Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zubawa Driver a mota ya tafi kai masa.
Ahleef yayi mamakin ganin girki lafiyayye Haka lallai Shukura ta samu uwa ta kirki Saudatu Zata koya mata komai, abinci ya zuba ya fara ci wani shegen dadi Wanda bai taba cin girki irinsa ba me dadi haka yana cikin ci yana santi Shukura ta kira wayarsa,ya dauka tace Yaya ya kaji ? Yace na nadaki sarauniyar iya girki ta Africa,ta dinga dariyar Jin dadi,Yace yau nasan sai na manta hanyar gidana nan ma ta tuntsire da dariya an yabi girkinta,ya cika baki da abinci da kyar yake magana yana Sani yayi haka dan taji dadi ba kyau ayi maka abin gwaninta ka kasa yabawa,yace yar kauye tafi yan birni iya girki tazo ta kwace musu bokonsu na iya girki,Tace kai Sir to gobe ma zanyi maka wani,yace dolenki ma ai naga waje,an nunawa kurciya baka,yanzu zan fadawa saurayinki shima yazo yaci,Shukura tace to idan yaci anjima da dare ka kirani ka bani labarin irin santinsa,yayi mata ta yara yace tam tare da kashe wayar.
Ahleef ya biyewa Shukura ya takurawa Farhan lallai sai yazo Office yaci abincin Amaryarsa wai dole Farhan yazo.








AsmaBaffa.
[7/22, 1:13 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO







10









official







By
AsmaBaffa








Kuyi Hakuri readers kwana biyu ina Busy ne shi yasa baku jini ba.

Ina matukar godiya ga masu Sharhi Allah ya biya ku,karku gaji pls aci gaba ina gani kuma zanyi kokarin ganin kowa na masa reply.






ASYCOOL,DIYAR KATIBI, HAFSAT KHAIRAN and ZEEMAMA wannan page din naku ne Sabo da Kauna.










Farhan yana shiga Office din yace na Niima ba.. Kafin ya karasa Ahleef yaja wani mugun tsaki Wanda bai taba yi ba, me zanyi da ita Allah ya kiyaye, Farhan yace Niimar taka ? Dama sai yanzu na gane wlh ba so Bane kawai Shakuwa ce ta zama waje daya da kuma son kyautatawa Momee da Abba,Kallonsa kawai Farhan yake yana mamaki,dama ba so bane kace ? Kwarai kuwa Allah ya taimakeni Bata aureni ba ni sai yanzu ma nake kara sonta kuma ta birgeni wajen taimaka min da tayi ban aure ta ba, Farhan ya fara dariya tare da cewa kaifa kace tafi matan duniya kyau, Lokacin ban gane ba amma Ko yar yarinyar nan Shukura ai ta linka ta sau dubu saba'in na tsaya ina batawa kaina lokaci,Uhm yanzu Shukura ta fita kenan ? Farhan ya tambaya,Nesa ba kusa bama budurwarka ta fita kyau, Ashar Farhan ya dura masa tare da cewa munafikin banza zakayi bayani,sai kazo kana fakewa dani budurwata budurwata munafuncin banza,Dariya Ahleef yayi tare da cewa Kasan Allah ba wani so tsakaninmu kawai taimako ne,ni me zanyi da mace yanzu babu class dina fata nake ma ka aureta wlh, harara Farhan ya watsa masa tare da cewa Allah kiyayeni kazo kana bibiyarmin mata,nan Gaba zaka yi bayani,baki Ahleef ya tabe baka ganewa wlh malam ga abincin nan ci ka tafi,Farhan yaci abinci shima yana zuba santi iri iri.

Da dare Ahleef sai yaga gidan yayi masa fadi,ba dadi shi kadai kamar maye gaskiya yayi missing Shukura, haka yayi shirin bacci ya kwanta 12am ya tuna bari ya kira Shukura ya bata labarin santin Saurayinta Farhan lokacin da yaci girkinta,Har yayi Dialing ya tuna dare yayi ya kashe ganin gobe Zata fara zuwa schl.
Washe gari da sassafe Umma Saudatu ta tashi Shukura, dake Shukura haka kawai Allah ya sa mata tsoron Saudatu da wuri ta tashi tayi shirin makaranta Uniform White and Green din yayi mata kyau Hijab dinta iya mazaunanta,Schl bag dinta ta shirya tsab sannan tayi break fast tare da mikewa taje har dakin Baba ta gaida shi da labadi,yace Shukura makaranta za aje tace ae Baba, to Allah bada sa'a ya zaro dari biyu ya Bata kudin makaranta,tayi Godiya ta amsa cike da murna ta rataya jakarta tare da musu Sallama ta fito,tana fitowa motocin Ahleef Suna shigowa gidan wasu sababbi dal dal guda shida tare da escorts nasa,Shukura ya hango tayi kyau cikin Uniform dinta,Guard ya bude masa motar ya kara 5mnt bai fito ba Sabo da Izza sai daga bisani ya zuro kafafunsa abin kallo yana fitowa Kamshinsa ya gauraye wajen,Yasha uban kyau cikin kana nan kayansa.

Direct wurin Umma ya nufa suka gaisa,Sai da sukayi Mintuna suna hira da Baba sannan ya musu sallama ya fito cikin takunsa na birgewa,Shukura ta rusuna tare da cewa Ina kwana Yaya,kin tashi lfy kawai yace sannan yace muje pls zakiyi Late,abinda bai Sani ba Shukura tafi son tayi late Sabo da bata son makaranta a rayuwarta, saida ta shiga Mota kusa da Ahleef gefensa sannan tace au nayi mantuwa ina zuwa ta bude ta fice tana tafiya kamar marar lfy wai dan tayi Late Bata so taje kan lokaci tafi so taje makaranta an kusa fita daga first period, cikin dakinta ta buya dan kar Umma ta ganeta,sai da ta dan dade sannan ta fito tana tafiyarta cikin sangaya har ta shiga mota,yace as from today Driver ne zai kaiki kullum, Baki ta turo tare da cewa ai makarantar ba nisa da kafa ma zan iya zuwa daga yau ni a kafa zan na zuwa ta furta dan kawai kar ta dinga zuwa schl akan lokaci,bata San makaratun birni dana kauye daban ba, shima bai ce mata komai kawai satar kallonta yayi kadan ta gefen ido,Kuruciyar tata tayi yawa Sabo da iyayenta Sam basu koya mata komai ba.

Jarida yake karantawa har Sukayi parking a Compound na schl din,wajen Principal ya kaita da kansa aka sa wata Senior student Namiji ya rakata Ss1 class dinsu tana tsoro tsoro yanda taji ana feso turanci ta ko ina. Ahleef ta kalla shima ita yake kallo, Hannu ya Mika mata Sukayi Handshake sannan yace jeki to bye,baki ta turo tare da cewa ya naji ana cewa Ss1 za a kaini ni fa a Ss3 nake repeating din yayi yawa,Baza ki gane ba sai nan gaba jeki class ya furta yana daga mata hannu, itama ta daga masa hannu tana kashe masa ido daya,dariya yayi kawai ta wuce.
Zata Shiga Class din malamar dake ciki tana koya darasi ta kalli Shukura tare da cewa Beautiful Lady can I Help u? Shukura tace Help ? Help...Help ta ci gaba itama ta tambayi malamar tare da cewa to Help me wiz Money or Wiz Meat, Chocolate,Ice Cream,Shawarma? Ta tambaya tana washe baki,yan Class har malamar suka kwashe da dariya wannan akwai son Dadi ga turancinta na Tsofaffin Hausawa Baza suce With ba sai wiz,Zey etc.
Malamar tace go and sit down,ta wuce sumi sumi ta zauna ita kadai can karshen baya,Maza da mata kallon Shukura akeyi ana gulmar kyanta kamar ita tayi kanta.

Tunanin yan class Shukura Bata da wani kokari tunda sunji kalar turancinta duk kyanta sai suka rainata,Period din Malama ta kare wani malamin Biology ya shigo,ya fara yiwa yan aji tambayoyi what is kaza what is kaza etc,yana yin tambayar farko ba Wanda ya daga hannu sai Shukura,shi kanshi ya girgiza da kyanta yace ta fada,ta Mike ta bada amsa dai dai kuma kawai turancinne idan anji an San Bata kware ba, Malamin yasa aka dinga tafa mata,ya kuma jefo ta biyu Shukura ta kara daga hannu tare da wasu yan aji ya kara nunata ta fada nan ma ta bada amsa dai dai Kafin ya bar ajin saida ta amsa questions hudu.
Wani ma ya shigo haka ta dinga kokari gaba daya sai gashi ta kankaro mutuncinta kowa yasan me kokari ce sai ga students mata da maza Sun fara mata magana dake ita Shukura zai wahala kaga tayi fushi ko ta Bata rai haka suka dan saba kadan ta saki jiki sama sama.
2pm suka tashi ta fito bakin Gate,Drivern Ahleef ta gani Yana jiranta ta shiga suka tafi gida,Yau ma tare da Umma sukayi abincin dare suka gama komai.

Washe Gari Driver ne zai kaita amma tace ita da kafa zata je,ta fito kenan Latifa ma ta fito Sabo da Niima ta bawa Latifa labarin cewa an kawo wata yarinya gidansu Bata da kunya an sata a schl ma Sabo da haka Zata yi mata transfer zuwa makarantar su Shukura domin hana Shukura karatu da Jin dadin schl baki daya,Sannan Niima ce zata dinga shirya komai yanda zai tafi dai dai,Niima tace Latifa ta shirya yau ita Zata fara kaita schl ma, Latifa da bata yarda zatayi ba Sabo da bata San wace ba, Sun fito Compound tayi arba da Shukura ta ganeta sai ta bawa Niima Labarin fadansu da Shukura a motar Ahleef sannan tace Alhmdllh dama na tsaneta tunda itace wlh sai inda karfina na ya kare sai karatu ya gagareta, Niima taji dadi suka tafi a mota,Shukura tana kallonsu ta fice ta tafi a kafa tana ta bata lokaci har first period Zata fita sannan taje schl.

Tana zuwa gate taga Niima tare da wasu malamai da kuma seniors baki daya tana fada musu cewar Shukura kanwarta ce,bata son karatu ne shi yasa aka yi mata Transfer zuwa wannan makaranta Sabo da Sun iya ladabtar da Soudent,kuma a kula Shukura barauniya ce,sannan tana zagin iyayenta kar a raga mata a schl din Sun kawota ne domin a hukuntata idan tayi laifi, PC yace ai yayanku ne ya kawota kuma baice musu haka ba, Niima ta zaro takarda ta mika masa tace gashi babansu su ne ya bayar a kawo kan halayen Shukura yana so schl su tayashi tarbiyantar da ita,pc ya karba kuma ya gamsu haka sauran malamai ma, ta kara miko takarda tace inji yayansu Ahleef yana bada Umarnin hukunta Shukura idan tayi laifi dama haka take ta damesu a gida Bata ji,karshe ta zaro kudi masu yawan gaske ta bawa malamai har senior student,kudin da ta bawa PC na daban ne nan Take suka gigice suna godewa Niima ta juya ta shige motarta ta bar schl din.

Lokacin kuma Shukura ta shigo gate din PC yace lallai gaskiya ne ga zahiri dan Iskanci tana New student sai yanzu Zata zo schl period daya ta fita salon ta lalata musu schl, to baza su yarda ba wlh dole su dauki mataki ba ruwansu da New student ce,Bulala PC yace a kawo masa,yace Shukura tayi kamun kunne,tun kafin tayi ta fara Kuka,haka ya sata kamun kunne, tsallen kwado sannan ya sa wasu malamai biyu suka zanewa Shukura jiki sai da suka fasa mata fata jikinta yayi rudu rudu,An daki sarkin Shagwaba,su kansu malaman sai da suka ce basu taba ganin yar shagwaba irinta ba daru take iri iri ana kallonta,idonta yayi jajir Sabo da kuka haka ta Shiga Class,tasan dama tunda taga Latifa tare da Niima a schl din dole tasan sai wani abu ya sameta.

Bayan anyi musu Break Latifa Har tayi frnds masu kudi yan wulakanci ta sanar musu Shukura yar aikin gidansu ce daga kauye aka kawo ta gashi kuma su a Ss2 suke seniors ne,Shukura tana gaban me Yogourt ta karba ta bar wajen taji kawai an shako Hijab dinta ta baya sai da ya yage ta wuyanta kafin tace komai wata ta fisge yogourt din me kankara,Ido Hudu sukayi da Latifa,Shukura a ranta tace bashi kika ci,Tana kallonsu wajen su Shidda suka dinga dungure mata kai suna mata dariya tare da wulakanci iri iri Student suna ta kallo masu dariya na yi masu Tausayin Shukura suna ji,Shukura kuwa Sun mata yawa mukus tayi kanta a kasa har suka gama suka tafi sannan taja kafarta da take dingisawa da kyar Sabo da tsallen kwadon da tayi ya tashi Tsohon rauninta da Igbo Man Wanda ya taba bige ta a mota ya ja mata. Motocin Ahleef ne suka keto cikin Schl din tare da Escorts Latifa ya fara hangowa cikin kawayenta marasa kunya,kallo ya koma kansa Gaba daya,Fitowa yayi cikin shiga ta Alfarma duk Wanda ya kalli Ahleef sai yasan lallai Allah Sarki daya ne,yan mata ko kyafta ido basa yi kansa,Latifa ta fara iyayi ga yayanta suka rankaya zasu kwasar gaisuwa,Ahleef da mamaki yace ke kuma me ya dawo dake wannan schl din ? Ko iyayin ne ya motsa ? Latifa tace nafi sonta Yaya,baki ya tabe tare da cewa taki schl din tafi wannan komai fa,anyway je ki Ss1 ki kira min Shukura,Munafuka Latifa sai ta nuna Sam Bata gane wa yake nufi ba sai da ya mata kwatance sannan wata ciki tace ta gane ta suka tafi jiki na rawa suka samu Shukura ta kwanta saman Sit tana tunani iri iri,Duka Latifa ta dada mata a cinya tare da cewa kije inji Wanda ya kawoki nan,tasan Wa take nufi,ta dauki jakarta suka fisge tare da zazzage komai na ciki a kasa sukayi tafiyarsu,Shukura abar tausayi ta sunkuya tare da kwashe komai ta mayar cikin bag sannan ta fita tana dingishi amma a ranta Dadi take ji na zuwan Ahleef Sabo da yanzu ganinsa takeyi kamar dan uwanta na jini.

Yana cikin mota yana shan AC ya hangota a birkice idonta Jajir kuma ba fara ar daya saba gani a fuskarta,sannan Uniform dinta duk sunyi Dirty bayan ya santa da tsabta.
karasowa tayi jikin motar daya ke ciki ana ta kallonsu,Murmushin dole tayi ta leka kanta ta Glass din tare da cewa Sannu da Zuwa Yaya,ba tare da ya kalleta ba yana latsa wayarsa cikin iyayinsa tare da murya me dadin sauraro yace me ya samu kafarki ? Kuka kikayi ? Uniform kuma sunyi Dirty,gefen yatsanki kamar shatin bulala,Rau rau tayi Zata fara kuka da kyar ta danne tace ba komai dazu ne aka ce yan class sunyi laifi shine aka zane mu duka tare da tsallen kwado,Kuka ta fashe masa dashi tace shi yasa nace ma wlh bana son yan birni mugaye ne saura kadan su kasheni dazu Allah ne ya kiyaye malaikan daukan rai bai karaso ba, dan Allah Sir bana son karatun ni na hakura wlh.
Ba kya son zama likita ko Lawyer,teacher etc ? Shuru tayi tace ni Soja nake son zama Sabo da na rama dukan da aka yi min yau ko Roadsafety wlh duk sai na kama motocin Malaman nan da sauran duk Wanda ya Bata min,Murmushi yayi tare da mika mata Wata ledar abinci da ya yi mata take away yace jeki to class,Murna ta lullubeta wannan kadai ya yaye mata bakin cikinta,godiya tayi tana murmushi, ko kallonta baiyi ba yace Farhan ne saurayinki yace a kawo miki, Allah sarki kayi Masa godiya ko ka bani number dinsa kawai pls? Zai baki da kansa nan gaba tafi class bye suka ja motocinsa, Class taje ta baje abinta kowa na kallo babu Wanda ta kula tunda Bata da kawaye haka ta cinye Namanta da sauran tarkacen ciye ciye dana sha,Students ana ta hadiyar yawu.

Bayan 1wk kuwa Latifa lallabawa tayi ajin su Shukura lokacin ta fita anyi Break ta Saci Dubu biyar wata a cikin jaka ta zuge bag din Shukura ta saka mata dubu biyar inda baza ta gani ba ta bar class din.
Bayan an dawo daga Break yarinya ta nemi dubu biyar finta ta rasa kuma aikenta akayi a gidansu after schl Zata kaiwa telansu,ta sanar a class duk Wanda ya dauki kudinta ya dawo mata Dashi class kowa yace bai dauka ba,aka ce ayi caje aka fara caje jiki da jaka a gaban Malamin da ya shigo shima yana taimakawa,sai aka samo dubu biyar cas a jakar Shukura aka fara ihu Thief...Thief.... aka fito da Shukura Waje Malamin yayi mata bulala goma yace dama yayarta tace barauniya ce ita haka a gida ma take sace kudin iyayenta,Hakan ma wai ya raga mata Sabo da New Student ce,Shukura Bata saba ba ta barke da kuka tana cewa wlh Sharri aka yi mata amma ba wanda ya saurareta sai ma dariya da yan Class suke mata,ita kanta Bata San waye ya kulla mata sharri haka ba, amma ta barwa Allah, Tun daga wannan rana Shukura ta daina zuwa late,ta fara taka tsan tsan da jakarta Sabo da kar a kuma kala mata sharri,bata kula kowa daga mata har maza Bata kulasu Sabo da Sun Bata Haushi da suka kala mata sata,duk Wasu doka na schl ta kiyayesu sai wani Masifar kokari da take tashen yi ba a magana turancinta kullum gyaruwa yakeyi ga kyau ga diri data kara.

Latifa ta Sanarwa Niima komai da Shukura ke ciki,Niima tace tana da saurin fushi kiyi mata wulakancin da Zata ji Haushi kuyi kokawa kice ta dakeki a gyara ta a schl din.
Latifa yau a dai dai gate ta jira Shukura da Sassafe ,Shukura Bata San da mutum ba tadan bigeta,Latifa taci kwalar Shukura ta fara zagin iyayenta,Shukura an zagar mata Iyaye yau ta gaji da hakuri, tunda tasan su Niima basu da mutunci ta daina shiga sabgarsu kuma kawar Latifa ta zago ta bawa Shukura labarin tuggun da suka hada mata iri iri, Shi yasa Shukura tayi zuciya suka fara kokawa ta zaro biro kawai ta cakawa Latifa a gefen kanta Wajen kawai ya tsille jini ya fara tsartuwa ta kafar,Nan fa schl ta hargitse malamai suka yo kansu tare da cewa a rufe gate kar kowa ya fita,Shukura ta kama katanga ta dane ta haure ta arce sai gida,Latifa kuma akayi asibiti da ita,Niima har taje tana ta kuka,Ahleef ma an fada masa,yana zuwa ya samu ba wata matsala har anyi wa wajen dinki an sallamesu,Gidan ya wuce Direct ya duba Latifa ta tsara masa karya da gaskiya amma yasan Sune da Laifi tunda yaga Latifa a schl din yasan Shukura zasu tsokana dole,Bai ce komai ba ya nufi part din Umma Saudatu kai tsaye yayi Sallama Shukura tana Sallar La'asar, Baba kuwa yana masallaci,Umma a zaune take tana gyara Garin Alkamar da zatayi tuwo.

gaisawa sukayi Umma tace kazo Jin rigimar da kanwarka ta kwaso ko,Murmushi yayi yace ai Bata ji ne Umma,Umma tace ta bani labarin komai gaskiya sune da laifi bari ta idar da Sallah tayi maka bayani 'yata Bata da laifi, suna hira sama sama Shukura ta Idar Umma kuma ta wuce kitchen.
gabansa Shukura ta zauna kasan kafafunsa ta kalleshi fuskarsa ba Rahma,a hankali ta gaisheshi,Me ya hadaku da Latifa dama fada na kaiki ki koya ? Shukura Bata Ce komai ba sai Shirin Kuka ma zatayi da kyar ta kwashe komai ta sanar masa har yanda Niima take bada kudi tana zuga malamai da Latifa,Ahleef ya jinjina lamarin,tace ka yarda dani Yaya bari na nuna ma sheda ka gani ta zare Hijab dinta abin mamaki sai yaga t-shirt dinsa a jikinta ta daura Skert a kasa,Damtsemta ya kalla ko ina shatin bulala,rigar ta janye kadan tare da juya baya tace kalla bayanta rudu rudu shima,Hijab dinta ta maida tace sannan kuma Last nazo gate taci kwalata ya ake so nayi,taya bazan tsille mata kai ba ko yar uban wace wlh Bata Isa ba,na baya ma hakuri nayi Sabo da Dan Adam ba komai za ayi maka ba kace lallai sai ka rama dole kayi hakuri.
Lallai sai yau Ahleef yasan Shukura tana da hankali ashe.

Kamar bazai ce komai ba yace gaskiya idan Saurayinki yaji Bazai ji dadi ba ana Dukar masa mata haka,Shukura ta turo baki cike da Shagwaba dan Allah Yaya ni ka daina ta furta tare da fadawa saman kujera kusa da shi,Kansa ya dauke daya barin tace juyo mu gani Sir, yaki juyowa ta koma can barin, gwiwoyinta suna kasa ta kifa cikinta saman kujera tana so wai dole sai tagani yana dariya ya daina fushi da ita,kansa ya Maida can barin,ta Mike tsaye tana dire diren kafafu wai sai ya tsaya shi kuma yaki yarda,hannayenta tasa biyu ta rike kan kam a saitin fuskarta tace to muga hakoranka,ido ya kafeta dashi tare da bude mata kuwa yana murmushi tace irin na Umma sai kuma taji kunyarsa ta.sakeshi da sauri,Umma ce ta kwala mata kira a kitchen,tana shiga tace haka ake saukar bako ? Tire ta nuna mata kai masa,a gabansa ta ajiye tire tare da zama a kasa kamar ita Zata ci,ta tsiyaya masa lemo ta Mika masa yace bazai sha ba shi ruwa zai sha,Shukura tace ni kuwa ina sha ta shanye lemon, ta bashi ruwa,Abincin kuma jullop Spaghetti ce taji hadi yace ta zuba masa dama yunwa yake ji, Umma fa ta gama yadda Shukura da Ahleef yan uwa ne sai ta bar musu Part din Gaba daya su samu suyi hirar zumunci,Ahleef hankali kwance yake cin abincinsa me dadi sosai,Shukura tana zaune kusa dashi ta zura masa ido kawai birgeta yakeyi a duniya ga komai nasa me kyau ne,shi kuwa yasan tana kallonsa kawai muryarsa taji yace Saurayinki zaki na kalla haka yace Sunday ma zaizo zance gobe kenan fa.

share zancen tayi tace amma ranar Monday kai zaka kaini schl din ? Indai naje ni kadai to kawai ku tanaji makara da likkafani, gaskiya Makarantun Birni basu da Imani a kauye kuwa ni kadai ce me kokari sai abinda nace,amma a nan shegu sai kokari kowa me kokari nice jakar ajinmu fa Yaya, dariya yayi yace jaka kuma ? Tace bakar ma kuwa irin marar mangala din nan, sai dai kayi hakuri nasan ta karshe zanzo yo wannan manyan kwari haka.
murmushinsa ya yi me tsada tare da cewa da bulala zanzo ranar karbar result kuwa,Zama tayi a gabansa kamar me daukan darasi tace kai yan gayu ne a makarantar mu kaga yanda suke tafiya wani dos dos ga daukan wanka,Kema sai ki koya ai,Ina nan zan fara kuwa amma ba a schl ba, yanzu Yaya inda kake me kyau haka ai sai me kyau akwai wata a class Dinmu sunanta Islam kyakyawa ce da zaka yarda da ka aureta kun dace,da ta ganka kazo wajena nace musu yayana ne, Sabo da Sonka fa yanzu take kulani kawata ce sosai har karatu take koya min Sabo da Sonka tayi ta siya min abubuwa,kuma tace gidansu Auren wuri ake musu kaga da tana gama secondary schl sai ka aureta wlh tana sonka tace dan Allah na hadaku,Ina da budurwa fa ni kin Sani karma ki soma a kai kasuwa,karki kuskura ki kara yi min zancen wata Mind ur Business bana sonta ya furta a fusace,Shukura tace Islam din ? Tsaki yaja ya mike tare da cewa Sai Sunday gobe zamu zo da Farhan zasu gaisa da Umma,har zai fita Shukura tace Yaya ga abu kamar ya makalema a hakori kawo na cire ma, Toothpick ta dauko,shi kuma ya zauna,tace mu gani ya bude kyawawan hakoransa tasa tsinken ta cire abin nama tare da cewa kalla ? kamar wani danta tana kula dashi,Zai Mike tace baka taje gashinka da gemunba, dariya yayi kadan yace dama ido kike sa min Ko,ya zaro Cumb dinsa da wani dan mitsitsin turaren gemu na gashi,da gudu ta dauko masa mudubi karami ta karasa masa a fuska yana kallo ya taje gashin da gemun tare da shafa masa turare yana sheki sannan ta matsar da mudubin tace Allah kaika lfy,yace Ameen ya wuce abinsa ba tare da ya kalle ta ba.

Zahra kuma kanwar Hafcy Babansu yace dole su jira har Abba ya dawo daga tafiya amma dole cikin su biyu wacce Ahleef yake so to ita za a hada su aure,Nan Suka fada neman mafita gwara tun yanzu ko wacce ta shigar da kanta gareshi Ko zai zabe ta, Hafcy tayi bincike sai da tasan yanda tayi ta nemi Niima suka zama frnds Sabo da ta hanyar Niima Zata dinga ganin Ahleef,sannan Niima ita kuma ta fada mata Ahleef ba a San asalinsa ba

1 Comments On JIN DADI SABO
avatar
mahamane-noura

2 years ago

Reply

Asalama alaikum, dan Allah yane ake sauke littafin akan waya

Please Login or Register in order to submit comment