Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

a gidan raino aka daukoshi ba dan Sunna bane, Sharri iri iri Niima ta kullawa Ahleef karshe tace shi yasa ma Bata aureshi ba,Hafcy tabe baki tayi tare da cewa Amma kin tafka asara irin wannan namiji haka to ni ko daga sama ya fado karewar rashin asali nasan Allah ne ya Halicce shi inasonsa,ko dan kudinsa da kyansa ai a so wannan gwarzon gwaraza, kawai ki tallafa min, nima idan kina neman wani abu zan ba abinda bazan miki ba, Niima kuma tasan Hafcy ta fita iya shege a kasar nan shi yasa sai ta yarda domin akwai wani mummunan kudirinta Wanda idan da Hafcy zai tafi dai dai,Ita kuma Hafcy ta sanarwa Mubaraq cewa ya zama ready Niima yanzu kawarta ce damarsa tazo shima,Murna kawai yakeyi ta fadi gasassa.

Zahra kuma bincikenta sai ya nuna mata Shukura yar uwar Ahleef ce da yafi so Sabo da haka idan tana tare da Shukura to zatayi Nasarar samun Ahleef cikin sauki,dama Service Zata fara sai kawai ta nemi a Bata teaching a makarantar su Shukura ta zama Malamarsu kuma tayi nasara an Bata yanzu kawai dole fa sai ta zama kawar Shukura ta gaske.

Islam kuma ganin Shukura kamar taki hadata da Ahleef sai ta koma barin Latifa domin hanata sakewa sannan Latifa ta hada ta da Ahleef.
Maman Su Hafcy akwai son kudi so takeyi Lallai Ahleef ya auri daya cikin yaranta sannan Mubaraq ya auri Niima yanzu itama jira kawai take Momee ta dawo daga tafiya ta koma kawarta sosai ta kwantar da kai yanda Zata ji dadin harka da ita,Shi kuwa Baban su Hafcy tsakani da Allah yake so Ahleef ya auri yarsa daya Sabo da burin yayansa ya cika shi duk abinda matarsa da yaransa ke so to dai dai ne kawai.

Oga Ahleef kuma Yanzu gani yake babu wacce ta Isa ya so ta a duniya,kuma Farhan yake so ya auri Shukura Sabo da yasan zai riketa da Amana,Shukura kuma so take Ahleef ya auri Islam tunda Islam kawarta ce Bata San cewar tuni Islam ta koma wajen Latifa ba.









Asm[7/22, 1:13 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO








11-15






Official






By
AsmaBaffa









Yau Sunday yau Ahleef yace zasu zo da Farhan,Shukura cikin Zumudin ganin Ahleef ta damu Umma sai sunyi girkin da yafi wanne dadi,Umma ma biye mata tayi Sabo da Ahleef abin a kyautata masa ne,Girki suka Shirya kala biyu da kayan sha,Shukura ta kara gyaran part din Yasha turaren wuta ko ina kamshi ke tashi na daban,tana yin sallar laasar ta shiga wanka ta tsiri shafe shafen da bata yi ma,cikin mayukanta Masu kamshi Wanda duk cikin kayan Ahleef ne da ya siya mata,tana gama shafawa ta bude kayan da gaba daya Ahleef ya siya mata su,ta zabi wata atamfa Green and black Riga da skert ta sa yar Bra dinta,dinkin das a jikinta ta cika skert din fam kamar a sace ta,Bata iya kwalliya ba sai ta shafa powder da jambaki Red kawai tasa kwallinta,tayi masifar kyau tana bulla kamshi abinta ta fito palo ta zauna tare da daukan littafi tana dubawa irin ba dan kowa tayi kwalliyarta ba wai dama haka take.

Umma ta kalleta kawai tayi murmushi tare da cewa Mashaallah duk Wannan kwalliyar ta Yayan ce ? Murmushi Shukura tayi tare da cewa Umma ai ni badan su nayi ba,Umma Bata ce komai ba tace to yan matanci ne ya motsa ashe ta furta tare da cewa bari na watsa ruwa ta shiga dakinta.
Umma na shiga Su Ahleef suka shugo bakinsu dauke da Sallama,Shukura ta amsa tare da cewa Oyoyo Yaya fuskarta dauke da fara'a,Farhan ma ya shigo yana karewa Shukura kallo ba kyafta ido yanda ta gaji da haduwa abin ba acewa komai,Ahleef kuwa yayi mamakin dama haka take da girma ko ina a cike amma sai yayi kamar bai ganta ba, ita kuma so take taga yana kallonta a nan Zata San lallai tayi kyau idan har Ahleef yana nacewa kallonta,amma ina Sam bai nuna ba ko kallonta baya yi,Farhan ne ya koma kamar yaga Tv, ta gaishesu tare da sanar musu Umma Zata fito yanzu ta shiga wanka,Kitchen ta mike ta shiga,Farhan yabi bayanta da kallo Ahleef yace mene haka kuma ? Sai kace maye a gaban yarinya dan Allah ni bana son haka so ya dinga masifa ba ji ba gani karshe yace a haka kake so na aura maka ita ni bana son ka jawo mana raini kaja mutuncinka aikin banza yau ka fara ganin mace? Farhan yace amma anyi dan iska wannan masifar fa ni da Babyna dan na kalleta sai nayi laifi ? Da ganin yanda kake masifa ma kishi kake ji,Ahleef yace sharrin da zaka min kenan ? Farhan yace nifa malam dalla rufe min baki wlh bazan taba son wannan na aureta ba kazo kana fakewa dani Kaje da abarka sai abu yayi nisa kazo kana Gaba dani kuje ku karata, Baka sonta fa kace,kamar Shukura zaka ce baka sonta a hasale ya furta,bafa nufina bana sonta ba No bada aure ba tafi karfina sai dai kai,Tsaki Ahleef yaja ni bana bukata wlh kaf mata babu wacce zan iya aura.

Murmushi Farhan yayi tare da cewa to Allah kyauta,idan so kake ka aurar da ita to ga Muhseen kasan bazai wuce tayinka ba,Har Ahleef zaiyi magana sai ga Umma ta fito suka gaisa tare da hira,Shima Farhan yasha mamaki Me kama da abokinsa,Baba ya dawo daga Masallaci ya zauna shima suka sha hira,Shukura kuma ta cika musu Gaba da kayan abinci,sannan ta koma gefen Farhan ta zauna kusa da shi,Babane ya mike ya shiga Bedroom Umma ta bi bayansa,Farhan kwakwalwarsa ta tsaya da aiki Sabo da kamar Baba da Ahleef haka Umma ma, Ahleef ne yace kawo min schl Bag dinki na gani,Wai dan karta zauna kusa da Farhan,taje ta kawo sai ya nuna mata gefensa tare da cewa Zauna mu duba books din,Farhan kuwa kallonsu yayi kawai yayi murmushi ya fara cin abinda aka kawo musu,Books dinta ya dinga tambayar abubuwa a ciki yaji duk ta iya, yaji dadi kuma ya jinjina mata, wani Assignment na English ta dakko masa tare da cewa Yah na kasa wannan wlh tun jiya,Sai da ya karba ya gani ba zato taji Saukar biro a kanta ya rankwala mata shi,wajen ta dafe tare da sakin yar kara Muryar Shagwaba tayi Yah da zafi fa,Koya mata yayi har ta iya sannan Shima yaci abinda zai iya sannan Umma ta fito suka mata sallama suka tafi tare da mikawa Shukura wata katuwar leda wai inji Farhan saurayinta kuma Ahleef ne ya siya komai,Farhan yace ka gama gulmarka.

yau Monday yaune kuma Zahra ta fara teaching dinta a makarantar su Shukura, Yau second period ta shiga ajin su Shukura,kamar abin kirki ta gama teaching dinta sai ta bada Test tare da cewa wace Shukura ? Shukura ta daga hannu,Zahra ta girgiza da ganin me kyau haka kamar ba mutum ba,tace a gidan su Ahleef kike ? Shukura tace ae,Murmushi Zahra tayi tare da cewa duk wanda ya gama ya bawa Shukura ta hada ta kawo mata ta fita abinta. Har Office Shukura ta samu Zahra da Test,Zahra ta kalleta da Fara'a tace Shukura kina da kyau,tnx Shukura tace itama tana murmushi,Idan Baza ki damu ba zanso mu zama frnds duk da na girmeki amma ni wlh kawai kina birgeni,Shukura ganin yar gayu irin Zahra kuma me kudi gashi tace tana sonta da kawa gaskiya mutuniyar kirki ce Zahra bata da wulakanci ai dole ma ta zama kawarta,a fili Shukura tace nima ina Sonki ba damuwa,Shukura ta dade suna Hira da Zahra har suka fara sabawa sannan ta koma class,Zahra kuma Shukura na fita ta tabe baki tare da cewa ina samun shiga wajen yayanki zan raba ku kema bazan so me kyau irinki ta rabeshi ba.

Allah sarki Shukura Bata da kawa murna takeyi Allah ya Bata kawa malama guda, Babba kuma yar gayu,Su Latifa Yanzu suna Jin tsoron Shukura tunda ta tsillewa Latifa kai suka rage yi mata abu, kullum yanzu idan anyi Break suna tare da Zahra suna hira Amma Bata yarda ta fada mata sirrinta, Zahra kuwa buri takeyi taga ranar da Ahleef zaizo wajen Shukura kuma taki nunawa tasan wani Ahleef ma,Hafcy kuwa kusan kullum tana gidan su Niima ko Zata ga Ahleef yazo amma Shuru ba labarinsa,Niima tace ta shirya suje har Office dinsa ranar Manday akwai wasu takardu da Momee tace a bawa Ahleef zai mata Posting dinsu zuwa Jordan,sun samu hanyar ganinsa ba tare da ajinsu ya zube ba,Hafcy Murna wajenta kamar zatayi Hauka ranar Monday wankan da bata taba yi ba shi tayi har gidan makeup taje kamar Amarya haka ta fito.

Shukura Sun samu Free period dab da za a tashe su,Zahra ta nemota Office suna hira har aka tashesu Zahra tace tazo ta kaita gida a motarta,Fitowarsu kenan sai ga Ahleef a wata mota sabuwa gal ta gaske fara kal kayansa ma shadda fara komai White ba karamin kyau yayi ba,Zahra ce ta fara Ankara dashi Ji take kamar ta dira tsalle sabo da murna,Shukura sai gani tayi kawai Zahra ta canja tafiya tana lankwashewa,Ahleef bai gane Zahra ba ko kadan Shukura ya dannawa Horn,laaaaa Yayana yazo yau shi zai daukeni Kawata kalleshi can,Wani kishi ne ya tokarewa Zahra a boye ta makawa Shukura Harara a fili kuma ta washe baki suka tafi har motar Ahleef,ta Window ta leka side dinsa tare da cewa ranka ya dade yaya fit ta zagaya da murna ta shige gaban mota sannan ta dagawa Zahra hannu bye Aunty kawas,Zahra tayi dariyar dole ta daga mata hannu tare da cewa Ina yini tana leka Motar kallon Up and down yayi mata da kyar ya iya cewa lfy, sai da tayi magana ma ya gane ta,Wani kallo da ya mata ya dauke kai sai da ta raina kanta jikinta yayi sanyi,yaja mota suka bar schl din direct Office dinsa ya nufa,Yaya Ina zamuje kuma ? Umma kar taga na dade wlh fada ne Da ita sosai idan anyi laifi Shukura ta furta kamar zatayi kuka,kallonta yayi kadan tare da cewa ashe kina da tsoro?ina kika samo kawa? Shukura tace malamar mu ce Aunty Zahra tana so na nima haka baka ga yanda takeso na ba, Hmm ki dai bi a hankali da kawaye musamman irinsu Ahleef ya rasa furta.

Shuru ta masa tana tsoron Umma ita dai, muryarsa ta tsinta yace naje gidan dazu Ai na fada mata sarkin tsoro,Murmushi tayi tare da cewa tsakanin ni da kai wa yafi tsoro kai,Dariya yayi lokacin ya tuno da Aljanun gidansa,katafaren Building dinsa yayi parking ma'aikata sai gaisuwa suke kwasa,Har Shukura ake gaisarwa Oga yazo da kanwarsa,Office dinsa ya bude suna shiga tare da ita sai kallon tsaruwa da haduwa Take sai kamshi tare da sanyi ke tashi, saman wata 2seater lafiyayya ta fada kai tare da kwanciya,Abinci yayi Order a kawo a katafaren wani eatery na manyan Masu kudi,Shukura gajiyar schl tasa Bata surutu Yah Ina toilet ya nuna mata can ciki ta dauki schl bag dinta yace toilet din zaki tafi da wata schl bag kuma,Ajiyewa tayi sannan ta bude ta cikin Hijab ta dauki pad dinta zaraf ta boye ta tafi toilet abinta,Dariya kawai Ahleef yayi kadan dama ya ganeta tun a mota Sabo da shi yana iya gane mata shi yasa yace kar ta shiga da bag Sabo da ganin kwakwaf.

tana shiga taga toilet neat sai ta sa key ta kulle tayi wankanta tas tare da maida kayan jikinta ta shirya Kanta,kafin ta fito kuma su Niima sukayi knocking Sabo da an santa shi yasa aka kyaleta ta wuce Direct wurin Boss,come in Ahleef ya furta cikin daddadar Muryarsa,Hafcy ce a gaba tana baza kamshi sai Niima,yana ganin Hafcy ya kara tsuke fuska,zama sukayi babu wata gaisuwa sai Sannu da aiki suka ce masa bai ko amsa ba yana ta rubuce rubucensa tare da daga waya ko kallonsu bai sake yi ba,Hafcy kuwa sai gyara kirji akeyi ana rangwada,Niima tace takardun Momee na kawo,ba tare da ya dago ba yace ajiye a table,tana daukowa Shukura ta bude toilet tare da fitowa daga ciki sanye da uniform dinta amma kowa ya kalleta yasan tayi wanka yanzu,Kallonsu tayi kawai duk Sun tare sit din zaman sai kawai ta zagaya kusa da Ahleef tana wata shagwaba kamar yarinyar Yah a ina zan zauna ni ? Da murmushi ya kalleta yasa hannu ya jawota ta bayansa sannan ya mike yace zauna a kujerata ki karasa aikin,takardun ya Nuna mata anan zakiyi ta Marking da biro tace na gane,Kallon Niima yayi tare da cewa bata documents din tasan me Zata yi.Shukura kuma kamar gaske sai jujjuyawa take a kujerar tana musu wani kallo tana aikinta da ya nuna mata, kamar hoto haka suka zama, shi kuma ya shige toilet zaiyi Alwala.

Gyaran Murya Shukura tayi tare da cewa keep it On the table cant u hear a simple English,ta kalli Hafcy tare da yin muryar Wanda ba bahaushe ba ko turanshi (turanci) babu? Nace a ajiye min a Table,Niima ranta ya gama jagulewa Ahleef ya yarfa ta a gaban frnd dinta Hafcy ma haka ranta ya konu ashe Niima aikin banza ce a wajensa amma ta Bata lokacinta,Shukura ta karo karfin AC taci Gaba da abinda takeyi ba tare da ta kallesu ba tace pls zaku iya tafiya i have done with u guys,Ahleef yana jinta yana ta dariya a toilet,Chewgum ta bare ta jefa a bakinta sannan ta jawo wardrope tare da ebo kudi 20k ta mikawa Niima take ths i know shi kuka zo nema Ko? Niima ce ta fara Mikewa a fusace Zata mari Shukura Ahleef ya fito tare da buga mata tsawa are u crazy kizo har Office dinta zaki Mareta Who the Hell are u, How Dear u,Niima tace Amma kasan kudin ubanmu ne ba naka ba,da bazar mu kake rawa,da ba a San asalin ka bane sai kace zaka bude mana ido,kai har kana da bakin magana marar asali tsintacce kayiwa iyayenmu asiri ka mallakesu harda kawo mana karuwarka gida ashe anan kuke sheke ayarku, bari su Momee su dawo wlh sai ka bar mana dukiyar mu,Hafcy tace ke Niima iya bakinki wannan yafi karfinki kuma ni a haka nake sonsa shine dalilin kulaki da nayi amma ni nafi karfin kawance dake wlh zaki zageshi shi yace a bashi dukiyar,Shukura ce tace Enough ku bar mana Office, Baraki ma ai iyawa ne wasu basu da darajar da zaiyi dasu, kun bada mata wlh get lost, Hafcy ce ta nuna Shukura da yatsa zamu hadu dake zaki maimaita kalamanki, ae din anji badai ya Sonki kuma bazai so ki ba Shegen kai kamar kwallon goruba, Kwafa Niima tayi Suka fita kuwa ba tare da sunce komai ba, Kujera Ahleef ya fada zuciyarsa tana masa radadi,Shukura ta fahimci hakan sai ta dawo kusa dashi,tana Bashi hakuri duk da Bata san labarinsa ba amma sai taji tausayinsa.

Yaya ta furta a hankali,kallonta yayi yana murmushin karfin hali yace dauko abinci gashi can kici,kafada ta makale ni tare zamu ci, lafiyayyun abincin ta bude tace dole suci tare haka suka ci abincin tare tana masa surutu har ya nemi damuwarsa ya rasa karshe ya karasa aikinsa ya sauketa a gida Bayan ya siya mata abubuwan ci iri iri, tana fita tace Yaya Bye banda tunani pls, I will try my Best inshaallah ya furta yana murmushi.

Hafcy tunawa da tayi da bukatar dan uwanta Mubaraq shi yasa taki yarda suyi fada Da Niima,kwanaki na ja Shukura yanzu ta kara gogewa tare da wayewa kuma hankali takeyi sosai Sabo da kulawar da su Umma ke kokarin yi akanta,ta iya kwalliya tare da girke girke abin ba a cewa komai, Ahleef kullum sai dai ya fake da Farhan yace Shine saurayinta.
Yau Momee da Abba zasu dawo Nigeria,gaba daya Sun tafi Airport Ahleef shine gaba kowa murna yakeyi,Alhmdllh Sun sauka lfy ana ta murna da ganin juna,Tattarawa sukayi aka tafi gida gaba daya,Washe gari Ahleef da kansa ya gabatar Umma, Baba da Shukura wajen Momee da Abba,Momee da fara'a cikin mutuntuwa ta amshesu Abba ma haka dama Momee tasan Shukura sabo da haka hira ta dinga janta dashi,abu daya ne ke damun Momee yanda taga tsantsar kamar Ahleef dasu Umma.

Sati biyu da dawowar su Alhji Baban su Hafcy ya samu Abba a Office kan maganar Auren Ahleef da Hafcy ko Zahra, Abba ya tuno rashin tarbiyar yaran sai yace ba damuwa indai Ahleef yana so shi bashi da Matsala amma bazai masa dole ba, zai tambayeshi yaji.
Yau Maman su Hafcy taje gida wajen Momee suna ta hira kamar abin arziki sai kuma ta fara kawo mata gulmace gulmacen Ahleef tana so taji ya suke da Momee Amma Momee Bata yarda tace komai ba duk kuwa da yawan zuwan da takeyi gidan.

Mubaraq yau shine ya kawo Hafcy wajen Niima,Sai da Hafcy ta gama abinda zatayi sannan ta fito zasu tafi Niima ta rakata har mota,Mubaraq a hankali yake dan janta da Hira Hafcy tana dariyar da ita kadai tasan nufinta tare da cewa Sister ga yayana da alama yana ciki a kular min dashi, Mubaraq dan gayu ne sosai ya iya wanka,Niima taji yana birgeta sosai Bata wani ja masa aji ba ta amshi soyayyar sa hannu biyu sukayi exchange na phone Number,suna Hira Shukura ta fito daga part dinsu Zata shiga wajen Momee tasha wankanta,Mubaraq ya ganta Gaba daya ya rude a ransa yana so ace ta zama matarsa,Niima na gabansa amma hankalinsa na kan Shukura Niima sai ta ji haushi kamar ita ba mace bace tana gabansa yana kallon wata can,da kyar ta danne fushinta har suka tafi,yau kuma Ahleef ya dawo gidan da zama Sabo da Abba ya matsa akan lallaai ya dawo gida..
Kullum yanzu Niina sai ta kai karar Ahleef da Shukura wajen Momee,ta kulla sharri tace Sun mata wani abu, tun Momee bata yarda har ta fara yarda ganin yanda Ahleef yake share Niima,shi ya jawo yanzu ta fara ja baya da Ahleef, Shukura kuwa kiri kiri yanzu Momee take nuna mata rashin Kauna,sabo da Me mutane suna cin arzikinsu suna zaune lfy Sabo da samun waje sai su dinga wulakanta Masu gida ita Baza ta yarda da wannan ba.

Tunda Ahleef ya dawo Shukura ke gyara masa daki,Haka abinci ma sai jefi jefi yake cin na Momee Umma ke dafawa dashi ta bawa Shukura ta kawo watarana har su Momee suna Ci Sabo da Umma karshe ce wajen iya girki,Shi yasa take kara Jin haushi kuma ta gaji to abun bazai yi kyau ba.
Tun safe yau Shukura tana farkawa tayi mika tare da cewa yau mugunta nake ji duk Wanda tsautsayi ya fada masa shi zanyi wa ba ruwana.







AsmaBaffa
[7/22, 1:13 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO






16-20








Official







By
AsmaBaffa








MAMAN FAHAD and HADIZA MUKTAR ga page naku ina Godiya.


MARCYCOOL jinjina me tarin yawa.








Shukura tuni tayi Sallar asuba wanka tayi ta fara kalailatar Shiryawa kamar Zata je party,Umma tana palo tana kallo Ahleef ya shigo da sallama dauke a bakinsa,a'a sannu da zuwa karaso mana ka zauna,murmushi dauke a fuskarsa sai da ya duka har kasa cike da girmamawa ya gaishe da ita kana ya zauna suna hira jefi jefi,jira yake yaga ta ina Shukura Zata fito,sai gata ta fito sanye da Arabian Gown fitted black me duwatsu tayi kyau sosai musamman da tayi acuci tare da tayi Rolling mayafin,ido biyu sukayi da Ahleef ta saki murmushi ya kashe mata ido daya, tana so itama ta kashe nata bata iya ba sai fari tayi farrr da ido, murmushi yayi tare da dauke kansa daga gareta, Umma ce ta kawo masa abin ci da sha,wata yar aiki ta bangaren Momee ta shigo tare da Cewa Saudatu kizo inji Momee,Haka kawai sai Ahleef yaji haushi da yar aikin ta kira ta da Saudatu kai tsaye Ko ba komai ai dattijuwa ce da an dan sakaya sunan.
Tsam Umma ta yafa mayafinta ta wuce part din Momee.

Shukura tace zanbi Umma wajen Momee gaskiya ban yarda da Kiran nan ba is better ayi komai a idona Sabo da Momee ta canja mana fuska kwana biyu Niima ta gama zugata, Hmm kina da gaskiya muje to,tare suka jera kamar ango da Amarya, a palo suka iske Niima,Momee,latifa tare da Abba,har Baba yana wajen.
Ahleef tare da Shukura suma waje suka nema tare da zama,Momee Bata Jin haushin kowa sai Shukura Akan yanda Niima take Bata labarin cewar kwadayi ne ya kawo Shukura gidansu,Momee kuma ta tuna tun a asibiti tasan Shukura da kwadayin abinci maybe har kudi ma shi yasa tasan yanda zatayi dole ta dawo gidansu da zama ta hanyar ahleef, Gashi Ahleef yana wulakanta yayanta akan Shukura wacce a duniya suka tsince ta,sannan ta fuskanci Ahleef yanzu yafi damuwa da Saudatu fiye da ita Wanda kwanan nan suka shigo gidansu gwara ayita ta kare kawai.

Abba ne ya fara magana Alhmdllh gaba daya gashi mun hadu,Ahleef kaine babba ta dalilinka kuma abubuwa suke faruwa a gidan nan marasa dadi Wanda bamu gane gaskiyar faruwan hakan ba, ke Niima gamu baki daya a nan fada mana abinda ke faruwa,Momee cikin fushi tace Abban Latifa ba haka za ayi ba gwara farko kowa yasan waye Ahleef a wajenmu har Wanda yake fifitawa akanmu su Sani ni bazan lamunci haka ba, nan fa Momee ta refe baki ta fara kwararo labari tun farkon batan sa har zuwa dalilin da yasa suka je gidan raino suka dauko shi har jarin da Abba ya bashi ya zama me kudi zuwa yanzu komai saida ta fada, Cikin fushi Abba yace Haba Momeen Yara ina hankalinki yake,mene na bayyana jarin da na bashi,wannan gori kika yi masa kuma shi ma danki ne kuma sai da kowa ya sheda kinfi sonsa da yaranki na cikinki,kuma jari dana bashi ki Sani kyauta ne halak malak ba bashi lauyoyi Sun sheda Sabo da irin wannan ranar dama nayi haka,nasan ku mata tunaninku kadan ne abinda zuciyarku ta baku sai ku aikata, ke ai abin kunya ne aji wannan a bakinki,halayen Niima waye bai sansu ba amma kin kasa fahimta.

Ahleef yace kuyi hakuri Abba da Momee Idan na Bata muku kuma bari na fada muku dalilin da yasa bana saurarar Niima da kuma haduwata da Shukura,Haka ya basu labarin Irin wulakanci da cin mutuncin da Niima ke masa da Wanda tayiwa Shukura iri iri, sannan ya basu labarin Haduwarsa da Shukura har zuwa yau, sai ya bada labarin haduwarsu da su Umma har Baba Bayan ya gama ya kara bawa Momee hakuri.

Saudatu tare da Baba Kuka suka fara yi,Abba yace kuyi hakuri wannan ba abin kuka Bane,Momee tace sayi Shuru tunda sunzo zasu dasa mana rashin zaman lafiya a gida musamman wannan kodaddiyar ta furta tana nuna Shukura, Shukura tayi murmushi Sabo da ita Bata wani fushi sai tace kodaddiya kamar Tsohuwar atamfa fa Momee...Babane ya Katse ta da cewar wannan Ahleef dai danmu ne na jini wlh,na dade ina bincike a kansa sabo da yanda mutane ke cewa kamarmu daya,ban fadawa kowa ba Sabo da kar ace karya nakeyi, bari nayi lokaci yayi na furta yau
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On JIN DADI SABO
avatar
mahamane-noura

11 months ago

Reply

Asalama alaikum, dan Allah yane ake sauke littafin akan waya

Please Login or Register in order to submit comment