Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan take buƙatar ji ba. Don haka ta luma ƙwayar idanunta cikin na likitan ta ce

"Don Allah ya jikin ƙanina?" Sai da ya kalle ta, ya ɗan yi jimm kafin ya ce

"In Sha Allah zai samu sauƙi. A je a kawo gwajin nan yanzun nan, za mu san abin yi ne bayan an yi su." Cikin sauri ta jinjina kai, ba ta sake cewa komai ba ta fice daga office ɗin. Sai kuma da ta fito ɗin sannan ta dakata tana kallan takardar tamkar idanunta za su faɗo. Sai a lokacin ƙwaƙwalwarta ta tuna mata babu ko sisin kwabo a jikinta, ba kuma ta da wanda za ta tunkara ya ba ta kuɗin yin gwajin. Ta lumshe idanunta tana ambatar sunan Allah daidai lokacin da ƙirjinta ya wani irin bugawa. Buɗe idanunta ta yi, ta shiga jefa su cikin asibitin kamar mai neman wani abu. Cikin rashin sanin abin yi ta shiga taka ƙafafunta, tunani birjik cikin ƙwaƙwalwarta, mafita kawai take nema, mafita kawai take so. Ameer take so ya sami lafiya, toh amma ta ya ya? Tana ci gaba da waɗannan tunanukan sai tsintar kanta ta yi cikin harabar asibitin. Ta sake wuwwulga idanunta tana kallon mutanen da ke zaune, wasu na tsaye, wasu kuma na hira. Kai tsaye ta soma takawa, ba ta jira komai ba, ta tsuguna har ƙasa lokacin da ta isa dab da wata mota, wadda wani babban mutum ke tsaye, gefensa kuma wata mata ce, ya yin da wani saurayi da a ƙalla zai yi shekaru 30, ke kusa da mutumin.

"Don girman Allah ku taimaka mini da kuɗin gwajin waɗannan, ƙanina ne ba shi da lafiya, kuma ba ni da komai, don Allah ku taimaka mini." Ta yi maganar idanunta a kan mutumin.

"Ka ga halin mutanen koh? Har sun fara." Matar ta faɗa tana jan tsaki a ƙarshen maganar tata. Kallon Daneen mutumin ya yi, kafin ya maida dubansa kan matarsa ya ce

"Idan ma ba su fara ba ba ni da nutsuwar saurarar kowa a yanzu.. Kai Yohanah ina jiran ka, kar ka ƙara ko da minti 10 ne a kan lokacin da na ba ka. Na dai faɗa maka, ka kuma kiyaye." Ya ƙare maganar yana kallon saurayin da ke gefensa, wanda ke sanye cikin wata riga da wando crazy. Kansa da wani banzan aski, ya yi cibiri-cibiri a tsakiyar kan.

"Toh sai na ƙaraso." Ya faɗa da gurɓatacciyar hausarsa, da tun daga fara maganarsa za ka fahimci ba bahaushe ba ne. Ko da yake fuskarsa ma kaɗai ka kalla za ka iya fahimtar hakan, daga zarar kuma ya yi magana shi ne za ka tabbatar. Bai jira wani ya sake cewa komai ba ya faɗa cikin motar, matarsa na gefensa ya ja ya fice daga asibitin. Daneen ta bi su da kallo tana jin wata faɗuwar gaba na kama ta. A hankali ta ɗan sake runtse idanunta tana miƙewa a kan ƙafafunta, har lokacin idanunta na bin ƙurar da mutumin nan ya bari.

"Nawa kike buƙata?" Ta ji an ambata daga bayanta. Da sauri ta juyo har tana ƙoƙarin yin tuntuɓe ta kalli matashin saurayin da a kira da 'Yohana'. Kawai sai ta miƙa masa takardar. Maimakon ya kalli takardar, sai ya ci gaba da bin ta da kallo, tun daga sama yake kallon ta har ƙasa, wanda har hakan ya ɗan so ya sa ta tsargu, har ta kai ga ta soma janyo addu'a cikin zuciyarta. Sai ya maida dubansa kan takardar ya shiga karantawa.

"Mu je." Ya ambata yana yin gaba. Babu musu Daneen ta soma binsa. Hausarsa kwata-kwata ba ta da daɗin saurara, saboda yadda bai iya ta ba, kawai dai yana kwaɓawa ne. Dukkan kuma wasu alamu sun nuna yarinyar nan da ke gabansa ba lallai ta iya turanci ba. Don haka suna ci gaba da tafiya ya ce

"Kina son taimako a kan duk abin da kike so na yi miki?" Duk da ya yi maganar a juye, amma tabbas ta fahimce shi, dalili kenan da ya sanya ta jinjina kai tana faɗin

"Ehh don Allah." Ajiyar zuciya ya sauke, kafin ya ce

"Alright, I will help you, but ke ma za ki taimaka mini a kan wani abu. Get it?"

"Zan taimaka maka idan dai har ka taimake ni, ni dai burina kawai ɗan'uwana ya samu lafiya."

"Ohk don't worry, he will be fine soon." Duk da ba wani turanci ake yi musu a makarantarsu ba, amma tabbas ta fahimci abin da yake nufi, don haka ta jinjina kai kawai.

Har bayan shuɗewar wasu awanni Daneen na tare da Yohana, bayan an yi wa Ameer gwaje-gwajen da likita ya buƙata. Kuma da taimakon Ubangiji, taimakon gaggawar da aka ba shi ya taimaka masa matuƙa, wanda har bayan dawowarsu daga gwajin ya samu wani wahalallen bacci ya ɗauke shi. Sosai Daneen ke ci gaba da jajanta kirkin Yohanah, don duk wasu alamu sun nuna ba musulmi ne ba. Abin da ya sa kuma ta ƙara tabbatarwa, shi ne da lokacin Sallah ya yi ba ta ga ya tashi ya yi ba. Sai dai taimaka matan da ya yi, ya matuƙar yi mata daɗi, ta kuma gode wa Allah da ya kawo mata shi a irin wannan lokacin da ta ke buƙatar taimako.

.."Zuciyarsa ta yi raunin da ana buƙatar a yi masa aiki, idan ba haka ba a kowanne irin lokaci za a iya rasa shi." Likitan ya faɗa yana kallan Yohanah. Dama ya san da wuya idan ba haka ne zai faru ba, saboda yadda shi kansa da ba likita ba ya ga yanayin Ameer ɗin, da kuma gwajin da aka masa. Hannu ya miƙa wa likitan suka gaisa kafin ya fita daga office ɗin. Kamar yadda ya tsammata kuwa, Daneen na ƙofar tana jiran sa. Kallon sa kawai take yi, tana jira ta ji abin da zai ce. Fahimtar hakan ya sanya shi faɗin

"Ana buƙatar a yi masa aiki a zuciya." Wani irin jiri ne ya kwashi Daneen, lokaci guda wani duhu ya zo ya mamaye ganinta. Ta yi gefe za ta faɗi, duk da yadda take ƙoƙarin ganin ba ta zube ba. Dalili kenan da ya sanya Yohana kai hannunsa ba tare da wani tunani ba ya riƙo ta. Wani irin runtse idanunta ta yi, tana komawa kan ƙafafunta, ta yi maza ta buɗe a kan hannunsa da ke kan nata hannun, sai kuma ya yi saurin janyewa yana furta

"Sorry girl, Sorry please." Ya faɗa saboda yadda ya ga tana bin sa da wani irin kallo. Ba tare da ta bi ta kan abin da yake faɗa ba, ta zube a kan ƙafafunta tana jin yadda bugun zuciyarta ya ƙaru. 'Aiki a zuciya?' Shi ne abin da take ta maimaitawa, hawaye tuni sun cika mata idanunta.

"Stop crying Cutie. Ki tashi mu samu mafita." Ya faɗa yana kallan yadda take kuka kamar Baby. Duk wasu alamu sun nuna yadda take matuƙar ƙaunar ɗan'uwanta. Gaba ɗaya aikinta da kuma maganganunta sun nuna shaƙuwa da kuma tsananin ƙaunarta da ɗan'uwanta. 'Me hakan ke nufi?' Ya tambayi kansa. Sai kuma ya yi gefe, ya fito da wayarsa daga cikin aljihu ya danna wa wata number kira.

"What's going on?" Ya faɗa bayan an ɗaga wayar. Shiru ya yi na ɗan wasu sakanni, yana saurarar abin da ake faɗa masa daga can ɓangaren, kafin ya ce

"Ya yi, send me the address now! I will call you later."

"Ohk." Ya sake faɗa bayan wasu sakanni. Jefa wayar ya yi cikin aljihu kafin ya koma inda ya bar Daneen, da ke zube a wajen tamkar wadda aka dasa.

"Tashi mu tafi." Da sauri ta ɗaga idanunta ta kalle shi. Ya jinjina mata kai kana ya ce

"Ehh, asibiti za mu sauya.. Za ki iya sadaukar da wani abin da kika mallaka saboda ɗan'uwanki."

"Matuƙar dai zai samu lafiya." Ta faɗa tana jinjina kai.

"Ohk let's go. But let me go and meet the doctor, I will explain everything to him. Wait for me here." Daga haka bai jira ta ce komai ba ya faɗa cikin office ɗin. Wajen minti 20, sai ga shi ya fito, tana tsaye kamar yadda ya bar ta. Ya miƙa mata takardun hannunsa kafin ya wuce ɗakin da Ameer yake.

Runtse idanunta Daneen ta yi tana sake gode wa Allah. Ba don Allah Ya kawo mata Yohanah ba, da ba ta san yadda za ta yi ba. A bayan motar Yohanah ɗin aka kwantar da Ameer, da na'ura ke taimaka masa wajen numfashi. A gaban motar Daneen ta zauna, ya yin da shi kuma ya zauna wajen mai tuƙi. Babu ɓata lokaci ya ja motar suka fice daga cikin asibitin. Suna tafiya Daneen na juya wa baya ta kalli Ameer, sai kuma ta dawo ta ci gaba da kallon titi. Ganin abun take tamkar a mafarki, tamkar ba Ameer ɗinta ba. Har suka yi tafiya mai nisa ba ta daina tunane-tunane ba. Tun daga bakin asibitin za ka fahimci lallai babban asibiti ne, babban ma irin babban da ya amsa sunansa babba. Hamshaƙi, haɗaɗɗe wanda kallo ɗaya za ka masa, ka san ya lamushe kuɗaɗe da yawa wajen gina shi. Idan kuwa aka shiga ciki ba za ka taɓa zata a cikin Nigeria kake ba, saboda matuƙar haɗuwa da ya yi. Kai tsaye a inda aka tanada don ajje motoci Yohanah ya yi parking na motarsa, Daneen kuwa ban da ci gaba da kallon cikin asibitin babu abin da ta yi, mamaki take toh me ya kawo su nan ɗin? Saboda yadda duk wasu alamu suka nuna nan ɗin bai yi kama da inda za a taimaka wa talaka ba. Ita tun da take ma, ko kuma ta ce tun da suka shigo garin Kano ba ta taɓa ganin waje mai kyau da tsaruwa irin wannan ba. Sai dai da yake gaba ɗaya hankalinta yana kan Ameer ya sa yana ida yin parking ta sauka daga motar ta koma inda Ameer yake. Shi ma saukar ya yi. Cikin ƙanƙanin lokaci aka shigar da Ameer cikin asibitin, da cikinsa ya fi harabarsa tsaruwa nesa ba kusa ba.


.. "Akwai wani cikin asibitin nan, mahaifinsa mugun mai kuɗi ne. Ƙodarsa ce ta lalace, ana buƙatar a sauya masa wata. Saboda haka idan dai har kika sadaukar da ƙodarki ga ɗansa, toh tabbas ko ma nawa ne, ko nawa ake buƙata, zai biya a yi wa Ameer aiki. Zai iya fitar da shi ma waje ƙwararrun likitoci su yi masa aiki. Ƙodarki guda ɗaya kawai za ki bayar, daga nan ki saka a ranki ɗan'uwanki ya samu lafiya." Tun da Yohanah ya fara magana Daneen ke kallonsa, tana rarrabe duk wata kalma da ya faɗa. Har bayan kusan minti ɗaya da gama maganar ba ta ce komai ba. Sai zuwa can sannan ta ce

"Ka tabbatar zai biya a yi wa Ameer aiki? Ko da an yi aikin kuma na mutu idan na bar Ameer a hannunka za ka kai mini shi wajen mahaifiyarmu?" Daneen ta faɗa cikin sanyayyiyar muryarta. Murmushi Yohanah ya yi, yana ɗan shafa gefen kumatunsa. Sai da ya soma girgiza kai sannan ya ce

"Nothing will happen. Just pray as much as you can, za a yi komai cikin nasara. Za ki samu lafiya, ɗan'uwanki ma haka." Ya yi maganar a nutse saboda ya ba ta ƙwarin gwuiwa. Ganin ta sake yin shiru ne, ya sanya shi faɗin

"Za ki iya zuwa ku yi magana da doctor, zai yi miki bayanin komai himself." Ajiyar zuciya Daneen ta sauke, kafin a hankali ta buɗe baki da ƙyar ta ce

"Na amince." Ba ƙoda ba, ko da zuciyarta ce za ta iya sadaukar wa a kan ɗan'uwanta, matuƙar zai samu lafiya. Ballantana ƙoda da aka ce mata guda biyu ce. Ubangiji Allah Ya dubi zuciyarta Ya ba wa ɗan'uwanta lafiya, da ita kanta da za a ciri wani abu daga cikin jikinta. Shi kuma wanda zai siya ƙodar tata Allah Ya sa ya ji tausayinsu, ko da kuɗin da ake buƙata wajen yin aikin, ya fi kuɗin da ya yi niyyar bayarwa, ya taimaka ya biya gaba ɗaya. Ya kuma saka a yi aikin cikin nasara.
Wani irin murmushi Yohanah ya saki, yana sauke ajiyar zuciya. Kai tsaye ya shiga office ɗin likitan don yi masa bayanin abin da ya kawo su cikin asibitin. Duk da da farko ba su nuna ba, don sai da ya bari aka karɓi Ameer tukunna, bayan ya ajje kuɗi masu ɗan tsoka kamar yadda yake a tsarin asibitin.


A sanyaye Abeey da ke sanye cikin wata bluen shadda, ɗinkin babbar riga, ya ke takawa zuwa cikin ɗakin. A hankali ya ɗora hannunsa kan hannun ƙofar ya tura. Har lokacin Maama na zaune kusa da ɗanta hannunta na cikin nasa. Yana kwance kan gadon, rabin jikinsa lulluɓe da bargo, ya yin da idanunsa ke a lumshe tamkar mai yin bacci. Ɗaga idanunta Maama ta yi ta kalli Abeey, bayan ta amsa sallamarsa. Ya ƙarasa cikin ɗakin, idanunsa na kallan fuskar ɗan nasa da ta yi fayau, ya ce

"Sannu Tareeq." Ya faɗa yana kallansa cike da tausayawa. A hankali ya shiga buɗe idanunsa da suka masa nauyi. Ya sauke su a kan Abeeyn, yana sauke numfashi a hankali kamar wanda ya yi aikin wahala.

"Sannu." Maama ta faɗa a hankali. Sai ya jinjina kai yana ƙaƙalo murmushi ya wanzar a kan fuskarsa kafin ya ce

"Yawwah." Ya ƙare har lokacin da murmushin ƙarfin hali a fuskarsa.

"Yanzu dai ba ka isa ka ce mini ka warke na yarda ba. Ka ma daina mini wanna yaƙen. Ni na fi so ko me kake ji ka sanar da ni Tareeq. Ba garin wannan ɓoye abin da ke damunka ɗin ba ne ya janyo haka ba. Ni dai Abeey ka faɗa masa ya daina wannan ɗab'iar tasa, idan da wani abun ya same shi kafin mu ankare fa? Ko kuma abin da ke damun nasa bai fito fili ba ya ci gaba da cin sa a cikin jikinsa fa?" Ta ƙare maganar tana kallan Abeey. Murmushi Abeey ya yi kana ya ce

"Ya isa haka, shi kenan faɗan ya isa haka. Yanzu dai ki yi haƙuri ki.." Kafin ya kai ga ƙarasa maganar, wayarsa ta ɗauki ruri. Ya zube idanunsa a kan wayar, ganin doctor ke kiransa ya sanya shi saurin ɗagawa. Shiru ya yi na tsawon mintina yana saurarar abin da likitan ke faɗa. Suka ɗan yi magana kafin ya ajje wayar. Ya kalli Maama murmushi na tashi a kan fuskarsa ya ce

"Tun kafin a je ko'ina, har an samu yarinyar da za ta sadaukar da ƙodarta gun yaronki." Da matuƙar mamaki Maama ta ce

"Da gaske Yallaɓai? Ita kuwa me take buƙata a rayuwarta wanda za mu iya biyan ta da shi?" Ta tambaya wani irin murmushin farin ciki na tashi a kan fuskarta.

"Abin mamaki, Likitan ya sanar da ni ba ta buƙatar komai." Shiru Maama ta yi tana kallon Abeey cike da mamakin jin furucinsa.

"Ba ta buƙatar komai kuma?" Jinjina kai Abeey ya yi kafin ya ce

"Ya ce ta bayar da ita ne saboda a yi wa ɗan'uwanta da ke kwance cikin asibitin nan addu'ar Allah Ya ba shi lafiya. Ban da wannan ba ta buƙatar ko sisi."


Littafin DANEEN na kuɗi ne, a kan 500. Sai dai daga farko har ƙarshen Book 1 free ne, Book 2&3 shi ne na kuɗi kuma duka a kan 500. Har yanzu kuma muna cikin Book 1 ne, wato (Free pages). Waɗanda za su fara payment yanzu, su tuntuɓe ni ta 08124818273. Waɗanda kuma sai mun gama Book 1 ne za su yi payment, zan saka muku yadda za ku yi a last page na Book 1.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 19

Jinjina kai Maama ta yi cike da mamakin jin abin da Abeey ya faɗa. Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce

"Allah Sarki! Amma abin kam da mamaki. Allah Ubangiji Ya saka mata da alkhairi, Ya ba wa ɗan'uwanta lafiya."

"Ameen." Abeey ya amsa da hakan, har lokacin annurin fuskarsa yana nan. Tun da Abeey ya fara magana Tareeq yake kallon sa har ya ƙare. A hankali ya ɗan gyara kwanciyarsa lokaci guda yana lumshe idanunsa. Da sauri Maama da ta lura da shi ta taso tana faɗin

"Me ya faru?" Girgiza kansa ya yi lokaci ɗaya yana buɗe idanunsa. A hankali ya soma faɗin

"Abeey wace ce ita? Ina son ganin ta tukunna." Ya faɗa cike da ƙarfin hali.

"Oh Yah Ilahy Tareeq, ka samu ka samu ka yi bacci kafin mu ji abin da Likita zai faɗa." Girgiza kai Tareeq ya yi kafin ya ce bayan ya riƙo hannun Maama.

"Maama ki bar ni na ga wadda za ta ba ni ƙodarta ba tare da wani dalili ba. Ina buƙatar ganin wace ce ita tabbas." Tun kafin ya ƙarasa Maama ta katse shi da faɗin

"Rashin yardarka ya yi yawa Tareeq, har a kan lafiyarka ma?" Ta ƙare tana kallon sa. Iska ya fesar daga bakinsa, ganin da ya yi kwata-kwata Maaman ta ƙi fahimtarsa, lokaci ɗaya kuma yana mayar da jikinsa ya kwantar a kan gadon, har lokacin idanunsa a lumshe.

"Ya isa haka Fatima. Kin fi kowa sanin halin ɗanki, ina ga kuma hakan ba laifi ba ne. Amma dai a halin da kake ciki ka fi buƙatar hutawa, so ka kwanta ka samu ka yi bacci zuwa an jima. Ni da mahaifiyarka za mu yi magana da yarinyar." Jinjina kai kawai ya yi daga inda yake kwance ba tare da ya ce komai ba. Maama ta bi shi da kallo cike da tausayawa. Hannunta ta kai a hankali ta taɓa wuyansa, jin da ta yi zafin ba sosai ba ya sanya ta sauke ajiyar zuciya har cikin ranta tana jin daɗi. Saboda yadda kwana biyu Tareeq ɗin ya din ga fama da matsanancin zazzaɓi mai zafin gaske. Babu daɗewa aka turo ƙofar ɗakin, Sultanah ce da Hidaya cikin dogayen riguna kusan iri ɗaya sai dai ba kala ɗaya ba ne. Da sauri suka ƙarasa inda Tareeq ɗin yake, kowacce jikinta a matuƙar sanyaye.

"Sannu Yah Tareeq." Suka kusan haɗa baki wajen faɗin hakan. Ɗan lumshe idanunsa ya yi kaɗan kafin ya ce

"Yawwah."

"Wai Yah Tareeq dama ka san da wannan ciwon?" Hidaya ta faɗa kamar za ta yi kuka. Girgiza kai ya yi, yana ɗan ƙaƙalo murmushi a hankali ya ce

"Kaɗan kaɗan.. Ban san abin ya kai haka ba, duk da ina karɓar gwajin lafiyata a kai a kai, ban san lamarin zai yi tsamari har haka ba." Ya ƙare a ɗan gajiye.

"Wallahi Yah Tareeq mun fi ka kula da lafiyarka. Kai dai kawai ciwon a jikinka yake, amma mun fi ka damuwa da shi." In ji Sultanah tana kallon sa. Yanzu kam sai da ya ɗan yi dariya, daidai lokacin da Abeey ya miƙe yana faɗin

"Ya kamata mu yi waje fa haka." Cikin girmamawa duk suka amsa da "Toh." Ba su ɗauki lokaci mai tsayi ba gaba ɗaya suka fice suka bar shi shi ɗaya zuciyarsa cunkushe da tunane-tunane.

Cikin ikon Allah aka gwada ƙodar Daneen, kuma za ya iya cira a saka wa Tareeq. Don haka Likitan ya tsayar da washe-gari a matsayin ranar da za a yi aikin.

Gaba ɗaya jikinta a matuƙar sanyaye yake, lokacin da take taka wa tana bin bayan wani da zai raka ta ɗakin da Ameer yake ciki. Sai da ya tura ƙofar ɗakin sannan ya juya ya bar wajen. Daneen ta bi shi da kallo kafin ta maida idanunta cikin ɗakin. Runtse idanunta ta yi, tana jin yadda zuciyarta ta karye, saboda hango ɗan'uwanta da ta yi kwance, har kuma lokacin ba ya iya numfashi shi ɗaya sai da taimakon na'ura. Kamar wadda ke tsoron taka ƙasa haka take takawa zuwa cikin ɗakin idanunta a kansa. Ta zuba wa kyakykyawar fuskar Ameer idanunta lokacin da yake bacci kai sai ka rantse cikin kwanciyar hankali yake, babu wani abu da ke damunsa. A nutse ta kai hannunta ta riƙo hannunsa cikin nata, tana jin wata irin ƙwalla na tarar mata. Idanunsa ya shiga buɗewa a hankali kamar ya san wadda ke tsaye a wajen. Sai dai shi ma cike yake da fatan a ce ya buɗe idanunsa ya ga 'yar'uwarsa a gefensa. Aikuwa cikin ikon Allah yana buɗe su ɗin kuwa ya sauke a kan Daneen. Runtse idanunsa ya yi kafin ya buɗe a hankali daidai lokacin da wasu kyawawan ƙwalla suka zubo daga cikin idanunsa.

"Ameer." Ta faɗa, tana kai hannunta kan bakinta ta toshe don kar kukan da take ta riƙewa ya fito.

"Adda." Ya yi ƙarfin halin faɗa. Rasa abin da za ta yi ne ya sanya ta zube wa a wajen kawai, ta kifa kanta a kan gadon ta shiga raira kukanta a hankali. Hannunta da ke kusa da na shi ya riƙo sosai, dalili kenan da ya sanya ta saka hannunta ta share fuskarta kafin ta miƙe tsaye tana kallon sa.

"Kin ga abin da na ja mana koh?" Ya faɗa a raunace. Girgiza kai ta yi tana barin hawayen cikin idanunta damar zubowa.

"Ka dena mini irin wannan maganar Ameer, ba ka ja mana komai ba. Duk abin da ka ga ya faru dama rubutacce ne. Bawa kuma ba ya taɓa wuce wa ƙaddararsa." Murmushin yaƙe Ameer ya yi, yana sake jin yadda gaba ɗaya duniyar ta fice masa a ransa. Ji yake tamkar zuciyarsa za ta yi bindiga saboda tsananin ciwon da yake ji a cikinta. Cikin sanyi da ƙarfin hali ya soma faɗin

"Adda ba na tunanin zan rayu kowanne irin aiki aka yi mini. Ni kaɗai na san abin da nake ji. Bayan zuciyata Adda cikina na yi mini wani irin ciwo da na kasa fahimtar wane iri ne shi. Idan na mutu ki nemar mini yafiya gurin Innarmu, duk abin da ya faru ni na jawo. Sai da kika ce mini kar mu baro ƙauyenmu amma na kafe, yanzu ga abin da ya faru." Ya kai ƙarshen maganar yana sauke wani numfashi a mugun wahalce.

"Ameer ba na so, ka dena na faɗa maka. Ba za mu koma wa Inna a wani irin hali ba, In Sha Allah za mu koma mata ne a yadda muka baro ƙauyenmu. Za ka warke da yardar Ubangiji. Na kuma roƙe ka da ka cire wannan damuwar da kake ɗora wa kanka ko don samun lafiyarka, Ameer ka san lafiyarka ita ce tawa don Allah." Daneen da muryarta ke fita da ƙyar cikin kuka ta faɗi haka. Girgiza kai kawai ya yi ya ce

"Toh Adda na dena, na dena.." Ya faɗa yana wani lumshe idanunsa. Sai da ya yi bacci tana cikin ɗakin sannan ta fice ƙwaƙwalwarta fall tunani kamar za ta tarwatse.


..Tana nan zaune inda Yohanah ya bar ta, bayan ya ba ta uzurin zai je ya dawo. Ta zauna ta yi shiru cikin rashin sanin abin yi. Ita kanta tunani nema yake ya yi wa ƙwaƙwalwarta yawa, sai dai babu yadda ta iya. Haka nan take zaune, a ido tana wajen amma a zahiri ita ce zaune a wajen kawai, amma gaba ɗaya hankali da duk wani tunaninta yana wani wajen daban.

"Doctor na son ganin ki." Shi ne kawai abin da ta ji, wanda ya yi nasarar dawo da ita daga dogon tunanin da ta tafi.

"Na'am?" Ta ƙare maganar da alamar tambaya tana kallon wadda ta yi mata magana. A karo na barkatai ta sake maimaita mata saƙon Likitan tana nazarinta. Miƙewa Daneen ta yi tana faɗin

"Tohm." Daga haka ta bi matar a baya zuwa office ɗin Likitan. A bakin wani ɗaki suka rabu, ya yin ita matar ta kalli Daneen ta ce

"Ki shiga." Kallon ta Daneen ta yi tamkar mai neman ƙarin bayani, sai dai kuma ba ta ce komai ba, illa jinjina kai da ta yi. Daga haka matar tayi gaba ya yin da ita kuma ta tura ƙofar ɗakin da sallama ɗauke a kan laɓɓanta. Kusan a tare suka amsa sallamar, dukkan su idanunsu a kanta. Kasancewar ba ta san za ta yi ido huɗu da wasu fuskokin ba, ya sanya ta yin turus tana ɗauke kanta daga kallon su.

"Ƙaraso mana." Maama ta faɗa har lokacin idanunta a kan Daneen. Cike da sassarfa Daneen ta ƙarasa cikin ɗakin tana jin bugun zuciyarta na ƙaruwa.

"Taho ki zauna a nan." Maama ta faɗa, ba tare da jin komai ba ta ja hannun Daneen ɗin ta yi mata mazauni a gefe kaɗan da ita. Babu musu Daneen ta zauna hannunta ɗaya cikin

Please Login or Register in order to submit comment