Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

bude kofar a hankali kawai taji Muryar Umma Ina Zaki je? Ba tare da ta juyo ba ta rumtse Ido sannan ta juyo cike da kunya ta fara kame kame ah...ahm....uhmm...can..can part din zanje dauko wasu Kaya,to koma ki kwanta ba inda zakije ai duk na San plan dinku,Ni zakuyiwa wayo,Sum sum Shukura ta koma Bedroom sannan ta Kira Ahleef a waya ta sanar Masa Umma ta kamata,Ahleef yace to zanzo Ni anjima,karfa a kamamu cewar Shukura,wayar ya datse,ita Kuma Umma tuni ta garkame kofar Palon da key Kuma ta bar key din ajiki yanda baza a iya budewa ba,Ahleef yazo yayi yayi kofa taki buduwa,yasa spare key shima yaji akwai wani a jiki.

Dole ya hakura ya koma part dinsu,Ya sanarwa da Shukura ta waya, Dole suka hakura yau.
Duk yanda Ahleef yaso suyiwa Umma wayo abin yaci tura,gashi har Shukura ta kusa arbain,Yana Murna Umma tace to Kauyensu zamuje sannan mu wuce Niger idan mun dawo daga ziyarar ganin dangi sai ta koma part dinku,takaici ya Hana Ahleef magana, Shukura Kuma sai dariya take Masa a boye.

Barin gidan yayi sai Gidan Momee,Momee ta ganshi hankali tashe, da sauri tace lfy son? Momee pls kije kiwa Umma fada mutum da Matarsa ace baza ta zauna a gidanta ba,dakin mijinta yafi karfinta sai can wurin Umma,Dan Allah kiyi magana Ko na bar kasar nan,Dariya Momee tayi sannan tace nasan Halinka Ahleef kayi hakuri Haka akewa masu jego,Akan Mace har yaji zakayi Haka me yayi zafi za a dawo ma da matarka,Takurawa Momee yayi sai da ta shirya ya kaita wajen Umma,Umma tace au karata ka Kai wajen Momeen taka,Umma da Momee sukayi magana Lallai baza a bashi Shukura ba sai tayi arbain,Ahleef tunaninsa Momee ta gyara komai,Amma sai yaga ba abinda ya faru.

Yau tunda ya shigo da dare Bayan Isha yaki tafiya jariri Yana hannunsa,duk inda Shukura tayi sai ya bita yuuuu da kallo,Umma ta koreshi yaki tashi,Kazo ka tafi bacci muke ji mu zamu rufe kofofi,Ahleef yace to Yana Jin haushi yayi fushi ya fice a fusace.

Haka yayi ta fushinsa ya daina zuwa part din Umma Baki daya,Shukura duk ta damu Ahleef Yana fushi da ita,tana yin arbain Shukura da Umma har Baba suka tafi garin su Shukura, Ahleef Yana ta fushi yace ba zai je ba,Suna dawowa suka wuce Niger abinsu,sati daya sukayi sannan suka dawo,Amma Umma tace Shukura sai ta je ziyara gidajen frnds da Yan Uwa,gidan su Momee,Niima,Latifa,suhail,Farhan etc Ahleef duk ya canjawa gidan tsari ya Kara haduwa an canja komai, Bayan ta Gama yawonta yau Sunday yaune Umma tasa masu aiki suka Kara gyara part din Shukura sannan aka Kai kayanta tare da Dattijuwa me taya rainon little Farhan.

Shukura wani wanka data dauka ka rantse ganin sarauniyar England zata je,Kamar sabuwar Amarya ga Umma dama ta Kara tsumata sosai.
Abin mamaki tunaninta Ahleef zaiyi fushi da ita sai taga ba abinda yayi jaririnsa ya dauka Yana Masa Wasa suka koma Bedroom,Shukura tace My Hero nayi tunanin baza ka kulani ba,Akan me? Ai ba Ke kika min laifi ba kuma idan banyi hakuri ba me zanyi,Rungumeshi Shukura tayi tare da cewa I love my Heart, love u more, dare Yana yi Farhan Yana wajen nanny dinsa, Ahleef sai zumudi yakeyi kamar Bai San Shukura ba,ji yake kamar yau aka kawo Masa ita Amarya.

Shukura kuwa har wani tsoro ma take ji yanda taga yanayinsa,Wanka yayi sannan ya karaci kakalen sa jikin mirror,Shukura ma tana wanka ta fito ta shirya tare da shafa turarukanta zata sa kayan bacci kenan Ahleef yayi sama da ita sai bisa bed ya zare Dan towel din ya jefar dashi, sannan ya Shiga Sarrafa ta yanda yaga dama tun tana nokewa har itama ta fara maida martani,maitarta ta tashi, suna tsaka da Holewa suka jiyo kukan Farhan Yana tsaga uban ihu,Ita kanta Nanny ta kasa lallashinsa, Shukura tace kaji kukan Farhan fa yaki yin Shuru mu Bari na lallashe shi idan yayi bacci sai muyi abinmu, Ahleef ko kulata baiyi ba,yaci gaba da aikinsa,Shukura tace Farhan fa Yana ta ihu kana jinsa,Ahleef da kyar ya saita muryarsa yace idan ya gaji ya daina,yaro bazai tashi kuka ba sai dare zai na Hana mutane sakewa.

Shukura Kuma uwa sarkin son danta ta ni dai bazan iya ba hankali na Yana kansa ka tsaya naje na dawo,Wlh kinji na rantse yaron Nan ko mutuwa zaiyi tsabar kuka baza a dakko shi ba, yaro sai kukan dare idan ya gaji ya daina.Tunda Shukura taji ya rantse kawai ta hakura suka ci gaba da soyewa,Yaro Kuma Yana ta tsaga uban ihu can kasa wurin nanny har ya gaji yayi bacci, ranar Sai da gari ya kusa wayewa Basu rabu da juna ba suna soyewa.

Haka rayuwa taci gaba cikin kwanciyar hankali da nishadi,Shukura tana kula da mijinta yanda ya kamata,shima Ahleef Haka,Momee da Umma Kuma sosai suke muamula,yayin da Matan su Sultan suka samu ciki, Fatima matar Farhan ma ta kusa haihuwa,Niima da Latifa ma suna dauke da juna biyu, Zahra da su Hafcy sunyi aurensu Suma suna Shan Amarcinsu.

Bayan Shekara uku Shukura ta Gama schl dinta,danta Farhan dagwas dashi Yana yawo ko Ina,Kuma Bata Sami ciki ba har yanzu,Sunyi wani kyau ga zuwa kasashen turawa suna Hutawa,duk Shekara Kuma Ahleef kaf yake biya musu makka Umrah harsu Niima.
Lokacin Matan sultan sun haihu,su Niima ma Sun haihu,Haka Hafcy da yarta mace,Zahra da Habiba Kuma ciki tsoho garesu.

Ahleef ya dauki Shukuransa zuwa England wannan lokacin Farhan a gida aka barshi wurin Umma,idan ya gaji Kuma a kaishi wajen Momee ko gidan Farhan yayi hutu can.
Sai da suka shafe wata biyar sannan suka dawo Nigeria Shukura dauke da cikinta Dan wata Uku,Sai Murna sukeyi zasu Kara haihuwa.
Bayan wata 6 Shukura ta haifi yarta mace,aka sa Mata suna Noor,kyakyawar gaske ce ta karshe,Farhan karami duk ya dameta da tsokana.

Bayan wata 7 Shukura abar kallo ce yanda take tashen kyau da iya daukan wankan Sugar,ga wayewa ta Zama gogagiyar gaske ta gaban kwatance,Ahleef wani ji yake da ita,yaransu masu tarbiya gwanin Sha'awa,Farhan Fatimansa tana Nan da tsohon ciki,Momee kuwa sosai take ji da yaran Ahleef,Haka su Niima dasu Hafcy duk sun zama kawayen Shukura suna ziyartar juna, Haka mazajen ma suna zumunci.
Umma da Baba suna zamansu lfy,Shukura tana zuwa wurin danginta ayi musu Sha Tara ta arziki,suna Alfahari da ita.

Yau ma Shukura da Ahleef sun fito Noor tana kafadar Ahleef tasha kyau cikin kana Nan kaya farare,gashinta yasha gyara na Yan gayu,Little Farhan ma Yana cikin kana nan Kaya Dan gayu dashi sabo da ko aski ba a fiye yi Masa ba style ake Masa da gashin kamar Dan turawa, Shukura Tasha Riga Arabian gown wacce Tasha aiki ga tsada black and blue,Ahleef yasa light blue shadda dinkin zamani,kowa ya gansu sai sun birgeka,da gudu guards suka bude mota suka Shiga ta alfarma sannan ga driver yaja yau ba escort zasu fita,sai Wani hadadden park na wasan Yara yaran masu hannu da shuni ke zuwa.

Basu dawo ba sai dare,Nanny ta karbi yaran tayi musu wanka tare da shiryasu cikin kayan bacci suka kwanta sai bacci sabo da Farhan ya fara zuwa schl kasancewar Yana da wayo ga Saurin girma.

Ahleef bayan Sunyi Shirin bacci ya manne Matarsa a jikinsa,a hankali Shukura ta juyo suna Facing juna ga wata Shagwaba da takeyi Masa me kashe Masa jiki,a hankali ta tallafi kumatunsa ta Shiga kissing dinsa sosai kamar zasu cinye bakunansu,ga wani kamshi dake tashi a jikinsu,Albarkatun Kirjinta Ahleef ya fara wasa dasu tana wani shidewa,ya furta Allah ya Miki Kira Honey ki godewa Allah Ni nayi Dace wannan basa zubewa kamar Yar 16 to 17 Haka suke naji dadina,ya Shiga tsotsarsu,Shukura tace karfa ka shanyewa Noor milk dinta tunda Kai har milk din shanyewa kakeyi dariya yayi kadan yace zan rage Mata ke Ina ruwanku mu da abinmu namune Ni da yarana.

Sun farantawa juna Rai sosai kamar yau suka San juna,Haka suka dinga kalamai masu dadi kowa Yana yabon Dan uwansa,suna zubar da kalaman soyayya wa juna,Ahleef sai albarka yake sawa Shukura da yaransa, tace I love my Hero, love u too Honey wani shaukin kauna na shigarsu. Basu da matsala sai wacce ba a rasa ba,ga addini ba Sanya...Allah ka bamu itasu muma da me typing da readers nace Allah biya Mana bukatunmu Na alkhairi.
Nan na bar su Ahleef suci gaba da rayuwarsu ta Jin dadi Dan na fara kishi da Shukura Nima.








ALHMDLLH








Na kawo karshen littafi lafiya,Masu karatu da Masu Sharhi,masoyana na ko Ina Ina matukar sonku,Ina kuma Godiya tare da sambada muka albarka,Allah ya biya Mana bukatunmu,ya yafe Mana kurakurenmu.

Allah yasa muyi amfani da darasin da muka koya na wannan Novel,abinda bashi da Amfani Allah ya bamu ikon watsi da shi Ameen.

Wannan Novel nayi delay wajen typing fans ayi min afwa,Inshallah Allah next Wk zamu fara sabo Wanda idan aka fara inshallah sai an Gama Babu Bata lokaci.
Kuyi min afwa time ne bana samu.



Masoyana Ina Miko gaisuwa da ban gajiya Allah bar zumunci.

Sabon Novel dina Next wk Inshallah
πŸ•HADIN KAIπŸ•
Wannan Novel akwai Comedy,love da Kuma fadakarwa,labarin me Dan tsawo ne.masu karatu aje a huta a dawo a sake bude sabon shafi.sannan Fans zaku Sha kyautar page ga masu Sharhi.
Allah ya nuna Mana da Rai da lfy.

πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ’‹












AsmaBaffa.
[7/22, 1:14 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO






81-90







Official






By
AsmaBaffa








AUTA tawa,DIYAR KATIBI, SAMEERAN GAYA,MARCYCOOL,ASYCOOL,HUMAIRA,JANNAT and JIDDA ZARIA
Yanzu kun girmi a baku page sai gaisuwa da jinjinar ban girma.


MASU SHARHI DA GODIYA wannan page naku ne fans.









Niima wacce ke zaune tana shayar da yarta,Hawaye suka zubo Mata tare da tausayin Khadija yarta gata Bata hanyar halak aka same ta ba ga Kuma ubanta mutumin banza,Momee tace Dana sani yanzu kin fara gani Niima tunda har kika zubar da mutunci a gari,Allah ya taimakemu ma da Ahleef da tuni talauci ya baibayemu,gashi yanzu Ahleef shine gatan mu a duniya rayuwa Kenan baka San me taimakonka a rayuwa ba.

Wanka Ahleef ya dauka sosai kamar zai je Dinner, sanye yake cikin wata shadda Yar gaske ta gani ta fada fara tas,yasha takalmi da hula,sai ka lakace wajen kallonsa ka kasa dauke Ido a kansa sabo da haduwarsa,Fitowar Shukura a kitchen kenan sanye take cikin English wear pencil tight blue trouser da rigarta pink color, gashinta yasha gyara da ribbom ba dankwali a kanta tana Kamshinta me dadin gaske ta Kara wani haske da Yar kiba tana sheki da walwalin kyau, tana sauri zata je wajen me gidanta,taganshi Yana sakkowa daga sama kamar wani basara ke Yana latsa makekiyar wayarsa da key din mota a hannunsa,gaban Shukura ne yace wani dummm ina zaije Kuma Haka ga yamma tayi Haka,Ido suka hada ya Mata wani shuumin kallon dake sumar da Shukura.
Ido ta lumshe Masa itama Bata fasa Hawa saman ba shima Bai fasa sakkowa ba so yake ya tsokaneta kawai sai yaki kulata ya raba ta gefenta ya wuce ya sauka kasa, har tayi niyyar kyaleshi taga baza ta iya jurewa ba sai ko ta sakko da sauri tace Ina zaka je ko magana Babu kamar muna gaba da juna? Murmushi ya saki yace sorry Honey sauri nake zanje gidan Farhan tunda yayi aure ban koma ba sai masifa yake min,zan biya gidan Momee na gansu.

Tunda Shukura taji ya ambaci gidan Momee sai ta hade Rai tare da Shagwabe fuska zatayi kuka tunaninta kawai Niima da Ahleef zasu hadu, Yaya dai Honey ko Zaki je muje tare da sauri tace ae zanje a tafi Dani,a ransa yake ta dariya yasan kishi ne kawai yake damun Shukura,da sauri ta haura sama kamar walkiya tayi wanka sharp sharp,Mai ma hannu da kafafu kawai ta shafa sannan ta dankara wani material me arnen tsada da kyau black and white,takalmi da Jakarta harda mayafi ma same color,powder ta shafa da Dan jambaki ta zizira kwalli a idonta abinka da me kyau sai gata ta fito wani das tana kamshi.

Mamaki Ahleef yayi abinda Shukura sai ta Dade Bata Gama shiri ba Amma yanzu gata 30mnt ta shirya ta fito,hannunta ya rike Yana Wasa dasu tayi Masa kyau matuka, Yar Jakarta ya karba ya rike Mata hannu suka fita,yau ba ruwansu da Driver ko escort shi zaiyi Driving da kansa.

Sai da ya bude mota da kansa ta Shiga sannan shima ya Shiga yaja suka bar gidan,Basu tsaya ba sai Gidan Farhan,Fatima na bude kofa taga Kawarta Shukura da matukar murna ta rungumeta kamar zasu Fadi,Ahleef yace yi min a hankali da ita pls karta Fadi ki jawo min,Dariya Fatima tayi kadan tace ayi Hakuri sannan suka zauna, gaba daya Shukura da Fatima suna zaune a 2seater.

Farhan ne ya fito daga kitchen dauke da plate da cup a hannunsa,Bai San ma Sunyi Baki ba,Yana fitowa yasha mamakin ganin Ahleef da Shukura, Ahleef yace to rufe bakin Yar talatuwa Kai Mata abincinta sai ki dawo,Dariya Farhan ya Shiga yi wlh baka da mutunci nice ma talatuwa din? to ba nata bane nawa ne bare kace, Shukura tace an dai kamaka zaka waske,Fatima tayi Murmushi tana Jin kunya tace to idan ma nawa ne Ina ruwanku Wai,Kuma ma mene a ciki,

Farhan dai da Yar jallabiyarsa tsangalalliya irin ta sabon Ango Yana hutawa ya zauna kusa da Ahleef suka tafa sannan suka tsunduma hirar duniya,Shukura Suma suna tasu Bayan Fatima ta kawo musu kayan ci da Sha,Gaskiya gidan Farhan ma ya Hadu karshe, Shukura ta zunguri Fatima suka tashi tsam sukayi Bedroom din Fatima tare da zubewa bakin Bed,Fatima ta kalli Shukura tace Shukura wlh ki yarda da maganata ciki ne dake kamar,Shukura tace ke bani da komai fa mutane ke ganin Haka,Gashi dun kin Kara fari da kiba komai naki ya karu,tabe Baki Shukura tayi tace Jin dadine kawai ki yarda Allah,kin San Hero na Yana ji dani.

Yanzu to tsuminki Zaki bani ko ki koya min mazan Nan naci garesu Farhan baya Bari ina Hutawa ko yaushe cikin yi yake,Murmushi Shukura tayi irin tsohon hannun Nan tace Zaki Saba ne yarinya Ni banga qbin naci da damuwa ba wannan abin dadi Haka to Ni wlh watarana Nike jajibo kayana yanzu idan ba ayi ba kullum bana Jin dadin duniya, Fatima ta bude Baki tace ke ko Harija ce to wannan jaraba haka, Ni bana so wlh,Shukura tace tab zauna Ni yanzu tafiyar kwana daya bazan iya ba gwara Ina kusa dashi,Ni Umma ke hada min Amma tana koya min wasu ma Ina yi da kaina,Bari zan koya Miki on WhatsApp sai Kuma zansa Umma ta Miki naki kema sai ki Aiko a karbar Miki Amma karki Bari ya gane kina yi, Fatima tace ai bazai sani ba dama hauka nake, Shukura tace harfa na maza Ana hada musu idan kina so kiji mijinki zam zam shima kina bashi kalar nasu na maza da Kuma na yayan itatuwa ingantattu,ba kawai kiyi ta gyara kanki ba shi kuma mijinki ba cikakkiyar lfy sai ku cutu,idan baya gamsar dake ma Zaki iya dinga hada Masa wasu fruits juice da abun sai ya shanye Bai sani ba ai idan sau goma kike a Rana shi zai iya dake, dariya Fatima tayi ke Dan ubanki Ina kika San salo haka? Umma ce wlh take nuna min hanya Amma ta dabara Ni Kuma sai na dau haske,gaskiya kinyi dacen suruka,Shukura tace aifa Kam Alhmdllh.

TV ce a room din Ana wani American film suka fara xxx a film din dama su ba kunya,Shukura tace ke kashe wannan abin karki sa yanzu na dauki Mijina mu koma gida,Fatima ta sheke da dariya tare da furta Amma maitar taki tayi yawa da gaske kikeyi,Shukura tace to mu fulani masu lfy ne,lafiyayyu ne mu,uhm naga Alama cewar Fatima.

Tare sukayi sallar Magrib su Kuma mazan suka je masallaci,Yana dawowa Ahleef yace Shukura ta fito su tafi,Fatima tace to Ni me zan Baki Shukura me kika gani kina so a gidana na Baki? Shukura tayi dariya sannan tace babu Hajiya Amarya mun wuce mu,har Mota suka raka su sannan suka dawo gida,su Kuma suka wuce gidan Momee.

Sallama sukayi a Palon Niima ce da Latifa zaune suna yiwa jaririya Wasa,tunda Niima taga Ahleef hankalinta ya tashi ta rasa ma Ina zata sa kanta sabo da murnar ganinsa,matukar so take yi Masa marar misali,Shukura ta koma jikin Ahleef kusa dashi ta makale kafin Nan suka gaisa dasu Niima faran faran,Latifa tace Bari na Kira Momee,Niima tace Shukura ya gida har yau Baki fara University ba? Cike da Shagwaba Shukura ta furta har yau nace ya kaini yaki sai sanda yaga dama,Ahleef kamar baiji su ba Yana Danna waya abinsa har Momee ta fito tana Shukura yau ma dake aka zo Ashe? Ae Momee Ina yini suka gaisa sosai har da Hira, Ahleef ma Haka,Sultan da Suhail suka shugo Ana ta hirar bikinsu ya kusa.

Niima in Banda kallon Ahleef ba abinda takeyi kamar zata Hadiye shi,Shukura tana kallonta duk abinda takeyi,hankalin Shukura duk ya tashi ta gama tsorata da Niima kamar Mayya.

Sultan yace Shukura yau lfy kike kuwa naganki so silent? Murmushin yake tayi tare da cewa lfy nake na gaji ne kawai, Murmushi Momee tayi tace tashi ku tafi gida Ahleef tunda ta gaji, kyaleta Momee sai munyi sallar Isha sai mu wuce, Shukura tana ji tayi Shuru da ita, Sultan sunje Masallaci sun dawo Suma su Shukura gaba daya Sunyi sallah ta dauki Yar Niima tana Mata Wasa Momee tace kowa yazo a ci abinci, a gidan suka ci suka Sha sannan yace tazo su tafi,kamar jira takeyi zumbur ta mike suka musu sallama suka tafi gida.

Ahleef kullum Kara kaunar Shukuransa yake yi suna zuba soyayya kamar zasu cinye juna har Allah ya kawo bikin su Suhail,an fara biki an Kare lfy ansha shagali ko wanne an Kai Masa Amaryarsa radeden gidansa da suke makwafta da juna,Ahleef da Shukura Sunyi rawar gani a bikin kusan komai Ahleef ne ya dauki nauyinsa.
Latifa Allah ya taimaketa a bikin ta samu wani Matashi cikin abokan angwaye Yousuf nutsatse shima da yayi shaye shaye Allah ya shiryeshi ya tuba Babban likita ne soyayya ta kullu tsakaninsu me karfi.

Hafcy tare da kannenta su Zahra aure suke so suyi yanzu koma waye sunce aura zasu yi,Amma Babu namijin dake neman su bare suyi auren duk sai na banza,Mama da Alhj Adamu suna ta Shiga cikin manya Akan a fitar da Mubaraq,Allah ya taimakesu Kuma wani abokin Alhj Adamu Asp ne ya Shiga case din Nan da kyar aka San yanda za ayi tunda kasar tamu cin hanci yayi yawa sai talaka ake kamawa a kulle Amma yaran masu kudi ko kisa sukayi ruwa Tasha.

Mama da Mijinta tare da su Hafcy murna sukeyi Mubaraq ya fito,gaba daya ya rame ya lalace ga uban duka da yaci sai Asibiti aka wuce dashi,Bayan komai ya lafa Mama tace Lallai ya shirya yaje yaga yarsa Khadija,mamaki,da tarin kunya suka rufe Mubaraq,Dana sani ya fara yi Yana zub da Hawaye, Mama ta mike tare da Shiga dakin Alhj Adamu daga kofar taji Muryar Mijin nata Yana waya da likitansa yace Doctor bazan iya fada Mata Ina da HIV ba,Idan taji da matsala,Doctor yace ya kamata a gwada ta idan tana dauke da ita a daura ta a magani,Wlh nayi mamakin ace Ni Alhj Adamu da Hiv,Sai da Momee ta Gama Jin komai Sannan ta banka cikin room tana kuka.

Rasa ma me zata ce tayi sabo da bacin Rai kawai ta zurma Hijab ta figi Mota sai asibitin kudi hankalinta a tashe,test din HIV akayi Mata sai ko gata dauke da cutar itama a jikinta,sai da aka gwada ta different Hospitals Kuma duk possitive ya nuna tana da cutar, Mama ta barke da kuka a asibiti cikin bainar jama'a tana kuka Ana Bata Baki da kyar wani Dattijo Babban malami ya sata a gaba da nasihohi masu ratsa jiki sannan taji sanyi a ranta har ta mike ta samu kwarin gwiwar zuwa a daurata a magani ta tafi gida. Ko data Isa gida yaranta ta Tara kaf har Mubaraq Wanda ya rame sabo da talaucin da yake ciki ya Saba rike kudi sabo da duk dukiyar dasu Momee suka bashi ya karar da ita ta hanyar safarar kwayoyi etc.

Mama tace tofa yarana duniya Dole mu dawo mu bita a sannu,mun shuka Abubuwa Marasa kyau gashi yanzu muna karbar sakamakonmu tun daga Nan duniya ku daure ku Mata kuyi aure tun muna Raye kafin lokacinmu yayi domin mu tamu ta Kare, Mubaraq Kaine Babba ka samu ka koma wajen wacce ka yaudara tare da dirka Mata ciki ka aure ta Haka tunda ta haihu ku hada kanku ku raini yarku Ni Nan da kuke gani na da gawa kuke magana tawa ta kare.

Hafcy ta fara zub da Hawaye tace Mama bamu gane gawa ba,me yake faruwa ne,Hawaye ya tsiyayowa Mama sannan tace Dole na fada muku cewar muna dauke da cutar HIV daga Ni har Babanku,ya dauko Mana cuta ya jona min, Palon ne ya rude da kuka,ba abinda kake ji sai kukan Yan Mata sun hada Kai suna rairawa,Ana Haka sai ga Alhj Adamu ya shigo ya samesu Haka,wuri ya nema shima ya zauna Yana tambaya lfy,Mama ta zuba Masa Harara sannan tace Allah ya Isa tsakanina da Kai,ka cuceni ka shafa min cuta fasiki ba abanza ba Ashe Mubaraq yayiwa wata ciki Ashe Kai ya gado algungumi,Mubaraq Wanda tsabar bacin Rai sai yanzu ya iya magana da Mama ya Isa Haka koma mene ya rigada ya faru sai yafiyar Allah data mutanen da muka zalunta kawai zamu nema.

Washe gari Niima tana zaune a Palo Me gadi ya shugo yace tazo tayi bako,Mamaki ya kamata waye Kuma Haka ta daure ta gyara kanta ta fita dauke da yarta Khadija wacce tayi wayo bulbul da ita,Mubaraq ta gani jingine jikin mota har zata juya sai ta fasa ta Karasa kawai tare da sallama,Sai kallon Khadija yakeyi da gani yarsa ce wani son yarinyar da kaunarta ya kama shi,hannu ya Mika Aiko Niima ta Mika Masa yarsa,ya dauketa Yana ta wani murna,sai da ya Gama Mata Wasa sannan ya durkusa har kasa Yana me bawa Niima hakuri akan laifin daya aikata Mata,tana Jin Sa har ya Gama, ba wani jayayya tunda itama tasan tayiwa wasu laifi Kuma sun yafe Mata kawai tace na yafe maka, wajen Momee ta rakashi.

Momee Bayan sun gaisa ya fara neman afwa, Momee ma tasan itama tayiwa wasu laifi an yafe Mata Babu ja tace na yafe maka kuma kudi ba rokar mu kayi ba Ni na kasa tunani me kyau na baka, duk hakkin Ahleef ne ya kama mu.

Mubaraq yaji dadi sosai anan yace zai auri Niima,Har Niima
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On JIN DADI SABO
avatar
mahamane-noura

11 months ago

Reply

Asalama alaikum, dan Allah yane ake sauke littafin akan waya

Please Login or Register in order to submit comment