Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kana ta ce

"Ba ni da matsala da kai, ai kai nawa ne. Yarinya kuma ga ta nan. Maza tashi ki bi shi shi ne zai samar miki aikin." Aunty ta faɗa tana taɓo Daneen. Wani tsinke wa da gaban Daneen ya sake yi ya faɗi shi ne ya sanya ta saurin runtse idanunta tana faɗin

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel." Mutumin ya sake bin Daneen da kallo lokacin da ta ɗago idanunta ta kalli Aunty.

"Shi zan bi?" Ta tambaya kamar wadda ba ta ji abin da Auntyn ta faɗa ba. Don kar shakku ya shiga zuciyar Daneen ɗin ya sanya Aunty faɗin

"Eh, shi zai kai ki gidan da za ki dinga yi wa aiki, kar ki damu."

Shiru ta yi na en wasu sakanni kafin ta sake ɗaga ido ta kalli Aunty. Abin da yake ta mata yawo a ƙwaƙwalwa shi ne ya sa ta buɗe baki ta ce a sanyaye

"Ƙanina Ameer." Ta faɗa cikin sanyayyiyar muryarta. Mutumin da ya yi nasarar biyan kuɗin da suka take na kowannensu ya wani lumshe ido yana jin yadda sanyayyiyar muryar Daneen ke neman kashe shi a zaune.

"Don Allah tashi ki kira mini ƙanin nata mu tafi." Ya faɗa yana miƙewa. Kallan sa Aunty ta yi ta ce da mamaki

"Da ƙanin nata za ku tafi?"

"Rabu da ita, kira mini shi, shi ma za a samar masa aikin yi. Ki yi da jiki please." Ba ta sake cewa komai ba, ta ɗauki wayarta ta bayar da umarnin fito da Ameer da ke can ɓangaren mazan gidan. Babu daɗewa kuwa sai ga shi wani ya rako shi, lokacin har sun fito waje, mutumin na ƙoƙarin shiga motarsa ya yin da Daneen da tunane-tunane ke ta shigar ta tana tsaye daga gefe. Sai a lokacin ta saki murmushi tana kallan Ameer, shi ma murmushin ya maida mata yana ƙarasawa ya kama hannunta ya ce

"Adda."

"Uhmm Ameer."

"Har na yi kewar ki Addatah, na ɗan wannan lokacin." Ya faɗa yana murmushi. Hannunta ta kai ta ja kumatunsa tana faɗin

"Ni ma haka ɗan'uwa." Daga haka babu daɗewa, suka shiga motar mutumin. Daneen na gaba, ya yin da Ameer ke baya. Ya shiga motar ya tayar, babu ɓata lokaci suka fice daga gidan.


.. A parking space na gidan ya yi parking na motarsa, kai tsaye palourn Dadaji ya wuce, yana cikin shigar ƙananan kayan da suka matuƙar yi masa kyau. Kansa babu komai sai tulin sumar da Allah Ya ba shi mai matuƙar kyau da ɗaukar idanu. Cikin nutsuwa da tafiyarsa mai cike da mazantaka ya ƙarasa ɗakin Dadaji, bakinsa ɗauke da sallama. Ya yi mamakin hayaniyar da ya ji tana tashi tun kafin ya ƙarasa cikin ɗakin. Sai dai duk da haka bai fasa shiga ba, ya shige cikin ɗakin.

"Wa alaika salam. Barka da zuwan Tareeq." Dadaji ta faɗa tana kallan sa. Sassanyan murmushin da ya kan daɗe wa bai yi shi ba ya wanzu a kan fuskarsa. Wanda idan ba sanin ainahin yadda fuskarsa take ka yi ba, ba za ka ɗauka murmushin ya yi ba.

"Dada ji." Ya faɗa lokacin da ya nemi waje ya zauna a kan kujerar ɗakin.

"Hala dai koro ka aka yi da farar yammar nan." Murmushi ya yi mai sauti yana gyara zamansa ya ce

"Dada jiii." Ya faɗa yana jan ƙarshen sunan nata. Kafin ta kai ga amsawa ya ce

"Hayaniyar me nake ji ne?" Kallan inda zai sada ka da cikin gidan Dada ji ta yi kana ta ce

"Kar ka nuna kamar ba ka san abin da ke faruwa ba mana." Girgiza kai ya yi da mamaki shimfiɗe a kan kyakkyawar fuskarsa. Gane abin da yake nufi ne ya sanya Dada ji faɗin

"Ba gobe ne Alhassan zai dawo ba?" Cike da mamakin dai ya cigaba da kallan Dada ji. Bayan shuɗewar wasu sakanni ya ce

"Abeey zai dawo, amma Maama ba ta sanar da ni ba? A taƙaice ma dai babu wanda ya sanar da ni. Rashin muhimmancin nawa ya kai haka?" Ya tambaya a nutse yana kallan Dada ji.

"A'ah, kar ranka ya ɓaci Tareeq. Duk na gida ne suka zo fa. Ƙannen mahaifinka ne kaɗai cikin gidan nan ba na waje ba."

"Sultanah ba ta shigo ba?" Ya kawar da waccan maganar ya kawo wannan.

"A'ah ta shigo babu daɗewa, uwarta ta aiko kiran ta za ta taya ta aiki. Ka san ita ma tana can tana shirye-shiryen dawowar Abeeyn naku." (Don en gidan gaba ɗayansu ba dai takatsantsan ba, musamman a kan abin da ya shafi cimarsu. Shi ya sa duk girman gidan nan babu mai dafa abinci, sai dai en aiki masu yin wasu ayyukan. Amma duk wani abu da ya shafi cikinsu su suke yi da kansu. Ko dai su iyayen su yi, ko kuma 'ya'yan su yi. Ko a ɓangaren Dadaji ma da take uwar masu gidan, ba ta da mai dafa mata abinci. Daga ɓangaren matan ɗan nata ake kawo mata. Ko kuma Sultanah ko Hidaya wata ta je ta girka mata idan tana free.)

Jinjina kai Tareeq ya yi kafin ya miƙe daidai lokacin da yake faɗin

"Bari na je, zan kira Abeeyn zuwa dare In Sha Allah."

"Toh Allah Ya yarda. Ɗazun nan ma Jawahir ke tambayarka." Har ya soma tafiya sannan ya ce

"Ki gaida ta, ina sauri ne." Daga haka ya fice daga ɗakin. Kai tsaye inda ya ajje motarsa ya nufa, yana tafe yana waya da Sultanah da ya sanar da ita za su yi maganar tun da yanzu da baƙi a gidan kuma tana aiki. Sosai ta yi wa yayan nata godiya kafin suka yi sallama. Har ya buɗe ƙofar motarsa yana ƙoƙarin shiga, sai kuma ya dakata idanunsa a kan wayarsa. Kusan mintuna wajen nawa yana kalla, kafin ya rufe motar kai tsaye ya koma cikin gidan. Part ɗinsa ya wuce a ɗan hanzarce zuciyarsa cike fall da saƙe-saƙe.


... A bakin wani tafkeken restaurant ya yi parking na motarsa, Daneen da Ameer suka bi shi da kallo lokacin da ya juya ya kalle ta ya ce

"Ku yi haƙuri ina ɗan zuwa, ba daɗewa zan yi ba." Jinjina kai kawai Daneen ta yi, don a lokacin ji take bakinta ya yi mata nauyi. Buɗe motar ya yi ya fice kai tsaye ya shige cikin restaurant ɗin. Bayan wasu sakanni Daneen ta juya ta kalli Ameer ta ce

"Guduwa za mu yi Ameer."

"Me ya sa Adda?" Ameer ya faɗa da mamaki.

"Kawai tafiya za mu yi Ameer, hankalina ya kasa kwanciya da mutanen nan, duk yadda aka yi akwai wani abun da suke ɓoye mini." Ta ƙare maganar muryarta a raunane.

"Amma na ji ya ce gidan aikin ze kai mu."

"Ameer zuciyata ta kasa samun sukuni, tun fitowar mu daga gida har zuwa yanzun. Yanzu kuma da zuwan mu gidan nan faɗuwar gaba ta ƙi bari na, duk kuwa da addu'ar da nake ta yi. Ina ganin babu alkhairi zuwan mu gidan nan. Da ƙyar idan haɗuwar mu da mutanen nan alkhairi ce. Kawai mu gudu mu bar su." Shiru Ameer ya yi yana cigaba da nazarin yayar tasa. Duk wasu alamomin ruɗewa sun bayyana a kan fuskarta, yadda take magana kuma kana gani ka san daga zuciyarta ne take faɗa. Don haka cikin son ba ta ƙwarin gwuiwa ya ce

"Toh mu tafi ɗin. Amma ta ya ya?" Ba tare da ta amsa wa Ameer tambayar da ya yi mata ba ta sanya hannunta a kan murfin ƙofar da ke gefen ta. Cikin karambani ta ga wajen da tabbas ya fi kama da inda za ta taɓa ƙofar ta buɗu, kamar yadda ta ga ya yi da zai fita. Sai dai kwata-kwata ta ƙi buɗuwa. Ta taɓa ta taɓa ta ƙi buɗuwa. Ameer da ya lura da yadda take yi, shi ma ya taɓa gefensa amma shiru ta ƙi buɗuwa.

"Ko dai ba haka ake ba?" Girgiza kai Daneen ta yi kafin ta ce

"Tabbas nan ya taɓa da zai fita. Sai dai kuma idan ana iya kulle wa kamar ƙofa."

"Eh kuma haka ne." Ameer ya faɗa yana jinjina kai.

"Toh yanzu ya za mu yi?" Kafin Daneen ta kai ga tunanin komai ko ta ce wani abun, aka buɗe ƙofar aka shigo. Mutumin ya ajje ledar hannunsa kafin ya tashi motar suka cigaba da tafiya. Shiru ne ya wanzu cikin motar, kowa da abin da yake saƙa wa cikin ransa. Har zuwa lokacin da ya sake tsaida motar, kamar ɗazun ya sake juyawa ya kalli Daneen ya ce

"Minti 1 gimbiya." Wannan gimbiyar da ya ambata ba ƙaramin kaɗa 'ya'yan cikin Daneen ya yi ba, cikin ƙanƙanin lokaci bugun zuciyarta ya ƙaru. Ta yi ƙarfin halin jinjina kai kawai. Hakan ne ya sa ya fice daga motar.

"Adda ya yi nisa fa." Ameer ya faɗa yana kallan Daneen da ke zaune tamkar wadda aka dasa. Duk da yadda tsoro ke shigar ta, wanda ya yi silar saka wa jikinta ya soma rawa. Hakan bai hana ta runtse idanunta ba, ta kai hannunta kan ƙofar ta sake tura wa cike da takatsantsan, cikin zuciyarta tana fatan kamar yadda suka tsammata su yi tozali da hakan, wato su ga ya bar motar a buɗe, a maimakon ɗazu da ya kulle su.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 14

Cikin sa'a kuwa sai jin ƙofar ta yi ta tafi, ta juya cikin wani irin farin ciki ta kalli Ameer. Farin cikin da ya gaza ɓoyuwa har a kan fuskarta. Ba tare da ta ce masa komai ba, ya saka hannu ya buɗe ƙofar gefen sa. Cikin sakannin da basu wuce biyar ba suka fice daga cikin motar. Ko tsayawa su rufe ma ba su yi ba, gaba ɗaya hankalinsu ya yi gaba. Don haka da gudu suka soma barin wajen hannayensu cikin na juna. Kasancewar duhun magribh ya mamaye garin ya sanya waɗanda ke lura da su ɗin ba su da yawa. Musamman da ya kasance hankalin da dama ya tafi kan masallacin da suke ƙoƙarin zuwa. Sai da suka yi mugun nisan da suka san sun yi wa mutumin nan nisa kafin suka suka soma rage gudun. Wani irin numfashi a gurguje a gurguje Daneen ke saukewa saboda yadda numfashinta ke sarƙewa. Hannun Ameer ta sake riƙowa tana dawo da shi baya lokacin da ta zube a wani waje tana ji tamkar numfashinta na ƙoƙarin barin gangar jikinta.

"Ameer.. na.. gaji." Ta harhaɗa kalmomin ta faɗa hannunta dafe da ƙirjinta. Dawowa ya yi ya zauna cikin matuƙar tashin hankali yana kallan fuskarta ya ce

"Sannu Adda. Ƙishirwa kike ji?" Ya tambaya yana kallan yadda take cigaba da ajje taggwan numfashi tana wani lumshe idanunta. Jinjina kai ta yi, har lokacin idanunta na lumshewa suna kuma buɗewa.

"Ki zauna a nan kin ji? Bari na je na samo miki ruwa." Ya faɗa yana miƙewa. Hannunsa ta sake riƙowa tana girgiza kai ta ce

"A'ah kar ka je ko'ina, zauna kawai." Girgiza kai Ameer ya yi tausayin er'uwar tasa na kama shi ya ce

"A'ah Adda, ƙishirwa kike ji. Ki zauna a nan don Allah kar ki je ko'ina ruwa kawai zan samo miki yanzun nan kin ji?" Be jira ta amsa ba, ya zame hannunsa ya bar wajen. Cigaba da zama ta yi kanta na kallan ƙasa tana ji tamkar ba za ta ƙara ƙwaƙwƙwaran minti 1 a wajen ba ran da ke gangar jikinta zai bar ta. Babu daɗewa kuwa sai ga Ameer nan ya dawo a guje hannunsa ɗauke da robar ruwa, ya ƙarasa da sauri yana kiran sunan Addar tasa.

"Tashi ki sha kin ji?" Ya faɗa yana ɗago ta, babu musu ta tashi zaune sosai. Ta karɓi ruwan duk da yadda hannunta ke rawa, ta kai baki. Tun da ta kafa ba ta sauke ba sai da ta shanye tass, kafin ta ajje tana sauke ajiyar zuciya.

"Sannu." Shi ne abin da Ameer ke ta maimaitawa yana kallan Daneen ɗin jikinsa a matuƙar sanyaye. Yana daga cikin halayensa shiga damuwa duk lokacin da Addar tasa ba ta da lafiya, shi ya sa ma ya fi so shi ya yi cutar a kan ita ta yi, don ta fi shi shan wahala. Musamman kuma a yanzu da suke su kaɗai babu Inna-wuronsu. Lallai sun yi matuƙar kuskuren baro ƙauyensu. Be ƙarasa tunanin ba ya jiyo muryar Daneen na faɗin

"Mu je mu yi Sallah, bacci nake ji Ameer." Kallan inda suke ya yi, idan har be yi kuskuren fahimta ba, kamar cikin kasuwa ne nan ɗin suke. Kuma lokacin da ya je nemo mata ruwa, ya ga mutane mata da maza ƙanana, almajirai da sauransu kowa ya kama waje kamar dai masu shirin kwana a wajen. Kenan idan haka ne su ma za su iya kwana a cikin kasuwar? Ya tambayi kansa yana cigaba da kallan cikin kasuwar.

"Sai dai mu kwana a cikin kasuwar nan Adda, na ga ba mu kaɗai ne mara sa gida ba. Idan ya so zuwa gobe sai mu nemi inda za mu samu kuɗin koma wa ƙauyenmu." Da sauri Daneen ta ɗaga idanunta ta kalli Ameer. Wato duk abin da ya faru tunani yake za su kuma shiga wani gidan su nemi aiki? Ta girgiza kai kafin ta ce a sanyaye

"Kowanne aiki za mu yi ba za mu kuma shiga gidan mutane ba. Gwara mu yi ko da aikin ƙarfi ne a cikin mutane mu karɓi kuɗinmu mu tafi." Ta ƙare tana ɗan sauke numfashi a hankali. Jinjina kai Ameer ya yi cike da amincewa da zancen Addar tasa.

.. A ɗaya ɓangaren kuwa, hannunsa ɗauke da wata leda ya fito. Tun kafin ya ƙarasa inda motar take ya ji gabansa ya faɗi, saboda yadda idanunsa ke masa wani mummunan gizo. Haka dai ya ƙarasa, sai dai tun kafin ya kai ga buɗe motar ya hangi yadda gaba ɗaya ƙofofi biyun motar suke a buɗe. Cike da fargaba ya ƙarasa, ya duba cikin motar, babu kowa. Ya sake dubawa duk da ya riga da ya tabbatar ba sa cikin motar. Juyawa ya shiga yi ko Allah zai sa ya hango inda suka nufa, sai dai ko ƙurarsu bai gani ba. Hannunsa har rawa yake lokacin da ya fiddo da wayarsa ya shiga neman layin Aunty, har wani huci yake fitar wa daga bakinsa.

"Yarinyar nan ta dawo ne?" Ya tambaya duk da a karan kansa sai da ya ji tambayar da ya yi kamar rainin hankali ce.

"Ban gane ba? Wace yarinya kenan?"

"Yarinyar da na siya yanzu a wajen ki mana." Ya ba ta amsa a fusace. Cikin tashin hankali da rashin sanin abin yi Aunty ta miƙe tsaye, tana jin faɗuwar gaba na ziyartarta. Da ƙyar ta iya ƙarfin halin faɗin

"Ba tare kuka fita ba?" Be ce komai ba sai katse wayar da ya yi. Ta sauke wayar daga kunnenta tana bin ta da kallo. Kenan yarinyar guduwa ta yi ko kuwa? Amma shi wane irin sake ya yi da har ta gudar masa, bayan uban kuɗin da ya biya ya siye ta? Soma zagaye ɗakin ta yi tana cigaba da tunane-tunane, ita ba komai ke ci mata tuwo a ƙwarya ba, illa yadda za ta maida masa da kuɗinsa idan har da gaske yarinyar guduwa ta yi.


.. A wajen su Daneen suka cigaba da zama har lokacin da dare ya yi. Suna ganin yadda mutane ke cigaba da kai komo, har zuwa lokacin da garin ya yi shiru. Sai er hayaniyar da ba a rasa ba. Zuwa lokacin Daneen ta lulluɓe jikinta cikin mayafi saboda wani irin sanyi me shiga jiki da ke ta ratsa ƙasusuwanta. Ameer dai na gefen ta, yana kallan abubuwan da ke wakana a gari, zuwa can dai sai ya juya ya kalli er'uwar tasa kafin ya juya ya cigaba da kalle-kalle.

"Addaneen." Ya faɗa yana kallan ta. Ɗaga lumsassun idanunta da suka buɗe da ƙyar saboda wani irin ciwon kai da ya zo ya mata dirar mikiya lokaci guda ta yi ta kalle shi, ba ta iya amsawa ba sai kallan sa kawai da ta yi.

"Ko ba ki da lafiya ne?" Ya tambaya yana kallan ta sosai. Jinjina kai ta yi, tana sake haɗe jikinta waje ɗaya ta ce a hankali

"Zazzaɓi nake ji Ameer." Cikin lokaci ƙanƙani fuskarsa ta sauya, ya shiga kallan ta cike da tausayawa

"Sannu Adda kin ji?" Ya faɗa bayan ya gyara zamansa. Jinjina kai ta yi tana ƙaƙalo murmushi ta wanzar a kan fuskarta. Haka suka cigaba da zama a wajen har cikin dare daga ita har shi babu wanda ya runtsa. Ita zazzaɓin ya hana ta baccin, ya yin da shi kuma tausayin er'uwarsa ne ya hana shi yi. Kafin safiya sosai zazzaɓin ya sake rufe Daneen, Ameer ya rasa yadda ze yi. Wajen ƙarfe 8 na safe ne, zuwa lokacin en kasuwa duk sun soma fitowa. Ya kalli Daneen ya ce

"Adda mu bar wajen nan tun da masu wajen sun fara zuwa." Kallan cikin kasuwar ta yi da idanunta da suka ɗan ƙanƙance kafin ta ce

"Toh." Daga haka ta soma ƙoƙarin miƙewa. Sai kuma Ameer ya katse ta da faɗin

"Zauna a nan bari na je na samo miki abinci." Girgiza kai ta yi da sauri tana faɗin

"A'ah mu je kawai." Duk da yadda take jin jikinta hakan be hana ta ƙoƙartawa ba, Ameer ya taimaka mata suka bar wajen. Sun yi tafiya me ɗan tsayi babu laifi, suna tafiya suna tsayawa saboda ta huta. Har zuwa lokacin da ta shiga sauke numfashi lokacin da take zaune a wani waje.

"Ameer na gaji." Ta faɗa a wahalce.

"Kina jin yunwa?" Ya tambaya don ya san dole za ta ji, dan ko shi ma yana jin ta. Yanzu kam babu musu ta jinjina kai. Ya kalli inda suke, ya sake kallan inda suke kafin ya maida duban sa kanta ya ce

"Ki jira ni a nan komai daɗewar da zan yi zan nemo mana abin da za mu ci kin ji? Kar ki je ko'ina a nan zan zo na same ki." Kallan sa ta yi na tsawon sakanni kafin ta ce

"Ameer ina za ka je?"

"Zan je ko ma ina ne Adda, yunwa kike ji. Zan yi aiki kowanne iri ne don na ga kin samu abin da za ki ci. Ki jira ni kin ji?" Ya sake faɗa yana kallan ta.

"Na fi so ko'ina za ka je ina kusa da kai Ameer, ba na son ka tafi wani wajen ni kuma ina nan."

"Adda ba ki da lafiya ai shi ya sa. Ki jira ni kin ji?" Sai ta jinjina kai kafin ta ce

"Allah Ya tsare."

"Ameen." Ya amsa da hakan da murmushi ɗauke a kan fuskarsa.


.. A ɗaya ɓangaren kuwa, ya shafe fiye da rabin awa a toilet ɗin, bayan ya sakar wa kansa ruwa mai ɗumi. Duk kuma daɗewar da ya yi tunani ne jibge a cikin ƙwaƙwalwarsa. Zuwa can dai ya ɗauro tattausan towel ya fito ɗakinsa. Be bi ta kan wayarsa da ke ajje kan gado ba, kai tsaye ya ƙarasa gaban mirror ya shiga sake kwantar da sumar kansa da ko da ze kwana nawa ba tare da ya taɓa ta ba ba za ta nuna ba. Sai dai da yake ya riga ya saba, duk lokacin da ya fito daga wanka ya kan gyara ta yadda take sake zama haɗaɗɗiya, mai matuƙar birgewa. Be jima ba ya ida shiryawa cikin wata tattausar jallabiya da ta matuƙar ɗaukar kalar fatarsa. Kasancewar ba zai sake fita daga gidan ba ya sanya shi jan laptop zuwa kan gadonsa, saƙon nan dai ya sake nemowa ya shiga yana sake karanta abin da ke rubuce da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai kamar wanda ke koyar yadda ake karatun. Ya yi nisa ba tare da ya ankara ba sai ji ya yi an turo ƙofar ɗakin. Da sauri ya ɗaga idanunsa ya kalli mai shigowar. Wata ƙatuwar ajiyar zuciya Maama ta sauke lokacin da ta ga ɗan nata zaune da alama cikin ƙoshin lafiya. Saurin rufe laptop ɗin gabansa ya yi, yana ajje ta gefe ya soma ƙoƙarin sakko wa daga kan gadon. Ƙarasawa Maama ta yi.

"Tareeq ina ka shiga ne tun ɗazu ina kiran wayarka ba ka ɗagawa? Ka san fa ba na son hakan, kana tayar mini da hankali wallahi." Maama ta faɗa tana kallan sa bayan ta nemi waje ta zauna. Sai da ya duba inda ya ajje wayarsa, ya janyo ta ya kunna ta. Tarin missed calls ɗin da ya gani danƙare a kan wayar tasa ya sanya shi ɗaga kai ya kalli Maama.

"Ki yi haƙuri Maama, na ajje wayar ne ban san kin kira ba."

"Wani abin kake yi ne?" Sai da ya ɗan kalli laptop ɗin kafin ya shafi gefen kansa ya girgiza kai

"A'ah, na ɗan duba wani aiki ne. Ki yi haƙuri Maama." Ya sake faɗa a karo na biyu. Murmushi ta yi kafin ta gyara zama ta ce

"Shi ke nan, za mu iya yin wata magana?" Jinjina kai ya yi kana ya buɗe bakinsa ya ce a nutse

"Eh." Sai da ta ɗan ja wasu sakanni kafin ta ce

"Ina takardun nan na Diyana?" Shiru ya yi kamar mai tunanin wani abin, kamar ba ze ce komai ba, sai kuma ya ɗan fesar da iska daga bakinsa kana ya ce

"Na ƙona su gaba ɗaya." Kallan sa Maama ta cigaba da yi, ya yin da ya basar duk da ya san shi take kalla.

"Toh Allah Ya ƙara kiyayewa. Amm kaa ga gobe idan Allah Ya kai mu Abeeynku zai dawo, Umman Jawahir kuma tana ta cigaba da yi mini maganar haɗa ka da Jawahir. Tun hankalina bai kwanta da hakan ba, har kuma ya zo ya kwanta. Tun da ko babu komai dai Jawahir er'uwarka ce. Don haka nake so na ji daga bakinka, idan dai har ka amince zan sanar wa da Abeeynku wannan maganar sai a san abin yi. Idan kuma ba ka amince ba shi ma ka sanar da ni, amma abin da nake so ka tuna shi ne ni mahaifiyarka na amince da haɗin ɗari bisa ɗari, musabbabin hakan kuma saboda kasancewar Jawahir er'uwarka." Tun da Maama ta soma magana yake kallan ta har ta ƙarasa. Ya yi mamaki matuƙa da ya kasance Maaman da kanta take yi masa zancen wata mace bayan abin da ya faru kwata-kwata ba a daɗe ba. Kamar ta san me yake tunani, sai cewa ta yi

"Kar ka damu Tareeq, na yi hakan ne sanin cewar a kurkusan nan ba lallai ka iya samun nutsuwar fitar da matar aure ba. Shi ya sa na amince da wannan al'amari. Ka yi tunani sosai zuwa gobe sai mu yi magana." Maama ta ƙare maganar tana kamo hannunsa ta riƙe har lokacin tana kallan sa. Ɗan dafe ƙirjinsa da ya yi masa nauyi ya yi, kafin ya janye hannunsa cikin sakannin da ba su wuce uku ba, ya ɗan lumshe idanunsa kafin ya buɗe a kan Maaman, yana tunanin abin da ya kamata ya ce mata. Shin ya amsa da cewar ya amince bayan abin da ya faru tsakaninsa da Diyana? Ko kuwa ya ce be amince ba saboda fidda rai da ya yi a kan mace. Idan ya buɗe baki ya ce ya amince ya kuma kasance ita kanta Jawahir ɗin halin su ɗaya da Diyana fa? Tun da ita ma Diyanan duk daɗewar da suka yi bai taɓa sanin halinta na zahiri ba sai ana dab da ɗaura musu aure.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 15

Cigaba da kallan sa Maama ta yi tana jira ta ji ko ze ce wani abu. A hankali ya zuro ƙafarsa daga kan gadon zuwa ƙasa. Ya miƙe a kan ƙafafun nasa kafin ya ce

"Shi kenan Maama, duk abin da kika yanke wa rayuwata daidai ne. Amma tun da kina son ji daga bakina In Sha Allah zan yi istihara duk yadda ake ciki zan sanar da ke. Babu damuwa za ki iya sanar da Abeey kafin lokacin." Ya ƙare maganar fuskarsa babu yabo babu fallasa. Cikin ransa fata yake ka da Maaman ta sake jan maganar da nisa, don kuwa har ta ginshe shi. Ba don ma Maaman da kanta ke masa maganar nan ba, da ko haɗin kai ba ze bayar ba. Murmushi ne ya wanzu a kan fuskar Maaman, ta miƙe ita ma kafin ta ce

"In Sha Allah. Allah Ya tabbatar mana da abin da ya fi zama alkhairi."

"Ameen." Ya amsa a saman laɓɓansa yana kai hannunsa guda cikin sumar kansa ya shafa. Maama

Please Login or Register in order to submit comment