Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yar uwata ce Jalila ma Yar uwata ce ta shi kibarmin daki"

Jalila kam taji komai duk zancen da sukayi taji a bayan kofa ta jingina jikinta tana zubar da hawaye me kona zuciya
Jiki a sanyaye tayi wanka tafito wankan dabata da tabbacin tafita

Tana fitowa Nana ta kalli Jalila cike da damuwa zatayi magana saboda tasan taji abinda Sa'ada tafada

Amma Jalila cikin karfin hali da dakewar zuciya tace
"Nanancy yau me za a girkamana ne ne yau?"

"Kinga Jalila Dan Allah.........

Jalila katseta tayi ta hanyar cewa
" yau muyi dambu kinsan mutumina ne amma Allah yasa kin iya Dan kinsan nafiki iya girki"

Duk yadda Nana taso suyi zancen maganganun da Sa'ada tayi domin tabata hakuri Jalila taki se ta basar da zancen

Jawwad kam yakada ya raya Jalal ya bishi suje masallaci yaki yace shi inyaje Gida yayi sallarsa
Haka Jawwad ya tafi massalaccin shikadai
Bayan yadawone yace bari yaje cikin gida yakuma duba Jalila Dan haka ya nufo cikin gidan

Nana ta kalli Jalila tace
"Maama kuwa tasan kindawo"?

"A'a naga tayi bakuwa shiyasa banjeba kar in takuramata" Jalila tabata amsa
" bafa wata bakuwa bace Yaya mairo ce yakamata tasan kin dawo ai "
"Hakane bari inje"

Yana shigowa palourn ya ga Yaya mairo da Sa'ada gefe ga Maama a zaune
"Yau manyan baki mukai kenan Anty mairo ina wuni"

"Eh kace haka mana yausha rabonka da gidana baka da zumunci Jawwad Sam wannan halin naka a dangin ubanka ka samo shi Dan mu bahaka muke ba"
Tafada cike da isa

Shikam har ga Allah Jawwad baya zuwa gidan yaya mairo dukda kasancewarta yayar mahaifiyarsa irin matan nanne masifaffu Wanda basa raina abin magana ga ta da mugun Sa ido kuma intana guri kawai so take abinda ta yanke shiza a yi ga shiga abinda ba ruwanta
Shiyasa Jawwad baya kaunar zuwa inda take yanzuma komeye na sako dangin babansa oho?

"To yanzu Dai Allah yabaki hakuri insha Allah hakan bazata sake faruwa ba insha Allah zaki dinga ganina har kigaji da zuwana"
"Kaji dashi dai"

"Maama ya jikin Jalilan kuwa?"

Ya fada cike da kulawa yana basar da zancen Yaya mairo

Maama ta Dan yatsina fuska
"Wace Jalilan kuma bayan wadda na baroku tare a asibiti "

"Maama to ai tun dazu muka dawo baki ganta bane?"

Har Jalila zata fita daga dakin "
Nana tace tsaya mutafi tare karki fadi a hanya"
"Hh Nana kenan yadda nake jina yanzu ko dambe zamuyi ai sena zaneki yi zamanki bari inje"
Dariya Nana tayi lallai kinji sauki

"Hmmm kingani ko dan Allah ji yadda yake wani nuna damuwa akanta jikar arna wallahi in baki wasa ba Zainab, yarinyar nan da uwarta se ta shanye miki ya'ya,
arna ba abun yadda bane karki tona sallar datake ganin idon mutane ne watakila a boye a can inda take ita da uwarta suna zuwa coci"

"Wlh nima bakiga wulakancin da Nana tayimin ba saboda wannan yarinyar hadda in fita in barmata daki"
Sa'ada ta tsoma baki, Sa'ada irin halinsu daya da uwata bata da kunya Sam
Daka ganta zakasan idonta a bude take fuskarta tayi Jawur saboda bleaching

Ran Jawwad ne ya baci matuka
"Haba Anty mairo wane irin cin zarafi ne wannan kuma hada mahaifiyarta wannan.......

" dalla rufemin baki sakarai Wanda besan me rayuwa take ciki ba ina magana kana gayamin wai cin zarafine, Yaya mairo ta katseshi a tsawace
Kingani ko Zainab kinga abinda nake fada miki ko kalli Jawwad ina fada yana fada saboda rashin kunya wallahi ki raba yayanki da waccan Yar arnan in ba hakaba wallahi wataran zaki gansu a church suma

"Kaga Jawwad ta shi kafita jeka"
Maama tafada tana nuna masa hanyar fita

Mikewar nan dazeyi yafita yaga Jalila a tsaye idanunta taf da hawaye alamun taji komai

Girgiza kai yayi yafice zuciyarsa a cunkushe ji yake kaman shi akayiwa wannan cin zarafin

Da gudu Jalila ta dawo daki ta shige bandaki ta rufe kofa
Abin yabawa Nana mamaki meyafaru haka
Kofar bandakin tafara bugawa a hankali
"Jalila meyafaru ne?"
Jalila ta daidaita nutsuwarta tace
"Ina zuwa"

"OK nagane inkin fito ga abincinki nan"
Nana tafada

Itakam Jalila gefen bath ta zauna ta dunga zubarda hawaye masu kona zuciya
Why meyasa akemin wannan cin zarafin nida ummina ake kiranmu arna naga dai ba Wanda zece kaf zuri'arsa tun saga farkonsu har karshensu musulmaine,

Ummi meyasa kika auri abina kika haifeni, tun tasowata dangin mahaifina kemin wannan cin zarafin har yanzu basu dena ba yaushe wannan abun ze kare,

Wasu zafafan hawayene suka cigaba da zuba daga idonta
Bata san tsahon lokacin data dauka a bandakin ba tana wannan kukan har tagaji ta fito,
Ta canza kaya ta dai daita nutsuwarta ta fito palourn,
Yaya mairo basu tafi ba

Nana tana parlour tana karanta wani English novel "the wish"
Maama kuma tana kitchen

Kaman kullum har kasa Jalila ta tsuguna
"Anty ina yuni"
"Lafiya "
Shine abinda ta fada a wulakance
Tashige dakin maama zatayi salla
Jalila kuwa seta nuna ko a jikinta

Nana ta kalleta
"Ashe Allah yayi miki fitowa daga bandakin, sekace me haihuwa kika shiga kikayi tsit"

Murmushi Jalila tayi
"To wayasani ko itan nayi"

Sa'ada kallon Jalila tayi a wulakance
Ta tabe baki
"A gurin arna haihuwar shege a bandaki ai ba sabon abu bane"
Sa'ada tafa da

A fusace Nana ta dago zatayi magana
Jalila ta rigata

"Aikuwa dai ba kunya sukeji ba tunda basa kunyar su raini cikin shege su Haifa su rains
wasu kuwa zubarwa sukeyi
Kinga, gara laifin arna Dana muna musulmi Wanda yasani ya take kodayake wasu ai sunan ana musulin cine ba asan ma'anarsa ba"

Tana gama fadin haka ta shige kitchen gurin maama
"Sannu da Gida maama"
"Yawwa ya jikin "

Maama tafada cike da basarwa
"Naji sauki akwai abinda zan tayaki ne"
"A'a jeki abinki"

A parlour kuwa Nana ce ta dingayiwa Sa'ada dariya tace gobe ma kikuma in baki yasan meze fada besan abinda za a mayar masa ba

Jalila kuwa daga kitchen din nan harabar gidan ta fito ta dauki kujera ta tafi gaban flowers ta zauna,,
Tanata tunani zuciyarta sam ba dadi, ga wani Abu da ya tokaremata a kirji Wanda tasan Bacin Raine, gashi rabonta da abinci tun Wanda taci da safe a asibiti Wanda Nana takawo mata dazu bataci ba ko yunwar bataji, saboda Bacin rai

taga hakan baze fishsheta ba dan haka tafara rera karatun Qur'ani cikin sauti me dadi

A hankali taji zuciyarta tana sanyi yanayin yayi mata dadi ga yammaci ga flowers din na dauke da furanni masu kyau Dan haka taci gaba da karatun cike da jin dadi da kwarin gwiwa

A hankali take jin taku ana tahowa inda take bata waigaba kuma bata dena karatunta ba

"Masha Allah "

Taji muryar Jawwad yafada seda ta kai karshen ayar sannan ta tsaya
Ko ba a gayamata ba tasan tare yake da mayennasa wato Jalal saboda taji kamshin turarensa
Gabanta ya zagayo ya tsugunna

"Dafatan ban katseki ba ya sayyada?"
Jawwad yafada
"A'a yayana, sannu dazuwa"
" cigaba da karatunki"

"Ai na idar dama Abeena nakewa Allah ya kaimasa ladan kabarinsa,
Babban abinda zamuyi idan iyayenmu na Raye shine muyi musu biyayya kar mu yadda muyi sa'insa dasu ko mudaga musu murya,
Fushinsu masifa ne a rayuwar mu, tunda bamu ISA mu biyasu ba dawainiyar dasukayi damu ba, in sun rasu kuma muyi musu addu'a saboda bamu da tamkarsu"

"Wannan gaskiyane sister lyk no other ina alfahari dake"

Lallai yarinyar nan kullum in muka hadu seta gayamin bakaken magana waini zatayiwa wa'azi
Kijira zakiga yanda zanyi maganinki a karo na gaba
Jalal yayi wannan maganar a zuciyarsa

"Jalila nasan kinji abinda Yaya mairo tafada amma Dan Allah.........
" shhhh ni banji komai ba Yaya kamanta kawai" Jalila tayi maganar tana murmushi

"Kai ni nagaji malam Kasan banason jira ka ta shi muje kabani abinda zakabani in tafi seka dawo ka cigaba da shirmen"

Hakan yayi daiยฒ da fitowar su Yaya mairo Maama tayo musu rakiya

"Zainab Dan Allah dubi danki kalleshi ga yadda ya gurfana a gabanta, kaman zata masa gafara wannan shegiyar yarinyar in baki da mataki akanta ba setasaki kika,
Wannan yaronnaki yadda yake rawar kai akanta seta dilmiya shi"

Jiki a sanyaye Jawwad ya mike ita kam Jalila sunkuyar da kai tayi
"Bahaka bane Anty mairo ina mata sannune"
"Ubanka kake mata ba sannu ba wadda kayi mata a asibitin bata isa ba sakarai kawai ka wani gurfana a gaban ta sekace uwarka"
Shikam Jalal tuni ransa ya gama baci yana kuma jinjina hakurin Jawwad da shine wallahi babu matar daze tsaya tana masa masifa haka

"Dan Allah Jawwad kaje kabani in tafi nagaji Kasan bana son tsayuwa kuma wannan matar tazo tanawa mutane hayaniya da shirme aka zata sawa mutane ciwon kai
๐Ÿ˜ฑ๐Ÿ˜ฑ๐Ÿ˜ฑ๐Ÿ˜ฑ
JALAL yayi maganar cike da masifa

"JALAL itama mahaifiya tace fa yayar maama ce"

Sakin baki Yaya mairo tayi tana kallon ikon Allah

Itakam Sa'ada ganin JALAL seda gabanta tayi mummunar faduwa

Maama tayi shiru saboda bata shiga shirgin abotar su tasan halin JALAL sarai

"To ni Ina ruwana kai ka taba ganin me uwa biyu
Dalla ka tsaya ana zaginka haifarka tayi meye na zaginka dan tana yar mamanka haka akeyi?"

"Wannan Dan iskan fa daga ina"
Yaya mairo tafada tana kallon Jawwad
"Emm da...

" magana nake maka kana kameยฒ nace wannan Dan iskan yaron Mara mutunci daga ina Zainab magana nake kunyi shiru kuna kallona"

Itakam Jalila silalewa tayi tabar gurin

JALAL yazo gaban Yaya mairo yatsaya "
fadi da kyau ni dan iska ne Mara mutunci, amma kinfini kama dasu tunda kema kin haifi dan iskan boye da bakowa yasan shiba

Dafa kafadarsa Jawwad tayi
"Bros Dan girman Allah kayi shiru mana Yayar uwata ai uwace ai yakamata kaimin kara" yafada jikinsa a sanyaye

"A'a kyaleshi yacigaba da zagina"
Tafada tana zare ido

Jalal ya kalli Jawwad

"a ganinka duk wannan ba kara nayi makaba,
kai kasan in wanine yagayamin haka da wani zancen ake ba wannan ba
Dalla cikani" ya fizge hannunsa yayi waje
Da kyar Maama ta lallaba Yaya mairo ta tafi se zageยฒ takeyi

Yau dai ansha drama a gidansu Jawwad


Jalal kuwa yana zuwa Gida dakinsa ya yatafi
"Mtseww munafukar mata waini ne Dan iska itama fa tanada yan iskan nan amma ta zageni, wallahi badan Jawwad ba da yanzu hakoranta se dai asaka ranar Samata na roba"

Haka yaita surutai shikadai wayarsa ce ta fara ringing
Dagawa tayi yasaka a kunnensa

"To ina zuwa"
shine kawai abinda yafada, ransa duk a bace yake yau, haka ya fito ya nufi cikin gidan




Ilham ce tai sallama ta kaiwa Jalila wayarta da ta Yar a gidansu lokacin data fadi
Sannan taga yamata cewar baban Jalal yana kiranta

"To Allah yasa ba laifi nayi masa ba"
"In munje kya gani"
Ilham tabata amsa

"Nana zo muje ki rakani"

"A'a aiki zatamin sekace za akamaki kije ki dawo"
Maama tayi maganar a takaice




Daddynsa ya tarar da mummy a zaune ba sallama balle gaisuwa fuskar nan ba fara'a
"Daddy gani"

"Yawwa Dan albarka dama magana nakeso muyi, mummynka tace ka dena zuwa makaranta, kuma wai Dubai zaka tafi? Ya akayi ne?"

Wani mugun kallo yai wa mummyn

"Eh hakane Dubai nakeso in tafi"

"Karatun fa mummy tafada a fusace

" bazanba" yabata amsa

"Kaji ko? hakafa nake fama dashi bayajin maganata baya ganin girmana,
Wallahi Jalal kar ka bari ka mutu baka dena abinda kake kana sabamin ba"

Su Jalila tun dazu suka shigo suka tarar ana wannan fafatawar

Mikewa yayi ya nufi hanyar fita yana masifa idonsa Jawur

"Ni akayiwa laifi ni yakamata anemi yafiya kece silar komai amma kin rufe idonki laifina kawai kikegani ni akayiw laifi kuma kece kika jamin duk wata kalar rayuwa Dana keyi"

JALAL Yayi maganar cikin karaji

"Bazaka taba canzawa ba, ba adagawa iyaye murya, ba a sa'insa dasu
Amma kai hakan ba komai ne a gurinka ba, ta Yaya zakaga haske a rayuwarka
Se mutane sunce Baka da tarbiyya kaji haushi, anya kanaso kagama da duniya lafiya?"
( Jalila kenan damusar kwali ga tsoro ga ban tsoro)

Aikuwa gadanยฒ JALAL ya nufi inda take idonsa babu alamar tausayi..

Share please

More comments more typing...........



๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š
[8/31, 8:26 AM] Safiyya: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

_ABDUL JALAL_
(2020)

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 9

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
What's https: //chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Is a free book

Ina yinku AbdulJalal novel fans irin๐Ÿ’ฏ๐Ÿ’ฏ๐Ÿ’ฏ da duk sauran masoya wannan novel ina jin dadin comments dinku love u all โคโคโค

I want comments not stickers or just thanks๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ข
Your comments give me courage

Wannan yarinyar kwai bakar Jarababbiya kome za ayi mata bazata dena magana ba in taga abin magana, kozaka kasheta setayi magana

Kallon ta Jalal ya cigaba dayi yana jinjina bakin taurin kai irin na Jalila

Itakam Jalila dariyarta ta cigaba dayi
"Tab wai akan wannan kike wannan kukan aiki yasamu wata, tab sannufa Ilham kin dorawa kanki wahala wallahi....."

Jalal kallon Jalila yayi cike da takaici
Jalal girgiza kai kawai yayi ya fice saboda ya fuskanci in yacigaba da biyewa maganganun yarinyar nan to tabbas bakin ciki ze iya masa illa

"Jalila meye hakane wai ina ruwanki dasu taho mu tafi"
Nana tai maganar tana janyo hannunta

"Munafukar banza kawai se tsabar shishshigi da Sa ido aikin banza kawai"
Ilham ta fada tana jujjuya Ido

Saboda cusa takaici se Jalila takara tuntsurewa da dariya

"Allah ya temaki matar Dan giya wannan soyayyar kaman a Bollywood ke kinga wani hawaye kaman ta tsaya agaban director hh mrs. Jalal"

"Na shiga uku nikam Jalila meye haka wai dama haka kike ba dadi fa
Ni dai taho mu tafi"
Nana ta fada tana kuma Jan hannun Jalila

Ilham kam rasa bakin magana tayi kamewa tayi tarasa abin cewa

Suna fitowa Nana ta kalli Jalila cike da damuwa
"Haba Jalila why? Abinda kikayiwa Ilham be dace ba wallahi bazataji dadi ba"

"Lallai Nana ke bakiga wulakancin da tayimn da farko ba har munafuka tacemin fa"

" haba Jalila da baki kulasu da bazata gaya miki ba "
"Sorry Nanancy kinsan bana gani inyi shirune kawai, in ta kwantar da hankalinta gobe insha Allah zan bar garin nan"
"Jalila dena tunamin banason tuna gobe in Allah ya kaimu zaki tafi duk se inji na damu"
Nana ta fada a sanyaye
"Nima banason barinku amma very soon zan dawo insha Allah"
"Allah yasa da gaske kike"
"Da gaske mana"

Dayake me Hali baya fasa halinsa sukaga Jalal a harabar Gidan yana kokarin bude motarsa

"Wai akan wannan ake kuka, Allah ya kyauta, har ake Neman a zageni gaskiya Ilham Yar wahala CE"

"Na shiga uku ni Nana, Jalila haka kike dama?"
"Ai ni nafi haka ma duk abinda nasan ba a so ko akemin gadara akansa to nikuma shi nakeyi"

Jalal da ya riga ya shiga mota yana jinsu dayake suna daf dashi tayi maganar shiru yayi bece uffan ba
Sema kokarin tada motarsa da yake

Washe gari da safe Jalila ji take kaman za asa ta a Aljanna yau zata koma gida gurin umminta,
Kuma zata rabu da wannan mugun, kuma se yaya mairo taganta zata kuma cin zarafinta,

se shirinta takeyi amma lokacin kanta yana mata ciwo tunda Jalal ya mareta kanta kemata ciwo

Nana tana wanka Jalila ta hada kayan ta cif Jawwad


ya shigo dakin yasameta tana kallon akwatin ta

"Yar gidan Ummi kingama shirin kenan?"
Jawwad yafada yana zama a gefen gado
"Eh Yaya nagama"
"To insha Allah in an sakko daga masallaci zamu tafi kizama cikin shiri in ma dawo zamu tafi"
"Aini ko yanzu kace mu tafi na shirya,"

"Eh kyace haka saboda kin gaji da zama damu ko?"
"A'a nifa nace muku bahaka bane"
Ta fada a shagwabe

"To shikenan naji kar kimin kuka"
Jawwad yayi maganar da sigar tsokana
Daga nan ya tashi ya tafi

Bayan fitarsa da ba dadewa Ilham ta shigo hannunta dauke da ledar bagco, ta tarar da Nana da Jalila su suna cin abinci suna hira

Jalila tana ganinta ta sunkuyar da kai tana dariya kasaยฒ
"Mtseww"
Nana taja uban tsaki ta direwa Jalila bagcon a gabanta "gashi nan Inji mummy, sakon daddy ma yana ciki"
Ta fada tare da juyawa zata tafi

"Haba Ilham kya tsaya kuyi sallama fa yau zata tafi"
"Ta sauka lafiya "
Shine abinda kawai Ilham tafada tai ficewarta

Itakam Jalila ta kudure a ranta seta tsokani Ilham amma tasan in tayi a gaban Nana mita zatayi mata Dan haka se cewa tayi
"Nana ina zuwa"
"Ina zaki?"
"2mint yanzu zan dawo"
Ta biyo bayan Ilham se ta hangeta ta tsaya tana waya a wajen flowers din gidan
Seta nufi inda Ilham take amma kafin takarasa taji tana waya

"Wallahi mami nafara gajiya wulakancin yau daban na gobe daban Sam Hankalinsa baya kaina jiyama bakiga wulakancin da yayimi ba am tired wallahi"
Jalila Batajin me akace daga daya bangaren

"Hakane mami, Allah ya nuna mana lokacin da burinmu ze cika zan cigaba da hakuri in cigaba da kokari se burinmu ya cika akan Jalal da mummyn Sa"

Buri kuma, Wane irin buri ne haka hasashe na ze zama gaskiya kenan
Jalila tayi maganar a zuciyarta
Fasa abinda tayi niyya tayi takoma cikin Gida

Kayan da aka aikomata daga gidansu Jalal taga Nana tana budewa
Less ne me kyau da agogo se turare da wani Dan karamin kit Ja anyi rubutun larabci a jiki Qur'ani ne izu sitting a ciki me matukar kyau
Se envelope da akasaka kudi dubu goma
A jiki aka rubuta
safe journey from daddy

"Yanzu duk wannan nawane?"
"Ai Jalila indai kyauta ne babansu Jalal akwai kyauta yana da kirki sosai"

"Nana ni duk Qur'anin nan yafi min kyau bazan dinga bude shi ba ajiye shi zan in dinga kallonsa yayi kyau sosai ajiya zan masa me kyau"

Nana ta kwashe da dariya
"To ai saboda ki karanta akabaki shi sekuma yazama abin kallo"

"Eh mana koba komai zan dinga tuna baban zalimu ne yabani"

"Me kikace Jalila?"
"Ba komai, bari inje in nunawa maama kayan"

Zuwa sukayi suka nuna mata ba fuskarta ba yabo ba fallasa tace yakamata taje tayi musu godiya
Sannan itama tabata abinda zata bata
Abba yayi mata nasiha sosai sannan yace university a kano zatayi in lokaci yayi zezo a Dakota daga Kaduna
Jalila ko a jikinta bata dauki abun serious ba ita dai babban burinta taga sun kama hangar Kaduna
haka yaimata alheri shima tare da yimata nasiha akan hakuri da rayuwa ta kula da tarbiyarta sannan tayi karatu.

Misalin karfe biyu tagama shirinta tsaf JAWWAD kawai take jira
after dress ce a jikinta baka se mayafin After dress din data yafa akanta tayi kyau matuka

Taje gidansu Jalal tayi musu godiya
Daddyn Jalal shima haka yayi mata nasiha tai musu godiya ta fito taga Ilham ta dawo maybe wani gurin taje

"Juliet INA romeon naki,?
Tafada cike da tsokana
Nikam yau zan koma inda na fi wayo nasan na bata miki a Dan zaman damukayi kiyi hakuri Ilham ni duk abinda na miki wasa ne"

Mtsewww Ilham taja wani dogon tsaki
"Ke kikasani ma gulmaciyar banza kawai"
Ilham ta fada tana ma Jalila kallon up and down
Jalila tayi wani kasaitaccen murmushi

"Nagode Yar wahala nice ma ke, let me tell u something ur mission will fail u will never succeed"
Tafice daga gidan tabar Ilham tsaye tana juya maganar Jalila
"Ur mission will fail"

A harabar gidan taga Jawwad da mayensa
Jawwad yasamata trolley dinta a boot
Jawwad na ganinta yace
"Masha Allah looking so gorgeous sisyna let's take a pic"

Kusa dashi Jalila taje ta tsaya sukai ta hotuna hada Nana

Shikam gogan wani uban tsaki ya dinga Ja ganin yadda JAWWAD yake biyewa wannan fitsararriyar yarinyar

Nana ce ta rungumo Jalila tana share kwalla "Dan Allah kikuma dawowa"
"Insha Allah karki damu Nanancy na zankuma zuwa insha Allah"

Suka shiga Jalila suka kuma sallama da maama sannan ta fito

Jawwad ya Riga ya shiga ya kunna mota yana jira ta karaso ta faki idon Jawwad
Tacewa Jalal to yau zan tafi se hankalinka ya kwanta bame kumayi maka shishshigi amma zan tuna maka ne ban yafema cin zalina da kaiba mugu kawai kuma insha Allah se......
Bige mata baki yayi
"Ki barni da Wanda akayi min a baya yake wahal dani, in kika sake kikamin mummunar addu'a a sena baki mamaki
A cikin gidan naku a gaban yayan ki zan tattakaki in koya mini hankali dama namiki alkawarin maida ke Irina amma tunda tafiya zakiyi yayanki zan mayar Irina, in ya aureki se aji dadin fada matar Dan giya

wuce ki bani guri ko in barar dake anan Mara kunya shaยณ"

Kaman munafuka haka ta wuce tana shafa baki taga ko Jini ya fito

Nana tafito da karfi race
"Jalila safe journey I will miss u"

Daga mata hannu kawai Jalila tayi ta shiga gaban motar saboda bakinta ji take kaman banata ba
Jalal ne yazagayo inda Jawwad yake dan uwana a sauka lafiya, ka dawo da wuri Dan Allah, akwai wani zazzafan guri dazaka rakani
Jalila ta dago da sauri tana kallonsa
Allah ka tsaremin yayana

"Ta Allah bataka ba "
Tafada a fili
"Ya dai magana kike ne"
Jalal yai mata tambayar

"Bakina ne a haka tabashi amsa"

"Na fuskanci dai ba kwa jituwa, Jalal ma fa yayankine"
Jawwad yai magNar yana kallon Jalila
"Allah ya kiyaye"

"Dan uwana ina dawowa zan raka ka insha Allah idan na dawo"
Jalal yafada yafara Jan mortar

"To seka dawo"

Sun hau kan kwalta sosai Jawwad tuki yake a hankali cikin kwarewa
Jalila tayi nisa cikin tunani

"KE YAKAMATA KINEMI YAFIYATA , DUK WANI ABU DANAKE AIKATAWA KECE SILA,
KINSAM GASKIYA AMMA KIN RUFE IDONKI KINAMIN FADA"

"ZANCIGABA DA HAKURI HAR BURINMU YA CIKA AKAN JALAL DA MUMMYN SA"

"KARKI SAKE KIMIN MUMMUNAR ADDU'A KIBARNI DA WANDA AKAYI MIN ABAYA YAKE WAHAL DANI"!!!!!!

Gaskiya akwai abubuwa masu rikitarwa game da rayuwar Jalal haka nan taji tana son Sani

" sisyna"
"Na'am yayana"
"Nasan abinda yasa kikeson komawa gida, yana da nasaba da abinda Yaya mairo taimiki, Amma Dan Allah kiyi hakuri ki dena bari irin wannan maganganun suna tasiri a zuciyarki kowa yasani dagake har Ummi mutanen kirki ne
Ni kaina banji dadinin abinda tayi ba"

"Yaya na nifa ba hakane yasa zan koma Gida ba kamanta kawai"
"Kin tabbata?"
"Eh na tabbata babban Yaya"
"To yanzu se yaushe zaki dawo?"

"Se wataran"
"Se wataran kuma ba rana kenan"
"Hhh da wataran zan dawo"
"Hmm to shikenan"

Shiru ya Dan ratsa
"Yaya Jawwad"

"Nana'am Anty JALILA"
Murmushi tayi
"Wadan dan Allah wace Ilham a gurin Jalal"

"Yaya JALAL dai shima yayanki ne"
Allah ya kiyaye Amma a fili se tace
"To naji zan dinga fada"

"Yawwa sisyna
Yadda muke dake cousins haka ILHAM take da Jalal da mummyn Jalal da mamann ILHAM ubansu daya
Gyada kai Jalila tayi
" to meyasa Jalal yake haka, meyasa kuma ka





ke abota dashi,? Gashi ya raina mamansa kaga abinda yake mata kuwa?
"JALAL ko?"
JAWWAD yafada yana kallonta
"Au namanta Yaya JALAL"

Ajiyar zuciya yayi yace

"Se randa kika dawo kano zan baki amsoshin tambayoyinki"

"Why not now?
Ta tambayeshi

" kawai sekin dawo Kano zan gaya miki ke dai in kinyi sallh kidinga Sa shi a addu'a

Gyada kai kawai tayi

Amma a ranta cewa tai tabdij nida kano ai seda wani babban dalili
A gefe data kuma zuciyarta na kwadaita mata son sanin waye Jalal



Share please


More comments more typing.......

Aimin afuwa page din yau bashi da yawa am busy that's why

Naji shiru ba akawon ragon salla ba
In ba abani ba nadena typing se bayan salla lolz๐Ÿ˜‚

Inayinku masoya wannan novel irin sosai din nan โคโคโค comments dinku na kayatarr dani
Ku biyoni a hankali domin ganin darrusan dake cikin littafin













๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ
[8/31, 8:26 AM] Safiyya: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

_ABDUL JALAL_
(2020)

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 8

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
What's https: //chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Is a free book

I want comments not stickers or just thanks๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ข๐Ÿ˜ข
Your comments give me courage

I dedicated this page to you sister like no other
Saddika Adam (baby)
can't love u less
But stop asking silly questions if not zan hadaki da JALAL lolz

_My first novel_

Aimin afuwa
Today's page is
Not Edited

Gadanยฒ yanufi inda Jalila take,
Kasa kwakwakwaran motsi Jalila tayi, ta kuramasa ido jira kawai take taga hukuncin daze mata
kawai se ya canza shawara ya koma ya fice daga palourn

Ajiyar zuciya Jalila

Please Login or Register in order to submit comment