Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai lokacin hankalinta ya kwanta tana ajiyar zuciya zata maida kayanta ya kwacesu ya zubesu a kasa ya shigar da ita jikinsa sosai cikin blanket baci me dadi ya kwashesu amma duk sanda ya farka ko motsi yayi ko tayi sai ya tambayeta lfy? Me ya faru yana murza albarkatun kirjinta.ita ma bata san sanda take shagwaba ba iri iri, cikin tsakiyar dare yace zai kara Romancing dinta taki yarda wai zata samu cikin yan biyu,gaf da asuba da kyar ya shawo kanta ta yarda suka kara murje juna,saida ta gama Jin dadinta ta ajiye Masa kuka iri iri ya Kara mata ciki zata haifi Yan biyu.

Bayan sunyi Sallah tare da azkhar suka koma baccinsu me dadi, har 11am basu tashi ba,Momee tana so ya fito yayi break amma shuru, har sun gaji da jiransa,bayan kuma sun san yana riga kowa tashi a gidan,Latifa tace Momee lfy yake kuwa, Momee tace bari naje na tasoshi,Tabe baki Niima tayi tare da cewa iyayi ne kawai so yake yaje wajen uwarsa yaci,uwar kinibibi tana jiransa shi yasa yaki fitowa yanzu sai mun gama munafukai,Momee tace ya isa ma wlh babu wanda ya isa na sha wahalarsa yace zai min iko dashi.

Knocking kofar tayi tare da murda handle a kulle tajita karon farko kenan da ya sawa dakinsa key,Shukura ce ta farka gabanta na faduwa za a kamata a dakin miji ba tare da ankai Amarya ba.
Jallabiya ya zura tare da bude kofar kadan ya leko da kansa Alamar bashi da gaskiya,Tsaki Momee taja tare da cewa baka da gaskiya, anyway breakfast is ready,Ok kawai yace ta juya ta tafi, wanka yayi ya shirya cikin wasu kana nan kaya,masu uban kyau da tsada,Shukura ma da sauri tayi wanka sannan ta shirya cikin rigar shaddarsa me kyau,kuma tayi tsananim kyau ta yafa dan wani gyalenta na abaya data daura a kanta jiya,turarukansa ta fesa tare da kara gyara dakin neat,hannunta ya rike zasu fito tace wlh kunyar Momee nake ji bazan iya fita ba, Kina matar tawa mene abin kunya?zasu ce ni nake bibiyarka,to sai me kuma common lets go ya figi hannunta suka sauka kasa tare,Gaba daya Momee suka saki salati kamar sunga mutuwa da sauri Shukura ta kwace hannunta ta fece da gudu zuwa part dinsu,Baki Momee ta rike tana kallon Ahleef kamar wanda yayi sata kana ta daure fuska tace haka kuma ka koma lalacewar taka ta kai haka kwafa tayi tace zan yi maganin abin,sumarsa ya Sosa cikin kunyar Momee din yayi shuru ya zauna tare da fara cin abincin,dan kadan yaci ya mike yace Momee na fita,Hmm Office ko kuma wajen waccen tsohuwar karuwar zaka je?

Tunda Mommee ke masa abubuwa bai taba Jin zafin kamar na yau ba,matarsa ta sunna zata kira da karuwa,ko a fuska Momee tasan ransa ya baci,amma sai tace bace min da gani sallamamme wacce ta raineka ka mai dani ba komai ba,dama matsalar rike dan wani kenan watarana sai ya ganka yace uwar banza to ni dai Allah ya gani nayi iya abinda zan iya.
Ahleef baice mata komai ba ya fita abinsa fuskarsa har ja takeyi sabo da bacin Rai,bai tsaya ko ina ba sai part din Umma,Umma na kallonsa ta gane yana cikin damuwa,bayan sun gaisa tace kaifa lfy? Lfy kawai yace,Mikewa tayi ta shiga dakin Shukura a nutse tace mijinki Yana cikin damuwa yata kiyi yanda zai samu farin ciki,na koya Miki komai karki bari ya fita da bacin Rai,Kunya ta kama Shukura da kyar tace to Umma,fita tayi daga dakin yana zaune cikin tunani ya tsinci Muryar Umma tana cewa shiga ciki tana Nan,ba sai na ganta ba Umma Office zan tafi wai shi kunya,Umma ta ganeshi sai tace A'a bana son musu kaje ka sameta Mikewa yayi ya nufi dakin.

a hankali ya tura kofar ya shiga da sallama,bayan labile ta boye,ba zato yaji hannunta cikin nasa,jikinsa ne ya dauki wani shock yarrr... da kyar ya iya dannewa,gabansa ta dawo da sauri tare da kura masa Ido,lips dinsa ya tsuke irin kallon ya isheshi haka,Ya naganka kamar kana da damuwa,gira daya ya dage mata I'm ok me kika gani? Nothing kawai dan na tambayi best frnd dina laifi nayi?yau baza kaje Office? Ango fa nake kin manta sai ayi min dariya ai a samu abin fada,kema baza kije schl ba sai nan da 3wks yana furtawa ya haye lafiyayyen bed dinta ko safarsa bai cire ba kuma yau zafi akeyi, bed ne me kyau wanda yasha gyara haka bedroom dinma Umma ta gyara mata da safe sai kamshi ke tashi.

Ac ta kunna masa tare da Dan karo karfinta kadan, gefen kafafunsa ta zauna a hankali ta cire masa safar kafafunsa,har zata kwanta sai ta fasa tunawa tayi da Umma kunya bai dace ba sai ma yaga bata da kunya kawai sai ta fita tare da rufe kofar a hankali,dama lumshe idonsa yayi ba bacci yakeyi ba,murmushi ya saki me kayatarwa wani dadi ya lullubeshi sabo da yanda yaga tana lallabashi tana ji dashi abin har mamaki ta bashi yar mitsilar yarinya da iya kula da miji.
Umma na Palo taga Shukura ta fito a kunyace ta zauna kusa da ita, bata Rai Umma tayi tare da cewa ya kika dawo Nan me zakiyi ga mijinki can yana cikin wani hali?haka na koya Miki? tashi ki bani wuri tunda ba kya ji,da sauri Shukura ta mike tace to Umma yayi fa bacci,Lallai zamu bata dake tunda abinda zakiyi kenan kin sanni Shukura ki kiyayeni.

Da sauri tace am so sorry Umma ta koma da sauri dakin,Murmushi kawai Umma tayi tare da cewa yaran zamani da haka ake kwace muku miji ko sure fada neman matan banza wai ku Jan aji.

Shukura kuwa a hankali ta shiga dakin ta rasa me zatayi shi kuma ya fara bacci tunani ta farayi to me zatayi masa kuma,kallon fuskarsa tayi a fili tace yafi mace kyau mutumin Nan zankadi Allah me baiwa,still gani tayi yana zufa kamar ma mafarki yakeyi me wahala,yana cewa no...karki tafi...tana tsaye ya farka a tsorace ya hada zufa,kusa dashi ta karasa kana tace sannu mafarki kayi ko,kallonta yakeyi tare da Mikewa zaune da kyar, yace ae scary Dream nayi,Hmmm kawai tace wace kar ta tafi ?naji kana furtawa a mafarki, watace ya bata amsa, wani kishi taji Nan take bata San sanda tace kyakyawace? kallonta yayi da sauri Yana nazarinta sannan yayi Dan guntun Murmushi tare da cewa ae She is so Beautiful,Baki ta tabe tare da cewa hmmm tana da kyau,to ni fa? Yace kema me kyau ce mana Yana leka fuskarta Yana zuba Murmushi,ban yarda ba sai dai ka zabi daya,yace ai kece du ta mafarkin,ba wani Nan zaka ce nice ta mike da niyyar tafiya abinta.

Da sauri ya riko hannunta ya jawota saman Bed din kusa dashi ta fada kwanciya yayi itama ya jawota jikinsa ya manne kirjinta da nasa tare da zame dankwalin kanta ya shiga shafa gashinta me dadin kamshi a hankali,zuciyarta ce ta shiga bugawa fat fat da karfi,a hankali yace mene kike Jin tsoro just relax,da kyar tace ba tsoro nake ji ba,yace gashi Nan zuciyarki na bugawa,ni din? Oh tambaya kike? Yes a Ina kaga tana bugawa,na nuna Miki ne? Bata San nufinsa tace yeah.
Dan matsawa yayi ya raba tsakajinsu tare da daura hannunsa saman kirjinta ya lumshe Ido ya bude har sun koma red idonsa,da sauri ta zame jikinta gefe ni Dan Allah kar na haifi Yan uku jiya Yan biyu ne a cikina yau zaka Kara yawwa na tuna muje asibitin pls a duba idan nayi ciki a cireshi kar abin kunya ya samu a gidan Nan,gani yayi tsakani da Allah take maganar sai ta bashi dariya da mamaki,Lallabashi ta shiga yi sai anje asibiti jiya yayi mata ciki kuma Yan biyu,da kyar ya lallabata ita Amarya ce ta bari sai jibi zasu je.
Momee kuwa sai da ta turo Niima ta Kira mata Ahleef wai me yakeyi bazai tafi Office ba idan bazai je office ba to yazo tana nemansa.

Haka Yana son zama tare da Frnd dinsa ya tafi,Yana zuwa Momee ta fara masifa wanne naci da rashin kunya ne ya tare a gindin Amarya daga aure,to ka shirya jibi zan aikeka Qatar tunda gobe Abba zai tafi ya samu Kiran gaggawa daga British,kai jibi zaka Ka tafi,Shukura kuma Nan da kwana uku zan kaita kauyensu idan ka dawo sai Shirin tarewarta,Ahleef har ga Allah bai so hakan ba,amma idan kana zaune gidan wani kuma akace rikeka akeyi tofa sai hakuri domin dole kayi biyayyar da baka yi niyya ba,kuma dole kayi biyayyar dole baka da yanci sai abinda akace tunda ba gidan ubanka bane.

Dole ya amsa ba tare da ya nuna komai a fuska ba.
Momee ta Kafa ta tsare ta hanashi sakewa shi da Shukura baza ta bari Shukura tazo wajensa ba,idan kuma yaje minti biyar za ta dinga masa aike yazo zai mata kaza,Saudatu ta kasa gane kan abin,ta bawa Baba lbr yace su kara hakuri a gani tukun,ranar da Ahleef zai tafi sallama Momee bata bari yaje yiwa Saudatu da Baba bare Matarsa Shukura,Shukura taci kwalliya zasuyi sallama ta fito da sauri wurin motar amma Momee na ganin haka ta bawa Driver Umarni su tafi airport dake tana motar wai sai ta rakashi,Shukura da Ahleef sai hangen juna ta window Yana kallon hawayenta da kyar ya danne nasa ya daga mata hannu itama ta daga masa,da Kai ya nuna mata ta daina kuka zai dawo,Duk Wanda ke wajen sai yaji tausayin Shukura sabo da Momee ta gama takura ta sosai ba sakewa,ita kuma tafi su iya shege idan so take ta karya komai nasu Dan tafi kowa iya satar hanya,tanayin biyayya wa Momee sabo da Ahleef kuma gashi a gidansu take zaune,idan tayi wani Abu taga Ahleef bai son a Raina Momee da zuriyarsu bata manta sanda ya zuba mata Mari akan Momee shi yasa ta hakura.

Saudatu ce tayi ta faman kwantarwa da Shukura hankali,Momee na dawowa daga airport sai ta tasa Shukura a gaba ta bata Address din kauyensu da Yan uwan babanta dana babarta,washe gari da wuri Momee tace Shukura ta shirya kayanta kaf,ta shirya harda Saudatu da Baba tunaninsu za aje a sanarwa da danginta aurenta da Ahleef, Momee tace Umma ai ba daku zamu tafi ba,ku koma ni na isa wakilci ga Niima da Kawarta Hafcy zamuje,Ba Shukura ba har Saudatu da Baba sai da suka tabbatar ba alkhairi su Momee zasu Kulla ba,har Baba zaiyi magana Shukura tace karkace komai Baba,idan Ahleef ya dawo ga Address Dina Nan idan Yana so na na tabbata zai nemeni komai dadewa,Umma na gode da rikeni da kukayi idan da rabo zamu sake haduwa Umma karku damu,ki fadawa Ahleef kar ya nemi wayata Momee ta kwaceta tun jiya,Nan sukayi sallama Ana hawaye ta fita tare da shiga mota.

Niima taja tsaki tace dole ayi kuka za a koma kauye cin miyar daddawa,Shukura itama ta tunzura tace daddawa kuma kitchin din me dirty dankwali ma akwai Ashe bamu kadai ke ci ba,da ba asan asalin ungulu ba da sai ace daga masar take,Hafcy tayi cagal rufemana Baki ko wlh ki gane kurenki,tsaki Shukura taja tace banza a banza man Kare ke har mutum ce dama,Hafcy haushi ya isheta tace dadin abin dai farin an Kara da mai,Shukura tace ke kuma ya shafa Baki kamar na tsuntsuwa chilikowa.
Momee ce ta buga musu tsawa tace ku kyaleta taji da haushin komawa kauye ga kuma rabuwa da Dana da za ayi dole uwar naki wlh. Shukura Bata Ce komai ba har suka je kauyensu ita ta nunawa Driver ma gidan kawunsu,Niima tace Lallai dole azo karuwanci Abuja,Hafcy tace a kauyen ma wannan kauye ne wai tab,Yara sunyi cincirun do Ana kallon mota da kuma Yan birni,da kyar dattijai da Yan uwan suka gane cewar Shukura ce Maji dadi yar Mirgayi,Nan aka dinga layin kallonta Maza da mata Shukura Maji dadi ta dawo daga karuwanci dama kauye tuni sunce karuwanci ta tafi birni,Yan uwan Baffa suka ce Shukura baza ta shigar musu gida ba yarinya taki aure ta gudu karuwanci wlh baza su laminta ba.
Murmushi Momee tayi tasa aka fito da kayan Shukura tas tace to Bayin Allah kuyi Hakuri ku karbeta gata Nan cikin shege tayi kwanan Nan aka gano a asibiti sati uku Nan gaba zaku ga ya girma,tazo ta likawa Dana Dan ya aureta ni kuma bazan yarda ba,sabo da kar na koreta Allah ya kamani yasa na dawo da ita garinsu kune Yan uwanta kune dolenta ni ba abinda ya hadamu da ita.

Tuni Hawaye ya jikewa Shukura Mayafinta ga tozarci gaban Yan uwan da alummar gari,gashi tasan Ahleef rannan yayi mata cikin Yan biyu yanzu idan ya girma zasu ce cikin shege ne tayi,tana Kuka tace Momee kiji tsoron Allah kazafi kika min,kuma wlh cikin Ahleef ne ya min rannan yasan da maganar ku tambayeshi sai da nace ya kaini asibiti a duba yace zamuje Nan da 2days kuma yayi tafiya,ta juya gaban danginta tace wlh wlh da aurena Kawu ku yarda Dani,Kawu sabo da takaicin Shukura ta bata musu zuriya ya samu ya masgeta da katuwar Sanda Nan take ta sume a wajen,Momee,Niima da Hafcy kansu ya kulle tam Jin Shukura tace Ahleef yayi mata ciki,kuma aurensu ko sati ba ayi ba,kenan dama Ahleef ciki yayiwa Shukura shi yasa suka hada dabara wajen daurin aure aka daura aurensu Dan kar asirinsu ya tonu,Nan Fa suka shiga mota suna ta Muhawara Ana saka da warwara,Momee tana ta tunani dama so take dole tasa ya auri Niima ko Hafcy tunda Ahleef lalataccene to sai dai ko Hafcy ta aureshi idan tana so amma baza ta aurawa yarta Niima Lalatacce ba,baza ta aurawa yarta mazinaci ba,Ashe abinda suka aikatawa kenan shi yasa Ahleef yake haba haba da Shukura,Maimakon Momee ta rufawa Ahleef asiri suna dawowa gida ta fesawa Saudatu da Baba,Saudatu su sun San gaskiya shirmen Shukura ne kawai ko ajikinsu,daga Nan Momee ta dinga fadawa Kawayenta da wasu cikin Yan uwan,Niima kuwa dama kadan take jira kowa daya shafeta ya sani,Hafcy ta fadawa mamansu dasu Zahra,Mama tace ba komai Hafcy ta dage ta aura haka zasu samu kudi ba matsala,Zahra tace ta fasa aurensa wlh duk da tasan itama ba budurwa ba ce Amma baza ta auri namiji me neman mata ba,Hafcy dai kafarta daya na ciki daya na waje.
Ahleef Yana can bai San me akeyi ba Yana ta gwada wayar Shukura Shuru Umma da Baba kuma sai dai suce masa Shukura tana Nan cikin koshin lfy kar ya damu,abin ya fara damunsa.











AsmaBaffa
[7/22, 1:13 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO







36-40







Official






By
AsmaBaffa









Sabo da Jin dadinku masu Sharhi na baku wannan....kuna birgeni tnx all.















Shukura kwance kasa ta sume,alummar kauye Ana kallonta dangin Innarta dana Baffa babu Wanda ya tausaya mata ko ya tsaya ya saurareta kowannensu ji suke kamar su kashe kowa ya huta da wannan abin kunya,wani Dan matashi ne cikin dangin Rabe ya kwara mata ruwa ta farfado tana zare Ido tana kallonsu tare da Kara tsanar danginta na rashin Zumuncinsu tare da nuna mata kiyayya sabo da iyayenta basa Raye,Nan Mutuwar iyayenta ta dawo mata sabuwa ta fara zubar da Hawaye masu dumi, su kuma manya da Yara mata da maza suna Kanta a tsaye suna mamakin ganin yanda Shukura ta goge ta Kara kyau da Haske,cikinsu wata tsohuwa tace ta tababbata juna biyu gareta gashi duk sai kyalli take.

Wata yar budurwa ta fashe da kuka tace shike Nan ta jawo Mana Babu Wanda zai auremu a garin Nan tayi Mana tambarin da bazai gogu ba,yanzu Ja'e nasan fasa aure na zaiyi yace muma bamu da tarbiya, kawu Babban banza yace share hawayenki ko da suratul Yusufa sai kin samu me sonki kuma yau zan fara rubuta Miki kina shanyewa maganin farin jini haka suka dinga cakaki akan Shukura har suka fara tafiya gidajensu Ana Allah wadai da Shukura,a hankali ta mike ta nufi gidan Kawu da niyyar shiga,Kawu yace Ahir dinki aradu kina tako kasar gidana zan karya Miki kafafu,tasan Halinsa ba Imani,sai ta nufi gidan wani Shima ya biyota da sanda,haka ta dinga zagawa kowa na korarta ta rasa Ina zata shiga,da kyar ta roki Megari ta zauna a gidansa zuwa wani lokaci Amma Megari guda yaki yarda yace saidai ta kwana a yar bukkarsa ta kofar gida ya bata Amma ba a gidansaba, haka ta hakura ta shiga dakin kofar gida kowa Yana kallonta. Matar Megari Talliya tace yo Kai Malam ai kawai ta dawo cikin gida da zama kaga na samu yar aiki,yo me zaisa mu Bata wajen kwana da abinci kyauta a banza tazo ta dinga min aikin gida Ana Bata wajen kwana da abinci

Megari yace Talliya kin kawo Shawara ga dakin cikin gida a Bata ta dawo,haka Liman yasa ta shugo da kayanta akwatuna, har Biyu,Talliya tace oh amma Shukura a barikin masu kudi kike harkalla dasu? Irin wannan Kaya haka ga kyau kin Kara,Shukura takaicin ya rufeta tace da aurena fa ni ba bariki nayi ba,mijina Yana Nan,Talliya tabe Baki tayi tare da cewa ke kika sani ni Dalla tashi ki Kai min Nika,ki dawo kuma aikace aikace na jiranki ba hutu kikazo yi ba abinci da wajen kwana fa zamu Baki duk lalacewarki danginki kaf sun gujeki Amma mu muka dauko wa kanmu,da can sanda iyayenki suna da Rai wanne irin iyayi ne bakiyi a garin Nan ba da tabara ke ga yar gata,to yanzu Ina gatan?

Shuru Shukura tayi tasan yanda Yan kauyen suke mata hassada tun asali sabo da ta fisu, karshe dai cike da bakin ciki ta fito Kai Nika,sai nuna ta akeyi a kauyen tayi cikin shege ta dawo daga bariki,ko bako ya shigo kauyen sai ya ji labarin, bayan Shukura ta kawo Nika ita tayi abincin gidan me gari ga uban yawa kamar na gidan biki ba karamar azaba Tasha ba,bayan ta gama sai da tayi wasu ayyukan a Daren sannan ta samu Talliya ta barta tayi wanka tare da sallah karshe aka Bata tuwon taci Wanda Babu dadi sabo da yawansa kuma ba kayan Hadi ne a cikin miyar ba,Amma duk da haka ranar da kyar aka samu miyar dumamen safe ta ragu kadan sabo da dadin girkin Shukura kowa yaji dadinshi.

Ko da Shukura ta kwanta in Banda tunanin mijinta Ahleef Babu abinda takeyi Nan ta tuno irin Jin dadin da sukayi ranar da suka kwana tare,Nan take ta lumshe Ido tare da dakko rigarsa jallabiya cikin kayanta tasa abarta ta kwanta tana tunaninsa Nan bakin cikinta ya yaye Baki daya duk da frnd dinta ne tana muradin kasancewa dashi har karshen rayuwarta.

Washe gari tun da asuba Talliya ta tasota a masife ta damawa Yan gidan Koko ga Yara kana na har da almajirai a gidan birjik, megari bayan yasha miyar jiya yaji kamar ya tsinke yatsansa sabo da dadi yau ma ya kurbi Koko a fili ya firta shegiya bariki badan ba abune me kyau ba ai da ka tura matarka ko Dan ta koyi girki,Harara Talliya ta watsa Masa tare da cewa to me kake nufi? Murmushi yayi tare da cewa ja'irar yarinya da ita Amma ta iya girki haka duk shagwabarta Ashe ta iya girki gaskiya ki koya,tsaki Talliya tayi ta bar dakin fuuuu a fusace.

Da Rana Shukura duk ta gama aikin da aka sata,sai rike kugu take ta gaji sosai tana rokon Allah kar cikin Ahleef ya zube, Amma Talliya ba Imani tace daura girkin Rana kiyi Mana dafadukan shinkafa da manja, Shukura ta gingima tukunya ga itace hayaki ga Rana haka ta kwaciba girkin,tana sani tayishi yanda bazai dadi bama, Ana zubawa me gari da almajirai da sauran yaran gida haba kowa Santi yake zubawa har ita kanta Talliyan,Shukura ta kasa cin abincin sabo da ba dadi Amma su a haka yafi na Talliya sau dubu,Megari sai washe Baki yakeyi,mamaki ya kama Shukura tana cikin haka ta fada tunanin Ahleef dinta Wanda ya fiye mata komai ita kadai sai gashi tun tana Murmushi ta koma sheka dariya, dukkan yaran gidan da Me gari kansa kowa kallonta ya koma yi Baki bude, wani cikin yaran yace Wlh wannan me kyau ce, Me gari yace ke Lfy?shuru Shukura tayi Nisa har kanta take girgizawa tana dariya,Talliya Baki bude tace ke Dan Uwarki ba dake ake ba iyeeee ta zabga mata duka a baya, da sauri ta dafe wajen tana sosawa cike da Shagwabarta tace wayyo Mijina,Talliya tayi zaton da Megari take ta kirashi da mijinta, tace karuwa uban waye Mijinkin?
Nan take Shukura ta saki sabon Murmushi kamar ka saceta sabo da kyau sannan ta kalli Talliya tare da turo mata Yan lips dinta jajaye tace Mijina fa can kin San sunansa ma abin so ne,Ahleef,kyakyawa,duk kyauna ya fini,Babu abinda nafi so a jikinsa irin idonsa,da Murmushinsa wlh Anty Talliya idan kika ganshi sai kin kusa Suma,ga kudi,ga ilmi,ga addini,ga hankali,ga nutsuwa,ga iya soyayya ni kadai naji me naji dole na haukace ko....Dalla rufe Mana baki Lallai Babban bariki kika buga,Shukura tace wlh mijine na sunna, Me gari yace Ke karki Raina mana hankali fa yanzu Kya bar Mana gida.kinje Karuwanci ae kinyi ki Mana shuru kawai ki ajiye iskancinki gefe can.

Shukura yau tayi sati guda a gidan Me gari Amma kullum aiki take kamar jaka a gidan, komai an sakar mata,duk tayi duhu ta rame kadan,ga tunanin Mijinta da ya addabeta,yanzu duk kayanta akwati Biyu manya Bata sawa sai Jallabiyar Ahleef da kuma wata rigar shaddarsa light blue,duk inda zata a garin a haka take fita sai dai ba kazanta zaka ganta fes kullum sabo da Megari Yana Bata kudin sabulun Dan ma watarana idan son dadi ya motsa sai ta siyi kifi soyayye da kudin taci abinci dasu.

Shukura ta koma wajen dangin mahaifinta Dana Innarta ko zasu karbe ta Amma sunki yarda taje yafi a irga Amma sunkiya,sai wahala take Sha gidan Megari da girki, gashi Me gari yaji dadin girkin ta baya so kowa yayi Masa girki sai Shukura,bashi da aiki sai yabon Shukura da iya girkinta Yana cewa kuma badan bariki ba ai tana da hali me kyau,kullum maganarsa Bata wuce ta Shukura a gaban abokansa,Liman ma abokinsa ne kawai sai ya bashi Shawara ya auri Shukura kawai,Me gari yace wuuuu tafi karfina wannan kaji yanda take bariki a gidana yanda Kiri Kiri take bamu labarin farkanta,yanda take sonsa kullum har mun gaji da ji,abin ya Kai kaga tana sheka dariya ita kadai idan ta motsa ma kuka zaka ga tanayi tana magana da turanci ko me take cewa oho,ni kuma kasan Liman ni mutum ne me tsananin kishi.

Liman dai ya karfafawa me gari Lallai ya auri Shukura ko ta wanne hali ne tunda shine me fada aji a garin,Da kwarin gwiwa Me gari ya dawo gida Nan ya iske masoyiyar tasa Shukura tana kwance saman wata Tsohuwar tabarma gindin bishiyar dake cikin gidan,Tana Hawaye sannan tana Dan Allah kazo gareni My Ahleef,Ina jiranka nasan zaka zo,Mijina I really missed u,my best frnd my Everything pls am waiting....sai maganganu take a fili kamar me aljanu,kishi ne ya soki zuciyar Dattijo MeGari Nan take zuciyarsa ta baci a fusace ya buga mata tsawa keee wai wannan turancin da kike me kike nufi ne idan zagin sauran Masoyanki kike yau kina fifita

1 Comments On JIN DADI SABO
avatar
mahamane-noura

2 years ago

Reply

Asalama alaikum, dan Allah yane ake sauke littafin akan waya

Please Login or Register in order to submit comment