Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mtseww, nii ban San meyake damuna ba Jawwad baya son giyar nan danake sha fa"
Jalila ta kalleshi
"Kai ni dalla ka isheni ka cikamin kunne, kayimin shiru, nina aikeka ka sha kalleka Dan Allah, mutum har mutum amma ba hankali, ko kunya bakaji kake shan giya kai ko tsoron Allah bakaji ma bana tunanin kayi sallar isha'i, kana kwance kana maye, kasa Yaya se wahala yake in bakayimin shiruba nida kaine"
Jalila se rashin M takewa Jalal shikam baya hayyacinsa, yacigaba da surutansa
"Ko wace kuma Hannah oho masa"
Wayar Jalal ce tafara ringing ta kalla sunan Hannah ta gani a kan screen din wayarsa,
"Hmm kishiyar Ilham ce Ashe"
Tayi banza da wayar takoma palour, wayarce ta cigaba da ringing ta cikawa Jalila kunne Dan haka ta mike ta koma bedroom din ta kai hannu ta daga wayar
"Dan Allah baiwar Allah kiyi hakuri, me wayar kin ganshi a kwance, tunda kika kira be dagaba ai seki hakura ko, saboda shirme a tsohon Daren nan haba, kinkira ba adagaba sekace mayya duk kincikamin kunne"
Jalila tai tsaki ta kashe wayar ta kai hannu zata aje wyar ya rike hannunta gam ya bude Jajayen idanuwansa fes akan JALILA
Kwalalo ido Jalila tayi ta firgita matuka
"Meye haka kacikamin hannuna"
Ko kyafta idonsa bayayi akanta gashi ya riketa gam ko motsa hannun bata iyawa, idonsa tsoror yake bata
"Na shiga uku nika cikani, dama ance watakila ka haukace"
Kara karfin rikon yayi mata
"Wai meye hakane"
Setaga hawaye na bin gefen idonsa can yayi wani yunkuri se yafara amai kumface kawai take fita daga bakinsa, yasaki hannun Jalila a hankali
Zare ido tayi dataga irin aman dayakeyi
"Nikam ina Yaya Jawwad ya tsaya haka"
Itakam Hannah mamakine ya cikata wace ta dauki wayar Jalal a Daren nan, OK ko Itace kanwar tasa da Jawwad yake fada, to me take masa a wannan lokacin haka?
"Tabdijan to wallahi da sake akwai matsala"
Jalila ta koma bakin kofa ta zuba masa ido Dan tarasa meya kamata tayi can jimawa Sega Jawwad ya dawo shida wani
"Sorry Jalila kinganni ban dawo da wuriba, seda naje Asibiti na dakko likitan"
"To gashi can dai wani irin amai yakeyi yana surutai"
Da sauri Jalal da likitan suka shiga cikin dakin
Likitan ya kalli bakin Jalal duk wannan kumfar fara
"Subhanallah" ya furta yasaka abu ya goge masa kumfar yayi masa wasu allurai
Jalal ya dinga aman abunda yaci
Likitan ya kalli Jawwad
"Jawwad Jalal wasu miyagun kwayoyi yasha Wanda besaba shan irinsu BA, suke nema suyi masa illa"
"Bayan giyar kuma hada kwayoyi"
Jalila tafada cikin mamaki
"To gashi nan dai, kuma da alama ya Dade beci abinci ba"
Likitan yabata amsa, girgiza kai kawai Jawwad yayi, Jalila ta koma palour
Shida likitan suka gyara gurinda Jalal yai aman suka canzamasa kaya zuwa Jallabiya
Kafar Jalal aka ciremasa kwalaben daya taka, sannan yasa masa drip, ya rubuta magunguna yacewa Jawwad da safe yaje ya siyo masa,
"Yaya ni Bacci nakeji seda safe"
"To baby mungode sosai, kiyi bacci me dadi"
"To Yaya kaima ka kwanta haka dare yayi"
Ya gyda mata kai likitanne ya kalli Jalila
"Baby ni baza ayimin sallama ba?"
Dan murmushi tayi
"Seda safe tafada a takaice"
Jawwad kam Dan hade rai yayi, ya kalli likitan "muje in maida kai"
"Jawwad dan Allah wannan babyn fa nifa na faller wallahi, Yar gayu da ita ga iyayi"
"Ina ruwanka da wacece, nifa banason irin wannan abun salis, muje in saukeka ni"
"Tuba nake sirikina amma nikam naga guri"
Fusata Jawwad yayi "kaga wuce muje"
Haka suka tafi ya maida doctor, se bayan karfe daya sannan Jawwad yasamu nutsuwa lokacin drip din jikin Jalal ya kare ya cire masa, sannan ya kwanta
Bayan sallar asuba Jalila take gayawa Nana a gidan Jalal ya kwana, yanata a man kwayoyin da yasha
"Tab to indai wannan ne sun saba, amma iya sanina baya shan miyagun kwayoyi, sedai giya da taba, watakila Suma yafara watsa abunsa wayasani, kice hadake akai jinya"
Nana tafada Dan Neman magana
"God forbid indai Dan ta shine, yaje ya karata ni Yaya Jawwad ne abun tausayi wallahi"
"Mutane dayawa na mamakin kaunar da sukewa Juna, Allah ne ya hada jininsu"
"Kuma a haka Aminiyarki take sonshi"?
" mhmm kema dai kyafada"
"Hakane, amma Nana Dan Allah wace Hannah"
"Hannah kuma? A ina take"
Se Jalila ta fuskanci Nana batasan zancenba Dan haka tace
"OK don't mind me kwanta kikoma baccinki, Dan nasan yanzu shiya dameki"
"Aikuwa kamar kuwa kinsani"
Jalila kam mikewa tayi ta tafi kitchen Dan sarrafa abunda za a bawa ciki, Jalila tana matukar son harkar girke²
Tunda sauran duhun asuba ta shiga kitchen zuwa bakwai da rabi ta kammala
A palour ta hadu da halima
"Anty leemat barka da safiya"
"Barka dai sayyada Jalila, naji kamshi yana tashi ba dai kingama girkin ba"
"Nagama, kina bacci ne shiyasa ban tasheki ba"
"Sannu da kokari, ke ba kyajin aiki Sam, amma tun asuba kika fara"
"Eh halima, wallahi kinga Jalal ne ba lafiya za a bashi magani da safe nasan Yaya Jawwad ni ze roka in hada musu breakfast, kinga gara ayi tunkafin yayi maganaa"
"Gaskiya kam, bari inje in karasa, aikin da ya rage"
Zuwan Jalila gidan nan ba karamin amfani yake musu ba Sam batada kyuya, ba ta San kazanta Sam, shiyasa Jawwad yake jin dadin sakata aiki ba kyuya, amma Nana yanzu zata bata rai tana tura baki, ga son jiki a cikin Nana, kuma Maama take biyemata
Ta hado kayan Abincin ta kai part din Jawwad, ta tarar yana zaune a palour da Azkar a hannunsa, sallama datayine yasashi dagowa
Murmushinsa ya fadada
"Sannu da kokari baby, yanzu nake tunanin yaza ayi da breakfast, naga jiya baki kwanta da wuri ba kar in takura miki, nagode da kulawar da kike bamu, sannu da kokari"
Karasawa tayi parlour ta ajiye kayan abincin ta kalleshi
"Barka da safiya, Dan uwa rabin jiki,"
"Au bazaki amsa sannun nawa ba"
"Ni lafiyata kalau, wancan mutumin na cikin dakinka zakayiwa sannu, shine Mara lafiya"
"Kinganki baby, Jalal dinne mutumi ko? In yajiki ba ruwana, kinsan boss din ba wasa"
"Hmmm lallai boss naga alama"
Sukayi dariya a tare JAWWAD yace
"Jikin nasa da sauki, ya tashi tun dazu yanzuma wanka yakeyi"
"To Allah ya sawwake"
"Ameen baby"
Kallonsa Jalila tayi sannan tace
"Dan uwana"
"Na am kanwata"
"Bakayi bacci sosai ba idonka ya nuna"
"Kema bakiyi bacci ba gashi kuma nasan kin gaji"
"Ni bangajiba"
"Dagaske"
"Eh mana, kasan wani abu"
"A a baby sekin fada"
"Yayana kaina mussamanne a cikin mutane, halinka halin Abba, kanada kirki yayana, Allah yaabamu itaku"
"Baby ni banga wani kirki danake dashi ba, kinfini kirki baby, sedai ince Allah yabamu itaku"
Zumbura baki Jalila tayi
"Nida ake cemin masifaffiya, uwar Neman magana,"
Dariya Jawwad yake sosai
"Wayagaya miki haka"?
Bude kofar bedroom din Jalal yayi ya fito yana dingisa kafarsa Jallabiyar Jawwad ce a jikinsa tayi masa kyau sedai fuskarsa ta rame
Karasowa yayi ya zauna a kusa da Jawwad
"Sannu Jalal ya jikin naka?"
Jawwad yafada cikin damuwa
"Da sauki, Nagode Jawwad"
Jalal yafada a hankali
"Kasan zamuyi fada ko tom yanzu ga breakfast baby ta kawo, ka karya se inje in gayawa mummy kadawo daga nan in siyo maka magani"
Gyada masa kai kawai Jalal yayi
"Baby bakiwa Jalal ya jiki ba"
"To ai naga ya warke tunda gashinan da kafarsa"
"Jalila sarkin magana yanzu dai jeki kawo mana ruwan dumi Wanda za a gasa masa kafarsa"
"To" ta mike tabar parlour, Jawwad yahada masa breakfast din sannan ya mike "bari inje in siyo maganin, in ta kawo ruwan dumin in bazaka iya gasawa ba kabari in dawo"
Jinjina kai Jalal yayi, har Jawwad ya nufi hanyar fita ya tsaya ya waigo
"Yawwa idan na dawo kuma zaka gayamin meyasa ka fasa kwalabe ka taka seka gayamin meyake damunka"
Still dai bece komai ba
Jawwad seda yaje yagayawa mummy yaga Jalal yanzu haka ma yana gidansu, amma bashi da lafiya
Mummy taita godiya tana sawa Jawwad albarka, Ilham kuwa najin haka ta gashi ta tafi gidansu Nana domin ganin Jalal, Jawwad kuma yatafi karbo magun gunan
Jalila ta kawo ruwan zafi a flask tai sallama amma yamata shiru tazo ta dire flask dina gefen Jalal
"Wai ba nace ka dinga amsa sallama ba,
Gashi nan ruwan zafine in kaga dama ka dumama ka gasa kafar taka in baka ga damaba ka zuba a haka" har zata fita dawo ta tsaya a gaban Jalal
"Saboda wauta waya gaya maka in abu na damun mutum haka akeyi kafasa kwalabe kabi ta kai, kuma kaje ka sha kwayoyi, kakusa kashe kanka daka mutu haka zaka farka a kabari
Ga laifin sabawa iyaye, ga shan giya, ga kashe kanka dakayi da abun yamaka yawa, in abu yana damun mutum a zuciyarsa addu a yakeyi ya koma ga Allah, ba ya aikata wannan shirmen da kakeyiba, duk Wanda be kiyaye salollinsa akan lokaciba haka kunci zeta damun rayuwarsa"
Yana jinta ya cigaba da cin Abincinsa dukda bawani ci yakeba cakala kawai yake, yana tausayawa ranar daze hukunta Jalila,
se yanzu ta kai duba ga cin abincin dayakeyi, da hannun hagu yakecin Abincin
"Subhanallah Kaikam komai naka na dabanne, komai naka ba irin na mutane ba"
Tasa hannu ta karbe cokalin hannunsa daga hannun hagu ta zira masa a hannun dama
"Shedan ne yake cin Abinci da hannun hagu, Allah yasa kayi bisimillah kan kafara cin abincin"
Dago idonsa yayi yasaka a cikin na Jalila
"Kin manta waye Jalal ko?"
"Eh namanta seka tunamin"
Ilham ce ta shigo palourn ba ko sallama a tare suka waigo suka kalli Ilham
Ilham ce tayi mutuwar tsaye ganin Jalila a tsaye a gaban Jalal shikuma yana kallonta ga abinci agabansa kamar wasu masoya
Watakilama a baki take bashi abincin wani sashi na Zuciyarta ya zigata
"Mezan gani haka? Yaya Jalal menayimaka haka, kake kokarin cin amanata wannan itace sakamakon soyayyar dana dau shekaru inamaka, lokaci daya kayimin haka dama abunda na Dade INA zargine yau Allah ya nunamin"
Saroro Jalila tayi tana kallonta
Ilham ta dawo da idonta kan Jalila
"Munafuka kina cemin Yar wahala Ashe kece babbar Yar wahala, Ashe hasashena ya tabbata son Jalal kike, to wallahi baki isaba kinyi kadan kiyi takara dani akan abunda nakeso bans.....
" enough malama karkiga nayi miki shiru kicigaba da zagina, mezanso anan" ta nuna Jalal
"Ni abu na kawo nake masa magana akan abunda ya aikatawa kansa banda haka ni babu abinda ze hadani da shi"
Shidai Jalal bece musu uffan ba sema mamakin hakikancewa da Ilham take, yakeyi
"Karya kike wallahi ko duk jikina kunne ne bazan yaddaba kuma wallahi Jalila sekinyi danasanin abunda kikayimin, sena baki mamaki
" ya isheki malama"
Jalila ta karaso gaban Ilham "bude idonki da kyau, ki bude kwakwalwarki kiga da wacce kikeyi, inkin manta bari in tuna miki Jalila ce dawo hayyacinki, Dan kinga ina lallabaki ba amin hauka wallahi yanzun nan zan saukemiki abunda yake damunki
Me akai akayi Jalal meye abinso a tareda Jalal wannan makakken Mara tarbiyya, shi kike nufi Jalila taso, ko ta nuna a matsayin uban yayanta, a tunaninki zan tsaya ina daga murya saboda shi
Yadda yake a maken nan ai se makakkiya Yar uwarsa, badai Jalila ba ni mutumin arziki zan aura Dan babu uban me hankalin daze bawa wannan yarsa a haka
Kema da kike sonnashi kinada manufar hakan badan hakaba yadda yake wulakantashi yaci ace kin hakura useless and hopeless creatures dagake harshi"
Tirkashi

Share please
More comments more typing......................
Ina alfahari daku a kullum masoyana da masuyimin addu a
Ina godiya me tarinyawa inajin daddin comments dinku❤❤❤

SANARWA!!!
wasu suna tambayata ko nayi joining wata kungiyane na online writers
Gaskiya ni banyi joining kowace kungiya ba, kamar yadda kuke gani wannan shine Novel dina na farko, kuma basirata ce nake amfani gurin nishadantar daku tareda aikawa da wasu sakonni, babu wata ko wani marubuci dayake bani gudunmuwa
Dafatan masu tambaya kun gamsu
Game gyara, comments, tambaya ko korafi, akwai lamabata danake sakawa a farkon kowane page a tuntubeni ta wannan lambar nagode
Taku har kullum Yar babanta(daddy's girl)


🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
[8/31, 8:30 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_
(2020)

_ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 34

PART 1
Share please

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa
ABDUL JALAL NOVEL FANS
Love u all guys ❤❤❤❤❤

-MY FIRST NOVEL-

Ja da baya ta dingayi yana Binta, har seda ta kai karshen bango sannan ta tsaya tana zazzare ido
"Kingama gudun?"
Saboda karfin hali irin na Jalila ta dubeshi
"Wallahi kasake ka karaso inda nake sena maka Illa, akan me baza a fadi gaskiya ba, ai duk abunda nake fada ba karya nayimaka ba haka kake"
Daka mata tsawa yayi, Wanda yasa taji hanjin cikinta sun nannade guri daya
"Shut up, akwai wata illa dazakiyimn Wanda yafi miyagun maganganun da kikeyimin, ke badan darajar Jawwad ba da tuni na dade da kakkaryaki na karya banza"
Dagowa Jalila tayi da sauri ta kalleshi,
"Eh in karya banza mana, in ban mantaba a wancan karon nagaya miki ba ruwanki dani kifita a sabgata kome nake aikatawa babu ruwanki, meyasa kike da taurin kai da shishshigi,?
Dakamata tsawa ya kumayi ba tambayarki nakeba
Banza tai masa ta dauke kanta
" kaga ni ban guri in wuce"
Ba musu yabata hanya, ta sa kai zata wuce cikin zafin nama yasa hannunsa yakamo hannunta guda daya, yai masa wata muguwar murdawa, Wanda in yakuma murdawa ze iya ballata
Bata San lokacin datayi wani uban zilloba ta fasa kara
Ya kalleta "da zafine?"
Kasa magana tayi se wani uban fitsari dataji ya matsota, gashi ko kwakwakwaran motsi takasa balle ta kwace hannunta
Be saketa ba, da daya hannun nasa yasaka yakamo kunnenta, cike da mugunta ya murda iya karfinsa, wannan karon batayi ihunba sedai taji kaman fitsarin yafara fitowa, Allah ya temaketa hawaye yafara zubowa daga idonta, yana daf da ita sosai Dan suna iya jin numfashin juna, ya Dan tsura mata ido sannan yace
"Nikike cewa makakke ko? Kuma Useless and hopeless creature ko, ke gaki wadda ta haifowa duniya rashin kunya, daga yau in kinga Jalal, kikuma kallon ko inda nake sena yi maganinki
Hada cewa kinfi karfin makakke irina, ke meye abunso a gurinki,, yana ina wata mummuna dake, banda rashin mutunci da rashin kunya baki iya komaiba"
Motsa baki take, tanaso tayi magana amma takasa
Har yanzu be saketa ba, yadan kalleta
"Ko kinada maganane"?
Girgiza kai tayi, fuskarta tayi jajawur, se ruwan hawaye dayake zuba wani nabin wani,"
Da kyar ta tattaro kalaman dazata fada
"N..Ni kasakeni, zan karye fa"
Yadda tayi maganar cikin kuka da kuma shagwaba, seyaji jikinsa yayi wani iri
"Au bakinki be mutu bako" yafara a hankali
Yasa kafarsa ya take mata yatsun kafarta
"Wayyo Allah Ummi, ze kasheni, Allah ka temakeni"
Yadda taketa kuka gwanin ban tausayi, Dan zuwa yanzu ji take kamar hannunta ya karye, sannan ta saddakar ya cire mata kunne, ga yatsun kafafuwanta dake wani zugi, kunenta yafara saki sannan yacika mata hannunta
Daya hannun tasaka ta rike hannun dayayiwa muguntar danji take kamar ya karye,
Dan kallonta yayi kamar yayi dariya amma ya dake
"Gobema kikuma sena tabbatar miki ni makakke ne, da giya naso nabaki kisha senaga bake yakamata in bawaba Jawwad zan bawa, in yasha kaman kinsha ne, stupid girl, tafi kibani guri"
Dukda haka be ishi Jalal ba Dan Sam be huce ba akan abubuwan data keyi masa, seda yamata kyakyawan rankwashi a tsakiyar kanta, aikuwa nan take ta tsuguna kasa ta fashe da kuka,
Shikuma yakoma kan kujerar da yataso yai zamansa yacigaba da abunda yake,
Kuka take sosai saboda batason atabamata kai ko kitso bata sonyi setace zafi yake mata, balle wannan katon ya rankwasheta, kuka take sosai hada sheshsheka
"Idan baki tashi kinbar dakin nan ba nazo gurin nan, sena danneki na baki giya, and I mean it"
Bashiri ta mike ta nufi hanyar fita, tana Jan kafa seda ta bude kofar, ta waigo ta kalleshi,
"Allah yasakamin wallahi, mugu kawai, kuma wallahi niba mummuna baceba,"
Shiru yayi mata, "bazata iya yin shiruba, bakinta baze mutu ba"
Tsayawa tayi ta share hawayenta daga waje Dan gujewa tambayoyim Nana, tana daf da shiga cikin gida Jawwad suka karaso shida doctor salis
"Munzo a dai² Jawwad waccan ba mutuniyar bace?"
Doctor salis yai maganar yana nunawa Jawwad Jalila"
Banza Jawwad yai masa yanemi guri yayi parking, Jalila tana kallonsu amma bata tsayaba tayi cikin gida, Allah ya temaketa bakowa a parlour tashiga dakinsu ta tarar halima tana ninkewa Nana kayan sawarta
"Halima ina Nana"?
" hajiyace ta kirata,afiya kuwa"
"Lafiya kalau"
Jalila ta shige toilet Dan kar halima ta dameta kunnenta yayi Ja ga hannunta da ya sage ji take kamar banata ba
Gaskiya Jalal azzalumine, ya iya salon mugunta, babban abunda ya dameta wannan rankwashi da yayi mata Dan tunda yayi mata take jin Jiri har yanzu, kanta har yafara ciwo, lallabawa tayi ta watsa ruwa, ta wanke fuskarta tayi alwala Dan magariba ta gabato sannan ta fito ta canza kaya, bata iya amfani sosai da hannun da Jalal ya murda mata, guri daya takoma ta dunkule lokaci² tana share hawaye
Nana tazo ta sameta a haka
"Lafiya kuwa?, daga zuwa duba Yaya Jawwad kinzauna"
"Naje baya nan yanzun nan ya dawo"
Jalila tabata amsa a takaice
"Wai meya sameki naga yanayinki ya canza?"
"Kainane yake ciwo"
"Eyyah sannu inada paracetamol inkinyi salla seki sha"
Jalila ta gyada mata kai, Nana kuma tayi waje
"Azzalumin banza wainice mummuna makaryaci kawai, wallahi ko makaho yasan niba mummuna bace"
Jalila taita mita tana kunkuni,

Doctor salis ya duba kafar Jalal yace masa babu sauran kwalba a ciki, Dan haka acigaba da gasa kafar da ruwan dumi yana shan magunguna zata warke gaba daya insha Allah
"To mungode sosai salis"
Jawwad yafada yana dafa salis, Dan ture hannunsa salis yayi, ya kalli Jalal
"Jalal a gaskiya Jawwad bashi da kirki, har innemi alfarma a gurinsa yakasa yimin"
Kallonsa Jalal yayi
"Anya zan yadda Dan uwana bashi da kirki, amma me yayi maka?"
"Wai ace inga kanwarsa ince inaso ya hademin rai, yace baze baniba"
Dan murmushi Jalal yayi, yayinda Jawwad yakuma hade rai, Jalal yace wace yarinyarce
"Wadda mukazo muka tarar da ita a gurinka ranar dabaka da lafiya, wata me iyayi, baby sunanta kome? Nidai kaman haka naji Jawwad yana cemata, ranar tana nan har karfe daya, seda kayi bacci Jawwad yatafi maidani sannan ta koma cikin Gida, yau muna shigowa na hangeta INA yiwa Jawwad maganarta amma ya shareni"
Kallon Jawwad Jalal yayi, aransa yace wannan Mara kunyar, sannan a fili yace
"Ba ruwana kaida shi, in yabaka shikenan, ina maka murna"
Doctor salis yadan bude baki
"Au hakaama zakace, bazaka tayani lallabashi ba"
"Niba ruwana"
Jawwad mikewa yayi
"In kungama ni natafi masallaci"

Akayi sallar magariba, da kyar Jalila ta mike tayi salla, tana idarwa ta zube a gurin saboda azababben ciwon dataji kanta yanayi,
Nana takuma shigowa ta tarar Da Jalila ta dunkule akan dadduma, durkusawa Nana tayi ta dafata
"Jalila har yanzu kanne yake miki ciwo"
Jinjina kai kawai Jalila tayi, mikewa Nana tayi ta dakko mata magani ta kawo mata, Jalila ta kalli maganin
"Nana ki bar maganin nan, ni banaso"
"Saboda me haka zaki zauna da ciwo"
"Kibari kawai ze dena, idan na sha maganin nan amai zanyi"
"Ohh my God, sannu amma kina cuta bazaki sha magani ba"?
Har wajen isha doctor salis yana gidan suna hira jefi², ya zauna ne koda Allah zesa yaga Jalila amma shiru be ganta ba,
Halima tayi sallama, ta kawo musu abinci, Jawwad ya kalli Halima yace
" Halima ina Jalila ne?"
"Bata jin dadine, ta kwanta nikadai nayi girki yau"
"Subhanallahi me yasameta haka"
Jawwad yafada a Dan tsorace
Halima tace "Naji tacewa Nana kanta yana ciwo"
"Ta sha magani ne"?
"Wallahi ban saniba"
"OK jeki, ki kirawomin ita, inzata iya zuwa, tunda salis be tafiba seya dubata"
"To bari inje"
Ta mike ta koma cikin gida, Jalal yana jinsu bece komaiba,
Doctor salis ya kalli JALAL
"Wace kuma JALILA, naga Dan uwanka ya damu, nidai nasan Nanace kawai kanwarsa"
"Kabari ta zo sekaga wace"
Jalal yabashi amsa
Halima ta koma cikin Gida, ta tarar da Nana tana bawa Jalila tea,
"Jalila yayanku yace kije likita yana nan ya dubaki"
Nana ta kalli halima
"Daga zuwa kai abinci Harkin gaya masa"
"A a tambayata yayi"
"To jeki angode"
Seda Jalila tagama shan tea sannan ta kama hannun Jalila suka fito
Suna daf da Barin palourn Maama ta hangosu
"Me Nana INA zakuje haka"
"Jalila CE bats da lafiya , shine Yaya JAWWAD ne yace taje doctor salis yazo se yadubata
" Allah ya sawwake"
Shine abunda Maama tace tashige kitchen, itakuma Nana suka fito
Nana ce tayi sallama, suka amsa
Jawwad ya mike da sauri,
"Subhanallah baby, abin har ya kai haka, sannu"
Jin ance baby yasa doctor salis saurin waigowa
Jalilace fuskarta duk tayi ja hawayene kawai ke fita daga idonta
"Subhanallah Ashe babynmuce ba lafiya"
Doctor salis yafada yana mikewa tsaye
Guri tasamu ta zauna,Nana ta zauna a kusa da ita
Nana takalli Jalal
"Yaya Jalal ina wuni"
"Lafiya sannu"
Hada ido sukayi da Jalila ta galla masa harara, kawai se yayi murmushi yacigaba da latsa wayarsa
Jawwad se jera mata sannu yake
Doctor salis ya kalleta
"Sannu baby dama sunanki Jalila, a very sweet name"
Shiru Jalila tayi masa ta kwantar da kanta akan cinyar Nana
Jawwad ya hade rai
"Kaga cewa nayi ka dubata ba ka dinga yimata shirme ba, in bazaka dubataba zan dauketa mutafi Asibiti"
"To ai dubatan zanyi, kake min masifa"
Doctor salis yakuma kallon Jalila
"Baby kidena kukan mana, kinfiye shagwaba in mutum bashi da lafiya ba kuka akeba,
Yaushe kan yafara miki ciwo?"
"Dazune" tafada a kasan makoshinta
Nana ce tayi yinkurin dagota tareda cewa
"Jalila ki tashi kiyi masa bayani, bayajinki fa"
Jalila ji tayi Nana ta fama mata hannunta da Jalal ya murda da sauri ta furta
"Wayyo Allah Nana hannuna"
Jawwad yakuma rudewa
"Baby mekuma yasamu hannun naki"
Jalal ta kalla, amma shi ya maida hankalinsa kan wayarsa, shi yadda Jawwad ya rudene yake bashi haushi
Wani hawayen takaicine ya zubo mata
"Bigewa nayi da kofan toilet"
"Gaskiya zanyi fama, baby haka kike shagwababbiya komai kuka"
Doctor salis yai maganar cikin zolaya
Wani mugun kallo Jalila tayi masa cikin tsiwa tace
"Sunana Jalila karka kuma cemin baby"
"To yi hakuri na dena, yanzu inane yake miki ciwo"?
Murmushi Jalal yai a ransa yace indai wannan yarinyar ce kacigaba dayimata shishshigi, ba karamin aikinta bane ta zageka
Doctor salis yagama yimata tambayoyin daze mata yace a Alluran dayayiwa Jalal akwai guda daya da ze mata sekuma magani daze bata
Zumbur ta mike zaune
" Allura kuma, Yaya Jawwad ina tsoron Allura,"
"Yi hakuri a hankali zeyimiki"
Shidai doctor salis wannan shagwabar ta Jalila birgeshi yake
Nana tace
"To ai maganinma ba sha kike ba gara ayi miki allurar"
Aka zuko Allura, Jalila tace sedai ayi mata a hannu, salis yace ta miko hannun, ta mika masa sannan tace
"A hankali Dan Allah"
"To shikenan a hankali zanyi miki"
Ta mika masa hannun, da kyar akayi allurar nan tana ta kuka,
Shikam goga ko uffan bece musuba dayaga suna biye mata haushi ya isheshi ya tashi yabar musu dakin
Salis yace allurar da yayiwa Jalila ta isa sedai in ciwon kan yaci gaba ai masa magana
Nana takama hannun Jalila suka koma cikin Gida a zaune tayi sallar isha'i saboda ciwon da kan yake mata tana idarwa ko canza kaya batayiba ta haye gado takama baccin wahala, Dan ta manta da batun duba Jarrabawa
(Gaskiya Jalal ya iya rankwashi,)
Da safe bayan tayi sallar asuba takoma baccinta, ranar ko tsinke bata dauke a gidanba balle tayi musu girki
Aikuwa dai Abincin yau da banbanci don Sam be kai dadin na Jalila ba
Har LA asar Jalila bata fitoba, sedai Yaya Jawwad har daki yazo ya dubata ya tarar tana bacci
Salis yakira Jawwad a waya ya tambayi ya jikin Jalila, Jawwad yace masa da sauki,
"Jawwad Dan Allah ka hadani da baby mana in mata ya jiki,"
Jawwad kashe wayarsa yayi, yana mita
Jalila tana daki da yamma, taji hayaniya a harabar gidan, Dan haka tafito dama wunin ranar bata fito ba, Abbane ya dawo daga lagos, ya canzawa Jawwad dankareriyar mota, duk anje an kewaye motar, yayinda Jalal ya kame a cikin motar sekace tasa
Murmushi Jalila tayi Abba sannu da zuwa gaba daya suka waigo suka kalleta, ta Dan rame sosai, idonta yayi wani iri
Abba ya kalleta
"Baby meyafaru ko bakida lafiya ne?"
"Lafiyata kalau bacci nayi"
Nana tai saurin cewa
"A a Abba batajin dadine"
"Eyya Nagani fuskanta ya nuna"
"Abba ciwon kaine fa kuma na warke"
Takalli motar
"Masha Allah, Abba mota tayi kyau Allah yasaka maka da mafificin alkhairi, Allah yakara arziki, amma wa aka saiwa motar naga me motar daban Wanda ya kame a cikin motar daban"
"Lallai yarinyar nan har yanzu bakinta be mutuba ga muryarta har ta dashe saboda kuka"
Jalal yai maganar a

Please Login or Register in order to submit comment