Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Bayan Jawwad sun gama cin Abinci suka fito suna hira, a harabar gidansu Jalal suka koma suna basket ball, se magariba suka bar gurin, bayan sallar magariba Jawwad yacewa Jalal, yazo suje gurin Mummy "muje muyi mata me?" "yakamata dai muje kwana biyu ban ganta ba bamu gaisa ba" "kaje kai kadai mana, ba dolene se naje ba" "Jalal ba shawararka nake nema ba, ka tashi mu tafi" Ganinda Jalal yai Jawwad ya hade rai sosai, shiyasa shi mikewa, "tashi muje" Jawwad ya tashi suka tafi cikin gidansu Jalal, Jalal ne a gaba Jawwad yana binsa, Ilham ce kadai a palourn kwance akan three seater tana daddanna wayarta, mikewa zaune tayi tareda fadin "sannunku da zuwa" Jawwad ne ya amsamata, "yawwa Ilham, ina Mummy ne?" "tana dakinta, inaga salla takeyi bari inje in kirata" ta mike ta nufi part din Mummy, Jalal dai se cika yake yana batsewa sekace wanda akayiwa wani laifi, ba a dadeba sega mummy ta fito, Ilham na bayanta, ta karaso ta nemi guri ta zauna a palourn, dan risinawa Jawwad yayi "Mummy ina wuni" "lafiya kalau Jawwad kwana biyu ya gida, yasu Maaman"
"tana lafiya" "Kwana biyu bamu hadu da ita ba, ina jira zata aikomin da kaya" "eh dazu naga an karbo, amma zata aikomiki ne" "Yayi kyau" shidai Jalal bece uffan ba, sema mike kafarsa da yayi ya kashingida, Jawwad yace "Mummy ranar Saturday yakama birthday din Jalal fa" "ina sane Jawwad, wannan karon ba tare zakuyi ba" "eh mummy, nashi zamu farayi tukuna, nace bari agaya miki" "Assalamu Alaikum" gaba daya suka amsa sallamar tareda waigawa, ko be juyoba yasan muryar Jalila ce, karasowa tayi cikin yanga, ta kalli Jawwad tai masa murmushi sannan ta durkusa kasa tace "Mummy ina wuni" "lafiya kalau 'yan mata kwana biyu, kin buya bana ganinki" murmushi Jalila ta kumayi "ina nan Mummy bana fitane kawai" "amma baki da lafiya ne, naga kin rame haka?" Jawwad yace Mummy ta danyi rashin lafiya kam""Allah sarki ba labari, Allah ya sawwake" suka amsa da Ameen banda Jalal da Ilham dan tunda ta shigo Ilham ke mata kallon banza
Mummy tace "Jalila yi hakuri bari in dan saki aiki, jeki dakina akwai drowern mirror dina akwai, key ki dauka ki bude wardrobe dina, zaki ga akwai wani kit kibude ki dakko kudin ciki
Ilham seda ta kalli Mummy dan sam Mummy bata sata harkar kudinta, amma yau ta tura Jalila har bedroom dinta ta dakko kudi, seda Jalila tayi Jim kaman bazata ba sannan ta mike, ta nufi dakin Mummy,
"Yawwa Jawwad ina jinka, yi hakuri na tsaya surutu" "bakomai Mummy dama cewa nayi, ko zaki halacci gurin birthday din nasa" Jalal ne ya dago da sauri yana wa Jawwad wani mugun kallo, shikuma ya dauke kai kaman besan me yake ba, murmushi Mummy tayi "waceni Jawwad, Allah ya temaka, ya raya Jalal sannan ya shiryamin shi"
Koda Jalila tashiga taga part din Mummy ma ya tsaru, katon palour ne, me dauke da kayan alatu, se tangamemen kofar bedroom dinta, ya tsaru matuka, kaikace a kasar wajene, Jalila ta nutsu ta dau abunda aka sata ta fito.
Jawwad ya gyara zama sannan yace "Mummy in bazakije ba ga Ilham, ko yan uwa ai yakamata sumana kara suyi attending" Jalal ji yake kaman ya make Jawwad, shi bayason gayyar surutu, amma Jawwad se gayyato masa tarkace yake Ilham tace "Jawwad aini ko ba ku gayyaceni ba zuwana gurin birthday din yayana dolene, dan haka zanje nida kawayena" wani uban tsaki Jalal yayi, duk suka juyo suka kalleshi, Mummy tace "kagani ko Jawwad, nikam Allah yakawo silar shiryuwar Jalal, yanzu a haka kake tunanin inyi attending gurin birthday dinsa, ya dizgani a gaban abokansa, Sam baya ganina da mutunci"
Ai kuwa Jalal a fusace yace "kagani, nidama bance tazo gurin birthday na ba, seda nace bazanzo ba amma ka janyoni kaga har zata faramin korafi sek....... Sekuma sukaji yayi shiru, ya koma ya kashingida, fitowar Jalila taji Jalal yana wannan masifar suka hada ido, ta girgiza masa kai, alamar ya dena, shine abunda yasashi yin shiru, yakoma ya kashingida, duk abun nan ba wanda ya lura dame ya faru se Ilham, wadda taji kaman an dakko dutse an sakamata a zuciyarta.
Jalila ta karaso ta durkusa tabawa mummy kudin, Mummy tace "tafi dasu, kibawa Maama kice kudin wancan kayanne, ban mata transfer bane saboda wayata, ta dan samu matsala" "to zan gaya mata Insha Allah, seda safenku" Jawwad yace "bazaki jirani ba" "a a yaya, seka taho"
Ilham ce tafara mikewa ta tafi dakinta, sannan Jalal, shima tashi yayi ya bar dakin, dan Jawwad yagama bata masa rai, Jawwad kuma ya tsaya, yaita rarrashin Mummy kan halayen Jalal, sannan yai mata sallama ya tafi.
Koda Ilham ta koma dakinta ji tayi kaman ta dora hannu akanta ta fasa ihu, wannan wace irin masifa ce, tunda take a gidan nan, mummy bata shigar da ita cikin sha anin kudinta, amma yau da kanta ta tura Jalila kan kudinta, kuma karewar abun takaici wai hartayiwa Jalal signa ta hanashi abu, kuma ya hanu, lallai akwai sauran aiki, meyasa wannan yarinyar ta shigo rayuwarmu tayi kane2 haka, me yakamata inyine, kozan yi yawo tsirara se burin mahaifiyata ya cika, amma ta yaya? Wata zuciyar ta tambayeta, shiru tayi zuwa can kuma tayi wani irin shu'umin murmushi, tareda jinjina kai, "muje zuwa, Jalila kin tara kin samu, senayi sanadiyar da mujiya seta fiki farinjini a cikin al umma"
A satin ranar Monday su Jalila suka fara zuwa makaranta, Abba ya daukar musu driver saboda Kar a dorawa Jawwad nauyi dayawa shima ga nasa karatun, Jalila taji dadin fara zuwa makaranta, in ka ganta kai kace irin salihar nan ce, dan ko magana batayi sosai, wanda yana cikin halin Jalila in taje guri seta karanci kowa tsaf sannan zaka san wacece, ko magana bata fiyeyi ba, sannan bata yadda tayi kawa ba har yanzu, a satin nan tunda tafara zuwa hijjabi take sakawa har kasa, se farin glass, yauma uban dogon hijjabinta dark blue har kasa ne a jikinta, se jakarta data rataya, sunfito daga lectures tana jikin wata bishiya inda suke haduwa da Nana, taji wasu suna zundenta wai ga ustazan jami a, gigin secondary ne ta shigo a ustaziyya kafin afita kuma anyi clean, irinsune mugayen tantiran makaranta in suka waye, itakam ko ta kansu batabiba, dan ko kallo basu isheta ba, a ranta tace "kucigaba karku fasa, ku bari in zama yar gari, zaku gane baku da wayo dan ba ruwana da wata jami a, mutun yayimin senayi masa, but now kuci karenku babu babbaka" tana tsaye nan Nana ta karaso, suka nufi motarsu, a hankali Jalila take gane halin yan ajinnasu, da yaran masu kudi, dana talakawa masu dorawa kansu karya, yan rainin hankalin lecturers, da masu iyayi, kowa tana ankare da halinsa, tana ganesu, amma still ba ruwanta da kowa, wasu suyi gulmarta a gabanta wasu a bayan idonta, seta nuna musu ita magana ma abun wahala ce a gurinta,
Nana kam hartayi kawaye daga zuwanta, yayinda dabi un Jalila suka tafi da imanin kawayen Nana, ta iya gayu maganarta kawai abun burgewa ce balle tafiyarta da sauran
mu amalarta, sedai suna mata kallon me girman kai, saboda gani suke kaman wulakanci take musu, inba Nana ba bata kulasu, dan ta yanayin shiga da mu amala tana iya gane, mutanen banza dana kirki, Jalila kenan me abubuwan ban mamaki

Ilham ta gayyaci kawayenta gurin birthday din Yayanta kuma masoyinta wato Jalal, se wani rawar kai take tana shirye2, ta gayyaci su yaseera da sauran kawayenta, se shiri takeyi, taje sabon gari ta sha kitso, tayi booking din make up, hatta shigar da zatayi sabon kaya ta siya.
Jalila ma nata shirin takeyi, saboda mugayen mafarkan da take da Jalal, dan haka da shirinta, zataje gurin birthday din nan, tanason tayi taka tsan2 sosai a gurin nan dan ita sam bata yadda da wannan birthday dinba, tana so taga suwaye abokan Jalal ne, mussaman Jeje, dakuma wasu abubuwa da take shirin yi a gurin, tanason tabattar wa Ilham Jalal baya gabanta, Bangaren Jeje ma shidasu hannah da abokan shaye2 sun shirya tsaf domin gudanar da mummunan kudirinsu akan ABDUL JALAL.
Ranar juma a da daddare, wanda yakama jajibir din birthday din Jalal, Jalila ta tafi Dakin Jawwad domin tana son magana dashi, tai sa a kuwa shikadai ta tarar a palourn, taje tasamu guri ta zauna, Jawwad ya kalleta"Babyn Yaya Jawwad, ya akayine?"
"gurin Yaya nazo" "to Yar gidan Yaya, ina jinki"
"Yaya Jawwad , gaskiya abokinka tunda mutane masu hankali zasuje gurin nan, dan Allah ka kaishi a rage mai gashin kansa, sannan kar kabari yasaka sarkan nan dayake sakawa sekace wani kare, ga wan..... Kai tsaye ba sallama sukaga Jalal ya shigo, hade rai Jalila tayi" a dai dinga yin sallama" banza Jalal yai mata, ya kalli Jawwad "kai gurinka nazo" Jawwad yace"ai gani, Allah yasa lafiya" wayar Jawwad tafara ringing "excuse me bari in amsa waya" yadaga wayar yasaka a kunnensa tareda yin sallama "Assalam Alaikum"
Muryar Hanan Jalila taji "wa alaikum salam barka da yamma Taurarona fatan kana lafiya?"
"lafiya kalau Hanan, ya gida, yasu Abdallah da daddy?" "suna lafiya, nice dai bani da lafiya" "yasalam meyasameki" "kewarka mana, itace take damuna, yanzu yaya queen take, naga kwana biyu haushina takeji" "tana lafiya, yanz... Juyawa yayi da nufin yabawa Jalila wayar, yaga Jalila ta cika ta batse, ta hade rai sosai, fasa bata wayar yayi, yace
" Queen dinki tana lafiya" "Masha Allah ina sirikata Nana, kodayake ita muna waya, dan Allah Yaya Jawwad yaushe zakuzo Kaduna ne, inaso inkuma ganinka, kullum senayi mafarkinka fa" Jalal dake gefe ya kalli fuskar Jalila kawai ya kwashe da dariya ganin yadda ta hade rai, Jalal ya tashi ya fita daga palourn, yana kuma yin dariya, ba karamin kyau Jalal yakeba idan yana dariya, Jawwad seda ya sha jinin jikinsa yakuma kallon Jalila, muryar Hanan ya kuma ji "my Haidar bakace komai ba, dan Allah yaushe zakuzo?" mikewa Jalila tayi ta fice daga palourn dan bazata iya cigaba da jin wannan hirar ba, ashe Hanan dagaske take son Jawwad tajeyi, kishi ya lullube Jalila ta fito ko ganin gabanta batayi, tazo fita taga Jalal a tsaye, a kofar fita, shiru tayi ba ta cemasa komaiba ya kalleta, yadda ta hade rai, tuntsurewa yakumayi da dariya, "kinji abunda Ilham takeji ko? Kinji yadda takeji idan taga kinamin shishshigi ko?, are u jealous of your brother" wani mugun harar tayi masa "ni matsa in wuce" Jalal yace"in naki fa? Ji yadda kike wani hade rai" sekuma ya hade rai kaman bashi yake dariyar nan ba yace "to bari in gayamiki, dakaina zan dauki Jawwad in kaiwa Hanan, ubanme Jawwad zeyi dake gaki mummuna gaki kwaila, se tsabar iyashege da rashin kunya da kikasa a gaba, ni zan tsayawa Hanan seta auri Jawwad, in yaso kije kinemi me tsautsayin daze aureki, wanda ze iya tolerating wannan nonsense din naki, sokuwa kawai, wuce ki ban guri" murguda masa baki tayi, tazo zata wuce ya kuma rufe hanyar, ya kalleta
"Kashedina dake na karshe, gobe in Allah ya kaimu kika sake na ganki gurin birthday na, duk abunda ya sameki kekika jawa kanki, idankuma kinkiji kinje gurin, idan kika sake kikayi wannan karambani a gurin, shima kome ya biyo baya ke kika sani,"
Cikin bacin rai tace" waini kadai ka tsana zakace bazanje ba, wallahi senaje, sedai in baza ayi ba, kuma wallahi niba mummuna bace ba, Mummuna tana gidanku wato Ilham" kallonta ya kumayi tsaf, sama da kasa, be kuma cemata komai ba, yabata hanya ta wuce, tana tafe tana mita, harta je dakinsu, Nana ta kalleta "lafiya dai, naganki kina fushi hada mita" "Ke rabu dani ba komai"
Sallar isha i tayi ko Abincin dare bataciba, tanemi guri ta kwanta, banda kishi da bacin rai ba abunda yake damunta, "haba Hanan yazaki min haka, meyasa kikeson Jawwad din, kema ina sonki, zan iya sadaukar miki da komai nawa da kikeso, saboda kaunar da nakemiki, amma banda yaya Jawwad dina" haka taita juye2 da kyar bacci ya dauketa

Jalal yana tsaye se fara a yakeyi, ga wani katon cake 🎂 agaban sa, ga mutane nata hada2 Hannah ta yanka cake ta dakko tasaka masa a baki, cake din na shiga bakinsa yazama baki, jini yafara zuba daga bakinsa ya fadi a gurin, da gudu Jalila ta karasa ta kifar da tebur din da cake din kafin ta juyo ba kowa a gurin daga ita se Jalal, ta tafi tana lekawa taga koda wanda ze temaka mata ya dauki jalal a kaishi Asibiti tana dawowa taga, Ilham ta shake Jalal tana kokarin kasheshi
"Subhanallah!!!" ta furta da karfi

Share please,
More Comments More typing...............................




🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
[9/28, 8:10 PM] Ayshercool: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 52
PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske,
Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what's app akan wannan lambar wayar
07063065680

_My First Novel _

A firgice ta mike zaune tana waige2, Nana ta tashi zaune itama, "lafiya Jalila, meyasaki ihu haka" Jalila ta hada zufa, se haki take hannu tasa ta dafe kanta "bakomai Nana, yi hakuri na tasheki, kwanta abunki, na dan tsorata ne kawai" "to shikenan, ki kwanta kema, darene sosai yanzu" "to zan kwanta" Nana ta cigaba da baccinta, yayinda bacci ya kauracewa idon Jalila, se tunani da yacika mata zuciya, da taga baccin ya gagareta, ummi ce ta fado mata a rai, dan tasan da ummi na nan da yanzu tana sallar dare, tashi tayi itama taje ta dauro alwala ta tada salla, tayi addu a sosai wanda galibin addu'ar ta ta, tana fatan Allah ya bayyana mata Ummi, dakuma fatan Allah ya shiryi Jalal, ya bata nasara akan makiyansa, a haka tasamu bacci yakuna daukanta.
Yau Saturday yakama ranar birthday din ABDUL JALAL, shirye shiryensu suke yayinda Jalila banda aikin tunani ba abunda takeyi, Jawwad ma a wani bangaren ya damu ganin yadda Jalila kishinta ya fito karara a fuskarta, duk ya damu gashi ya kira layinta amma a kashe, gashi yana tsoron ummi dayaje da kansa gurinta.
Ilham se shiri take kaman wadda zata biki tun safe take hada2, tana waya da kawayenta akan yadda abun ze kasance,
Abun duniya duk ya ishi Jalila dan haka ta dau mayafinta ta fita, se azahar ta dawo, ba wanda tagayawa ina taje, tana dawowa ta hadu da Jawwad a harabar gidan, yaji dadin ganinta sedai besan mezece mata ba yana ganin har yanzu tana fushi dashi,
"Baby daga ina haka da ranan nan?" fuskarta a sake tace masa
"Yaya na dan fitane, ai ban dade da fita ba"
"to shikenan kidena yawo a rana, kar kanki yayi ciwo, bazan so hakan ba" murmushi Jalila tayi
"to Yaya, amma kaima ai naga a ranar zaka fita, kaima bazanso kanka yayi ciwo ba ai"
"Baby dolene yasa zan fita ai"
"Amma ranar da zafi fa" ta fada a shagwabe, dariya yamata "zaki fara rigima ko" tuno wayar da sukayi da hanan jiya tayi, nan da nan taji ba dadi, ranta ya baci dan haka ta wuce cikin gida ta barshi a gurin.
Jeje yanata jadaddawa Hannah, karta bari a samu matsala akan aikin dazasu gabatar yau akan Jalal babbar dama ce suka samu, karta bari ta kubu cemusu.
Allah ya temaki Jawwad ya lallaba Jalal ya kaishi aka rage masa sumar kansa, anyi masa gyaran fuska yayi kyau sosai, amma shi Jalal se mita yake wai Jawwad yasa an masa aski an maida shi mummuna, bayan sun dawo daga gurin askin ne suka hadu da Nana da Jalila a hanya sunje sunyo siyayya suka dakkosu, Jawwad yace "in anjima tare zamu tafine kokuma yaya?"
Jalila tai farat tace "A a tafiyarku daban tamu daban"
Jawwad yace "meyasa?"
"bakomai amma bazamu tafi daku ba, ka dau abokinka ku tafi, dan bana son mita da korafi" "Wane me mitar da kuma me korafin" "nidai ban kama suna ba" dariya Nana tayi
"hmm Allah ya shirya Baby Jalila"
"Ameen" duk abubuwan nan da takeyi karfin haline, dan ji take duk jikinta yayi sanyi,
Bayan sallar magariba, Ilham ta shirya tsaf, ta dawo daga gurin make up, tayi kyau ba laifi abunka da farar mace ga kwala2 idanuwa inji Hanan, dogon wando tasaka baki, da
t shirt blue wadda tazo har cinyarta, kanta ya sha kitson attach, ta dakko dan karamin bakin mayafi tasaka akanta, wrist watch dinta ma baki ne ga wani takalmi me uban tsini shima baki, se dan karamin jakarta data rataya, tayi kyau matuka, ta fito palour ta tarar da mummy, mummy tana ganinta tai murmushi
"Masha Allah, uwargidan Jalal kinyi kyau fa" murmushi Ilham tayi "Mummy har kinsa naji dadi wallahi"
"se tafiya" "eh mummy tafiya zanyi" "to a dawo lafiya, kikula da kanki" "to mummy, ki bani key din" mummy ta mikomata key din mota tace gashi nan "ayi tuki a hankali" Ilham ta karbi key ta fita
Nana ma tayi kyau ba karamin haduwa tayi ba, dan ita high west tasaka baki da jan body hook se ta kawo mayafi tayi rolling din kanta dashi,
Har Nana ta gama shiri Jalila bata da niyyar ta shi ta shirya tayi wankanta tsaf amma ta nemi guri ta zauna, seda Nana ta fara mita sannan ta tashi, Nana tasata a gaba tayi mata light make up, kamar wadda kwai ya fashewa a ciki Jalila ta tashi ta dakko wata doguwar riga purple wadda ta sha adon duwatsu, ta taje gashinta tasaka masa ribbon, kasancewar kanta ba dan kwali, gashin gaban kanta me laushi irin na fulani ya kwanta kai dagani kasan kan akwai gashi, ta dauki mayafin rigar ta dora akanta, Nana tai murmushi "fa tubarakallahu ahsanil khalikin, wallahi Jalila kinyi kyau sekace y'ar sudan, dressing din ya miki kyau" "ke rufamin asiri, wani irin larabawa ana zaman lafiya, da an cuci larabawa" "amma kinsan fulani koba mu kai larabawa ba da kyanmu" "ji wani cika baki ina kyan anan" dariya Nana tayi "ni karasa shiryawa mutafi" Jalila ta dau Jakarta purple, se takalmi me tudu. Tayi kyau kaikace wata yar hamshakin attajiri ce. Suka jero suka fito
Maama ta kallesu, sedai hassada amma ita kanta tasan Jalila ba laifi tayi gadon dangin mahaifinta sosai a kyau, kamanta daya da babanta, mahaifiyarta ma ba baya ba wajen kyau, Nana ma ba laifi tana ds kyau amma sam bata kai Jalila ba
"har kunfito?" "eh Maama zamu tafi" Nana ta bata amsa "to Allah ya kiyaye, kar kuyi dare ku dawo da wuri" Jalila tace Insha Allah " suna fitowa harabar gidan Driver su yake jira, suka bude mota suka shiga, suna tafe Nana tana ta musu hotuna, ana zuwa wani guri Jalila tace a tsaya zata karbi sako, ta fita ta karbo sakon tabude boot ta saka, sannan ta dawo mota tace a tafi, Nana tace" mekika karbone? "
" abune "" abu wane iri"
"kinji mace kin aikenine?" "a a ban aikeki ba jarababbiya" "eh naji jarababbiya" haka suka tafi suna fada
Suna zuwa gurin Nana ta bude mota ta fita yayinda Jalila ta kame a cikin mota taki fita
"fito mana" "yi gaba zan taho" Nana ta wuce cikin gurin.
Abunda ya daurewa Jeje kai be wuce ganin yan uwan Jalal dake ta zuwa ba, dukda matasane amma abun ya bashi mamaki, dole sukara shiri su saka ido sosai, saboda kar a samu matsala. koda Nana ta tafi Jalila tacewa driver
"manu dan Allah karkayi nisa akwai ajiyata a cikin motar nan anjima kadan zanzo in dauka"
"karkiji komai Uwadakina, ina nan ina jiranku harku gama"
Jalila ta bude motar ta fito seda ta karewa harabar gurin kallo, taga yanayin mutanen dasuke shiga suna fita, mutanen kirki dana banza, wasu daga cikin wanda tagani suna kama da mummy dan haka ta tabattar yan uwan su Jalal ne, dama Jalal sunada yan uwa haka, amma basa zuwa gidansu Jalal, gakuma yan iskan abokansa nan wanda da gani base an gayamaka ba kasan yan giya ne, kowa se hada2 yake, a hankali ta bude jakarta ta dakko katon glass baki tasa a idonta, tafara wannan tafiyarta ta me daukan hankali, hall din ya hadu yana da girma, kaikace biki ake ba birthday ba, an kawata gurin matuka guri ta samu a gefe ita ka dai ta zauna a wata kujera tana kallon kowa one by one, ta hangi table din da Ilham take ita da kawayenta su yaseera da wasu yan uwansu, se hotuna suke suna dariya, Hannah ta hango tasha kananan kaya tana up and down cikin maza ko kunya bataji, murmushi Jalila tayi a ranta tace "yakamata hanna su san juna itada Ilham" tanata kalle kallenta wani matashi yazo ya zauna a kujerar kusada Jalila, "sannu yan mata" banza tayi masa tama kara dauke kanta
"haba yazaki dauke kai haka, nazone in tayaki hira kawai kafin a fara, naga ke kadaice" juyowa tayi "to cemaka nayi na damu senayi hira da wanine" gani tayi yana dan kaama da Jalal, hakan yasa ta gane dan uwansane
"to in bakyason hirar ni inaso, muryarki da dadi gaskiya, gashi kinyimin kyau sosai" shiru takuma yi masa
Hannah ce tazo wucewa taji anata Ilham, da sauri ta dan tsaya ta juyo, amma setaga ba wadda take tunani bace, "may be sunan ne dai yazo daya"
Jalila gani tai wannan gayen ya cika mata kunne da surutu, dan haka ta mike ta bashi guri ta tafi gurin Nana, ta ajiyewa Nana jakarta "Nana ina zuwa dan Allah" daga haka ta tafi dan nesa dasu Ilham, Hannah ce takuma dawowa taji Ilham tana "kai wai ina yaya Jalal ya tsaya haka, by now yaci ace anfara fa, Yaya Jalal kenan, zuma seda wuta" Hannah tsayawa tayi cak ta dan dawo da baya tace
"dan Allah kece Ilham, kanwar Jalal fa" Ilham ta mata kallon up and down "yeah nice, kanwarsa kuma matar daze aura" Hannah tace "anya kuwa, last time kaman ba dake muka haduba"
"ke wai meye haka zakizo kinamin tambayoyi hakane, ke wace niban taba ganinki ba se yau, meye hakane"
"Hannah manyan mata, kuma me da'awar soyayya a gurin ABDUL JALAL, gaskiyarki wannan itace Ilham ba niba" Jalila tasa hannu ta cire glass din fuskar ta,
"yes itace Ilham nikuma Jalila" gaba daya suka tsaya suna kallon Jalila, suka ma rasa abun cewa
"dama ya dace kusan juna, Ilham ga Hannah, Hannah ga Ilham yanzu kusan juna, so u should count me out of your troubles, Ilham, Hanna, niba budurwar Jalal bace, bani da lokacin da zan bata akan soyayya da wani Jalal, dan haka idan kuna abunku to ku cire Jalila a ciki" tana gama fadin haka tai tafiyarta ta kyalesu, kallon kallo aka shigayi tsakanin Hannah da Ilham, wani shu'umin murmushi Hannah tayi, Ilham tace "ashe kece Hannah, ni na dauka zanga wata hamshakiyar mace meji da kanta, ashe ma karyar bariki ce kawai" Hannah ma tayi wata shu umar dariya sannan tace "ashe kece opponent dina ba waccan ba, thank God kece, bazam sha wahala ba, da waccan me siffar aljanunce da sena damu, dan ba karamin daukar hankali zatayi ba, amama me ban daukeki cikakkiyar mace ba ma balle in damu kaina, dan dake da namiji ba ku da banbanci" taana gama fadar haka ta wuce tabar Ilham,
Jalila kam tafita harabar gurin, tana waige2, tana tsaye taji ance Jeje da sauri ta waiga, tana ganinsa taga yaci sunan nasa jeje kai kace wani kasurgumin arne ne, gajeren wandone a jikinsa, da riga amless duk

Please Login or Register in order to submit comment