Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma kar wani ya gane ba ita ta haife ta ba. Duk wata kulawa da ya kamata uwa ta ba wa ɗiyarta ta ba wa Umma. Babu abin da ta rage ta da shi wanda uwa za ta yi wa ɗanta. Sai ga shi lokaci ɗaya ta guji jininta, don kawai Allah Ya jarabce shi da ciwo. Ciwon da suke fata da addu'ar Allah Ya yaye masa, Ya sa ya warke. Amma ita da ɗiyarta sun juya masa baya, sun nuna ba su yarda da ƙaddara ba, sun fito fili sun nuna dalilin da ya sa suke son Tareeq, ba tare da tunanin yadda hakan zai janyo tangarɗa wa zumuncinsu ba.

"Za ku iya tafiya. Allah Ya saka da alkhairi." Abeey ya faɗa yana jin yadda zuciyarsa ke zafi. Ya fi jin zafin ƙanwar tasa a kan ɗiyarta, domin bai taɓa zaton haka daga gare ta ba. Ba su ce komai ba dukkansu suka miƙe, ba tare da sun kalli kowa ba, suka fice daga ɗakin. Daidai lokacin da suka fito daga ɗakin, ita ma Maami ta fito daga nata sashen. Ta kalle su saboda yadda ta gan su kamar a birkice. Ba wani mutunci suke yi da Umman ba, amma yau ɗin sai ta ji ina ma a ce suna yi, ko don ta ji abin da ya faru, saboda yadda yanayin Umman ya nuna kamar ba lafiya ba. Kamar ba ita ba, ta ce bayan ta ɗan rage tazarar da ke tsakanin su

"Lafiya me ya faru?" Ta faɗa tana ƙare musu kallo, kallon da a idanunsu ya fi kama da na rainin hankali ko wulaƙanci. Wani banzan tsaki Umma ta sauke tana jan hannun Jawahir, kamar ba za ta ce komai ba, don kwata-kwata ba ta yin Maamin, amma sai ta ce

"Ban sani ba. Idan gulmar kike so, me ya hana ki zuwa taron da Yaya ya shirya? Ba fa na son iya-shege." Umma ta ƙare maganar tana jefa mata wani banzan kallo. Daga haka ba ta jira ta ce komai ba, ta ja hannun Jawahir suka wuce suka bar ta a wajen. Bin su ta yi da wani wulaƙantaccen kallo, tana ji yau ɗin gaba ɗaya ta gama muzanta. Me ya sa ma ta yi mata magana bayan dama tun can ba shiri suke yi ba? Ta ja tsaki tamkar za ta tsinka harshenta. Baƙin ciki ya bi ya cika mata zuciya. Kawai sai ta juya ta koma sashenta ranta a mugun ɓace.

A ɗaya ɓangaren kuwa tun bayan da suka fita shiru ne ya biyo baya na tsawon mintuna masu yawa. Babu wanda ke da niyyar cewa komai, saboda yadda dukkanninsu kowa da abin da yake saƙawa. Sosai zuciyarsa ke masa wani irin zafi. Wanda rabon da ya ji shi tun bayan rabuwarsa da Diyana. Me ya sa ba shi da sa'a ne shi kam? Sun yi soyayya da Diyana kamar babu gobe, sai dai ashe gaba ɗaya tana son shi ne don dukiyarsa, dukiyar da ta yi ƙoƙarin mallake ta tun kafin ta kai ga shigowa gidansa. Ba domin ikon Allah ba da tuni wani zancen ake ba wannan ba. Bai so Jawahir ba, amma kuma ya amince da aurenta, ita kuma ga abin da ya faru. Kenan shi ƙaddararsa a kan soyayya take? Ko kuwa ya kira ta a kan mace ne? Macen ma wadda sai yana dab da aurenta?

"Hidaya." Da kaushashshiyar muryarsa ya ambaci sunan, bayan ya buɗe idanunsa da suka rine daga fari fat, zuwa ja. Shi kaɗai ya san irin zafin da yake ji a ƙirjinsa. Ba ya tunanin zai iya ci gaba da zama cikin ɗakin, gwara ya samu ya keɓance kansa ko ya ji sukunin abin da yake ji.

"Na'am Yah Tareeq." Ta faɗa a matuƙar sanyaye tana kallon ɗan'uwan nata cike da tausayawa. Tun kafin ya yi magana ta fahimci abin da yake nufi, don haka ta miƙe, kai tsaye ta ƙarasa bayansa ta shiga tura shi. Daidai suna dab da gifta Maama ta yi ƙarfin halin faɗin

"Ba na son tunani Tareeq. Ka samu ka yi bacci, za mu yi magana zuwa safiya. In Sha Allah hakan ne mafi alkairi, kar ka saka wa kanka damuwa. Hakan ma taimakonmu Allah Ya yi, ta hanyar nuna mana masoyanmu na gaske da kuma waɗanda ba na gaske ba." Shiru ya yi yana saurarar abin da Maaman take faɗa, bai ce komai ba kawai ya jinjina kansa, suka wuce. Ita ma Dada ji bin su ta yi da kallo cike da tausayin jikan nata.


... "Wai me kike jira ne? Ko dai kin haƙura kin fasa ɗaukar fansar ɗan'uwan naki? Ko dai ba kya so a hukunta Tareeq ne?" Maganganun da Yohana ya faɗa mata ke nan, waɗanda suka saka ta yin shiru kamar mai nazari. Kafin ta kai ga cewa komai ya sake faɗin

"Anya kuwa kina lissafin ragowar kwanakin da muke da su? Cikin sati biyu kwana nawa muke da shi? Ki faɗa mini idan kin fasa ne in daina damun kaina." Sai a lokacin sannan ta sauke ajiyar zuciya, ta buɗe baki da ƙyar ta soma faɗin

"Ina nan ina iya ƙoƙarina. Na matuƙar gode da kulawa, kuma in Allah Ya yarda za ka ji ni zuwa gobe. Na gaji da zaman gidan nan kwata-kwata, ba na son ci gaba da kasancewa gida ɗaya da mutumin nan. Ba na son ganinsa ko kaɗan, duk lokacin da na gan shi kewar ɗan'uwana dawo mini take. Ina jin zuciyata na mini zafi, wani irin abu ke tokare mini a ƙirji ya din ga tokare mini numfashi. Ba na son ganin sa ko kaɗan. Zan yi ƙoƙari in Allah Ya yarda a cikin kwana biyu in san yadda zan yi in shiga ɗakinsa." Jinjina kai Yohana ya yi kafin ya ce

"Yawwah, ki ƙoƙarta. Kar ki manta har yanzu ruhin ɗan'uwanki na can cikin rashin salama. Gwara a yi maza a hukunta shi ko ruhinsa ya samu salama." Jinjina kai kawai Daneen ta yi kamar yana gabanta. Soma fahimtar halinta da ya yi ne ya sanya shi fahimtar ta ji abin da ya faɗa. Don haka bai sake cewa komai ba, kawai ya katse wayar. Daidai lokacin da aka turo ƙofar ɗakin aka shigo. Ita ma kuma daidai lokacin ta fito daga cikin toilet. Hidaya da Sultanah ne, suka sakar mata murmushi kusan lokaci guda. Maida musu da martanin murmushin ta yi, kana ta ƙaraso cikin ɗakin.

"Ohh, kwata-kwata ba na jin daɗin jikina yau ɗin nan wallahi." Sultanah ta faɗa tana ɗan dafe kanta bayan ta zube a kan luntsumemen gadonsu.

"Ke dai malama kawai ki ce Yah Abdoul bai kira ki ba." Hidaya ta faɗa tana dariya. Harara Sultanah ta jefa mata kana ta ce

"Lallai ma Sisi, wallahi ba ki da dama. Toh ko damuwar Yah Tareeq ai ta isa ta hana mu walwala daga ni har ke ɗin." Cikin na'am da zancen Sultanah Hidaya ta kwantar da kanta kan pillow kana ta ce

"Wallahi ke kam ki bari kawai. Duk jikina a sanyaye yake tun jiya wallahi."

"Daneen." Hidaya ta faɗa tana kallon Daneen da ta yi shiru tana kallon wani wajen kamar mai tunani. Da sauri ta kalli Hidayan ba tare da ta ce komai ba. Cikin mamaki ta ce

"Lafiya kuwa?" Ɗan murmushin yaƙe ta aro ta yafa a kan fuskarta kafin ta ce

"Babu komai."

"Kin tabbatar 'yar'uwa?" Hidaya ta sake tambaya cikin kulawa. Jinjina kanta ta yi tana miƙewa. Ta ce bayan ta kalli Hidaya

"Bari na ɗan fita." Jinjina kai Hidaya ta yi tana faɗin

"Tohm." Daga haka Daneen ta fice daga ɗakin, ya yin da Hidaya da Sultanah suka bi ta da kallo har ta fice.

"Ba ta da walwala gaba ɗaya, kamar akwai wani abu da ke damun ta." Sultanah ta faɗa har lokacin ba ta daina kallon inda Daneen ta ɓace wa ganinsu ba. Cike da amincewa da zancen nata Hidaya ta jinjina kai kana ta ce

"Na gani fa.. Ga shi ba ta saurin sabo. Ta ƙi sakin jikinta kwata-kwata ballantana mu shiga jikinta."

"Wallahi, abin na ba ni mamaki." In ji Sultanah.

A hankali take taka wa cikin palourn, sanye take cikin doguwar rigar atamfa, da kuma dogon hijabin da ya wuce har ƙasan gwuiwarta.

"Ohk." Shi ne kawai abin da ta ji, wanda hakan ya matuƙar tsorata ta, don ba ta yi tsammanin akwai wata halitta cikin ɗakin ba. Domin dai kuwa ita ba ta gani ba.

"Wayyo Allah na." Ta faɗa bayan ta dafe ƙirjinta, maganar tata ke nan da ta ɗauki hankalinsa. Ya ɗaga kai ya kalle ta, daidai lokacin da ita ma ta sauke nata a kansa. Sam ba ta yi tsammanin ganinsa a wannan lokacin ba. Kafin haɗuwar idanunsu waje ɗaya ta yi saurin janye nata tana sakin ajiyar zuciya, lokaci guda rashin annurin fuskarta na sake bayyana. Wani irin ɓacin rai tuni ya mamaye ta.

'Kar ki kwafsa' Ta ji wani ɓangare na zuciyarta ya gargaɗe ta. Ji take kamar ba za ta iya ba, amma haka ta daure, ta cije, ta kuma yi iya bakin ƙoƙarinta wajen haɗa kalmomi ta ce

"Barka da wannan lokacin." Shiru ya yi yana nazarinta na tsawon sakanni. Kamar kuma ba shi ba, sai ya janye idanunsa kafin ya ce

"Barka dai. Ina za ki je?" Ya ji tambayar da yake tsarawa cikin ransa ta yi masa katsalandan wajen fitowa. Har ta ware idanunta da niyyar kallon sa, sai kuma ta fasa, don ba ta so kallon fuskarsa ya tuna mata da waye shi. Dalili ke nan da ya sanya ta faɗin

"Na ga su Hidaya suna hutawa, shi ne na ce bari na tambaye ka ko za a gyara maka ɗaki ne." Ta ƙare maganar ita a karan kanta tana jin wani banbarakwai. Shiru ya yi na tsawon sakanni ba tare da ya ce komai ba. Har ta cire ran zai amsa, ta kuma ji haushin kanta sannan ta jiyo muryarsa can ƙasa ya ce

"Yanzu dai ba na buƙata kam." Ya dakata a nan. Bai yi niyyar sake cewa wani abu ba, sai dai ko babu komai ita ɗin mace ce mai muhimmanci a rayuwarsa, bayan haka kulawa ce ta nuna a gare shi, yana da kyau ko ya ya ya nuna ya yaba. Don haka ya ce

"Amma idan ina buƙata zan yi miki magana. Kira mini Sultanah ko Hidaya." Ya yi maganar lokaci guda. Cike da takaici da haushi ta juya ba tare da ta ce komai ba. Ya ɗan lumshe idanunsa na tsawon lokaci yana saƙe-saƙe a cikin zuciyarsa. Har bai san lokacin da Sultanah ta ƙaraso cikin ɗakin ba. Sai da ya ji hannunta saman kujerar da yake kai sannan ya ankara.

"Yah Tareeq." Ta faɗa tana kallon yadda duk wasu alamomi suka nuna ya dawo daga tunani ne. Ba tare da ya amsa kiran sunansa da ta yi ba ya ce

"Kai ni ɗakin Maama." Ya faɗa kai tsaye. Babu musu ta tura shi har zuwa bedroom ɗin Maaman. Daga haka ta juya. Maama ta kalle shi tana faɗin

"A'ah, ƙarasowa ka yi kenan." Jinjina kai ya yi kana ya ce

"Ehh Maama, wata muhimmiyar magana nake so mu yi."

"Toh! Ikon Allah! Me ya faru kai kam? Sanar da ni." Maama ta ƙare tana gyara zamanta. Ya yi shiru yana nazarin ta inda zai fara maganar, duk da yadda duka jikinsa ya yi na'am da abin da ya yanke. Bai san ya daɗe cikin ɗakin ba tare da ya ce komai ba, sai da Maama ta ce

"Tareeq!" Ta kira sunansa cike da mamakin yadda ta ga ya faɗa duniyar tunani. Duk da ta ga tarin damuwa a kan fuskarsa, sai dai hakan ba abin mamaki ba ne, duba da abin da ya sake faruwa tsananinsa da Jawahir. A hankali ya ɗan lumshe idanunsa a nutse kana ya buɗe su a kan Maama. Cikin nutsuwa ya soma magana, kamar wanda ba ya so a ji abin da yake faɗa.

"Maama.."

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 30

"Ina ganin idan har kin amince da abin da zan faɗa, toh na samu mata." Ya ƙare maganar yana kallon ta. Cike da mamaki wanda ya bayyana a kan fuskarta, Maama ke kallon sa. Jin abin take kamar a mafarki. Ya samu mata fa yake faɗi? Ta yaya? A ina? Yaushe hakan ta faru? Anya kuwa ma Tareeq ɗin ne? Duka waɗannan tambayoyin ita kaɗai take yi wa kanta cikin zuciyarta, sai dai har lokacin idanunta na kansa. Bayan wajen shuɗewar sakanni talatin sannan ta ce

"Mata kuma Tareeq? A ina? Wace ce ita? Yaushe kuma kuka haɗu har ka ji ta kwanta maka a rai, har za ka iya auren ta? Faɗa mini Tareeq." Ta yi maganar cike da zaƙuwa da jin amsar da za ta fito daga bakinsa. Hannunsa ya kai a hankali ya ɗan murza goshinsa, kafin ya lumshe idanunsa a nutse yana jin wani irin nauyi cikin ƙirjinsa. Ta ɗauka hakan da ya yi yana nuni ne da ya haƙura da yin maganar saboda yadda ya ga tsananin mamaki a kan fuskarta. Sai dai ga mamakinta sai ji ta yi ya ce

"Maama idan dai har kin amince, zan auri Daneen, idan ita ma ta amince." Wani irin kallo Maama take bin Tareeq da shi, kallon da lokaci guda ya fassara shi da 'Anya kana da hankali?' Bin sa da kallo Maama ta ci gaba da yi ba tare ta ce komai ba. Cikin zuciyarta addu'a take yi, Allah Ya sa ba ƙwaƙwalwar yaronta ce ta taɓu ba. Daneen fa? Cike da fargabar da ta zo ta yi mata dirar mikiya lokaci guda ta ce

"Tareeq." Ta faɗa bayan ta sake kafe shi da idanunta. Saukar da kansa ƙasa ya yi, jikinsa a matuƙar sanyaye. Bai yi tunanin samun cikas tun a wajen Maama ba, shi ya sa ma ya fara yi mata maganar.

"Ka san me kake cewa kuwa? Daneen ce matar da kake nufi ka samu? Da gaske kake yi?" Ta faɗa cike da tashin hankali. A nutse ya ɗan sauke ajiyar zuciya, yana jin har cikin ransa daɗin tambayar da Maaman ta yi masa. Ko babu komai zai fayyace mata komai, dalilansa na son auren Daneen ɗin. Ya ɗan ja numfashi kaɗan yana ajiyewa, kafin ya buɗe baki a nutse ya soma faɗin

"Maama na yi tunani, na yi tunani har na gaji. A zamanin nan ban san kuma wace mace ce za ta so ni tsakani da Allah ba. Na gwada ta waje, ta ba ni kunya. Kun gwada 'yar'uwa, ita ma ta ba mu kunya. Toh a duk tunanin da na yi, na ga babu wadda ta dace in aura da ta wuce Daneen." Daga haka ya ɗan dakata bayan ya sauke gajeren numfashi a hankali. Ba ya buƙatar jin wani abu daga bakin Maama a kan maganar da ya yi, don haka ya ci gaba da faɗin

"Yarinyar nan ta ɗauki ƙodarta ta ba ni, ba tare da sanin waye ni ba. Ba tare da buƙatar komai ba Maama. Ba kya tunanin ta cancanta na aure ta?"

"Idan kuma da wata manufar ta bayar fa?" Maama ta yi saurin katse shi da faɗin hakan, tun kafin ya ida sauke maganar. Lumshe idanunsa ya yi a hankali, yana buɗewa lokaci guda.

"Ba haka ba ne Maama, hakan ne amma kuma har yanzu ba mu gane ta ba? Ko ma hakan ne ƙoda fa ta ba ni Maama, idan dai har dukiyata take so, ba ma sai ta yi abin da Diyana ta yi ba, wallahi zan iya mallaka mata. Wanda ba na tunanin ma hakan ce a ranta. Idan kuma za ta ƙi ni ne saboda wani abu, ina ganin a yau ɗin nan zan fahimta. Don kuwa idan har kin ba ni dama, toh zan je in same ta ne da maganar a yau ɗin nan. Ina so ranar da su Abeey suka shirya ɗaura aurenmu da Jawahir, a ɗaura a ranar kar a fasa, idan dai kun amince." Ya ja wata ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa cike da gajiya da dogwayen maganar da yake ta yi, wanda za ka iya fahimta ta cikin muryar tasa.

"Ko dai da ma tuntuni kana sonta ne?" Maama ta faɗa idanunta a kansa. Ɗan murmushin gefen baki ya yi kafin ya ce

"Maama, a jiya na yanke shawarar auren ta, da ba a fasa aure na da Jawahir ba ba zan yi wannan tunanin ba. Hakan na nufin akasin abin da kika faɗa kenan?" Ya ƙare maganar kamar mai neman amsa, sai dai ba amsar yake so ba, don haka ya ɗora da faɗin

"Amma dai tabbas na amince zan aure ta, a matsayin mace mafi muhimmanci a rayuwata. Wadda ta sadaukar da wani sashe na jikinta ta ba ni. Sannan kuma ta amince da aure na, duk da yadda 'yar'uwata ta ƙi ni saboda ƙafata."

"Idan ta amince ke nan?" Maama ta yi masa wannan tambayar. Sai ya jinjina kai kawai a nutse. Maama ta gyara zaman ta kana ta ce

"Ba mu san wace ce ita ba, ba mu san zuciyarta ba. Saboda haka sanar da ni, auren naku na tsawon wane lokaci ne? Abin da kake nufi, za ka aure ta ne har zuwa lokacin da za ka warke ko kuwa me kake nufi?" Cike da mamaki yake kallon Maaman, bai taɓa tunanin waɗannan maganganun daga bakinta ba. Sai yake ganin kamar ba Maamansa ba. Anya kuwa ita ɗin ce? Ya tambayi kansa. Sai dai abin da bai sani ba, tsantsar soyayyar ɗanta ce ke nema ta rufe mata idanu.

"Ke nan hakan na nufin in aure ta saboda wata manufa Maama? Idan na yi hakan na yi wa kaina adalci kuwa? Muna tare da Jawahir da Umma tun yarinta, amma ba mu taɓa sanin abin da ke zuciyarsu ba sai yanzun. Kin ga ke nan rashin sanin wace ce Daneen ba komai ba ne. Amma Maama ki faɗi duk abin da kike so na aikata, In Sha Allah ni mai biyayya ne a gare ki." Shiru Maama ta yi na tsawon mintuna ba tare da ta ce komai ba. Bai ma yi tunanin za ta kuma cewa komai ba, sai zuwa can ya ji ta soma faɗin

"Shi ke nan Tareeq, ina addu'a a kan duk abin da ya zama alkairi a gare ka ya dawwamar da shi. Abin da ba shi da alkairi ya nesanta mini kai da shi. Duk da ban ji hakan ya kwanta mini ba, amma kuma kai ya kwanta maka, na kuma san ba za ka zauna haka ba tare da neman zaɓin Allah ba. Don haka na amince ɗari bisa ɗari, Allah Ya tabbatar da abin da ya fi alkairi." Lumshe idanunsa ya yi yana jin nauyin da ke ƙirjinsa ya ɗan ragu, ya kai wajen minti ɗaya a hakan, kafin ya buɗe idanunsa a kan Maama.

"Na gode sosai Maama, Allah Ya saka da alkairi." Ba ta iya amsawa ba, sai murmushi kawai da ta yi a hankali.

... Da mamaki take kallon Hidayar da ta shigo ɗakin tana faɗin wai Maama na kiran ta. Ta tashi zaune daga kwancen da take, idanunta sun sauya kala kamar wadda ta yi kuka.

"Maama na kiran ki." Hidaya ta sake maimaitawa ganin da ta yi kamar ba ta fahimci abin da take faɗa ba. Jinjina kai ta yi tana faɗin

"Toh." Daga haka ta miƙe jiki a sanyaye ta bi bayan Hidayan.

"Ɗiyata, ki bi Hidaya, Yayanku na jiran ki za ku yi magana." Shi ne abin da Maama ta ce bayan sun je inda take. Da sauri ta ɗaga kai ta kalli Maama cike da mamaki. A kan laɓɓanta ta furta 'Yayanmu?' Har cikin zuciyarta tana jin wani banbarakwai, kuma da gaske wallahi ba ta gane abin da take nufi ba. Ita ma Hidaya da ba ta san dalilin kiran Maaman ba, ya sanya cike da mamaki ta ce

"Yah Tareeq?" Ta faɗa bayan ta buɗe manyan idanunta irin na Tareeq.

"Shi." Maama ta faɗa tana jinjina kai. Kiran sunansa da Hidaya ta yi, shi ne ya ƙara mata haske a kan maganar Maaman. Nan take duk wani ragowar annurin fuskarta ya ɗauke ɗiff, take ta ji wani irin bugun zuciya. Toh ke nan me ye dalilinsa na son ganin ta? Wace magana za su yi? Ita kwata-kwata ba ta da buƙatar ganin sa, ballantana kuma har wata magana ta haɗa su.

"Maza Hidaya ki raka ta." Shi ne abin da Maama ta faɗa da ɗan murmushi a kan fuskarta. Kamar wata saƙaguwa, haka ta soma tafiya, zuciyarta cunkushe da tunanunnuka kala-kala. Gaba ɗaya kuma fuskarta a cunkushe. Dab suke da ƙarasowa inda yake, daga nesa tana iya hangen sa daga kan kujerar da yake kai. Ba ka iya ganin komai na jikinsa sai baƙar kwantacciyar sumar kansa, da ke ta sheƙi. 'Babu yadda za a yi ma ka ƙare rayuwarka da ƙafa, mugu kawai. Allah ne Ya fara nuna maka iyakarka, sakayya ka fara gani tun kafin a je ko'ina. Ka kuma jira hukuncin da alƙali zai yanke maka daga zarar na gama abin da ya kawo ni cikin gidan nan' Abin da take raya wa a cikin zuciyarta ke nan, zuciyarta na mata wani irin zafi.

"Yah Tareeq ga ta in ji Maama, bari na koma." Hidaya ta faɗa tana murmushi. Ɗan gajeren murmushi ya maida mata, kana ya jinjina mata hannu, alamar girmamawa. Ta yi dariya kafin ta wuce daga wajen. Ci gaba da tsayawa ta yi a wajen kamar wata saƙaguwa. Ba tare da ta kalle shi ba, don ba ta so ƙoƙarin wanzar da murmushi a kan fuskarta da take ta yi ya gagara. Bayan wajen minti 2, don har ta gaji da tsayuwar, sannan ta jiyo muryarsa a nutse

"Ki zauna mana." Runtse idanunta ta yi tana ji kamar ta buɗe baki ta ce 'Ba zan zauna ba' Sai kuma ta cije, ta daure ta ɗaga ƙafafunta da ƙyar ta nemi waje ta zauna. Ajiyar zuciya Tareeq ya sauke yana tunanin ta inda zai fara. Idan ya ce zai fara ne ta gabatar da kansa kamar hakan ɓata lokaci ne, idan ya ce zai gabatar da kansa a matsayin masoyinta, nan ma tabbas ya yi ƙarya. Hakan ne ya sa bayan shuɗewar wasu mintuna sannan ya ce

"Daneen." Ya kira sunan da wani irin sauti, da duk da ya saba faɗin sunan ba ta jin ya taɓa faɗa da irin wannan sautin. Dalili ke nan da ya sa ta ɗan shiga ruɗani, kada dai ya gano ta? Kada dai ya gano wace ce ita? Kar dai ya gano dalilin zuwan ta gidan? Wannan ruɗewar da ta yi, ita ce dalilin da ya sanya ta ɗaga raunanan idanunta ta kalle shi, sai dai ko sakan 10 ba ta yi ba ta sauke tana jin yadda zuciyarta ke bugawa, so take kawai ta ji ya ambaci abin da ya sa aka kira ta. Sai da ya ɗan yi shiru, yana tunanin ta inda zai fara, don sai yake jin abin wani banbarakwai, kamar yana shirin aikata saɓo. Amma sai ya fesar da iska daga bakinsa kafin ya soma faɗin

"Na san za ki yi mamakin sakawa da na yi aka kira ki. Toh a zahirin gaskiya dai ina ganin babu amfanin kwane-kwane, duk da cewar ke yarinya ce, amma idan aka yi duba da nutsuwarki, hankalinki, hangen nesa da sauransu In Sha Allah hakan ba abin damuwa ne." Ban da bugawa babu abin da zuciyar Daneen ke yi, wannan zagaye-zagayen da yake ta yi babu abin da yake sake jefa zuciyarta sai tsoro. Kamar ya san me take tunani, sai ya ci gaba da faɗin

"A taƙaice dai, idan har kin amince na zo da ƙoƙon barar neman auren ki cikin ƙanƙanin lokaci." A razane Daneen ta ɗaga narkakkun idanunta ta zube a kansa, daidai lokacin da shi ma ya ɗaga nasa idanun ya kalle ta. Hakan ya ba wa idanunsu damar sarƙafewa cikin na juna. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunta suka soma sauya kala, duk da yadda idanunta ke cikin nasa, hakan bai sanya ta janyewa ba. Duk kuwa da matuƙar tasiri da kuma kaifin su. Sosai ƙirjinta ke wani irin zafi, zuciyarta na ci gaba da bugawa tamkar za ta faso ƙirjinta. Maimakon ya janye idanunsa sai ya ji yana so ya ci gaba da kallon ƙwayar idanun nata, saboda ya karanci wasu abubuwan daga cikinsu.

"Allah Ya kiyaye ni auren mugu, fasiƙi, wanda ba ya tsoron Allah."

A zahiri

Please Login or Register in order to submit comment