Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace semunci"
Jawwad yayi dariya
"Allah sarki rayuwa, kokuma ta dumama tuwo tace shi zamuci, ka wuni da yunwa"
"Mu wuni dai, ai kaima bakaci"
Suka kuma kwashewa da dariya,
Hanan ta Dan taba Jalila sannan tai magana a hankali
"Jalila kin yadda da abunda nagaya miki game da Jalal,?"
Abdallah ya jefoma Hanan handkchief dinsa
"Kai Hanan kiji tsoron Allah me kike gayamata haka"
"Ina ruwanka sirrine"
Wayar Hanan ta fara ringing, ta mike zata fita ta amsa wayar, Jalila tace
"Kunyarmu akeji dabaza a amsa a gabanmuba"
"Allah ya kiyaye inji kunyarki, inma kunyarce kunyar Nana zanji itace sirikata"
Abdallah yace "ji Mara kunya to wa Nana zata baki"
"Idan ma Nana bata baniba nasan Yaya Jalal ze bani"
"Wa kikeso in baki"
Nana ta tambayeta
"Rabu dasu sirrine se mun kebe da Nana zan gayamata"
Tayi waje abunta
Tafito tana amsa waya turo gate din gidan akayi, yaseera da Ilham suka shigo
Kai tsaye suka nufi inda Hanan take

Share please
More comments more typing..........................



🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_
(2020)

_ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 40

PART 1
Share please

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa
ABDUL JALAL NOVEL FANS
Love u all guys ❤❤❤❤❤

-MY FIRST NOVEL-

Suka karasa inda Hanan take waya, tagama wayar ta juyo ta kallesu, sannan tace
"Lafiya naga kunzo kunsani a gaba"?
Yaseera tayi murmushi
" baki gane niba ne"?
"Eh ban ganekiba, yauma nafara ganinki"
Aikuwa Ilham a fusace tace "kingani ko yaseera tsabar
rainin hankali wai bata ganeki ba, nagayamiki muguwar Yar rainin hankalice"
"Haba Ilham meye hakane? Meye Dan bata ganeni ba seta iya yuwa ta manta ne"
"Kizo shekaran jiyan sannan yau tace ta mantaki"
Hanan ta kallesu
"In Baku da abin cewa, ni ina da abunyi"
Yaseera tace "A a Jalila, Yaseera ce fa, da mukazo shekaranjiya"
Hanan ta fuskanci basu San ba Jalila bace, Hanan a ranta tace wannan ce Ilham kenan, hada ita a cikin labarin da Siyama tabata, na Jalal
Ta kallesu tai musu kallon tsaf sannan tace "wannan Hanan ce ba Jalila ba"
"Kamar ya?"
"Kamar yadda nagaya muku mana"
Yaseera tace "Dan Allah Jalila a dena Jokes din nan gurinki mukazo zamuyi magana"
Hanan tace
"Maganar Me?"
"Akan abunda yafaru jiya har Jalal ya huce akan Ilham, abunne yabamu mamaki kwarai"
Hanan a ranta tace lallai wannan basu da hankali su nan gaba daya sun yadda Queen ce,.to ni mema zance musu nida bansan meya faruba,
"Nima abun yabani mamaki kam, amma yanzu ina wani abunne, kubari anjima,.semu hadu"
"To shikenan ina Nana?"
Yaseera ta tambaya
"Nana tayi bakine tana part din Jawwad"
"OK mungode se anjima"
Suka juya suka fita
Ilham ta kalli yaseera "ji wani sabon iyayi, ga yadda ta canza magana, tanawa mutane magana da isa sekace wata basarakiya"
"Nima nagani Ilham ai wannan se munbi a sannu"
Suna fita Hanan ta dinga dariya sannan tace amma gaskiya wannan sakarkarune,
Takoma ta tarar sunata cin abincinsu banda Jalila da take ta tsakura duk a takure take
Hanan ta danyi murmushi sannan tace
"Yaya Jalal kufa ci Abincin nan sosai, inba hakaba Abdallah cinyewa ze ya barku"
Jalal yai murmushi,
"Meyasa kika takurawa yayankin nan haka"?
" Abdallah yace tambayeta dai, ni dai ba kunyarku zanjiba Dan in ban koshiba zan karane"
Hanan tace "Nima ai haka kake min kaita kunyatani a gaban mutane"
Jalila tace
"To suda uwar magana ki zauna kici abinci ni bansan yadda akayi bakinki ya bude hakaba, kika koyi surutu"
"Hh au haba zama dake ne yasa na koya, ni na manta ma kinyi baki fa, yanzun nan"
Jalila tace mata "suwaye"?
" ban sansu ba,.wasu matane su biyu suka ganni a waje sun dauka kece suka faramin surutu, nikuma nace sutafi aiki nake sudawo anjima"
"Dan wulakanci gaskiya baki kyautaba"
Cewar Abdallah, Hanan ta kalleshi " Abdallah bana son ganin gushewar wannan farincikin da nake gani a fuskokinku, nasan in Jalila ta tashi tsareta zasuyi da surutu, Dan daganinsu ba wani abun kirkinne yakawosuba"
JALILA tace
"Ni mamakima nakeyi suwaye haka?"
Hanan tace "wata fara dai me kwalakwalan idanuwa, se wani kallon banza takemin da wata kuma me surutu, se magana take wai lallai sena ganeta sunzo shekaranjiya ko baseera kowa oho dai"
Jalila ta kalleta "kai Hanan meyasa kikace su tafi"
"To me zasuyi miki, wannan me kwalkwalan idanuwan sewanj kallon banza takemin, shine ya tabbatar min ba abun arziki ya kawosuba"
Nana tai dariya
"Kanwar Yaya Jalal ce fa, Ilham ko?"
Dan zare Ido Hanan tayi,
"Dagaske amma basa kama, wata Mara.. Sekuma tayi shiru
Jawwad yace " Hanan kanwar Jalalce cousin dinshi ce"
"Sedai cousin din Dan basa kama, gashi se wani..
Bata karasaba Jalila ta janyota
" haba Hanan zubar ya isa kici Abinci mana"
"To nayi shiru"
Suka cigaba da cin Abinci
Jalal a ransa yake jin wani nishadi, Wanda rabon dayaji shi har ya manta, a ransa yake jin inama a ce wadan nan duk yan uwansa ne shima yace yau yanada yan uwa amma shikadaine kamar rai
Suka gama cin Abincin sannan su Hanan suka kwashe kayan suka tafi cikin gida
Suka koma dakin su Nana, Nana ta tafi dakin Maama don basu guri Naja se masifa take wai Nana ta rike bare ta manta da ita
Hanan ta kalli Jalila "Queen do you believe now Jalila, nagaya miki Jalal yana bukatar kulawane kawai, kadaici yana taka rawa a rayuwarsa"
"Hanan gaskiya nayi mamaki, bantaba ganinsa cikin nishadi ba, koyana dariya kullum fuskarsa babu fara a, kinga wadda sukazo nemana din nan farar, cousin dinsa ce a gidansu take itace take sonshi bakiga dukan dayaake mata ba baya shiga harkar mata, Nima fada muke, yabani mamaki danaga ya kulaki"
JALILA ta kwashe labarin Jalal zuwa yadda suke fafatawa dashi, halayensa dayakewa mahaifiyarsa, har zuwa mafarkan da takeyi dashi"
Hanan ta kyalkyale da dariya
"Jalila ta kalleta, meye haka kuma, Maya baki dariya"
Hanan ta sassauta dariyarta
"Ashe bani kadai rashin kunya ba taiwa ranaba, kut naso inga idonki lokacin daya baki sigari, kut gaskiya Jalal Dan duniyane yayi maganinki"
Tafada tana kuma kyakyata dariya
"Mtseeww nifa bana son wulakanci"
"Yi hakuri queen, let's be serious, Jalila kiyi wani abu, zaki iya temakon rayuwar Jalal"
"Ta yaya zan iya wannan Jarababben Dan taurin kan"
"Bashi da taurin kai Jalila, he is simple, yanzu dai yakamata kisan meyasa bayason mahaifiyarsa, ki gano wayeshi, Jalila ke Alkhairi ce a duk inda kikaje, kiyi wani abu sannan kidingayi masa addu a kidena yi masa rashin kunya naga alamar bayason rainin"
"Hmm mugun Dan rainin hankaline Hanan bazaki ganeba"
"To kicigaba dayimasa rashin kunya randa yabaki giya, kya kirani kibani labari"
"Allah ya kiyaye"
Halima tayi sallama suka amsamata
Ta kallesu sannan tace "wacce ce Jalilan ne tunda tazo na dena ganeki"
JALILA tayi dariya
"Ya akayi leemart"
"Dama Cewa akayi wai kushirya in anyi sallar la asar, Hanan zasu tafi"
"To shikenan"
Sukayi sallar LA asar Hanan tanata Nanatawa Jalila, ta temaki rayuwar Jalal,.sannan duk abunda ake ciki ta kira ta a waya tagaya mata,
Hanan ta fito tayi sallama da Maama, Maama tabata kyautar agogo, sannan Sukafito
A harabar gidan suka tarar dasu Jalal Suma sun fito
Abdallah ya kallesu, yace "Yakamata muyi hotuna fa, domin tarihi"
"Gaskiya kam" cewar Jawwad
"A fara yimana nida JAWWAD"
Inji Hanan
Ta tafi kusada Jawwad akayi tayi musu
Sannan akaimata itada Jalal, da Abdallah dakuma Nana
Takalli Jalila "Queen come forward"
Ta janyo hannun Jalalila zuwa kusada Jalal,
Kallon Jalila yayi, Jalila kuma ta hade rai
Hanan tace "Haba queen meye haka kiyi dariya mana, kin wani hade rai kamar wata boss"
Dariya sukayi, Hanan tai musu photo, a haka aka dinga hotunan nan, Naja ce ta fito harabar gidan tai tozali da Abdallah gaba daya ta rikice tarasa nutsuwarta, kai Allah yayi Halitta a nan, basu kula da itaba sukaji gaba da hotunansu,
Nana ce suka kuma dawowa da Yaseera suka tarar anata budurin hotuna Jalal kamar bashiba, se fara a
Se yanzu suka gane, ashe dazu ba Jalila suka ganiba tsabar kamace kawai dasukeyi, Jalal na ganin Ilham ya hade rai, suka karaso inda su Jalal Suke, Yaseera ta kalli Jalila tace"dazu munzo gurinki Ashe bake bace" Jalila tayi dariya tace "bani bace Hanan ce"
"To shikenan bari muje naga kunada baki,"
"A a bakomai bari inzo"
"A a ki bari zamu dawo"
Jalila tace"to shikenan "
Ilham, Jalal kawai take kallo da mamaki, ya kalleta, maganar Hanan ya tuna wai fara me kwalakwalan idanuwa
Kawai yadanyi murmushi.
Su Hanan sukayi haramar tafiya har bakin mota su Jalila suka rakasu, Hanan ta kallesu
"Kamar kar mu rabu, haduwar nan tayimin dadi, muna fatan kuma wataran zaku kawo mana ziyara"
"Insha Allah, muma zamu kawo muku ziyara"
Ta kalli Nana sannan tace
"Nana zanyi missing din murmushinsa, Dan Allah kibani shi"
Nana tace "wa kenan?"
Ta kalli Jawwad
"Gashi nan"
Gaban Jalila yafadi, shikansa Jawwad sedaya kalli Hanan,
Abdallah yace
"Aliyu kaga ku kyale Hanan, wani lokacin bata da hankali"
Ya bude mata mota "wuce muje"
Ta rike murfin motar sannan ta kalli Jalal
"Yaya Jalal da Nana da Queen bakinsu daya naga kamar bazasu bani ba, Dan Allah kai kabani shi"
Jalal ya kalli JALILA ya kalli Jawwad yaga duk Jikinsu yayi sanyi kaman Wanda akace za a kashe se yayi murmushi
"Yace indai Jawwad ne nabaki shi,"
Abdallah ya kalleshi
"Tab Jawwad kar ka yadda ka auri fitsararriya wannan, kyanta tsayayyen soja Wanda ze zaneta in tayi ba dai² ba"
Dariya sukayi amma banda Jalila
Hanan ta shiga gaban mota ta sauke glass ta kalli Jawwad,
"I will miss you Yaya Jawwad dina, keep me close to your heart"
Juyawa Jalila tayi ta shige cikin Gida, saboda ji tayi wani abu ya tokaremata a kirji, takasa tsayuwa
Hanan ta jingina da Jikin kujera, tayi murmushi tareda lumshe ido a hankali ta furta "am sorry queen"
Abdallah ya kalleta "ya dai uwar magana"
"Ba komai, ina cikin farincikine kawai"

Ilham ta kalli yaseera tace "yaseera Dan Allah mubar batun yarinyar nan kawai munemi mafita"
"Wace mafita Ilham, so muke mu tabbatar da zarginmu tukuna"
"Yaseera lokaci fa kuremin yake, nagaji zanyi abunda naga ya dace"
"Ilham kibi komai a sannu kar garaje yakaiki ya baroki"
"Nasan yadda zan tsara komai ki manta da ita kawai"
"To Allah ya taimaka"


Suna shiga Gida Jalila bata tsaya ko inaba ta nufi dakin su,
Jawwad jikinsa yayi sanyi sosai, Jalal ya kalleshi yaga Jawwad yayi wani iri kaman Wanda yayi wani babban zunubi
Dariya Jalal yai
"Wai meya sameka ne kawaniyi shiru"
"Hmm ba komai," inni Jawwad
"Dan tace tana sonka shine kawani damu, meye a ciki to, naga dai su biyun duk dayane"
Jawwad ya kalleshi
"Allah ko? Eh ai shiyasa kai gakanan kun jone da Ilham, Dan tace tana sonka, kana sonta kaima"
"Mtseww Dan Allah idan ina magana kadena sakamin maganar banza"
"Ilham dince maganar banza?"
"Ban saniba"
Ya mike yai waje yabarwa Jawwad dakin
Jawwad yayi murmushi "Ashe ba dadi"
Yana zuwa Gida yaji yanason shan madara, Dan haka ya duba fridge dinsa, bawani lemon kirki a ciki duk se giya, rufe fridge din yayi, ya mike ya tafi cikin Gida, yana zuwa yatarar da Ilham a palour bebi takanta ba ya wuce fridge ya bude ya dau abunda yakeso, yana rufe fridge din ya juyo yaga Ilham tsaye a bayansa
Gefenta yayi ze wuce, takuma dawowa gabansa
Ya kalleta "meye Haka?"
"Abunda kagani mana, Yaya Jalal meyasaka nishadi haka? yau, naganka kana dariya dakuma fara'a abunda ni bakayimin,"
"Zaki bani hanya kosena barar dake a gurin nan"
Hannu ta mika masa "bani in tayaka daukar kayan"
"Jalal dama kana gidan nan, amma baka Neman inda nake"
Suka jiyo muryar mummy, ya juyo ya kalli mummy
"Idan nazo mezan miki? Bani da wani amfani dazan miki, be kamata in dinga zuwa ba"
"Ni kake gayawa haka ko?"
"Yau nafara gaya miki? Kina son maida hannun agogo bayane kawai"
"Jalal kaji tsoron Allah, anya kanaso ka gama da duniya lafiya"
"Mummy ke yakamata kiji tsoron Allah tun a farko ba a yanzuba da aikin gama ya Riga ya gama"
Ilham ta Dan juya baya tayi murmushi, a ranta tace Ashe kana sane da komai, Jalal mahaifiyarka tayi kuskuren da kake karbar hukuncin
Mummy ta kalli Jalal
"Yanzu JALAL....
" Enough mummy, baki da abunda zaki gayamin in saurareki"
Yana zuwa nan a zancensa yai waje, yayinda mummy ta zauna akan daya daga cikin kujerun palourn tafara kuka

Naja ta shigo dakin su Nana ta tarar da Jalila kwance akan gado Nana kuma tana gyara dressing mirror, kalli Nana "Nana wai bakin sun tafine?"
"Eh sun tafi" ta kuma gyara tsayuwa sannan tace
"Y'an uwansu Jalilane?"
"Eh ya akayi"?
"Naga suna kamane sosai da wannan yarinyar, amma wannan namijin dasukazo tarefa?"
"Yayan Hanan ne" Nana tabata amsa
Jalila tana jinsu tayi musu banza
NaJa takuma cewa
"Yana da aurene"?
Nana ta dan bude baki, ta kalli Jalila sannan ta kalli Naja
"To ai Jalila zaki tambaya bani ba"
Jalila ta kalli Naja
"Kinada damuwa da hakanne, ina ruwanki ne, Suma daga dangin arnan suke, kinada matsala da hakanne?"
Jalila tayi maganar a fusace, da son huce takaicinta akan Naja, ta mike ta shige toilet
Nana kam dariya takama yi, "to hajiya Naja, kinji dai inma sokike seki hakura"
Bayan sallar magariba Jalila ta kira Abdallah, yace mata sun isa Kaduna lafiya tai masa godiya da bangajiya
Nana ta shigo da katon Leda a hannunta
"Nima bari in Dana Queen inji Hanan"
"Sarkin tsokana,"
"Ba wani tsokana, zomuje kirakani please"
"Ba inda zani"
"Maama ce fa tace kirakani"
"Ina?"
"Gurin mummy"
"Waike kullum sekinje gidansu Ilham ne?
" to queen ya zanyi Maama ce ta aikeni,"
"Ba sunana queen ba,"
"To Baby Jalila, na dena"
"Kyaji dashi dai" Jalila tasaka hijjabi tabi Nana zuwa gidansu Jalal
Suna zuwa suka tarar da mummy tana kuka a palour Ilham kuma tana kan kujera tana chatting,
Ilham tace "mummy lafiya kuwa?"
Ta goge hawaye, "bakomai Nana bari in dakko miki kudin"
Ta karbi kayan hannun Nana ta wuce dakinta
Nana ta kalli Ilham "Ilham me akayiwa mummy take kuka?"
"Ta tsuniyar gizo ai bata wuce koki, ita da danta ne, yamata rashin kunya ya fita"
Nana ta girgiza kai "kai abun ba dadi Allah ya shiryi Yaya Jalal"
Jalila ce kawai tace Ameen yayinda Ilham ta maida kai kan wayarta
Jalila tace "yawwa Ilham nikam Neman me kukemin dazu?"
Ilham ta Dan daga kai ta kalleta
"Manta kawai ya Riga ya wuce"
Daga nan Jalila bata kuma cewa komaiba
Mummy ta fito tabasu kudin ta koma dakinta
Ilham ma ta mike tabasu guri Dan zuwa yanzu ba Jalila ba har Nana ma haushinta takeji.
Suka koma Gida Nana ta tafi kaiwa Maama kudi, Jalila kuma ta shiga dakin Halima
Suketa hirar zuwansu hanan Jalila take gayamata farincikin datayi,
Tace kinsan wani abu Halima
Halima tace "a a"
"Yau abunda yabani mamaki ganin Jalal yana dariya"
"Naganku kunata hotuna kaman bashiba"
"Wallahi kuwa,Allah sarki mahaifiyarsa ce babban abun tausayi, tanada da kamar Jalal da yakamata ace, tana cikin farinciki amma kullum cikin tashin hankali take"
Halima ta kalli Jalila
"Tab wannan matarce abun tausayi, amma bata taba shukamiki rashin mutunciba"?
Jalila ta kalleta da mamaki
"Me kike nufi Halima?"


Share please
More comments more typing....................

🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
[9/12, 6:02 AM] +234 816 830 7871: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_
(2020)

_ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 41

PART 1
Share please

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa
ABDUL JALAL NOVEL FANS
Love u all guys ❤❤❤❤❤

-MY FIRST NOVEL-

Halima ta kalli Jalila sannan tace
"Hmm Jalila kenan abar zancen kawai Allah ya kyauta"
"Amma halima yakamata kigayamin"
"Jalila fadan bashi da amfani, amma kiyi hankali da matar nan"
Daga haka Jalila ta mike ta tafi dakinsu, itakam takasa gane kan wannan al'amari ita dai a haka bataga aibun Mummy, amma meyasa Halima tace bata da kirki, kuma gashi taki gayamata meyasa,
Da wannan tunanin ta shiga toilet tai wanka tai alwala tazo ta tayar da sallar shafa'i da wuturi
Shikam Jalal daya koma part dinsa ji yayi baya kaunar shan madarar Mummy tagama bashi haushi, Dan haka ya kunna sigarinsa ya dinga sha, dayagama kuma ya sha giyarsa iya son ransa, sannan ya baje a gurin
Jeje ne a gaban wannan mutumin na rannan, mutumin ya kalli Jeje fuskarsa Sam babu alamar tausayi sannan yace
"Jeje nagaji fa, a wannan karon na raina kokarinka, har yanzu abu yaki karewa, har yanzu ace kunkasa aikata abunda nakeso"
"Jeje yace haba Oga KB duk kokarin danayi abaya, se wannan zaka kasa hakuri, aiko iya haka muka kyaleshi nayi maka kokari, balle ma ina kokari fa"
"Hakane amma gani nai yanzu kana nema kayi sanya, a wannan shekarun da kunyi tafiyar nan Dubai da dayan biyu ko akama shi saboda miyagun kwayoyin damuka Sa akayansa, ko kuma da kun tsallake da yanzu munyi arziki fiye da yanzu"
"Hakane Oga abun ne da matukar wahala, wannan Jawwad din shiyake hana ayyukan mu tafiya yadda yakamata, Hannah ma tanata nata kokarin amma hankalinsa baya kan mata, yafi ganewa shaye²"
Wanda aka kira Oga KB ya nisa sannan ya kalli Jeje
"Bawata yarinyar da za a iya sakawa aikin dole se Hannah?"
"Oga a matan da nasani na bariki a irin taurin kan Jalal inba, Hannah ba ba wadda zata iya,"
"To shikenan amma ka ninninka kokarinka, gaskiya sonake yaron nan ya lalace fiye da yanzu, sonake yazama kaman Dan akuya sabida bin mata, yasha miyagun kwayoyi yayi safararsu, sonake bakin cikin ABDUL JALAL Yayi sanadiyar rasa ran Hadiza sannan ya kare rayuwarsa a gidan yari"
"Kwantar da hankalinka Oga komai ze tafi yadda kakeso mu dai ka Dan karamana lokaci"
"To shikenan ina jira inji kyakykyawan labari"
"Kar kadamu zakajine Oga, kwanan nan ranar zagayowar haihuwarsa zeyi, zamu shirya masa party, a nan zamuyi kokarin ganin komai ya kasance"
"To shikenan ina saurarenku"

Da safe Jawwad yaita zuba ido yaga Jalila ta kawo musu breakfast amma shiru, ga Jalal ma bezo ba daga karshe ma Halima ce ta kawo breakfast din, Jawwad ya tambayi Halima,
"Halima ina Jalila?"
"Tana cikin Gida"
"Meyasa bata kawo Abincin da kanta ba"?
"Wallahi bansaniba, kawai tacemin in kawo"
Ya gyada kai
"OK shikenan, Nagode"
Daga nan ya mike ya dau kayan Abincin zuwa gidansu Jalal dan yau be zoba,
Kamar yadda yai tsamanni, Jalal be tashi daga bacci ba, yana kwance a parlour, ko kayan jikinsa be canza ba, ga kwalaban giya da yasha da ragowar sigarin da ya zuke, Dan girgiza kai yai sannan ya tashi Jalal yasashi yai wanka yai sallar asuba,
Jawwad ya kalli Jalal
"Jalal baza kayiwa kanka fada ba ko? Lafiyarka fa Jalal, zasu iya yi maka illa"
Kallon Jawwad yayi ya sunkuyar da kai
"Jiya nayi iya kokarina kar in sha matar gidan nan tabata min rai, shiyasa na sha"
"Haba Dan uwa, in rai yabaci hankali baya gushewa, ka dinga hakuri, Mummy mahaifiyar kace, ka dinga hakuri da ita"
"Jawwad kasan komai Dan haka karka kuma batamin rai"
"Shikenan yi hakuri bari mu karya"
Jalila ta na gyara gadon su dan Nana ta tashi daga baccin ta shiga wanka, wayar Jalila ta fara ringing, tana dubawa taga Hanan setaga bata kyautaba bata kira Hanan tayi mata ya hanya ba, tasa hannu ta daga wayar
Hanan tace "Queen shine ko ki kirani kimin ya hanya ko?"
"Am sorry Hanan nakira Yaya Abdallah"
"Shi daban ni daban"
"To Allah yabaki hakuri"
"Ameen kin temaki kanki da kika bani hakuri, da baki banba ko hmmm"
"To ai ya wuce tunda nabada hakurin"
"To naji, yanzu dai ya Yaya Jawwad dina fatan ya tashi lafiya"
Jimm Jalila ta yi taki cewa komai
"Magana fa nake Jalila, nace ya Jawwad dina, kwana nayi ina mafarkinsa, yanamin wannan kasaitaccen murmushin, kaman inyi tsuntsuwa inzo in kuma ganinsa"
"Mhmmm" shine kawai abunda Jalila ta ce
"Tunda bazaki gayamin ya yake ba shikenan, ni nakirashi inji, ya Jalal dinki"?
"Jalal dina kuma?"
"Eh mana, tunda bazaki gayamin ya, Jawwad Dina ba, se in tambayeki ya Jalal, tunda bakya iya danne kishinki queen"
Dan dabarbarcewa Jalila tayi
"Kin fiye shirme Hanan, wane irin kishi, ya Mummy da Yaya Abdallah"
"Ya kike kokarin canza maganar ne, anyway kowa lafiya, hau what's app kiga status dina"
"To naji, saura inga shirme"
Hanan ta yi dariya
"Koma dai meye zaki gani"
Jalila ta bude what's app dinta taga Hanan ta turomata messages, ta bude hotunan dasukayine, hotunan sunyi kyau, tana duba dp din Hanan taga hoton Hanan da Jawwad, gashi be iya hade raiba, yayi murmushi, sunyi kyau shida Hanan, Jalila ji tayi kaman ta buga wayar da kasa
Dagaske kishin Yaya Jawwad nake, "yasalam" status din Hanan ta bude hotunan ne dai akan status din nanma ta rubuta kalaman soyayya, akan hotunanta da Jawwad
"Wai dagaske Hanan Yaya Jawwad takeso ko wasa, Hanan karkimin haka mana"
Tana kuma shiga daya hoton setaga hotonta da Jalal, wanda hanan tasata tai dariyar dole, shikuma Jalal yana kallonta Hanan ta rubuta
"perfect Match, Jalal and Jalila"
"Kutmelesi baki da hankali, kinci kai Hanan, Allah yayi min tsari, da mutum irin Jalal,"
Ta turawa Hanan daga nan ta rufe data dinta ta kashe wayar gaba daya
Sakkowa ta yi ta karasa gyaran gadon
Sannan tabar dakin gaskiyar Hanan Jalila kishi take, tarasa meyake mata dadi, harabar gidan ta fito, tana son ganin Jawwad, yau ba ta kaimasa abinci ba rabon data ganshi tun jiya da su Hanan suka tafi,
"Maybe ma Hanan ta kirashi suna shan soyayyarsu" wata zuciyar ta raya mata, tsaki Jalila tayi a fili, tarasa abunyi, kawai ta shiga gayaran flowers din harabar gidan, lokaci² tana tsaki
Abba ne ya fito ze fita yaganta tana gyaran flours, yayi murmushi yakarasa inda take yace
"Barka da safiya, yarinyar kirki, da kanki kike gyaran flowers din"
Murmushi ta yi
"Abba barka da fitowa"
"Yawwa Yar albarka, dakanki kike wannan, akin nasaka a nemo wani megadin daze dinga kulada flowers din"
"Abba dan dai gyaran flowers ai ba wuya koni se indingayi"
"A a baza ayi hakaba inkika fara zuwa school fa, wannan ba aikinki bane,
Yawwa munyi waya da umminki, tacemin tana nan tafe next week insha Allah, zatayi tafiyar nan"
"To Abba nima tagayamin,"
"Masha Allah, Allah yakawo mana ita lafiya"
"Ameen Abba"
Abba ya kalleta
"Ina fatan ba wata matsala zamanki a gidan nan ko"?
" babu wata Matsala Abba"
"Masha Allah, in akwai wani abu dai kimin magana"
"To Abba, Adawo lafiya"
"Allah yasa Jalila"
Daga haka Abba ya shiga motarsa ya fita

Bayan sun gama breakfast Jawwad ya kalli Jalal yace
"Am going"
"Where?" Jalal ya tambayeshi
"Gida mana ina son ganin Baby, naga kaman tana fushi dani, tun jiya ban kuma ganintaba, yauma ba ita ta kawo min Abinci ba"
Jalal ya mike kafa ba tareda ya kalli Jawwad ba yace
"Laifin me kamata, zatayi fushi?"
"Nima bansaniba Jalal, zan tambayeta dai, na damu da rashin ganinta"
Tsaki Jalal yayi
"Kafiye abun Haushi,"
"Eh naji, nikam se an nima"
"A sauka lafiya"
Daga haka Jawwad ya tafi Gida a harabar gidan ya Tarar da Jalila ta na gyaran flowers, tabawa gate bata, dan haka batasan ya shigo ba, a hankali ya karasa inda take, juyowa tayi kawai tai tozali da Jawwad, seda ta dan tsorata
Murmushi yayi mata "matsoraciya ga idonki, am sorry nabaki tsoro ko"
Murmushi itama tayi masa ta girgiza kai, kallonsa take ta tuna maganar Hanan
"Kwana nayi ina mafarkinsa yanamin wannan murmushin"
Dan hade rai Jalila ta yi, wata zuciyar ta ce mata "wata kilama sunyi ways da Hanan" kara bata rai tayi,
Karasowa yayi daf da ita ya kalleta
"Baby laifin menayi miki hakane, kike hademin rai, yau duk bana jin dadi ban gankiba"
Rasa me zatace masa tayi dan kuwa babu laifin da yayi mata
"Yayana bakayimin laifin komaiba"
"Are u sure, naga kina fushi dani"
"Bazan iya fushi da kaiba"
"To shikenan kin tashi lafiya"?
" lafiya kalau,?
"Meyasa baki kawomin Abinci ba yau"? dan sunkuyar da kai tayi kasa
"Bakomai"
Maama ce tafito zata fita unguwa ta gansu tare, kallonsu ta yi ta dauke kai, Jawwad yace "Maama fita zakiyi?"
"Ka aikeni ne?"
"A a Maama a dawo lafiya"
Ta amsa da "Allah yasa"
Jalila ma tace "Adawo lafiya"
Kallon Jalila tayi ta dauke kai, taje ta bude motarta, ta shige tai waje,
Jawwad ya dawo da kallonsa kan Jalila
"Baby

Please Login or Register in order to submit comment