantana ya nuna ya ji zafin hakan. Shi kansa kallan Inna-wuron kawai yake don jin amsar da za ta fito daga bakinta.

"Baffa ciki ne da ni, shi kuma ba ya so. Wallahi shi ne kawai dalilin, ya ce ya yanke duk wata alaƙa ta da shi, har 'ya'yana ma."

Ɗauke wuta gaba ɗaya kansu ya yi, musamman Baffa. Ya rasa me ze ce? Ya ma rasa ta ina ze fara. Sai kawai ya kama bakinsa ya yi shiru yana jira ya ji abin da Dada za ta faɗa. Wane hukunci za ta yanke a kan Inna-wuron wanda duk hukuncin da ta yanke ya riga ya zauna daram.

"Kin cuce mu wallahi, kin cuce mu." Dada ta yi maganar cikin ƙunar zuciya, tana fashewa da wani sabon kukan baƙin ciki. Ji take kamar ta rufe Inna-wuron da duka ko ta ji daɗi, sai dai yadda take jin zuciyarta idan ta fara dukan ta san za ta iya mata lahani. Tsabar takaici ma ta kasa ko da

Please Login or Register in order to submit comment