Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daze miki kidena zuciya da shi, sannan kidena jin tsoransa, sannan kidinga kokari kema kina dafa abinci ki bashi, in wataran beci ba wataran zeci"
Ilham ta Dan girgiza kai
"Yaseera gani kike shawo kan Jalal abune me sauki ko? Mugun Dan taurin Kaine, ga shi jarababbe, yaseera tsawon shekarun nan danayi a gidansu ko inda yake bayaso inje, am about to give up"
"Ita Jalilan dayake daga mata kafa ba mace bace kamarki, iya bariki kawai tafiki, ki bar wani batun seya soki malama kawai ya aureki a wuce gurin"
"To yaseera insha Allah zan kuma jajircewa, Wallahi nida zuciyata tafara bani kawai inyi duk me yiwuwa kawai inyi me gaba daya"
Da sauri yaseera ta kalleta
"Baki da hankaline? Inkuma aka samu akasi fa"
"Nima abunda yasa nafasa kenan"
"Karki kuskura ki fara, kibi komai a hankali"
"To shikenan yaseera, zan cigaba da kokari"
Haka yaseera taita zigata sannan sukayi sallama, Ilham ta shiga Gida yaseera kuma ta tafi
Hannah ta kira wayar Jalal harta gaji dama seyaga dama yake amsa wayarta, yau ta kudurce wa ranta kome ze faru sedai yafaru Dan Gida zata bishi, lokaci yayi da yakamata tafara wasan kwallo dashi daga shi har kanwar tasa dole sugane wace Hannah,

Jalila bin Jalal tayi da kallo, wannan akwai Dan rainin hankali, shima Yaya Jawwad sekace Jaraba kowa da gidan ubansa ya zauna a can amma shi inbe bishiba shi ze biyo shi, a ranta tace kacigaba zan rama ne wannan wulakancin da kakemin bakaci bulus ba
A zahiri kuma ta ba sar ta kuma serving din Jawwad
"Yawwa Yar Baby, mungode sosai"
"To yayan Baby, permit me to leave"
"U can leave dear"
Tana komawa cikin Gida Maama ta kuma aikenta gidansu Jalal, waita karbo kaya anjima wasu customers zasuzo tun safe Jalila take aiki bata huta ba gashi bata son abunda ze hadata da Ilham, ba tayi musu ba ta juya ta kuma tafiya aiken da akayimata,
Tana fitowa taga wata mota a tsaye a kofar gidansu Jalal, harta gifta mortar, aka danyi reverse da motar saitin inda Jalila take, sauke glass din motar akayi wata matashiyar budurwa ce a cikin motar
"Sannu dai" tacewa Jalila
"Yawwa sannu"
"Dan Allah tambaya nake"?
" Allah yasa nasani"
"Naga kamar cikin gidan nan zaki shiga"
"Au kamace baki tabbatarba"
"Ohh sorry Dan Allah Jalal nake nema"
Kallonta Jalila tayi, tayi nazarinta na wasu yan mintuna sannan tace
"Me Jalal ze miki"?
" inason ganinsane"
"Baki da lambarsane?"
"Nakira bata shiga"
"Injiwa zance masa"?
"Kawai kice masa yayi bakuwa"
"Bahaka nakeba, inkina son ganinsa kifadi sunanki"
"Hannah ce, koke ce Ilham din da Jawwad yake gayamin kanwarsa da kike sonshi"
Da sauri Jalila ta kalleta, ta Dan kuramata ido wasu yan mintuna sannan tai murmushi
"Hannah"
Jalila ta maimaita
"Yeah I am Hannah"
Jalila ta kuma murmushi
"Zata iya yuwuwa nice Ilham kuma zata iya yuwuwa bani baceba, for now bazaki ga Jalal ba ki tafi kawai inma kin tsaya bazan bari ya fitoba, kune masu kara ingiza lalacewarsa, kalleki, kalli shigar jikinki a matsayinki na ya mace kina yawo half nicked, kinzo gurin namiji saboda abun kunya, me kike tsammani in mutane suka ganshi da ke, kibari in yaje inda kuke haduwa kya Ganshi amma ba anan ba, juya kikoma inda kika fito" Jalila ta hade rai tareda nuna mata hanya

Share please
More comments more typing.........................
Masoyana abun alfaharina comments dinku yana kayatar dani Allah yabar kauna


🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
[8/31, 8:30 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_
(2020)

_ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 37

PART 1
Share please

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa
ABDUL JALAL NOVEL FANS
Love u all guys ❤❤❤❤❤

-MY FIRST NOVEL-

Karewa Jalila kallo tsaf Hannah tayi, ta tabbatar Jalila Sa ar kanwarta ce, badan kartayi karyaba setace kanwa ta biyu ma, bude motar tayi sannan ta fito ta kalli Jalila sama da kasa, ta danyi murmushi sannan tace
"Ni kike kora kike cewa in tafi in bar nan gurin"
"Au tambayata ma kike, lallai na fuskanci saboda irinku ake double period a class, saboda ba kwa dauka a daya"
Mamakine yacika Hannah, tace
"Bari in gaya miki wani abu dabaki saniba ni.....
Jalila ta dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu tareda fadin
" NO need saboda babu wani abu me amfani ko me mahimmanci Wanda ze amfaneni dazaki fada, as I said it before, kibar nan gurin in ba hakaba zan baki mamaki"
"Ni Hannah zaki bawa mamaki"
"Kwaraikuwa kedin"
Nuna Jalila tayi da Dan yatsa zatayi magana, batayi maganarba Jalila tasa hannu ta sauke yatsan Hannah
"Duk wata magana muyita amma ba a nunani da Dan yatsa, daga haka nagama magana dake, nabarki lafiya, inkin gadama kicigaba da tsayuwa"
Jalila na zuwa nan a zancenta ta shige gidansu Jalal tabar Hannah tsaye sororo tana mamaki
Jalila ta shiga cikin gidan da sallama, Ilham tana palourn tana danna waya tayi mata banza, Jalila ta kuma nanata sallama amma Ilham mirsisi taki amsa sallamar Jalila
Karasawa Jalila tayi tasa hannu ta fizge wayar hannun Nana
"Haba kekuwa, kome nayi miki a rayuwa be kyautu inyi sallama kimin banza ba"
A fusace Ilham ta kalleta
"Bani wayata malama"
"Kiramin mummy, seki karbi wayarki"
"Ke kin isa kisani aiki,"
"Ban isaba alfarma na nema"
Sannan ta bawa Ilham wayarta,
Ana haka mummy tafito da alama unguwa zata fita
Suka gaisa da Jalila, Jalila ta gayamata Aiken da akayi mata, mummy tace taje yanzu fita zatayi in ta dawo zata aiko,
Da haka Jalila ta fito ta tafi gida,.data fito ta tarar Hannah ta tafi, Jalila a ranta tace kin kyautawa kanki dakika tafi ai
Hannah tana barin gurin takira wayar Jeje ta tambayeshi ina zasu hadu yagaya mata, ta nufi gurin kai tsaye, tana zuwa ko tasameshi a can, yanayin fuskarta kawai ya nuna masa akwai matsala, saboda yadda take huci
"Me idon zinare, lafiya kuwa"?
" ina fa lafiya, gidansu Jalal naje, saboda yan kwanakin nan baya daga wayata, naje nasamu wata a kofar gidansu, wata yarinya taci min mutunci"
"Kamarya taci miki mutunci, miye hadinki da ita?"
"Ina kyautata zaton itace budurwar tasa, da Jawwad yake fada Ilham take kowa, hada cewa bazata bari ya fito ba, sedai injira muhadu inda mukasaba"
"Jalal din, to karya takeyi barazana ce kawai, uwar da ta haifeshi ma bata isa ta hanashi abinda yyi niyya ba, balle wata Ilham, gayen da soyayya bata gabansa, kema kinciri tuta ne da yake sauraronki, amma ya akayi kika San Ilham dince"?
"Na tambayeta amma ta rainamin hankal, Amma nayi mamaki, yanda nake zaton Ilham din na dauka wadda zanyi maganice a take amma naga itama a tsaye take Dan bata da kunya"
Dan shiru Jeje yayi sannan yace
"Tabbas Ilham ma masifaffiya ce amma bana tunanin ta kai yadda kike fada haka"
"Hmm, bakaga wulakancin datayi minba kuma na girmeta, sena raina rashin kunyata Dan fafur hanani magana tayi, mamaki da takaici suka cikani"
"Gaskiya Hannah kin bani kunya duk bakin naki, kinsan a duniya Jalal ya tsani mace ta dinga juyashi"
"Ba a nan takeba Jeje hausawa kance yaki Dan zamba ne Dan haka, zan nuna mata duk Wanda yarigaka kwana ze rigaka tashi, idan takamarta rashin kunya, nikuma takamata bariki, zan daga shi har ita zan basu mamaki"
Jalila ta sanar da Abba zuwan captain Rasheed da yayansa domin kawo musu ziyara, Yaya farinciki sosai da jin haka, Jalila ji take kamar ta janyo ranar Saturday su Hanan suzo, se murna takeyi
Daren yau dai Jalal yasaci jiki ya tafi gurin shan giyarsa, yaje babu dadewa be fara shaba, mayyar tasa tazo wato Hannah, tazo ta nemi guri ta zauna tai shiru batace komaiba
Ya Dan kalleta, yanayin fuskarta ya nuna tana cikin damuwa,
"Ya akayine sarkin matsala, mekuma ya faru?"
Ta dago ta kalleshi, tayi kalar tausayi sannan tace
"Jalal kwana nawa ina kiranka kaki ka daga wayata, naturomaka messages kaki reply haba Jalal, gashi aka cimin mutunci saboda kai, yakamata ka tausayamin"
"Ya akayi aka cimiki mutunci sabodani?"
"Kanwarka mana"
"Wake nan?"
"Wace kanwar kake da ita, banda wadda Jawwad yacemin tana Sonka?"
Shiru ya danyi yana kallon Hannah, tacigaba da magana
"Ranar nakiraka baka dagaba, ita ta daga ta min rashin mutunci ni kana cemin Mara kamun kai amma me kanwarka take a gurinka shabiyun dare, har tana gayamin bacci kake ta zageni hadda cemin mayya"
Shikam Jalal kasa cewa komai yayi se ido da ya zuba mata,
"Har yanzu ni banga cin mutuncin dakike fada tayi miki ba"
Kallonshi tayi
"Au hakama zakace? Metakeyi a gurinka shabiyun dare harta daga wayarka?"
"Meye kuma na bin diddgi ina ruwanki dame take a gurina shabiyun dare?"
" haba Jalal,Yauma nakasa jurewa da rashin ganinka Dan haka naje gidanku, na hadu da ita a kofar Gida daga tambayar kana ina ta dinga zagina
Harda cewa baka isa tahanaka abu kayi ba Dan haka bazata bari ka fitoba, saboda baka tsallake maganarta, tana juyaka yadda taga dama, haka ta dinga fadar maganganu, abun ya dauremin kai"
Dan dagowa yayi da sauri
"Inji Ilham din?"
"Eh mana, ni babban bakin cikina yadda ta dinga gayamin miyagun maganganu saboda kai, wallahi Jalal ba Dan kanwarka bace senasa ankoyamata iya magana, harni zata cewa mutuniyar banza? Ita ma ai ta banzarce tunda zata iya zuwa dakinka shabiyun.......
" Enough malama, karki kuskura ki zagi kanwata, kuma wallahi duk abunda yasameta a kwanan nan kikuka da kanki, Ilham ba mutuniyar banza bace, ni shedane, ki kiyaye baki isa ki zageta a gabana ba, and then zanje gidan in sameta, zatayi bayani"
Yana zuwa nan ya tashi ya tafi yabar Hannah baki a bude, saboda mamaki se yanzu takuma tabbatarwa kanta tsawon wannan lokacin, har yanzu Jalal be fada tarkon sonta ba kenan tunda har ya fifita Yar uwarsa akanta kenan ya fara son Ilham, amma ko ba komai tasan abunda ta fada din nan ze tunzirashi, gaba dayanku, sena nuna muku ni gogaggiyace a bariki

Jalila hartayi shirin kwanciya Abdallah ya kirata suketa hira dashi da ita da hanan, a wannan lokacin kiran JAWWAD yaita shigowa amma line busy, Jawwad ransa babu dadi ya kwanta, yana tunanin dawa Jalila take waya tsawon wannan lokacin

Tunda Jalal ya tafi yake tunanin ya akayi Ilham ta daga masa waya, meya kaita part dinsa shabiyun dare ( besan Jalilace ta amsa wayarba, lokacin da bashi da lafiya")
Shi babban takaicinsa ma cewar da tayi inta hanashi abu be isa yayiba, yaushe yake shiga harkarta dazatayi masa karya, ta zubar masa da kima a gurin wata mace daban aikuwa se ya hukunta Ilham Dan baya son karya (Ilham zata amsa query maimakon JALILA 😂😂)
Ya koma Gida yana zuwa ya tafi part dinsa don kuwa by now yasan mutan gidan sunyi bacci, yanazuwa yai wanka ya canza kaya sannan yasha giyarsa iya son ransa sannan ya kwanta bacci
Daren ranar Ilham tayita sake² yadda zata canza takunta na zama a gidan, domin Janyo hankalin Jalal kanta Dan wannan karon ta sawa zuciyarta lallai seta cika burinta.
Da safe Jalila kaman yadda ta saba tayiwa halima Karin karatun Qur'ani sannan suka tashi sukayi aikace² daya kamata suka hada breakfast
Kamar kullum Da sassafe Jalal yake zuwa saboda suna motsa jiki, in sukayi suka gamane we yayi wanka ya canza kaya, a gidan,
Ya lura da rashin walwala na Jawwad amma bayaso yafiye takura masa, bayan sungama exercise ne Jawwad yai wanka yaketa shirin tafiya makaranta, saboda ze shiga lectures karfe tara
JALAL ya kalleshi " wai yanaga Janata shirin tafiya makaranta breakfast dinfa"?
"Nakoshi"
Dan zare ido Jalal yayi
"ka koshi kuma, me akayi maka ne? Naga se fushi kake, meyasa kake so ka tafi makaranta bakayi break fast ba"
"Haka nan, yau bana son cin abincine"
"Ban yadda da abunda kafada ba, baka fiye yin fushiba, kana iya boye damuwarka, amma tunda nagane kana cikin damuwa nasan matsalar babbace,"
Dan murmushi kawak Jawwad yayi "meyasa bazaka yadda ba ne?"
"Shikenan naji amma ban yadda ba"
Jawwad ya cigaba da shirinsa, Jalila ce tai sallama
Jawwad ya amsa tareda basar da ita yacigaba da shirinsa, dama JALAL ba amsawa zeyiba
"Barka da safiya Yaya Jawwad"
"Yawwa barka"
"Naga kana shirin fita abincinfa?"
"Nakoshi"
"Meyasa?"
Shiru yayi mata yasamu guri ya zauna yana kokarin daura agogonsa,
JALAL yana kallonsu bece musu uffan ba
kan hannun kujerar da Jawwad yake JALILA ta je zauna, tasaka hannu ta karbe agogon hannunsa
Dagowa yai yana kallonta, ba tareda ta kalleshi ba tace
"Gayamin meyasa yau bazakaci abincina ba? Laifin menayi maka?"
Y miko mata hannunsa tareda fadin
"Babu abinda kikayimin, ban agogona kar in makara"
janye hannunta tayi
"Ko shine yayi maka wani ABU?"
"Shiwa"
"Wancan" tafada tana nuna JALAL, gaskiya JALILA Yar rinin hankali ce
Jawwad yace "ba sunansa wancanba,"
"Yaya Jawwad na fuskanci ninayi maka laifi, Dan Allah kayi hakuri"
Dan kuramata ido Jawwad yayi, ta damu sosai
"Jalila me kikeso ayi yanzu?"
"Kaci abincin, sannan ka dinga kulani"
Murmushi Jawwad yayi Wanda seda hakoransa suka fito yanayin yadda tayi maganar ya birgeshi matuka
"Baby meyasa baki daga wayata ba jiya da daddare for more than 30 minutes wayarki busy"
"Yasalam Yaya Jawwad Hanan ce fa kasan gobe in Allah ya kaimu zasuzo, ita ta kirani taketa min surutu labarin makaranta, Gida, da sauransu, muna gamawa siyama ma takirani, naso in kuma kiranka, se nayi tunanin kayi bacci ne,
Amma tuba nake yayana bazan kumaba insha Allah"
"Baby bazan iya fushi dakeba Sam, kawo abincin"
Jalal ji yayi kaman yasamu bulala ya zanewa Jawwad jikinsa, saboda bacin rai dama akan wannan, shugabar marasa mutuncin yake ta wannan fushin gaskiya Jawwad Dan wahala ne
Tea Jalila ta hada masa ta zuba doya da miyan sos ta bawa Jawwad
"Nagode sisyna, amma kinsan mu biyune yaya Jalal fa, shima a bashi"
"Ya jira Ilham in tazo ta hada ta bashi,"
"Kai Baby, meyasa hakane nida Jalal dayane, indai zakiyiwa Jalal haka nima zaki iya yimin"
"A gurinka ne daya ni..... Bata gama maganar ba
Kamar yadda yai mata jiya yanzunma Jalal zuwa yayi ya kwace na hannun Jawwad yai tafiyarsa kan kujerar da ya taso
"Yaya kana kallonsa ko?"
"To Baby ya zanyi indai bazaki bashi Abinci ba abun akaina ze kare, nawa ze karba ya cinye"
Zuciya Jalila tayi ta mike tareda fadin
"Ai sekuyi tayi,"
Murmushi Jawwad yayi sannan ya kalli Jalal
"Bros meyasa ba kwa jituwa da baby ne, why"?
" saboda bazan iya wannan shirmen da rashin aikin yinba, kalli saboda abunda be taka kara ya karyaba kake ta fushi, na dauka wani abun akayi maka, Ashe saboda wannan uwar rashin kunyan ne, shirme kawai"
"Allah yabaka hakuri, amma bazaka ganeba Jalal"
"Ameen naji bazan ganeba din"

Jawwad yagama breakfast dinshi ya tashi ya shiga cikin Gida suka gaisa dasu Abba, sannan yacewa Halima Dan Allah in Jalila tagama abunda take ga dakinsa nan a temaka a gyara masa daga nan yai waje domin tafiya makaranta
Ilham da kanta ranar tayi breakfast, bata bari masu aiki sunyiba, dukda ba wata kwararriya bace a fannin girki, tagama tayi kwalliya ta kai part din Jalal amma baya nan ta ajiye masa takoma dakinta, har gurin karfe Tara ba Jalal babu alamarsa, se zarya take koya dawo amma bata ganshiba
Halima taje daki ta sanarwa da Jalila sakon Jawwad
Nana ta kalleta
"Aifa ke yanzu kin kade haka zasu maida ke kamar baiwarsu"
"Nana kenan meye abun bauta a ciki,?"
"Tab lallai aikuwa zasu rainaki, tun yanzuma gashi, ke zakiyi musu girki, ki gyara musu daki, agaisheki nikam bazan iya wannan wahalar ba"
Jalila tayi murmushi
"Nana kenan, meye a ciki, duk abunda nayiwa Yaya Jawwad ko wani Wanda ya rabeshi ban fadiba, kaina nayiwa"
"Hmm Allah ya temaka, kema wataran zaki gaji Dan matsalarsu bata karewa"
"Ai bazan gajiba Hajiya Nana, kema gara kisaba gaba akeji"
Jalila ta mike ta tafi gyarawa Jawwad daki, ta tarar Jalal yagama karyawa ya bar kwanukan a gurin, ko tartare kwanukan guri daya beyiba
Jalila ta kalleshi ta kalli gurin da
Jalal ya bata
"Mtsewww Dan Allah malam in an gama cin abinci hade kwanukan akeyi ba a cinye abincin ciki a bajesuba,"
Jalila tafada a fili tareda kwashe kwanukan tai cikin gida, kodaga kai beba Balle ya kalleta
Ilham tagaji da jiran da Jalal, tasan dai baze wuce gidansu Jalal ba Dan haka ta dau mayafi ta nufi gidansu Nana, tana zuwa part din Jawwad ta nufa, kaitsaye Dan tasan baze wuce nan ba tunda motarsa tana Gida, taje ta tura kofar palourn
Jalal ta hanga a zaune a kan carpet din palourn Jawwad, da remote a hannunsa, shiga tayi cikin palourn da sallama ya Dan dago ya kalleta, ta karasa shigowa cikin dakin
"Ina kwana Yaya Jalal"
"Lafiya kalau"
Ta Dan gyara zama, "Yaya na hada maka breakfast ne shine.....
" da can ke kike hadamin?"
"A a Yaya amma....
" tsaya dama ina son magana dake, me kika cewa yarinyar da tazo nemana jiya"?
"Ni kuma?"
"Akwai wata a gurin nan bayan ke?"
"To aini jiya ban hadu da kowa ba"
"Nima rainamin hankalin zakiyi"?
"A a Yaya Jalal ni ba wata wadda tazo nemanka damuka hadu"
"Ilham wallahi zan tattakaki,
Sa anki ne ni? Nace me kika cewa Hannah jiya, nizakiyiwa karya!!!"
Hade rai tayi itama dan bata gane inda rainin hankalin Jalal na yau ya dosa ba, ta mike tsaye ta kalleshi
"Ni ban San mezance maka ba kuma, nagayamaka abunda nasani ni ba wata wadda muka hadu jiya, kasake dai tambayarta"
"Ni kike gayawa haka?"
"To me kakeso ince?"

Share please
More comments more typing...........................

Comments dinku nabani nishadi am proud of you masoyana masoya wannan littfi

🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️



[8/31, 8:30 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_
(2020)

_ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 38

PART 1
Share please

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa
ABDUL JALAL NOVEL FANS
Love u all guys ❤❤❤❤❤

-MY FIRST NOVEL-

Ransa ne ya kara baci ya kalli Ilham
"Ni kike kallo kike gayawa wannan maganar? Ke kinyimn laifi kuma ki tsaya kina gayamin magana, kuma uban wayasaki kika dagamin waya har kike zagin Wanda ya kirani? Kwana biyu kinga nayi sanyi shine kikemin rashin kunya ko?"
Mamakine yacika Ilham wannan wace kasurgumar makaryaciyar ce take mata sharri haka, to mema zatace masa ne
Maganar yaseera ce ta fado mata "kidena jin tsoransa"
"Au to kar in kare kaina, kana gayamin magana akan abunda bansan nayiba, sekuma inyi shiru wannan lokacin ya wuce Yaya Jalal nima nadena daga maka kafa ina kallonka kana min wulakanci, se wasu maganganu kake Wanda bangane inda suka dosaba, duk saboda kawai ina sonka, so fa ba karya bane ba, kuma ina nan akan bakana, duk macen datayi gangancin shigowa rayuwarmu senayi maganinta, ka dawo hayyacinka Dan ni......
Tas ya dauketa da mari, dafe inda ya mareta tayi, tana kallonsa
" ke kin isa ki tsaya a gabana kina gayamin abunda kika gadama, kinje kinyimn karya, kina cewa wai ban isa inyi abunda ba kyaso ba ke a wa? Wani matsayi kika taka a gurina da kike da wannan ikon,"?
Sauke hannunta tayi daga kuncinta, ta kalli cikin kwayar idonsa
"Matsayin kanwarka kuma masoyiyarka na taka, ka gayawa ita wadda ta gaya maka hakan, ta tinkareni ni da ita tayimin, ba wai ta koma bayan fage ba, kuma wallahi daga yanzu kadena jibgata a banza kasawa zuciyarka bashi kakeci seka biya wannan abun da kakemin, kuma wallahi indai ina raye baka da wata mata in baniba seka aureni, baka da imani Jalal ko sau daya yakamata ka dubeni da idon rahama, kodayake kai babu tausayi a zuciyarka"
Kuma harzuka yayi,
"Ni kike gayawa haka, ke wace irin Jaka ce da ba kya ganewa ana so dolene, bana sonki kuma bazan taba sonki ba, Jahila kawai fita kibani guri kafin in sauya miki, kamanni, kinsanni sarai bana son hauka amma kullum ke haukanki kara yawa yake shiyasa ko shirginki bana shiga fita dallah"
Tundaga waje Jalila take jiyo hayaniyarsu Dan haka da sauri takarasa,
ILHAM ta kalleshi sannan tace
"Jalal duk haukan da yake kaina be kai Wanda yake kanka ba amma na dage nakesonka a haka wani irin mutum ne kai"
Wani Marin yakuma bata,.yana shirin karamata ne Jalila ta shigo da air freshener a hannunta, zata gyara dakin Jawwad ganin abunda yake faruwa yasata rugawa da sauri ta shiga tsakanin Jalal da Ilham, ta janye Ilham baya, sannan ta kalli Jalal
"Wannan abun kunya kake aikatawa karasa inda zaka zage kwanjinka se akan mace, macen ma kanwarka, me yake damunka haka"
Daka mata tsawa yayi
"Matsa ki bani guri ko in hada dake, in tattakaki"
Itakam Ilham gefe tayi tana maida numfashi saboda taji zafin marukan da yayi mata,
JALILA ta kalleshi up and down
"To ka tattakanin mana ragon maza, karasa inda zaka nuna karfinka sekan mace, in karfi kakeson nunawa seka tafi gaidan dambe, jarumin namiji bada zuciyarsa yake yanke hukunciba da kwakwalwarsa dakuma hikima yakeyi, ba wai jibgar mace ba"
Kallon JALILA yayi idonsa cikin nata yana nazarin meze mata
Ilham daga inda take tsaye sukaji tace
"Wallahi Yaya kowace tayimin wannan sharrin idona idonta kagaya mata senaga bayanta, kuma Marin dakayimin bashi ka dauka, don ka dauki alhakina, niba wadda muka hadu jiya amma ka hukuntani akan abunda bani nayiba, duk laifukan nan ba Wanda nasan nayi maka kowace karya tayimin,
Tayi nasara wannan karon nima ta saurari abunda zan mata koma wace munafukarce dani take zancen wallahi" ta karasa maganar tana hawaye, se yanzu JALILA tagane inda fadan nasu ya dosa, amma ta juyo ta kalli Ilham
"Kekam Iska na wahalar dame kayan kara, kalli tun ba yauba kike shan wahala a hannunsa ya dakeki, ya zageki, sekace ubanki kekuma dayake zuciyarki kin Yar kare ya cinye se manne masa kike kumayi, ni banga abun mannewa a gurin wannan abunba"
Tafada tana kallon Jalal, wani irin huci Jalal yakeyi, yama rasa me yakamata yayi,
"Ke saurara, ba ruwanki a cikin rayuwarmu, uwar shishshigi, kuma ma inda Sa hannunki acikin abunda yake yimin zan baki mamaki wallahi,"
Ta daga jajayen idanuwanta ta kalli Jalal
"Wallahi Jalal wahalar dani din nan dakake shekara da shekaru, wallahi se ka biya duk randa kazo hannuna seka zubar da hawaye fiye da Wanda na zubar, zan fito maka a ainihin Ilham dina babu daga kafa ko ragawa tsakanina da kai, koni ko kai kokuma duk wani munafiki dake shiga tsakaninmu"
Yinkurowa yayi zeyi kan Ilham, JALILA takuma shan gabansa
"Dan girman Allah ka kyaleta"
Hannu daya yasa, yai wurgi da Jalila daga gabansa tayi gefe
Ilham kuma ta tsaya kyam taki tafiya
Tas! Tas! Guda biyu a jere
"Dan kaunar da kakewa manzon Allah karka kuma dukanta, jininka cefa, kanwarka ce, indai so yana zama laifi, Ashe wataran zaka iya rabuwa da Jawwad"
Cak ya tsaya be juyoba amma
Jalila tacigaba da fadin
"Kome tayi maka kishinka ne yasa tayi, baka tunanin alhakinta yakamaka ne, at least kaima ka sota mana koda irin na yan uwantaka ne kalli yadda ta.................
(Zancigaba da hakuri, har lokacin da burinmu ze cika akan JALAL da mahaifiyarsa)
Wannan kalaman da Jalila ta haba ji Ilham ta tabayi a wayane suka dawowa Jalila Wanda hakan yasa takasa karasa abunda tayi niyyar fada
Juyowa yayi ya nufo inda Jalila take, Ilham na ganin haka ta sulale ta gudu, yazo gaban Jalila ya tsaya
" meyasa ba kyajin maganane? Ke dole sekin gayamin me zanyi? Rayuwarki daban tawa daban, meyasa kike hakane, ke in dai baki shiga harkata ba ba kyajin dadi, meyasa ba kya ganewa ne, kinsan metayimin ne?
Ya karasa maganar cikin shouting, Dan

Please Login or Register in order to submit comment