Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lumshe a kan ƙofar sashen nasa. A hankali ta saka hannunta ta tura. Kamar yadda ta tsammata kuwa, a buɗe take. Ta ji wani sanyi ya ratsa ta, ta saki murmushi tana saka kanta cikin sashen nasa. Sai dai yaɓe-yaɓe! Don kuwa tana taɓa ƙofar ɗakin ta ji ta ɓame da mukulli. Dakatawa ta yi tana jin yadda zuciyarta ke bugawa. 'Anya kuwa a kullen take?' Ta raya hakan a ranta tana kallon ƙofar ɗakin. Sai kawai ta sake saka hannunta da ke ɗan rawa kaɗan da niyyar turawa, nan ma dai shiru. 'Kenan ƙarya yake, da ya ce sashen nasa a buɗe yake?' Ta tambayi kanta har lokacin idanunta a kan ƙofar. Shiru ta yi na tsawon sakanni, 'Toh ko dai yana nufin sashen ne kawai a buɗe ban da ɗakunansa' Cikin lokaci ƙanƙani wannan tunanin ya faɗo mata. Tunanin da ɗazun kwata-kwata bai kawo mata ba. Saboda yadda ta ƙagu da neman hanyar shiga sashensa kafin cikar sati biyun nan. Cike da ɓacin rai ta fito daga sashe. Ko dubawa ma ba ta yi ba ko da wanda ke kallon ta. Ta ci gaba da takawa gaba ɗaya fuskarta a cakuɗe, jikinta a sanyaye ya yin da take taku cike da sassarfa kuma a hanzarce. A haka har ta ƙarasa sashen Maama. Kamar wadda ba ta da laka, haka taka takawa cikin sashen, zuciyarta gaba ɗaya a cunkushe. Ta ma rasa wanne tunanin za ta ba wa zuciyarta haɗin kai su yi? Ita dai ta san burinta ɗaya ta samu damar shiga ɗakin Tareeq. Don haka dole ne ta miƙe tsaye, ta samo ɗin ko a yi a wuce wajen.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Shi ne abin da kunnuwanta suka soma tsinto mata lokacin da take dab da shiga ɗakin. Ta dakata tana jin yadda zuciyarta ta harba lokaci guda.

"Hatsari kuma? A ina? Tareeq? Hasbunallahu wa ni'imal wakeel." Maama ta faɗa cikin wani masifaffen tashin hankali. Cikin sakannin da ba su wuce goma ba, jikin Daneen ya ɗauki rawa ba kaɗan ba. Ta runtse idanunta tana ci gaba da jin yadda kalaman Maaman ke mata amsa-kuwwa a cikin kunne. Ta kai wajen minti 5 a hakan kafin ta buɗe idanunta.

"Yanzun nan zai fita? Yawwah ki yi amfani da wannan damar wajen shiga sashen nasa, kar ki yi sanya. Na san ba yanzu zai dawo ba. Don haka ki yi abin da na sanar da ke. Sannan kuma tsaya, ki sake tabbatar mini da yanzun zai fita." Maganganun da suka koma yi mata amsa-kuwwa kenan a maimakon na Maama. Tuni ɓarin jikinta ya ƙaru, gumi ya shiga tsatstsafowa daga ko'ina na jikinta. Ta runtse idanunta a karo na barkatai tana tunanin shin me yake faruwa ne?


Afwan da ji na da kuka yi shiru kwana biyu. Na ɗan yi busy ne a kwana biyun, saboda ba na gida. Amma In Sha Allah daga gobe shi kenan.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 26

Duk da yadda take jin ƙirjinta na bugawa ba a daidai ba. A hankali yake bugawa, sai dai da wani irin ƙarfi, hakan bai hana ta yin kasada ba, kawai ta runtse idanunta sannan ta faɗa cikin ɗakin. Daidai lokacin da Maama da idanunta suka yi jajir take faɗin

"Dada ji Tareeq ne wai ya samu hatsari." Yadda ƙafar Dada ji ta yi ƙass ne, tun farkon da ta ji Maama ta ambaci sunan Tareeq ya sanya ta saurin koma wa ta zauna hannunta a kan ƙafar tata. Sai dai cikin tashin hankali take faɗin; idanunta a kan Maama

"Hatsari? Ya Hayyu Ya Qayyum." Ta faɗa har lokacin hannunta na kan ƙafarta. Duk da yadda take jin tana mata zafi, amma tashin hankalin da ta ji kanta a ciki na hatsarin Tareeq ɗin ya danne komai. Ɗaukar mayafi kawai Maama ta yi tana shirin yin waje, Hidaya ta shigo cikin ɗakin. Haka kawai ta ji zuciyarta ta buga tun kafin ta ji abin da ya faru. Kamar kar ta tambaya saboda duk wasu alamu sun nuna ba lafiya ba. Amma kuma hakan ba za ta yiwu ba, don haka ta ce bayan ta ɗan lumshe idanunta

"Maama me ya faru?"

"Hidaya zo ki taimaka mini in miƙe mu tafi. Yayanku ne ya samu hatsari yanzun nan." Wani irin harbawa da ta ji zuciyarta ta yi, shi ne abin da ya sanya ta saurin kai hannunta saitin zuciyarta ta dafe. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunta suka tara hawaye fall. Kwata-kwata ma sai ta kasa furta komai. Ficewar da Maama ta yi ita ta dawo da ita daga hayyacinta. Kawai sai ta fashe da kuka, daidai lokacin da ta ƙarasa inda Dada ji take. Ta sanya hannunta da ke karkarwa ta taimaka mata ta miƙe.

"Ya isa, kukan ya isa haka Hidaya. In Sha Allah ba wani abu ne babba ba." Cikin muryar kuka ta furta

"Ameen." Tana kai hannunta kan fuskarta ta share hawayen. A ranta kawai hasaso ɗan'uwanta take. Fata take Allah Ya sa ba wani abu babba ne ya samu ɗan'uwan nata ba. A tsaye kawai take kamar wadda aka dasa, ban da karkarwa babu abin da jikinta yake yi. Sai da suka fice daga ɗakin gaba ɗaya sannan ta ƙarasa shigewa ciki. Kawai sai ta zube a kan kujerar tana sauke numfashi. Ta kai wajen mintina biyar, kafin ta miƙe ta faɗa cikin ɗakinsu. Ba ta yi wata-wata ba, wajen danna wa number Yohana kira ba. Ringing 1 ya ɗaga wayar, yana shirin fara magana ta katse shi da faɗin

"Me ye alaƙarka da hatsarin da Tareeq ya yi?" Cikin wani irin amo Yohana ya furta

"Hatsari kuma? Yaushe? Ina Tareeq ɗin yake?" Cike da tsoron kar abin da take zargi ya tabbata ta ce cikin dakiya.

"Kar ka nuna kamar ba ka sani ba mana." Ta faɗa da gaba ɗaya gaskiyarta, bayan ta yi ƙoƙari wajen danne duk wani tsoro da fargabar da take ji.

"Amma ba ki kyauta mini ba Daneen, kuma a gaskiya zan faɗa miki ban ji daɗi ba. Me ya sa zan saka hannu wajen yin wani mummunan abu a kan Tareeq? Bayan dukkanmu so muke a hukunta shi a hukumance. Na ɗauka na tura miki abin da nake so ki samo mini a wajen Tareeq, takardu ne fa kawai. Ban da su babu komai. Ke ce fa mai fansar da ta fi muhimmanci da kuma girma, so kike a ɗaukar miki fansar ɗan'uwanki. Kuma shi ne dalilin da ya sa na dage, nake kuma son ke ma ki dage. Amma idan kin ga ba za ki iya ba, ko kuma za ki saka zargi a cikin ranki, toh ina ga babu amfanin ci gaba da zaman ki cikin gidan nan, kawai ki fito ki koma ƙauyenku, ki sanar da su mutuwar Ameer kawai. Idan ya so sai ku nemi wata hanyar da kuke ganin za a iya hukunta Tareeq ɗin." Ya ƙare maganar cikin wani irin yanayi, da ke nuni da yadda ya ji babu daɗi da gaske. Shiru Daneen ta yi, tana jin yadda jikinta ke ƙara yin sanyi. Sai da ta daure, ta yakice komai, sannan ta iya yago magana ta ce

"Toh amma me ya sa ka din ga tambaya ta da gaske yanzu zai fita?" Ta tambaya a sanyaye.

"Kawai so nake na ji, saboda ki je sashensa. Shi ne kawai dalilin da ya sa na tambaye ki. Ban da haka ina ruwana da inda zai je da kuma yake? Duk fa saboda ke ne. Ki yi tunani mana." Shiru Daneen ta yi tana nazarin duk maganganun da ya faɗa. Wajen minti 2, sannan ta sauke ajiyar zuciya, wadda shi kansa sai da ya jiyo sautinta. Ya gyara zamansa daga inda yake zaune kafin ya ce

"Ban ji daɗin yadda zargi ya shiga tsakaninmu ba." Ya faɗa a hankali. Wata ajiyar zuciyar Daneen ta sake saukewa kana ta ce

"Ka yi haƙuri, na kasa ƙaryata abin da zuciyata ke ta hasaso mini ne." Daga haka kawai sai ta ajiye wayar ba tare da ta sake jin wani abu da ya ce ba. Ta zauna yaɓar a kan gadon ɗakin zuciyarta na wani irin zafi. Wata irin kewar Innarta ta ji tana ratsa ta, gefe guda kuma tunanin Ameer ɗin da kullum yana cikin mafarkinta. Ta ƙagu komai ya kammala ta gan ta a kusa da Innarta. Ko ta samu ta ɗora kanta a kan kafaɗarta ko cinyarta su yi kukan rashin Ameer tare, su yi wa Ameer addu'a tare, su kuma tuna shi tare. Miƙewa ta yi a hankali ta shiga zagaye ɗakin, hannunta duka biyun cikin na juna. Gaba ɗaya kwanyarta ta cushe da tunanunnuka kala-kala. Tsoron ta ɗaya kada a ce Tareeq ya rasu a asibiti yanzun. Ba ta so ya mutu ba tare da an hukunta shi ba, ba ta so ya mutu ba tare da an masa hukunci daidai da muguntar da ya yi wa ɗan'uwanta ba. Don haka za ta yi ta masa addu'ar ya rayu, ko don ya karɓi kashinsa a hannu. Tana ci gaba da zagaye ɗakin Sultanah ta shigo da sauri.

"Sister shirya mu wuce asibitin da aka kai Yah Tareeq. Yah Tareeq ne ya yi hatsari." Sultanah ta yi maganar, gaba ɗaya yanayinta na nuni da yadda take cikin tashin hankali. Bin ta da ido kawai Daneen ta yi, ita ma duk nata hankalin a tashe yake. Sai dai ba na komai ba ne face kar ta je Tareeq ya mutu ya bar ta da fansar da ba ta ɗauka ba. Dogon hijab ɗinta Sultanah ta ɗauka ta saka a gaggauce, sai da ta yi hanyar fita sannan ta ce

"Ki fito mu tafi." Daga haka ba ta jira Daneen ɗin ta ce komai ba ta fice daga ɗakin. Babu musu Daneen ta bi bayanta, gwara ta kasance tana kusa, ko babu komai za ta din ga sanin a halin da Tareeq ɗin yake ciki.

... Lokacin da suka isa, an daɗe da shigar da Tareeq emergency, saboda mummunan raunin da ya samu a ƙafarsa. Babu wanda ya samu damar ganinsa. Dukka sai suka yi cirko-cirko suna jiran jin halin da yake ciki hankali a tashe. Sai dai kowannen su addu'a yake, Allah Ya sa ko ma mene ne zai zo ya zo da sauƙi.

"Ubangiji Allah Ya ba ka lafiya yaron nan." Dada ji ta faɗa a sanyaye. Sultanah ce ta iya amsa wa da "Ameen." Ita ma jiki a sanyaye. Ita dai Daneen sai raba ido take. A zahiri ita kanta ma neman lafiyar tasa take, sai dai abin nasu ya fita daban. Don su suna so ne ya samu lafiya kawai, ya yin da ita kuma nata son ya samu lafiyar saboda fansarta ne. A nan suka ci gaba da zama har zuwa shuɗewar wasu lokuta masu tsayi. Zuwa lokacin har Abeey ma ya iso shi da babban amininsa Alhaji Abubakar. Abdoul ma tuni ya iso, don har ya riga ma su Abeey zuwa cikin asibitin.


... Kansa a kwance yake a kan pillow, ya yin da hannunsa ɗaya ke kan fuskar tasa, idanunsa a rufe. Turo ƙofar da aka yi ne ya sanya shi buɗe lumsassun idanunsa da kalarsu ta ɗan sauya. Bai yi yunƙurin tashi ba, duk da ba ya iya ganin mai shigowar. Sai dai tun kafin ta ƙaraso ya fahimci wace ce, don haka a hankali ya shiga miƙewa zaune. Da sauri Maama ta ƙarasa ta gyara masa zaman. Ya zube idanunsa da suka faɗa a kan Maaman yana jin wani irin rauni na kama shi. Ita ma shi take kallo ba tare da ta ce komai ba. Ta ma rasa me za ta ce, ko kuma ta ina za ta fara.

"Maama ni kuma ƙaddarata a ciwwuwwuka take. Ina ta saka ku cikin fargaba koh? Ni kaina ba na jin daɗin hakan. Amma ya zan yi Maama?" Ya ƙare maganar a sanyaye. Kafe shi da idanunta Maama ta yi, tuni fuskarta ta ɗinke tsaff. Kamar ba za ta ce komai ba, sai kuma ta girgiza kai ta ce

"Ga ka dai a haka kamar ka girma ka yi hankali, har kana da ƙannen da za ka tsawatarwa, ashe ba haka ba ne. Tareeq yanzu ni za ka kalla faɗa wa wannan maganar? Waye yake ɗora cuta? Akwai wanda haka kawai yana sane zai ɗora wa kansa cuta? Allahn da Ya jarabce ka da ita shi zai yaye maka In Sha Allah. Za ka samu lafiya cikin yardar Ubangiji." Lumshe kyawawan idanunsa ya yi a hankali kamar mai jin bacci, ya buɗe su a kan Maama kafin ya ce

"Ki yi haƙuri Maama. Amma kuma kina tunanin wannan ƙafar za ta warke kuwa?" Ya ƙare maganar idanunsa a kan ƙafarsa da ke ajje kawai a nannaɗe. Shi kaɗai ya san azabar da yake ji daga cikinta, tamkar ana daddatsa ta da wuƙa irin kakkaifar nan. Ita ma kallon ƙafar tasa ta yi da jajayen idanunta, ta kai wajen minti 1 tana kalla kamar mai nazarin wani abu, sannan ta buɗe baki a nutse ta ce

"Ai Allah na ce." Jinjina kai kawai ya yi, yana koma wa baya, ya jinjina da pillow. A hankali ya ɗan fesar da iska daga bakinsa, kamar wanda ke shirin sake cewa wani abun. Sai kuma ya tsuke bakinsa ya yi shiru. Maama ta nemi waje ta zauna tana kallon ɗan nata cike da tausayawa.


...."Alhamdulillahi, cikin ikon Allah abubuwa da dama da sauƙi. Sai dai kuma.." Likitan ya ɗan dakata a nan yana girgiza bironsa a kan takardar gabansa. Jinjina kai Abeey ya yi alamar yana tare da shi, hakan ne ya sanya shi ɗan ajiye numfashi kafin ya ci gaba da faɗin

"Ƙafarsa.. Gaskiya ƙafarsa ta samu mummunan rauni sakamakon yadda ta maƙale cikin motar sosai, da ƙyar aka iya zaro ta. Kamar yadda aka sanar da ni kenan. Wannan ne dalilin da ya sa.." Sai ya sake dakatawa a nan.

"Ya Hayyu Ya Qayyum." Abeey ya faɗa a fili idanunsa a lumshe. A ransa yana ji lallai lokaci ya yi da Tareeq zai ajiye ko ma mene ne, ya tsayar da hankalinsa a kan kasuwanci kawai. A hankali ya juya ya kalli likitan, yana jin yadda ilahirin jikinsa ya yi matuƙar sanyi, sannan ya ce

"Kaa ga kada ka ɓoye mini komai. Tareeq ɗana ne, saboda haka ka sanar da ni komai a kan matsalar ƙafar tasa."

"Ba zan ɓoye maka ba Ranka ya daɗe, fatanmu na warkewar ƙafarsa har ya miƙe ya ci gaba da tafiya ba shi da yawa. Ƙafarsa ta samu mummunan rauni kamar yadda na faɗa maka, wanda zai iya taɓa lafiyar tafiyarsa. Ba ma fata, ba kuma za mu cire rai ba, In Sha Allah za mu yi masa aikin da idan Allah Ya yarda za a dace. Amma sai dai ka yi haƙuri Yallaɓai, don hakan ba lallai ba ne." Likitan ya ƙare maganar a sanyaye, saboda yadda ya ga yanayin Abeey. Ya san yadda yake matuƙar ƙaunar yaransa, musamman ma kuma Tareeq. Sai dai ga shi Allah Ya fi jarabtarsa da ciwuka. Bai ga kuma amfanin ɓoye masa komai ba, tun da da kansa ya nemi ya sanar da shi hakan. Gwara ma ya sanar da shi gaskiyar, ba su da tabbacin za a samu nasara a aikin, saboda kar sai an yi ba a dace ba, a zo ana wallahi tallahi.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 27

Ɗan jimm Abeey ya yi na tsawon minti ɗaya ba tare da ya ce komai ba. Kafin zuwa can ya sauke ajiyar zuciya, a hankali a kan laɓɓansa ya furta

"Ya Ilahy." Kafin ya maida dubansa kan Likitan ya ce, ilahirin jikinsa a sanyaye.

"Na gode." Shi ne abin da ya iya furtawa kawai, daga haka ya miƙe ya miƙa masa
hannu kana ya juya ya fice daga office ɗin. Bin sa da kallo Likitan ya yi, yana jin wani irin tausayinsa da na ɗan nasa na kama shi. Kai tsaye Abeey ɗakin da Tareeq ke ciki ya nufa. A hankali ya tura ƙofar ɗakin har lokacin jikinsa a matuƙar sanyaye. Har zuwa lokacin Maama tana zaune gefen ɗan nata. Ya ƙarasa a sanyaye bakinsa ɗauke da Sallama, ya ja kujera ya zauna daidai lokacin da Maama ke amsa sallamar tasa. Gaba ɗaya idanunsa na kan Tareeq da sai a lokacin ya amsa sallamar Abeeyn, saboda yadda hankalinsa ya ɗan yi wani wajen.

"Tareeq." Abeey ya ambaci sunansa.

"Na'am Abeey." Ya amsa yana kallon sa. Sai da ya kalli ƙafarsa kafin ya ce bayan ya maida duban sa kan Tareeq ɗin.

"Ya ƙafar taka? Ya kake jin duka jikinka?" Shiru Tareeq ya yi na ɗan wasu sakanni, yana nazarin abin da ya kamata ya ce. Don kuwa idan har gaskiya zai faɗa, toh ba zai iya kwatanta abin da yake ji a cikin ƙafarsa ba. Ya ɗan sosa goshinsa a nutse kafin ya ce

"Alhamdulillahi Abeey, da sauƙi." Murmushin yaƙe Abeey ya yi, a ransa yana ji ina ma a ce hakan ne. Domin kuwa, daga yanayin yadda Tareeq ɗin ya yi magana za ka fahimci kawai ya faɗa ne.

"Allah Ya ƙara lafiya Tareeq. In Sha Allah za ka samu lafiya, kamar ba ka taɓa yin ciwo ba." Jinjina kai ya yi yana murmushi, lokaci ɗaya yana gyara zamansa saboda ciwon da ƙafarsa take ya ɗan motsa. Maama ce ta amsa da "Ameen." Ya yin da shi kuma ya sake kwantar da kansa gefe idanunsa a lumshe.


.... Kallon ta kawai Umma take, duk lokacin da ta shigo ba tare da ta ce da ita ko uffan ba. Ita ma ba ta ce wa Umman komai ba, fita kawai take yi, ta ɗauko kayan ta shigo da su sai kuma ta sake fita. Har zuwa lokacin da ta dawo cikin ɗakin ta zauna jagab a kan kujera tana faɗin

"Washh.." Ta yi maganar tana zame hular kanta idanunta a lumshe. Sai a lokacin sannan Umma ta ce, bayan ta ɗauke duban ta daga kan kayan zuwa kan Jawahir.

"Jawahir, waɗannan kayan fa?" Ta faɗa tana nuna su. Buɗe idanunta Jawahir ta yi ta kalli kayan, sannan ta gyara zamanta a kan kujerar ta ce

"Umma kayan kitchen ne fa." Ta ƙare maganar tana turo baki.

"Iyeeee, yau na ga ikon Allah. Wai Jawahir me ye haka ne? Ba za ki iya haƙuri cikin satin nan na je na siyo miki duk abin da kike buƙata ba?" Sake tura bakinta ta yi kafin ta ce

"Toh Umma ba ga shi na rage miki wasu abubuwan ba. Kuma ma na ga har yanzu kin ƙi zuwa, bayan bikin saura 'yan kwanaki." Dariya Umma ta yi tana girgiza kai. 'Wato a kan Tareeq Jawahir ba ta da kunya.' Ta raya hakan cikin zuciyarta. Ya yin da a fili kuma sai cewa ta yi

"Toh ya yi, sai ki tashi ki shigar da su ciki ki wuce mu je mu duba jikin Tareeq." A razane ta ce

"Jikinsa kuma? Me ya faru da Yah Tareeq ɗin?" Ajiyar zuciya Umma ta sauke kafin ta ce

"Ba ki ga missed call ɗina a wayarki ba? Wallahi ya samu hatsari ne."

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Na shiga uku? Amma dai babu abin da ya same shi?" Ta tambaya a ruɗe idanunta a kan Umman.

"Tashi mu je." Umma ta faɗa tana miƙewa. Ko sake bi ta kan kayan ba ta yi ba, ta ɗauki jakarta ta zura a hammata, har tana riga Umman ma ficewa daga ɗakin.


A cikin satin aka yi wa Tareeq aiki a ƙafarsa, aikin da cikin ikon Allah aka dace matuƙa yadda ba su yi tsammani ba. Don haka cikin farin ciki Likitan da ya jagoranci aikin yake miƙa wa Abeey hannu fuskarsa ɗauke da murmushi yake faɗin

"Congratulations Sir, an yi aiki cikin nasara In Sha Allah." Cikin wani irin farin ciki Abeey ya miƙa masa hannu suka gaisa, fuskarsa na nuni da irin farin cikin da yake ciki.

"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah." Shi ne abin da Abeey ya din ga faɗa. Likitan bai tari numfashinsa ba, sai da ya gama sannan ya ce

"Sai dai za a ɗan ɗauki lokaci gaskiya kafin ya iya taka wa da ƙafar tasa. Ina nufin za a samar masa kujera ne ya din ga duk wasu abubuwa da zai yi a kai. Aikin ƙafa kam an yi nasara, amma ba yanzu zai iya takawa ba, sai zuwa lokacin da Allah Ya nufa, amma fa a yadda muka ga ƙafar tasa, muna kyautata zaton nan ba da daɗewa ba ne In Sha Allah." Jinjina kai Abeey ya yi, duk da yadda ya ji jikinsa ya yi sanyi. Amma kuma idan ya tuna inda Allah Ya taimake su aka yi aikin lafiya sai ya ji sanyi a ransa. Godiya sosai ya yi wa Likitan da ya yi ta sinnar da kai cike da kunyar jin Alhaji Dikko guda na yi masa godiya haka tamkar wanda ya yi masa wani babban abu na musamman.

Ta ɓangaren Daneen kuwa abubuwa sun cakuɗe mata, domin kuwa idan dai har tana lissafi daidai, yanzu haka saura sati ɗaya bikin Tareeq. Don haka gaba ɗaya ta ruɗe, duk wata hanya da za ta sada ta da ɗaki, wajen ajiyar kayan Tareeq kawai shi take nema. Sau da dama ta kan faki idanun mutane ta je sashen nasa, sai dai kamar kodayaushe a kulle dai. Ga shi kusan kullum suna asibiti. Babu damar ta ce ba za ta je ba, don tana tsoron kar a zargi wani abun.


.... "Sannu Yah Tareeq." Hidaya ta faɗa a karo na barkatai. Murmushi Tareeq ya yi har fararen jerarrun haƙoransa na bayyana kaɗan.

"Hidayaaaa.." Ya ɗan ja ƙarshen sunan, jin yadda motsi kaɗan sai ta ce masa sannu. Murmushi ta yi kana ta ce

"Na'am Yah Tareeq."

"Na warke fa." Ya faɗa yana ɗan gyara zaman ƙafarsa.

"Allah Ya sa." Ta faɗa a sanyaye. A hankali ya ɗan kalli gefensa kafin ya maida duban sa kanta ya ce

"Ina Daneen?" Da mamaki shimfiɗe a kan fuskarta ta ɗaga kai ta kalle shi. Tana matuƙar mamakin yadda yake iya kula da rayuwar Daneen ɗin, sosai da sosai yake barin ta da mamaki ya kusan kashe ta. Yadda ya haddace sunanta cikin ƙanƙanin lokaci, yana ɗaya daga cikin abin da ke matuƙar ba ta mamaki. Sai dai abin da ba ta sani ba, kula da rayuwar Daneen ya zama dole a wajensa. Ko babu komai yanzu haka rayuwa take a cikin gidansu. Ya zama dole ya saka wa duk wani takunta ido. Duk yadda aka yi ma Hidaya manta halinsa ta yi. Gefe guda kuma take-taken yarinyar bai yi masa ba. Dalili kenan da ya sa yake lura da duk wani motsinta.

"Yah Tareeq.." Ta ambata cike da mamaki ba tare da ta ba shi amsar tambayar da ya yi masa ba. Sarai ya fahimci abin da take nufi, don haka ya saki wani miskilin murmushi da ya matuƙar ƙawata fuskarsa kafin ya ce

"Ba ni amsa ta." Ya faɗa cikin basarwa. Kafin ta kai ga cewa komai, Daneen ta yi sallama cikin ɗakin kanta a ƙasa kamar wata munafuka. Dukkan su suka bi ta da kallo, kafin Tareeq ya janye nasa idanun. Ga maɗaukakin mamakinsa, abin da bai taɓa ji daga bakin yarinyar ba, sai ga shi ta ce

"Barka da wannan lokacin." Kusan a tare shi da Hidaya suka sake kallon kyakykyawar fuskarta da har zuwa lokacin ba ta ɗaga ta ta kalle su ba. A karo na biyu ya sake janye idanunsa yana ɗan taɓe bakinsa, kamar ba zai amsa ba sai kuma ya ce

"Barka dai. Ya jikinki?" Har ta ɗaga kai za ta kalle shi, sai kuma ta fasa, don so take duk wani zargi da ta fara karanta a kan fuskarsa ya fice masa a rai. Don haka so take ya ɗauka kunya ce da rashin sabo ke hana ta gaishe shi, ko kuma yi masa ya jiki, duk da yadda shi ba ya gajiya, a kullum idan za su haɗu sai ya yi mata ya jiki, duk kuwa da ta warke, sai ɗan abin da ba a rasa ba.

"Alhamdulillah. Ya jiki?" Ta yi ƙarfin halin faɗar hakan, a yanzu tana kallonsa. Ba tare da ya kalle ta ba ya amsa da "Alhamdulillah." Daga haka gurin ya ɗauki shiru. Ita dai Hidaya kallon su kawai take yi su duka kamar ta samu T.V. Sai zuwa can sannan ta ce

"Sister ki zo ki zauna mu yi hira." Murmushin nan na yaƙe, wanda ake cewa ya fi kuka ciwo Daneen ta saki tana girgiza kanta. Da ƙyar ta

Please Login or Register in order to submit comment