Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baki guri"
Haka Maama ta fita ta bar dakin, lallai yayi fushi, abune mawuyaci kaga fushinsa, bashi da hayaniya sam amma wannan karon ransa ya gama baci.
Dare yayi Nana ta samu guri ta kwanta, Jawwad kuma ya zauna akan kujerar dakin a haka bacci ya daukesu, cikin dare Jalila tafara motsawa tana atishawa, da sauri Jawwad ya tashi yana kiran sunan ta, tana gama atishawar tacigaba da baccinta, ba tareda ta tashiba, tunda ga wannan farkawar da tayi, Jawwad be kuma komawa bacci ba har gari ya waye,
Da safe Abba ya shirya ba tareda ya kula Maama ba, a palour ya tarar da halima da hijjabinta, ta gaishe da Abba ya amsa, tace
"dan Allah sonake in bika inga jikin Jalila, tunda aka kaita Asibiti ban dubata ba"
Ta karashe maganar kaman zatayi kuka, Abba yace ta taho su tafi, da sauri Halima taje kitchen ta dakko, kayan tea data dafa ta bi Abba, Abba a ransa yace "Baby ko bayan raina, nasan bazata rasa mutanen kirki dazasu kula da itaba, kodan saboda kyawawan halayenta, Halima me aiki duk ta damu, hada dawainiya haka, amma matarsa dayake tareda ita yake kyautata mata da danginta amma takasa yimasa alfarma akan yar dan uwansa saboda wani dalilinta mara tushe"
Haka Halima ta shiga bayan motar suka tafi Asibiti, koda suka isa Asibitin, Halima taga Jalila da yadda ta rame seta fashe da kuka, Abba yace tayi shiru ta dinga yimata addu a, bayan Abba ya duba Jalila ya tafi gurin aikinsa,
Hawaye halima ta cigaba da sharewa,
Jawwad yace "Halima kidena kuka cikin dare tayi atishawa akwai yuwuwar, ta farka a kowane lokaci, daga yanzu, kidena kuka, kimata addu a" gyada kai Halima tayi sannan
Jawwad yace tunda ga Halima tazo, bari ya kai Nana gida tayi wanka taci Abinci, Nana ta tashi suka tafi, aka bar Halima a gurin Jalila,
halima ta mike ta koma kujerar gaban gadon Jalila, ta kifa kanta a gefen Jalila tana share hawaye,
"Allah yabaki lafiya, Jalila, Allah ya dubi maraicinki, ya baki lafiya"
Doctor salis da kansa ya shigo yayiwa Jalila allurai, ya samata wani ruwan, yauma tsayawa yayi yana karewa Jalila kallo, Halima ta dan kalleshi,
"Likita wai yaushe zata farkane? kwananta biyu a haka fa" doctor salis ya kalli Halima, "karki damu muna sa ran zata tashi ba dadewa,"
Halima tace "Allah yasa"
Daga haka doctor ya fita,
Yayi awa daya da tafiyar su Jawwad, Halima taji an turo kofar dakin, dan dago kai tayi ta waiwayo, da mamakinta taga Jalal ne, seda gabanta ya dan fadi, dan batayi zaton ganinsa ba, ran nan nasa a hade ba fara a, babu alamarta, mikewa halima tayi daga kan kujerar da take, ta koma gefe
Ta dan risina sannan tace "Ina kwana" be amsaba yace mata
"Ina Jawwad?"
"dazu suka koma gida, amma zasu dawo"
Gyada kai yayi ya jawo wata kujerar ya zauna ya harde kafa, yana karkadawa sekace wani basarake, ya zaro sigarinsa ya kunna, Halima ji tayi duk ta tsargu, ga mara lafiya a kwance amma taba yake sha, ji tayi duk ta takura, dan haka ta mike ta fita ta bar dakin,
Yana nan zaune yana shan tabarsa, yaga kafar Jalila tana motsawa, a hankali ta fara motsawa, tana kokarin bude idonta, a hankali ta cigaba da motsawa, ta bude idonta, dishi2 take gani kafin daga baya kuma ta bude idonta fes akan Jalal zaune kan kujera da taba a hannunsa, kallon dakin dake ciki tayi, tana kokarin gane mafarki takeyi kokuma a gaske ne, yunkurawa tayi zata tashi zaune amma taji cikinta ya kulle, ta kasa tashi, Jalal yana kallon ta amma be cemata uffan ba,
Yunkurawa tayi zata kuma tashi zaune, ga drip da yake shiga jikinta, tana nema tasa ya goce, Jalal ya kalleta,
"Malama kikoma ki kwanta, idan ruwan ya goce kuma fa, wayace ki tashi zaune daga farkawarki," ya fada a dan tsawace se yanzu Jalila ta tabbatar da ba mafarki take ba, tashi yayi yaje ya zare ruwan da ke shiga jikinta,
Yai waje, office din doctor salis yaje ya gaya masa Jalila ta tashi, da sauri salis ya Mike yana fadi" Alhamdilillah, gani nan zuwa " Jalal yakoma ya tarar Jalila ta lumshe ido, tanajin motsin Jalal ta dan bude ido tana kallonsa, ko ta kanta be kuma biba yasamu guri ya zauna, doctor salis ya shigo, yai sallama, ya kalli Jalila, ya kira sunanta a hankali ta bude ido ta kalleshi,
" sannu ya jikin naki" gyada masa kai kawai tayi, doctor salis yace
"Yanzu me yake miki ciwo" cikin muryar marasa lafiya, tareda shagwaba tace "Ni sonake in tashi in zauna, cikina kuma ciwo yakemin, nagaji da kwanciya amma nakasa tashi" ba karamin jin dadin muryarta doctor salis yaiba
"Ok zaki iya tashi zaunen"?
"A a nakasa tashin"
"Ok let me help you, sit up" ya kai hannu yana kokarin tabata, da sauri tace "A a nika kyaleni zan tashi da kaina"
"Bazaki iya tashiba, ki bari in temakamiki"
Yamutsa fuska tayi, "Nace maka ka kyaleni"
Jalal dake gefe yace "to ka kyaleta mana dolene, tunda tace bata so, base tayi ta kwanciyar ba,"
Kallon Jalal tayi ta dauke kai, salis yana jin tsoron Jalal, saboda yanada matukar kwarjini, dan haka yabar maganar temakamata ta tashi zaune, yace, "in Jawwad yazo, akwai magani daze siyo abata, amma a tabbatar taci abinci, dan zata bukaci abinci, asamu abu me dan ruwa2 abata ta sha,"
Jalal bece komai ba, doctor yai waje, Jalila trying ta kumayi ta tashi amma gefen cikinta a kulle, taji kamar an soka mata wani abu a cikinta zuwa zuciyarta, a hankali ta danyi kara, ta koma ta kwanta, kukanta ne ya karu yanzu hada sauti, da sheshsheka, takeyi, Jalal ya kalleta yai tsaki
"Malama kimin shiru kincikamin kunne,"
Banza tayi masa ta cigaba da kukanta
"Ni wallahi nagaji da wannan kwanciyar bayana ciwo yakemin"
Shiru Jalal yai mata, yacigaba da danna wayarsa, ita mamaki ma takeyi, me take a asibiti ita da Jalal ina yan gidansu, tanaga dai mafarki takeyi, kukanta tacigaba hawayene na bin gefen idonta,
tashi Jalal yayi ze fita, har yaje bakin kofa, ya dawo ya kalli Jalila yasa hannu ya dago Jalila daga kwanciyar da take, ya jinginar da ita, ji tayi gefen cikinta ya kara kullewa, saboda ba a hankali ya dagata ba
Ihu tayi ta rike hannunsa da karfi tana fadin
"Wayyo Allah cikina, ni cewa nayi ka dagani, saboda mugunta, bakasan me nakejiba, zaka dagoni a haka wayace ka tabani" ta fada tana hawaye, dan tsuramata ido yayi, ita dai bazata canzaba da kyar take magana, kai dakaji muryarta kasan tanajin jiki, amma bazatayi shiruba
"yimin shiru ko in maidake inda kika taso" dauke kanta tayi, kamshin turaren Jalal da warin sigarin dayakene Yasa Jalila taji tana yinkurin amai, dama gashi kwanakin nan cikinta ba komai, shi ya haddasa mata kullewar cikin,
Daga haka Jalal yai waje ya barta, Halima tana reception taga wucewar Jalal dan haka ta mike ta nufi dakin da Jalila take, tana zuwa ta tarar da Jalila a zaune, zare ido Halima tayi, ganin Jalila a zaune "Jalila kin tashi sannu"
Murmushi Jalila tayi, kafin tayi magana, Jawwad yai sallama, shima da mamaki yaga Jalila a zaune, da sauri ya karasa gaban gadon "Baby kin tashi sannu, ya jikin"
"Da sauki yaya Jawwad, ina kuka tafi kuka barni, anan ni kadai, waima me nakeyi anan"
"Bakida lafiya ne muka kawoki nan, yanzu me ke damunki"
"Cikina ne yakemin ciwo, da kirjina,"
"Ok Sannu bari inkira salis"
Halima tace "likitan yazo dazu yace abata abume ruwa2 ya mata allurai"
"Ok temakamata tayi brush, ina zuwa"
Jawwad na fita Jalila tace "Halima wai meyasameni ne, aka kawoni Asibiti"
"Bakida lafiyane kawai"
Halima ta dakko toothpaste da brush amma Jalila takasa sakkowa daga kan gadon, dan data motsa ko ina ciwo yake mata, bama ya cikinta,
Haka ta hakura, ta zauna akan gadon tayi brush tai alwala, ta kalli Halima
"Halima yaushe aka kawoni nakasa tuna komai, bansan sallan me zanyiba yanzu"
Dan shiru Halima tayi, dan bata san mezatace mata ba,
Jawwad ya shigo da leda a hannunsa, "sannu halima tayi brush dinne?"
"Eh tayi,"
Tea yasa halima ta hada, yazo gaban gadon Jalila ya zauna, yace "Baby karbi kisha se kisha magani"
Ta kalleshi "Yaya Jawwad salla zanyi, amma meyasameni aka kawoni asibiti"
"kinga kiyi hakuri, fara sha tukuna zamuyi magana"
Karba tayi ta dan sha kadan, yana shiga cikinta, taji ya murda ajiyewa tayi, idonta ya ciko da hawaye, zeyi magana wayarsa tafara ringing,
Yana dakko wayar yaga Abdallah ne yake kiransa
Dagawa yai yasaka a kunnensa tareda yin sallama, suka gaisa da Abdallah,
"Aliyu meyasamu wayan Jalilane? Hanan ta kirata tagaji bata shiga"
"Eyya batada lafiyane, kwananta biyu tana asibiti"
"Subhanallah me yasameta haka?" seda Jawwad ya kalli Jalila sannan yace
"ba ta jin dadine, amma taji sauki Alhamdilillah"
"Allah sarki, amata sannu dan Allah, zan gaya ma Hanan din insha Allah"
"to shikenan a gaida mutanen gidan"
Jawwad ya maida hankalinsa kan Jalila, hawaye ya gani shabe2 a fuskarta
"meya farune, Dan Allah baby kisha kinji"
"Yaya Jawwad ni na koshi, cikina ciwo yakemin"
Ana haka Jalal ya dawo, "Jawwad kana nan". "eh Jalal nakoma gida na maida Nana ne, sannu da zuwa dan uwa"
"Yawwa yanemi guri ya zauna"
Jawwad ya maida hankalinsa kan Jalila, suka cigaba da fafatawa da Jalila taki cin Abincin, Jawwad se wani lallabata yake tana wani shagwaba, taki cin Abincin balle ta sha maganin, Jalal ransa yabaci ya dan kalli Jawwad
"Namanta ban gaya maka ba, dazu kafin inshigo doctor Salis yace kaje, yana son ganinka"
"Ok bari ta ci Abincin se inje"
"No kaje kaji kowani abunne mana"
Jawwad ya mike " to Bari inje," ya juya ya kalli Jalila"baby dan Allah kisha tea din nan kinji, yanzu zan dawo" Jawwad ya juya ya fita, yana fita ya rage daga Jalila, Halima se Jalal,
Jalal ya kalli halima yace "hada wani tea din a katon cup" ba musu Halima ta hada, yasa hannu ya dauka ya mike ya nufo gadon Jalila, yana zuwa ya dire cup din a gefenta, ya hade rai
"dauki ki shanye"
Zunbura baki tayi "nina koshi, tayaya zan iya shan wannan uban shayin" tsawa ya dakamata "Ki dauka nace, se wani shirme kikeyi shikuma yana biye miki, inkin ki sha, wa kikayiwa inba kankiba, ki dauka ki shanye nace, kokuma wallahi in danneki se kinsha katon cup din nan biyu, danni ba Jawwad bane"
Kallon cup din tayi, ta kalleshi yanayin fuskarsa ya tabbatar mata he mean what he said, fuskarsa babu alamar annuri, Halima kam tana gefe tana kallon ikon Allah, hannunta na rawa ta dau cup din, tana fara sha seda taji kaman ana kuma nannade mata hanji, yamutsa fuska tayi, tana dan sha a hankali, shikuma ya kakkafeta da jajayen idanunsa duk ya takurata, dire kofin tayi "ni gaskiya na koshi"
Bece mata komai ba, ya cigaba da kallonta, itama kallonsa tayi, "to waini bana koshi ba" wani mugun kallo yacigaba dayi mata, ba shiri takuma daukan kofin tana sha tana haawaye ga wani amai dayake tasomata,
"Wallahi kikayimin amai sekinsha cup uku"
Da kyar da nishi Jalila ta shanye tea din nan tana zare ido tana kuka, seda ta shanye shi tas, sannan ya koma inda ya tashi ya zauna,
Jawwad ya dawo da magani a hannunsa, ya duba cup din tea yaga ba komai a ciki yace "Yawwa baby ashe kinsha saura magani kuma" shima maganin da kyar tasha, taji dadin jikinta sosai, har tasamu tafara rama sallolin da suke kanta
Jawwad ya kira Abba yagaya masa Jalila ta tashi, Abba yayi murna yace Insha Allah yana dawowa zezo ya dubata,
anci sa a Maama tazo ta dubata, bisa shawarar yaya mairo, amma ta tsorata dataga Jalila dan ba karamar rama tayi ba,
Jalila tace "Maama ina Nana"
"anan ta kwana, shiyasa yanzu nahanata zuwa, gara ta zauna ta huta" daga nan Jalila bata kuma cewa uffan ba, Mama batafi minti goma da zuwaba ta tafi abunta,
Bayan tafiyar Mama, Jalila ta kalli Halima tace "Halima wai kwana na nawa a asibitin nan ne? Ni dai nasan lafiya ta kalau"
"Kwananki biyu cif"
"Kwana biyu kuma"?
Jalila tayi shiru tana tunani kaman an tsinkuleta ta fashe da kuka ta kalli Jawwd
"Yaya Jawwad ina Ummi ba a ganta ba ko? Wai dama duk abun nan ba mafarki nakeba, Jawwad ina Ummi, ta mutu ko?"
Jawwad yace "A a Baby Ummi bata mutu ba har yanzu ana nemanta"
"Yaya Jawwad kacemin ta mutu kawai, shikenan nikam ita kadai taragemin dama, nasan ta mutu, haba Ummi, meyasa kika tafi kika barni, dan Allah Ummi ki dawo"
"Ke dalla kiyi mana shiru, daga farkawarki kina ma mutane kururuwa a asibiti, wayace miki mutuwa tayi,? Zaki dinga yimana ihu, kowa ba gatansa Allah ba"
"Ba ruwanka dani nayi kukan, ko dan kai bakasan darajar uwaba kake gani kowama haka ne agurinsa, dole inyi kuka, bansan halin da uwata ke cikiba, dakasan soyayyar da da uwa dabakamin tsawa ba, ita kadaice dani, ba uwa ba uba ba dangin uwa, " tana maganar tana hawaye numfashinta na fita da sauri
Jalal zuba mata ido yayi, wani abu na sukarsa a zuciyarsa, tabbas besan soyayyar tsakanin da da uwaba,
" Jalila meye haka, sa ankine shi, kike gaya masa haka"

Jawwad ya dakawa Jalila tsawa abunda be tabayiba

Share please
More comments more typing.............................


🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
🌹🌹[9/23, 10:27 AM] +234 802 426 7634: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 47
PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske,
Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what's app akan wannan lambar wayar
07063065680
Ina godiya matuka Allah yabar kauna

_My first novel_

Mamakine yakama Jalila jin yadda Jawwad ya mata tsawa, abunda betaba yi mataba,
"Jalila meyasa kike haka, na sha gayamiki Jalal ma kamanni yake agurinki yayanki ne shima"
Dauke kanta Jalila tayi, ta cigaba da zubar da hawaye, Jalal juyawa yayi ya fita yabar dakin, Jawwad ya bi bayansa
"Jalal dan Allah kayi hakuri, rashin fahimta ne tsakaninka da Jalila amma bazata karaba, yanzuma tana cikin damuwane shiyasa"
Murmushi Jalal yayi "Never mind dan uwana, nima ba fushi nayi ba, Allah yakara sauki" daga haka ya nufi motarsa ya shige, sam Jawwad beji dadin abunda Jalilan tayiba bata kyauta ba, be kamata ace tagayawa Jalal wannan maganar ba dukda basa jituwa, yasan ba danshiba babu wanda ya isa yagaya masa wannan maganar ya kyale,
Ya juya ya koma cikin Asibiti, yaje ya tarar da Still Jalila tana kuka, tana surutai akan Ummi, Halima nata bata hakuri, bebi takanta ba, ya kwashi wayoyinsa ya kwasa ya fice daga dakin.
Ana idar da sallar magariba Abba yazo, yaji dadin ganin Jalila, ta farfado ta fara samun sauki, sedai tarame sosai, ta danyi duhu, shima Abban haka ta dinga masa kuka, tana surutai, ita ummi,
Abba ya shiga yi mata nasiha me ratsa jiki
"Jalila ki karbi kaddararki a duk yadda tazo miki, nima inata kokarin inga munsamu inda take amma abun ya gagara, inkika mika al amuranki ga Allah komai zezo da sauki, jikina yana bani har yanzu tana raye, kuma zata dawo, karki cutar da kanki da wannan kukan da kikeyi, "
Abba ya kalleta sannan ya kira sunanta" Jalila"
"Na am Abba"
Ya cigaba da cewa "nidin nan ma misaline a gurinki, ba uwa ba uba, ba danuwana, gashi bamu da wasu dangi nakusa kona nesa, nasan bazaki rasa sanin tarihinmu ba nida mahifinki a gurin umminkiba, mu biyune kawai a gurin iyayenmu, kuma suma ba yan garin nan bane, gudun hijira sukayo, a yanzu haka bani da kowa, daga Allah seku ya'yana, ku nake kallo inji dadi, lokacin da nake kan ganiyar bukatar kulawar dangina, Allah ya karbesu gaba daya, amma hakan be hanani rayuwa ba, dukda har yanzu inata fafutuka ko Allah zesa insamu wani daga cikin danginmu,
Dan haka ki kwantar da hankalinki, kinada Allah kuma ni mahaifine a gurinki, duk rintsi duk wuya, babu abunda zesa in juya miki baya, ko Ummi na nan kobata nan, ina kaunarki yata ce ke jinin dan uwana, kicigaba da addu'a ki kwantar da hankalinki, kinji yarinyar kirki, zuciyata na shiga kunci idan naga hawayen marainiyar nan kuma amanar Aliyu, bana son zubar hawayenki, kiyi hakuri duk lokacin da kike kuka ji nake kaman naci amanane, "
Sosai nasihar Abba ta ratsa zuciyar Jalila, wanda yasa jikinta yin sanyi matuka ga kuma tausayinsa daya kamata
"insha Allah, Abba zan cigaba da addu'a in tana raye Allah yasa tana hannu nagari, inta rasu kuma Allah ya.......... Kawai seta fashe da kuka
Sosai tausayinta ya kama Abba, Halima dake gefe ma kuka take, Jawwad ma ji yayi kaman ya tayata
Abba yace" tana rayema Insha Allah, kuma zamu gano inda take "
Gyada masa kai tayi, Jawwad yace
"Abba Maama tazo dazu ta dubata"
"yayi kyau" shine kawai abunda Abba ya fada, ya tashi ya tafi, bayan tafiyar Abba, Jawwad ma barin dakin yayi, yaje office din doctor Salis, bayan sun gaisa, Jawwad yake tambayarsa yaushe ze sallami Jalila
"se ta dan kara hutawa, nan da ko kwana biyune, tana bukatar kulawa, saboda abunda ze iya biyo baya, amma nan da kwana biyu ze sallameta Insha Allah" daga haka sukayi sallama ya fito, Jawwad koda ya fito bekoma gurin Jalila ba ya tafi gida, seda akayi sallar isha'i sannan ya dauki Nana ya kaita Asibiti, daya kaita ma a gate ya tsaya ta sauka ya juya, Nana tayi murna ganin Jikin Jalila da sauki, hira Nana take tayi mata amma tayi shiru, zuciyarta duk babu dadi, dakewa kawai takeyi,
"Nana ina yaya Jawwad"?
"Ai yana ajiyeni ya juya, inaga ko wani gurin zashi" Jalila ta dan jinjina kai,

Jalal kwance a dakinsa ya kurawa ceiling ido, dagani yayi zurfi sosai cikin tunani, dan lumshe ido yayi, tareda yin Ajiyar zuciya, kirjinsa yamasa nauyi matuka, ya mike zaune ya dafe kansa da hannunsa biyu, sallama tayi a palournsa, yai shiru be amsa ba, ta karaso da tray a hannunta ta nemi guri ta zauna a kusa da shi, hannunta biyu ta saka ta cire masa tagumin
"Yaya Jalal meyake damunka tagumi fa babu kyau" dan kurawa Ilham ido yayi ya dauke kansa
"Yaya kayimin magana mana, naganka wani iri"
"Me kikazo yimin nan?"
"Fruit na kawo maka, kuma naga kwana biyu baka zama a gida, kwana uku banganka ba, duk na damu, ko cikin gida baka lekamu"
"Inkingama ki tashi kibani guri"
"Haba yaya Jalal, in damu da kai har inzo inda kake amma ka koreni, please yaya Jalal kabani dama mana a rayuwa, wallahi I love you Yayana, please marry me, in ba kaiba rayuwata tana cikin hatsari ina bukatar kulawarka, bazan iya auren wani ba kaiba"
"Idan kika bari na kuma yi miki maganar ki barmun dakina, sena miki abunda baki taba zatoba, sha3 mahaukaciya kawai" daga haka ya tashi yabar palourn ya shige bedroom dinsa,
Mutuwar zaune tayi, gaba daya notin kanta ya kwance tarasa mezatayi, ita namiji yake wulakantawa haka, dole tanemi mafita, Jalal yafara kaita bango matuka, tana cikin nazarinne wayar Jalal daya bari a hannun kujera tafara ringing, amma setaga lambace ba suna, hannu ta kai ta daga wayar tasaka a kunnenta, da dagawarta taji muryar mace tafara magana
"Haba my Jalal, kwana na uku ban ganka ba, ban saka a idona ba duk na damu, gashi baka daga wayata ina ka shigane, I want surprise you"
Ran Ilham ne ya baci, dan haka cikin masifa tace "Ke dalla Malama dakata mahaukaciya, dabbar inace ke, to Wallahi bari kiji in gaya miki, ko ke kika kaso maita duniya bakisa ki auri Jalal ba, Jalal nawane ni kadai, inbiki kiyayeni ba wallahi se kinyi danasanin zuwanki duniya, gara tun wuri kisan inda dare yai miki, Jalal bashi da wata mata in ba niba, munafukar banza data wofi, maci amana"
Hannah tace
"Ke saurara Me kike da suna, karki kuskura kice zaki zageni, bani da lokacin ki, haduwarmu ta farko kin gayamin magana son ranki, na kyaleki, bani da lokacinki, kuma idan ina raye Wallahi karya kike kema ki auri Jalal muzuba nidake, dan halak ka fasa, sokuwa kawai"
Jin hargowar Ilham ne yasa JALAL fitowa daga bedroom dinsa, yana zuwa ya tarar da Ilham rike da wayarsa tanata bala'i da surutai, karasawa inda take yayi, yasa hannu ya karbe wayarsa, ya juya ya nufi dakinsa, mikewa Ilham tayi tabi bayan Jalal tana masifa, a kunnensa ya kara wayar
"Ya akayi?"
"haba Jalal, meyasa kanwarka mahaukaciya ce, toka gayamata idan a wancan lokacin mun hadu ta zageni na kyaleta ta kiyayeni(a zatonta Jalila ce Ilham) , kasan halina zan mata rashin mutunci, kuma ka gaggauta gaya mata, nida ita shege kafasa"
"meyasa ke baki gaya mata ba"?
"Hakama zaka ce? Shikenan Jalal, ina ta wahala akanka, amma wata tana cimin mutunci ko, shikenan zatasan wata zaga wallahi, kasani duk me shirin kawomin matsala tsakanina da kai, sena gwada masa ni a mata ta dabance"
"Look Hannah bana son shirme kaina kemin ciwo, kuje kuyi tayi, tunda daga ke har ita baku da hankali, banzaye kawai"
Hannah kuma Ilham ta faada a hankali ba Jalila ba, wace kuma hannah, inma rainamin hankali suke, zasuga tsiya, yana gama wayar ya ajiyeta, wannan jarababbun sun kara hargitsa masa lissafi ransa a matukar bace yake, ya balle rigarsa ya aje kan gado ya juyo, yaga still Ilham tana tsaye, tana huci
"Meye haka ina cire kaya kinzo kin sani gaba, malama ki wuce ki bani guri, bana son shirme ds hauka"
"Wallahi Yaya Jalal, bazaka tabbatar da nayi hauka ba se ranar dana fara yimaka haukan, ni kake cewa mahaukaciya ko?.......
Tinkarota yayi gadan2 ta juya da gudu ta fice, dan data bari ya karaso ta san sauran, amma shi a gurinsa yayine dan ya tsorata ta, saboda tun ranar da Jalila tace masa ragon namiji shike dukan mata, be kara dukan Ilham ba, sedai yayi mata tsawa, shiyasa tasamu damar kara yi masa shishshigi, tana juyawa ta tafi, ya dawo ya zauna yai shiru, sun kara dagula masa lissafi, ga maganganun Jalila sun tsaya masa a rai, daga baya yaga bashi da mafita, ya tashi ya dakko mutuniyar tasa, yaiwa kansa caji ya kwanta anan, yafara bacci.
Jalila ta fuskanci Jawwad fushi yake, a lokacin itama taga rashin dacewar abunda tayi amma ba yadda zatayi, itama bata san tayiba, tana cikin dimuwane, shikuma yasata gaba da jaraba, tana wannan tunanin bacci yai awon gaba da ita

Yana kwance akan cinyarta, tana shafa sumarsa, tafara magana cikin sigar rarrashi, da daddadar muryarta me cike da iyayi da shagwaba
"AbdulJalal dina, kadena shan giya kaji, banason abunda kakeyi, bana son ganinka a irin wannan yanayin raina bayamin dadi, sonake kazama mutumin kirki kaman kowa, mutane sudena kyamarka,"
Murmushi yayi,
"To Babyna, nima bana son abunda nakeyi, zuciyata bataso bansan meyasa nakasa denawa ba, amma ki dinga yimin addu'a zan dena, amma nima kidena yimin wulakanci a gaban mutane banaso"
"Kullum ina yimaka, addu a, idan naga kana rashin kyautawa, gaba daya rainane yake baci, shiyasa nakema ka haka, amma nima na dena, amma promise me kaima zaka dena"
Murmushi ya kumayi "Allah yayi miki albarka My queen u mean a lot to me, Insha Allah ze wuce kaman banyiba, yayinda mutane ke guduna da kyamar halayena, lokacin kuke kaunata ke da yayanki, can't forget your sacrifice "same to me, u mean a lot to me, ABDUL JALAL, fuskarta ta sunkuyo zata sumbaci goshinsa, "
"Jalal ka tashi rana tayi haske fa, nasan ko salla bakayiba, se wani Murmushi kake a cikin bacci, wai me kake ganine a baccin"?
Se yanzu Jalal ya gane mafarki yakeyi, Kallon Jawwad, Jalal yayi

Please Login or Register in order to submit comment