Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafin ka ga mace ma aiki ne. Shi ya sa ya ce ta zauna, idan ya gama aikin sai ya dawo. Ranar ma be dawo da wuri ba, sai da ya kai kamar jiya sannan ya dawo da abinci mai rai da lafiya. Kamar jiya ma cikin farin ciki ya kawo wa 'yar'uwar tasa abincin, ɗan kuɗin da ya samo suka yi amfani da su wajen abubuwan buƙata, ya yin da Daneen ta ɗauki wani abun ta ajje musu, wanda za ta din ga ɗauka kullum ta ajiye har su kai adadin wanda suke buƙata su nufi ƙauyensu.

Haka Daneen da Ameer suka ci gaba da kasancewa a wannan wajen. Da safe bayan sun gama abin da za su yi Ameer zai tafi wajen aiki, ita kuma ta ci gaba da zama a wajen har ya dawo. Sai dai ga mamakin Daneen, sai ta lura da tun ranar da Ameer ya samu aiki, da kuma washe gari da yake dawowa cikin matuƙar farin ciki, be sake dawowa kamar haka ba. Tun daga ranar duk lokacin da ya dawo jikinsa a matuƙar sanyaye yake. Babu wannan nishaɗin, sai tarin damuwa da kuma tunani.

"Wai Ameer me kake ɓoye mini? Me yake faruwa?" Daneen ta faɗa tana kallansa, cike da sake nazarinsa. Da sauri ya ɗaga idanunsa ya kalle ta a nutse kafin ya buɗe baki ya ce

"Babu komai Adda.. Wani abun kika gani?" Girgiza kai ta yi cikin ɗan faɗa ta ce

"Shi kenan, amma ka sani daga yau ba za ka sake zuwa wajen aikin nan kai ɗaya ba. Idan ba haka ba kuma sai dai ka dena zuwa gaba ɗaya. A haƙura da tara kuɗin kawai." Be san lokacin da ya ɗaga idanunsa ya kalle ta ba, daidai lokacin da ƙirjinsa ya wani mahaukacin bugawa. Sai ya shiga girgiza kai kamar wani ƙadangare kafin ya ce

"A'ah Adda, kin san gidan biredi babu mata, ba ze yiwu ki ce za ki din ga zuwa ba. Idan ba haka ba za su kore ni gaba ɗaya."

"Eh, gwara su kore ka, idan dai har za ka ci gaba da dawowa da damuwa." Sauke numfashi Ameer ya yi, ya lumshe idanunsa masu kama da na Daneen, ya rasa me yake damun ƙwaƙwalwarsa. Gaba ɗaya kansa a hargitse yake. Idan da zai dena zuwa da sai ya fi kowa farin ciki. Sai dai kuma yadda yake ji tamkar ana azalzalarsa da zuwa wajen ya ji kwata-kwata ba ze iya daina zuwa ba. Kai ko da ma Daneen ɗin ce ta ce ya dena zuwa, a yadda yake jin gaba ɗaya tunaninsa da nutsuwarsa ta tafi can ɗin ba ya tunanin zai iya amincewa da hakan. Sai dai kuma gefe guda yana ji shi kansa da zai iya hana kansa dena zuwa da ya dena. Wannan dalilin ne ke sanya shi jinsa tamkar wani zautacce, saboda yadda tunani da ra'ayi biyu ke ta masa yawo a cikin kwanya, kwanyarsa shi ɗaya. Kuma duka hankalinsa ya kwanta da su.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 17

Ƙura masa idanu Daneen ta yi, tana so ta ga ko za ta iya karantar abin da yake ɓoye mata, don tabbas tafarar ɗaya ta fahimci hakan. Sai dai ba ta ce masa komai ba, har zuwa lokacin da ya dawo daga mara armashin tunaninsa ya sauke idanunsa a kanta. Duk kuma sai ya so ya duburbuce saboda ganin tana masa wani kallo da ya fi kama da na tuhuma.

"Adda." Ya faɗa a sanyaye. Da sauri ta girgiza kai

"Kar ka kira sunana, kawai ka buɗe baki ka faɗa mini abin da ke faruwa, idan ba haka ba na faɗa maka ba za ka sake zuwa ba." Ta ƙare maganar da iya gaskiyarta har lokacin tana kallon sa. A sanyayen dai ya sake faɗin

"Ki yi haƙuri Addatah, shi kenan ki shirya mu din ga tafiya tare ai shi kenan koh?" Sai a lokacin ta yi murmushi kafin ta ce

"Toh damuwar ta mene ne?"

"Gajiya ce fa kawai." Ya faɗa bayan ya langaɓar da kansa.

"Ai dai mun kusa koma wa wajen Innarmu In Sha Allah." Jinjina kai Ameer ya yi yana murmushi, sai dai bai ce komai ba.

Kamar yadda ya faɗa kuwa, washe gari tare suka tafi wajen aikin shi da Daneen. Suna tafe suna hira, tana kallon duk inda suka wuce, saboda ita ba ta taɓa zuwa wajen ba. Don iyakincinta cikin kasuwa, idan suna buƙatar wani abu ta shiga ta siyo musu, daga nan ta koma inda suke ta zauna. Sun yi tafiya mai ɗan tsayi kafin Ameer ya kalle ta ya ce

"Ki zauna a nan, kin ga cikin layin nan a nan gidan biredin yake, zan je idan na gama sai na fito mu tafi." Kallon layin ta yi kamar mai son hango gidan biredin. Sai dai ba ta hango ba, amma ko babu komai nan ɗin zai fi mata kwanciyar hankali tun da tana kusa da ɗan'uwanta. Don haka ta gyara tsayuwarta ta ce

"Toh shi kenan Ameer, Allah Ya ba da sa'a, ina jiran ka fa." Ta ƙare a hankali tana kallon sa.

"Toh Adda bari na je." Ya ƙare yana ɗan murmushi, wanda ya yi nasarar lulluɓe tulin damuwar da ke danƙare a zuciyarsa. Wadda ta hana zuciya da ƙwaƙwalwarsa sukuni.

"Allah Ya tsare." Ta sake maimaitawa tana bin sa da kallo har ya bar wajen a sanyaye. Sai da ya ɓace mata da gani sannan ta dena kallon sa, gaba ɗaya wani burinta ya tafi kan yadda za su yi maza su koma wajen Innarsu. Ba za ta sake barin ɗan'uwanta ya din ga aikin wahala ba. Tana fata ta yi kuɗi a rayuwarta, Ameer ya ji daɗi. Haka zalika Innarsu ma ta ji daɗi. Gaba ɗayansu su dena aikin wahala. Zama ta ci gaba da yi a wajen, ta yi shiru tamkar mai tunani. Sai dai zuwa can idan ta gaji sai ta ɗaga kai ta kalli abin da ke faruwa a gefenta sai kuma ta maida fuskarta kan cinyarta. A nan ta yi sallah, ko bi ta kan wani abinci ba ta yi ba, ta ci gaba da jiran Ameer. Zuwa can kuwa sai ga shi ya dawo. Ya wanzar da murmushi a kan fuskarsa da ta sauya daga da, wadda take koyaushe cikin matuƙar annushuwa, zuwa wata daban. Sai dai duk iya ƙoƙarinsa yake don kar Addar tasa ta fahimci wani abin. Duk da ya san hakan ma ba mai yiwuwa ba ne. Sai dai inda Allah Ya taimake shi, yadda damuwar da ke shimfiɗe a kan fuskarsa ta ta'allaƙa ta da gajiyar aiki kamar yadda ya sanar da ita. Ko minti 2 ba su ƙara ba, suka yi gaba zuwa wajen da suke zama, suka kuma saba. A nan suka ci abinci sannan suka ci gaba da zama.

A 'yan kwanakin da suka biyo baya, sosai al'amuran Ameer ke ci gaba da sauyawa, ba shi da aiki sai tunani da kuma damuwa. Har ta kai yanzu ba ma ya iya ɓoye damuwar a gaban Daneen ɗin saboda yadda ya gajiya. Duk wani ƙwarin gwuiwarsa ya ƙare. Ji yake kamar ƙwaƙwalwarsa za ta yi bindiga idan ya cika tunani.

Dare ne, domin kuwa wajen ƙarfe 10pm ne. Daga shi har ita babu wanda ya soma ƙoƙarin neman wajen kwanciya. Ita ta yi shiru ne kawai tana kallon sa, mamaki take yadda take ganin shimfiɗaɗɗiyar damuwa a kan fuskarsa amma ya ƙi faɗa mata. Bayan hakan ba halinsa ba ne. Ta rasa gane abin da ke damun Ameer ɗin, wanda ya sauya shi cikin kwanaki kaɗan haka. Ta rasa yadda za ta yi, don haka kawai sai ta zuba masa idanu ta ji ko zai sanar da ita damuwarsa. Sai dai abin da ma ta lura da shi, tamkar hakan ƙara ba shi lasisin yin tunani ne ta yi. Don kuwa kwantar da kansa ya yi jikin wani gini da ke gefensa ya yi shiru. Daga inda take zaune take ci gaba da kallon sa, tunani barkatai cikin ƙwaƙwalwarta. Ba tun yanzu ba take hango shi yana gyara zamansa, daga baya ma sai ya tashi daga inda yake ya sauya waje. A hankali ta miƙe jin da ta yi gabanta ya ɗan faɗi, kai tsaye ta ƙarasa inda yake.

"Ameer." Ta faɗa bayan ta dafa hannunta a kan kafaɗarsa. Ɗaga jajayen idanunsa ya yi ya kalle ta hannunsa dafe da cikinsa. Ta bi hannun nasa da kallo ba tare da ta lura da idanunsa ba ta ce

"Me yake damun ka Ameer?" Ta faɗa a ɗan gigice da muryarta da ke rawa. Girgiza kai ya yi kafin ya ce

"Adda cikina ke ciwo."

"Cikinka kuma?" Ta faɗa tana riƙo hannun nasa. Jinjina kai ya yi yana sake dafe cikinsa. Cikin matuƙar ruɗewa da rashin sanin abin yi Daneen ta ce

"Me ka ci Ameer? Me ya sami cikin naka?"

"Babu abin da na ci fa." Ya faɗa har lokacin hannunsa a kan cikinsa. Da sauri ta shiga girgiza kai, daidai lokacin da idanunta suka cika taff da ƙwalla ta soma faɗin

"Me ya sa kake mini haka ne Ameer? Me na maka? Me ya sa kake ta ɓoye mini abubuwa da dama? Me ya sa ka tsiro da wasu halaye bayan da ba haka kake ba? Idan wani abu ya same ka me zan faɗa wa Inna? Ba za ka buɗe baki ka yi mini magana ba Ameer?" Ta ƙare maganar lokacin da wasu kyawawan hawaye suka sauka a kan kuncinta. Abin da ya matuƙar ba wa Daneen mamaki shi ne yadda Ameer ya fashe da kuka, kuka kuma ba irin na wasa ba, kuka sosai tamkar wanda ake duka ko ake yi wa wani mummunan abu. Maimakon ta ɗan ji sassauci, sai kukan nasa ya sake dugunzuma mata hankali, cikin rawar murya ta ce

"Na shiga uku Ameer, faɗa mini abin da ya faru? Cikin ne?" Ta tambaya a ruɗe tana sake riƙo hannun da ke riƙe da cikinsa.

"Ki yi haƙuri Addatah, ki yi haƙuri kin ji?" Shi ne abin da ya faɗa har lokacin yana kuka tamkar mace. Cikin ƙanƙanin lokaci jikinta ya ɗauki rawa, muryarta da ta shige ta yi ƙoƙarin janyo ta wajen faɗin

"Sanar da ni abin da ke faruwa Ameer, na shiga uku." Ta faɗa tana jin yadda wani bala'in tashin hankali ke ci gaba da rikito mata. Sai da ya sake girgiza kai, idanunsa da suke a lumshe ya buɗe, ya ɗora su a kan Daneen, ya sauke hannunsa da ke kan cikinsa, duk da yadda yake jin cikin nasa tamkar ba a jikinsa yake ba, amma ya yi ƙarfin halin kamo hannayenta duka biyun. Muryarsa har wani sarƙewa take yi lokacin da ya soma faɗin

"Adda ki yi haƙuri, na rasa yadda zan yi, ban san ya zan yi na raba kaina da mutanen nan ba, ban san tsautsayin da ya haɗa ni da su ba. Ban san abin da ke damun ƙwaƙwalwata ba. Ni dai kawai na ji ba na son rabuwa da su, ko da zan yi ƙoƙarin hakan ma ba zan iya ba. Adda maza ne su ba mutum ɗaya ba ba biyu ba, kullum sai sun yi amfani da ni Adda. Ba su taɓa ce mini kar na sanar wa da kowa ba, amma tamkar an rufe bakina na kasa faɗa miki, na kuma kasa hana kai kaina inda suke. Na kasa barin ki ki san inda nake zuwa Adda, ina tsoron kar ki hana ni zuwa kuma in ƙi hanuwa. Don ji nake yanzu haka in da zan wayi gari cikin ƙoshin lafiya toh zan koma wajen nasu. Kullum cikin kuka nake Adda cikin dare. Na rasa yadda zan yi, na rasa mene ne mafita. Na rasa abin da ke mini daɗi. Ina jin tamkar ƙwaƙwalwata ba ta jikina, ina ji tamkar wani noti da ke kaina ya kwance. Adda na rasa abin da ke mini daɗi. Ni da kaina fa nake kai kaina wajen su, me yake damu na? Anya kuwa ni ɗin ne? Ya zan yi ne ni kam? Na rasa abin da ke mini daɗi. Na rasa ya zan yi, don Allah Adda ki yi haƙuri ki sanar da ni abin da zan yi, ki yi haƙuri kar ki ɗauki matakin da ba zan iya jurewa ba. Zuciyata zafi take mini, ina ji ina numfashi da ƙyar. Ki yafe mini Adda." Ya ƙare maganar yana sake fashewa da wani marayan kuka. A hankali ta shiga zame hannunta daga cikin na Ameer, idanunta da suka ƙafe ƙaff, babu hawaye ko ɗigo a kan fuskarsa. Kallon sa kawai take yi tamkar wadda ta soma ganinsa a yau ɗin nan. Wani irin gudu zuciyarta take, wanda ya mugun wuce ƙa'ida. Don kuwa idan da za ka kalli ƙirjinta a lokacin, za ka iya ganin yadda zuciyarta ke bugawa a haukace. Kallon sa kawai take yi, shin da gaske abin da take ji daga bakin Ameer gaskiya ne yake faɗa mata? Ameer Ameer dai nata shi ne yake faɗin wasu maza suna amfani da shi? Idan dai har ta fahimci abin da yake nufi kenan wasu sun yi lalata da shi? 'Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un' Ta ambata a fili muryarta na wani irin karkarwa tamkar yadda jikinta ke wani mahaukacin ɓari tamkar wadda ke shirin zube wa a ƙasa. Dalili kenan da ya sanya Ameer ya ɗaga idanunsa da suka yi jajur, har sun yi wani luhu-luhu ya kalle ta, ita ma shi take kalla. Ya girgiza mata kai kafin cikin sanyi ya furta

"Ba laifina ba ne Adda." Maganar da ya yi, ita ce ta ba wa kukan da ya maƙale mata damar fitowa, ta shiga rera shi kamar za ta shiɗe. Zube wa ta yi a kan ƙafafunta ta shiga rera shi kamar ranta zai fita. Ita kam wannan wace kalar baƙar rana ce a wajenta? Wace kalar mummunar rana ce wannan? Wanne kalar bala'i ne wannan ya shigo cikin rayuwarsu ita da ɗan'uwanta? 'Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un' Ta sake maimaitawa, daidai lokacin da Ameer ya ƙaraso inda take zaune ya zube shi ma a kan ƙafafunsa. A karo na barkatai ya sake furta

"Ki yi haƙuri Addatah, ban san yadda aka yi hakan ta faru ba. Kin fi kowa sanin halin ɗan'uwanki." Maganarsa da ke fita a wani hahharɗe ta daki dodon kunnenta. Sai a lokacin sannan ta samu ƙwarin gwuiwar soma magana.

"Me ya sa za ka mana haka Ameer? Me ya sa ba ka bari mun mutu da yunwa da rashin gata ba, a kan wannan abin. Iyee Ameer? Ba gwara mu mutu ba, da ka jefa kanka cikin wannan ɗabi'ar. Ameer me ya sa ka yi mana haka? Me ya sa ka canja daga Ameer ɗina da na sani? Me ya sa haka Ameer?" Ta ƙare hannunta a kan kwalar rigarsa tana ja kamar za ta cire rigar. Tun daga ƙasan zuciyarta maganar take fitowa, muryarta cikin kuka tamkar ba za ta iya ƙarasa maganar ba. Yanzu kam kukan Ameer babu sauti, sai hawayen da ke ta tsere a kan kuncinsa.

"Ki kashe ni kawai Adda, ko na dena jin zafin da nake ji a cikin zuciyata. Ki ɗauki wani abun ki caka mini a ƙahon zuciyata Adda, na san tabbas zan ji sassaucin abin da nake ji a zuciyata. Ni kaɗai na san me nake ji, ni kaɗai na san irin raɗaɗi da zafin da nake ji Adda. Don Allah ki kashe ni ko na huta, ke ma ki huta da wannan baƙin cikin da na ja miki, ko hakan ze sa Inna kar ta ji labarin nan." Ya ƙare a raunane yana jujjuya kansa idanunsa na wani irin lumshewa kamar me shirin yin bacci.

"Haɗuwata da su kawai zan iya tunawa. Ban san abin da suke yi ba, har na tsawon kwana biyu. Sun ce mini aikin biredi ne zan din ga yi. Tun daga ranar kamar an sauya ni, shi ne suka soma amfani da ni, ban san yadda aka yi na kasa ƙin komawa gobe ba. Duk da yadda zan ji a zuciyata Allah zai kama mu, zai kuma yi mana azaba, hakan ba ya hana ni zuwa wajen su kullum. Kuma kullum cikin kuka nake Adda, amma ni.. na rasa ma me zan ce." I zuwa lokacin ta dena kukan kallon sa kawai take tana nazarin maganganunsa. Lokacin da ya kai ƙarshe, sai ta ji wasu guntayen hawaye sun sauko mata a kan fuskarta. Ta ja ɗan'uwanta ta rungume tana jin wani sabon kukan na taho mata. Ko babu komai ta san zai samu sassauci a kan abin da yake ji, ko babu komai ze yi kuka a kan kafaɗar 'yar'uwarsa ya ji tabbas fa yana da wajen da zai iya ɗora kansa ya yi kuka. Ai kuwa sai ya lumshe idanunsa yana barin hawayen na sauka a kan fuskarsa tamkar za su ƙare. Sun shafe wajen mintina goma a haka kafin ta ji yana sauke numfashi da gudun gaske. Ta yi azamar sanya hannu ta ɗago shi tana kallan sa.

"Ameer." Ta faɗa ganin yana ci gaba da lullumshe idanunsa. Fahimtar abin da take nufi ne ya sanya shi faɗin

"Cikina, da ƙirjina Adda.. Ina ji tamkar za su bar jikina. Wani abu nake ji ya tokare mini numfashina." Ya faɗa yana ci gaba da kokawa da numfashinsa. Da sauri ta gyara zamanta tana faɗi cikin rawar murya

"Kar ka damu, za ka samu sauƙi. Kwanta ka yi bacci kaa ji?" Ta faɗa tana taimaka masa, ta kwantar da kansa a kan cinyarta. Runtse idanunsa ya yi ruff, hannunsa na kan ƙirjinsa da yanzun ya fi masa ciwo a kan cikinsa. Ji yake tamkar duk wasu abubuwa da ke cikin ƙirjinsa suna dab da fitowa fili saboda wani irin yanayi da tun da Inna ta haife shi bai taɓa jinsa ba. Shiru Daneen ta yi tana kallon yadda yake sauke numfashi a wahalce, ta runtse idanunta da hawayen suka ƙeƙashe, suka ƙafe gaba ɗaya. Haƙiƙa yau ɗin wata rana ce wadda ba za ta taɓa mantawa da ita ba, yau ɗin wata rana ce da ta kafa musu mummunan tarihi cikin tarihin rayuwarsu. Abin da suke ji a nesa da su sai ga shi ya faru a kan ƙaninta, rabin jikinta. Su kuwa waɗannan mutanen su waye su? Waɗanne irin mugaye ne su, da suka rasa wanda za su lalata sai ƙaramin yaro Ameer? Daga zuwa neman aikin yi don su samar wa kansu abin da za su ci da wanda za su yi guzurin tafiya ƙauyensu? Don mugupnta da rashin tsoron Allah sun lalata mata rayuwar ƙani? Ba sau ɗaya ba ma har fiye da a ƙirga? Sun kuma yi amfani da wani abun can wajen rufe masa baki da jan hankalinsa zuwa wajen, duk da wayo da takatsantsan irin na Ameer? 'Hasbunallahu wa ni'imal wakeel' Ta faɗa a kan laɓɓanta tana runtse idanunta har lokacin bugun zuciyarta bai koma daidai ba. Lallai ko ma mene ne har abada sun gama neman aiki daga ita har ɗan'uwanta, gari na wayewa za su ɗauki hanyar tafiya ƙauyensu da ƙafafunsu, idan ya so in Allah Ya yi su isa suna a raye, idan kuma bai ƙaddara ba Allah Ya ji ƙan su. Haka wannan baƙar ranar ta ƙare suna zaune a wajen, ko wajen da take kwana ba ta koma ba, haka ta ci gaba da zama, kan Ameer na kan cinyarta har zuwa wayewar gari. Sai dai kafin gari ya gama yin haske jikin Ameer ya yi wani irin mahaukacin zafi, ban da karkarwa babu abin da yake yi, da ƙyar yake iya buɗe idanunsa saboda zafin ciwo. Zuwa lokacin Daneen ta gama ruɗewa, tun tana ƙoƙarin danne kukan da ke taho mata har ta kasa. Ta bar shi ya fito saman fuskarta da ke shimfiɗe da damuwa fall.

"Sannu Ameer." Ta sake faɗa a karo na barkatai. Da kansa ya yi amfani wajen ɗaga mata alamar ya ji ta. Sai dai jikinsa babu abin da ke sake yi sai ɗaukar uban zafi mara misaltuwa.

"Adda ina ji kamar ana daddatsa mini ƙashi, zuciyata ta yi mini nauyi." Ya faɗa a sanyaye har lokacin idanunsa a lumshe.

"Sannu Ameer, ko dai mu je asibiti ne?" Ta yi maganar kamar mai tambaya, sai dai kuma a zahiri ba jiran amsar wani take nema ba. Wannan ne dalilin da ya sanya ta miƙewa cikin mutuƙar rikicewa ta nemi taimakon wasu don a ɗaukar mata Ameer ɗin ta kai shi asibiti. Kwata-kwata hankalinta bai kawo mata abin da asibitin za su iya nema ba, ita dai kawai ta ga Ameer ɗin a asibiti a duba shi a ba shi magani ya warke shi ne burinta, inda kuma hankalinta ya tafi.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 18

Da taimakon wasu bayin Allah aka saka mata Ameer cikin napep ɗin da aka tarar mata. Ta yi saurin faɗa wa ciki tana jin gaba ɗaya jikinta na ci gaba da rawa, tamkar ma ƙafarta ba za ta ɗauki nauyin jikinta ba. Babu ɓata lokaci drivern ya ja motar suka soma tafiya ba tare da ya jira jin ta bakinta ba. Saboda ko ba ta masa bayani ba, ya san idan ba asibiti ba babu inda za su tunkara a yanzu. Don haka ya yi hanyar asibitin da ya san ya fi kusa da inda suke. Yadda numfashin Ameer ke wani irin rikicewa, yana kai masa cafka cikin ficewar hayyaci, shi ne abin da ya sake tsorata Daneen. Ta rungumo shi cikin jikinta hawaye na gangaro wa a kan kuncinta, cikin wata dashashshiyar murya ta furta

"Don Allah Ameer kar ka yi mini haka.." Ta kai ƙarshen maganar tana sake sauke idanunta a kan fuskarsa da idanunsa ke kusan a rufe, hannunsa ɗaya na sautin zuciyarsa, ya yin da numfashinsa ke ci gaba da ƙoƙarin barin gangar jikinsa. Abin da ya sanya mai napep ɗin ƙara gudu kenan, don ƙoƙarin ganin sun isa asibiti a ceci ran wannan bawan Allahn da shi kansa yake ganin tamkar abubuwan da yake na fitar rai ne. A haka suka ƙarasa cikin asibitin, Ameer na rungume jikin Daneen, gaba ɗaya ta rasa sukuni, daga zarar ta janyo wannan addu'ar sai ta ji ta kufce mata, hawaye kuwa har ta gaji da tsaida su, ban da sauka kan kuncinta babu abin da suke yi. Zuciyarta na ci gaba da bugun da take ji tamkar za ta faso ƙirjinta ne ta fito. Mai napep ɗin da kansa ya sauka ya ɗaukar mata Ameer da har lokacin ba ya cikin hayyacinsa. Wani irin numfashi yake yi a wahalce, idan ka gan shi ma ba za ka ɗauka yana da rai ba, saboda yadda gaba ɗaya jikinsa ya saki. Sai dai idan ka kalli fuskarsa, ko kuma ka ƙura wa ƙirjinsa ido, shi ne za ka ga yadda yake ɗagawa a wani irin hankali. Bayansa Daneen ta bi da sauri, kamar yadda shi ma yake saurin. Tana tafe tana goge fuskarta da hannayenta, ba tare da ta san abin da take furtawa ba take ci gaba da faɗin abin da ya zo mata a rai.

"Ameer kar ka yi mini haka.. Ka tashi ka warke mu koma wajen Innarmu don girman Allah." Ire-iren maganganun nan take ta furtawa tana bin bayan mai napep ɗin. Har zuwa lokacin da suka isa emergency. Cikin gaggawa aka karɓi Ameer saboda yadda jikinsa ya yi mugun tsamari. Daneen ta zube a kan gwuiwoyinta tana sake fashewa da wani sabon kukan. Ta jima a wajen, ba tare da ta san abin da ya ci gaba da faruwa ba. Ita dai burinta ɗaya ta ji halin da ɗan'uwanta yake ciki.

"Ki yi haƙuri, In Sha Allah zai samu sauƙi. Addu'a za ki yi masa ba kuka ba." Ta jiyo muryar mai napep ɗin nan yana faɗa mata. A hankali ta ɗan ɗaga jajayen idanunta ta kalle shi, da ƙyar cikin dashashshiyar murya ta ce

"Na gode sosai, Allah Ya saka maka da alkhairi." Ta faɗa tana lumshe idanunta.

"Babu komai." Ya faɗa, kafin ya gyara tsayuwarsa ya ce

"Bari na wuce, Allah Ya ƙara sauƙi. In Allah Ya yarda zuwa an jima zan shigo."

"Toh." Ta faɗa a sanyaye. Ko minti 5 bai yi da tafiya ba, aka nemi ganin waɗanda suka kawo Ameer. Da wani irin sauri Daneen ta miƙe ta shiga office ɗin likitan. Gwaje-gwaje aka ba su rubuce a takarda. Ita dai Daneen ba

Please Login or Register in order to submit comment