Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

meyafaru bane amma ni kaina nayi missing dinki"
"Wallahi kika kuma cemin Azumi tashi zanyi in tafiyata ya za ayi a samun siyama ki dinga wani cemin Azumi kamar wata tsohuwa"
"Yi hakuri aminiya siyama na dena"

"Kin temaki kanki, wato kikaje kano kika tare kin manta da batun haddar islamiyya, gashi baki ba da uzurinki ba kinsan malam nazeeru ba afuwa
Waima ya akayi kika dawo Ummi tace min se hutun school ya kare zaki dawo"

Jalila ta nisa
"Kinga yanzu bar batun malam Nazeeru nasan yadda zanyi dashi"
Jalila ta kwashe kaf abunda yafaru zamanta a kano ta gayawa siyama ciki hada dramar su da Jalal,
Jin siyama take kamar Yar uwata ta jini basa boyewa juna komai
Jalila tacigaba da cewa

"Siyama bazan kuma zuwa kano ba,"
Jalila ta fada in a serious tone

" aikuwa ke zuwa kano ya kama zaman Kaduna banaki bane"
Siyama ta bata amsa

"Azumi ki kiyayeni dagaske nake bani ba kano"

" kina kuma cemin Azumi zan dinga cemiki matar Jalal"

"Allah ya kiyaye, ya za ayi in gayamiki magana kina Neman jamin bala'i Dan giyane fa, naji bazan kuma cemiki Azumi ba amma meyasa kikace dole in koma kano"
"Yanzu a ce yaya Jawwad ne yake abinda Jalal yake kikaji abinda Ilham tace zuba ido zakiyi kenan??"

"Allah ya kiyaye Yaya na ba irinsa bane bahaka muke ba
Narasa dalilin dayasa ya mannewa Yaya Jawwad"

"Aminiya babu Wanda yafi karfin kaddara"

"Siyama abinda Jalal yake ba kaddara bane son zuciya ne".



Jalal ne kwance akan wani makeken gado ya tada kai da hannunsa yana ta baccinsa cikin nutsuwa fuskarsa tayi fes kaman Wanda yake jinya, gashi ya rame sosai
Wata matace da Wasu mutane a bayanta suka shigo dakin da Jalal yake kwance, suka zagaye gadon da yake duk sun rufe fuskokin, su matar tasaka kaya tundaga sama har kasa ta rufe ko ina da bakaken kaya
Hannunta ta mika baya daya daga cikin mutanen dasuka zo tare ya mikomata wata zukekiyar wuka se kyalli takeyi
Ta zo kan Jalal ta saita cikinshi da tsinin wukar nan ta daga wukar sama

Share please

More comments more typing....................

Proud of u my fans wannan page din barka da salla ne

๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ
๏ธ[8/31, 8:26 AM] Safiyya: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

_ABDUL JALAL_
(2020)

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 14

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680

I want comments not stickers or just thanks๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ข
Your comments give me courage

-my first Novel-

"Karki caka masa, dan Allah
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!!!"

Shine abinda Jalila tafada da karfi ta farka daga mummunan mafarkin da take Wanda ya kasance tsakiyar dare
Da gudu Ummi ta yanke sallar da take ta taho kan gadon ta dago Jalila
"Lafiya me yasameki Jalila,?"
"Bakomai Ummi mafarki nayi"
"Kinyi adduar kwanciya bacci?"
Gyada kai Jalila tayi alamar eh
"Alwala fa"
"Itama nayi Ummi"
"Jeki sake alwalar sekizo ki kwanta"
Mikewa Jalila tayi taje ta yo alwala ta dawo ta kwanta tayi shiru tana kuma tunanin mafarkin da tayi
A hankali Ummi ta zo ta rungume Jalila tana mata
addu a, amma har yanzu kirjin Jalila bugawa yakeyi da sauriยฒ
Washe gari da safe suna karyawa, amma hankalin Jalila yana kan mafarkin da tayi jiya Ummi ta lura da ita dan haka, ta yanke shawarar tambayar Jalila mafarkin da tayi take ihu cikin dare

"Jalila mafarkin me yasaki ihu cikin dare jiya"?
"Ba komai"
Jalila tabata amsa

"Kaman ya ba komai kin firgitani"
"Ummi ni dai nasan nayi mafarkin tsoro amma na manta me nagani"
Kallonta Ummi ta yi
"Baby kenan adinga addu'a dai"
"Inayi ai Ummi amma zan kara insha Allah"
"Yayi kyau kici abinci kidena wannan tunanin"
Gyada kai Jalila tayi ta Dan cakali abincin ta bari
Uniform din islamiyyarta ta dakko tana gogewa, amma duk kokarin ta, ta cigaba da harkokinta tana tuna mafarkin nan se gabanta yayi mummunar faduwa
"Subhanallah"
Shine abinda Jalila take fada in ta tuna mafarkin, haka ta karasa gugar tasaka uniform din islamiyya tana zaman jiran siyama ta karaso su tafi islamiyya
Qur'anin da Daddyn Jalal yabata ta je ta dakko tasamu guri tazauna tana kallonsa tana shafawa se jujjuya shi take a hannunta
Sallamar Siyama ta ji amma bats motsa daga inda take ba Siyama suka gaisa da Ummi a tsakar gida
"Ummi ina Jalilan take?"

"Tana cikin dakinta yau narasa meyake damunta yau tun safe tana daki"
"To Ummi bari ingani kinsan ta wani lokacin se a hankali"
"Aikam halin Jalila ai se hakuri"

Dakin Jalila ta shiga ta tarar da ita tana ta jujjuya Qur'ani a hannunta
"Aminiya lafiya dai yau kuwa,wannan Qur'anin fa me kyau, kice har babban guzuri kika taho mana da shi"

Ita dai Jalila ba tace mata komai ba ta mika mata
"Masha Allah gaskiya yayi kyau box din da yake ciki ma gwanin sha awa bari in sashi a Jaka mutafi da shi Islamiyya munyi sabon Al Qur'ani

"Bani"
Jalila tasaka hannu ta karbe Al Qur'anin daga hannunta Jalila

"wannan ba na zuwa islamiyya bane kallonsa kawai zan dinga yi"
"Kamar ya "?
" kamar yadda nagaya miki"
"Allah yabaki hakuri naga yau tambotsai kikeji"
Jalila bata kuma kulata ba ta dauki hijjabinta ta saka ta maida Qur'anin cikin cover dinsa ta adana shi
Suka fito
"Ummi zamu tafi"
Siyama tayi maganar tana risinawa
"To adawo lafiya Allah yayi Albarka"
"Ameen Ummi"
duk wannan maganar da ake Jalila batace uffan ba
Har sunkusa fita Ummi tace
"Ke madiga ina taki Jakar makarantar?"
"Ban gan taba sena dawo zan duba"
Tafada tana sunkuyar da kai
Girgiza kai kawai Ummi tayi sukuma suka tafi

Daga office dinsa ya dinga jiyo hayaniyar Jalila ta dawo daga ajin dake gaban office dinsa
Tsaki ya ja ya kalli dayan malamin
"Aifa bismillahi wannan baki abun maganar ta dawo yanzu bamu da sakat saboda surutun dalibai"
Daya malamin ne ya kalleshi
"Lallai kam malam naziru indai Jalilace baki abun magana, ga surutu ga Neman magana, inda take birgeni kwakwalwarta tana Ja sosai, kuma duk tsiwarta intai laifi akwai bada hakuri"

"Hmm kaidai bari kawai idan nafara lissafo maka halin yarinyar nan ai se dai addu'a"
Murmushi daya malamin yayi sukayi musabiha ya bar office din
Mamakine ya cika shi kodai kunnensa beji daiยฒ ba yaji ana Jalila ta dawo amma yaji ajin shiru kaman an cinyesu se Dan surutu da suke kasaยฒ
Har yayi gaba ya dawo ya leka Ajin aikuwa itance amma fuskarta Sam ba walwala ta koma gefe tayi shiru se Siyama dake gefenta tana mata magana
Kai tsaye ya dawo kofa ya shiga ajin gaba daya suka nutsu
"Baku San me yakawoku nan bane Ku dakko Qur'anin Ku kufara tilawa,"
Ya kai dubansa kan Jalila
"Ke yau kwananki kusan goma bakizo makaranta ba, kuma baki bada wani uzuri ba"
Siyama tai saurin cewa
"Malam Naziru nafa gaya maka.."
"Ke rufemin baki marasa da'a ina magana zaki katseni"

Ya maida dubansa ga Jalila
"in anjima zanzo karbar hadda duk na kwanna Goman nan sekin bani haddasu
Kukama Ku dakko Qur'anin Ku nace"
Kowacce kokarin dakko Qur'anin Sa yake banda Jalila wadda kamar an dasata
"Ke ina naki Al Qur'anin"?
Ya dakamata tsawa
Qur'anin hannun Siyama ta nuna masa
Ya kalli siyama " ke ina naki?"
Itama Qur'anin ta nuna masa "rainamin hankali zakuyi kenan?"

Fita yayi be dade ba se gashi da wata katuwar dorina yana zuwa ya fara takan Siyama ya zaneta sannan ya nufo inda Jalila take
Zumbur ta mike ta fara ja da baya
"Dawo nan ki tsaya, fara bani haddar yanzu zan karba"
Yafada yana muzurai yana nuna mata gabansa
"Ni wallahi banyi haddan nan ba kuma in kada keni da wannan bulalan suma zanyi"
"Ai ko mutuwa zakiyi yau sena zaneki Dan kun rainamin hankali wai Qur'anin Ku daya Ku biyu"
Aikuwa Jalila ta dage ta kwala ihu tare da fadin
"Malam babba kazo ka temakeni, danka ze kasheni, za a daki amanarka Dan Allah kazo"

Daga ajin da dattijon yake zaune yana biyawa dalibai karatu ya jiyo ihunta tana kiran sunansa
Malam babba shine mamallakin makarantar malam, Naziru kuma dansa ne dabasa jituwa da Jalila
Wataran ya daketa tayi suman karya, aka kaita Gida lokacin Abban su Jawwad yazo, hankalinsa ya tashi sosai yazo har makarantar ya samu malam babba akan dukan da akayiwa Jalila yayi yawa, malam babba yaita bashi hakuri, shine Abban Jawwad "yace malam ga yata nan Amana dan Allah a hannunka marainiya CE adinga hakuri da halinta"
shikuma yace ya karba, indai za a daketa har cikin zuciyarsa yakeji bayason kukanta
Itakuma Allah be hada jininta da malam Naziru ba, kusan kullum Seya nemi abinda zesa ya daketa

Tashi yayi da sauri ya taho ajin dayake jiyo ihunta yaganta ta makale a lungun ajin tanata kuka ga kuma malam Naziru a tsaye da bulala
"Naziru lafiya nakejin kukan 'yata"
Nan malam Naziru ya shiga gayamasa abunda akayi da Wanda ba ayiba
"To ina nema mata afuwa bana son ana samun ita kuka dukda Yar tawa tafiye Jan magana"

Gyada kai malam Naziru yayi ya fita daga ajin zuciyarsa fal bakin cikin rashin Zane yarinyar nan.
Malam babba ya hada litattafan makaranta yabawa Jalila sannan yace ze aikomata da Jakar makaranta

Itakam siyama har aka tashi daga Islamiyya kukan dukan da akayi mata take Dan tana tsoron bulala, mafi akasari in Jalila tai lefi akanta abun yake karewa.
Da aka tashi Har Gida Jalila ta raka siyama tana ta bata hakuri

Kwana biyu Jalila tacigaba da harkokinta hankalinta kwance amma data tuna mafarkin nan se ta ji jikinta yayi sanyi
Tana kwance a dakinta gidan bakowa tanata tunani bacci ya kwasheta Ummi bata nan ta tafi kasuwa

Jeje ne zaune yana ta busa shisha, shikuma Jalal yasaka Bluetooth a kunnensa ya jingina da kujerar da yake kai
Jeje yadan taba shi alamar yanason zeyi magana da shi cire Bluetooth din kunnensa yayi yana kallon Jeje alamun ina jinka
Jeje yai gyaran murya
"Man wai ya batun tafiyarmu Dubai ne naji ka shiru"

Lumshe ido Jalal yayi
"Tafiya tana nan daddy ya turomin kudi nayi arranging din next week ne insha Allah"

"That's good my man but a yanmatan nan baka ganin yakamata mu tafi da wasu abun zefi dadi inda mata a harkar"
Hade rai sosai Jalal yayi murya a kaushashe yace

"Amma kasan a tsarina babu mata ko? bana gayyatowa kaina ciwon kai, in kaga bazaka ba seda mata to kawai ka zauna, ba Y'ar Wanda zan dauka in tafi da ita"
Lallai gayen nan, amma a hankali da matan zamu kafa maka tarkon dabaka Isa ka tsallake ba, tarkon daza mu rikeka a wuya jeje yai maganar a zuciyarsa
A fili kuma yace
"As u wish my boss abar maganar mata mutafi kawai"
Jalal bekuma tanka masa ba Yakoma ya jingina da kujerar da yake

"Are u serious Jalal wai damaa dagaske kake tafiya Dubai zakayi, mahaifiyarka fa bata so mahaifinka ma ba a son ransa zaka tafi ba meyasa bazaka hakura ba? Haba Dan uwana kayi tunani mana"
Jawwad ya karasa maganar a sigar rarrashi
"Ina ruwana da rashin yaddata data yadda da karta yadda duk matsalarta ne, daddy kuma tunda ya yadda ya turamin kudin ai ya yadda kenan"

"Haba Jalal duk abunda kayi ba da yadda iyaye ba kosa albarkarsu ba karshen al'amarin lalacewa"
"Indai albarkarta ce banaso ta babana ta isheni"
JALAL yai maganar yana hade rai

A fusace Jawwad ya kalleshi
"JALAL uwa uwace komai lalacewarta balle babu lalacewa a iyaye meyasa kai baka yafiyane? Kamanta mana komai ya wuce hawayenta masifa ne a rayuwarka"

"Idan na tsallake nabar Nigeria seta manta dani kafin na dawo kaga ta huta ta dena hawayen"

"Haba Jalal mahaifiyarka CE fa meyasa kafiye taurin kai ne meyasa baka yafiyaa me"?

"Dole kace haka tunda ba kai kake irin rayuwar danake ba, ba kai ka samu kanka a halin da nake ciki ba, mutane na kyamarka shiyasa kake cewa in manta komai ya wuce,
Idan nabar kasar nan seta ganni zatayi kukan ai lokaciยฒ nazo inga daddy"
"Jalal anya Kasan soyayyar dake tsakanin d'a da uwa kuwa baka tunanin halin daza ta shiga in ka tafi?"
Jawwad ya fada yana kallon Jalal da yake shirya kayansa a trolley
Be dago kai ya kalleshi ba yabashi amsa
"Kai kasanta ita soyayyar d'a da uwar, gobe insha Allah zan bar kasar nan kudena ganina balle ranku ya cigaba da baci akaina"

Jalal ne da Jawwad ke zaune suna hira gwanin sha'awa sunayi suna dariya suna cin yayan itatuwa a wani lambu me matukar kyau da korayen bishiyu
Wani mutum ne ya zagayo ta bayan su Jalal ya rife fuskarsa ba a iya gane waye, yabawa Jalal wani abu, Jalal ya karbi abun yafito da shi ya dubi kirjin Jawwad ya zaro wata siririyar kibiya Yar Karama ya sokawa kirjin Jawwad din saitin zuciyarsa, nan take Jini ya balle, sekuma Jalal ya yadda kibiyar ya rungume Jawwad yana kuka, wannan matar ce ta rannan tazo tafara Jan Jalal,
Nan da nan gurin Yakoma baki bishiyoyin gurin suka bushe,
Ta dinga janshi zuwa wani katon rami ita da wani mutum
Jalal mikowa Jawwad hannu yake
"Dan uwa ka temakeni kar kabari sujani cikin Ramin nan"
Jawwad dafe da Inda Jalal ya sokamasa kibiya jini na zuba yake fadin
Bazan iyaba Dan uwa
Jalila!Jalila!!Jalila!!!
Kitema kawa Jalal karki bari su jashi cikin ramin nan

Siyama dake sallama a tsakar Gida ta jiyo kukan Jalila da Sauri ta karasa Inda take jin kukan nata
Tana kwance akan gadon Ummi ta hada gumi se kace tayi dambe da zaki ga hawaye a fuskarta,
se jujjuya kai take tana fadin

"A'a nima bazan iyaba Yaya Jawwad bazan iya temaka masaba nima zasu hada dani"

Subhanallah siyama tafada tare da jijjiga Jalila
A firgice Jalila ta farka daga mummunan mafarkin datake tana haki
"Jalila lafiyanki kuwa meyasameki? ina ummi?
Tun dazu na shigo nake sallama ba Wanda ya amsa me yasaki wannan kukan"
"Bakomai"
Tabawa siyama amsa

"Kamarya ba komai kalli fa yadda kika hada gumi ga kuka kinayi"
Siyama tafada tana nunata

Mikewa Jalila tayi ta tafi gaban mudubi
Ta kalli kanta taga yadda ta hada gumi ga hawaye, idonta har yayi ja kaman ta wani tana kuka
Wayarta ta ta dakko ta dawo inda ta tashi ta zauna
"Aminiya waime yake damunki ne akwai matsala ne?"
Girgiza mata kai Jalila tayi tana duba wayarta lamabar Yaya Jawwad tayi dialing bugu biyu ya daga sekuma tayi shiru tarasa mezata CE

Jalal ne ya katse shirun ta hanyar Sa wayar a hands free sannan ya yimata sallama
"Salamu alaikum warahmatullah sisyna yakike ya Ummi"
Ajiyar zuciya tayi

Alhamdilillah yana raye
"Me kikace?"
"Duk Muna lafiya ya maama da Nana"
"Muna lafiya sisyna, ya karatu"
"Yaya Jawwad"
Takira sunansa
"Na'am sisyna ya akayi?"
"Kana inane?"
"Akwai matsalane? yau weekends muna gida ina tare da yayanki Jalal ina ta fama dashi wai se ya tafi Dubai ya barni, in ya tafi kuma wai baze dawoba
Dan karamin tsaki Jalila tayi sannan tace
" to Yaya seme? kabarshi yaita tafiya daga nan har bangon duniya ya tafi ai gara hakama tunda baze karatu ba kaman sauran mutane ba seya tafi yayi abunda ya dace dashi kaima ka nutsu ka maida hankali akan naka karatun"

Cak ya tsaya da hada kayan dayake saboda yanajin duk abinda Jalila take fada saboda Jawwad a hands free yasaka wayar wannan Jarababbiyar yarinyar bazata fasa aibata shiba kenan

Shikam Jawwad saroro yayi yama rasa meze ce
Da kyar Jawwad ya hadiye yawu yayi gyaran murya

"Sisy bana gayamiki addu'arki Jalal yake bukata ba shima fa dan uwanki ne kidena fadan maganganu marasa dadi akansa kinji ko"
"To naji nadena ka gaida maama da Nana"
Haka dai suka gama wayar da Jalila
Jawwad ne ya kalli Jalal sannan ya kira sunansa da nufin yaba shi hakuri akan abinda Jalila take masa

Daga masa hannu Jalal yayi
" gara in bar muku kasar hankalinku ya kwanta hankalin kanwarka ya kwanta kar in lalata ka" yacigaba da abunda yake
"Jalal bahak.....
Daga masa hannu Jalal yayi
" no need to say anything "

"Aminiya wai bazaki gayamin meke faruwa ba"?
Siyama takuma tambayarta

" ke kin isheni nace miki ba komai amma kin isheni kibarni inji da abunda yake damuna!"
Jalila tayi Wa siyama maganar a hasale
Dan zaro ido siyama tayi

"Sorry Allah yabaki hakuri laifina ne danazo inda kike kuma na damu da damuwarki dama zuwa nayi in gayamiki dazu malam babba yace agayamiki akwai musabaka next week insha Allah"

Tana zuwa nan ta tashi tafita tabawa Jalila guri
Sam Jalila jinta take wani iri wannan wane irin mafarkai takeyine akan Jalal

A haka Ummi tadawo ta tarar da ita wani iri kaman Mara lafiya tana nuna mata abubuwan data siyo amma hankalinta baya kanta
"Baby waime ke damunkine?"
"Ummi marata ce take ciwo kuma na sha magani"
Dayake tana cikin period ta wayance da hakan

"Allah ya sawwake"
"Ameen"

Ummi ce tayi musu girkin dare
"Wai har yanzu marar ce tashi kici abinci ki kuma shan magani"
"Ummi na koshi da abincin"
"Baby kin fiye taurin kai shiyasa bana son rashin lafiyarki kin fiye gaddama tashi ko tea kisha"

Tea din kawai ta sha ta nemi guri ta nema ta kwanta amma fargabar yin baccin take saboda bata San mezata kuma gani ba
Se jujjuya mafarkan da tayi takeyi a zuciyarta dayake bacci barawone haka yayi awon gaba da ita dukda tarin fargabar da take ranta

"Karki bari Jalal yayi tafiyar nan in har yayi tafiyar nan rayuwarsa zata lalace fiye da da burinsu ze cika, Wanda abun ze iya shafar rayuwar Jawwad , ze lalace fiye da baya kiyi wani abu a kai Jalila kar ki bari Jalal ya tafi...........
TURKASHI

MORE COMMENTS MORE TYPING.........

YAYINDA COMMENTS DINKU YAYI KASA ZAN DENA TYPING KULLUM
KUNA COMMENTS INA JIN DADI INA MUKU TYPING
๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ
KUNA BARI INA LALACI
LOVE U ALL
โคโคโคโคโค

INA ALFAHARI DAKU MASOYA NA INA GODIYA
โคโคโค๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน



๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ
[8/31, 8:26 AM] Safiyya: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

_ABDUL JALAL_
(2020)

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 15

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

๐ŸŒนhttps://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

I want comments not stickers or just thanks๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ข
Your comments give me courage

Aimin afuwa the page is not edited
-my first Novel-


Ni bazan iyaba wallahi, idan suka kashe nifa, niba abunda zan iya yatafi ina ruwana

"Ke Jalila wai meye hakane
Ba magana nake miki ba"
Tashi Ummi tayi taje ta jijjigata a firgice ta tashi tana rarraba ido
"Wai meyake damunki a yan kwanakin nan kusan kullum sekin tayar min da hankali in dare yayi ko dai gamo kikayi da Aljanu"
"Niba wasu aljanu kawai tsorata nake"
Jalila tafada tana ya mutsa fuska
"Au tsoratanne kawai, to tunda kawai ne kika kuma min kuka a cikin bacci bulala zan saka in zaneki ta shi kije kiyo alwala kiyi salla ki dau Qurani ki karanta Allah yasa kina Azkar"
"Ummi bana salla"
"To jekiyo Alwala kibiya Wanda kika haddace"
Ba musu taje tayo alwala tazo taita bitar Qurani da ka bacci kam gagararta yayi se dai juyeยฒ

Yauma kamar kullum haka ta tashi jikinta kaman Mara lafiya ko abincin kirki takasa ci ga idonta daya kumbura saboda rashin bacci Ummi kallonta kawai take dakinta ta koma ta nemi guri ta kwanta tayi shiru

(Karki bari Jalal yayi tafiyar nan in har yayi tafiyar nan rayuwarsa zata lalace fiye da da burinsu ze cika, Wanda abun ze iya shafar rayuwar Jawwad , ze lalace fiye da baya kiyi wani abu a kai Jalila kar ki bari Jalal ya tafi!!!)
Tas kalaman da akayi mata a mafarki suke dawo mata kwakwalwarta Wanda yayi daiยฒ da wani mugun bugawa da zuciyarta tayi da karfi, kanta ya Sara
"Nashiga uku ni Jalila wannan wani irin bala'i ne meye hadina da wannan mutumin ake tsoratani akanshi wani tsautsayin ne ya kaini kano wanannan wani irin jarabane ana nema a haukatani why?"
Tafada tareda yin jifa da pillows din kan katifar ta yage bedsheet din kan gadon ta kifa kanta akan katifar

"Dan Allah ji abinda nake kamar mahaukaciya Ta Yaya zan hanashi tafiya ina nan yana can how? Be duba amincinsu da Yaya Jawwad yafasa tafiyar ba se ni da bama shiri to ni ya zanyi?
Kawai shirmen mafarkine kimanta kicigaba da harkokinki
Wani bangare na zuciyarta ya gayamata,
aikam ta yadda da abinda zuciyarta ta gayamata na ta manta shirmen mafarkine
Ga bacci a idonta kanta har ciwo yake amma bazata iya ba saboda fargabar inta kwanta me zata gani
Duk yadda taso ta manta takasa zuciyarta se bugawa take da sauriยฒ hankalinta yaki kwanciya
" Nashiga uku ni Jalila meke shirin faruwa dani haka ya zanyine?
Ko ingaya Ummi me
Karki kuskura hakan be dace ba mussaman intaji abinda yayi miki bazataji dadi ba, wani sashi na zuciyarta ya gargadeta
Siyama ce ta fadomata a rai, dan haka da sauri ta mike taje ta wanke fuskarta tasaka hijjabi ta fito, ta tarar da Ummi tana saka a dakinta
"Ummi inaso zanje gurin siyama"
"Adawo lafiya kigaidamin da ummanta saura ki dade inkika dade kin kori gaba kinsan halina"
Gyada kai Jalila tayi ta fita ta nufi hanyar gidansu siyama

Haka nan take tafiyar kaman wadda kwai ya fashewa a ciki, haka takarasa gidansu siyama.
makeken Gida ne Wanda yayi matukar haduwa da tsaruwa baban siyama yana da kudi sosai custom ne daga shi har Maman siyama mutane ne masu saukin kai kuma sun yaba da hankalin Jalila shiyasa suka kyale kawancen nasu
Siyama Sam bata da girman kai a makarantar boko suka hadu da Jalila tun primary suke tare makarantar 'yay'an masu kudi ita Jalila takeyi saboda Jajircewa da rikon amana na baban su Jawwad
Kawancensu har tsakanin iyayensu mata Wanda yakai har kasuwanci sukeyi tare, umman Siyama ta San komai game da rayuwar ummin Jalila ta dauketa kaman Yar uwatta ummin Jalila bata fiye shiga harkar mutane ba amma tana mu'amala sosai da umman Siyama

A tangamemen parlour Jalila ta tarar da Umma (mahaifiyar siyama)
"Hajiya Umma brk da rana"
"Anya Jalila zan amsa gaisuwar nan taki, kinyi tafiya ba sallama kin dawoma bakizo mun gaisa ba balle insa ran tsaraba to ni nayi fushi"
Umman tafada cikin zolaya
"Haba Umma tuba nake yau ai gani Nazo"
"Bawani kinzo dai gurin Siyama sekije tana daki,
Nikuma zamu gauraya dake naganki wani iri ko baki laafiya ne"?
"Hajiya Umma kenan, lafiyata kalau, bari inje gurin siyama, Ummi tana gaisheki "
"Ina amsawa"

Jalila ta mike ta haura sama dakin siyama
Siyama ce kwance akan katafaren gadonta tayi rub da ciki tana game a waya,
Sallama Jalila tayi, siyama ta amsamata ba tare data daga kai ta kalleta ba
"Aminiya gurinki nazo akwai matsala"
Banza siyama tayimata tacigaba da abinda take
"Aminiya magana fa nake kika min banza"
Jalila ta maimaita
"Ni a wa zan San matsalarki, ni na isa ko kin manta wulakancin dakika yimin A gidanku"
Siyama ta bata amsa ba tare da ta dago ba
"Ohh God am sorry aminiya lokacin ina cikin tashin hankaline, Dan Allah kimin afuwa ki saurareni, right now ma a cikin wata matsalar nake siyama jinake kaman zanyi hauka, yanzu haka zuciyata bikiji bugun data keyi ba"
A razane siyama ta mike zaune tana kallon Jalila
"Kaman Yaya? Meyafaru?"
Ajiyar zuciya Jalila tayi sannan ta labarta mata duk halin da ake ciki
"Ni yanzu babban tashin hankalina aminiya ni bansan ta Yaya zan hana shi tafiyar nan ba yana kano ina Kaduna,
Tunda na fara mafarkan nan bana nutsuwa se inji kaman zan haukace"
"Easy, don't said that again please karki kuma batun hauka
Kinga maganata ce fito dama nagaya miki zaman Kaduna bana kibane inkika temake shi kanki kikayiwa kamar kin temaki Jawwad ne"
"Kinga ni ba wannan surutun ba kigaya min mafita siyama kaina ya kulle"
"Aikuwa dole kibude shi, shi tunanin naki, yaya Jawwad zaki kira ki zigashi akan kar yabarshi ya tafi saboda besan meze faruba in ya tafi zuciyar Yaya Jawwad zzaki karya yadda zaki ingiza shi ya hana shi tafiya"
"Siyama bana tunanin hakan me yiwuwa

Please Login or Register in order to submit comment