Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai a lalace Kuma Hajiya ta Zama tantiriya Yara Kuma suna Abubuwa Marasa kyau,Allah yasa mu Dace kudi su daina rudarmu suna halakar damu.

Tunda Mubaraq ya karbi dukiyar Ahleef da Momee ta damka Masa shike Nan su Hafcy gaba daya suka dauke kafarsu da zuwa gidan wata Momee,Mubaraq ma yanzu ya Dan fara rage haduwa da Niima sai tayi ta nemansa da kyar yake samu yace tazo su hadu a gidansa inda a Nan zai Kara lallaba ta ya kwashi gara,maganin Hana daukan ciki kuwa dankararsu kawai takeyi sabo da Mubaraq yace sam baya Jin dadin xxx idan yasa Condom.

2pm aka tashi su Shukura daga schl, sun fito suna Hira Fatima kawar Shukura ta kalleta sosai tace sai Naga kamar kina tafiya wani iri kamar Yar koyo ko rauni kika ji a kafar, Murmushin karfin Hali Shukura tayi sannan tace bugewa nayi a gwiwa ta sosai,Latifa sai Harara take zubawa Shukura ganin tana ci gaba.
Fitowarsu kenan sai ga Ahleef yasha Boyal dark Brown yasha kyau har ya gaji Shukura tana ganin motar Ahleef tace Fatima Mijina yazo dauka ta sai gobe na tafi,Fatima itama driver dinsu ne yazo ta shiga motarsu suka tafi tana dagawa Shukura Hannu.

Ahleef Yana daga cikin mota mazaunin Driver Shukura ta bude Bayan mota ta jefa Jakarta ta dawo gaba ta bude tare da shiga cikin motar bakinta dauke da sallama,amsa Mata yayi kawai ba fara'a a fuskarsa,Shukura ta kalleshi taga kamar Yana cikin damuwa,ko me ya faru dashi oho, tunda ta shiga mota taga Yana tunani ko motar ya kasa matsawa bare su tafi gida, a hankali ta kamo hannunsa tare da furta lfy Sweet heart? a hankali ya kalleta ya Dan saki Murmushi sannan yaja Motar suka tafi,suna kan hanyarsu taji muryarsa yace ya jikin? Kallonsa kawai tayi tace da sauki amma Me yake damunka? Kamar kana cikin damuwa, yace hmm Honey Dad din Farhan ne ya Bata Mana Rai Ni da Farhan,anjima zamuyi maganar. Sai hakuri cewar Shukura.

Bayan sun koma gida Umma tuni ta Gama komai da komai gidan a gyare tsab Yana kamshi abinci ma du tayi ta Gama, Umma tace Sannu da zuwa suka Amsa suna gaida Umma suka wuce Bedroom, tare sukayi wanka tare da shiryawa sannan suka fito Dining, Shukura tace Umma Ina Baba? ya fita wurin abokansa tsofaffi irinsu can unguwar su Hafcy inda mukayi aiki da,Baba Yana son zuwa wurin mutanan Nan,Ai an Saba ne da juna can cewar Umma, Ahleef yace Haka ne,Shukura ce ta zuba Musu abinda suke so a plate daya suke ci tare,lemo ma a cup daya suka zuba suna Sha cike da shauki,Umma tana kitchen tana aiki.

10pm Sunyi Shirin bacci suna saman Bed Ahleef Yana rungume da Shukuransa Yana shafa gashinta,Shukura cike da Shagwaba da shauki tace My Hero baka bani labari ba me Dad din Farhan yayi muku? Hmm Honey Wai Munje yace zai bani jari Amma karki ga fadan daya shiga yi min wai na tabbatar na biyashi kudinsa Nan da 1yr dama mu Yara mun Saba barnatar da kudi maganganu iri iri banji dadin kalamansa ba,yanzu har Ni zai fadawa tattali,ko iya Business sabo da zai bani rancen kudi kafin na biyashi sabo da yanzu yaga bani da shi.
Kirjinsa Shukura take shafawa a hankali tace Kayi hakuri Haka rayuwa take,ka daina damuwa kaji mijina ai Dad dinku ne,idan Kuma kaga da matsala ka bar Masa kudinsa kawai Allah ya baka naka, Honey harfa da cewa Wai idan kudinsa ya salwanta sai ya daure Ni har Farhan zai daure yace, Shukura tace to bar Masa kudinsa kawai Amma muyi Shawara da Baba ko Umma muji me zasuce, Allah ya kaimu gobe sai na sanar musu muji cewar Ahleef, Zancen su ne ya canja salo zuwa na soyayya Nan suka shiga farantawa juna Rai ba tare da yayi Xxx ba sabo da Shukuransa Bata warke ba.














AsmaBaffa



Ayi min afwa fans bana baku kullum Busy nake tnx all😍😍😍.
[7/22, 1:14 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO






66-70







Official







By
AsmaBaffa









Washe gari da safe sabo da makaranta da wuri Shukura ta fada kitchen zata fara girki kenan Umma ta isketa suka gaisa,Umma tace kiyi iya cikinki da safe Kinga mu bama karyawa da Sassafe ke Kuma ga makaranta,Murmushi Shukura tayi tare da cewa to Umma ba matsala,Nan Shukura ta hada chips and Egg sai tea,tana Gama ci ta Shiga wanka,Bayan ta fito ta tashi Ahleef ya kaita schl, da sauri ya shirya suka yiwa Baba da Umma sallama suka wuce.

Bayan Ahleef ya dawo ya samu Umma da Baba ya sanar musu yanda sukayi da Dad din Farhan,Umma tace Shawara daya karka karba kawai bar Masa kudinsa,Baba ma yace hakane kawai kace ya barshi ka samu wasu sun Isheka,Farhan yace to sannan ya mike ya koma Bedroom dinsu kawai yaji gidan ya Masa zafi ba Shukura tunaninta ya addabe shi,ita kawai yake son gani suyi Hira, wanka yayi ya shirya tare da Fita ko karyawa bai yi ba,Umma tace yaci yace a koshe yake,Take away ya tsaya yayi na lafiyayyen Fried rice and chicken tare da Drinks ya wuce Schl din su Shukura yaga an kusa yi musu Break ma.

Yana zuwa lokacin sun fito Break tare da Fatima Kawarta suna Hira Shukura ta hango kamar Motar Ahleef, laa Fatima Kinga Mijina yazo nasan ma shine Maybe abinci ya kawo min,Murmushi Fatima tayi tare da cewa Lallai Yana ji dake,Fari Shukura tayi da Ido kana tace sosai yake Sona nima Ina mugun kaunar abina,Kirji ta dafe tana Allah sarki Dan Mijina muje na ganshi naji sanyi sanyi a Raina,Dariya Fatima tayi tace sai dai kije ke kadai Ni bazan je ba kunyarsa nake ji,Naga baya dariya ga kowa sai ke kadai yake yima,inje ya min kallon Tara saura quarter, ke kika sani cewar Shukura ta bar Fatima tsaye ta wuce wurin Mijinta.

A hankali take takunta cikin nutsuwa har takarasa tare da bude gaban motar ta Shiga tana dauke da sallama a bakinta, amsa Mata yayi sannan yace ya karatu?Yana Mai sakar Mata Murmushinsa Wanda ke Kara Masa kyau, Alhmdllh ta furta tare da cewa My Hero abinci ka kawo min? Dariya yayi sarkin Kwadayi ba abinda na kawo,Cike da Shagwaba ta kwabe fuska kamar zatayi kuka to kaje Ka siyo min Mana yanzu idan kana da kudi,Wai naga kamar bakayi Breakfast ba Baby? Ledar take away ya Mika Mata, ta karba cike da murna tana godiya,daya ledar ya dago Mata Kinga nawa,Murmushi ta saki tam Sweetheart ka cika cikinka dam idan na dawo Naga kaci kadan dure zan maka, dariya yayi kadan kana ya rungumeta tare da kissing din lips nata ya Mata sallama ta koma ajinsu shi kuma ya tafi,tare da Fatima suka ci abincin tas suka Sha ruwansu da lemo sannan suka koma aji, Ana tashinsu lokacin Ahleef suna tare da Farhan neman Mafita, ya Duba agogon hannunsa zumbur ya mike yace an tashi Su Honey zan dakko ta a schl,Farhan ya bude Baki sannan yace ka bari nasa Driver na ya dakko maka ita sai mu Gama maganar mu,A',a ni ban yarda ba da kaina zan dakko ta,Driver yayi min gudun ganganci da matata ba zai yuwu ba da kaina zan dakko ta,Dariya Farhan yayi yace Allah kiyaye hanya da yamma nazo gidan,Ahleef yace Allah ya kaimu yayi gaba.
Yana zuwa Already Shukura tana bakin gate tana jiransa, aiko ya dauko abarsa.

Yamma Liss Farhan yazo suna tare da Ahleef suna tattauna ya za ayi Ahleef ya samu Jari masu yawa,Farhan Yace Man kyale kudin Dad kar ya hanamu sakewa sabo da Dad shima akwai son Kudi, Gidana Na Lagos Dana Gina kasan yanzu zai kar Million dari kawai a siyar dashi kaci gaba da harkokinka,Ahleef yace no idan anyi Haka ai baka da kadarar da ta Kai wannan kudi ai kuma na takuraka,Masifa Farhan ya Shiga yi kamar zai tashi sama,To kudin Dana yi waye yamin silar samunsu idan ba Kai ba,Ni jarin nawa ka bani har na Zama abinda na Zama,Ko Dad bai min abinda kayi min ba a duniya duk abinda na Samu ta silarka ne Sannan yanzu Dan na baka Abu shine zaka min iyayi,Ni duk abinda na mallaka wlh zan iya mallaka maka shi Amma kana Fuck up,Ahleef zaiyi magana Farhan ya mike a fusace zai fita dai dai lokacin Shukura ta shigo dauke da tire na kayan Sha Dana ci, tace ah Ina zaka je Haka Kuma? Murmushi Farhan yayi mijinki ya Bata min Rai.

Murmushi Shukura tayi tace Dan kace Zaka bashi jari ko? Ya fada min jiya nace ya karba Amma karka saurareshi ka kawo kudin Ni zan karba Kuma Dole ya karba,ko ka tura min a accnt Dina zanyi maganinsa Ni da kaina,Dariya sukayi gaba daya Har Ahleef yanda Shukura tayi maganar kamar Babarsa, Farhan ya koma ya zauna tare da cewa to kaji abinda tace Mijin tace, Ahleef Yana dariya yace Totally Surrender abinda yace an Gama Yana dagawa Shukura gira daya,ta ajiye abincin ta zuba ta mikawa Ahleef nasa tace Gwauro Kuma ya zubawa kansa,Farhan yace na kusa daina zuwa gidan Nan tunda Ware Ni akeyi Ana min Gori.
Shukura tana Murmushi ta bar dakin suna ta hirarsu akan Business din da Ahleef zaiyi da kudin Farhan daya bashi.

Bayan wata daya kudin su Momi Sunyi kasa sosai ga Business baya tafiya kudi sai Bata sukeyi basa gaba,Mubaraq ya Gama tatike su kullum baya kasar Momee so take ma ta ganshi ta tambayeshi ya kudi suke Bata da Masifar yawa Haka,Amma Mubaraq Sam yaki yarda ma su San inda yake,Idan Niima ta tambayi Hafcy ko Mamansu basa fada sai suce su Basu San ma Mubaraq Yana juya musu kudi ba,Basu San inda yake ba,kudi Kuma da kadarori sai Bata suke wasu kadarorin ma suna tambaya za ace ai tuni an siyar da su.

Niima kuma sai cuta takeyi Ga Amai da tofar da yawu,Momee ta kaita asibiti aka ce ciki gareta har na 3mnths,Momee kuka sosai takeyi,Ga Latifa kullum sai Shan kwayoyi da giya tana club kullum, Women Leader ma da aka bawa Momee tuni an Kai sukar cewar ba Yar siyasa bace sabo da Haka Dole sai labari taji an tsigeta an Sa Yar siyasa.

Momee duniya ta fara Mata zafi musamman idan ta kalli Niima da Latifa sai ta zubar da Hawaye,A waya ta Kira Sultan da Suhail ta sanar musu halin da suke ciki,Sultan yace Momee lokacin da muka fada muku maganar gaskiya laifinmu ma kika gani,gashi yanzu kin Kai yaran wasu an lalata su,Kinga Dole ayiwa naki yaran,Haka Matar ya Ahleef kika Mata kazafi yanzu Kuma gashi Dole kina daukan karatun Duniya,dama idan baka ji nasihar mutane ba to duniya da kanta zata yi maka Kuma Dole ka ji nata, Momee tana Hawaye tace Ni dai kuzo a San yanda za ayi da Niima,Sultan yace wlh ba ruwanmu Kuna zubar da ciki kunyi kisan Kai again,Kuma kika Bata da danginki kaf Momee Akan abin duniya dare daya kika canja hali.

Visa Momee tayi ta nufi USA da niyyar ta karbe kudi da kadarar da Abba ya barwa Ahleef kyauta.
Tana zuwa mutumin yace bazai bayar ba sabo da Amana Abba ya bashi yace Kar ya bawa kowa kudin sai Ahleef yazo da kansa,Kuma da court din us akayi komai,tana takura Masa zaisa a daure ta,ba shiri Momee ta dawo gida ta dauki Niima zuwa asibiti Wai a cire ciki, Bayan aune aune aka gano Niima ta Gama kashe mahaifarta da Shan kwayoyin Hana daukan ciki,sabo da Haka ciki bazai zubu ba,idan aka cire to zata rasa ranta dolensu suka dawo gida suka ci gaba da rayuwa Kullum Kuma kadara da kudi suna karewa,Momee da kyar ta lallaba ta kwashe wasu kudaden masu yawa ta canja account sannan kadarar da ba a siyar ba ta siyar ta hada kan kudin kaf ta ajiye a accnt.

Ahleef Bayan kwana Hudu ya Gama dagawa Shukura kafa,kamar kullum yau da dare ya dawo gida,Shukura tana kwance a jikinsa suna kallo.
Wani mayen kallo yake binta da shi,Shukura ta tsorata gaba daya,a wayance tace Bari naje wajen Umma na karbo sako, Ahleef ya kalleta tare da cewa da Daren Nan? Wanne dare Kuma just 9:30 kace dare yayi,yanzu zan dawo pls ba musu yace alright da kansa ya mikar da ita tsaye tasa hijab tayi waje tana fita ta tsaya a Palo tana sauke numfashin tsoro tare da dafe kirji Wanda ke bugawa sabo da tsoro Tasha wahala first night yanzu Kuma taga take taken Ahleef.

Ta Dade a tsaye taki komawa sai ga Umma ta fito da niyyar zuwa kitchen zata hadawa Baba tea, Shukura tana ganinta ta buya Amma Umma ta rigada ta ganta,Muryar Umma kawai taji tace lfy ke Kuma? Dole ta fito fili tana Ina..Ina...dama..uhmm...kitchen zanje zan dafa Indomie ....au tea zan hada, Murmushi kawai Umma tayi tace to dama Nima Babanku zan hadawa zo sai na dafa daku,Shukura ba shiri tabi Bayan Umma har kitchen.
Fridge Umma ta bude ta dauko wani tsumi na mata tace ungo shanye yanzu,Shukura ta kalli abin tace Umma du kalli fa da yawa,ban son surutu na gyaran jiki ne ki shanye ki bani rubber ta,Shukura ta daga Kai ta kwankwade shi ta mikawa Umma robar, kafin Umma ta Gama dafa tea tuni magani ya fara aiki,Shukura duk taji ta Zama wet ga wata Yar Shaawa na kamata kadan taji ba Wanda take bukata sai Ahleef, ta rasa dalili,so take ma tayi sauri ta koma room dinsu,Umma na Gama dafa tea Shukura ta karba tace sai da safe Umma, to kin manta sugar din cewar Umma,da sauri ta dauki Sugar tayi gaba,Umma tace Spoon fa Baki dauka ba Wai meke damunki ne,da sauri ta Kara dawowa bula bula da Hijab dinta ta dauki spoon,Umma tace cups fa? Nan ma ba magana ta sura tayi gaba abinta.

Ahleef kuwa ya gaji da jira har ya mike zai je ya daukota sai yaga ta banko kofa bata kulashi ba tace ga tea Nan Bari nayi wanka,ta fada toilet tayi wanka da brush,tana fitowa ta shirya tana zuba kamshi cikin kayan bacci masu daukan hankali, Ahleef tunda ya Shiga yaki fitowa daga wankan da wuri,dama shi wankansa sai ya Dade sosai,Shukura taje jikin kofar tace Ni zanyi baccina Kuma idan na kwanta bazan tashi na hada ma tea ba,karma ka tasheni,Wai wayo ta hada Nan,Ahleef Bai gane ba yace no karkiyi bacci pls shugo toilet din ki jira Ni, naki Ni bazan shugo ba ta furta da Shagwaba,Yana fitowa ta zuba Masa idonta tana Kare wa halittarsa kallo tana dauke Kai Dan kar ya gano ta,Yana shiryawa yace bini muyi nafeela,Shukura tace Ni dai yau Allah bazan iya ba,bacci nake ji,sai dai kayi Kai kadai Kuma bazan jiraka ba zanyi bacci na kana tayar da sallah zanyi bacci abina, yau Sallar ma baza ki Bari ayi ba.

Ni Bari nayi tawa Ni kadai,zai tayar kenan Shukura taje tayi tsalle ta bayansa ta daneshi du ta makalkaleshi tana dariya tace Allah baza kayi ba kaima kazo ka fini samun Lada,fafur taki sauka Dole ya hakura da sallar, tea ta hada Masa ta Mika masa Yana gefen Bed ya kunna tv ya kamo tashar ball Yana kallo Yana Shan tea dinsa Shukura tayi matashi da cinyarsa, yace Bari mu kallon match din Nan sai mu kwanta ko?

Shukura tace sam wannan tsinanniyar ball za a kalla Ni bana gane me sukeyi,a rasa abinda za a kalla sai ball,wancen Dan iskan Messi din me Ido kamar na tururuwa su zamu kalla ta Danna remote ta kashe tv,ta karbe tea din dake hannun Ahleef yasha rabi kawai ta kwankwade Rabin tare cewa sai yanga kake kwanta bacci to za ayi Kuma karka tasheni, ta kwanta abinta Ahleef Yana Murmushi ya kwanta suna facing din juna,Bai taba ta ba sabo da tunaninsa zata Hana ta kama kukan da ta Saba,sai ko hugging baiyi ba Yana tunanin Taya zai bullo Mata,Shukura ta kashe light tare da rufe Ido Wai tayi bacci ita, a hankali Ahleef ya dawo da ita jikinsa sai ko yaga ta Kara makaleshi Bata ce komai ba, gashinta me tsayi da santsi ya warware ya nutsa yatsunsa ciki Yana shafa Mata a hankali cikin salon kwarewa.

Shukura idonta ta lumshe da kanta ta fara kissing dinsa tun tanayin kadan ta koma so Deep,sai Rada take Masa a kunne tana Masa wasanni a kunne da harshenta,Ahleef ya rude Basu San sanda suka zarewa juna Kaya ba,kowannensu cikin kwarewa da salon bajinta yake sarrafa Dan uwansa suna jiyar da juna dadi,sosai Shukura ta ba da hadin Kai duk da yauma taji zafi Amma ba sosai ba, Ahleef yau sabo da sweet din Shukura sai da yayi hawayen dadi,Hawaye sosai, Bayan sun tsarkake jikinsu bacci me karfi ya kwashesu, 2:30am Ahleef ya farka da Jarabarsa sallar dare ya Saba Yana yi tare da Shukura Amma wannan karon Yana tashinta yace yau ba sunnar Nafeela za ayi ba, Shukura da Tasha tsumin Umma Haka ta bada hadin Kai suka Kara darje juna, da Asuba ma Haka suka sake sabo Shukura tana Jin zafi Amma sabo da maita mukus takeyi Bata kin yarda sai dai tana cin uban gashi kamar zata Kone wajen da ruwan zafi,Ahleef kuwa kawai kwasar harkoki yake abinsa, ranar ko schl Shukura Bata je ba,Kuma tunda suka fito suka gaida Umma da Baba suka koma dakinsu abinci ma sai dai Ahleef yaje ya ebo musu ya dawo, a room suka yini sai yamma Bayan Sallar laasar suka fito,Baba sai fada yakewa Ahleef yau Bai samu jam'i ba ko daya, Shukura tace ai yanzu Baba zaije Magrib da Isha dazu ma kansa ne yake ta ciwo tun jiya sai yanzu yaji sauki,Baba yace Kash Allah ya sawwake kasha magani ko asibiti zaka je? Ido suka hada da Shukura suka yiwa juna signa sannan yace ai dazu Naga maganin a jakata na Sha shine ma na Samu sauki, Shukura tace da har zanzo na fada muku Baba yace Wai kar na fada tun jiya yasha wahala gaskiya,Umma ita kanta ta yarda da Shukura tace idan ba sakarci irin naku ba mutum ya kwana Yana ciwon Kai baza ki fada ba,Dazu kazo ka ebi abinci safe da Rana wa yaci?

Ahleef yace tun jiya take ta faman kuka sabo da ina ciwon Kai taki cin komai shine Dana ji sauki sauki nazo na ebar mata, Umma tace eyya to Allah bada lfy, Suka ce Ameen,Ahleef yace Bari zanje wurin Farhan anjima zan dawo,Hannun Shukura ya kamo yace ko Zaki je? Umma tace ba inda zata je jiya kunce bakuyi bacci ba kana cuta yanzu ai gwara ta huta,Shukura tace Umma Dan Allah zanje pls Kinga fa na Dade ban fita ba,Ke da idonki tunda Zaki iya sai kuje,da sauri taje ta shirya cikin wani arnen lace dinta milk da ratsin Orange takalmi da jaka tare da mayafi Orange tayi Masifar kyau, Ahleef kuwa cikin Milk shadda me tsada Tasha dinkin zamani na Matasa Yan gayu, sai kamshi sukeyi suka yiwa su Baba sallama suka fita hannunsu rike da juna,Ahleef yace dama ba wajen Farhan zanje bafa yawo zamuyi a kafa muga unguwar Nan, Umma idan ta sani maybe tace baza kije ba,Shukura tace Amma naji dadi, weather me dadi suna tafiya a hankali suna hirarsu ta masoya suna kwasar fresh air abinsu dake Abuja ne ba ruwan wani da wani kowa ya gansu sai sun birge, suna shaukinsu Sai ga Farhan da mota zaije gidansu ya wuce ya dawo baya tare da sauke Glass kasa Yana dariya yace Allah ya shiryeka Dan Iska, hannu Ahleef ya Mika Masa suka tafa,Shukura ma ta gaidashi,yace to kuzo mu koma dama gidanku zanje,Ahleef yace wlh baza mu koma ba sai dai kaje ka jira mu a gida sai sanda muka dawo ko ka tafi gobe ka dawo ko Nazo amma baka Isa mun koma ba,yawo muka fito da Honey,Farhan yace zaka sani ne Nima wlh indai nayi aure sai na Rama suna dariya yaja mota ya tafi gidan su Ahleef,Umma da Baba basusan a kafa suka fita yawo ba sai Farhan ne ya tona su.

Wata sabuwa Bayan kwananki kadan Ciwon Koda me tsanani ya kama Momee,kullum suna hanyar asibiti Ana cinye wannan dukiya,samari da wasu Yan film tare da karuwai sunga Momee kudi Babu ga ciwo ya kamata suka zare jikinsu ko dubiya ba wacce ta leko,Haka dangin Momee sunji labari Amma ko leke,Niima tayi kuka har ta godewa Allah,Latifa kuwa ba ruwanta kullum tana yawonta,Niima da katon ciki Haka take kula da Momee,Yan aiki duk Babu sun arce, Ahleef kuwa bai da labari sabo da tunda ya tafi bai sake leko su ba

Bayan wasu watanni Ahleef Alhmdllh ya sake Zama wani Hamshakin me kudi na gasken gaske,Haka Allah yayi shi komai ya taba sai yayi albarka, tuni ya Gina musu rantsatsen gidan da Babu irinsa, Kuma gidan da Farhan ya siyar ya bashi tuni yaje ya siyawa Farhan Wanda ya fishi kyauta, yanzu duk inda Ahleef yake sai kaga Shukura a gefensa yawancin meeting ko wani abu da ita yake zuwa,Kuma duk takardun da zai cike Yana rubuta ta a Itace magajiyarsa Next of kin, Shukura ta Kara wani wayewa ta goge sosai,sun kusa zana waec da Neco, Ana yawan Nuna Ahleef a gidan Tv ko radio yanda yake bawa kasa gudun mawa Yana taimakawa Marasa karfi.

Bayan Shukura sun gama ssce exam Visa Ahleef yayiwa Shukura tare da shi zuwa London,Umma da Baba Kuma ya biya misu Saudiya, Bai San wanne Hali su Momee ke ciki ba suka dage zuwa London,Suna cikin jirgi Shukura ta lafe a jikinsa tana bacci abinta cikin kwanciyar hankali sai wani lallabata Ahleef keyi,da dare misalin 8pm suka Isa London,mota suka shiga zuwa masaukinsu wani katafaren Hotel,tun a taxi Ahleef ya tsaya yasiyawa Shukura Lemo me shegen dadi da wani snacks, Shukura tunda suka sauka taji Niima a garin ga wani dadin sanyi,kasa kamar aljannar duniya,tana kora lemo tace My Hero Allah wadai da halin shugabanninmu ,dariya Ahleef ya dingayi yace Babu kyau fa zagin shugaba kin sani,me suka Miki? Shukura ta Kara daga lemo ta zuka sannan tace Nigeria baza mu taba ci gaba ba har Kiyama ta tsaya,gamu da kudi Amma gaba daya da shugaban nin da mu Yan kasar Babu na gari sai dai dai,yanzu jibi kasar Nan kamshinta ma daban ne,kalli Amma mu sai dai a sace kudin kasar,na kasa ma ko tallafi shugaba ya bada a raba kafin yazo hannun talakawa duk sun cinye kudin.

Ahleef ya kafeta da kallo tana ta ciye ciyenta Yana Kara Jin wani sonta da shaawarta na ratsashi, ba tare da ta kalleshi ba tace kallonfa na mene,rungumeta yayi a jikinsa gaba daya tare da Rada Mata I Love u Honey, Murmushi ta saki tace me too Sweety.
Suna zuwa Hotel dama tuni ya musu booking da karamar trolley dinsu suka wuce ciki.

Momee kwance a gadon asibiti Niima da Dan karamin cikinta tana aikin jinya sai masifa take zazzagawa Momee, Dan Allah Momee Ni ki karbi magani Kisha sai wahalar Dani kike duk kokarin da nake Bakya gani,Hawaye ya zubowa Momee tace Wai Ni kikewa tsawa Haka Niima? Cikin radadin ciwo Hawaye ya zubo wa Momee,da kyar tace Ina...na...na....Latifa?
Tsaki Niima taja kadan sannan tace tana

1 Comments On JIN DADI SABO
avatar
mahamane-noura

2 years ago

Reply

Asalama alaikum, dan Allah yane ake sauke littafin akan waya

Please Login or Register in order to submit comment