Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baka haka ake fada a kauyen,Baffa harda tuntube wajen sauri yana zuwa kuwa yace a bashi biredin Mata aka bashi ya biya kudin duk tunanin Baffa wani Bread ne Me dadi a ciki,ya kawo mata gashi Shukurere ta aci da yawa kinji tace to Baffa,yace wannan katon Bread ai sai da lemo Shukura, Inna tace kayi sauri ka siyo mata Maltina tunda tafi Sonta,nan ma jikin Baffa na rawa ya siyo mata Maltina me sanyi yace tasha da biredinta.
Sosai suke ji da Shukura gata sai wanda ta gani,kullum haka take a rayuwarta cikin gata da jin dadi sabo da haka kuma mutanen kauyen sai suka tsaneta sosai kowa burinsa ya zaiga Shukura ta tozarta ta wulakanta amma ba dama Allah ya riga ya bata masu hassada sai kallo.

Ahleef tare da Farhan suna garden sai shirye shiryen biki sukeyi sosai ganin saura 2mnths bikin sai matsowa yakeyi, Ahleef ya Kalli Farhan cike da iyayinsa da ya saba yace Man ina ganin Matsala a wajen Niima abin yana damuna,na tambayeta ko da matsala tace a'a,murmushi Farhan yayi shima da Iyayi yace kai dai tsoro Kake ji so yayi maka yawa,hmm baza ka gane ba sam ba caring yanzu wani shareni takeyi na rasa me nayi Mata gaisuwa ma yanzu sai taga dama,bata ma so mu hadu,kasan fa mata haka sukewa ango idan za ayi musu aure haushin angon suke ji,pls ka daina damuwa tunda har itace ta Amince idan bata sonka baza ta yarda ba, Kai wace ta isa taganka tace bata so ko baturiya yace ai tayi karya,Ahleef yayi murmushi yace haka Momee ma tace dana fada mata amma wlh kaji na rantse da matsala a wajen yarinyar nan sai dai kawai Addua.

suna zaune saiko ga Niima tazo tana tafka uban Selfie ita da kawayenta su biyu ta Kalli su Farhan shekeke tare da galla musu harara,sai suka matsa gefe kawayenta suna yaushe zamuje Government House dinne? Tace munyi waya execelency na yace Next wk yana nemana,sannan jibi Senator dina zaizo gida wajena ban San ya zanyi da wannan angon nawa ba, dariya yan matan sukayi tare da cewa ai ba a daura ba bare ya Hanaki kula wasu shegen angon naki sai shegen iyayi ga rainin hankali dan kawai yana da kyau da kudi, daya a ciki tace Niima Allah yayi Miki baiwa da miji kamar Ahleef amma kina so ki cuci bawan Allah,Niima ta turo baki tare da cewa ke kin san dai nima kyakyawa ce ga farin jini idan ma yatafi dubu zasu zo min mutimin da ba'a san asalinsa ba har wani kyansa za a gani,idan kuma kudi ne ga Manyan kusoshin Gomnati nan duk ina dasu kuma nima ina da kudin haka ubana Ma.
Su kansu kawayenta sunga haukar Niima tare da butulci.
Niima haka kullum burinta ta dinga gulmar Ahleef Tana aibatashi tana zaginsa cikin mutane har zancen ya Fara dawowa kunnen Momee amma tayi shuru taga gudun ruwan Niima yarta.
Shiko Ango kullum yabon Amaryarsa yakeyi sonta na karuwa a ransa kullum yana manne wajen Abba da Momee suna shawarar biki.
Kwanaki na ja biki saura 1wks ango ba zama Amarya kullum cikin bakin ciki take bata shirya aure ba za a tauye mata rayuwa,yanzu idan ta yarda da auren shike nan Alhazawanta sai mijinta kawai.

Shukura kwance take cikin dare Tana ta kwasar baccinta taji kamar hayaniya a hankali ta bude idonta ta kunna torchlight kenan taji ashar da zage zage,ai sai ta kashe torch ta leka ta window nan take ta hangame baki tare da fara Hawaye taga Baffanta da Innarta an dauresu ga wasu jibga jibgan arna sunkai su 15 dauke da bindigu,Baffa taga sun kafe da mari,da sauri ta bude kofa ta fito da gudu Tana kuka tana rokonsu su bar mata Baffanta itama mari suka zuba mata nan take ta sume sharaf a kasa Inna ta fasa Ihu sabo da rashin Imani wani yasa wuka yayi mata yankan rago,Baffa ya rafka salati tare da dafe zuciyarsa nan ya fadi matacce zuciyarsa ta buga.

Arnan dariya suka dinga Yi ta mugaye sannan suka kada shanu da dabbobin Baffa kaf suka tafi dasu,a garin basu kadai ba har sauran fulani da dama wasu an kashe su an tafi da dabbobinsu, Tunda Shukura ta suma bata farfado ba sai da gari yayi haske lokacin Mutane sun cika gidan taf,da kuka hade da salati ta farka Tana Ihun Baffa...Inna.... Wayyo...nan tayi arba da gawarwakin Inna da Baffa sai ta haukace gaba daya tana birgima da ihu tana na Shiga uku ina zan sa kaina na huta,gatana ya kare Inna... Baffa sambatu takeyi Kala kala sai da kowa ya tausaya mata harda masu kuka gaba daya ta haukace bata san inda kanta yake ba, har akayiwa Inna da Baffa sutura tare da kaisu makwancinsu ana ta zaman makoki,Shukura kuwa suman ta yafi sau goma tana farfadowa kamar zata sheka lahira,sai maza ne suka riketa aka shiga yi mata addua tare da Kiran Nasuru me Chemist yayi mata allurar bacci ya sa mata Drip nan bacci ya kwasheta,bata farka ba sai dare Ta dora daga inda ta tsaya ana mata nasiha amma abanza cewa take ni bazan Hakura ba, in Allah ya yarda kuma sai iyayenku sun mutu Allah yasa babanku da babarku su mutu suma,bazan ba kowa hakuri ba sabo da nima bazan hakura ba.

wata tsohuwa tukuf ta shigo gaisuwa gidan Shukura wacce ta gama rama sallolinta Tana kuka ta Kalli tsohuwar tace ai gwara da wannan ce ta mutu tunda ta tsufa bata da amfani mene amfaninki,wata ma cikin dangin Baffa na sallama tace ga wannan Ma shekara nawa kullum cuta takeyi ai da ita ta mutu,matar tace Allah sarki yar nan kowa na can ne lokaci nane baiyi ba.
Wasu yan mata su biyu sunzo gaisuwa Zaraf shukura tace ga Baban wannan Ma shanyashi ake a Rana sai an kwantar sai an tayar mene amfaninsa Ai ni wlh iyayena sunfi na kowa Amfani, ana mutuwa amma mutuwar su Baffa ta musamman ce..ba shiri Nasuru me Chemist yazo ya kara dannawa Shukura allurar bacci da Drip, bata farka ba sai washe gari,ba laifi ta dan dawo hankalinta amma sai taji masu zaman makoki dangin Baffa suna lissafa mutanen da arnan suka kashe a garin,nan Sai ko akaji Shukura ta kece da dariya tace Alhmdllh uban kowa ya mutu wlh tunda ubana ya mutu uwar kowa ta mutu tunda na rasa tawa,yanzu har Dantani Baban Aishalle ya mutu?kai Alhmdllh amma Allah na gode maka,yawwa gwara Kowa iyayensa su mutu duk mu zama daya,ai wlh bazan Kara jimamin mutuwa ba, Ni mutum ya sake yace min ubansa ko uwarsa ta rasu sai dai aga ina nishadi wlh.
Wani ne ya rafka sallama tare da cewa bayin Allah Ashe arnan Jos har rigar yan jalo suka je sunyi kashe kashe da yawa yafi na wannan kauyen namu,ayyiriri nanaye akaji Shukura tace yawwa su dandana suma suji Me naji.
Kwana uku kullum sai anyiwa Shukura Allurar bacci bata ci bata sha sai an mata Jan Ido har akayi Bakwai.

Kullum Shukura bata daina kuka tana Tuna iyayenta zata fashe da kuka,haka har aka kwashe 40days Dan abinda Baffa da Inna suka mallaka aka siyar gaba daya har gidan da Shukura ke ciki,dangin Baffa dama tunda akayi bakwai suka tafi da Shukura gidansu,haka aka raba gado yanda Allah yace aka bawa shukura kudi dubu Dari biyar kasancewar Kauye ne filaye da gonaki basa tsada,Shukura ba kunya ta karbe kudinta a ledar Viva tana kukan su Baffa.
nan ta samu Kudin nan ta Fara dagargazar dadi,ba irin shawarar da yan Uwa basu ba shukura ba yanda zatayi da kudinta ta Samu ci gaba amma tace a'a Sabo Da tun farko bata da mafadi sai abinda taga dama take yi ba a sata ba a hanata, gashi bata daukan ko tsinke a gidan dama sun San halinta ganin maraicin da take ciki suke daga mata kafa,ga shegen iyayi wajenta, kudinta ta sasu gaba tayi kyauta taci dadi,yauma da Yamma liss taga wani katon zabuwa Tana yawo tace nawa wannan Zanbon Goggo ko na uban waye zan siya a siyar min shi,Goggo ta tabe baki tare da cewa nawa ne kuma ni dubu biyu zan siyar,nan ta zaro 2k ta biya tasa yara suka Kama mata shi aka yanka Sabo da Kiwa ma wata budurwa ta bawa tace gyara naman nan ki soya min Zan baki Dari biyar,jiki na Rawa budurwa ta Karbe tayi yanda take so, ta karba tare da figawa mutanen gidan nasu sabo da bata da rowa,zama Tayi da Maltinarta a gefe tana ci tana kora Maltina sai kuma ta fashe da kuka ta tuno Baffanta da Inna yanda watarana ma abincin a baki suke bata ana lallabata taci,haka takeyi kullum barnar kudi ga Dunkuna tana faman yi iri Iri har shopping taje cikin garin Jos ta siyo cosmetics da turaruka masu kyau,abinda kawai take birge mutane dashi addini ne da ita sosai bata wasa da addini.
A kwana a tashi Dangin Baffa suka takura su ta ishesu tayi girma da yawa dole sai tayi aure ko su bata duk wanda suka ga dama,ita kuma tace ba wanda ya isa yayi mata dole,su kuma Suka ce baza ta ja musu abin kunya ba sai dai ta bar musu gida baza su iya da halinta ba, Kawunta ta samu tace Kawu kasan bana Zance bani da saurayi kuma ina so na cikawa Baffa burinsa na zuwa abuja nayi kallo kallo.

Takaici ya kama Kawu kawai ya jawo sanda ya fara zane Shukura Yana Karuwanci zaki shiga tsinanniya,sai da ya farfasa mata jiki abinda iyayenta ko zagi basu taba yi Mata ba, haka suka bi suka tsaneta a gidan da sauran dangi bata da ikon magana sai duka kuma yanzu aiki ake sata sosai a gidan kamar jaka lallai taga maraici, ko wanke wanke idan tayi To ranar da zazzabi zata kwana bata saba ba,Kwatsam sai Kawu sukayi shawara a junansu suka zabowa Shukura miji wani Me kiwon Shanu Halilu,Halilu Dan shaye shaye ga neman mata kaf garin an sanshi,Shukura bata da labari sai da bikinta ya rage saura 1wk taji ana kiranta da Amarya tana tambaya taji a garin ana ta mata dariya anga karshen iyayi da jin dadi.

Kukan Maraici Tayi tana tuna so da gatan da iyayenta ke nuna mata amma ga yanda ta koma dare daya,ragowar kudinta ta duba saura Dubu Saba'in kacal Duk ta kashesu a siyi banza siyi Wofi Trolley dinta ta jawo ta shirya kayanta a ciki kaf sauran da bata so ta barsu,Handbag dinta ta zuba kayan kwalliyarta ciki tare da kudinta ta shirya tsab,sai da ta Bari an shiga masallaci sallar asuba ta sadada cikin duhu ta bar Garin bata tsaya ko ina ba sai garin Jos ta zarce Tasha inda zata shiga motar Abuja,a Tashar tayi sallar asuba da Asuba,ta dauko Toothpaste dinta da Brush tayi da ruwa pure water,a tashar ta siyi kosai da biredi tare da shayi hadin kauri taci ta koshi sannan ta wanke fuskarta da sabulunta harda shafa powder da jan baki sama Sama,ji tayi Driver yana cewa shigo yan mata zamu wuce,da sauri ta shiga ta zauna mota ta tashi sai Abuja.

Bikin Ahleef saura kwana uku ango ba zama Sun gama gayyatar abokai,ba abinda ba a gama ba na shiri,sun narkar da kudi,Abba yana sama a dakinsa yaji ance yazo ga manyan danginsa sunzo Maza biyu da mata biyu,ya fito Sun gaisa kenan sai ga yayan Momee da kaninta tare da yayarta,abin ya basu mamaki,bayan an gaisa anci ansha,suka ce abinda yake tafe damu ba komai bane sai akan auren Niima,Gaskiya bamuji dadi ba Sam da ilminku da komai zakuyi mata auren dole,jiya taje mana Tana kuka ita bata so auren dole za ayi mata,Abba ne ya dakatar dasu yace ku bari Niima tazo shima Ahleef yazo, Nan Momee ta Kirasu a waya,5mnt dukkansu suka zo, Momee tace gata nan gashi kuji daga bakinsu,Ahleef suka kalla kai kaine da kanka kake son Niima tsakani da Allah?da Sauri Ahleef yace ae,Niima kefa?kinje kin Kai mana kukanki yanzu maimaita a gaban kowa,ai kuwa ba tsoro Niima tace uhmm... Ahmm..Ina sonsa amma bada aure ba,ni ban shirya aure ba, kuma ni bana...Mari taji Abba ya kifa mata shi,Tana kuka tace wlh ni bana son aurensa,Abba Hawaye suka gangaro masa,Momee kam dama zancen ya dade da zuwa kunnenta,a hankali tace Baban Suhail kyaleta,ai dai kin tabbatar bakya sonsa ko? Niima tace ae,Abba yace ni zaki wulakanta sai ki fada mana sabo da me? Tana kuka tace bashi da asali wa ya sani ko shege ne,Momee Kuka kawai take shekawa, Abba yana Jin haka yace Ahleef kayi tawakali kayi hakuri,Allah zai baka wacce ta fita,ke kuma baza muyi miki baki ba amma ki sani sai kinyi nadama,yan Uwansa ya kalla yace na gode kuje kawai,jiki ba kwari suka tafi,itama Niima ranta Fari kal ta koma dakinta tana bugawa samari da yanmata frnds nata waya Tana Murna suma haka.
shiko Ahleef ya mike kenan ya yanke jiki ya fadi kasa sumamme,

Momee da Abba da gudu sukayi kansa ana kiran Driver duk abinda za ayi masa anyi bai farfado ba da taimakon yan aiki aka kwasheshi zuwa Hospital,Private Hospital suka tafi amma duk likitoci sunyi iya yinsu sun kasa dawo dashi yaki farfadowa,Kwana daya bai farfado ba,Momee tare da Farhan ne ke kula dashi sai Abba dake sintiri,Kwana biyu bai farfado ba har dare yayi Momee ta damke hannunsa tana zubar da hawaye Tana masa addua cikin ikon Allah sai ya fara motsi,Momee ta rungumeshi tana Murna tare da godiya ga Allah, kamar ba Namiji ba taga yana Kuka sosai,Ahleef Momee ta kira sunansa,kuka kawai yakeyi Har Farhan ya shigo ya tausawa abokinsa duk dauriyarsa gashi yana kuka akan Mace,Momee ta Tallafo fuskarsa kayi Hakuri Son wlh mu kamar iyayenka ne,karka dauki maganar Niima kasa a ranka kaji na rantse munfi kaunarka fiye da yaran da muka haifa,kuma a yanzu Niima ko tace tana sonka bazan Bari ka aureta ba tunda Tayi Ma haka Allah sai ya baka wacce tafita komai da komai, Har abada Niima tayiwa kanta,kayi tawakali jarabtarkace,Farhan ya dora da cewa Maybe ma ba alkhairi bace a tare da kai shi yasa,kuma Allah zai ma sakayya dama can ba matarka bace,Momee da Farhan tare da Abba haka suka sa Ahleef a gaba da Nasiha iri Iri,Suhail da Salman Ma haka yar auta Latifa ma ba a barta a baya ba, ita kuwa Niima yau kwana 4 kenan suna asibiti amma ko dubiya bata leka ba,Momee da Abba duk sun daina kulata har su Salman.

ganin ba Wanda ke kulata a gidan tace zataje dubiya Momee tace karta soma ganin kafarta,Ahleef Sabo da Nasiha da kula da yake Samu yaji sauki ya dan warware amma ya daina magana da kowa sai ta zama dole baifi a Rana yayi manana sau uku ba, kullim fuska a cinkushe take shi kadai yasan irin kunci da baking cikin da yake ciki.






AsmaBaffa
[7/22, 1:09 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO







4








Official







By
AsmaBaffa










Masu sharhi ina godiya wannan page naku Ne.











Tunda aka sallamosu yayi tozali da Niima Sonta ya dawo sabo ciwonsa ya tashi suka kara komawa asibiti,kwana daya aka sallamosu Duk ya kara fari ya rame,Niima sai harkarta takeyi ba ruwanta,Momee killum Nasiha da fada take masa yayi hakuri,Farhan shi ya dinga sanarwa cewa an dage bikin Ahleef sai nan gaba idan an sa Rana za a sanar mutane sunyi mamaki Wanda suka san labarin sun tsinewa Amarya ba adadi.
Ahleef ya zama kamar kurma fuska ba Rahma,Sai kallon hoton Niima kullum aikinsa Kenan,Momee tayi fadan har ta gaji,shima Abba haka,Har Saudiya Momee ta shirya musu ita da Abba tare da Ahleef suka tafi,sai da suka kwashe 3wks suka dawo Alhmdllh Ahleef ya samu afwa har kiba da kyau yayi sosai,sai rashin magana da fara'a ya dawo abin Tsoro,kwarjininsa ya Karu ya maida Hankalinsa wajen aikinsa Kawai,duk ranar da zaiga Niima to sai hankalinsa ya tashi ganin haka yasa Momee tace maza Niima ta shirya ta koma Kaduna wajen yayarta ta zauna kafin wani lokaci,Niima murna tayi zata ji dadin Shanawa da samarinta a can, Zata yi yawonta inda taga dama.
Ahleef ya riga da ya tabbatar bazai taba aure a duniya ba tunda ya rasa wacce yafi so Niima to bashi ba kara kula mata, kullum dare sai ya zubar da hawaye ya kasa hakura da Niima,har aka kwashe 3mnth a haka yake ba canji yana shan wahala.

Shukura ko da ta sauka a Abuja da yamma ta rasa ina zatayi kawai tayi zamanta a tasha a nan taci abinci har dare,sai kallonta akeyi gata da shegen kyau,a tashar nan ta kwana dake Abuja ne ba ruwan wani da wani ba wanda ya kulata,gidan wanka na mata ta shiga ta biya kudi Tayi wankanta Tayi brush tare da shiryawa tsaf ta fito ko vaseline bata shafa ba kaya kawai ta canja taja akwatinta Tayi gaba,tana fitowa gefen Titi taga wasu arnayen motoci guda biyar sun wuce da matsiyacin gudu sai ko daya daga cikin motocin suka kade wani dattijo nan take ya mutu,dattijon da dansa namiji abin tausayi yaron zai Kai 25yrs sai ihun kuka yake yayin da wannan motoci suka gangare gefen titi,mutanen suka fito,Ahleef yana motor dake tsakiya Duk escort dinsa ne,fuska ba rahma ya fito cikin takunsa kamar Sarki, Shukura dake gefe bata da burin da ya wuce taga baban wani ko babar wasu ta mutu sabo da nata Sun rasu,wajen gawar taja akwatinta bakinta har kunne sabo da Murna,yaron yana ta zunduma ihu Yoruba ne ko Hausa baya ji,Shukura ta kutsa ta cikin mutane har gaban yaron ta dinga tuntsira dariya,kowa yana kallonta gashi ko ba Dan Allah ba sai ka Kalli Shukura sabo da kyanta,Ahleef ya kalleta sau daya kirjinsa ya buga,Shukura tace amma Allah yayi muku albarka masu motoci gwara iyayen kowa su mutu a duniya nima nawa Sun mutu.

Kallonta mutane suka fara yi masu Jin Hausa suna Mamaki wasu na dariya, matashin Yoruba ya daura hannu aka yana rusa kuka yana Help me ooooo My Papa,Help me Jesus ,Oh..God Papa....yana ta sambatu Ahleef ya karasa da niyyar taba jikin Wanda suka bige da mota caraf yaji an rike masa Damtse,a fusace ya juyo da mamakinsa sai yaga Shukura ce duk da bai santa ba ya zuba mata Harara,kwarjininsa yasa tayi saurin sadda kanta kasa tana cewa Allah baza ka kaishi asibiti ba sai ya mutu shima tunda ubana ya mutu,Hannunsa ya fisge da karfi har sai da ta kusa faduwa kasa Bata hakura ba ta jawo rigarsa nan ma ya fisgeta yana bawa Guards dinsa Umarni a daukeshi zuwa Hospital,sanan aka kira Police suka shige mota suka bar Shukura da sauran mutane.
Itama akwatinta ta ja tayi gaba abinta ko ina zata je Oho. Ahleef kuwa ya cika da mamakin Irin rashin Imani na Shukura,Sunje Hospital anyi komai tare da Police,wanda ya mutu an kaishi gida tare da Tallafin kudade da kayan abinci,wanda kuma ya kade mutimin ba musulmi bane bare ace azumi ya kamashi.Abba da Momee ma duk sunje Sun kai musu tallafi,Yaron matashin ma Salman ya bashi aiki a Company nasa.

Shukura kuwa Hotels ta dinga zagawa sai da ta samu Me kwana daya dubu goma sha tara a Maitama,cikin gwarancin turancinta ta samu ta kama daki da kyar ma suka barta wai tayi yarinya,cikin dubu sabain dinta,taci abinci na dubu biyar, kamar wacce ta dawo daga kasar waje sai dai ana kallonta daga karkara tazo,kwana uku ta kwashe kudinta suka kare saura 3k Amma sai tace masu Hotel su kara mata 3days zata biya Idan ta shiga bank babu cash a hannunta kullum Bread take fita taci da ruwa ta dawo Hotel,ana haka 3days ta cika, masu Hotel gani suke kudi ne Da Shukura,da safe tayi wanka ta shirya tsaf cikin doguwar Riga silver color,tayi kyau kamar balarabiya kuma yar birni,akwatin kayanta ta ajiye a Room dinta ko Hand back Bata dauka ba sai kudinta dubu biyu ta fito tare da sanarwa ma'aikatan cewar ta tafi bank zata dawo yanzu kayanta har Handbag suna ciki yanzu zata dawo ta biya su.

Ganin har hakorin makka ne da ita guda daya Sun San ma Hajiya ce kuma sunga yanda take wasa da kudi,Shukura tana yin nesa da Hotel din tace ruwa ta sha ta shiga taxi tace ya kaita wani restaurant mutanen wajen dama Sun saba da Shakura tana zuwa tayi musu wasa da kudi farkon zuwanta Abuja da kudinta, suna ganinta suka fara washe baki, Ta zauna duk abinda takeso sai da tasa suka cika mata table da abinci,ta ware ciki taci ta koshi karshe ta duba ta zaro 2k sai ta mayar taja tsaki ta dauko Voter card dinta ta matseta a hannu yanda za a hango kamar Atm card ne sai tace bari naje nan Opposite Bank na ciro kudi just 2k ya rage a hannuna,mutanen duk arna ne musulmi yana musu kwarjini kuma suna ganin masu gaskiya ne most of them kawai suka ce taje ko gobe ma ta kawo,aiko da gwarancinta na turanci tace OK thanks ta fita Bata tsaya komai ba ta mike layin tana tafiya,alhazawa da manyan masu kudi sai kallonta akeyi Sabo da kyau Irin na Shukura,duk motar data wuce sai ta kalleta,Tafiya takeyi tana tunani wai ina zataje ? Ina zata kwana,wata dalleliyar motace tayi slow a gaban Shakura,da sauri ta kalli na cikin motar wani jibgegen Alhaji ne kamar zai fashe sabo da kiba kansa kuma dan karami Horn ya danna mata tare da yafitota tazo,bata San mazan Abuja ba sai ta je tare da gaisheshi tun a nan yasan Bata waye ba kuma bakuwa ce ya samu banza.
yace yan mata shigo muyi magana mana,ba musu ta shiga mota,shiko farin ciki ya kamashi,yace Hajiya na ganki ne kuma naji ina sonki,gaki kin hadu gaskiya kina da kyau irinki nake mafarkin samu,murmushi tayi kawai,yace ina ne gidanku na kaiki can ? Tace nima bakuwa ce kwana nan babanmu yaci dan Majalisar tarayya muka dawo nan da zama amma ni yar kauyen Jos ce fulanin daji,Alhaji dadi ya rufeshi ya samu yar gidan me kudi nan take yace a wanne Hotel zamu hadu ? nan ta gane me Alhajin ke nufi da ita,kawai sai tace karfe 12 na dare ai zaifi Ko ? Yace ashe dai kin gane gaskiya kin hadu ta ko ina.a boye ta maka masa Harara suna hada ido ta saki murmushi,tace hmm Muje kasan layin nan zanje wani Mall zan siyo waya sabuwa,Ki bari mu hadu a Hotel Idan mun gama Jin dadinmu sai na siya miki wacce kike so me tsada,nan taga fa baza ta samu sisi ba sai yayi lalata da ita sai tace to bari na koma gida sai mun hadu ltr, ta fice a motar yana washe baki zaiji dadi yau,sun rabu ya tafi itama ta kara Gaba tafiya take a kafa gashi Bata san ko ina ba a garin kawai tafiya take.

Momee Dalilin abinda Niima tayiwa Ahleef yasa Hawan jini me karfi ya kamata ta fara cuta me tsanani tun tana boyewa har ta kasa motsi gashi lokacin su Salman Sun koma Uk sai Latifa kawai, Ahleef kuma yanzu tunda abin ya faru Sam baya zama sosai a gidan yafi zama a katafaren wani gidansa daban can wata Unguwar da turawa suka fi zama ciki,ba ruwan wani da wani,kamar malaikan mutuwa haka ya koma ba fara'a ba komai ko magana sai ta kama wannan abin ne ya damu

1 Comments On JIN DADI SABO
avatar
mahamane-noura

2 years ago

Reply

Asalama alaikum, dan Allah yane ake sauke littafin akan waya

Please Login or Register in order to submit comment