Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naji zancen wurin Abbanku sai ranka ya baci.

Momee ya kyale kawai ya fita da sauri bai zarce ko ina ba sai wajen su Saudatu da Baba ya sanar musu komai,Umma ta shafa sumarsa tare da cewa yanzu Sun fimu iko da kai kayi halacci kayi musu biyayya da shi kadai zaka saka musu sannan ka dage da addua kawai.
Godiya yayi musu ya wuce wajen Farhan tare da bashi labarin komai Farhan ma nasiha yayi masa kan yayi biyayya kawai,amma banji dadi ba a rasa wacce za a baka sai Nafeesa yarinyar da kullum tana titi yau wannan kasa gobe ma waccan kasa tana barikinta Momee batayi tunani ba,yanzu zancen da nake maka saurayinta wani dan china ya dauketa Sun tafi Korea idan ta dawo kuma ta fake da Business,Wlh ni ko Bed bazan iya hadawa da ita ba cewar Ahleef, Farhan sai dariya yake masa.bayan kwana biyu Ahleef ya tambayi securities na Momee wanne state suka kaita ? Amma sai suka ki fada Momee ta hanasu wai,dole ya hakura ya koma addua.

Ahleef bai taba tunanin haka ya damu da Shukura sai yanzu, ba wai So ba kawai birgeshi takeyi sannan da tausayinta da yake ji shi yasa ma ya shiga wani hali a kanta,kwanaki kadan kowa yasan Alheef yana da damuwa,Komai gagararsa yake yi har Office ma komai a hanun Secretary ya barshi,baya murmushi Ko Kadan ya gama fita a hayyacinsa,bashi da aiki sai tunanin Shukuransa yana tuna yanda suka zauna tare gida daya tana masa kuruciya iri iri,haka ma yake tuna murmushinta tare da dariyarta,bata fushi Sam,watarana idan ya tuna yanzu tana can maybe rayuwarta ma ta lalace har kwalla yakeyi,ga Auren Nafeesa da Momee tace dole ne domin Abba har sunje sunyi tambaya tare da sa ranar aure nan da 1mnths,Abba baiyi da ka ba saida ya tambayi Ahleef idan baya so Baza ayi masa dole ba, ganin Momee tana so kawai sai yace yana so,amma Momee anan tayi son kai,lokacin da Niima taki yarda da Auren Ahleef ai Bata yi mata dole ba, gashi kullum a kawo samari take amma bata ce komai ba, shi kuma Ahleef ganin tun yana jariri ta raineshi tasan bazai mata musu ba tunda bashi da gata sai su shine ta nuna son kai akan Shukura tayi fada Da yaranta,Tana son Ahleef amma akan Shukura ta jefashi wani hali kuma babu alamar fasawa.

Hafcy kuma sunji Ahleef zaiyi aure bakin ciki ba Wanda basuyi ba karshe ko wacce tace Baza ta hakura ba sai Sun tabbatar an fasa wannan aure sai Sun tarwatsa komai,Mubaraq bai samu shiga wajen Niima ba, wani yaro take so Wanda da Auren wuri tayi sai ta haifi kamarsa.

Baba da Umma suna zamansu lfy da Momee ba wata matsala tana kyautata musu sunyi kyau tare da murjewa. Sunji ba dadi da za ayiwa Ahleef Auren dole amma basu da iko a kansa dole sai dai kallo gudun kar su yi butulci shi yasa suka sa ido.
Amarya Nafeesa kuwa tunda taji Ahleef Zata aura take sheka uban murna kamar ta zunguro lokacin, Ango ko zance baije ba baibi ta kanta ba.

Makarantar su Shukura sunji labarin barin gida da tayi Latifa ta Baza cewar ta tafi yawon karuwanci.
Kamar Kullum Ahleef kwance yake saman lafiyayyan Bed dinsa yana faman tunanin Shukura bai ma san ya fara hawaye ba, Momee ce ta turo kofar a hankali,da sauri ya goge ido tare da fara baccin karya,Momee ta juya tuna ninta Bacci yakeyi.Tana barin dakin yaci gaba da tunaninsa wanda kullum karuwa yakeyi baya sauki,Harkar bikinsa kuwa Farhan da sauran frnds su suke komai.

Shukura tunda arna suka kifota da Adduna Bata tsaya ba sai da taje jikin wani gida shima a kauyen,Wani dattijon iyamuri yayi mata turanci Hey! Young Lady where are you going ? Whats Happening ? Shukura tana haki tace i need a help,wasu ne suka saceta amma ta manta inane garinsu,mutumin yace ta suje gidansu yana da mata sai ta zauna zuwa kwana biyu dodon tsafinsu zai fadi garinsu,Matarma me kirki ce ta bawa Shukura wajen kwana da abinci kalar nasu,tace amma da Snail tayi miyar,Shukura tace ko bera ne a ciki Zata ci haka bare wani snail, dare ya tsala gari tsit Mutumin ya sadada a hankali ya kwanta a bayan Shukura kamar matarsa yana mata goge,tana farkawa ta tsala ihu yatashi a guje zai koma wajen matarsa,matar kuma taji ihu ta fito a guje sukayi karo da kai gwaraf,sai Ihu suka koma daki Gaba daya,matar dama tasan halin mijinta, Washe gari kuwa da sassafe matar tace Shukura ta bar mata gida Zata kwace mata miji.
tafiya Shukura ta dingayi a hanya har ta hadu da wani matashi tace ya taimaketa ita yar arewa ce, nan take ya kaita inda Zata hau mota,Ba Bata lokaci ya sata a motar Anambra City tare da fada mata yanda zatayi,ya biya mata kudin motar sannan ya bata 3k,ta dinga zuba masa gidiya sannan suka wuce tana mamakin ashe a ko ina akwai mutanen kirki.

Me taxi ne ya sata a Motar Kaduna state da kyar ma suka dauketa kudinta bai kai ba, wani bahaushe dan cirani Wanda shima Kaduna zaije shine ya cika mata kudin motar.
sun sha tafiya sai cikin dare suka sauka a Kaduna lfy,Matashin yace to shifa kauye zaije a kauye yake,Shukura tace dan Allah ya taimaka ya tafi da ita gidansu can kauyen kaduna saceta akayi kafin ta gane gidansu sai ta tafi,Matashin yace ba damuwa muje,taji dadi tace ya sunanka ? Yace Jamilu ke kuma fa ? Shukura ta furta sannan suka shiga motar kauyen.

Jamilu neman kudi yake zuwa Anambra dan cirani ne,iyayensa Sun rasu kakanninsa suna raye su suka rikeshi har ya girma suke tare gida daya,baiyi karatu ba Sabo da rashin Gata shi yasa yake tafiya neman kudi.
Dattijon me Suna Malam Hari zaune yake kusa da matarsa Rahina suna hira a tsakar gida sai ga Jamilu da Shukura Sun shigo da sallama,Ko zama Jamilu baiyi ba ya sanar dasu abinda Shukura ta fada masa a kanta,babu wani damuwa suka tarbeta a mutunce,Tun Bata saba dasu ba har suka saba da juna ci sha da komai suke Bata duk da cewar na kauye ne Shukura Bata Jin dadinsa Sabo da ita ko a kauyensu ma cimarta dabance, sati daya Kakan Jamilu wato Hari yace tunda har tana iya tuna garinsu a kauyen Jos to zai Bata dubu uku kudin mota,baza su iya riketa ba dan Adam abin tsoro ne,Rahina ma tace wannan gaskiya ne ta tafi wurin danginta amma a kyaleta zuwa sati biyu ko uku.

Sati biyu tsakani Shukura ta koma Normal ta tuna Ahleef da Abuja da komai ma,ta dawo Hayyacinta,matsalarta daya tunanin Ahleef daya addabi ranta ba dare ba rana,yanzu ta tabbata Son Ahleef Ya kamata sosai,tun bata yarda ba har ta yarda,tana tsaye cikin daddazon mutane a kauyen mata da maza ana wasannin gargajiya,sai kallonta akeyi a kauyen anga kyakyawa,tunawa tayi yau rabonta da Abuja 3wks kenan karfa Ahleef yaje ya manta da ita ya auri wata,kara ta saki kowa sai da ya firgita ana kallonta ta dafe bakinta da hannu tare da tsayawa cak,sai ji akayi tace Ahleef zai so wata,sai ta fara falfala sauri kafin kace me ta koma gidansu Su Jamilu tace Zata tafi ita gida, Rahina tace ta bari sai gobe amma fafur Shukura tace tafiya zatayi, kakan Jamilu ma ya hanata tafiya yace ta bari wani satin zai kaita Abuja da kansa,ba damar tayi musu kuka kawai ta fashe musu dashi.Shukura Bata san ma bikin Ahleef saura kwana bakwai ba.

Kullum Shukura kuka takeyi ba ji ba gani Bata iya cin komai ita sai ta tafi tun Su Jamilu Suna Bata baki har suka kyaleta,Malam yace 'yar nan kudi nake jira na samu sai mu tafi,Cikin sheshekar kuka Shukura tace ni a kyaleni a gani ko ba sisi sai na koma Abuja ko da Allazi wahidin ne,dariya su kaka suka dinga yi, Shukura tace kaka wajen mijin da zan aura fa zanje, So kuke yayi sabuwar budurwa ina nan,Rahina tace oh yaran yanzu ba kunya,Shukura tace yo ke kaka me kuka iya a soyayya, Kin taba zama kamar yini daya kinyi tunanin Malam Hari? Rahina tace mu da ake mana Auren zumunci tun muna yara ina muka San wani tunani yar nan,.

Shukura tace tab wlh an cuceku ni kuwa ina yin tunaninsa kullum kullum,harfa tunaninsa nakeyi yana min dariya,Malam yace ya sunansa yar nan ? Ahleef sunan larabawa ne baku ganshi ba kyakyawa cewar Shukura, to wai kai malam ka taba siyawa Kaka kayan dadi ? Malam yace bazan iya tunawa ba, ni kuwa kullum sai ya siya min,muje yawo dan Allah kaka mu tafi gobe,Kaka yace sai kudi sunzo,Shukura tace sai kace mutum haka zasu zo su sameka da kafarsu?

Washe gari da safe Shukura dasu Malam suna zaune ta kalli buhunan masara,gero,dawa etc tace kaka kuna da wannan amma bakwa cin dadi,ku siyar dasu mana mu a yanka mana zabbi sai ku zauna kullum kuna cin tuwo,Kaka yace sarkin kwadayi kenan ke dole sai anji dadi, ba wai kullum ba Kaka amma idan akwai sai aci,idan babu an san babu sai a hakura, Kuka ta kara fashewa dashi sai an siyar da buhun masara Sun tafi Abuja,Hari da son kudi yace Baza ta sabu ba bindiga a ruwa, Shukura tace to bani bashi muje Ahleef zai biya me kudi ne,Malam yace bada ni ba yar nan. Jamilu yana son Shukura amma yasan tafi karfinsa matar manya ce shi yasa ma bai damu kansa ba.

Ahleef kuwa ya rame ya kara haske kullum tunanin Shukura yakeyi shine dalilin da yasa aka ce ba party ba komai kawai aure za a daura a kai Amarya,bangaren Amare ma sunyi shiri tsab an kashe kudi duk da cewar ango bai taba zuwa zance ba,itace take binsa Office baya saurarta ko kallon arziki Bata samu,Amarya kuma da iyayenta laifin Momee suke gani,Nafeesa taci alwashin tana Auren Ahleef Zata mallakeshi sai abinda tace,Momee sai ta koma abin kyama wajen Ahleef.
Umma da Baba su nasiha da addua kawai sukewa Ahleef.

Kwanci tashi yau ne daurin Auren Ahleef 12pm za a daura, mutane kasa kasa suke sauka,yaune kuma Baba, Jamilu tare da Shukura suka shiga motar dake tashi 7:30am na safe,mota ta tashi Sun fara tafiya duk inda Shukura taga mutane sai ta leko da kanta ta Window din motar ta kwala magana da karfi Sai Abuja ko da kafar katako Masu dariya suyi,murna takeyi kamar zatayi hauka.11:30am suna Abuja Sun shiga taxi tiryan tiryan Shukura ta fadi Adress gidan Momee a kofar gidan ta hango mazaje sunsha wankan Shadda da alama biki akeyi gabanta ya fadi,Baba ta hango ya dau wanka ya fito,da gudu Shukura ta karasa wajensa ta kyale Jamilu da kaka a mota,Baba ya dinga murna Shukura ta dawo,Shukura tace Baba ina yaya ? a takaice Baba ya Bata labarin komai,Shukura sai kuka,cikin kuka ta dan bawa Baba labarin komai na saceta da akayi.

Baba kaga Wanda suka dawo dani dan Allah shiga mota Baba muje wajen daurin Auren, Baba yace yar nan kina mace ina ke ina zuwa wajen daurin aure,Baza ka gane ba Baba akwai matsala babba Baba dole muje kafin a daura aure,haka Shukura tayiwa Baba wayo shima ya gigice ya fada motarsu taxi suka bi bayan motar su Salman, Malam da Jamilu sai kallon masu kudi sukeyi ashe Shukura gaskiya ta fada masu kudi ne Ahleef.

can Nesa sukayi parking,Shukura so take kawai taga Ahleef amma mutane sunyi yawa,har an fara khudubar daurin aure kowa naji,Shukura ta runtse ido tana hawaye da addua, Baba ma da Kaka har Jamilu sun karasa wajen,Ahleef da dasu Abba suna cikin masallacin,Baban Nafeesa da yan uwansu ne suka ce a dakata kar Wanda ya daura aure,Shuru akayi ana sauraronsu,Yace sunyi bincike an sanar dasu Ahleef baida asali, bashi da iyaye a gidan raino aka dauko shi,shi yasa suka fasa aurawa Niima shi dake yarsu ce shine aka kulla za a cucesu shine za suce yarsu ta aureshi to Allah ya taimakesu ba'a daura ba, kuma Baza ayi da tasu ba karshe yace zamu dawo da kaya tare da kudade da aka kawo amma aure a daura da yar wani ba tasu ba.

A bin Haushin ga yan jarida haka Abba cikin bacin rai ya Mike ya bada tarihinsu dana Ahleef har na Saudatu da Baba,kowa sai da ya tausaya gashi anyi tonon silili a bainar mutane,su kansu iyayen Nafeesa sai jiki yayi sanyi suka ce to Sun yarda a daura,Abba ya rantse sau uku bazai daura ba wlh shima bazai daura da Ahleef ba su bawa yarsu me asali ba dai Ahleef ba, Shukura tana Jin komai tar a kunnenta tsalle ta buga tare da cewa yessss Alhmdllh. Da kanta ta fara keta dubban mazaje ana kallon ikon Allah ta Isa har inda Baba, Kaka da Jamilu suke da sauri ta jawosu gefe can tace Baba da Kaka ku zama waliyai na dan Allah kuce a daura da Shukura Muhammad, Wani farin ciki ya lullube Baba,yace yan uwanki fa ? Ba matsala ? Cike da kunya tace Baba kun San tarihina fa, idan komai ya lafa zamuje kauyen.

Da sauri Su Baba suka rankaya tare da kaka suka kirawo Abba gefe suka labarta masa komai murna wajen Abba ba a magana,yace ayiwa Shukura godiya ta fitar dasu kunya,farko Niima ce ta tozarta su aka fasa yau ma again kai Alhmdllh.Abba ne yace aci Gaba da Khuduba,Ahleef dai wani takaici ne ya kara ziyartarsa tunaninsa daidaitawa akayi da iyayen Nafeesa za a daura auren,idonsa yayi jajir Sabo da bacin rai,Baba da Kaka sune na Shukura,Abba da Yayan Momee kuma na Ahleef, nan take aka Naura Auren Ahleef da Shukura kan Sadaki dubu dari,Abba shi ya biya sadaki,Maroka Masu kade kade ana ta yi.

Ana ta kara Sanarwa da daurin aure ya dauru,mutane Sun sheda, Shukura saida tayi Sujjada ta godewa Allah,sannan ta karbi biro hannun wani ta rubuta short note a jikin yagin kwalin taba data tsinta a kasa.
Baba ka fadawa Ahleef da sauran Masu sona na tafi gidan kawata a Apo qrts cikin Abuja ina nan zan dawo gobe.wani saurayi ta bawa tace idan yaga Baba ko Ahleef ango ko Abba ya bashi,taxi ta shiga tayi tafiyarta cike da farin ciki.

Ahleef kuwa yaji dadin daura aure da Shukura duk da ba soyayya Suke ba,amma taya za a daura aure kuma Sun San Shukura ta bace ? Amma kuma wani irin farin ciki yake ji marar misaltuwa.Farhan da sauran abokai ma haka,labari tuni ya kai kunnen Momee amma taji haushi dole sai da aka daura da jarababba Shukura Ai gwara a kyale Ahleef ba aure akan a bashi Shukura.

Su Niima,Hafcy,Islam etc basu ji dadin lamarin ba, Zahra kuwa tace sai ta raba Auren sannu a hankali.
kowa da abinda yake furtawa har akayi hotuna da komai mutane suka watse sai ango da abokanansa shakikai suna guess house dinsa ana ta tsokanarsa musamamman da Baba ya bashi dan Note din da Shukura ta rubuta.Kaka da Jamilu an kaisu masauki can gidansu Farhan aka kaisu Sabo da matsalar Momee.

Angwaye Suna zaune sai tsokanar Ahleef Sukeyi dan gatan Amarya da kanta tazo wajen ta bada Umarni a daura da ita,Shukura ta birge mutane ta fitar da ango kunya tayi halacci ana ta mata addua,Nafeesa kusan haukacewa tayi da taji ba da ita aka daura ba, laifin iyayenta take gani,fushi tayi tace wlh kuma baraki yanzu ta soma tunda su suka jawo ba a daura da ita ba.

Su Niima Dasu Momee Sai tuge kwalliyarsu sukayi tunda da shukura aka daura to baza suyi kwalliyar bikin ba.

Shukura kuma gidan wata Fauziyya yar makarantarsu taje Suna dan shiri da ita kuma Fauziyya nutsatsiyace ga kirki da wayewa gata ta Iya kwalliya, abinda yasa Shukura taje can Sabo da Momee sannan tafi so ango ya ganta Amarya kamar kowacce.
Ango ya rude kawai shi Shukura yake son gani,ba wai dan tana Amaryarsa ba Dan ya dade bai ganta ba, kuma yana so yaji ina aka kaita wacce rayuwa ta tsinci kanta,yana son ganin lafiyarta.










AsmaBaffa
[7/22, 1:13 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO






26-30








Official






By
AsmaBaffa






JANNAT,MAMAN MEENAT, QUEEN KK da BBY LUV
Page nakune.








Fauziyya ta damu Shukura da zancen ina kika tafi ana ta cewa karuwanci kika tafi tafi,Shukura tace nasan Latifa ce ta fada bani da lokacin wannan ni yanzu ma da kika Sani Amarya ce wlh so nake ki karbo min rancen Dubu talatin tunda gidanku Masu kudi ne gobe zan baki, so nake na fito a amarya ta kamar kowacce,mamaki Fauziyya tayi ace kamar yar Shukura da aure abin mamaki,a fili tace to Mama ta bani dubu hamsim zan kai mata bank,zan cire talatin ciki na baki zuwa gobe lallai ki karbo wurin ango a sa mata kudinta ba tare da ta gane ba,Shukura tace Inshaallah,yanzu ta Ina za a fara yamma nayi,gidan gyaran jiki zamuje Masu sauki ayi miki na rana daya Kafin ango yazo ya bada kudin na 3mnths,Fauziyya Mamansu ta fadawa komai na iya bikin Shukura,Mama tace kuje gidan sady me gyara tayi mata kyauta ni zan biya,da murna suka tafi driver ya kaisu,Sady tace yanzu za ayi miki gobe ma haka,idan Miji kuma ya yarda sai kiyi ta zuwa har tsawon 2-3mths,kaf jikinta aka yiwa gyaran, sai kuma gashinta yasha uban gyara sai kyalli da sheki.

Lalle aka Zana mata na Amare,da yake Fara ce sai kaji kamar ka saceta tsabar kyau,sai 8pm suka gama sannan,Maman Fauziyya tace saura tsumi kuje gidan Hajiya Mariya itace me tsuma Amare yanda ya dace,basu koma gida ba sai da suka je karbo maganin kala kala Wanda ya dace da Amarya wacce bata taba aure ba tayi amfani dasu,a gajiye suka koma gida, Maman Fauziyya tausayin Shukura takeyi shi yasa bata bari ta kashe kudinta ba albarkacin kawar yarta ce yasa tayi mata,Sabo da haka sai kawai suka siyo ready Made wata Riga ta dubu goma wata yar ubansu,Takalmi da jaka,Sai lace da suka siyo dan dubu goma suka bawa tela Emergency zasu karba gobe da safe komai Sun tsarashi Ahleef ji yake kamar ya zunguro gobe tayi yaga Shukura, da kyar bacci ya saceshi sabo da Murna.

Washe gari da sassafe suka koma gyaran jiki aka yi mata etc.
Sai 5pm Shukura zata ta nemi inda Ahleef yake ba tare da ta koma gidan Momee ba.
Ahleef da wuri ya tashi yana ta duba agogo ko zaiga Shukura,har Bakin gate yake fitowa ya tsaya amma Shuru ya koma Bedroom ta Window kawai yake kalon kofar har 2pm ta wuce sunyi Sallah ana hira amma banda Ahleef ya kasa cin abinci,4pm yana yin Sallah ya fada toilet yayi wanka yasa wata Shadda fara kar dinkin zamani,ba karamin kyau yayi ba sumarsa tasha gyara kamshi kawai yakeyi da sheki,yau harda coka hula baka a gaban goshi,yasa Bakin takalmi,kowa yasan ba karya ya hadu karshen karshe,da sauri ya sakko kasa da niyyar zuwa ya binciko Shukura duk inda take,Farhan da sauran Frnds suka kulle kofar da key zasu tsokane shi,ai kuwa ya dinga masifa suka ki budewa har 5:44pm sannan suka bude suna masa dariya,tsaki yaja tare da ficewa.

Yana fitowa inda motocinsu suke,Sai ga Fauziyya taci uban wanka dake itama me kyau ce fara amma ba kar ba, Sai wata budurwa makwaftan su Fauziyya itama tasha wanka tace sai ta bisu taga bikin Masu kyau da kudi Zeenat kenan, Shukura ce ke binsu a baya tasha doguwar rigar material black and White kamar tasan Ahleef shima Black and White yasa, dinkin irin na Amare ba karamin kyau ta tsula ba, Bata Sa gogoro ba, Dan siririn gyalen Rigar sharara ta yana a saman kanta, ba kowa zai gane Shukura ba zai rantse bakuwar balarabiya ce ko yar India.
takalminta me dan tudu black dai dai tana tafiya dos dos har pose din ta black,Ahleef kallo daya ya mata ya gane abarsa.

Tsayawa yayi jikin motar tare da kafeta da kallo kana ya sakar mata murmushi me kayatarwa,Shukura kunya ta kamata kawai sai ta sadda kai kasa tana tafiya,Su Fauziyya dariya ma ta basu,wani farin ciki ya lullubesu gaba daya kowannensu yana ji kamar ya hadiya dan uwansa,Dago kanta tayi a hankali tana murmushi idanunsu suka sarke da juna,kafin ta karaso shima ya taka yaje har inda take,Su Fauziyya suka gaisar da shi ya amsa,yace su dan jirashi a garden,hannun Shukura ya rike kawai ya jata suka nufi daya Part din,Shukura kuma cewa take Yaya ayi party mu gaskiya,yace yau da kafa daya zanyi rawa cewar Ahleef,dariya tayi tare da cewa kana rawa da kafa daya ni kuma ina dariya da hakori daya,muje muyi wata magana ya furta.

a palo ya zauna saman kujera itama ta samu one Seater, bani lbr me ya faru Bayan sun saceki ? Tiryan tiryan ta bashi labarin komai shi kuma ya kafeta da ido,zuciyarsa cike da tausayinta,waya ya zaro tare da kiran Abba ya sanar masa ya za ayi da Amarya kar Momee ta bada matsala, Abba yace karka damu dole za a kaita gidanka yanzu so nake jibi mu shirya da kai tare da Shukura, Baba da Ummanka muje kauyen yarinyar a sanar musu sannan ta zauna kamar 2wks sai danginta su kawota gidanka kamar ko wacce Amarya,Momee fa Abba ? Kyaleta wannan zanyi maganinta karka damu,bayan ya gama wayar Shukura tayi bacci ashe,a hankali ya taka zuwa gabanta yana kare mata kallo tun daga sama zuwa kasa,lallenta ne ya tafi da hankalinsa ya shiga kallo yana yabawa a zuciyarsa,Kasa daurewa yayi har saida ya rike hannunta yana shafawa,rigarta ya yaye kadan ya shiga kallon Zanen lallen dake kafarta,yafi 10mnt yana kallonta farin ciki yana ratsashi.

Farhan ya kira a waya yaje wajen su Fauziyya ya kaisu gida wajen Umma, shi anjima zai taho da Shukura ta samesu a can.
Yasa an masa take away na abinci yasan tana tashi sai tace abinci Zata ci,sai wuraren magrib ta farka lokacin Ahleef tuni Sun fita Masallaci,bakinta ta wanke yau Bata sallah shi yasa ta zauna tana jiran Ango ya dawo ita kuma ta tafi,
Ahleef ya dan jima sannan ya dawo direct wurin Shukura ya nufa,a Zaune ya isketa,tana ganin ya shigo tace Yaya yunwa,ba tare da yayi magana ba ya nuna mata ledar abunci,a nutse ta zauna taci abinta a hankali har ta gama yana kallonta kasa kasa,Toilet ta shiga tare da wanke hannayenta ta gyara kwalliyarta sannan ta fito,muje na kaiki wurin kawayenki can Wurin Umma suke,bata yi musu ba suka jera kamar ka sace su, kayan jikinsu kamar anko sukayi dama,Escort dinsa ne da motoci Sun kai takwas suka shiga,Ango da Amarya suna Bayan mota Sun lafe abinsu,Sauran Frnds nasa da suka ga Shukura sai mamaki suke dama haka take me kyau,lallai Ahleef yayi dace.

Parking sukayi yan biki hankalin kowa ya koma kansu,Part din Momee suka fara zuwa,tana tsakiya cikin yan uwanta suna hira taga Ahleef tare da Shukura,Shukura har kasa ta gaidasu,amma Momee Bata amsa ba sai ma harara da take aikawa Shukura,Ahleef yana gaishe ta sai

1 Comments On JIN DADI SABO
avatar
mahamane-noura

2 years ago

Reply

Asalama alaikum, dan Allah yane ake sauke littafin akan waya

Please Login or Register in order to submit comment