Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abin da ya kamata ta furta ke nan, sai dai bugun da zuciyarta ke yi, ya tabbatar mata ba ta amince da hakan ba. A karan kanta ma sai take ji idan har muggan kalamai suka fito daga bakinta zuwa Tareeq ɗin, shi ke nan ta kwafsa komai. Komai ya ruguje musu. Toh amma kuma idan ba ta ce hakan ba, me za ta ce? Za ta buɗe baki ne ta ce ta amince da aurensa ko kuwa? Kusan mintuna biyar a haka, kafin ta sauke idanunta bayan sun yi wani irin ja. Shiru Tareeq ya yi na tsawon mintuna yana sake faɗaɗa tunaninsa a kan irin kallon da ya ga Daneen ɗin na yi masa. Sai dai kafin ya ida tunanin, ya tsinto muryarta tana faɗin

"Ba zan iya ba. Ni ba kowa ba ce, face wadda ke zaune a cikin gidanku saboda alfarma. Kar ka ce za ka saka mini ba ka ƙoda da na yi ta hanyar aure na. Ba zan iya ba." Ta ƙare maganar tana fashewa da kuka. Duk da ba har zuciyarta take faɗar hakan ba, kawai ta faɗa ne don kare kanta, saboda yadda ta lura da kallon tuhuma ɗin da yake bin ta da shi. Doguwar ajiyar zuciya Tareeq ya sauke mara sauti. Ko babu komai wannan maganganun da ta faɗa sun ruguza wannan karyayyen tunanin nasa da ya fara.

"Kar ki yanke hukunci cikin gaggawa. Ki je gaba ɗaya yinin yau ki yi tunani. Abin da nake so da ke kuma, ki cire wannan tunanin na cewar zan aure ki ne saboda in biya ki ƙodarki da kika ba ni. A'ah." Ya faɗa yana girgiza kai.

"Har abada ba zan iya biyan ki ba."

"Ba zan iya ba." Ta faɗa da ƙarfin gaske, tana jin wata irin wutar ƙiyayyarsa na sake ruruwa a cikin zuciyarta. Wannan wace irin rana ce? Wanda ya zamo silar mutuwar Ameer shi ne yake neman da ta amince ta aure shi? Wane irin sakaci ita kuwa ta yi? Ta yaya ma za ta iya aurensa bayan ta shigo gidan ne da niyyar ɗaukar fansa, ba kuma a kan kowa ba face shi? Ta aure shi ta ce ta auri me ke nan?

"Saboda yanzu ba na taka wa a kan ƙafata?" Ya jefa mata tambayar muryarsa a dake. Da sauri ta ɗaga idanunta ta kalle shi. Ya jinjina mata kai bayan ya ɗan saki wani murmushi ya ce

"Duk abin da kika yanke ki sanar da ni. Amma ki sani, idan ba ki amince ba, zan ɗauki hakan a matsayin saboda abin da ya sami ƙafata ne. Ko da yake, babu damuwa za ki iya tafiya." Ai tun kafin ya dire maganar ta soma barin wajen cike da sassarfa, haɗa hanya kawai take yi, kamar za ta kifa. A haka dai har ta ƙarasa ɗakinsu. Zubewa ta yi a kan gadon tana fashewa da wani kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Yau ɗin wata irin kewar Ameer ce ta dawo mata sabuwa, sai take ji tamkar yau ne Ameer ɗinta ya tafi ya bar ta. Sai take ji tamkar a yanzu ne suke magana ita da Ameer, maganar tasu da ta zamo ta ƙarshe. Ta cure cikin bargo waje ɗaya tana ci gaba da sheshsheƙar kuka cike da kewar Ameer da Innarsu. Ji take kamar ta watsar da komai ta koma ƙauyensu. Toh amma kuma ba ta da tabbacin idan ta koma ƙauyen ma za ta sami Innarsu, uwa uba kuma idan har ta bar gidan, ke nan hakan na nufin ruhin Ameer ya tafi a banza ke nan? Bayan ga shi tana da damar da za ta iya yin wani abu, wanda har zai kai su ga samun nasara. Wannan dalili, shi ne kaɗai abin da ya sa ta ji zuciyarta ta yi na'am da ci gaba da zaman ta cikin gidan, daga nan sai ta bazama ƙauyensu don biɗar Innarsu. Ta shafe fiye da awa ɗaya a wajen, kafin kamar wadda aka mintsina ta sakko daga kan gadon, kai tsaye toilet ta faɗa, ta rufe shi, sannan ta danna kiran Yohana. Jin tana neman katsewa kafin ya ɗaga ne ya sanya ta faɗin

"Ka ɗaga mana, ka ɗaga mana.." Daf da za ta tsinke ɗin kuwa ya ɗaga, ta sauke wata ƙatuwar ajiyar zuciya.

"Daneen." Ya ambata kamar yadda ya saba kullum saboda tsaro.

"Na'am." Ta ambata da muryarta da ta fara dashewa saboda kukan da ta sha.

"Oh my gosh! Me ya faru Cutie?" Ya faɗa cike da mamakin yadda ya ji muryarta ta sauya. Sai da ta ja wata ajiyar zuciyar kafin ba tare da ɓata lokaci ba ta shiga kora masa duk wasu abubuwa da suka faru.

"Puhahaha..." Ya sheƙe da wata mahaukaciyar dariya, wadda ta matuƙar ba wa Daneen mamaki, wanda har hakan sai da ya bayyana a kan fuskarta. Ya kai wajen minti ɗaya kafin ya ce hallau dai cikin gurɓatacciyar hausarsa.

"Buɗe kunnenki da kyau ki ji. Wannan wata dama ce muka samu. Sanar da shi kin amince da aurensa, da ma ba hanyar shiga ɗakinsa muke nema ba? Idan kika aure shi ai dole ki shiga ɗakinsa, ko ma in ce dole a kai ki ɗakinsa. Kin ga damar da muke so ta samu, a cikin kwana biyu za ki iya samar mana abin da muke buƙata, kin fahimta? Saboda haka kar ki damu, aure ne kawai da za ku yi na kwanaki ƙidayayyu, daga zarar kin samo mana abin da muke nema shi ke nan sai ki nemi takardar saki." Tun da ya fara magana take jin zuciyarta na wani irin harbawa kamar za ta fito daga ƙirjinta. Ita dai haka nan kawai take jin tsoro na shigar ta, duk da kamar yadda ya faɗa ɗin hakan shi ne mafitar su, toh amma ta yaya za ta yi aure ba tare da sanin Innarta ba?

"Kuma ko an ce za a je ƙauyenku don sanar da kishiyar kakarku kamar yadda kika faɗa wa Alhaji Dikko, ki san yadda za ki ki hana, saboda kar a kwaɓa mana aiki." Ta jiyo muryar Yohanan kamar ya san abin da take tunani. Ta sake yin shiru na tsawon wasu sakannin kafin ta buɗe baki da ƙyar ta ce

"Toh." Daga haka ta katse wayar, ta yi shiru tana sake nazarin abubuwan da ya faɗa. Tabbas idan dai har mafita suke so, toh abin da Yohana ya faɗa shi ne daidai. Sai dai kuma idan ta haƙura da ɗaukar fansar ne. Abin da kuma ba ta ji zuciyarta ta yi na'am da hakan ba. Ran ɗan'uwanta fa, Ran Ameer ɗinta fa. Ta runtse idanunta a hankali zuciyarta a cunkushe, wanda ta rasa dalilin hakan.


... "Sultanah ina yi miki magana kin yi shiru, wai ma ni sa'ar ki ce ne?" Maami ta faɗa a fusace tana kallon ta. Runtse idanunta Sultanah ta yi cikin rashin sanin abin yi, ta rasa me Maamin take nufi da ita. Ruwan da ke gaban ta Maami ta ɗauka ta kai bakinta ko za ta daina jin zafin da take ji cikin zuciyarta.

"Maami ba zan iya auren wani idan ba Yah Abdoul ba. Ban taɓa faɗa miki ba ne, amma na daɗe da soyayyar Yah Abdoul danƙare a cikin zuciyata. Kuma maganar da nake miki yanzu ma haka mun yi nisa ni da shi, har ya ce ma nan da lokaci kaɗan zai sanar wa da Abbansa." Wata daƙiƙiyar ƙwarewa da Maami ta yi, ita ce ta sanya Sultanah tana kai ƙarshen maganar da ta ɗauko ta yi shiru. Ta miƙe da sauri tana faɗin

"Sannu Maami." Ta faɗa bayan ta zuba ruwa cikin tambulan ta miƙa mata. Hannu Maami ta saka ta karɓa kawai, sai dai maimakon ta sha ruwan sai ta ci gaba da tarin har zuwa lokacin da ya yi sauƙi ba tare da ta sha ruwan ba. Kallon ta kawai Sultanah take yi, tana fata ta kalle ta da idon rahama, ta kalle ta da idon tausayi irin na mahaifiya.

"Wanne Abdoul ɗin kike nufi?" Wata irin ajiyar zuciya Sultanah ta sauke, tana jin daɗin tambayar Maamin. Ta yi murmushi kana ta ce

"Maami Yah Abdoul fa namu, Yah Abdoul na Yah Tareeq." Ajiye kofin hannunta Maami ta yi, duk wani tashin hankali ya gama bayyana a kan fuskarta. Sai dai cikin dakiya ta ce, duk da yadda harshenta ke ƙoƙarin bijire mata wajen yin maganar, amma haka ta daure, ta cije ta yi iya bakin ƙoƙarinta.

"Na riga na zaɓa miki miji Sultanah." Shi ne kawai abin da ta iya faɗa. A take idanun Sultanah suka tara ƙwalla, ban da bugawa babu abin da zuciyarta ke yi. Cikin tashin hankali ta ce

"Maami ki yi mini afuwa. Ina son Yah Abdoul, wallahi ina son shi matuƙa, zuciyata za ta iya bugawa idan ban same shi ba. Maami taɓa ki ji yadda zuciyata ke harbawa, ban san halin da zan tsinci kaina ciki ba idan maganar da kike faɗa ta zama gaskiya. Maami Abdoul fa abokin Yah Tareeq, ɗan gidan aminin Abeey, kuma ɗan gidan amiyarki. Ki yi mini wannan alfarmar don girman Allah Maami." Ta ƙare maganar tana fashewa da sabon kuka. Kukan da ke fitowa tun daga ƙasan zuciyarta, wadda ke mata wani irin zafi, zafin da rabon da ta ji shi tun kafin Abdoul ya zo mata da tayin soyayyarsa. Ta daɗe rabon da ta ji shi, har ta fara sabawa da farin ciki, sai ga shi rana ɗaya, Maami na neman tarwatsa mata wannan farin cikin. Don kuwa ta san raba ta da Abdoul babban abu ne, wanda ba ta sani ba ko zuciyarta na da ƙarfin ɗauka. Ganin da ta yi Maami ta yi mata shiru ne ya sanya jikinta ya ƙara yin sanyi. Ta girgiza kanta tana jin yadda lokaci guda ya yi mata wani gingirin.

"Maamina ki ce wani abu mana don Allah." Ta faɗa cikin kuka. Sai bayan shuɗewar wasu sakanni masu yawa, sannan Maami ta miƙe, cikin ƙarfin hali ta ce

"Gwara ma ki cire ranki, don wallahi ba za ki auri Abdoul ba. Ke kika ce za ki ɗaga mini hankali wallahi sai na tsine miki a banza. Ki kama kanki, idan ba haka ba ran kowa ya ɓaci. Idan na ce kowa ina nufin kowa." Ta dakata a nan sannan ta ci gaba da faɗin

"Kuma idan kika sake kika fita daga cikin ɗakin nan za mu haɗu da ke. A nan za ki kwana daga nan har zuwa lokacin da za ki amince da ƙudirina." Daga haka ta bar wajen cike da sassarfa ta shige ɗakinta. Runtse idanunta Sultanah ta yi tana jinginar da kanta a kan kujera, yau kam wace irin baƙar rana ce a gare ta? Me Maami take faɗa haka? Shin da gaske abin da yake faruwa gaskiya ne, ko kuwa wani mummunan mafarki ne take yi, wanda ke neman datse mata farin ciki? Sai a lokacin sannan ta iya fashe wa da wani marayan kuka, ta cure waje ɗaya tana kifa kanta a tsakiyar gwuiwoyinta, ta shiga raira shi, cikin rashin sanin abin yi.


... Jinjina kai Dada ji take yi cike da mamakin wannan al'amari na Ubangiji, wato ba ta taɓa kawo wa har cikin ranta Tareeq ɗin zai yi wannan tunanin mai matuƙar amfani ba. Sai ga shi da kansa ya samar wa kansa mafita.

"Wato ina ga na fi kowa farin ciki da wannan abu ya faru, Ubangiji Allah Ya tabbatar da alkhairi, Ya yi muku albarka. Alhassan." Ta ƙare maganar tana kallon Abeey. Cikin girmamawa Abeey ya ce

"Na'am Dada ji."

"Ina ganin a gobe goben nan, ba sai wata rana ba, a ɗaura auren nan kowa ma ya huta." Cikin na'am da zancen Dada ji Abeey ya ce

"In Sha Allah Dada, duk yadda kika faɗa haka za a yi." Ya faɗa har cikin muryarsa za ka iya fahimtar yana cikin farin ciki. Don kuwa tabbas ya yi farin cikin matuƙa.

"Amma ina so da kaina na ji daga bakin yarinyar, kafin nan sai na san abin yi." Jinjina kai Dada ji ta yi kafin ta ce

"Gaskiya ne wannan, hakan na da kyau."

Wayarsa Abeey ya ɗauka ya kira number Hidaya.

"Turo mini Daneen yanzu." Kasancewar ta san inda suke ya sanya ta amsa wa da "Toh Abeey." Daga haka ta miƙe ta je ta kira Daneen ɗin, a ranta tana fatan Allah Ya sa abin da take tunani ne yake shirin kasancewa. Har ƙofar ɗakin Abeey ta raka ta, tana shirin juyawa Daneen ta yi saurin riƙo hannunta tana faɗin

"Hidaya."

"Na'am." Hidaya ta amsa bayan ta kalle ta. Narkar da fuska ta yi, kamar wadda ke shirin yin kuka ta ce

"Tsoro nake ji, ba zan iya shiga ni kaɗai ba." Hannunta Hidaya ta kama tana murmushi

"Toh mu je in raka ki." Ajiyar zuciya Daneen ta sauke, kana ta bi bayanta suka shige ɗakin Abeeyn.

Sai da suka gaisar da kowa, sannan wajen ya ɗauki shiru na tsawon mintuna. Zuwa can Abeey ya soma faɗin

"Ɗiyata Daneen, shin kin amince da auren Tareeq kamar yadda ya sanar da ni?" Runtse idanunta Daneen ta yi na tsawon sakanni, kafin tun kafin ta kwafsa, kawai sai ta ɗaga kanta a sanyaye.

"Ma Sha Allah! Alhamdulillah." Dada ji ta faɗa cikin wani irin farin ciki. Shi ma ajiyar zuciya Tareeq ya sauke, yana ji bayan wani lokaci yau ga wata mace ta amince da aurensa, ba don dukiyarsa ba, ba da niyyar mallake masa dukiya ba, ba kuma don ƙirar jikinsa ba, ba kuma don tana son shi ba. Sai kawai don kimarsa da darajarsa a wajenta. Lallai kuwa Daneen ɗin za ta ci gaba da kasancewa mai daraja da kuma ƙima a wajensa. Bayan wajen shuɗewar mintuna goma Abeey ya ce

"Zan ɗauke ki mu je ƙauyenku saboda sanar da mariƙiyarki batun aurenki da za a gabatar a gobe." Tun kafin ya ƙarasa maganar ta ji zuciyarta ta buga. Don haka yana ida wa ta fara faɗin bayan ta ɗaga kanta karo na farko ta kalli Abeeyn. Sai a lokacin ne ma sannan ta fahimci Hidaya ba ta cikin ɗakin.

"A'ah kar ka je don Allah. Za ta iya yin duk wani abu don kar a yi auren nan. Ka yi haƙuri kar ka je." Ta faɗa har lokacin tana girgiza kai ƙirjinta na ci gaba da bugawa. Cike da tausayawa Tareeq ke kallon Daneen, lallai tabbas rayuwar yarinyar nan akwai tarin ƙalubale a cikinta. Gaba ɗaya 'yan ɗakin ma da kallon tausayin suke bin ta da shi. Abeey ya sauke ajiyar zuciya tausayin yarinyar na sake kashe masa jiki.

"Kar ki damu, kar kuma ki yi kuka. A yanzu ɗin nan mu ne iyayenki In Sha Allah. Ba ma za ta ji labarin ba ballantana ta hana."

"Alhassan kamar yadda ta faɗa ɗin a bari idan babu damuwa. Idan komai ya lafa shi Tareeq da kansa sai ya ɗauke ta ya kai ta can ƙauyen nasu wajen kishiyar kakar tasu." Dada ji ta faɗa. Jinjina kai Abeey ya yi kana ya ce

"Abin da nake nufi ke nan ni ma Dada." Ya dakata a nan kafin ya maida duban sa kan Maama ya ci gaba da faɗin

"Saboda haka ku fara shirye-shiryen duk wasu abubuwa da suka dace, In Sha Allah gobe ne ɗaurin auren. Duk wasu abu da ake buƙata a yi su daga baya."


... Tsaki ya ja a karon farko yana kallon mai kiran nasa. Kamar kar ya ɗaga, sai kuma ya tamke fuskarsa, yana shirin ɗagawa kiran 4ps ya shigo wayar. Sai ya sauke ajiyar zuciya, duk da ya san shi ma ɗin ba lallai ne su kwashe ta da daɗi ba. Kara wayar ya yi a kunnensa bayan ya ɗaga, daga can ɓangaren Pops ya ce

"Yohana."

"Yes, Pops."

"Kana ina?" Pops ɗin ya faɗa, cikin muryarsa babu alamun wasa.

"Me ya faru?" Ya katse shi da tambayar hakan.

"Ka zo ka ɗauke ajiyar ka."

"Amma Pops.."

"Na dai faɗa maka, barin garin ma za mu yi gaba ɗaya. Idan kuma ba ka yi hakan ba za ka ga ba daidai ba." Numfashi ya sauke yana jin ransa na ɓaci, be ce komai ba ya datse kiran yana jan tsaki. Har wani huci yake fitarwa saboda tsabar ɓacin rai. Wato Babansa na son ya kwaɓa masa aiki. Ya dafe goshinsa yana tunanin ta ina zai fara?


... Tun ɗazu yake ganin wayar tana kawo haske babu ƙaƙƙautawa. Alamar kira ne ke ta shigowa. Don haka ya ɗan ja gajeren tsaki, kafin ya janyo wayar. Ganin sabuwar number ce ya sanya shi jefar da wayar ya kwantar da kansa kan bangon gadon idanunsa a lumshe. Zuwa can sai ya ji alamar shigowar saƙo, ya ɗan gyara zamansa kana ya janyo wayar ya buɗe saƙon, cikin zuciyarsa yana mamakin yadda ya ji ya zaƙu da son karanta labarin tun da ya ji alamar shigowar saƙo.

"Shege, wai har ni za ka nuna wa ba ka gane waye ni ba? Duk iya shegen nan fa mu ma mun iya shi, ka fi kowa sanin hakan. Shi ya sa na yi yadda zan yi na nemo number ɗinka, na kikkira kuma ka ƙi ɗagawa. Dalili kawai nake so na ji na abin da ka aikata. Amma dai kar ka manta duk iya shegen nan ni ma na iya fa, musamman ma kuma yanzu da na ƙaro wani."

Ya karanta message ɗin ya kai sau biyar, kamar wanda ke shirin haddace duk wani rubutu, da kuma wasalin da aka yi amfani da su wajen rubuto saƙon. Ya yi shiru yana jin yadda zuciyarsa ke ɗan bugawa, wanda hakan ya tilasta masa lumshe idanunsa. A hankali ya sake kwantar da kansa jikin bangon gadon, yana jin yadda saƙon ke ci gaba da yi masa amsa-kuwwa cikin kunnuwansa, tamkar wanda ake sake karantowa. Ba ya fatan abin da yake tunani ya tabbata. Ya fi awa ɗaya a hakan, yana ci gaba da saƙawa da warwarewa, zuciyarsa tamkar za ta yi bindiga. 'Ko kuwa dai batun aurensa ne ya zagaya har inda ba su yi tunani ba, wanda hakan ka iya janyo tabbatuwar tunaninsa?' Ya tambayi kansa, duk da ya san babu mai ba shi wannan amsar.


... Washe-gari ta kasance ranar Juma'a, wato ranar da za a ɗaura aure. Bayan an yi Sallahr Azahar, a babban masallacin Dikko da ke cikin unguwarsu, Abeey da ya zama waliyyin amarya, ya karɓi sadakinta a hannun Alhaji Abubakar (Mahaifin Abdoul) wanda shi kuma ya zamo waliyyin ango. Cikin ƙanƙanin lokaci dubban mutane suka shaida ɗaurin auren DANEEN da kuma angonta TAREEQ ALHASSAN DIKKO. Ɗaurin auren da duk da ba a wani shirya masa ba, amma manyan mutane da dama sun samu halartar ɗaurin auren. Kafin ka ce mene ne wannan, tuni maroƙa sun fara shela, ta hanyar faɗin

"Allah Ya nufa. Tabbas Allah Ya nufa. Aure ne irin na girma, an ɗaura auren Shalele, ɗa ga Alhaji Dikko, Tareeq, tare da amayarsa Daneen. Alƙawarin Allah Ya cika." Maganganun da suka tilasta shi runtse idanunsa ke nan, wani babban al'amari da bai yi tsammani ba, shi ne bugun zuciyar da ya ji ya ziyarce shi. A nutse ya buɗe bakinsa, a kan laɓɓansa ya shiga furta.

"Ya Hayyu Ya Qayyum."


Alhamdulillah! A nan na kawo ƙarshen littafin DANEEN Book 1. Mai son ci gaba da karanta DANEEN Book 2 har zuwa Book 3, zai tura ₦500 ne ta..

8124818273
Zahra'u Yusuf Ishaq
Opay

Shaidar biya ta wannan number 08124818273

Ko kuma kai tsaye a tuntuɓe ni ta 08124818273.


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment