Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jalal,
'me yasa kika rikeni kika hanani daukar mataki akanta yafada a fili Dan karamin flower base din dake kan side bed dinsa ya dauka yayi jifa dashi yana huci,

"Waima Yar uban waye daga ina take"
Kaman yataba ganinta amma yamanta a ina ne

wayarsa CE tafara ringing, bros jawwad ne yafito akan screen din wayarsa, yadaga wayar yakara a kunnensa, "
"Dan uwana meyasameka tun dazu nake nemanka kazo ka karbi ajiyarka,
Wai yanaji kanata hucine me yafarune,"
"bari bros bakomai zan fitane inna dawo zamuyi magana wata Yar iskar yarinyace ta zageni kuma idona idonta sena lahira yafita jin dadi" JALAL yayi maganar a hasale,

"Subhanallah haba Dan uwana ya kake fadin haka kaifa me hakurine fushi banakabane nasan maybe wani Abun kayi mataa kamanta da ita kawai yanzu dai kana ina"

"Bazan mantaba din wallahi sena koya mata hankali" cewar JALAL

"Easy bross karkayi fushi Manzon Allah salallahu"

"...........alaihi wassalam" Jalal yakarasa masa, "zaka fara Toni fita zanyi semun hadu da anyi magana sekace mutum yayi hakuri ka dauka kowa irin Kane"

"Dan uwana ina maka nasiha kaji tsoron Allah Dan an bata maka rai kar in kafita kasha giya Dan Allah kar kasha giya koka aikata abinda ba shikenanba babu abinda zata qara maka se bacin rai,
garaka... .."

kitt JALAL ya kashe wayar in yatsaya cigaba da sauraron JAWWAD ze kuma bata masa rai,

Lamabar Jeje ya nemo bugu biyu ya dauka ya kara wayar a kunnensa
"Man where are u now?" Banji me akace daga daya bangarenba
"OK I will be there"
Ya kashe wayar yafice daga gidan

Da gudu ta karasa cikin gidan sukayi karo da Abba a hanyar shiga gidan tanata haki kaman tayi wrestling,
"Meyakoromin ke haka diya tagari"
"Am..mmm... Maama CE ta aikemu shine nayo gaba wani kare yabiyoni tafada tana maida numfashi"

"Shine kike wannan gudun in kika fadi fa matsoraciya kawai ba a yiwa kare gudu inbahakaba wataran seya cijeki" yafada cikin wasa
"Tunda kin shigo Gida seki tafi a hankali"
"To nadena abbana"
"Good girl, kodayake yanzu tazama lady"
Murmushi tayi tashige ciki kai tsaye ta tafi dakinsu tana kuma sauke numfashi

"Tab daya kamani dana gane kuskurena yadda idonsa yayi ze iya sumar dani fa"
Tayi maganar a zuciyarta
wayarta ta laluba tafara trying lambar Ummi amma taki shiga har tagaji ta aje wayar,
ta mike tashiga bandaki tayo Alwala tafara gabatar da sallar isha'i ta idar da sallah ta canza kaya zuwa na bacci ta nashirin kwanciya Sega Nana tashigo

"Se yanzu?"
"Eh nai ta zaman jiranki baki dawoba nagaji shine na karbi sakon na taho, dama atamfofine maama zata Cuba"
"Hmm yayi kyau" cewar Jalila.

Can na hango shi yana zaune kan wasu fararen kujeru matasa ne maza da mata suke kaiwa suna komowa daganinsu kaga yayan Hutu masu karancin tarbiyya,
fuskar nan tasa a tsuke kansa dauke da wani irin aski ga Suma fal akansa se cika yake yana batsewa da anjima yadan ja tsaki.

"Man what's actually wrong with u tun dazu bakacemin komai ba what's happening"

Jalal ya danja karamin tsaki kawai se yakasa gayawa jeje abinda yabata masa rai

"Just forget"
Shine abinda ya iya cewa ransa fal takaici
"Anyway since u decide not to share ur problem with me Dan ja kaya at least it will help u reduce ur temper"

Ya fada tare da tsiyaya masa Wayne a cup ya mikamasa ya Sa hannu ya dauka ya shanye ya kara masa yakuma shanyewa yana shirin kuma zuba masane

"DAN UWANA KAJI TSORON ALLAH DUK INDA ZAKAJE KAR KASHA GIYA KO KA AIKATA ABU MARA KYAU BA ABUNDA ZATA KARA MAKA SE BACIN RAI"

Kalaman Jawwad ne suke dawo masa se yaji haka nan jikinsa ya danyi sanyi.

Hannu yadagawa jeje yacemasa"enough "
"Kana nufin ta isheka" cewar jeje"
"Yeah" yafada a takaice

"Am going " Jalal yafada yana duba agogon hannunsa
"But man kaman akwai abunda yake damunka"

"Bakomai ni na wuce Gida"
Yafice daga gurin.

"Nana dakika baro gidansu jalal kinganshi kafin kifito"

"Aa nadai ji fitarsa a mota amma bamu hadu ba, akwai matsala ne"
"Aa babu koma".

***********************************
Washegari da safe Jawwad ya shiga gidansu Jalal, seda ya shiga suka gaisa da mummyn jalal sannan ya fito ya nufi sashen Jalal,.
Kofar bedroom dinsa ya bude ya shiga yana kwance yanata bacci, agogo Jawwad ya kalla 9:30am amma Jalal be tashiba, girgiza kai yayi.

Ya taba Jalal " bross wake up gari ya waye fa kalli rana tayi sosai "

Dan motsawa yayi kaman baze tashi ba, sannan ya tashi zaune yayi mika yana Dan yatsina fuska

"Jalal anya kayi salla kuwa?"
"Banyi ba"
yafada hankalinsa kwance
"Haba Jalal sekace ba musulmi ba quarter to 10 fa amma bakayi sallar asuba ba why?"

"In kai zanyiwa innayi kar ka karba" yafada yana shirin mikewa

"No am sorry jekayi sallar kazo muyi breakfast"
Yafita yakoma palour yana jiransa

Mikewa yayi yayo wanka tareda alwala yazo yayi salla itama dai sallar gata nan wata kilama badan Jawwad yazoba bazeyi ba,

(Sallar karfe 10am Jalal kai lefunka naka sunyi yawa Allah ya yafe mana)
Bayan ya idar ne yafito ya tarar da Jawad a palour yasamu guri ya zauna a kujerar datake fuskantar Jawad

Jawad yayi gyaran murya yace "Jalal wai me akayi maka jiyane meyafaru"
Yayi shiru kaman ba zece komai ba

"Wata yarinya CE jiya da daddare ina magana da mummy kawai ta fito ta tsoma baki hadace min Mara tarbiyya"

Dan zaro ido Jawwad yayi aransa yace ai batayi karyaba abokina watakila ma rashin mutuncin kakewa mahaifiyarka agaban mutane amma a fili seyace
"Wace yarinyar CE"

"Toni ina nasanta naga dai kaman na taba ganinta amma namanta inda nasanta,
Amma tabbas duk ranar dana ganta sena mata abinda bazata manta dani ba zan tabbatar mata bani da tarbiyya shaยณ yarinya"

"Yi hakuri bros yanzu taso muje gidanmu muci abinci tunda yanzu dai baka ganta ba kamanta kacigaba da harkokinka kawai"
Ya janyo hannunsa suka fita daga gidan, zuwa gidan su

Bayan sun kammala cin abincin ne Jawwad yayi gyaran murya yace
"mutumina Jalilana fa tazo yau kwananta hudu a kano"

"Wace hakan?" Jalal yafada cikin ko in kula
" kaifa kafiye wulakanci kanwata fa danake gayamaka ta Kaduna"

Murmushi Jalal yayi "to shine kake wannan fara ar haka?"
"Bazaka ganeba Jalal irin yadda nakesonta, ba iya son yan uwantaka nake mata ba Jalal ina kaunarta ne sonake in kasance tare da ita har karshen rayuwata ganinta kawai yana Sani farinciki Ina kaunar Jalila matuka zan iya komai akan farin cikinta"

Kyakyacewa Jalal yayi da dariya tare da kunna sigarinsa ya fesa hayakin sama tare da wani kasaitaccen murmushi,
"Gaskiya ka faller over bross irin wannan bege haka ina mamakin me akeji a soyayya ni har yanzu banga macen dazata Sani wannan sambatun ba"
ya karashe maganar da wata irin,
dariya
"Jalal irinkune soyayya bata muku ta dadi wato dariyama nabaka ko hmm rai dai Allah yabamu rai da lafiya"

"Yaya Jawwad barka da Sadiya INA fatan katashi lafiya, Abba yace kazo yanason ganinka,"

Daram kirjin Jalal ya buga muryarta ce!!,

"Yar halak taki ambato barka da safiya kanwata,
Jalal gata fa Jalila kenan danake gaya maka kanwata juyowa yayi suka yi ido hudu da ita

Kallonta yayi tabbas itace, yarinyar da tazageshi agaban mahaifiyarasa jiya da daddare nan da nan annurin fuskarsa ya dauke yafara zaro idanu,

Cikinta ne ya duri ruwa tafara rarraba idanu zuciyartace take bugawa da karfi yau kam ta shiga uku
(Marar kunyar karya kin debo ruwan dafa kanki)

More comments more typing........



๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ
[8/31, 8:26 AM] Safiyya: ๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

_ABDUL JALAL_

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 4
PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

I want comments not stickers๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ข
Comments dinku shine kwarin gwiwata

Special thanks to u my motivator
I dedicate this page to you
Anty MARYAM

_My first novel_

"Shigomana ya kika tsaya anan"

Dagewa tayi ta boye tsoronta ta dai dai ta nutsuwarta, tashiga cikin dakin

"Kanwata ga Abokina kuma Dan uwana wato Jalal dukda kin sanshi amma nasan bazaki tunashi ba lokacin kina Karama sosai "

Kallon Jalal tayi taga mugun kallon dayake mata amma ta basar
"Sannu"

abinda tafada kenan ta maida kallonta kan Jawwad

"Yaya naga kanada bako in kungama na dawo karka manta da kiran Abba"
Ta juya tafita tana godewa Allah a zuciyarta da Jalal bemata komai ba

"Wannan ce kanwartaka?"
"Yeah ya kaganta so gentle and innocent"
"Good"
shine abinda yafada kawai
Mikewa yayi tsaye zetafi

"Bros yazaka tafi muna magana"

"Inada abunyi ne"

Ya fice wato ma kanwar Jawwad ce tabdijan yanzu ta zagi banza kenan anya kuwa ze kyaleta ko dai yagaywa Jawwad yaja kunnen kanwarsa tafita a harkarsa, to meye amfanin hakan,

Tana ganin Jalal yafita ta koma gurin Jawwad tasameshi inda tabarshi be tashi ba, shiga tayi ta zauna tace
"Yaya Jawwad magana nakeson muyi"
"Am all ears sisyna ina jinki fadi abinda kikeso"

ta Dan gyara zamanta tana fuskantarsa Wanda bayan kujerar dayake ya kasance window ne

Zancen zuci yacigaba gsky y zama dole ya dau mataki inma ya kyaleta taci bulus kenan yana cikin wannan tunaninne se jeje yafado masa bari ya kirashi yaji wani shawaran ze bashi ne,
hannunsa ya zura a aljihu da niyyan ya dauka wayan se yaji babu yadan yi shiru seya tuna tana kan kujerar da ya zauna a dakin Jawwad

"Yaya Jawwad meye hadinka da mutumin nan ne?"
"Kina nufin Jalal?"
"Eh shi nake nufi"
"Abokina ne kuma Dan uwana"

"Ta Yaya yazama Dan uwanka Yaya Jawwad wannan ba aminin arziki bane halinku Sam ba daya bane kallafa sigari yake shamaka a daki da ganin idonsa kasan tarbiyya ba ta wadace shi ba, kalli askin kansa, daganin bakinsa wannan yana shayeยฒ
Zamanka tare da shi mutane zasu zata halinku daya Sam bashi da tarbiyya"
ta daga kanta wazata gani kawai taga Jalal a tsaye a bakin window yana kallonta da jajayen idanuwansa
Wanda hakan ya tabbatar mata yaji abinda tace

Ras! Ras!! Ras!!! Gabanta yafadi

cikin palourn ya shigo ya dauki wayarsa bece komai ba ya fice
Jawwad be kawo komai a ransa ba Dan yasan halayen Jalal shiyasa bekawo yaji wani abuba kuma yabawa window baya Dan haka besan yazo wajen ba.

"Kinaji kanwata Jalal mutumin arziki ne ba yadda kike tunaniba inayimasa addu a in Allah ya yadda wataran zakiga ya dena ze wuce kaman ba ayiba kema kisashi cikin adduo'inki kidinga masa fatan shiriya"

"Yayana ka kula da kanka Dan Allah karka bari dabi'unsa su rinjayeka wataran Dan Allah"

"Karki damu kanwata ba abinda ze faru mun Dade tare da Jalal da zan zama irinsa da tuni na zama shima abinda kikaga yanayi kaddara ce babu abinda ze faru da yaddar Allah"

"To shikenan" ta fada tana mikewa
"Karka manta da kiran Abba
"to shikenan zanje insha Allah "

Jalal kam Shiru yayi yana tunanin wani mataki yakamata ya dauka akan yarinyar nan gata kanwar amininsa kanwarma kuma wadda yakeso ta yaze hukunta yarinyar nan ya bakanta mata ba tare da Jawwad ya gane ba baya son batawa abokinsa rai Dan tabbas in yayi mata wani abun Jawwad bazeji dadi ba,
Ko in kira Jeje yabani shawara idan na kirashima mezemin? wata zuciyar taba shi amsa
Mara tarbiyya!!! Wai nine bani da tarbiyya mtseeww yaja tsaki zakiga rashin tarbiyya ganin idonki.

(Kai JALAL bafa karya tayiba )

Jalila kuwa Cikin gida ta koma tunda ta shigo maama ta bita da wani irin kallo na zanyi maganinki ita kuwa Jalila bata san tanayi ba,

Gurin Abba nufa ta durkusa tace

"Abba nagaya masa yace yana zuwa"
"To shikenan diyata"

Wucewa tayi dakin su ta je ta tarar da Nana tana ninkin kaya taje ta zauna kusa da ita
"Nana kinsan me yafaru?"
Nana ta juyo ta bata dukkan attention dinta
"A'a sekin fada"
"Ingaya miki Jalal nagani adakin Yaya Jawwad yana ta shan sigari"

"Hmmm to ai bakiga komai ba Dan dai sigari kawai karewa har giya yake sha masa a daki wataran in yaje yasha yana tambelansa Yaya Jawwad ne yake nemo shi a club yakawo shi dakinsa ya kwantar da shi har giyar ta sake shi
Ke baki San komai bane shiyasa nace miki rabashi da Jalal ba abune me sauki ba" Nana ta karashe zancen jikinta a sanyaye

"Tabdijan kice abun babba ne ai in gaya miki dana ganshi a dakin bayan ya fita nakoma gurin Yaya Jawwad nai masa magana akan ya rabu da Jalal bashi da tarbiyya Ashe yadawo daukar wayarsa yaji duk abinda nafada bakiga kallon da yayi min ba"
Dan zaro ido Nana tayi
"Are u serious"
"Wlh dagaske nake yaji me nace bakiga mugun kallon da ya dingamin ba"
"Tabdijan Jalila garin Yaya haka tafaru aikuwa kinci sa a Yaya Jawwad yana gurin da wallahi inaga seya kusa sumar dake"
"To dai Allah ya rufamin asiri
Bari in Dan kwanta in huta"
"Sarkin bacci ko gajiya ba kyayi Allah ya kiyaye haduwarki dashi"
"Shi wa?"
"Kinfini Sani"
Murmushi kawai tayi ta hau gadon ta kwanta.
Nana kuma tacigaba da ninke kayanta,
Befi 10 minutes da kwanciyar Jalila ba
Ilham tayi sallama

"Mutuniyar kinji gori kenan yau se gashi kinzo anya makuwa bawani abun yakawoki ba" Nana tafada cikeda zolaya

"Hmmm ke dai bari Nana akwai magana ne,
sister dinki bacci takene?"

"Eh bacci takeyi meyafaru"
Cike da damuwa ta kalli Nana
"Nana Yaya Jalal ne"

"Wani abunne yasameshi?"
Nana ta tambaya
"Aa Nana kin San dai zancen, ta tsuniyar gizo bata wuce koki hankalin yaya Jalal Sam baya kaina wlh ko kallo ban isheshi ba komai nayi bana birgeshi ke mukwana gida daya mu tashi amma semu shafe kwanaki ko kallon inda nake beba
Abun yana damuna Nana ina matukar kaunarshi amma shiko a jikinsa ni ban San meyake damun saba kaman ba mutum ba"
Nana ta dan dafata da sigar rarrashi
"Ilham inso cutane hakuri maganine kicigaba da hakuri kina addu'a insha Allah komai zezo karshe"

"Nana in ba ya Jalal na aura ba bazan iya zaman aure ba, dashi nake so na rayu yazama uban yayana ,
nifa ko karatu bazan iya cigaba ba sonake munayin SSCE ya aureni narasa yadda zanyi gashi mummy ma ba jin maganarta yake ba itama tayi kokarinta amma yaki saurarona
Dama daddy ba a maganarsa don baze taba tursasa shi ba Ina cikin damuwa"
Daga inda Jalila take kwance ta tashi zaune Dan taji hirar dasuke ba bacci take ba, dannan waya take,
"Aikuwa kina tattare da nasani a rayuwarki damuwa yanzu kikafara muddun kika zabi dan giya a matsayin uban yayanki karki biyewa son zuciya ki cutar da yayan dazaki Haifa a nan gaba auren Jalal babu abinda zaki kwasa bayan bacin rai da dunbin danasani"

Kallonta Ilham tayi tana nanata Kalmar Dan giya aranta lallai Jalila bata da mutunci a gabanta take kiran Jalal Dan giya banda shishshigi da munafurci wayasakota a ciki
Lallai bata sanniba akan Yaya Jalal banki imbata da kowace ce ba
Ta kalli Jalila rai a bace

"Kekuma wayasa dake a gabana kike cin zarafin Dan uwana kuma masoyina Dan giya wannan ba magana bace at least yana abokin yayanki ya cancan ci ki mutuntashi"

"Taya kike tunanin in girmama Wanda be girmama mahaifiyarsa ba, Sam Jalal ba abin girmamawa bane, kema zuciya yace take rudarki, kokuma akwai wani sirri a ranki da kike boyewa, Wanda bakowa yasani ba
in bahakaba babu macen dazatayi sha'awar rayuwar aure da Wanda bayajin maganar iyayensa inba kema irinsa bace fitinanniya""

Da sauri Ilham ta kalli Jalila,

Jalila ta Dan daga mata gira
"Nayi karyane"

Gaban Ilham ne yafadi akwai wani abu danake boyewa da bakowa yasani ba ya akai tasan hakan???

"Ba abin mamaki ko tuhuma a maganata, shawarace kawai tun wuri kisake tunani kinemi hanya me bullewa wannan shshashan be cancanci zama miji ba balle uba in bahakaba seyasaki kukan da kekanki bazaki iya hana kanki ba" cewar Jalila

"Enough please meyasa baki da ta ido kinacin zarafin dan uwana kina kiransa da dan giya agabana!!" Ilham tafada cikin shouting

"Hold on madam ba ayimin shouting" Jalila ta katseta

"Haba mene haka kukeyine bafa yarane kuba wannan be kamata ba we are all sisters"

Tabe baki Jalila tayi tace
"Ilham nasan zakiji ba dadi amma gaskiya nagaya miki"
Bari inje waje in Baku guri ina bukatar recharge card zani insiyo ta dau hijabinta tasaka tafice

Gajiya yayi da kwanciya ga bacin rai yana fama a banza akan wannan shedaniyar yarinyar yafito kofar Gida da sigarinsa a hannu kaman kullum

Bari yaje Jawwad yazo yarakashi su Dan zaga gari koze rage takaici ya sha sigari kusan kara 7 amma har yanzu ransa a bace yake

Cikin gidansu Jawwad yakoma yanufi bangaren Jawwad wayarsa tafara ringing tsayawa yayi ya dakko wayar Cwt dad ne ke kiransa murmushi yadanyi yadaga wayar.

Tazo fita taganshi tsaye bangaren Yaya Jawwad yana amsa waya yana murmushi
Kai amma wannan akwai nacin bala'i wai dama yana murmushi

Dogon tsaki taja Wanda yasashi waigowa
" dubeshi dan Allah kalli askin kanka daganin wannan askin bana mutanene kirki bane kullum baki cikin fidda hayaki kaman salansan tifa ko gajiya bakayi, kuma kazo ka likewa Dan uwana mutumin kirki kana nema ka lalata shi,
Kai dashi akwai banbanci shi yana da tarbiyya yana girmama iyayensa sabanin kai kaga kunada banbanci!!!"".

(Turkashi kindebota da zafi Jalila mekuke tunani zefaru keep following aakwai cakwakiya fa!!!!!!!!!)

Please share โ–ถโ–ถโ–ถ
more comments more typing............

https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL.

๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ
[8/31, 8:26 AM] Safiyya: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

_ABDUL JALAL_

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 6

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

I want comments not stickers๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ข
Comments dinku shine kwarin gwiwata

_My first novel_

"Gobe ma in kikaga Jalal kikuma zaginsa useless creature kawai"

Yayi tafiyarsa ya barta a gurin tana ta mimmikewa tana fama da numfashi ta galabaita har a tafara fita hayyacinta.

Mummy ce tafito daga sashen daddy zata shiga kitchen ta dinga jin kakari da nishi, dawowa tayi da baya a Dan tsorace, tana duba meke wannan nishin,
Jalila tagani a zube a gurin tafita hayyacinta numfashinta nata fita da sauri

(Lallai JALILA ta sha hayaki)

" subhanallah ke Jalila meyafaru meke damunki??"
Tazo tana taba ta
"Ohh ni khadija meke damun ta kodama tanada athma ne

" Ilham!, Ilham!!, Ilham!!!,"

Tashiga kwala mata kira

"Ke Ilham kifito da sauri"

Itakam Nana gajiya tayi da jiran Jalila Dan haka kawai tayi tafiyarta ta shige Gida,kai tsaye taje dakin mummy
"Mummy mun dawo "
"To sannunku ina Jalilan?"
"Wayarta ta manta ta koma dakkowa shine na taho"

Kai inkuma Yaya Jalal ne yamata wani abunfa tai wannan tunanin a ranta
da sauri tafito ta nufi gidansu Jalal

Shikuwa Jalal gurin Jawwad yatafi abunsa, kaman be aikata komai ba hankalinsa kwance
Amma lokaci2 in ya tuna maganganun Jalila se ransa yabaci .

Da gudu Ilham tafito
"Mummy lafiya kuwa?

" zo kiga Ilham dama tanada asthma ne ko wani cutan?"
Ilham ta Dan zaro ido

"Mummy ya za ayi in Sani"?

" maza jeki gidansu kifada suzo akaita Asibiti kar ta mace min a Gida"
"To bari in je"
Mayafi Ilaham ta dauka ta fito da sauri a bakin gate taci karo da Nana
" yawwa Nana Jalila dama tanada asthma ne kowani cutan?"

A firgice Nana ta kalleta
"Asthma kuma? Bata da wani asthma, me yasameta?"
"Zo muje kyagani"

Ilham tafada tana janyo hannunta zuwa cikin gidan

"Subhanallah Jalila meya sameki?"

Nana tafada tana jijjiga Jalila amma Jalila bata San me akeba tafita hayyacinta
Da gudu Nana ta tafi gida domin sanar dasu abinda yake faruwa,
tana shiga gida a harabar gidan ta ci karo da su Jawwad

"Ke Nana lafiyarki kike gudu haka? sekace wata karamar yarinya mene haka"
Jawwad ne yayi maganar a Dan fusace

"Yaya Jalila CE"
"Me yafaru da ita?"
Yafada hankalinsa a tashe

Nima bansaniba yaya tana gidansu Yaya Jalal yanzu muke tare da ita takoma dakko wayarta yanzu kuma ta suma bata iya numfashi sosai
"Suma kuma"
Ai bejira tagama bayanin ba yayi hanyar waje da sauri

Wani Dan guntun murmushi Jalal yayi sannan yabi bayan Jawwad

Itama Ilham ta karasa cikin Gida dan ta sanar da maama abinda yake faruwa

Suna zuwa suka tarar da Jalila kwance akan cinyar mummy bata numfashi, se kadanยฒ

"Subhanallah Jalal bani key din motarka mu kaita Asibiti" Jawwad yafada da sauri
Key din ya danka masa
memakon ya raka Jawwad sema ta shi da yayi yai ficewarsa

Jawwad beyi wataยฒ ba ya dauki Jalila yayi waje da ita yasaka ta a mota ya tada motar kenan
Nana ta shigo gidan ya tsaya ta Shiga motar

"Yaya maama tace muyi gaba zata taho in Abba ya dawo"
Be amsa mata ba yaja motar

"Ilham ki bisu mana kirakasu ko Asibitinne kinga ni badamar in fita yau babanku ya dawo" maama tayi maganar tana duban Ilham

"Ba inda zani wallahi Allah ya bata lafiya in nabisu ai bani zan bata lafiya ba"

"Haba Ilham amma ai a gidanmu abun yasameta"
"Ni wallahi mummy a gajiye nake ba inda zan iya zuwa yadda nagajin nan hutawa nake sonyi"

Ta wuce daki abunta
"Ohh ni hadiza yaran nan se a hankali kowanne da halinsa

Suna zuwa Asibitin aka karbesu aka shiga da Jalila emergency don ceto rayuwarta

Wajen karfe Tara na dare Maama sukazo asibitin ita da Abba

Wanda yai daiยฒDa fito da Jalila daga emergency aka basu daki
Alhamdilillah numfashinta ya dawo daiยฒ se dai tanata bacci ga drip da aka saka mata

" Allah sarki diyata Allah yabaki lafiya, Amma nayi mamaki iya sanina bata da wani ciwo makamancin haka"
Abba yafada cike da damuwa yana kallon maama
Dan tabe baki maama tayi

"A'a to ai ba dolene kasaniba watakila tana dashi mune bamu saniba kasan uwatta bakomai zata gaya mana ba tunda...."

"Ya isa haka Zainab.." Abba ya katse maama
"Yanzu lafiyarta muke fata ba wani surutu ba"

Likitan ne ya shigo domin kara dubata

Jawwad ne yayi gyaran murya
"doctor meyake damunta ne?"

"Eh blockage ne akasamu a airways dinta maybe ta kwarene ko kuma ta shide da wani abun,
Zatasamu lafiya insha Allah munyi mata allurai zatayi bacci karku damu Allah yabata lafiya" suka amsa da Ameen

Guraren sha daya na dare
Abba da Jawwad suka tafi Gida akabar Nana da da maama suka kwana a gurin Jalila

Washe gari da sassafe Jawwad ya tashi ya shirya da nufin ya koma Asibiti, dayake motar Jalal a hannunsa ta kwana kafin ya wuce ya maida motar gidansu Jalal,
Jawwad ya tsaya suka gaisa dame Gadi yayai masa yame jiki dayake yasan meyafaru,
ya" amsa da sauki,"

Jawwad ya juya zefita se yadawo da baya ya kalli me gadin
"Jalal yana nan ne"
"Eh yana nan yana bangarensa"
"Nagode"
Jawwad ya juya ya nufi part din Jalal Lamar kullum ya na kwance yayi daiยฒ yana bacci babu alamar yayi salla
Jawwad ya daddaki pillown da Jalal yake kwance
A hankali Jalal ya bude ido

"Tashi kayi sallah Dan nasan bakayi ba"
Seda yadan ja seconds sannan ya tashi zaune yana hamma bece masa komai ba ya mike yaje
Yai alwala yagabatar da sallar asuba karfe 7:30am

"Jalal fushi nake da kai"
Jawwad yafada tare da Dan hade rai
Jalal ya kalleshi
"Why"
"Kanwata ba lafiya rai a hannun Allah amma ko ka tambayeni ya jikinta talk less of kace zaka min kara ka dubota to ni na roki arziki ka rakani Asibiti"

Dabeyi niyyar zuwa ba amma yaga in yai haka be kyautawa amininsa ba wato Jawwad Dan haka yace

"Sorry bross karkayi fushi dani bari in shirya muje"

"Seda na roka?" Jawwad yafada yana Dan hada rai

Murmushi Jalal yayi "to koma mene ai nace zani in kuma bakasone in koma baccina"
"Kai ka isa ni yi Sauri karmu makara ni sonake tana farkawa tafara tozali da fuskata"

Girgiza kai kawai Jalal yai a ransa yace ka dorawa kanka wahala saboda wannan banzar yarinyar Mara kunya
Kafin Jalal yagama shiryawa Jawwad yakira maama
A waya bugu seda ta kusa tsinkewa sannan ta daga
" salami alaikum maama barka da safiya "
"Yawwa barka ya daddynaka"?
"Muna lafiya dama tahowa zanyi nace ko kuna bukatar wani abun?

" a'a bama bukatar komai ka hanzarta dai inaso indawo Gida in huta

Please Login or Register in order to submit comment