Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya furta

"A'ah, bari na ɗan je waje." Ta yi maganar tun kafin ma Hidaya ta ce komai ta fice daga ɗakin. Hidaya ta bi ta da kallo tana murmushi kafin ta maida duban ta kan Tareeq.


.... Shiru Maama da Dada ji suka yi, bayan da suka gama sauraron bayanin Abeey duka. Bayan wajen shuɗewar mintina biyu sannan Maama ta ce

"Yanzu ya za a yi kenan?" Ta tambaya a sukwane. Ajiyar zuciya Abeey ya sauke kana ya ce

"Toh! Ni dai ban yanke komai ba. Amma abin da yake akwai kawai shi ne aurensa da Jawahir za a yi cikin satin nan kar a fasa. Idan ya so kin ga faɗuwa ta zo daidai da zama, sai ta ci gaba da kula da shi. Amma ya kika ce Dada ji?" Cikin na'am da zancen Abeey Dada ji ta ce

"Tabbas zancenka ya yi Alhassan, kuma In Sha Allah hakan shi ne mafita. Ko babu komai Jawahir 'yar'uwar Tareeq ce, kuma tana son shi, kula da shi a yanayin da yake ciki In Allah Ya yarda ba zai zama matsala ba. Abin da nake so da ku kawai, ku fara shirye-shiryen aure, domin kuwa kamar yadda aka tsaida shi sati mai zuwa, ba za a daɗa ba, ba za a rage ba. Za a ɗaura shi In Sha Allah. Allah Ya sa hakan ne mafi alkhairi, Allah Ya ba su zaman lafiya, Ya ba wa yarinyar nan ikon kula da Tareeq har zuwa lokacin da zai warke."

"Ameen." Dukkansu suka amsa da hakan, cikin na'am da maganar Dada jin ɗari bisa ɗari.


.... A karo na barkatai ya sake kallon kyakykyawar matarsa da ke zaune a kan kujera. Sai dai ta kwantar da kanta a kan hannun kujerar da take kai ne, hannunta ɗaya yana gefenta kan kujerar, ya yin da ɗayan yake lilo kusa da kanta. Idanunta a lumshe suke, sai dai duk da haka, hakan bai hana ƙwalla sauka a kan kyakykyawar fuskarta ba. Cike da tausayawa yake kallon ta. A kullum a kodayaushe yana rasa ta ina zai soma rarrashinta? Ta ina zai ba ta baki a kan yanayin da ta tsinci kanta? Yana ji a jikinsa tamkar shi ne sila, shi ne silar rugujewar farin cikinta. Sai dai duk da haka, ya zai yi? Ta ya ya zai iya jure ci gaba da kallon ta cikin wannan yanayin? Tunani ya yi wa ƙwaƙwalwarta yawa, a kodayaushe tunani take. Idan aiki take tunani take, idan ta zauna ta yi shiru tunani take, idan bacci take ma duk mafarkin abu ɗaya take, haka zalika ko magana suke, sai dai ya ji shiru, idan ya kalle ta kawai sai ya ga alamar ta faɗa wata duniyar tunani. Wataran kuma sai dai kawai ta zauna ta yi ta kuka, musamman ma idan ba ya kusa da ita, shi ya sa kwata-kwata ba ya son yin nesa da ita. Don ba ya so abin ya yi yawa, kar ya janyo mata babbar matsalar da ta fi wadda take ciki a yanzun wato Depression.

"Fatoum.." Ya faɗa a sanyaye kamar yadda ya saba kiran ta da hakan. A karo na farko ba ta ji ba, sai da ya sake maimaitawa sannan ta buɗe idanunta da sauri ta tashi zaune sosai tana kallon sa da jajayen idanunta.

"Na'am." Ta faɗa tana yin amfani da hannunta wajen goge fuskarta.

"Ba za ki yi ƙoƙari wajen rage damuwar nan ba koh? Kin manta abin da Likita ya faɗa koh? Ki yi haƙuri don Allah ko da ba za ki daina duka ba, don na san hakan abu ne mai matuƙar wahala, amma a ƙalla ki rage don Allah. Ko da ni ma zan samu salamar zuci. A kullum idan na kalle ki cikin irin wannan yanayin, ina ji tamkar ni ne sila, kai ba ma tamka ba, ni ɗin ne dai sila. Don Allah ki yi haƙuri Fatoum ki fawwala wa Allah komai, za mu dace In Sha Allah." Duk tsayin maganar nan da ya yi, murmushi kawai ta yi idanunta na kallon wani wajen ta ce

"Uhumm." Ta faɗa tana girgiza kai. Shiru ya yi yana kallon ta, ya sauke ajiyar zuciya kafin a sanyaye ya sake kiran sunanta a tausashe. Sai a lokacin tamkar wadda ta dawo daga tunani sannan ta kalle shi, a hankali ya ɗaga mata kai kafin ya ce

"Ki yi mini magana mana." Tamkar jira take, sai kuwa ta shiga girgiza kai, tana jin ɗacin kalaman da take tattarawa za ta faɗa. Tun kafin fitar su ma tana jin ɗacinsu ballantana kuma ta faɗe su. Sai dai duk da haka, hakan bai hana ta soma faɗin

"Na rasa yadda zan yi, ban san me zan yi in ji daɗi ba. Tunanin nan da nake zaunawa na yi shi kaɗai ne mafita ta. Duk da yadda nake ji tamkar ƙwaƙwalwata za ta tarwatse. Amma ba zan iya hana kaina tunanin yarana ba. Ni idan da mutuwa ne ma suka yi, zan haƙura, na san zuciyata za ta fi samun salamar suna can cikin kwanciyar hankali In Sha Allah. Amma yanzu fa? Ban san inda suke ba, ban san suna cikin wane irin hali ba. Shin a wane waje suke rayuwa? Shi ma ban sani ba. Yaushe ne Allah zai haɗa mu? Duk ban sani ba. Yallaɓai ina ji tamkar zuciyata za ta faso ƙirjina ne ta fito ta tarwatse, ina ji kamar ƙwaƙwalwata za ta fashe idan ina tuna su. Ina iya ƙoƙarina wajen ganin na bar wa Allah komai, amma na kasa daina tunaninsu. Kullum suna cikin ko'ina na jikina a manne, komai nake su ɗin ne dai a raina. Shin ya zan yi ni kam da raina? Ina zan ga yarana?" Ta yi maganar a raunace. Ajiyar zuciya ya sauke, yana jin daɗin yadda yau ɗin ta amayar da abin da ke cikin zuciyarta. Ba kamar sauran ranaku da ta fi son ta yi shiru, ko kuma ta yi guntuwar magana ba. Ya runtse idanunsa yana ji da gasken gaske shi ne sila! Shi ne silar raba wannan uwar da 'ya'yanta. Shin me ya sa ma ya shiga rayuwar Fatima? Tabbas da ya san haka ne zai faru, da bai yi yunƙurin neman auren Fatima ba. Ko kuma ma tun farko ya yi fatan kar Allah Ya haɗa shi da Fatima.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 28

Ya shafe kusan mintuna biyu ba tare da ya ce komai ba. Kallon ta kawai yake yi cike da tausayawa, zuciyarsa kuwa wani irin raɗaɗi yake ji, raɗaɗin kuma ba na komai ba, sai na zamowarsa silar rugujewar farin cikin Fatimarsa.

"Ki yi haƙuri, in sha Allah yaran nan suna cikin ƙoshin lafiya, kuma za su dawo miki cikin ƙoshin lafiyar. Abin da nake so da ke kawai ki ci gaba da addu'a, sannan ki rage wannan damuwar da kike yi. Kada ki manta da shawarwarin likita da ya ba mu. In Allah Ya yarda nan ba daɗewa ba za mu samu labarin inda suke, tun da har yanzu ban daina cigiya ko Allah zai saka a dace ba. Ki yi haƙuri ki yi shiru." Ya ƙare maganar cikin rarrashi da taushin murya. Hannu Inna-wuro ta saka ta goge fuskarta a nutse, idanunta a lumshe tana ci gaba da jin bugun zuciyar da take fama da shi kusan kowanne lokaci. A hankali ta buɗe baki da ƙyar ta furta

"Allah Ya sa." Ta faɗa tana maida bayanta ta kwantar kan kujerar da take kai cikin rashin sanin abin yi. Bin ta ya yi da kallo ba tare da ya ce komai ba. Ya rasa ta inda zai ɓillowa wannan al'amari. Shiru kawai ya yi ya ci gaba da kallon ta yana tunanin hanyar da zai bi wajen tsananta bincike ko Allah zai sa a dace su sami inda yaran nan suke.


... Turo ƙofar da aka yi shi ne ya sanya Maama ɗaga ido ta kalli mai shigowar. Umma da kuma Jawahir suka ƙaraso cikin ɗakin. Da murmushi ta miƙe tana faɗin

"Lale marhaba." Maida mata da martanin murmushin suka yi kana Umma ta nemi waje ta zauna. Ya yin da Jawahir ta tsaya a gefen kujerar Umman tana sunnar da kai ƙasa. Gaisawa Umma da Maama suka yi, Umman na tambayar jikin Tareeq.

"Jiki Alhamdulillahi wallahi, zuwa gobe ma idan Allah Ya kai mu, muke saka ran sallama, kamar yadda suka faɗa."

"Kai Alhamdulillah, Alhamdulillah. Ashe ƙafar ta yi sauƙi ke nan, ko ma in ce ta warke?" Umma ta faɗa tana murmushi. Sai da Maama ta kalli ƙafar Tareeq ɗin da idanunsa ke a lumshe kamar mai bacci kafin ta ce

"Alhamdulillah kam, ta warke za a ce. Sai dai... Ba ku yi magana da yayan naki ba ne?" Ta ƙare maganar da sigar tambaya. Girgiza kai Umma ta yi tana faɗin

"A'ah, ba mu yi ba kam. Amma yau sun haɗu za su yi magana da Abban Jawahir."

"Barka da wannan lokacin Maama." Jawahir ta faɗa tana murmushi. Amsa mata gaisuwar Maama ta yi cikin sakin fuska, har ranta tana ji in Allah Ya yarda ta yi sa'ar suruka. Sun kwashe wajen minti 20, kafin Tareeq ya buɗe idanunsa.

"Sannu Tareeq." Umma ta faɗa tana kallon sa. Sai da ya ɗan saki murmushi kaɗan, wanda ya ƙawata kyakykyawar fuskarsa sannan ya ce

"Yawwah, Barka da wannan lokacin." Ya yi maganar a haɗe.

"Barka dai, ya jikin?" Sai da ya jinjina kai sannan ya amsa da

"Alhamdulillahi." Nan ta sake yi masa fatan samun sauƙi, Maama ta amsa da "Ameen."

"Yah Tareeq ina wuni?" Jawahir ta faɗa tana satar kallon wannan kyawawan ƙwayar idanun nasa. Ta kafe shi da idanunta, tun kafin ma ya ɗago nasa ta kasa kalla. A hankali ya ɗaga nasa idanun ya kalle ta, ya ɗan lumshe su, lokaci guda yana buɗewa ya ce

"Alhamdulillah Jawahir, kina lafiya?" Ya yi ƙarfin halin faɗin hakan. Sai da ta gyara tsayuwa tana jin wani irin farin ciki na mamaye ta sannan ta ce

"Lafiya ƙalau." Daga haka ta sake mazewa a gefe ba tare da ta zauna ba. Hannu Maama ta saka ta yafito ta tana faɗin

"Kin ga ni ba na son wata kunya zo ki zauna. Baƙuwarki ce ni?" Ta ƙare maganar tana dariya. Ita ma Umman dariya ta yi, ya yin da Jawahir ke ta murmushi kawai. Kamar yadda Maaman ta faɗa, don haka ta nemi waje ta zauna kuwa.

Bayan shuɗewar wasu mintuna aka fara kiraye-kirayen Sallahr Maghrib, duk suka yi alwala suka dawo cikin ɗakin. Maama ta kalli Tareeq ta ce

"Za ka yi alwalar ne?"

"Ehh.." Ya amsa mata da hakan. Ƙarasawa ta yi keɓantaccen wajen da aka ajje masa kujerar da ba a daɗe da kawo ta ba, ta ɗakko ta, ta ƙaraso da ita inda yake. A hankali ta shiga taimaka masa don ganin ya zauna a kan kujerar. Wani irin ƙwarewa Umma da ta zuba ruwa a tambulan tana sha ta yi, ruwan da ta ji ya shige mata har tsakar ka. Ta saka hannunta ta shiga bubbuga kanta har lokacin idanunta a kan Tareeq. Har ba ta san lokacin da ta furta

"Ba ya iya tafiya ne?" Ta faɗa tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki na bayyana cikin muryarta. Ba tare da kawo komai a ranta ba Maama ta ce

"Wallahi kuwa, kin ga dai ikon Allah." Wani irin bugawa zuciyar Umma ta shiga yi fat!fat!fat! Ba za ta iya jurewa ba, don haka jiki duk a sanyaye ta ce

"Kenan har tsawon wane lokaci zai ɗauka yana zama kan kujerar nan?" Tana ci gaba da taimaka masa ɗin dai ta ce

"Har zuwa lokacin da Allah Ya nufa. Su kansu likitocin ba su sani ba, sun dai ba mu tabbacin idan Allah Ya yarda watarana zai iya miƙewa a kan ƙafarsa. Shi ne ma dalilin da ya sa Abeeyn Tareeq yake so a yi auren daga zarar an sallame shi, kin ga daga an ɗaura aure sai Jawahir ta ci gaba da kula da shi."

Wani irin kuka mai ƙarfi Jawahir ta fashe da shi, tana jin yadda ilahirin jikinta ke karkarwa. Kawai sai ta zube a kan gwuiwoyinta tana ci gaba da raira shi. Maama ta kalle ta cike da tausayi, don ta san kukan na tausayin halin da Tareeq ya tsinci kansa a ciki ne. Duk da ba ta sake jin wata magana daga bakin Umma ba, ba ta damu ba, ta shiga tura Tareeq zuwa toilet don ya ɗauro alwala. Shi dai bai ce komai ba, bai kuma nuna alamar yana tare da su ba, duk da yadda cikin zuciyarsa yanayin yadda Umma ta yi magana ya shigar da shi wani yanayi na kokwanto da kuma fargaba. Komawa Umma ta yi kawai ta zauna a kan gado idanunta a kan Jawahir. Shiru ba tare da ta ce komai ba, take ci gaba da kallon ta. Ta kasa furta komai, ta kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ne. Ita ta haifi Jawahir, ta kuma fi kowa sanin halinta. Wannan kukan da take, daga ita Jawahir ɗin, sai kuma ita suka san na mene ne.

Suna yin Sallahr Maghrib suka bar asibitin, bayan sun yi sallama da Maama a gaggauce. Shi dai Tareeq bin su kawai ya yi da kallo, don ba ƙaramin mamaki yanayin yadda suka fita daga asibitin ya ba shi ba. Ita kuwa Maama ba ta kawo komai a ranta ba, ta ci gaba da harkokinta.


... "Toh shi ke nan, amma kin san abin da za a yi?" Maami da ke riƙe da waya kare a kunnenta ta faɗa bayan ta nemi waje ta zauna. Daga can ɓangaren aka ce

"A'ah."

"Kin san halin 'yar taki, ba za ta taɓa yarda da auren haɗi ba. Saboda haka ki turo yaron ya zo da niyyar ya zo gaishe ni, daga nan zan san yadda za a yi su haɗu. Bayan ya tafi sai na sanar da ita ya nemi da a ba shi numberta. Kin fahimci fa'idar yin hakan?" Jinjina kai matar ta yi kamar Maamin na gabanta kafin ta ce

"Ehh, na gane. Hakan kuma ya yi matuƙa, Allah Ya haɗa mana kansu."

"Ameen." Maami ta amsa da hakan. Daga haka ba su ƙara wasu mintuna masu yawa ba, suka yi sallama. Murmushi Maama ta saki tana kallon Maman Abdoul da ke zaune kujerar da ke kusa da tata.

"Barkan ki da wannan lokacin Madam."

"Barka dai Hajiyata.. Wai Sultanah ake nema wa abokin haɗi?" Ta haɗe gaisuwar da tambayar ta yi su lokaci guda. Jinjina kai Maami ta yi kafin ta ce

"Ita fa. Amma ki yi a hankali kar ta ji. Kin san halin Sultanah."

"Na sani kam. Amma me zai hana tun da ga na gida a tafi wani wajen? Wallahi da mun haɗa ta da Abdoul. Ina son yarinyar wallahi, ko don nutsuwarta." Girgiza kai Maama ta shiga yi kana ta ce bayan ta yi murmushin yaƙe

"A'ah ke kam, wani irin haɗi kuma tsakanin Abdoul da Sultanah?"

"Wallahi kuwa ƙawata, na ɗauka kamar sai ya fi koh?" Sake girgiza kai Maami ta yi ta ce

"Toh ai kin ga mun riga mun gama magana da Hajiya Ati, da ba mu yi magana ba sai a yi yadda kika faɗa ɗin." Ɗan jujjuya kanta Maman Abdoul ta yi sannan ta ce

"Toh hakan ma ya yi. Allah Ya tabbatar da alkhairi." Sai a lokacin sannan Maami ta saki murmushi tana faɗin

"Ameen, ƙawata."


... Gyara zamansa Abeey ya yi, kafin ya ɗan sauke ajiyar zuciya. Dukka hankalin 'yan ɗakin sai ya dawo gare shi. Sai da ya gabatar da addu'a sannan ya soma faɗin

"Wato dalilin haɗa wannan taro da na yi ba komai ba ne, face don na sanar da ku ɗaurin auren Tareeq da za a gabatar da shi ranar juma'ar nan mai zuwa idan Allah Ya yarda. Ba kuma shi da kowa ba face 'yar'uwarsa Jawahir. Muna fatan Allah Ya tabbatar da alkhairi, Ya kuma kaɗe dukkanin abin ƙi. Idan wani na da magana zai iya yi."

"Toh, Allah Ya amsa addu'o'in nan, sannan kuma Ya yi muku albarka gaba ɗaya. Ni kam me ya kamata na ce? Bayan godiya ga Allah. Tun da ga shi jikokina biyu suna ƙoƙarin auren junansu. Allah Ubangiji Ya sanya albarka." Dada ji ta faɗa, har cikin muryarta farin cikin da take jin ta ciki na bayyana.

"Ameen." Maama ta faɗa tana murmushi.

Wani banzan kallo Umma take watsa wa Jawahir daga inda take zaune. Duk da sanin halin 'yar tata, amma ko babu komai ta san za ta ji kunyar buɗe baki ta yi magana, musamman saboda kwarjinin Abeey. Amma ya za su yi? Ya zame musu dole su magantu. Ita dai Jawahir ta rasa ta inda za ta fara. Shin me za ta furta kai tsaye ba tare da wani kwane-kwane ba, wanda ko ba ta yi bayani ba za a fahimci abin da take nufi? Tabbas ta san tana son Tareeq, ba kuma don komai ba sai don kyawunsa, kyawun surar da Allah Ya ba shi. Tafiyarsa, komai nasa su ne suke burge ta, ko kuma ta ce su ne take so. Toh yanzu kuma ga shi babu ƙafa, yana zaune ne a kan kujera, ya zama gurgu, mara ƙafa. Kenan me za a kira shi? 'Musaki?' Ta ji zuciyarta ta yi saurin ba ta amsa. Ta runtse idanunta tana jin yadda zuciyarta ke ci gaba da bugawa. Ke nan duk yadda ta tsarawa rayuwarta hakan ba zai yiwu ba? Wato suna nufin ta auri Tareeq a yadda yake a yanzun, ke nan me za ta je yi gidan auren? 'Bauta' Ta sake jiyo hakan a cikin kwanyarta. Tuni har ta fara hasaso kanta a cikin gidan Tareeq. Duk da kayan alatun da ke gidan, ta san muddin ta shiga gidan nan tata ta ƙare. Sai dai ta lalace a banza a wofi wajen kula da nakashashshshen mijin da ake ƙoƙarin liƙa mata. Ita ba ta san da gaske ba shi take so ba, ƙirar jikinsa take so ba sai yanzu. Yadda kuma ta ji zuciyarta ta yi na'am da hukuncin da suka yanke ita da Ummanta ya ƙara tabbatar mata da hakan. Don haka cikin ƙarfin hali, ta tattaro jarumta ta afawa kanta. Ta haɗiye tsoron da take ji, kafin ta runtse idanunta na tsawon wasu sakanni, kana ta buɗe. A hankali ta buɗe bakinta da ƙyar ta soma faɗin

"Abeey don Allah ka yi haƙuri, amma ba zan iya auren Yah Tareeq a halin yanzu ba." Gaba ɗaya mutanen ɗakin kallon ta suke yi cikin matuƙar tashin hankali, idan ka cire Umma. Cikin matuƙar mamaki Maama ke ci gaba da kallon ta, tana jin abin kamar wani wasan yara. Cikin ƙarfin hali ta furta

"Jawahir, kin san me kike faɗa kuwa?" Ta faɗa jikinta a matuƙar sanyaye, wanda ya ja har muryarta ma a sanyayen take. Shiru Jawahir ta yi, ta kasa ɗaga ido ta kalli Maaman. Sam Maama ba ta yi tunanin za ta sake jin wata magana daga bakin Jawahir ba, duk kuwa da ita ta tambaye ta. Amma sai ta ji ta ce

"Eh Maama. A yi haƙuri don Allah."
Wani irin kallo Sultanah da Hidaya suke bin Jawahir da shi. Gaba ɗayansu sun kasa furta komai. Ganin abin suke kamar almara, ko kuma shirin film. Anya kuwa Jawahir ɗin ce? Jawahir dai Jawahir masoyiyar Yah Tareeq? Cike da ƙarfin hali, da kuma ƙaryata abin da kunnuwanta suka jiye mata Dada ji ta ce bayan ta sauke duka idanunta a kan Umma.

"Maimunatu, kin ji abin da yarinyarki take faɗa kuwa?"

Ɗaga idanunta Umma ta yi ta kalli Dada ji. Karo na farko da ta fara kallon Dada ji ɗin ba a matsayin mahaifiyarta ba, bayan tsawon shekaru masu yawa. Ba za ta iya bari a ce tana ji tana gani, duk yadda ta ci buri da 'yarta a ce ta ƙare a auren nakashashshshe, musaki, mara ƙafa ba. Wanda ko likitoci ba su da tabbacin zai warke ko kuwa nan gaba kaɗan za a yanke ƙafar ne idan ta daina aiki. Daga lokacin kenan sunan ɗiyarta zai tashi daga Jawahir ya koma 'Matar Gurgu' Abin da ba za ta iya jurewa ba ke nan. Tabbas ta matuƙar so haɗin Tareeq da Jawahir, ko don yadda Jawahir ɗin ke son shi. Ita kuma tana matuƙar ƙaunar abin da ɗiyarta ke so, shi ya sa ta yi ta fafutuka wajen ganin auren nan ya yiwu. Amma fa a lokacin ba ta taɓa tunanin Tareeq ɗin zai tashi daga cikakke kuma lafiyayyen mutum zuwa nakashashshshe ba. Don haka ba za ta iya jure ganin 'yarta ta ƙare rayuwarta wajen kula da miji ba, a banza a wofi ta lalace. Kullum babu hutu, sai dai kula da nakashashshshen miji. Ina za ta iya zuba ido ta din ga kallon shalelen 'yarta cikin wannan hali? Hakan ne ya sanya ta ɗan jan wani numfashi, tana ji ya zama dole ta buɗe baki ita ma ta magantu ko da hakan na nufin rugujewar zumuncinsu.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 29

"Ki yi haƙuri Dada ji, ban san me zan yi mata ba." Shi ne abin da ta faɗa, ba tare da ta bari sun haɗa ido da ita ba. Kallon ta kawai Dada ji take yi cike da tsananin mamakin da ya hana ta furta komai. Ji take kamar ba gaske ba ne, waɗannan maganganun ba daga bakin Maimunatun suke fitowa ba.

"Jawahir har cikin zuciyarki kike faɗar wannan maganar?" Abeey ya faɗa bayan ya kalli Jawahir ɗin. Kasa haɗa ido ta yi da shi, kawai ta ci gaba da kallon wani wajen kana ta buɗe baki da niyyar soma magana, Abeey ya katse ta da faɗin

"Ɗaga idanunki ki kalle ni sannan ki tabbatar mini da abin da kika faɗa." Kamar ba za ta ɗaga idanun nata ba, haka dai ta daure ta kalli Abeeyn a ɗan tsorace. Ba ta buƙatar ƙarin bayani, don ta san abin da yake buƙatar ta ce, don haka ta buɗe baki ta ce

"Eh Abeey a yi haƙu..." Ɗaga mata hannun da Abeey ya yi, shi ne ya sanya ta katse maganar da ta fara, ta yi saurin yin ƙasa da kanta. Tun da ta fara magana ya ɗaga lumsassun idanunsa ya kafe ta da su, ba ya buƙatar wani ƙarin bayani daga Jawahir. Domin kuwa, duk wani bayani da yake so ya sani ya fuskance shi daga cikin muryarta. Ya san Jawahir tana son shi, bai kuma taɓa tunanin tana son shi don ƙirar jikinsa ba, duk da yadda ya kamata ya fahimta, ko don yadda maganganunta da yawa ba sa wuce a kan kyawunsa ne da sauran su. Amma bai taɓa barin hakan ya yi tasiri a zuciyarsa ba. Sai ga shi yanzun ƙiri-ƙiri ta bayyana ba za ta iya aurensa ba, ba kuma don komai ba sai don nakasar da ya samu a ƙafarsa. A hankali ya lumshe idanunsa yana jinginar da kansa kan kujerar da yake kai ba tare da ya ce komai ba. Dubansa Abeey ya maida kan Umma ya ce

"Maimunatu kin amince da abin da yarinyar nan take faɗa?" Ya ƙare maganar har lokacin yana kallon ta. Shiru ta yi na tsawon sakanni kamar mai tunani, kafin ta gyara zama ta ce

"Toh ya zan yi da ita Yaya? Ita ta ce tana so tun farko, yanzu kuma ta ce ba ta so saboda wani dalili. Sai nake ganin kamar babu abin damuwa, tun da dai ra'ayi ne. A yi haƙuri kamar yadda ta faɗa ɗin." Tun da ta fara magana Abeey ke kallon ta har ta ƙarasa. Ya yi matuƙar mamaki, maganar Umma da ita kanta Jawahir ɗin sun ba shi mamaki. Ya kuma jefa shi cikin shakkun halayya da ɗabi'un mutane da ka iya sauyawa cikin ƙanƙanin lokaci. Bai taɓa tunanin haka daga Umman Jawahir ba. Bai taɓa tunanin akwai ranar da za ta zo, don Tareeq ya samu nakasa a ƙafarsa ta bi bayan ɗiyarta na ƙin aurensa ba. Ta ɓangaren Dada ji kuwa shiru ta yi tana kallon Maimunatun. Lallai duk inda aka ce ɗa ba naka ba ne, wani lokacin sai hakan ya bayyana. Tun da ta ɗauki Maimunatu take riƙe da ita tsakani da Allah ba tare da ta taɓa nuna mata wani bambanci tsakaninta da Alhassan ba. Duk wanda ma bai sani ba, ba zai taɓa cewa Umman ba 'yar Dada ji ce ba. Don kuwa tun da take ba ta taɓa buɗe baki ta ce ba 'yarta ba ce. Kullum burin ta

Please Login or Register in order to submit comment