Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aliyu ana kiranta inna mairo amma ita se dai tace mata mama

Malam ya tsaida ranar daurin auren maryam da Aliyu sati biyu
Usman shi ya hadawa Aliyu lefen da aka bawa maryam itakuma tace ai tana da kayan sawa
Inna mairo tace mata wannan itace Al'adarmu ana hadawa mace kayan lafe abata

A lokaci kankani mutan gidan nan suka saki jiki da maryam ta shiga ransu saboda tsabar nutsuwa da biyayya gashi kullum tana tare da Jawwad yaron yana sonta wataran hada JALAL in an kawo shi,
amma banda Zainab wadda ba ruwanta da ita
yan gidansu Zainab musamman sukazo don ganin maryam suka dinga Yar mata da bakaken magana yayarta wadda suke cewa Yaya mairo ta dinga ziga Zainab,
"Ba ruwanki da ita kuma karki kara yadda danki yaje inda take don arna mugayen kazamai ne gasu da asiri na bala'i dan haka ki rike kanki karki bari a mayar miki d'a da irinta dan wannan tuban nata be kai zuci ba mumafuka CE yaudararku kawai takeyi"
Haka sukayi ta zigata sannan da yamma suka fito zasu tafi suka tarar maryam tana wanke² a tsakar Gida

Se Yaya mairo ta waigo ta kalli Zainab
"wai ya sunan ta ne"
Ta tabe baki
"Wai maryam" Zainab ta fada a wilakance

"Kutt dan wulakanci sunana aka samata"
Itakam maryam tana ganinsu ta fara murmushi
"Sister zaki tafi ki gaida gida Allah ya kiyaye hanya mungode"
Tai maganar tana dan durkusawa
"Au dama ta iya hausa, tab wai Allah ya kiyaye Ashe tasan Allah"
Yaya mairo tafada tana wani kebe baki
Da maryam ta fuskanci wulakanci zasuyi mata seta cigaba da aikinta
"Tab an baro iyaye an fake da za a musulinta an ta ho bariki,
Allah dai ya kiyayemun kanwata"
Ido taf hawaye maryam ta dago tana kallonsu
"Meye kuma na kura mana ido to indai kurwarmu ce kwalelenki dangin maita, banda jaraba wannan kanin mijin naki yarasa wadda ze aura se tubabbiya tir"
"Nawa ubanki yabani gudunmuwar auren da zanyi?"
Sukaji yo muryar Aliyu dama shi ba sabgar matar wansa yake shiga ba saboda ya fuskanci bata da mutunci ita da yan gidansu
"Zainab bari in gaya miki wani abu guda daya tunda iyayena suka karbi maryam banga matar da ta isa tazo tana zaganmin mata ba muddin kika kuma kuskuren zaginta zan baki mamaki munafukan banza kawai marasa tarbiyya"
"Noorat aje wanke² kikoma daki rabu da su jahilai kawai"

Lokaci² maryam kanyi kuka inta tuna da iyayenta tana kewarsu

Yayinda ya kasance bangaren iyayen maryam ma haka mamanta kullum setayi kukan bakin cikin rabuwa da yarta kullum cikin tunanin Allah yasa kar yarta ta fuskanci kalubalen da ta fuskanta a gurin al ummar hausawa ubangiji yasa tana hannu nagari.

Ranar wata juma'a bayan sallar juma'a aka daura auren Aliyu da kuma maryam
Malam imam shi yayiwa maryam kayan daki yayinda Usman shi yabiya kudin sadakin maryam
Suma aka basu guri a cikin gidan ranar maryam bakinta kasa rufuwa yayi ji take kaman mafarki waita mallaki Aliyunta
Haka rayuwa tacigaba da gudana yayinda maryam ke fuskantar wulakanci daban² daga bangaren Zainab, danginta, kawayenta da kuma sauran yan unguwa
Ko ruwa maryam ta sha da Kofi Zainab bazata kara taba kofin ba datayi abu zata fara cemata tubabbiya ta baro danginta ta taho yawon ta zubar indai Jawwad yaje inda take har dukansa takeyi amma kullum shida Jalal suna manne da maryam
Maryam bata taba kulata ba, ita soyayyar da Aliyu da iyayensa suke mata yafiye mata komai dayake Allah besa ta samu haihuwa da wuri ba
Aliyu ya maida ita makaranta takuma yin waec bata samu admission ba dan haka se ta shiga poly ta karanta catering
Rashin haihuwar da batayiba ya dameta matuka Aliyu ke kwantar mata da hankali, yana cemata gasu da Jawwad ga Jalal suma yayan sine
yayinda Zainab take cewa tunda an saba zubar da ciki sannan akai aure ya za ayi yanzu asamu haihuwa tunda angama barar da kwayayen a titi sannan aka tsallako aka taho wai an tuba,
Itakam maryam bata tanka mata, se dai in Aliyu yaji yazo ya kare mata tas,
malam imam ya sha Jan kunnen Zainab akan wannan abubuwan data ke wa maryam amma bata fasa ba dan ba kunyace da ita ba.
Katsam maryam tasamu ciki ta fara laulayi tayi farinciki sosai da wannan cikin dukda kasancewar cikin na wahalda ita Aliyu shiyake mata komai har cikinta ya fara girma sannan tasamu sassauci
Amma bangaren cin mutinci daga yan uwan Zainab da sauran yan unguwa se abinda yayi gaba yayinda
Zainab ta dinga cewa watakila ma cikin bana Aliyu bane cin zarafi daban²
Babban bakin cikin Zainab maryam bata kulata kome zatayi

Wata tara cif Allah y sauki maryam lafiya ta haifi ya mace me matukar kyau kamanta daya da Yaya mairo kalar Fulani sosai

Tunda aka haifi yarinyar nan JAWWAD da JALAL suka zama yan raino JALAL baya tafiya Gida kullum yana manne da jaririyar nan,
JALAL Ya dinga bin Aliyu yana cewa Abee (yanda JAWWAD take kiransa) yana cewa dan Allah Asama jaririyar JALAL dariya Aliyu ya dinga yi yana cewa JALAL kataba ganin ansawa mece sunan maza
Shidai ya dage asawa babyn sunansa
"Kar ka damu yarona ko dan kaunar da kakewa dana Jawwad zanyima yanda kakeso"
Ranar suna ta zagayo akasawa jaririya suna Jalila
Watan Jalila 3 Zainab ta haihu itama ta haifi ya mace lokacin Jawwad yana da shekaru Tara
Ranar suna akasama yarinya Nana Fiddausi sunan Jakarta
Nana da JALILA suka tashi kamar yan biyu
Jalila ba abinda ta bari bangaren halin mahaifinta na fada da Neman magana in tafita bata da aiki se Neman magana da cin zalin yayan mutane, sukuma iyayensu su kamata su daka tare da yimata gorin Yar tubabbiya jikar arena
Abin yana bakantawa maryam da shikansa Aliyu maryam ta dauki son duniya ta dorawa Jalila in dai aka taba Jalila ji take har cikin zuciyarta amma se ta kauda kai,
A cikin Gida ma Maman jawwad yimata take ko Yaya Jalila ta kwace Abu a hannun Nana, in dai Nana tayi kuka Zainab ta dinga zage² kenan tana cin mutuncin maryam
Wata rana hakan ya kuma kasancewa inna mairo bata nan, Jalila tasaka Nana kuka Zainab kuwa ta wankawa Jalila mari sekace sa'arta, Jalila seda ta fadi tana kuka, sannan Zainab ta dinga zaginta tana cemata Yar gaba da al fatiha jikar arna

"In kika kuma sheganta min yarinya zan baki mamaki dukanta ne kiyi tayi kezaki ji kunya dan anjima tare zasu cigaba da wasa kuma ko kinki yan uwanta ne"
Maryam ta fada tanaama Zainab kashedi

"Na fada Yar gaba da alfatiha Yar arna ai ba karya nayiba, kuma Ya"ya na daban ita daban su duk danginmu musulmine tun daga farkonmu har karshe"
Murmushi maryam tayi

"Kina bakanuwa kike cewa kaf zuri'arku musulmine watakila ma hada kakanki ake zagaye Dala tsirara kinga watakila garani damuke kiristoci akan Wanda suke bautawa tsunburbura
Jahilar banza se fadan musulinci abaki amma ke babbar Jahila ce manyan sahabban manzon Allah salallahu alaihi wassalam a cikinsu wasunsu bautar gunki sukayi amma daga baya suka zama manyan hadiman musulinci babu banbanci a musulinci annabi be taba kyamatarsu ba"
(Kunsan me hakuri be iya fushi ba)

"Nice kakana ya zagaye Dala tsirara"
Zainab tafda tana nunkanta da yatsa
"Au tambayata kike kina bakanuwa wata kilama shine barbushe"
Maryam tabata amsa
Ana haka Sega Yaya mairo sunzo ta Tarar ana wannan rigimar
Sukazo suyiwa maryam taron dangi Sega Aliyu ya dawo ba shiri suka watse don suna tsoronsa yanayin fuskar maryam ya nuna masa akwai Matsala dan haka da suka shiga daki
Ya kalleta "noorat meyake damunki ne, gayamin me ya faru"
Batai aune ba se taji hawaye

"Habiby bana jindadin yadda ake treating baby(JALILA) ana mata gorin wai ita Yar arna CE ga baby da Neman magana aita zaginta nafara gajiya nafara rama mata am tired suma dasukazo a musulmi ai ba dabarar su bace"
Ta karasa maganar cikin kuka
Ajiyar zuciya yayi
Ya janyo ta jikinsa yana share mata hawaye
"Tunda naga wannan matar tazo nasan a Rina maybe itace ta taba minke, kiyi hakuri Nima abun yana damuna amma kibani dan lokaci wani mataki nake shirin dauka"
"My love wani matakin zaka Dauaka AbU ya Riga yazaga gari"
"don't mind u will see"
"To shikenan bari naje na wanke mana kaya"
"Just relax baby zanyi mana, yanzu ki huta kawai"

Bayan wani dan lokaci Aliyu ya nemi aiki a Kaduna ya kuma samu aikin sannan ya nemawa maryam admission a ABU Zaria
Malam yayita fada dan meyasa ze bar Gida ya koma wani gari da bashi da kowa

Yaiwa malam bayanin yana tsoron abunda ya faru da mahaifiyar maryam itama ya faru da ita a dalilin cin zarafin da ake mata kar itama ta karaya ta koma cikin ahalinta ta koma addininta na baya, haka malam ya yadda badan yaso ba
Usman ma da inna mairo sunyi bakin ciki nesa da Aliyu ze yi dasu tun tasowarsu suna tare amma yanzu ze tsallake ya barsu

shima Aliyu ba a son ransa ba sedan samun nutsuwar matarsa da kuma kare mutuncin iyalansa daga wannan kyama da cin zarafi da ake musu ze bar gidansu da yan uwansa
Haka ya tattara matarsa da yarsa suka koma Kaduna inda ba Wanda yasansu
Su Jawwad ma har kuka sukayi dukda sun fara girma lokacin baban Jalal yana ta shirin kaisu boarding school Jawwad da Jalal in zasu shiga Jss 1

Akasaka Jalila a makarantar Islamiyya da zamani halin Jalila na Neman magana yana nan bata denaba
yayinda maryam ke zuwa makaranta kuma take taba kasuwanci
Aliyu ma aikinsa yake yana samun rufin asiri dai² gwargwado har ya mallaki gidan kansa
Hankalin maryam ya kwanta sosai yanzu ba Wanda yasan asalinta balle yayi mata gori
Lokaci² suna zuwa kano su gaishesu Usman ma yana zuwa ya dakko Jawwad Jalal da nana yazo dasu amma koda wasa Zainab bata taba zuwa inda suke ba

Bayan shekaru biyu da dawowar Aliyu Kaduna Allah yayiwa malam imam rasuwa
Sunyi bakin ciki sun shiga tashin hankali ba kadan ba sunyi kuka har suka hakura
Bayan rasuwar ne Zainab ta hurawa Usman wuta cewar tunda yana samun kudi sosai tun da har kasashen waje yafara fita kan harkar
Kasuwanci, dan haka dole Suma subar gidan nan dan be kamata ace kamarta tana zaune a wannan Gida ba Usman yayita nuna mata saboda inna mairo karsu barta ita kadai gashi ta Riga ta saba da unguwar, amma Zainab ta rufe ido taitamasa fitina
Haka yaje yasamu inna mairo da zancen ta shi daga Gida tace ba komai ita subarta anan su su tashi,
Amma yaki yadda, wataran inna mairo ta ta shi da amai da gudawa aka kaita Asibiti ta galabaita matuka dan haka Usman ya kira Aliyu ya sanar masa da safe
Be dau wani lokaci ba Aliyu yayo kano dan maryam bata San ya tafi ba
Se bayan la'asar kawai setaga Usman yazo yace mata su shirya kano zasu tafi,
"Me zamuyi a kano INA abu Jalila"?
" shima yana can"
"Dan Allah abban Jawwad in wani abu ne yake faruwa ka gayamin"
"Babu komai inna CE ba lafiya"
A kidime ta shirya ita da Jalila suka yo kano
Kai tsaye Asibiti suka nufa inda ya kaisu wani daki
Tana shiga Aliyu ta gani a kwance akan gado rai a hannun Allah jini na fita ta hanci ta bakinsa gashi ko kwarzane babu a jikinsa amma da yayi numfashi ze gudan jini ta hanci ta bakin......

Share please

More comments more typing

Ina amfani da wannan dama domin mika barka da sallaha layya ga al ummar musulmi a duk fadin duniya sekuma Allah ya kaimu bayan salla
Saura aki bani naman salla

Love u all
Abduljalal novel fans
❤❤❤❤❤❤


🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊
[8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_
(2020)

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 13

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Domin joining group dina follow this link
What's https: //chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Is a free book

Ina yinku AbdulJalal novel fans irin💯💯💯 da duk sauran masoya wannan novel ina jin dadin comments dinku love u all ❤❤❤

I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢
Your comments give me courage

Ina amfani da wannan damar gurin mika sakon barka da sallar layya ga dukkan al ummar musulmi
Ubangiji Allah ya maimai tamana

-my first Novel-

Da sauri maryam takarasa bakin gadon da Aliyu yake kwance yana ta fidda jini ta hanci tabaki ga wani wahalallen numfashi da yake saukewa da kyar, da gudu take ta zube a gabansa
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Aliyu meya sameka haka"
Shine abinda maryam tafada cikin kuka
Jalila ma da gudu ta tafi gurin abbanta cikin karfin hali ya rungume Jalila tareda janyo maryam kirjinsa
"Noor kiyi hakuri na taho kano ban gayamiki ba Usman ne yakirani jikin innarmu yayi tsanani shine na taho muka samu accident a hanya"

"Sannu abu Jalila Dan Allah ka warke ka tashi mucigaba da rayuwa u are my life habibi"
"Is not complicated dear kawai internal injury ne kuma likitoci zasuyimin aiki zan warke insha Allah
Dama haka kike matukar sona noor irin wannan rikicewa haka I love u too my dear u mean a lot to me maryam"

Yafada cikin karfin hali da son kawar wa da maryam damuwa
"Abu Jalila is not time for joke lafiyarka tafiyemin komai nikam, inaso mu rayu tare kacigaba dabani farin ciki nida baby Kaine garkuwarmu kai ka dai ka ragemin "
Tafada tana zubda hawaye

"I love u too ummu Jalila, kije kuduba inna se ki turomin Dan uwana zamuyi magana"

Harta yunkura zata tashi
"Maryaman Aliyu"
Ya kira sunanta dawowa tayi ta zauna ta kuma riko hannunsa

"Dan Allah ko bayan raina kar abinda matar usaman take miki yasa ki raba zumuncin dake tsakanin yayanmu"
Gyada masa kai tayi sannaan
Ta mike jiki a sanyaye ta nufi kofar fita,
Usman yana waje a bakin kofa yanajin duk hirarsu gwanin ban tausayi, haka usman ya dinga share hawaye kaman karamin yaro
Jiki a sanyaye Tafito daga dakin Usman ya nuna mata dakin da aka kwantar da inna
Usman ya koma dakin da Aliyu yake yaje gaban gadon Aliyu ya zauna ya riko hannunsa

"Dan uwana ya jikin naka ya kake ji yanzu"
"Yayana mutuwa zanyi bazan rayuba inaso in barmaka amana ne da duk duniya bame rikemin se kai"
Aliyu ya fada yana Jan numfashi da kyar
Yacigaba da cewa

"Dan Allah karkabari babyna tai kukan maraici, ko aure maryam tayi ban yadda ta tafi da yata agolanci ba, inason baby tayi karatu me zurfi, na addini Dana zamani
idan ta isa Shiga Jami a inaso takoma hannunka kasan tarbiyar ya mace seda tsayayyen namiji,"

Yayi tari jini yana fitowa daga bakinsa
Usman ne yake share masa jinin yana masa sannu,
Sannan ya cigaba da cewa

"Kar kayi yinkurin raba baby da maryam yanzu, seta isa shiga Jami a nakeso takoma hannunka, sannan ka tabbatar in baby ta girma maryam takoma garinsu tanemi yafiyar iyayenta, nasan kafin nan sun huce daga fushin dasuke da ita baby taga dangin mahaifiyar ta
Tunda kaga mu kenan bamu dayawa,
Yayana bana so iyalina suyi maraicina in baby na ta isa aure kazaba mata miji nagari karka manta ka rike alkawarinmu dan uwana,
Kacewa innarmu ta yafemin, kagayawa maryam da diyata da soyayyarsu zan koma ga Allah"
Ya kalli Usman dake ta zubarda hawaye INA kaunarka Dan uwana"
Tarine yakuma sarke Aliyu yana numfashi da kyar
Kalmar shahada ya dinga nana tawa, sekuma yayi shiru jikinsa ya saki
Usman rungume gawar Aliyu yayi ya fashe da kuka seda yayi me isarsa sannan ya mike ya nufi dakin da aka kwantar da inna mairo, maryam ya gani a gabanta tana bata ruwa tana shan ruwan da kyar wani yana dawowa

Yana shigowa inna ta dago kai ta kalleshi tare da fadin ya mutu ko Usman, Aliyu na shima ya tafi,"
Ta fashe da kuka tacigaba da fadin
" Allah ya karbi bakuncinka Aliyu na yafe maka duniya da lahira
Maryam kikula da kanki ki rike mana Jalila kaima Usman kakula da amanar da Dan uwanka ya bar maka, maryama karki manta da abunda nagaya miki inna mairo tayi maganar tana kuka tare da numfar fashi.

Lokacin da Aliyu yayi hatsarin aka kawoshi asibitin da inna take, an turota a wheel chair ta dubashi,, tunda ta Ganshi taga halin da dannata yake ciki ta karaya jikinta ya kuma rikicewa,

Duk abin naan da ake Zainab bata taka kafarta Asibiti ta duba jikin inna Mairo ba balle Aliyu da ba Sa shiri

Da gudu maryam ta fita ta koma dakin da Aliyu yake ta tarar da shi an rufeshi da bargo dagaske dai Aliyun ta ya mutu
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un maryam ta dinga maimaitawa tare da silalewa kasa sumammiya
Kafin akawo motar daza a dau gawar Aliyu inna mairoma ta cika
*************************
Ummi na zuwa nan a duniyar tunani ta fashe da wani matsanancin kuka tare da furta Allah ya jikanka Aliyu na"
ta fada hankali.
"Ummina kiyi hakuri idan magana ta ce tabata miki rai kiyi hakuri banyi Dan in bata miki rai ba "
Jalila tayi maganar daga inda take kwance ba tare da ta juyo ba Ummi bata CE mata komai ba taci gaba da kukanta daga karshe ma ta fita ta dauro alwalaa ta tada salla

Washe gari da safe Jalila ta fuskanci still umminta bata walwala fuskarta ta kumbura saboda kuka
Jalila aikace² kawai take ba tare da ta kula ummin na ta ba seda tagama komai ta hado musu breakfast ta shiga dakin ta tarar da Ummi ta baje hotuna a gabanta tarike guda daya tanata kuka
Ajiye tray din hannunta tayi ta karasa gaban Ummi ta Sa hannu ta zare hoton da yake hannun ummin nata ta duba
Hotonta ne ita da Aliyu sun kalli juna suna dariya
Jalila ta dago ta kalli umminta, "

"Ummina soyayyar ce ta motsa kika Sa hoton abeena a gaba kina kuka,?"
Jalila tai maganar tana dan murmushi wanda iyakacinsa lebenta, saboda in da Sabo Jalila tasaba da ganin umminta ta dau hoton abeenta tasa agaba tana kuka, kokuma hoton family ta

Jalila ta cigaba da cewa

"haba ummina idan ina ganin karaya a fuskarki me kike tsammani daga gareni duk lokacin danaga hawaye a idonki karaya nakeyi ummina bana son ganin hawayenki kaddararmu kenan semu karbeta a haka muciga ba da hakuri Allah shiyasan abunda yake boye"

Jalila Tafada jikinta a sanyaye tana sharewa Ummi hawaye yayinda itama take zubda hawayen
Dukda karancin shekarun Jalila, in tana magana tana tsara zance daki² dukda tarin kuruciya dake dawainiya da ita wani lokacin tana tunani irin na manya

Riko hannun Jalila Ummi tayi tare da ajiyar zuciya,

"babyna Kidena kuka nima na dena ina tuna abubuwan dasuka wuce ne a baya Jalila bazan manta da halaccin mahaifinki ba a gareni, da kakaninki sunmin halacci ina miki fatan samun managarcin miji me kaunarki kaman mahaifinki sukuma Allah ya kai rahama kabarinsu"

"Ameen Ummi"
Sukayi breakfast bayan sungama ne Jalila takuma Cuban umminta tace

"ummina amma meyasa ba kyason muje garinku, nifa nagaji da cin zarafin da akemin akan danginki ni ko Yaya suke ina so nagansu a haka ko basu da addini ina sonsu ummi"

Jalila Ummi takira sunanta
Jalila ta dago ta kalleta ba tare da ta amsa ba

"Meyasa kika dawo gida hutunku be kare ba nasan akwai damuwa me ya faru"?
Turo baki Jalila tayi

"To ni Ummi meye be faru ba, wannan Yaya mairon tazo tana cin zarafina, tun ina yarinya bana gane kyamar da take min har na girma nagane ba ta dena ba why?"

Ajiyar zuciya Ummi tayi
"Nasan abun da matukar wuya amma kiyi hakuri, kaman yadda kikace qaddararmu ce haka"

"To Ummi su mutane basu San kaddara bane dan mutum ya musulinta daga baya se yazama laifi yazama aabin kyama, wannan wane irin abune
Ummi ni mukoma danginki ya fiye min wannan cin zarafin Indai zasu bari muyi addinin mu, gara mu zauna a cikinsu da hujja insan ni jikar kiristoci ce, a fada da hujja tun INA zanin goyo bansan komai ba Ummi mutane ke nunamin kyama saboda kawai daga baya kika tuba, ina kema a da musulma ce uminna enough is enough am tired asarar hawayen damuke yayi yawa"
Ummi kallonta kawai takeyi gaba daya setaga Jalila ta juye takoma mata Aliyu sak irin halinsu daya Jalila akwai saukin kai ita dai batta da Neman magana tana da kawaici amma bata iya fushi ba gaba daya hargitsewa take sekace Aliyu
Janyota Ummi tayi jikinta ta zaro wani hoto
"Baby na kinga hoton ki kina Jaririya kamanki daya da kakarki, wani lokacin kuma in kikai abu senaga kaman mahaifiyata"
"Haba Ummi yakike kokarin basar da maganar damukeyi, Ummi I mean what I said fa tun kafin ki haifeni kike fuskantar wannan matsalar, Ummi irin wannan cin mutunci da hausawa keyiwa Wanda suka musulinta daga baya har ina"
"A'a Jalila yan adamne mu in an mana ba dai² ba se muduba Alkhairan mutum kinsan wani Abu, baby na Alkhairan mahaifinki Dan uwansa da kakaninki gareni se in manta da laifin da wasu daga cikin hausawa maraasa fahimta suke min kinemi yardar Allah bana mutum ba
Kiduba tunda mahaifinki ya rasu dan uwansa yake dawainiya damu bamu taba kukan babu ba, a garin nan kalli yadda Mike zaune da kowa lafiyaa, indai bazaki dinga duba alkhairan mutane ba se sharri to bazaki taba yi musu adalci ba"
Nannauyar Ajiyar zuciya JALILA ta sauke
"Am proud of u ummina kinsa jikina yayi sanyi, to shikenan amma meyasa ba kyason zuwa Gida?"
"JALILA inason zuwa amma sekinyi aure in muka je yanzu bazasu kara bari in taho ba nikuma nafiso sekin yi aure semuje ki gansu, tsawon lokacin danayi ba tare dasu ba zuciyata na tare da su, nafiso koni zasu rikeni ke yazamana kina dakin mijinki shizesa hankalina ya kwanta"

Ya mutsa fuska Jalila tayi
"Ke kullum zancenki aure²"
"To ai shine cikar mutuncin ya mace nidai fatana kirike mutun cinki a rayuwa Jalila kizama ya tagari abar Alfahari, kuma kizama garkuwa ga mijin dazaki aura ko ya yake,"

"Insha Allah ummina bazan baki kunya ba"
Ummi ta cigaba da cewa
"sannan kirike zumunci da yan uwanki Jalila kar abunda mahaifiyarsu da danginta kemana yasa ki gujesu wannan shine abinda mahaifinki yaita gayamin kan ya rasu"

"Naji amma bazan kuma zuwa kano ba in sun damu dani su suzo inda nake"
Dan zaro ido Ummi tayi
"Meyasa?"

"daf nake da wataran in wankawa Yaya Mairon nan mari wallahi,"
"Jalila ni ban koya miki wannan tarbiyyar ba, duk abinda hakuri bebaka ba rashinsa baze Baka ba"
"To Ummi tuba nake"
Ta fada tana mikewa tsaye

" ga wannan azzalumin shima Dan giya yadda ya dinga cin zalina bazan kuma zuwa kano ba"
Tayi maganar a hankali
"Me kikace ?"
"Ba komai Ummi, cewa nayi siyama bata zo nemana ba tunda na tafi bamuyi waya ba"
Tafa Dan kar Ummi ta gane me tace
"Tazo amma jiya da safe kafin Ku iso seda takuma zuwa nace mata baki dawo ba"
Murmushi Jalila tayi tareda cewa
"Allah sarki Aminiya"
Jalila tafada tana murmushi

Allah sarki babyna kin makara komawarki kano yazama dole Ummi tayi maganar a zuciyarta

Sallama akayi Ummi ta amsa Jalila kam bata tsaya ba data ji me sallamar ta fito da gudu daga dakin suka rungume juna dame sallamar
"Aminiyata nayi missing dinki"
Tureta siyama tayi ta Dan hade rai
"eh shiyasa naga kullum semunyi waya, nakiraki ba kya dagawa duk cikin missing din nawane"
A hankali Jalila tai mata magana
"Sorry aminiya Akwai labari"

Gyda kai siyama tayi ta Shiga suka gaisa da Ummi sannna ta fito suka koma dakin Jalila,
Dakin da dashi da babu kusan daya a gurin Jalila Dan komai Nata yana dakin Ummi se dai in sunyi fada seta koma dakinta kokuma in kawayenta sunzo

Suka shiga suka samu guri gefen katifar dakin suka zauna
"Bari Azumi baki San

Please Login or Register in order to submit comment