Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah buwaya gagara misali, wanda ya ba ta Alhaji Abubakar. Mutumin da tun kafin a yi nisa duk wasu kyawawan halayensa suka bayyana, mutumin da ya nuna ƙaunar 'ya'yanta, ya nuna zai kula da su duk da kasancewar ba shi ya haife su ba. Ita kuwa me za ta yi idan ba ta cigaba da gode wa Allah ba?.

Tana sanye cikin atamfa riga da zani, da mayafi sabbi gall. Ta yi kyau matuƙa, idan dai har ba sani ka yi ba, ba za ka ce ita ce ta ajje Daneen da Ameer ba. Sabuwar wayarta da Alhaji Abubakar ya ba ta ita ce ta shiga ƙara. Ameer da ya fi kusa da wayar ya ɗauka ya miƙa mata yana faɗin

"Inna ana kiran ki." Miƙa hannu ta yi tana faɗin

"Miƙo mini." Babu musu Ameer ya miƙa mata, ta karɓa idanunta a kan fuskar wayar don ganin mai kiran.

"Inna in haɗa har da wannan?" Daneen da ke haɗa kayanta da na Ameer ta faɗa tana kallan Innar. Ɗaga kai Innar ta yi ta kalli kayan kafin ta ce

"Eh ki haɗa da shi, haɗa da wancan ma." Ta ƙarasa maganar tana mai nuni da wasu kaya cikin kayan da Daneen ɗin ke duba wa. Sai ta ɗauka kuwa ta haɗa cikin waɗanda take haɗa wa. Ya yin da ita kuma Inna-wuro ta ɗaga kiran da ake mata.

"Amarya ba kya laifi." Daga can ɓangaren Alhaji Abubakar ya faɗa yana murmushi. Duk sai ta ji kunya ta kama ta. Ta yi murmushi tana gaida shi. Amsa wa ya yi, kafin ya ɗora da

"Na san dai kina cikin gida yanzu haka. Toh idan babu damuwa ki leƙo akwai wata muhimmiyar magana da za mu yi." Haka nan kawai ta ji faɗuwar gaba ta ziyarce ta, sai dai ta basar kafin ta ce

"Toh ga ni nan." Daga haka ta katse wayar. Ta ɗan yi shiru na wasu sakanni kana ta maida duban ta kan Ameer ta ce

"Ameer ka tashi ka taya Addarka shirya kayan nan, ka bar ta tun ɗazun tana yi ita ɗaya." Miƙe wa ya yi yana faɗin

"Toh Inna."

"Kafin na dawo kun gama uhmm?"

"Toh Inna sai kin dawo." Daneen ta faɗa har lokacin idanunta na kan kayan da take shirya wa.

Kamar yadda ya faɗa ɗin kuwa, yana ƙofar gidan, ganin ta da ya yi ya sanya shi faɗaɗa murmushin kan fuskarsa. Ya ƙaraso yana sake zolayarta. Ita dai sai babbasarwa take yi dan har ga Allah kunya yake ba ta.

"Amm.." ya faɗa bayan ya yi gyaran murya. Nan ma sai da ta ji gabanta ya tsinke ya faɗi. Ta yi saurin runtse idanunta tana ambatar sunan Allah.

"Wato Fatima tafiya ce ta taso mini bagatatan, yau yau ɗin nan zuwa Abuja ya taso mini. Yanzu ma haka ni ake jira mu wuce. Ban san da wane ido zan kalle ki in sanar da ke yau ɗin za mu wuce Abuja ne tare da ke kawai ba. Idan ya so da mun tashi dawo wa, kai tsaye nan za mu dawo mu ɗauki 'ya'yanmu mu wuce da su gida." Cikin lokaci ƙanƙani zuciyarta ta cigaba da bugawa fiye da zato. Jin da ya yi ba ta ce komai ba ne ya sanya shi faɗin

"Kar ki damu, kwata-kwata ba za mu wuce sati ɗaya a can ɗin ba. Na kuma yi miki alƙawarin daga can ɗin nan za mu wuto babu wani tsaye-tsaye." Ya ƙare a tausashe duk dan ta fahimce shi. Duk da yadda ya yi maganar tabbas ta ji ta yadda da abin da yake faɗa, sai dai ba ta san dalilin da ya sa zuciyarta ta ƙi na'am da hakan ba. Sam hankalinta ya ƙi kwanciya, ji take kamar ba za ta iya barin 'ya'yanta na tsawon sati guda cikin gidan nan bayan ba ta cikinsa ba. Sam ta kasa gane dalilin hakan. Ga kuma faɗuwar gaban da ta ƙi barin ta har zuwa yanzun.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 09

Jin da ya yi ta yi shiru na fiye da tsawon minti ɗaya, ya sanya shi gyara tsayuwarsa ya ce a tausashe

"Ki yi haƙuri, kar ki ce ban yi miki adalci ba. Ban san wannan tafiyar za ta taso ba, ina mai sake ba ki haƙuri." Kalmar haƙurin da yake ta maimaitawa tabbas ta yi matuƙar tasiri a zuciyarta, sai dai duk da haka, ba ta dena jin bugun zuciyar ba. Ta yi ƙarfin halin buɗe baki da ƙyar ta ce

"Babu komai, Allah Ya sa haka ne mafi alkhairi." Sai a lokacin ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce

"Ameen, na gode."

Shiru ne ya wanzu a wajen na tsawon mintuna, zuwa can Alhaji Abubakar ya ce

"Bari na jira ki sai ki shirya koh? Kafin nan mun yi magana da Baffa." Da kai ta amsa masa maganar, ba ta sake cewa komai ba ta faɗa cikin gidan tana tunanin ta inda za ta fara sanar wa da 'ya'yanta tafiyar sati da za ta yi ta bar su cikin gidan. Kamar yadda ta umarci Ameer kuwa, yanzu haka tare da Daneen ta same su suna shirya kayansu cikin jaka. Ya yin da ragowar da ba za su ɗauka ba suna ninkewa suna mayar da su wajen kayansu. Ƙarasawa cikin ɗakin ta yi jikinta a matuƙar sanyaye ta nemi waje ta zauna tana cigaba da kallan su.

"Inna mun gana haɗawa fa." Ameer ya faɗa yana murmushi. Ji yake tamkar ya yi ta tsalle saboda farin ciki, don zai iya cewa kaff cikin su ya fi su farin ciki da barin ƙauyen nan da za su yi. Murmushin yaƙe Inna-wuro ta yi kafin ta ce

"Ku zo ku zauna ku ji." Kusan a tare Ameer da Daneen suka ɗaga ido suka kalli Innar tasu jin yadda maganarta ta sauya cikin ƙanƙanin lokaci. Wannan ɗin ba sabon abu ba ne a wajen su, fahimtar halin da ɗaya daga cikin su ke ciki ko da ta magana ne kuwa, ba tare da ya sanar da su ba. Ajiye Hijab ɗin da ke hannunta Daneen ta yi, ta ƙarasa gaban Innar tasu da sauri ta zauna, ya yin da Ameer ma ya zauna a gefen ta, gaba ɗayan su jiki a sanyaye.

"Ku buɗe kunne da kyau ku saurare ni, ba don na so ba sai don haka Allah Ya tsara, zan bar ku cikin gidan nan na tsawon sati guda. Kai tsaye nan za mu dawo mu ɗauke ku mu wuce da ku inda za mu zauna. Kar ku damu, kar ku ɗaga hankalinku." Ta ƙare maganar a nutse, duk da ita ma ba ta da nutsuwar zuciya, sai don kawai ta ba wa 'ya'yan nata ƙwarin gwuiwa.

"Inna.." Shi ne abin da Ameer ya yi ƙarfin halin faɗi yana cigaba da kallan Innar. Wata ƙwalla da ta ji ta taho mata ita ce ta sanya ta saurin saukar da kanta ƙasa, wajen sakanni 30 kafin ta ɗago tana kallan su su duka. Ta kamo hannayensu ta sanya cikin nata.

"Ba mu taɓa rabuwa ba tun da muke, sai ga shi yau ɗin za mu rabu na tsahon kwana bakwai. Ina so na yi amfani da wannan damar wajen neman alfarmar yin haƙuri da zama da Dada cikin gidan nan bayan ba na cikinsa. Akwai kuɗi a cikin jakata, duk abin da kuke buƙata ku yi amfani da shi. Daneen ga Ameer nan, ki kula mini da shi har na dawo. Ameer ga Daneen nan ka kula mini da ita har na dawo. Allah Ya yi muku albarka, Ya albarkaci rayuwarku, Ya raya mini ku." I zuwa lokacin gaba ɗaya jikinsu ya yi sanyin da suka kasa amsa addu'ar Innar. Kowanne da abin da yake saƙa wa a cikin ransa.

"Kar ku mini kuka." Inna ta faɗa tana girgiza kai lokaci ɗaya tana kallan su duk da ita ma nata idanun cike suke da ƙwalla.

"Toh maza ki fito Hajjaju ta ɗaka, mijinki na jiran ki. Ko kuwa ƙaramar yarinya ce ke da sai an zo an rarrashe ki kafin ki fito." Ta jiyo muryar Dada na faɗin hakan. Hannu ta kai ta goge fuskarta da zuwa lokacin hawaye sun fara sauka, ta yi saurin ɗauke su don kar ta sake karyar wa da 'ya'yanta zuciya.

"Toh gani nan." Ta ɗaga murya wajen faɗar hakan, don Dadar ta ji. A hankali ta miƙe har lokacin hannunta na cikin na 'ya'yanta da suka kasa furta komai.

"Ku yi haƙuri kar da ku karya mini zuciya. Ba na tafi kenan ba, nan da sati ɗaya zan dawo in ɗauke ku da yardar Allah."

"Inna don Allah kar ki tafi." Daneen ta faɗa da muryarta da ke rawa, lokaci ɗaya tana rungume Innar. Kukan da Inna ta ji ta fashe da shi shi ne ya sanya ta runtse idanunta, ta saka hannu ta ja Ameer jikinta, ta haɗa su ta rungume waje ɗaya. Sun kai wajen minti biyu a haka kafin suka saki juna. Inna-wuro ta saka hannu ta ɗauki jakar kayanta. Bin bayanta suka yi har zuwa tsakar gidan. Kafin su kai ga fita daga cikin gidan wata da take kusa da Dada ta ce

"Wai dama ba a nan za ta zauna ba."

"A'ah nan cikin Kano ne fa za ta zauna." In ji Dada tana gyara zama lokacin da Inna-wuro ta nemi waje ta zauna. Ba wata addu'a daga Dadar har Baffan suka yi mata ba, haka dai ta ja ƙafafunta suka fice daga gidan. A sanyaye su Daneen suka gaishe da Alhaji Abubakar, ya amsa cikin sakin fuska kafin ya karɓi jakar hannun Inna-wuro ya saka cikin mota.

"A kula, Allah Ya tsare mini ku, sai na dawo." Inna ta faɗa tana kallan su.

"Allah Ya tsare Inna." Suka haɗa baki wajen faɗar hakan. Ta lumshe idanunta tana juya wa a hankali ta soma tafiya zuwa wajen motar. Dab da za ta ƙarasa, ta sake juya wa ta kalli 'ya'yan nata. Sai ta juya da sauri ta shige cikin motar, saboda yadda ta ji a yanzun ba za ta iya jurewa ba, zuciyarta ta gama karyewa. Ƙarasawa Alhaji Abubakar ya yi ya shiga motar, bayan wasu sakanni ya tashi motar. Ƙasa da kanta Inna-wuro ta yi don tabbas idan ta cigaba da kallan 'ya'yanta za ta iya bijire wa umarnin mijinta ta ƙi binsa ta cigaba da zama da su. Don haka har ya soma tafiya ba ta ɗaga kanta ba. Daneen da Ameer, suka cigaba da bin motar da kallo, har zuwa lokacin da ta ɓace wa ganin su. Hannun Ameer Daneen ta kama ta riƙe sosai tana runtse idanunta. Wani irin bugu zuciyarta take yi. A hankali kuma sai ta soma takawa zuwa cikin gidan, ya yin da Ameer ya rufa mata baya.

Bin su da kallo Dada ta yi lokacin da ta ga shigowar su cikin gidan. Ta taɓe baki tana jinjina kanta. Ita dama burinta bai wuce a bar mata 'ya'yan Inna-wuro a wajenta ba, ko babu komai ta san za su dinga zuwa a kai a kai ana ajiye mata kuɗi da sauran su. Amma idan suka tafi da 'ya'yan suka manta da ita da wa ta ɓare kenan? Bar mata su da aka yi yana nufin samun wata mafitar kafin su dawo, wadda za ta hana su tafiya da su duk da sun yi niyya.

Kai tsaye ɗakinsu suka nufa suka yi shiru kowa da abin da yake saƙa wa. Ranar haka suka wuni kamar masu zaman makoki, babu wanda ke cewa da ɗan'uwansa ko uffan ne.

Washegari jiki a sanyaye duk suka farka, sai suke jin su wasu daban, ba su taɓa farkawa ba su ga Innarsu ba sai a yau ɗin. Ba su taɓa rabuwa da Innarsu ba sai a wannan karon. Suna ta farin ciki abin farin ciki ya same su, ashe ba su sani ba kafin samuwar farin cikin sai sun soma rayuwar kaɗaici. Da yake ranar babu makaranta ya sanya suna gida, tun safe bayan sun fito daga ɗaki ba su koma ba. Shi Ameer yana can aiken da Dada ke ta masa, da kuma wasu ayyukan. Ya yin da Daneen ke yi wa Dada girki da sauran ayyukan cikin gida.


.. "Me kake yi haka ne Ameer?" Daneen ta faɗa tana kallan Ameer da ke cusa kayan sakawarsa cikin jakar islamiyya. Sai da ya ƙarasa cusa wadda ya ɗakko sannan ya ɗaga ido ya kalle ta ya ce

"Inna zan bi." Da mamaki matuƙa Daneen ke kallansa idanunta a waje. Cike da mamakin dai ta ce

"Inna kuma Ameer? Ka san inda ta je ne?" Jinjina kai ya yi kana ya ce

"Ehh, jiya na ji Dada tana faɗa wa ƙawarta wai sunan garin Kano. Ko ban san gidan ba, na san muna zuwa muka tambayi Mai gari gidan Alhaji Abubakar ya sani. Tunda kin ga mu ma a garin nan gidan waye Mai gari bai sani ba?"

"Ni yi mini shiru dallah.. Tashi ka tafi toh." Daneen ta faɗa tana shirin miƙe wa. Maida ta ya yi ta zauna ta hanyar riƙo hannunta. Ya shiga girgiza kai yana faɗin

"Kar ki mini haka Addata. Idan har ke ba ki amince mini ba waye zai amince mini? Don Allah ki duba abin da na faɗa ki bari mu tafi. Ni ba zan iya cigaba da zama da Dada ba wallahi. Ko ba ki amince na bar garin nan ba, toh zan bar cikin gidan nan in tafi ko ma ina ne."

"Wai Ameer ba ka da hankali?" Daneen ta faɗa tana kallan sa a tsorace.

"Toh ki yarda da abin da na faɗa."

"Ba zan yarda ba." Ta faɗa tana jefa masa harara.

"Don Allah Addaneen tawa ni kaɗai. Don Allah.." Ya ƙare a marairaice. Sai a lokacin sannan ta sake juyawa ta kalle shi sosai ta ce a hankali kamar me raɗa.

"Ameer wai da gaske kake?" Jinjina kai ya shiga yi lokaci ɗaya yana furta

"Wallahi da gaske Adda. Ji nake kamar ana azalzalata da in bar gidan nan, ki taimaka ki amince mu bi Inna garin da ta je." Shiru Daneen ta yi na tsawon wasu mintuna. Rashin yawan tazarar shekarun da ke tsakaninta da Ameer ya sanya wayonsu kusan ɗaya ne. Wani lokacin ma har ya fita wayo. Don idan ya yi wani abun sai ka ɗauka shi ne babba, sai kuma wani lokacin ko ba a faɗa maka ba za ka fahimci Daneen ce babba.

"Amma idan Inna ta yi faɗa fa? Tun da ka ga ta ce nan da sati ɗaya za ta zo ta ɗauke mu."

"Ba za ta yi ba Adda, ba za ta yi ba. Shi ma kuma sabon Abban ai yana da mutunci. Sai mu ce zuwa muka yi mu gaishe su." Shiru Daneen ta yi na tsawon wasu mintuna kafin ta shiga jinjina kai ta ce

"Toh." Ta ƙare tana ajje numfashi.

"Yawwah Addata." Ameer ya faɗa yana murmushi. Cikin zuciyarsa yana jin wani shahararren farin ciki na kama shi. Da gaske har cikin ransa ji yake tamkar ana azalzalarsa da barin gidan. Kuma da gaske yadda ya faɗa ɗin tabbas da Addar tasa ba ta amince da bin Innarsu ba, yau ba zai kwana cikin gida ɗaya da Dada ba. Shi da kansa ya tashi ya ɗauki jakar islamiyyar Daneen ya shiga saka mata kayan sakawarta ciki. Ya samu dama da yawa kuwa sun shiga saboda yadda yake cusa su don ma kar a gane meye a ciki. Sai da suka gama tsaff, kafin ya miƙe ya ce

"Adda riƙe jakarki mu tafi." Babu musu ta karɓa ta rataya ta cikin hijabin makarantar islamiyya da ta saka. Shi ma ya rataya tasa jakar saman uniform ɗin islamiyyar. Ba tare da tunanin komai ba suka fito daga cikin ɗakin. Dada na zaune tana jin Radio a kan tabarma, ya yin da Baffa ke mata fifita yana daga gefen ta.

"Dada, Baffa mun tafi." Daneen ta faɗa, don tana da tabbacin idan ba ta faɗa ba Ameer ba zai faɗa ba. Ɗaga idanunta Dada ta yi ta kalle su, Radion da take ji ya sa ba ta iya tantance iya Daneen ce kaɗai ta mata magana ba. Tsaki ta ja kafin ta soma faɗin

"Ni fa makarantar ma na gaji da ganin ku kuna zuwan ta wallahi. Haba." Ta ƙare yanzu kuma tana sakin ƙwafa.

"Kin ga ƙyale su su tafi, kar shirin nan ya wuce ki. Idan kin gama ji in ya so duk hukuncin da za ki yanke sai ki yanke kafin su dawo." Baffa da ke cigaba da firfitarsa ya faɗa yana kallan ta. Shiru ta yi na tsawon wasu sakanni kafin cikin na'am da zancen nasa ta ce

"Haka ne kuma.. Ku tashi ku tafi." Tun kafin ta ida faɗa har Ameer ya miƙe, kafin ka ce mene wannan ya fice daga cikin gidan. Ta ja ƙwafa tana cije gefen leɓenta, a ranta tana saƙa yadda za ta yi maganin yaron cikin ƙanƙanin lokaci.

"Kin gani ko Adda? Kin ga abin da nake faɗa miki koh? Kin ji fa wai makarantar ma hana mu zuwa za ta yi, toh me ya sa?" Ya ƙare tambayar yana kallan Daneen da ta sauke ajiyar zuciya saboda ganin da ta yi Dada ba ta gane kaya ne a cikin jakunkunansu ba. Jinjina kai ta yi ba tare da ta ce komai ba. Cigaba da tafiya suka yi, sai da suka yi tafiya mai nisa kafin suka isa wani titi. A nan suka samu motar da za ta fitar da su inda za su samu motar da za ta kai su Kano. Da kuɗin da Inna ta ba su suka yi amfani wajen biyan mai motar kuɗinsa lokacin da ya sauke su. Sai suka sake tarar wata motar wadda ita ma dai ba Kanon direct za ta wuce ba. Don haka bayan ta sauke su a nan suka yi tambaya suka samu motar da za ta wuce Kano. Cikin matuƙar farin ciki suka hau motar. Motar da ba ta kai ga cika ba, don haka aka tsaya ana jiran wasu passengers ɗin kafin motar ta tashi.

"Adda yunwa nake ji." Ameer ya faɗa yana ɓata rai. Hannu ta saka ta karɓi jakar hannunsa, ta ce tana kallan waje

"Ka ga wata mai siyar da awara can, je ka siya ka ci." Ta faɗa tana zaro kuɗi a jakar Inna ta miƙa masa. Hannu ya saka ya karɓa yana sauka daga motar, kai tsaye wajen mai awarar ya wuce. Ta bi shi da kallo tana lumshe idanunta, daidai lokacin da bugun da numfashinta ke yi ya cigaba da fita a gurguje kamar wadda ta yi tsere. Bayan wasu mintuna sai ga shi ya dawo. Yana dawowa kuma, motar na gama cika. Don haka bai daɗe da zama ba, motar ta tashi aka soma tafiya.


.. "Maza maza mun zo tasha. Ina na Kano su sauko." Abin da kwandastan motar ke ta faɗa kenan lokacin da yake a waje, hannunsa ɗore a kan motar yana ɗan bubbugawa. Kallan juna Daneen da Ameer suka yi, kafin a sukwane suka sakko daga cikin motar. Dama tuni sun ba wa kwandastan kuɗinsa, don haka sai suka soma taka wa suna rarraba idanunsu a inda suke. Daneen ta haɗiye wani busshashshen yawu da ya haɗu cikin bakinta da ƙyar zuwa maƙogwaronta. Ta kalli dogon titin da suke kai, wanda kwata-kwata bai yi mata kama da titin ƙauyen su ba. Ita kwata-kwata ma ba ta ganin ƙarshensa, kai ba ma ƙarshensa ba, wajaje take gani duk inda ta juya, maimakon ta gan su a haɗe kamar yadda nasu gidajen suke. Sai dai kwata-kwata ma ita ba ta hangi wani gida ba, kenan ina ne gidan mai gari? Shi dai Ameer ban da sake rungume jakarsa babu abin da yake yi, lokaci ɗaya kuma yana bin garin da duhu ke sake mamaye shi da kallo. A karo na barkatai suka sake kallan juna, idanun kowannensu ya yi tsilli-tsilli, ya raina fata, gaba ɗayansu kuma da abin da suke saƙa wa a cikin ransu. Sai dai abin da ya fi yawo a zuciyar kowannen su shi ne 'Shin ina ne nan ɗin suka kawo kansu?'

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 10

Idanunta da suka yi rau-rau ta ɗaga ta kalli Ameer ta ce jikinta a matuƙar sanyaye

"Na shiga uku Ameer, ina ne nan?" Cikin rashin sanin abin yi Ameer ya girgiza kai kafin ya ce

"Ni ma ban sani ba Adda." Ya faɗa yana sake maida kansa inda suke. Duk da yadda take jin tsoro na sake shigar ta, hakan bai hana ta kallan wani mutum da ke gefen su ba. Cikin sanyin murya ta gaida shi, ya amsa yana kallan yanayin shigarta.

"Don Allah gidan Mai gari muke nema." Ta yi ƙundunbalar faɗin hakan, cike da fatan su samu abin da suke so.

"Toh ikon Allah! Mai gari ko Mai Unguwa?" Ya tambaya yana kallan ta. Shiru Daneen ta yi tana tunanin abin da ya kamata ta ce, sai dai kafin ta ida tunanin ta tsinto muryar Ameer ya ce

"Eh shi." Ya yi maganar yana jinjina kai kamar ƙadangare, lokaci ɗaya kuma yana sake rungume jakarsa a hammata.

"Toh da yake dai babu nisa daga nan, ku biyo ni na nuna muku, idan ya so sai na wuce inda zan je." Cikin matuƙar farin ciki suka shiga yi masa godiya, a ransu duka ji suke tamkar su taka rawa. Bin bayan nasa kuwa suka yi kamar yadda ya faɗa, suka soma tafiya. Duk inda suka gifta sai sun bi wajen da kallo.

"Ai dama na faɗa miki Adda, yanzu ba ga shi ba har mun samu gidan." Ameer ya faɗa farin cikin da yake ji na bayyana a kan fuskarsa da kuma muryarsa. Ita ma murmushin ta yi kana ta ce

"Ai kuwa dai. Allah har na ƙagu na yi ido biyu da Innarmu." Ta yi maganar daidai lokacin da mutumin ya juyo ya kalle su, sai da ya soma nuna musu wani gida da ke ɗan nesa kaɗan da inda suke kafin ya ce

"Kun ga wancan gidan, shi ne gidan Mai Unguwar nan Unguwar." Ba tare da damuwa da bayanin da ya musu ba suka sake masa godiya cikin matuƙar farin ciki. Daga haka ya yi musu sallama ya ƙara gaba, ya yin da suka nufi inda ya nuna musu.

Lokacin da suka isa, sun samu wani yaro tsaye a ƙofar gidan. Suka sanar da shi abin da ke tafe da su na son ganin Mai gari.

"Ai kuwa dai Mai Unguwa ba ya nan, ya yi tafiya an yi masa mutuwa. Amma idan wani abun ne ku faɗa sai na taimaka muku." Kallan juna Daneen da Ameer suka yi, kafin suka maida duban su kan yaron.

"Dama zuwa muka yi mu tambayi gidan wani Alhaji Abubakar, wanda ya yi aure kwanan nan, ya auri wata Fatima." Tsayawa yaron ya yi yana kallan su irin kallan rainin hankalin nan. Sai dai abin da ma ba su sani ba, cikin ransa tunani yake anya kansu ɗaya? Ya duk girman unguwar nan amma su zo suna tambayar gidan Alhaji Abubakar wai wanda ya auri Fatima. Anya kuwa?

"Ba a nan garin kuke ba ne?" Girgiza kai suka yi. A wannan karon ma dai Ameer ne ya ce

"Daga ƙauyenmu muke. Muna neman su ne shi ya sa muka taho kai tsaye gidan Mai gari. Tun da yadda muka sani duk wani gida da ke a ƙarƙashin ƙauyen Mai gari ya san masu gidan,lll shi ya sa muka zo." Sai a lokacin yaron ya kaɗa kai, shi dama ya san a rina, ashe daga ƙauye suke.

"Kun ga, nan fa ba ƙauye ba ne. Ba a ƙauyenku kuke ba. Kun ga ku rufa wa kanku asiri ku koma inda kuka fito, tun da ba ku san inda waɗanda kuka fito nema suke ba. Wannan garin yana da faɗi, ba kamar yadda ƙauyenku yake ba. Mu nan ba iya garin nan ba, duk wata unguwa da ke cikin garin nan tana da Mai Unguwa, kuma Mai Unguwa ba shi da hurumin sanin mutanen da ke cikin unguwarsa. Ka ga kenan ba za ku taɓa samun abin da kuke nema ba." Tun da ya soma maganar suke kallan sa, har ya ƙare. Jiki a matuƙar sanyaye suka yi masa godiya. Bayan ya yi musu sallama ya wuce cikin gida. Ba su taɓa tunanin haka abin yake ba. Sun ɗauka tamkar yadda ƙauyensu yake nan ɗin ma haka yake. Shi ne dalilin da ya sa suka taho ba tare da wani tunani ba.

***
"Sister ban san

Please Login or Register in order to submit comment