Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka dinga shigowa wayarsa
Tsaki yayi ya dau wayar yafara duba messages din
"Haba fitilar rayuwata meyasa zakamin rowa, just want hear your sweet voice
I really care for u, bazan iya bacci ba in banji muryarka ba love u baby
From your lovely bae"

Ire² wannan messages dinne ake ta turomasa tsaki yayi sannan ya danyi shiru yana zancen zuci anya kuwa Ilham ce take turo masa wannan messages din, wacece ta kira dazu sukayi waya da Jawwad?
Ya tambayi kansa still wayar ce tafara ringing da Sauri Jalal ya yinkurin dagawa domin yiwa ko wacece rashin mutunci seyaga Jawwad ne yake kiransa dan zaro ido yayi sannan ya daga wayar
"Jalal kana ina?"
Jawwad ya tambayeshi
"Na dan fitane"
"Hmmm daga samun saukinka harka fita ko ka tafi gurin Wanda sukafi kowa mutumci a idonka shikenan seda safe"
Jawwad ya katse kiran mikewa Jalal yayi yadauki mukullan motarsa ze fice
Jeje ya kalleshi
"Ya dai ba dai tafiya zakayi ba?"
"Tafiya zanyi mana dama bana jin dadi Jawwad yaje bana nan naji ransa a bace dole in tafi inje ba shi hakuri"
Wani bakin cikine ya tokarewa jeje ji yayi kamar ya rufe Jalal da duka,
Yadda Jalal baya son bacin ran Jawwad da iyayensa yakewa haka da ya dace
Anya ba asiri Jawwad yayiwa Jalal ba jeje yayi maganar a zuciyarsa
Shikam Jalal besan yanayi ba dan tuni ya bar gurin

Ilham ce ke ta safa da marwa a dakinta tare da fatan Jalal ya sha tea din nan da se tafi kowa farin ciki gajiya tayi da tunane² dan haka ta yanke shawarar ta dan fita taje gurin Nana
A daki ta tarar da Nana suna waya da Jalila dan haka ta nemi guri ta zauna daga baya data fuskanci Nana da Jalila take waya seta wani hade rai
"Naji kaman kinyi bakuwa se anjima"
Jalila tayi maganar
"Ba wata bakuwa ceba Ilham ce fa"
"Hh kice Juliet ce, to kice mata a dai dinga sassauta masa adena wahalar dashi"
Dariya Nana tayi tare da fadin
"To Ilham kinji dai sakon Jalila"
Tsaki Ilham tayi dan yanzu ta kara tsanar Jalila mussaman akan abunda yafaru shekaran jiya Jalal ya dinga zaginta

"Kinga ni na tafi nazo gurinki kina rainamin hankali"
Ilham tai maganar tana mikewa
Nana tayi saurin rikota tare da kashe wayar
"Ke bakisan wasa ba indai Jalila ce wataran se ta saki kuka"
Da Sauri Ilham ta kalleta "kamar ya?"
"Eh mana ai ita yayinda taga ba kyason abu to lokacin zata dinga yimiki dan tabaki haushi"
"Wallahi nafi karfin kamata wata Jalila ta Sani kuka"
"A'a dai yadda kike da saurin fushin nan Lokacin daza tasaki kukan ma baki Sani ba
Amma abunda yake burgeni da ita shine akwai kwanya musabaka sukaje Abuja fa tazo ta biyu"
"Ai nasani"
Ilham tabata amsa
"Ya akayi kika Sani?"
"Ke ni mu bar wannan zancen Nana damuwata kullum karuwa take akan Yaya Jalal amma gani nake ba wadda tsana kamar ni"
Ta karasa maganar cike da damuwa
Nana ta dafa ta
"Ilham ba tsanarki yai ba kinsan shi kawai miskiline baya son shiga sabgar mata mazan ma kinga ba kowa yake kulawa ba Sam baya son mutane watakila fa a ransa yana sonki, inaga Ku da haka naku labarin soyayyar ze fara"
Nana tai maganar cike da kwarin gwiwa
"Dagaske Nana kumafa se hakan yakasance ko?"
"Sosai makuwa wannan ai ba abun mamaki bane"
"Shiyasa kike burgeni Nana bakiji yadda hankalina ya dan kwanta da maganganun nan nakiba"
"Ai irin miskilan mutanen nan abune mawuyaci kagane inda sukasa gaba da wuri karkiyi mamaki sonki yana nan fal a zuciyarsa"
"Allah yasa haka Nana"
"Ai hakanne ma insha Allah Mrs. Jalal to be"
Haka Nana ta dinga ziga Ilham tana kwantar mata da hankali Akan abunda bata da tabbas akai

Jalila tana daki tana gugar uniform zasu koma makarantar boko Ummi kuma tayi bakuwa
Jalila taji kaman ana harbe² a waje da sauri ta fito tsakar Gida
"Ummi bakiji karan bindiga ba"
Bakuwar Ummi tace
"Wani captain ne na sojoji yake tarewa a anguwar nan bakiga wani kerarren Gida ba da aka gama kwanan nan ai nasane wallahi gidan ya keru kaman a kasar waje "
"To shine kuma za a zo a cikamana kunne da karar bindiga saboda shirme, ni gidan ma nakeso in gani inga iya keruwarsa"
"Allah yabaki sa'a kije Neman magana duk yadda zasuyi dake se dai suyi dan ba abunda zan iya indai sojojine zaki yabawa aya zakinta"
Ummi tai maganar cikin bacin rai shiru Jalila tayi ta koma daki

Jawwad ne yakema Jalal fada akan fitar da yayi daga samun saukinsa
Yayinda Jalal ke bashi hakuri
"Ai gani dai na dawo ban zauna a can ba hankalinka ya kwanta"
"Bawani hankalina ya kwanta kabata min raine ka dinga sassautawa kanka wannan abubuwan dakake durawa cikinka"
Hade rai Jalal yayi "naji kuma ina nace kayi hakuri "
"Haka ka iya ai saura ka kara fita"
Jawwad yayi maganar da alamun gargadi
Dariya Jalal yayi
"Sorry yayana bazan kuma fitaba a yau insha Allah"
Murmushi Jawwad yayi sannan ya fita
Bayan fitar Jawwad
Jalal ya saka wayarsa a caji ya mike yatafi cikin Gida part din daddy yaje suka sha hira
Cikin hikima daddyn yake masa nasiha
"Daddy nima bana jin dadin abunda nake amma kacigaba dayimin addu'a wataran zakaga kaman banyiba"
"Nima ina fatan hakan yaron kirki"
Se kusan shabiyundare Jalal ya fito daga part din daddy shima mummy ce taje part din daddy shiyasa ya fito
Ilham tana kwance akan kijerun parlour tana kallon Bollywood
Waiwayawa tayi taga Jalal
"Sannu Yaya ya jiki?"
"Da sauki"
Rannan a hade Yabata amsa ya fice
Yana zuwa dakinsa ya tarar missed calls kusan takwas
Da wannan unknown number din
Tsaki yayi yaje yayi wanka yazo ya nemi gurin kwanciya ya dakko wayarsa hotonsa ne da Jawwad akan wallpaper dinsa kallon hoton yayi sunyi kyau a hoton matuka murmushi yayi ze bude what's app dinsa message ya shigo wayarsa budewa yayi

"Haba baby at least ko sau daya yakamata ka dau wayata kasan kuwa yadda zuciya ta takeyi I feel u in my every heart beat, nayi missing innocent face dinka gashi kaki yadda ko muryarka inji help me baeb na damu da kai
From ur lovely Bae"
"Wai wannan wace irin Jaraba ce haka, wace ce wannan take Neman yimasa kutse haka a cikin rayuwarsa shi baze iya wannan shirmen ba wannan soyayyar duk haukane da bata lokaci"
Yana cikin wannan mitar ne wayarsa kuma takama ringing unknown number din ce dai
Dagawa yayi a fusace
"Waike wace irin mahaukaciyace karfe nawa yanzu nibana wannan haukan ki kyaleni tun kafin ta kaimu ga bata miki rai"
"Wow komai naka birgeni yake baby jin muryan nan taka kawai ta isheni bacci me dadi,
Mark you ba abunda zakamin Wanda ze batamin rai
Love u.......
Katse wayar yayi ya kasheta gaba daya ya jefa wayar kasa nonsense yafada a hankali

Washe gari bayan sallar asuba Ummi taga Jalila ta koma bacci
" ke baby ba ankoma school ba kwana biyu da komawa amma kina nade a Gida tashi ki shirya yau makaranra zaki tafi"
"Ummi bangama shiryawa ba in nagama zan koma"
"Aikuwa sekin koma yau din nan"
"Ummi bani da socks fa, kuma ni sekin canzamin school bag zan koma"
"Kibari inzo gurin nan baki tashi kinyi shirin makaranta ba ni da kene"
Ummi ta fita daga dakin Ummi na fita Jalila tacigaba da baccinta har kusan karfe bakawai Ummi tazaci Jalila ta tashi amma tana zuwa ta tarar da ita a cikin bargo
Ran ummjne ya baci ta yaye bargon ta Dala mata duka tashi dan kaniyarki dama baki tashi ba tashi kisa uniform kitafi
"Ummi dan Allah kiyi hakuri, banga socks dina bane"
Girgiza kai Ummi tayi
"Allah ka shiryamin yarinyar nan, ai tunda baki gadama ba nasan bazakiba zakiga tsiya"
Wunin ranar Sam Ummi taki kula Jalila
Ta dinga binta tana bata hakuri tana mata magiyar ta saimata wata jakar daga karshe seda Ummi ta bata kudin Jaka da socks din hankalinta ya kwanta
Amma Ummi tace bazata fita ba seda yamma

Washe gari se bayan sallar la'asar sannan Jalal ya kunna wayarsa amma yana kunnawa sakonine sukacika masa waya wasu na bin wasu
"Wannan wane irin Jaraba ce haka"
Sakonta na karshe ya duba "Baby in baka bude wayarka ba zanzo har inda kake, tun safe nakasa nutsuwa ko har yanzu baka da lafiya ne?
Na damu da kai baby
From your lovely Bae"

"Wannan wace irin Jarababbiya ce da take uzzurawa rayuwata ne"
Yana cikin wannan tunanin Sega Ilham ta shigo da kayan abinci ta samu guri ta ajiye
"Yaya ga abinci inji mummy
Harta mike zata fita ya kira sunanta
"Ilham"
"Na'am"
"Zo nan" seda cikinta yayi kara gabanta ya fadi Allah yasa ba wani abun nayi masa ba jiki a sanyaye ta nufi inda yake guri ya nuna mata kusa dashi ta zauna wayarsa ya dakko ya shiga messages din nan ya nunamata
"Ke kike turomin wannan shirmen ko?"
Gabanta ne yafadi ita ba tuhumar dayake matane ta sata faduwar gaba ba se fargabar wace wannan take shirin yi mata kutse
"Tambayarki fa nake"
Jiki a sanyaye ta daga kai ta kalleshi
"Bani bace ba"
Jawwad ne ya shigo
"Inyee yau zumunci ake jine Yaya da kanwa"
Basu kulashiba ya karasa ciki ya zauna yaga ran Jalal a bace Yana ma Ilham magana

"To waye?"
Jalal Ya tambayeta
"Ya za ayi in sani yaya, nidai nasan bani bace"
Tabashi amsa hawaye na gangarowa daga idonta
"Uban me na miki zakimin kuka"
Wani irin kallo tayi masa
"Yaya Jalal tambayata kake meyasa nake maka kuka ko?
Ina nuna kulawata akanka, baka damu dani ba bakajin me nake ji a raina hasali ma ka tsaneni, amma wata a waje tana shirin rusani ga sakonin da take turomaka, kuma kake tuhumata ni ina naga fuskar da zan turo maka wannan sakonnin "
Cikin hargowa ya mike ze zazzaga mata bala'i
Jawwad ya ga tsananin kishi kwance a idon Ilham, tausayinta ne Yakama Jawwad dan haka ya dakatar dashi
"Ilham gaskiya ta fada Jalal"
Jawwad Ya kalli Ilham yace
"Tashi kikoma ciki"
Sannan ya kalli Jalal

Yamma nayi Jalila ta shirya ta dau kudin safa da Jakarta tayi waje
Kai tsaye inda ake fadan gidan sojan nan ta nufa daga waje ta karewa gidan kallo
Aranta take fadin gaskiya gidan nan ya hadu saura kuma inshiga inga meye a ciki yadda ya hadu daga wajen nan cikin kuma ai nasan yafi haduwa
Daga nan ta mika ta nufi inda zata sayi jaka amma seta hango wani kanti da sojoji a bakin gurin dan haka ta yanke shawarar zuwa taga meye akeyi a gurin
Kai tsaye ta kutsa cikin kantin wani soja ne ya daka mata tsawa yace ta tsaya a waje se sungama sun tafi tukuna
"Dan Allah kabari abu zan siya kawai in tafi ni ba gurinka nazo ba "
Zekuma magana wani sojan yace ya batta ta shiga
Tana shiga taga wani babban mutum a zaune akan kujera fuskar nan tashi murtuk babu annuri
"Ina wuni"
Jalila ta gaisheshi be amsa ba
"Baba gaisheka fa nake nace ina wuni"
Dan juyowa yayi ya kalleta ya danyi murmushi jin takirashi da baba
"Lafiya kalau sannu yan mata"
"Yawwa"
Ta sai chocolate dinta ta mutumin nan yace abawa Jalila shize biya
Seda ta risina sannan tace
"Baba nagode sosai"
"Bakomai adinga shan chocolate din a hankali yana kashe hakori"
Murmushi Jalila tayi ta fito "aikin banza na daukama wani abun ake a gurin to me sojoji suke anan ko gadinwa suke oho"
Ta siyo Jakarta ta fito dayake kusa da kantin ake saida jakunkuna
ta hangi mutumin dazu ya fito daga kantin nan ze shiga mota se ya yadda wallet dinsa da sauri ta je ta dauka, amma tuni sunyi nisa sun bar gurin sun nufi layin gidan wannan sojan
Ta dinga jujjuya wallet din nan kawai ta tafi Gida da wallet din
Bata nunawa Ummi ba ta boye wallet din
Ta faki idon Ummi taje ta dau wallet din ta bude kudin kasar wajene a ciki da ID card bata tsaya bin ta ID card dinba ta aje wallet din cikin sabuwar jakar makarantar ta cikin litattafanta

Washe gari Ummi ta tursasata ta shirya ta tafi makaranta, ta wannan layindai na gidan nan Jalila tabi dan takuma ganin gidan nan kuma ko Allah zesa taga mutumin nan
Tanata kallon gidan wani soja ya kalleta
"Ke me kike kallo wuce ki tafi makarantar ki"
Ya mutsa fuska Jalila tayi
"Ina ruwanka da makaranta ta?kallo kawai zanyi in tafi"
"Ba a son yawan ganin mutane a arear gurin nan saboda tsaro dan haka wuce ki tafi"
"Did I look like criminal, da uniform dina na makaranta balle kace wani abun zanyi, sekace gidan shugaban kasa naga dai gidan mutum ne ba aljan ba in me gidan yasan bayaso a dinga wucewa ta hanyar gidan ai da seyaje duniyar wata ya Gina gidan ba duniyar mutane ba"
"Kut wace irin yarinya ce wannan?"
Aikuwa sojan nan beyi wata² ba ya zare beilt da nufin ya koya mata hankali se su kaga wasu motoci suna shigowa Latin manyan motoci ne glasses din duk tint ne mutumin jiya da ya sai mata chocolate ne ya fito daga daya daga cikin motocin
Wannan sojan da ya zare belt ne ya kame yana saramasa da ido yai masa magana sojan ya tsaya
"Laa baba ina kwana"
Jalila ta tsuguna tana gaisheshi "lafiya kalau Yar baba, meyahada ki da wannan"
Ya nuna mata sojan nan da ya biyota
Bata boye masa komaiba ta gayamasa murmushi yayi a ransa yace lallai wannan yarinyar Yar rigima ce amma a fili yace
"Yar baba yanzu kin makara ki tafi makarantarki rabu da shi
Kai baka ganin Yar makaranta ce kawai daga kallon Gida se a ce za a bigeta ina nema mata afuwa"
Jalila tasaka hannun a Jakarta ta dakko wallet din nan ta mika masa
"Jiya ka yaddashi bayan kafito daga kantin nan"
Hannu yasa ya karba tasan ce kuwa yana ta dubawa tun jiya be ganta ba yayi zaton yayi miss placing dinta ne
Murmushi yayi "nagode sosai Yar baba Allah ya albarkaci rayuwarki "
"Ameen nagode"
Ta juya ta tafi hanyar makarantar su ta makara sosai amma taci sa'a ba malami a ajinsu dan haka ta shige tanufi ajinsu
Class dinsu ne ya kaure da hayaniya ga Queen ta dawo nickname dinta kenan a makarantar boko Queen J
Kai tsaye bayan sungama murnar ganin juna da yan ajinsu gurin zamanta ta nufa amma me setaga wata hakima ta hakimce mata a seat Jalila dai bata Santa a ajinsu ba maybe newcomer ce dan haka Jalila tace
"Sannu dai excuse me gurin zama nane ina bukatar zan zauna"
Banza yarinyar tayiwa Jalila
"Ko kurma ce ne? Nace kifito nan gurin Jalila ne fada tace"
"Wallahi mun gaya mata har malamai sun San nan gurinkine amma tace ita kuma dole anan zata zauna"
Cewar wata daliba
Ita kuwa sabuwar zuwan nan bata da niyyar magana balle Jalila tasa ran zata tashi sema wani kashingida tayi ta kurawa Jalila ido tana hura hanci tana kallon Jalila up and down
"Ke yau kome kikeji zan sauke miki shi yau koda uban me kike yawo wallahi sekin bar seat din nan uwarkice ni a rashin mutunci"
Dariya yarinyar tayi "ok yi abinda zaki iya nikuma na miki alkawarin kawo karshen rashin kunyarki a yau base gobe ba"
"Queen J dan Allah kiyi hakuri ki kyaleta babanta fa babban sojane ranar Monday aka kawota"
Wata dalibar tai maganar tana kokarin Jan hannun Jalila
dukan benci Jalila tayi
"Wallahi ko Yar gidan bullet ce, ke Allah yasa baban tane AK47 wallahi seta tashi this is my kingdom, in ubanta ya tsaya mata ni Allah ya tsayamin, Kafin kiyi maganina ni zan fara maganin wannan izzar taki, ko kina wa kowa hauka ba ayiwa Jalila"
Hannu biyu Jalila tasaka ta fizgo yarinyar nan daga cikin benci aikuwa yarinyar nan ta wankawa Jalila mari,
Wasu daga cikin dalibai suka tafi kirawo malamai domin raba fadan nan
Amma tuni Jalila ta rama marin nan ta kara mata wani, Jalila ta dage ta hankada yarinyar nan kan bencina nan take goshinta ya fashe jini yashiga fita

Share please
More comments more typing.......

Proud of you my fans INA jin dadin adduoinku nagode kwarai Allah yabar kauna
❤❤❤❤❤
Team JALILA kunga abinda yau ta dakko to ni ba ruwana😎😎

🖊️🖊️🖊️🖊️🖊
[9/12, 6:02 AM] +234 816 830 7871: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_
(2020)

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 24

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢
Your comments give me courage


-My First Novel-
Not Edited

Yayan Hanan se kallon Abba yake kaman yasan shi.

Tunda Jalila ta shiga office din taje tasamu guri ta durkusa kanta a sunkuye kai kace wata mutumiyar kwarai ce
Ga director na makarantar, ga Ummi, da Abban su Jawwad, sekuma baban Hanan da yayanta, se mukarabbansa da suke waje bakin office din sekuma Jalila da hanan dasuka shigo yanzu
Baban Hanan Bin Jalila yayi da kallo sannan yayi Murmushi a zuciyarsa indai wannan ce zata aikata don bata da tsoro

Kanta a sunkuye tace "Abba ina kwana"
"Lafiya kalau Jalila ya rashin ji"?
Shiru tayi ba tace komaiba
"Abbanki kawai kikasani ko Jalila,?"
Director ya tambayeta batace komai ba still shiru tayi

"Was nake gani haka kadai ace Yar baba ce wannan?"
Da sauri ta dago ta kalleshi dan murmushi tayi se yanzu ta ganeshi mutumin nan ne daya hana wannan sojan zaneta, Wanda ta tsinci wallet dinsa
"Sannu baba ina kwana"
"Lafiya kalau Yar baba"
"Dake akayi fadan kenan, dama haka kike da fada, ai wannan sister dinki ce" ya nuna hanan

"Ni ba sister na bace nikadai Ummi ta Haifa, se kanwata daya Nana" Jalila tai maganar ba tare data dago ba
Dariya tabasu gami da mamaki babu nadama a tare da Jalila ita haryanzu a ganinta ba laifi tayiba tunda ita aka takala da fada
"Daddy wai kasantane"?
Yayan Hanan yai tambayar yana kallon mahaifinsu
"Eh nasanta 'yata ce shekaranjiya Allah yabani ita"
Baban Hanan yabada amsa
Ya kalli Abba da Ummi
"Ai Dana San itace ma bazanzo ba yarinyarku mutuniyar kirkice, fitina CE kawai ta yara kuma ga dukkan alamu bata son wargine ko Yar baba?"
Ya tambayeta yana murmushi
"Komai ya wuce amma Yar baba kidena Neman magana kinji yarinyar kirki kin dagawa mamanki hankali da babanki, gaskiya suna sonki dayawa"
Gyada masa kai Jalila tayi

"To baba na dena insha Allah"
A ranta kuwa tace dama wai wannan shine captain din da ake ta fada wani salihi dashi haduwar mu biyu be tabamin rashin mutunci irin na sojoji ba
Ni na daukama zanga tunda ga bakin office anfara kwallo dani

"Daddy wai yanaga ka maida abun jokes jini fa ta fitar min kuma ta zageka"
Hanan tai maganar cikin shagwaba da hawaye a idonta
"Ohh sorry dear itama yata ce daga yau na hadaku kawance"
"What ba dai dani ba wallahi, Allah ya kiyaye"
Hanan tai maganar cikin tsiwa
"Baba nikuma na karbi kawancen nagode sosai daga yau tazama kawata"
Jalila tai maganar tana murmushi tare da kallon hanan
"Allah yayi miki Albarka Yar baba"
Abun ya daure musu kai yaushe mutumin nan yazo anguwar amma har yasan Jalila gaskiya a sojojin ma yana da matukar kirki, gaba daya kasa cewa komai sukayi

"Daddy ni gani nayima tana kama da Hanan wallahi"
Yayan Hanan ya fada yana kuma kallon Jalila
"Nima nagani Abdallah"
"Kinsan Aliyu Usman Imam"
Yayan Hanan ya tambayi Jalila
Dagowa Jalila tayi ta kalleshi
"Kai Yaya Jawwad kake nufi ga Abbanmu nan" ta nuna masa Abba "no wonder naga suna kama kuma ance shine abbanki shine class ref dinmu a BuK yana da kirki ga kokari amma gaskiya shi ba fitinanne bane kamarki"
"Waze hada ma shi Jawwad yaron kirkine kaman ma ba sunansa Aliyu ba amma wannan sekace kura saboda fada"
Ummi tayi maganar tana nuna Jalila
"Dan Allah kuyi hakuri bazan karaba Insha Allah"
Takoma gaban Abba shima ta tsuguna
" Abbana Dan Allah kaima kayi hakuri nadena insha Allah, Dan Allah kuyi hakuri"
Kara birge baban Hanan tayi tasan tayi laifi kuma ta bada hakuri, ita damuwar iyayenta ce bata so yaji inama Hanan ce keda wannan tarbiyyar tayi laifi tabada hakuri ai sedai in kaga dama ka kasheta ko ka barta da rai amma bata laifi ta bada hakuri indai Hanan CE
Director ko a ransa yace lallai wannan yarinyar ita fushin iyayenta ne a gabanta bata damu data bawa su Hanan hakuri ba suda akayiwa laifi a fili kuwa yace
"To Alhamdilillah tunda itama 'yarka ce mungode da wannan karamci naka yallabai,
Kamar yadda ka fada Jalila yarinyar kirkice saboda a dalilinta makarantarmu tasamu awards, tana da kokari ga hazaka, muna alfahari da ita a cikin dalibai, ita babba damuwarta ita da dalibaine, shima kuma insha Allah daga wannan shikenan tace bazata karaba"
Director yayi maganar yana kallon Captain Abdurrasheed
"Hakane dama dan Adam Tara yake be cika goma ba, muna kara bada hakuri dai ayi hakuri"
Abban Jawwad ne yai maganar yana kuma kallon baban Hanan
Itakam Jalila bataga dalilin bada hakurin dasu Abba suke tayi ba
"Karku damu ba komai yariga ya wuce ai, Allah ya shiryamana yara gaba daya, yayi musu albarka"
Suka amsa da Ameen gaba daya
Haduwar da akayi domin hukunta Jalila da yin sasanci se yakoma haduwar hada zumunci inda hira ta barke a office din director
Malaman da suke ta jira suga an fara casa Jalila se sukaga akasin haka
Daddyn Hanan ne yagaya musu yadda yasan Jalila daga ranar da ya saimata chocolate zuwa tsintar wallet dinsa, har exchanging lambar waya captain yayi da Abba, sukayi sallama kowa ya watse
Ummi ta saka Jalila a gaba Abba ya dauke su zuwa Gida

"Impossible wallahi a fitarwa da yata Jini sannan kace wai ba komai ka kyale yarinyar ta daki banza akan me?
" look safiyya shi da na kowane, kinsan halin Hanan sarai itama wani lokacin ta fiye fitina, da wulakanta mutane, for now ayi hakuri na rufe wannan case din"
"Aikuwa be rufu ba ni a gurina, dan mene Za a daukarmin yarinya sannan kace ka rufe case, waye uban yarinyar da yatsaya mata ta dokarmin yarinya"
"Ohhh my God mum Abdallah kinfiye rikici fa, wallahi ba Yar wani bace ba kawai dai she's so kind, yarinyar and she regrets what she did, ni yarinyar ma tausayi tabani wallahi mamanta duk ta damu, gashi kuma kanwar abokin Abdallah ce"
"Kaga ya isa haka bana bukatar jin wani abu ya isheni haka, ko uwar abokin Abdallah ce senasa an koyamata hankali balle wata kanwar aboki, in kai ka hakura ni ban hakuraba wallahi...
" Enough "
Ya daka mata tsawa nan take ya juye ya koma sojansa fuskar nan kaman be taba dariya ba
"Idan kika kuskura kikayi wani abu akan yarinyar nan kinsan meze biyo baya kinsanni sarai"
Yayi maganar cikin tsawa sannan ya fice ya bar mata dakin

"Wai Jawwad meyake damunka ne tun dazu ka kasa zama, ka kasa tsaye se zagaye kakeyi"
Jalal ne dake kwance akan gadon Jawwad yai maganar yana kallon Jawwad
"Ta yaya zan iya zama bansan wani hali akeciki ba ko sojan da Jalila ta dakarwa yarinya ya hakura, bansan me ake cikiba nakira wayoyinsu gaba daya basu daga ba Allah yasa dai lafiya, Allah yasa basuyi mata wani abun ba"
Jawwad yai maganar cikin damuwa
Dariya Jalal yayi "to meye abun tada hankali in suka karairayota se ka tafi Kaduna jiyya"
Jalal ya karashe maganar yana dariya
Tsaki Jawwad yayi Wanda yayi dai² da ringing din wayar Jawwad
Da sauri ya dakko wayar yadaga a zatonsa Abbana
"Hello hey Aliyu yakake"
"Ina lafiya Alhamdilillah , amma ban gane me magana ba"
"A Rasheed ne"
Aka bashi amsa
"Ohhh Abdallah ban dauki muryarka bane, kuma bani da wannan lambar taka"
"Wallahi kuwa na canza layine"
"Allah sarki ya kake ya mutan gidan"
"Kowa lafiya Alhamdilillah, yau naga kanwarka"
"Kanwata wacce kenan ai Nana tana kano"
"Ba itaba wata Jalila"
Gaban Jawwad ne yafadi
"A ina kaganata ya akayi kasan kanwata CE?"
"Sabani suka samu da Hanan mummy ta daga hankalinta mukaje nida daddy, har muka hadu da abbanku"
Ajiyar zuciya Jawwad yayi sanan yace
"Alhamdilillah Abdallah ya ake ciki Dan Allah kuyi hakuri kabawa daddy hakuri,"
"Karka damu, ai

Please Login or Register in order to submit comment