Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi tsaki
Jawwad yace "Ya dai?"
Ajiyar zuciya Jalal yayi "Bakomai"
"Bakomai kake ta murmushi a bacci haka, gayamin mafarkin me kake?"
"Kaga ni ka rabu dani"
"Anyway kaje kayi salla, takwas da rabi fa" Jalal bekuma cewa komai ba ya mike yaje yai wanka, yai alwala yai salla
Ilham ta boye damuwarta tayi breakfast, bayan tagama breakfast ta mike ta nufi gidansu Nana, bakowa a palourn gidan, dan haka ta wuce dakinsu Nana, taje ta tarar da Nana tana wanka, amma bataga Jalila ba, neman guri tayi ta zauna, ta jira Nana ta fito, Nana ta kalleta
"Lafiya kuwa da safiyan nan? Naga kwana biyu ma bana ganinki, ko kun jone da Yaya Jalal ne no more matsala, shiyasa kika yadani"
"Nana ba wannan ba ina yar uwarki?"
"aini dama a kule nake dake Ilham, kwanan Jalila uku a Asibiti se jiya ta farfado, amma kokice tana ina, ta sha jiki kaman zata mutu" Ilham a ranta tace " A a tana asibiti to wace ce mukayi waya jiya,? cikin ko in kula Ilham tace
"Niban saniba, bansan bata da lafiya ba, Allah ya sawwake"
"Ah haba zakicemin baki saniba, bayan yaya Jalal ya jejje Asibiti dubata"
Ji Ilham tayi kaman Nana ta soka mata kibiya, "yaje dubata fa kikace"
"wallahi kuwa, kullum se yaje, nima yabani mamaki, amma kinsan kobeje dan kowaba yaje dan Yaya Jawwad"
Jinjina kai Ilham tayi, ta Mike "na tafi se anjima"
"daga zuwanki zaki tafi"
"eh naga kaman fita zakiyi"
"A a ba inda zani Asibiti ne se anjima zani"
Bata kuma bi takan, Nana ba, Daga haka tai waje, zuciyarta fal takaici, wai kullum se yaje asibiti tunda aka kwantar da ita, "ko uban me yake zuwa yi, ta tabbatar ko uwarsa a aka kwantar baze je dubata kullum ba, tokuma wace ta kirashi, jiya? Karfa inje ina can ina hauka, aikin gama ya gama ina gefe, kai da sake wallahi, dole in tada balli" daga nan tai gida kaman mahukaciya.
Bayan su Jalal sun gama breakfast, Jawwad ya tafi asibiti be takurawa Jalal seyaje ba dan ko shine baze komaba sabida abunda baby tayi masa.
Doctor salis ya shigo yai mata allura ta cannula, bayan yagama ne ya kalleta
"Baby ya jikin" banza tayi masa
"ya kikayi shiru?"
"nace maka ba sunana Baby ba"
"Amma yayanki yake gaya miki"
"to ba Yayana kace ba, ko kai yaya nane? "
"am sorry, Jalila ya jiki"
"da sauki Alhamdilillah"
"Masha Allah, Allah yakara miki lafiya, jinake ciwon nan kaman ya dawo jikina, duk na damu wallahi"
Dan ya mutsa fuska tayi
"dan Allah ni ka sallameni yau"
"Amma meyasa?"
"To zaman me nake bayan na warke, ni kawai ka sallameni nagaji da zaman asibitin nan, gara in koma gida"
"Dan Allah kiyi hakuri nasan in kika tafi ba lallai inkuma ganinki ba"
"wani mugun kallo Jalila tayi masa, to in zauna in maka mene? Ni gaskiya nagaji gida nakeson komawa, kobaka sallameniba sena tafi, ko in Abba yazo in gaya masa mekace"
"A a yi hakuri, zan sallameki yau Insha Allah tunda kin warware"
"da dai yafi maka"
A ransa yace lallai haka wannan yarinyar take da tsiwa, lallai Jalal yayi gaskiya, amma shidai a hakan yana sonta don komai nata yana birgeshi, ana haka Jawwad yazo suka gaisa da doctor salis, ya gayawa Jawwad yau ze sallami Jalila, tace ita tagaji da zaman Asibitin, Jawwad yai murna sosai yace "indai ba wani matsala ai gara a sallamemu,"
Bayan fitar doctor Salis, Jawwad ya nemi guri zauna, ko kula Jalila beyiba,
"Yaya Jawwad, ina kwana?"
"lafiya kalau" shine abunda Jawwad yace,
Daga nan bekuma cewa komai ba, wayarsa ce ta fara ringing ya dakko ya daga
"Salamu alaikum"
"Wa alaikum salam, My Jawwad barka da safiya,"
Muryar ya dauka, ya gane me maganar, dan haka yayi murmushi
"Hanan kin tashi lafiya" seda Jalila ta waigo ta kalleshi
"Lafiya kalau, yame Jiki, Abdallah yacemin batada lafiya, da sauki jikin nata? Ko kuwa? "
"Kwantar da hankalinki, Hanan taji sauki, muna sa ran Insha Allah yau za a sallameta"
"Me yasameta ne"?
"Ta samu stroke ne, amma yanzu ta farfado tana lafiya"
"Allah sarki na kira wayarta ne bata shiga, itakam baby me yayi zafi haka, har tasamu stroke? in kana kusa da ita bani muyi magana"
Wayar a hansfree take Jalila tana jin komai
Ya kalli Jalila sannan yace
"Bacci take in ta tashi zan gaya mata"
"to shikenan"
"kayi saving lambata, mu dingayin waya"
"to shikenan, karki damu" sukayi sallama da Hanan
Ya mike ze fita Jalila ta kira sunansa, tsayawa yai ya waigo yana kallonta
Idonta taf hawaye "Yaya Jawwad fushi kake dani ko? Dan Allah kayi hakuri, bazan, kuma ba" takarasa maganan hawaye na gangarowa daga idonta, ita dai zubda hawaye baya mata wahala
Dawowa yai yazo gefen gadon ya zauna
"Baby sam banji dadin abunda kikayiwa Jalal ba, haba baby, gaba yake dake fa, indai zakiyi masa haka nima zaki iya yimin kenan"
Girgiza kai tayi "A a Yaya dan Allah kayi hakuri, nima ba a son raina na fada ba, raina ne a bace, shikuma yafaramin masifa, amma kayi hakuri"
"Bani zaki bawa hakuri ba, inkina so in hakura, Jalal zaki bawa hakuri"
Da sauri ta dago ta kalli Jawwad


Share please
More Comments More typing..............................


🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
[9/23, 10:27 AM] +234 802 426 7634: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 48
PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske,
Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what's app akan wannan lambar wayar
07063065680
Ina godiya matuka Allah yabar kauna

_My first novel_


Jawwad ya dan daga mata gira
"Yes se kin bashi hakuri, sannan nima zan hakura", lallaima wai sena bashi hakuri, ajiyar zuciya tayi
"to yaya Jawwad, zan bashi hakuri Insha Allah"
"Yawwa baby, Allah yaba ki lafiya"
Jikinta a sanyaye, tace "Ameen"
Kamar yadda doctor yai mata alkawari, da yamma aka rubuta musu sallama, jikinta yayai kyau sedai rama, duk yadda doctor Salis yaso Jalila ta dan sakarmasa fuska ya samu kafa kansa taki, dan ita wannan shishshigin daya kemata haushi yake bata, shiyasa kome yace setayi masa shiru, ta hade rai, haka ya gaji ya hakura, suka shirya suka hada kayansu, Jawwad ya daukesu se gida, Abba yayi murna matuka da ganin an sallamo Jalila, Nana ma se murna take, Jalila ta dawo, saboda Jalila ba karamin alkhairi bace a gidan
Har yanzu Abba yana fushi da Maama akan Jalila, tayi mamakin tsawon lokacin daya dauka haka, yana fushi akan wannan yarinyar, yanzu takuma tabbatar da idan har batayi taka tsan2 ba aurenta ze iya mutuwa saboda ita, se yanzu taga gaskiyar maganar yaya mairo, su Nana ma ba bi takanta sukeba, duk saboda Jalila, lallai tayi kuskuren yadda da Jalila ta zauna mata a gida, gashi tafara hada mata husuma a gida, dole tasan abunyi.
Kwana biyu da sallaman Jalila daga asibiti ta kara murmurewa, ta shiga sabgoginta, amma takan kebe ita kadai tayi kuka me isarta, gudun tayarwa da mutan gidan hankali, sannan tanata addu'a In Ummi na raye Allah ya bayyanata, tana cikin matukar damuwa amma, tayi iya kokarinta domin dannewa, kar a gane duk abunda take karfin haline kawai, Jalila ta lura Abba baya kula Maama, da tasaba kullum ta rakoshi in befita da wuriba, sucu Abinci ai wasa ai dariya, amma yanzu taga ko magana tayi se yayi mata banza, Jalila setaga hakan ba dadi, gidan ma ba dadi da suke zaune a haka, itako Nana ko a jikinta sabgoginta take.
Yau Maama ta fita bata gida da yamma, har magariba bata dawo ba, dan haka bayan an idar da sallar maghariba, Jawwad yasamu damar kiran Nana a waya yace ta tura masa Jalila,
Ba musu Jalila ta tashi ta dau dan sirin gyale tasaka akanta, ta fita, part dinsa, da sallama ta shiga, taje ta tarar da shi yana aiki akan system dinshi, tana zuwa ya kashe system din, ya dago ya amsa sallamarta, karasawa tayi taje ta zauna a kasan carfet
"Yaya gani, Nana tace kana kirana"
"Eh Jalila, ya jikin naki"
"da sauki Alhamdilillah yaya"
"masha Allah haka akeso, dama kiranki nayi inji ya maganarmu ta rannan, kin bashi hakurin kuwa"?
Dan hade rai Jalila tayi
"To yaya ni ina zan ganshi, niban bashiba" ta fada tana dan zumbura baki
"To taso muje"
"Yaya ina zamu?"
"Zo muje seki gani" yafada yana tashi tsaye
Ba musu itama ta mike tabi bayansa, waje ya fita tana biye dashi, gidansu Jalal ya nufa, suna zuwa yai musu jagora zuwa part din Jalal, Jalila tayi mamaki duk yadda take ganin kyan dakin Jawwad amma na Jalal ya fishi dayake Jalila bata taba zuwa part dinba, babban part ne, dan seka zata amaryace a ciki, an zuba dukiya a ciki sosai, Suna shiga ta karewa dakin kallo, palournsa katone sosai da dakuna biyu a ciki, akwai kitchen da toilet a palourn, ba laifi ko ina tsaf yake, ga katon tv plasma kusan rabin bango, palourn yasha labulaye da kujeru,sekace dakin amarya, ga kamshin turare yana tashi, kai bakace dakin mashayi bane
Jalal yana kwance akan 3 seater daga shi se wando 3 quarter da vest, yana ta danna wayarsa, yanajin sallamar Jawwad ya amsa a hankali, inba ka kalli Jalal ba bazaka san ya amsa ba, idonsa a lumshe yace,
"Jawwad kai nake jira dama"
"to gani ai, tashi kabani abunda zaka bani"
Jawwad ya amsa suna karasa shiga cikin palourn, Jalal sam be san Jawwad shida Jalila bane, sedayaji Jawwad yace "Jalila, karaso ki zauna mana" Jalal ya bude idonsa ya waiga yaga Jalila ce dagaske, seda gabansa ya fadi, doguwar riga ce a jikinta na material, se karamin mayafi da ta dora akanta, rigar kaman a jikinta aka dinka ta, se yanzu ya kara ganin ta rame sosai se idanuwa, gashi ta danyi duhu amma tayi kyau sosai, dauke kansa yayi daga kanta, be kuma cewa komai ba, Jalila ta shigo cikin palourn ta samu guri ta zauna a kasa kan carfet, kusa da kafar Jawwad, se zumbura baki take, Jawwad yace "Jalal gurinka mukazo fa"
"Ina jinka"
"Ka tashi mana, kaji dame mukazo"
Ba musu ya mike zaune, yana kallon Jawwad, "ina jinka"
"Dama abunda ya farune a Asibiti tsakaninka da Jalila shine mukazo mu baka hakuri, dan Allah kayi hakuri nasan bata kyauta ba, amma gata nan munzo tabaka hakuri"
Wallahi ba dan Yaya Jawwad ba babu abunda zesa Jalila tabawa wani Jalal hakuri kome zatayi masa na rashin kyautawa kuwa,
Jawwad ya kalli Jalila "Jalila kibawa Yayanki hakuri"
Sedata yatsuna fuska, dayake Jawwad baya ganinta, amma tana facing Jalal,
"Dan Allah kayi hakuri, bazan kara ba" Jalal yace
"Hmmm Jawwad kenan, ni nacemaka nayi fushine?"
"A a baka cemin ba, amma bamu kyauta bane, dole mu bada hakuri, da fatan an hakura"
"Se anwa mutum laifine za a bashi hakuri, ai har a tambayi koya hakura"
"Haba Jalal wannan ai gwalewa ne, tunda ta baka hakuri kayi hakuri mana"
Wani mugun hara Jalila takewa Jalal ganin se wani raina musu hankali yakeyi,
Wayar Jawwad ce tafara ringing, Hanan ce ta kirashi, bazeso yadaga agaban Jalila ba, dan yaga Hanan itama muguwar yar rigimace, yanzu setayi abunda Jalila zataji haushi, dan haka yace "please excuse me, Jalila jirani ina zuwa" ya tashi ya fita amsa waya, Jalal ya dora kafarsa daya kan daya, shima yaja tasa wayar, yana dannawa, Jalila se jan tsaki take, wayar Jalal ta fara vibration, ya saka a kunnensa "Ya JJ ina jinka" Jalila ta dan kalleshi, Jeje in bata mantaba Jawwad ya gaya mata shine farkon lalacewar Jalal,
"Birthday kuma Jeje, ni kuka shiryawa birthday, yaushe kenan"? Ya danyi shiru sekuma yace
"Ok Allah ya kaimu, zanyi shawara ingani, if i can attend" yakuma cewa
"Eh kwana biyunne akwai abunda nakeyine, shiyasa bakwa ganina, amma zanzo very soon"
Jalila a zuciyarta tace
"gaskiya zanso inga wannan Jejen, inga ya yake, kuma meye manufarsa akan Jalal" Jalal ya gama wayar yayinda ta danyi nisa a cikin tunani, kamar an tsunkuleta ta daga kanta kawai sukayi ido hudu da Jalal yana kallonta, cikeda tsiwa, da gadara tace "Meye haka zaka wani tsuramin ido, lafiya?" Jalal yace
"idan kika kuma, zuwa inda nake da wannan dan gyalen, zan nuna miki ba lafiya ba, kalli dan gyalen da kika saka" dan bude baki Jalila tayi da mamaki,
"to ina ruwanka dani, dazaka dinga kallona, ni banason kallo, inma tsirara nake yawo meya shafeka"
"meye abun kallo a jikinki, mummuna dake, kwaila"
Jalika rasa meza tace tayi, dan batayi zaton jin wannan maganar daga bakinsa ba, shi kuma ya dauke kansa ya kunna sigari,
Ya tashi ya dakko, giya a fridge ya dawo ya zauna, binsa Jalila tayi da ido, ya bude ya dakko wayne cup dinsa ze zuba, da sauri tace
"Giya ce fa? Kai yanzu baka kunyar ubangiji, baka kunyar kowa, zaka sha giya a cikinka, meye hakane?"
Shiru yamata yafara zubawa a cup
"Wai dagaske shan zakayi,? Mikewa tayi cikin zafin nama, ta nufoshi a fusace daa nufin ta fizge, ko a jikinsa kuma be fasa abunda yai niyya ba
" in kika karaso inda nake zan baki mamaki, stay where u are, wallahi kikazo sekema kinsha, kuma ko a gaban Jawwad ne, se dai ya hadiyi zuciya" ba shiri Jalila taci birki,
"Wallahi tir da halinka, me abun kunya, angirma amma ba hankali, Allah ya tsareni da shan giya, yamin tsari da hali irin naka, gaba daya ka gama bata rayuwarka, baka da wani amfani daza kayiwa kanka ko kayiwa wani, a dai canza hali"
Banza yamata, yaci gaba da abunda yake, yayinda ta cigaba dagaya masa magan ganu son ranta, ganin bashi da niyyar denawa yasata nufi hanyar fita aiko tai karo da Jawwad
" Am sorry na barki kina jira ko, yi hakuri dan jirani kadan ss mu tafi? "
Ranta a bace tace" ni tafiya zanyi gaskiya "
" Me yasa? Ko fadan kuka sakeyi? "
"ni bazan cigaba da zama ana sabon Allah a gabana ba, ko kunya bayaji ya dakko giya yana sha, ni tafiya zanyi," daga hakka fuuuuu tai waje, Jawwad ya kalli inda Jalal yake, tabbas giyar yake sha, jikin Jawwad a sanyaye ya taka ya karasa gurin Jalal, sannan yace" Jalal yakamata kadinga boyewa in zaka sha giyar nan, bayyanar da lefunka ze cigaba da zubar maka da mutunci a idon mutane, bekamata ka sha giya a gaban Jalila ba, Jalal u have to do something good for your life rayuwa bazata tafi a haka ba"
A hankali JALAL ya aje cup din hannunsa ya dan kalli Jawwad
"Jawwad in har banji kunyar ubangiji ba na sha giya, meye kuma abun boyewa wani abun halitta, da bashi da wuta bashi da aljanna, Jawwad i don't know what to do, nasani abunda Jalila take fada gaskiyane bani da wani amfani dazanwa kaina ko nayiwa wani, ban san meyakamata inyi ba, ban san meyake damuna ba, fita kabani guri Jawwad, ka tashi kabarni, leave me alone i want have some rest "
Ilham tana kitchen tana hada tea zata sha, dayake window kitchen a bude yake, kuma kana ganin harabar gidan ta nan, kawai taga Jalila ta fito daga part din Jalal, ta tsaya ta dan gyara mayafinta sannan ta nufi gate, mutsukke idonta takumayi don tabbatar da gaskiyar abinda ta gani, anya kuwa itace, da sauri ta juya ta bar kitchen din
Jalal yafara fita hayyacinsa, idonsa yafara wannan abun, ga jijiyoyin kansa sun tashi, ya fadi kasa,Jawwad ya zo gabansa ya dutkusa ya dan dafashi "Allah yaye maka wannan matsalar" daga haka Jawwad ya Mike ya fito, dan haka shine samun nutsuwar Jalal, jawwad ya girgiza kai tareda yiwa Jalal fatan samun sassauci a rayuwarsa,
Fitar Jawwad keda wuya, Ilham ta fito daga cikin gida, ta nufi part din Jalal, sam bata hadu da Jawwad ba, tana zuwa kamshin turaren Jalila ya daki hancinta, tana kokarin tabbatarwa ne taga handkchief a tsakar palourn, da sauri takarasa ta dauka, ta kai hancinta ta shinshina, tabbas na Jalila ne, ga Jalal taganshi zube a kasa yana bacci, dora hannu tai aka ta fasa ihu, sekuma tayi saurin toshe bakinta,
"Na shiga uku Allah yasa ba abunda nake tunani bane, Jalal in kamin haka bakamin adalci ba, kaci amanata, kuma wallahi na tabbatar da abunda nake zargi sena kasheka na kasheta wallahi," shikam yafadi a gurin yana baccinsa
Surutu ta cigaba dayi, tana zambarwa a gurin, Jalal besan tanayi ba, tagaji tayi waje ta nufi cikin gida, dakinta ta shige ta kulle kofa, ta dinga zarya, wayarta ta dauka, ta kira malamin su, akayi sa a bugu biyu ya daga
"Malam akwai matsala fa"
"Mastalar mene haka?"
"sonake ka bincikamin, kagani aikin nan kuwa ba a samu wata matsala ba?"
"Matsala kuma kaman yaya, wani abu yafarune"?
"ni dai kawai ka bincikamin dan Allah,"
"To shikenan amma kibari seda safe, zan kiraki"
Sukayi sallama da malam, amma fafur batun bacci ya kauracewa idon Ilham se surutai da zage2, kaman ta zare, kai kace mahaukaciya ce, yadda taga rana haka taga dare.
Da safe Jalila dan cin Abinci tayi kadan bata wani ci dayawa ba takoma daki, dan tunda aka sallamota daga asibiti a daki take wuni, seda wani dalili take fitowa, Nana ta tafi gidan kawarta yau, ga Halima taje ganin gida, dama Maama ba shiga sabgarta take ba, tunani duk ya addabi Jalila, ga batada nutsuwa saboda rashin Ummi, ga kuma tunani daya addabeta akan rayuwar Jalal, hankalinta ya karkata kan son zuwa birthday Jalal, domin ganin waye Wannan Jejen,
Tunani duk ya dameta, dan haka ta tashi ta fito harabar gidan, tasamu guri ta zauna, tai shiru tana kallon flowers,
Da safe Ilham ta kuma kiran Malam a waya don tambayarsa ko ya bincikamata, yace
"Na duba, nayi bincike amma ba abunda ya sauya, aikinmu yana nan a tareda shi, aikin da akayivakansa har yanzu yana tareda shi"
Ajiyar zuciya Ilhan tayi, "har naji dadi, nagode sosai malam har naji hankalina ya kwanta"
"Ai bakiga ta kwanciyar hankali ba indai baki kauda wannan yarinyar ba, yakamata fa kisan halin da kike ciki don tabbatar da cikar burunku keda mahaifiyarki, asiri kawai baze tasiri akanta ba dole ki tashi kisan meya kamata kiyi, ina ganin itace zata kawo wa aikin nan matsala, ni nariga nagaya miki yanzu, shawara da dabara yarage naki"
"To shikenan nagode sosai, nikuma zan san abunda zanyi," sukayi sallama ta dakko handkerchief din Jalila ta fito se gidansu Nana, tayi sa a Jalila tana harabar gidan a zaune, gurin Jalila ta nufa, tana zuwa ta kalleta
"Gurin ki nazo zamuyi magana"
Banza Jalila tayi mata, "magana fa nake miki"
"in har zakizo inda nake bakimin sallama ba, banida lokacin saurararki" Ilham tasan inbatayi yadda Jalila take so ba, bazata kulata ba dan haka tai mata sallama
Jalila ta amsa sannan tace "ina jinki"
Ta kalli Jalila ta nuna mata handkerchief din tace mata "wannan kaman naki ko?"
Jalila ta kalli hannunta tace "ba kama bace nawane"
"A ina kika barshi?"
"A inda kika tsince shi" Jalila tabata amsa cike da rainin hankali
"zuwa nayi muyi magana ta fahimta, bata fada ba"
"Inma ta fadan kikazo a shirye nake"
"Jalila meya kai handkerchief dinki dakin Jalal, meye hadinki dashi?, Jalila ina miki kashedi na karshe tun kafin insa ki zubarda hawayenki, inma akwai wani abu a ranki akan Jalal gara ki cire, kishiga hankalinki dan wallahi zan iya illata kowaye akansa, duk wanda yai niyyar hana min cikar burina senasashi zubda hawaye, Jalila wannan ne kashedina dake na karshe, kifita a harkar Jalal, tun kafin ta kwabe miki"
Jalila tai mata kallon tsaf sannan tace
"A matsayinki nawa kike min wannan kashedin haka? Matsayin uwata ko ubana ko wadda ta isa dani? Hmmm gaskiyar dan uwanki dayake cewa bakida hankali, ni kinga wani abu me kama da soyayya tsakanin da wannaan bugaggen dabe maida sabon Allah komai ba,? Ilham ko mazan duniya sun kare ba abunda zanyi dashi, banga abun so a gurinsa ba, Allah ya tsareni son Jalal, bashida kamala da cikar dazesa inso mutum kamarshi, baya jerin irin mazan dasuke birge Jalila, dukda bansan naki kudurin akansa ba, nima ina da nawa kudirin akansa, babu soyayya, ko auren Jalal a kudurina, kuma ki dena wannan tunanin, amma kisani idan har kudurinki yaci karo da nawa akan Jalal to tabbas kisawa zuciyarki sena tarwatsa naki!!! Ban taba sa abu agabana nakasa ba Ilham, ina iya tarwatsa ko shirin uban waye domin biyan bukata ta, wallahi Ilham kinyi kadan kisani kuka, idan harkika sani kuka, nikuma namiki alkawarin zan illataki a inda babu wanda ze gani balle ya miki magani, Ilham zuciyarki zanwa Illa ta har gaba da abada, ganin Jalila kike bakisan wace itaba, tunda kika zabi zaman takun saka dani am ready for you "daga haka Jalila ta fizge handkerchief dinta tai cikin gida, yayinda Ilham ta sandare a gurin




Share please

Dan Allah kuyimin afuwa rashin jina akan lokaci, dakuma karancin pages din wasu lokutan, ayyuka ne sunmin yawa, in baku mantaba a baya kullum nake mumu posting, yanzu abubuwa ne sukamin yawa amma ina neman afuwar ku,
Ina alfahari daku, kuma ina sonku irin sosai din nan masoya, muje zuwa kucigaba da bina a sannu domin jin yadda zata kaya a cikin wannan novel
Taku har kullum
Daddys girl 😍😍😍😍😘



More Comments More typing..............................


🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
[9/23, 10:27 AM] +234 802 426 7634: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 49
PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske,
Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what's app akan wannan lambar wayar
07063065680
Ina godiya matuka Allah yabar kauna

Ina amfani da wannan dama, domin mika ta a ziyyata ga yan uwa mutanen zazzau da dukkanin al ummar musulmi, na rashin sarkin zazzau
Alhaji shehu idris, ina fatan Allah ya jikansa yasa mutuwa hutuce, dashi da dukkanin al ummar musulmi da suka gabacemu
Allah ya rahamshesu in tamu tazo Allah yasa mucika da imani

_My first novel_


Jalila na zuwa dakinsu ta kife akan gadonsu,
"Nikam Jalila nashiga uku, wace kaddara ce ta kawoni kano har nasan Jalal ne, wanda har rayuwarsa take neman hanamin tawa nutsuwar, Ummi dan Allah in kina raye duk inda kike ki dawo, nagaji da zaman nan ina cikin damuwa, Allah ka temakeni, kabani ikon jarraboyina na rayuwa"
Ta karasa maganar tan zubda hawaye, tayi me isarta sannan ta mike ta duba wayarta ta kira Hanan, seda ta kusa katsewa sannan Hanan ta daga, tana dagawa tace
"Tace afuwan ranki ya dade, ina wankane, ya jiki Jalila?
" Da sauki Hanan, ya Baba na dasu Abdallah "
" Baba baya gari yana bauchi, Yaya Abdallah ma haka dagani se mummy, ya jikin kinji sauki"
"jiki Alhamdilillah na warke ganima a gida"
"masha Allah, nakira Jawwad nace ya hadani dake amma se yacemin ba kya kusa, siyama ma takiraki bata shiga ki kirata dan Allah"
"zankirata Insha Allah"
Hanan ta ce
"nikan Jalila meyasameki haka har ya kai ga kisamu stroke ko wani abu na damunki ne?"
Se Jalila taji kaman Hanan ta sosamata inda yake mata kaikayine, batasan

Please Login or Register in order to submit comment