Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi dataga be mata komai ba

Ilham ta kalli Jalila cike da bacin rai
"Waike Dan Allah meyasa kika fiye shishshigine ina ruwanki da shi wannan fa sabgar family ce meye naki a ciki Yar karere"?

Jalila ta kalleta tai maganar kasa²
"Hmm so hana ganin laifi"

Daddyn Jalal ne yayi gyaran murya yace
"A'a Ilham abinda yayanki yake baya kyautawa abinda takwararsa tafada gaskiyane se dai muyi masa fatan Allah ya shiryeshi"

Wani dam kirjin Ilham yayi takwararsa kuma?
Tai maganar a zuciyar ta

Jalila ta karasa cikin palourn ta durkusa har kasa ta gaishe da daddyn Jalal

Mummy kuwa tuni tabar palourn ranta yana daci game da abubuwan da Jalal yakeyi Sam baya ganin kimarta a matsayinsa na Dan da ta haifa

Fuskarsa a sake ya amsa mata gaisuwar
"Jiya ake gayamin baki da lafiya har an kaiki Asibiti, dazu mummyn su zata je dubaki da safe akace Baku dawo ba,
"Yanzu ya jikin naki"?

" ai naji sauki daddy "
Tayi maganar kanta a kasa

"To dama kiran kenan in miki sannu
Ya gurin mamanki ?"
"Tana nan lafiya"
"Masha Allah kin dawo nan ne gaba daya"?

"A'a zuwa nayi nakusa komawa"
"Allah sarki in kin tashi tafiya kizo muyi sallama kafin kitafi"

"To daddy nagode"
"Yawwa Allah yabaki lafiya"
"Ameen"
Ta amsa
"To daddy seda safe"

"Allah ya tashemu lafiya daddy nagode"
"Ameen Yar albarka
Allah yayi miki Albarka"
"Ameen ta mike ta nufi hanyar fita"

"Daddy dama kasanta ne?"
Ilham tafada tana ya mutsa fuska

"Nasanta Ilham amma tun tana Karama nasan mahaifinta kanin Alhaji Mahmud ne (baban su Jawwad) mutumin kirkine sosai"

Dan tabe baki kawai Ilham tayi

Jalila kam kama hanyar fita tayi
taji an riketa a firgice ta waiwayo taga waye da wannan aikin
Jalal tagani idon Sa Jawur yana wani irin huci

Ya daga hannu ya wanka mata mari, ta gigice tana nema ta fadi, ya dagota yakuma wanka mata wani Marin
Hannu biyu tasa ta dafe fuskarta lokaci guda kuma hawaye na zubowa daga idonta,

"Why meyasa kike son shiga rayuwata?
Ina ruwanki dani?
Sa'anki ne ni ko dankinga ina kyaleki saboda yayanki nake daga miki kafa, amma ki tambayeshi waye ABDULJALAL!!!
ba a shigowa hanyata duk Wanda ya shiga rayuwata se na tabbatar Dana koya masa darasin da har ya mutu baze manta ba,
Kifita daga rayuwata nagaya miki sha³ kawai I hate u!!!"

Yafada yana kuma zazzaro mata ido

"Bazan fita ba, in har bazaka rabu da yayana ba kuma bari in gayamaka baka isa kamin abinda Allah bemin ba"

Ta fizge hannunta tai tafiyarta fuskarta na cigaba da radadi saboda Marin ya shigeta seda tai gaba ta tsaya ta waigo ta kalleshi

"Ka rubuta ka ajiye Marin nan dakayi min seka biya shi kuma na fada Mara tarbiyya, in kaji haushi kadena abinda kake, sannan ka koma makaranta Dan wannan abinda kake ba alamar Ilimi a tare da kai in kaga dama ka yayyankani ka cinye I hate u too,

Tai ficewarta ta tafi Gida, harta shiga gidan, ta tafi dakinsu bata ci karo da kowa ba,
Nana ma bata dakin, dan haka ta dau wayarta da Ilham ta kawo mata dazu
Missed calls din Ummi tagani a ciki dayawa sekuma na kawarta siyama
" Allah sarki Ummi na nayi missing dinki, dole ma inzo in tattara kayana in bar garin nan tsakanin Jiya da yau nayi Dana sanin zuwa kano ga cin zarafin da wannan matar tayimin, ga kuma wannan Azzalumin Dan shaye² da yakeneman illatani
In na tafi bazan sake zuwa kano ba insha Allah gobe zanyiwa Abba magana ni Gida zan koma"

Tai dialing lambar Ummi bugu biyu ta dauka
"Jalila meya faru nake ta kiran wayarki tun jiya da daddare amma baki daga ba?"
Ummi tayi maganar cike da damuwa

"Ummi wayace a silent kuma na manta inda na ajiyeta se dazu na ganta"

"Jalila akwai matsalane? Naji muryarki wani iri, ko baki da lafiya ne?"

"A" a lafiyata kalau mura nake ne"

Badan Ummi ta yarda ba ta bar zancen
"Ya gidan ya yan uwan baki?"

"Kowa lafiya Ummi"
"Ina fatan ba wata Matsala dai ko?"

Matsala kam akwaita very soon ma zan dawo Gida amma a zahiri se cewa tayi

"Eh babu wata matsala amma a satin nan zan dawo Gida insha Allah"

"Kin fasa hutun a nan ne?
" Eh nafasa kewarki ce ta dameni Gida zan dawo "

Ummi ta fuskanci akwai matsala Jalila bata son gaya mata ne.

"To shikenan se da safe ki gaida mutan gidan naku"

"Zasuji insha Allah, mu kwana lafiya kyakykyawar uwa"
"Ameen yar albarka"

Tagama wayar kenan Sega Nana ta shigo
"Yar uwa kin dawo Ashe ? Kiran me akayi miki ince ko lafiya"
"Lafiya kalau, dama babansu Jalal ne yamin ya Jiki, sannan yace ranar dazan tafi inzo,"
"Allah sarki babansu Jalal akwai kirki kaddarace tasa Allah ya hada shi da tantirin da, kodayake yana Dan ganin girman babansa akan mummyn shi"

"To Allah ya shiryeshi in me shiryuwane"
Jalila ta fada tana mikewa domin ta gabatar da sallar isha'i

Bayan sun kwanta Jalila takasa bacci se Juyi take kanta har ciwo yake saboda zafin Marin da ta sha

"NI KIKAYIWA LAIFI YAFIYATA YAKAMATA KINEMA BANI ZANNEMI YAFIYARKI BA KIN SAN GASKIYA AMMA KIN RUFE IDO KINAMIN FADA KECE SILAR KOWACE RAYUWA NAKE A YANZU"

Maganganun Jalal suka dawo mata To me hakan ke nufi lallai akwai wani abu a kasa

Wai meyasa duk lokacin dazan hadu da yarinyar nan se tayi abunda zata konamin rai, seta gayamin maganganun dazasu bata min rai
Meyasa ta kenema ta Shiga rayuwata, ba Wanda ya isa ya tsaya gabana yana gayamin abinda ya gadama,
Ina daga mata kafa ne saboda aminina,

Ire iren wannan tunanin Jalal ya dingayi ga mummy itama ta caza mai kai ransa yagama baci zuciyarsa a cunkushe

Dan haka ya yanke shawarar abinda ze fishsheshi Dan haka ya dau motarsa ya tafi mashaya gurin Jeje.

Jawwad ganin abinda yafaru dazu tsakanin Yaya mairo da Jalal yasan
Jalal fushi yake dashi Dan haka ya yanke shawarar zuwa yabashi hakuri.

Yaje part din Jalal amma bayanan, yashiga cikin gidansu nan ma bayanan
Ya dinga kiransa a waya amma shiru be dauka ba.
Dan haka ya koma Gida har ya kwanta yaji yanaso yasan inda Jalal ya tafi.
Danhaka ya kuma komawa gidansu Jalal don ya duba ko ya dawo,dayake Jawwad yana shiga gidansu Jalal koda yaushene tunda iyakacinsa, part din Jalal be fiye Shiga cikin gidanba se da dalili
Dan haka Jawwad yanazuwa me gadi yake bude masa ya shiga Dan shima Dan gidane.

Har yanzu Jalal be dawo ba
Har had JAWWAD ya juya ze tafi, seyaga kawai so yake yaga Jalal yaji inda ya tafi haka

Jeje kuwa yakara ingiza Jalal ya dinga tuttulawa Jalal giya, se dayaga yayi mankas ba iya komai ya dauko shi yasahi a mota yadawo dasshi gida.
Rungumo Jalal Jeje yayi ya shige dashi part dinsa saboda Sam Jalal baya hayyacinsa tangadi kawai yake

Tunda Jawwad yaji karar motar Jalal yafito kofar part dinsa ya tsaya yana jiran Sa amma seyaga Jeje rungume da Jalal ko ba a gaya masa ba yasan Jalal a bige yake, Jawwad be kulasu ba,
Hanya yabasu Jeje ya wuce da Jalal bedroom dinsa ya kwantar dashi, yazo fita Jawwad yasha gaban Jeje

"Me kabashi?sannan daga ina kuke?"
Yayiwa Jeje tambayar ransa a bace
Jeje ya kalli JAWWAD a wulakance
"Wane irin tambaya ne wannan? Kaima kasan me yasha giya CE meye kuma na tambayata ina mukaje ai kasan inda yake zuwa

" kashedi nawa nayi maka game da Jalal, kai kake kara hure masa kunne meyasa kake bibiyarsa haka?
Why? "

"Bani yakamata in baka wannann amsan ba kajira lokaci"
Daga haka jeje yasa kai yai ficewarsa

Jawwad kuwa ransa a bace yashiga bedroom din, Jalal ya tarar yana ta bacci, hade da surutai cike da maye
Girgiza kai kawai Jawwad yayi Allah ka shiryi bawanka Allah ka nunamin Jalal yazama mutumin Arziki.

Washe gari da safe iyalan gidan sun hadu a palour suna karyawa, kowa ya maida kai yanacin abinci amma banda Jalila wadda taketa juya cokali tana cakalar abincin JAWWAD ne ya kalleta

"Lafiya kuwa sisy ba kyacin abincin fa ko akwai damuwane?"
Jawwad yafada cike da kulawa

"Nima na lura da hakan bros tun jiya naga bata walwala"
Nana ta fada tana kallon Jalila

Maama kaam Dan kallonta yayi ta tabe baki ta cigaba da cin abincinta

"Duk Ku tsaya Yar albarka gayamin meke faruwa ne"?
Abba yafada cike da kula yana kallon Jalila

Hawaye ne yazu bo mata Wanda bata San zasu zubo ba,

" subhanallah Jalila meyafaru, me akayi miki"
Suka shiga hero mata tambayoyi

Jimin munafukar yarinya wayamata wani abu dazata kama yiwa mutane kuka kalli yadda duk suka bats attention lallai maganar Yaya mairo akwai kamshin gaskiya
maama tayi zancen a zuciyarta

Gaba daya attention dinsu ya dawo kanta suna mata tambayoyi

"Abba ni Gida nake so in koma"
Tafada a hankali

"Wani abun mukayi mikine?"
Nana tafada kaman zatayi kuka

"Kunga Ku tsaya, Jalila anyimiki wani laifinne in wani abun mukayi miki kigaya mana"
Jawwad yayi maganar yana kallon cikin idon Jalila
Abba yayi gyaran murya yace

"Yarinyar kirki meyasa kikeso kikoma Gida? ko mune ba kyasan zama damu"

Girgiza kai tayi
"a'a Abba ni ba abinda kuka yimin kawai ina kewar ummi ne, sonake inkoma gurinta"

Maama ji tayi kaman ta kwashe Jalila da mari saboda gulma Dan kawai tanaso takoma Gida shine zata yiwa mutane kuka salon ace wani Abu sukayi mata

(Wato maama taji zigar yaya mairo)

"To shikenan yarinyar kirki yaushe kikeso ki koma gidan?
Tunda kin gaji da zama damu"

"A'a Abba ba gajiya nai da zama daku ba, ba abinda kukayi min,
Gobe nakeso in koma"
Tafada tana sunkuyar da kai

"To kibari ranar juma'a insha Allah se Jawwad ya maida ke gida hakan yayi miki?"

Murmushi Jalila tayi tare da gyada kai

"Shagwababbiya kawai shine seki mana kuka Dan kina kewar Ummi?"
Jalal yafada cikin zolaya

Maama dai batace uffan ba
Haka dai suka kammala breakfast din

Suna komawa daki Nana ta kalli Jalila
"Jalila me mukayi miki zaki tafi kibarni
, hutu fa be Kareba
Naji dadin zuwanki meyasa zaki tafi ki barni"?
"Haba Nanancy na nifa bukuyi min komai ba kawai inaso in komane"

"To yaushe zaki kuma zuwa"?
"Zan kuma zuwa Nana karki damu"
"To shikenan zanyi missing dinki"

Nana ko zan kuma zuwa gidanku se bayan dogon lokaci, idan nacigaba da rabar Ku kiyayyar da mahaifiyarku kemin zata fito fili
Ga wannan azzalumin makocin naku abokin Jawwad

Amma a zahiri se ta rungume Nana
Karki damu Yar uwata I will miss you too

Ran Alhamis da daddare Shirin komawa Gida sosai Jalila takeyi ta hada kayanta cif ji take kaman ba itaba zata koma Gida gurin umminta

Nana ce ta raka Jalila gidansu Jalal domin tai musu sallama,

Ilham suka Tatar tana shirya abinci a palour
Kaman kullum Ilham se hararan Jalila takeyi kuma har Jalila tai kwanciyar Asibiti bata taba cemata ya jiki ba

"Gurin mummy mukazo ba gurin Jalal ba naga kina hararata"

Jalila tafada da sigar Neman magana
"In ma gurin nasa kikazo biki isheshi kallo ba Dan ba macen dayake gani bayan Ilham"
Ilham tai maganar cike da tsiwa dakuma gadara

Aikuwa Jalila tafara dariya
"Shi Jalal dinko, yanzu akansa kike wannan abun hh wani jan idonsa kaman ansa masa tear gas"
Jalila tai maganar tana dariya

Iya kuluwa Ilham ta kulu amma kafin tayi maganar Nana tace
"Dan Allah kuyi hakuri wannan wasannaku karshensa fadane
Ina mummy? gurinta mukazo"

Haka Ilham ta kaisu part din daddy Dan mummyn tana can
Itakuma tadawo palour

Jalila tayi musu sallama cewa gobe in Allah ya yadda zata tafi
Daddy yace to ta gaida mamanta yayi mata addu'a kuma insha Allah zemata aike haka sukayi sallama da mummy ma

Suna fitowa daga part din Daddy kaman kullum wata dramar ake

JALAL da Ilham se masifa yake zazzaga mata kaman ze dake ta tana bashi hakuri kaman wani ubanta

"Kina abu kaman wata dabba kinfiye naci wallahi inkina da zuciya karki kara zuwa inda nake kokice zaki dafa wani abu kibani, bana so ko ana dolene?"
Idon Ilham taf hawaye
"Dan Allah kayi hakuri Yaya bazan iya dena zuwa inda kake ba"

Aikuwa dariya Jalila ta kwashe da ita
"Tab laila majnun amma gaskiya iska tana wahalar dame kayan kara"

Wannan wace irin mayyar yarinyace tantiriya me bakin naci

Share please


Nasan kunada Tarin tambayoyi but keep following me amsoshin suna nan tafe cikin littafin
ABDUL JALAL (2020)


More comments more typing...............

🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
[8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_
(2020)

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 11

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
What's https: //chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Is a free book

Ina yinku AbdulJalal novel fans irin💯💯💯 da duk sauran masoya wannan novel ina jin dadin comments dinku love u all ❤❤❤

I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢
Your comments give me courage



-my first Novel-

Kafin su Ankara takuma yi musu wani shouting din
"Ku tafi kubani guri"
Sun² suka fice su ka bar gurin dakinta ta koma ta cigaba da sintiri to yanzu ya zatayi meye mafita washe gari takuma sawa aka nemo mata
Abiola da yarabanci sukayi magana wannan karon

(kunsan dai ni ba yarabanci nake ji ba Dan haka bansan me suka ce ba)

Naga Abiola ya daga kai ya kalleta a razane

"Ko bazakayi ba"
ta tambayeshi

"Zanyi yanda kikece"
Ya fada Kansa a kasa

"Mark u idan maganar nan ta fita wani yajita hukuncinka shine..
Tai taku biyu
" life imprisoned!!! "
Ya dago da sauri ya kalleta

"Yes " tafada tana kallonsa "you can leave"

Da la'asar har camp Abiola yaje ya lallabo Aliyu ya fito da shi kan cewar za suje yawon shakatawa ne,

Wani hadadden lambu ya kai Aliyu, an kawata lambun da kayan itatuwa masu matukar kyau gurin yayiwa Aliyu kyau matuka,

"Gaskiya gurin nan yayi kyau so cool"
Aliyu yayi maganar yana murmushi tare da shafa Kansa

"Dagaske gurin yayi maka kyau"
Sukaji muryar mace a bayansu
Abiola yasan muryar wace dan haka yakara nutsuwa tare da sunkuyar da kai

Aliyu ne ya waigo yaga me maganar sanye take da riga da skirts na atamfa kanta ba Dan kwali
matashiyar budurwace bazata fi shekara goma sha takwas ba ba dai fara ce ba amma tana da kyau black beauty ce

Takuma maimaita abinda tace
"dagaske gurin nan yai maka kyau"
Tafada tana murmushi, Wanda seda dimples dinta ya lotsa ta kara kyau
Shima Aliyu murmushi yayi mata

"Sosai makuwa gurin yayi matukar kyau kuma da kikazo seyakara haskawa kyansa ya kara fitowa"
Murmushi ta kuma yi

"That's good"
Tafada tana kallonsa
"Akwai gurare masu kyau a garin nan gurare masu saka nishadi, Wanda nasan babu su a garinku"
Tafada tana Dan kashe masa Ido

"Kinsan garin namune kika fadi haka"

"No ba kayi kama da yan garin nan ba shiyasa nasan ba Dan garin nan bane kuma bana tunanin kanajin yarenmu"

Shikam abiola gefe yakoma ya nutsu kaman bashiba

"Hmm to garinmu yafi naku kyau"

"Wane gari kenan?"
Ta tambaya

"Se dai ki canka"
Ta Dan kalleshi
"Kana kama da hausawa"

"Yes ni bahaushene"

Jikinta ne ya danyi sanyi ta dan tafi tunani

"Akwai matsalane?"
Girgiza kai tayi
"A'a babu"
"Bari in tafi kar mamana tai min fada na Dade"
Ta juya tafara tafiya

"To ai baki gayamin sunanki ba"
"Marry"
Tabashi amsa a takaice
"Maryam, a nice name"

"Ki ban lambarki mu dinga gaisawa mana kinga semuje ki nunamin inda yafi garinmu kyau"
Murmushi tayi masa ta bashi lambarta sannan ta tafi

"Abiola naga tunda yarinyar nan tazo kawani kame a gefe ko kasanta ne kokuma akwai matsalane baka gayamin ba?"

MatsalaBabba ma kuwa
Amma a fili se yace

"A'a bawani matsala kawai dai na Baku gurine"

Tun daga nan Aliyu ya jone da marry kullum cikin waya suke in tanaso ta ganshi se tace su hadu a lambu

Yayi² ta nuna masa gidansu amma se tace in mamanta ta ganta da wani zatayi mata fada ne
Sunyi matukar shakuwa soyayya suke sosai mussaman tayi masa girki sufita guraren bude ido
Dukda kasan cewarta kirista bata shigar banza sedai yawo ba dan kwali shima Aliyu ya hanata

In lokacin salla yayi zata jirashi yayi salla koma ta tuna masa, suka shaku matuka amma besan wacece ita ba, tanayin abubuwan dasu kan bashi mamaki, indai zasu hadu ko Suyi waya setayi masa sallama, gashi lokaci zuwa lokaci yakan ji tace masha Allah, subhanallah da maka mantansu
Se yayi zaton kawai saboda yana yawan fada ne itama takeyi

A kwana a tashi gidansu marry aka fuskanci sauyi a tare da ita sakamakon yawan fita datakeyi,
Kuma fitar ma ita kadai dan haka aka tsaurara mata tsaro ta shiga damuwa sosai rashin ganin Aliyu da batayi sedai suyi waya abun ya dameta matuka,

Aliyu yace tabarshi yazo shi Inda take amma tace masa baze yiwu ba,

Wasa² suka shiga matukar damuwa saboda rashin ganin juna
Abiola yake gayawa abinda yake faruwa
Abiola ya tausayawa Aliyu ganin yadda marry ta jashi fage me matukar wahala dakuma hatsari
(Wato soyayya)
Gakuma banbancin addini da kabila ga kuma uwa uba dokar masarautarsu

Aliyu yasaka ranar zuwa kano domin yaga gida don kusan watansa hudu a kogi state haduwarsa da marry ne ya mantar dashi kewar Gida datake damunsa da farko,

Wata rana Suna waya da daddare shida marry yake gayamata yanaso yaje kano domin ganin Gida

Kuka sosai ta kama yi masa ya shiga damuwa

"Haba maryam ya haka zaki tayarmin da hankali kin hanani zuwa inda kike kinki bari mu hadu,
bakisan yadda nakeji ba ne naga kaman baki damu ba ko baki yadda dani bane bansani ba"
"Noo bahaka bane nima ina cikin damuwa an samun tsaro sosai, am sorry Aliyu akwai abunda na boye maka amma inaso mu hadu kafin ka tafi"
"A ina zamu hadu ?"
Yai mata tambayar cike zakuwa

"Inda muka saba haduwa a garden"
"To shikenan kaman karfe Nawa?"
"Da yamma by God will"
"Allah ya kaimu da rai da lafiya"
"I love u Aliyu"
"Love u more my dear"
"Kamin wani Alkawari"

"Wane Alkawari ?"
"Will u marry me?"

"I will me sunan mum insha Allah in dai family dinku zasu yarda dani su bani auren ki, bantaba soyayya ba se akanki, akanki nafara kuma daga kanki nagama insha Allah"
Ajiyar zuciya tayi

"Aliyu ka kwanta karka makara sallar Asuba kaimin addu a lamuran suzo da sauki"

"Kullum inayimana kiyi bacci me dadi zanzo a mafarkinki muje yawo"
Dariya sukayi suka kashe wayar

Kaman yadda tayi masa Alkawari haka tayi kokari seda ta fito daga Gida bawanda yasani

Inda suka saba haduwa yauma anan suka hadu
Se dai sabanin sauran kwanaki dasuka saba haduwa yau fuskarta dauke take damuwa

Kusa dashi ta zauna shiru ya Dan ratsa
Sannan ya kalleta
"Baki da lafiyane?"

Ta girgiza masa kai
"Ya akai kikayi wannan ramar haka meyake damunki, tell me, meyake faruwa"
Idonta taf hawaye ta kalleshi

"In ka tafi yaushe zaka dawo?"
"Bazan Dade ba insha Allah"
"Dagaske kake zaka aureni?"
"Am serious ina sonki son da bantaba zaton zanyiwa wani makamancinsa ba bayan Dan uwana I love u with all my heart"
"Aliyu ina sonka Dan Allah in kagama service ka tafi dani garinku ka aureni musulunta zanyi"

Mamakine yacika Aliyu ba maganar da tayine ya bashi mamaki ba illa magana da tayi da harshen Hausa Wanda be taba zaton ko zo tasani da hausaba

" Noor (sunan da yake kiranta dashi kenan)
Dama kin iya Hausa?"

"Na iya Hausa"
Tabashi amsa
"How comes ban taba ji kinyiba"

Wata nannauyar ajiya zuciya ta sauke

"Mamana kiristace babana kuma musulmi ne kuma ba haushe ne family din babana dukansu musulmai ne kuma musulmi suke aure

Baba nane kadai ya auri kirista wadda ta kasance ya mace tilo a masarautarmu yan uwanta duk mazane dan haka ake matukar sonta a cikin masarautar da ta ISA aure ta dage akan wannan musulmi take so akayi² ta hakura taki Dan haka aka kyaleta ta aureshi
Tunda ta aureshi ya tafi da ita take samun cusgunawa daga dangin mahaifina suka takura mata da kyama da tsangwama a daddafe ta haifeni ta yayeni babanta yece sedai ta dawo Gida a hakura da auren ba za adinga wulakanta masa ya ba a matsayinsa na sarki me fada a aji amma ace ana wulakanta yarsa a gidan aure
Dangin mahaifina suka kwaceni shekarata takwas a hannunsu babana ya rasu a gurin kakata na zauna ita ke koyamin karatun addini shekarata takwas amma na haddace izu ashirin na Qur'ani

Da mamana taji rasuwar mahaifina ta daga hankalinta akan se an batani ,
An kai ruwa rana seda kakana ya hada da karfin mulkinsa sannan aka karbeni daga dangin mahaifina

A gurin kakannina ni musulma ce na iya abubuwa dayawa kuma na tashi da Hausa a bakina dana dawo nan mamana ta maidani addinin ta sannan tayi Alkawari bazata bari inyi gangancin datayi ba, family dinmu ba a auren Wanda ba yarenmu ba ko kuma ba addinin mu ba tun daga kan mamana akasaka wannan dokar"

Tana kaiwa nan ta sauke ajiyar zuciya

"Meyasa tun farko kika boyemin hakan, why"?

Idonta taf da hawaye ta kalleshi
" please Aliyu don't leave me tun randa kukazo da abiola na ganka naji ina sonka kate makamin Aliyu, in kai haka zaka ceceni daga halaka danakee ciki zan samu damar komawa addnina na musulinci"

"Lallai abiola munafiki ne shine ya kyaleni nake ta fama ko Ashe yasan komai"

"Ni nahana shi yagaya maka Dan Allah Aliyu kar kaarabu dani kayi Alkawari zaka aureni"
Kuka take sosai

"Is OK ai bance miki nafasa ba Dan haka kiyi shiru zansan yadda za ayi zanzo innemi aurenki a gidanku"

Zaro ido tayi tace baze yiwu ba ita dai kawai ya tafi da ita basu saniba

"Idan nayi haka banyiwa iyayenki adalci ba kibari inje kano in dawo zamuyi abinda yakamata"
Haka sukayi sallama kaman bazasu rabu ba

Aliyu ya dawo kano cike da tunanin noor (marry) sunyi farinciki da ganinsa, dayake da weekends ya dawo yaita zuba ido yaga Jawwad amma be Ganshi ba

"Wai INA Dana ne" ya tambayi Usman
"Hmm wallahi wani yaro ya hadu dashi a kusa da makarantarsu, sun likewa juna yaita kuka se an kaishi gurin yaron, shima yaron in aka tashi daga tasu makarantar seyabiyo shi gida direbansa da malaman makarantarsu suyita nemanshi se mun maida shi makarantarsu yayita kuka,
To shine babansa yace Dan Allah da weekends akai Jawwad kokuma shi akawo shi akawo shi nan"

"wannan wane irin shirmen banza ne kawai Ku dauki da Ku kaiwa mutanen da Baku Sani ba to ni ban yaddaba, akan me kawai ni gayamin inane inje in dakko shi"

"Sannu sarkin azarbabi kai ko kara babu, gidan mutanen kirki ne har nan mahaifin yaron yazo ya roki alfarma yanzu yasakasu a islamiyya daya"
Inna mairo ce take wannan jawabin

"Au saboda wulakanci had da canza masa makaranta haka akeyi kaikuma kana zaune"

Seda aka gaya masa gidansu yaron yana gadon kaya Yakama hanya ya tafi dakko JAWWAD,
yana zuwa ya tarar an shiryasu me gidan ze fita da su Jawwad da wani yaro da befi sa'an jawwad ba
Da gudu Jawwad ya tafi ya rungume Aliyu ganin haka yasa shima Yaron ya tafi ya rungume Aliyu, ya rungume su gaba daya
Suka gaisa da mutumin
Aliyu Yace masa

"Dana Nazo dauka"
"Wanne kenan?"
Mutumin ya tambayeshi
"Jawwad mana"
"To ai har gida na tura aka dakko shi da izinin mahaifinsa"

"To ai nine babansa tafiya nayi ne kuma na dawo abani Dana ban yadda ya dinga zuwa wani guri yana zama ba"
Yayi maganar yana janyo hannun Jawwad aikuwa Jalal ya fashe da kuka ya bisu yana "daddy kace ya dawo min da shi"
Aliyu ba yadda beyi ba adena kai Jawwad gidansu jalal amma abu yaki,
Inma ba akai Jawwad ba za akawo JALAL sekace tagwaye

A yan kwanakin da Aliyu yayi a kano Dan uwansa ya fuskanci akwai abunda yake damunsa saboda Sam baya walwala sosai

Usman ne yaje ya sameshi adaki yana waya da marry ya jirashi ya gama sannan ya mai tambayar

"Dan uwana me yake damunka ne naga Sam Baka da walwala ko akwai wata damuwa ne"?

" akwai kam yayana"
"Me yafaru?"

Usman ya fada yana kallonsa
Be boye masa komai ba ya gaya masa halin dayake ciki

Jinjina kai yayi
"Gaskiya Dan uwa ka debo da zafi shawarar da zan Baka ka hakura bana tunanin abin nan ze yiwu kasamu wata anaan ka aura"
" a lokacin da ka dakko naka Auren waya hanaka, kamin addu a kawai bana son wanna shawarar taka , tashi kabani guri'"
Aliyu ya fada yana nuna masa hanyar fita

Satinsa daya a kano ya koma kogi state an kai ruwa rana sosai a gidansu marry da aka gano tana soyayya da

Please Login or Register in order to submit comment