Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Momee har cuta ta kamata,Abba ma Yana Tunusia bai Sani ba boye masa takeyi,Ahleef ne ya shigo da safe gidan yaci uwar wanka Cikin wani yard hadadden gaske dinkin ya masa kyau sai kamshi yake zubawa,ga wani agogo malam abin kallo,Sumar nan tasa kyalli takeyi lips dinsa yana sheki jajur dasu.
Cikin takunsa na kasaita ya shiga bedroom din Momee yana bulbula kamshi,Subhanallah ya furta hangota yayi kwance ta dafe kirji tana tari tare da haki ta rame,da gudu ya karasa kusa da ita bai ma Bata lokacin yin magana ba cak ya dauketa ya sauka kasa cikin sarsarfa escort dinsa suka figi motoci sai wani katafaren asibiti Emergency,likitoci suka rufu kanta har aka samu ta farfado sai aka canja mata daki suka ce dole sai tayi 1wk Ko 2wks kafin a sallameta,Momee tana jin dan sauki tace kar Ahleef ya fadawa kowa sai ta warke,yace to Momee Tawa Allah baki lfy tace Ameen,Tunani yakeyi wacce mace zai dakko wacce zata iya kula masa da Momee.

Shukura yau titi ta yini tana yawo ga yunwa da take cinta,tana zaune jikin wata bishiya a zaune mararta ta murda ta fara ciwo sosai take ciwo da alama Period zata fara,ta Mike a hankali ciwo na cinta Bata kula ba ta tsallaka titi sai mota ta fyallo da gudu saura kadan ta maketa Allah ya taimaketa kadan ta dan bigi Kafarta sai ta fadi can gefe,dalleliyar motar ce tayi parking wani katon arne Igbo ya fito da sauri yaga jini na bin kafafunta tunaninsa motarce ta mata rauni haka bai san period take ba dama kuma ba pad jikinta,a motar ya sata ya figeta tana kuka za'a saceta,bai tsaya ko ina ba sai asibitin da aka kwantar da Momee tasu Ahleef, sai kuwa aka rasa dakin da za a kwantar da Shakura sai dakin da Momee ke ciki suka shiga neman izini tunda daki mutum daya ake bawa.

Ahleef na zaune gefen Momee suka shiga suka nemi izini tunda dakin da aka sa Momee na mutum biyu ne normal, Ahleef yace bai yarda ba, Momee tace Son kyale a taimaketa a kawota ba damuwa.
Shukura kukan Shagwaba kawai takeyi Wanda dama ta saba,jini na bin kafafunta aka turota Saman bed har dakin,duk ta cikawa mutane kunne.
Ahleef Sam bai ganeta ba,amma kamar ya santa amma ya manta a Ina,Momee tace sannu yarinya ko cikine daita tayi barinsa Allah Sarki gata kyakyawa Mashaallah,Likitoci sukace Ahleef ya fita zasuyi aiki yace wlh ba inda zaije me zai gani bayan sunsa wani labile Sun kare yarinyar,suna Jin Kukan Shukura tana kwarototo wayyo....Marata zata belle,meke damunki ? Kina da ciki ne ? Shukura ce tace ni Jinin Haila nakeyi ubanku ne yayi min Cikin ? Ai Dazu wani yace mu hadu a Hotel kuma banje ba wai ni zai yiwa wayo,kara ta kuma kwallawa tace wlh haka zaita zubowa haka yake min duk watan Allah, Innata ma Kafin ta mutu tace nafi wata me haihuwar ma wlh, yiiiii.... Taci Gaba da kuka nurses sai dariya sukeyi Wanda Suke Jin Hausa,Ahleef da Momee suna jinta sai dariya Momee takeyi kasa kasa,Ahleef yana ji ya daure fuska a yana wannan yarinya bata da sirri ta fiye surutu ga kukan tsiya yaja tsaki.
Anzo za ayi mata Allura ta fara tsandara kuka ita bata so,aka canja mata magani nan ma ta fara kuka ita Bata sha, Ahleef ta kaici yasa bai san sanda ya daka mata tsawa ba, Ta Cikin labile taji gaba daya ta firgita,ta kidime da sauri tace to ayi min Allurar,sai anzo za a tsira sai tace wash...ta fara guduwa Momee ce ta dan yiwa Ahleef magana Da ido wai ya kara mata magana,ba Wanda yasan fuskar kowa ta labile taji muryar dazu me shegen dadi amma ba alamar mutunci a cikinta ba shiri tace ayi min zan tsaya, sai da aka gama yi mata komai sukace taje tayi wanka,Igbon daya kadeta shine ya siyo mata doguwar Riga ta wani material me shegen kyau da tsada harda pad da parties kala biyar tunda ya basu,suka ce kwana uku zatayi a asibitin sai kafarta data ji rauni ta warke, kawai yace a bashi Bill zai biya sai da ya biya komai sannan ya samu wata Nurse ya Bata kudi kullum ana siyawa Shukura abinda takeso tana ci har a sallameta kuma su kula da ita sosai,sai ranar da za a Bata sallama zai dawo ya dauketa.

Shukura kuwa Wanka tayi ta shirya kanta ta wanke Wanda ta Bata sannan ta fito wow ba karamin kyau Material din yayi mata ba kamar a saceta,an gyara room din sai kamshi kawai ke tashi,an cire labilen da suka raba tsakaninsu da Momee,nurse ce ta shigo gashi baza ta iya tambaya da turanci ba ina zata shanya kayanta ?
Kawai sai ta kwanta Saman Bed dinta ta fashe da kuka,tana shure shure,Ahleef sai yanzu ya tuna da mutum fa a wancan bed din,Momee tace yan mata lfy ? cikin kuka tace ni ban... Iya...turanci ba...small small nakeji kuma so nake na tambaya wannan Nurse din ina zan shanya kayana nayi nayi na tuna sunan shanya da turanci na kasa,Momee tace to ai ba kuka zakiyi ba Nima na iya ga dana ma, Shukura sai ta Mike zaune tace tsohuwa dake yaushe kika koyi turanci ? Yanzu dama irinku kuna Jin turanci a birni ? Momee tayi dariya tace ae mana, Amma Gwaggo tun Jahiliya ke Babanki wayayyene, Tab niko Inna ta Allah yaji kanta tana dariya ta karasa da wlh kwakwalwarta a dinke aka yi mata ita kamar ansa zare da Allure a dinke ta,Ahleef dariya ta kamashi da kyar ya iya dannewa,Shukura taci gaba yanzu wannan baturen danki ne ? Momee tace ae mana shine yake jinyata,Uhm kawai Shukura tace har ta kwanta ta kara mikewa zaune tace Gwaggo wai dan Allah ya sunan jakin babangida da turanci dama tun Baffa yana da rai nake ta so muzo birni na tambayi yan gayu,Momee tace ke kin cika surutu ki kwanta ki huta Nurse ta kawo miki abinci kici,Shukura tayi dariya tare da cewa dan baku San wace ni ba,kaf garinmu babu kamata,miskila ce ni,shuru shuru bana magana yanzu ma dan ku yan gayu ne kawai shi yasa nake so na karu daku kafin na tafi.
tsaki Ahleef yaja ba shiri ta kwanta tayi luf,nurse da kanta ta shanya mata kayan ta Bayan room dinsu,an kawo mata abinci shinkafa da miya tare da yankan nama biyu, bude abincin Shukura tayi da sauri ta rufe tana ni bazanci wannan ba shinkafa da miya tsura sai gutun nama ina laifin ace da salat ma tare da Ko balangu ne daban Bazan iya cin wannan ba sai ta fara kuka tana da Baffa na yana da rai wlh saniya zai yanka min ma,Momee tace ikon Allah ki dinga hakuri da lamarin duniya tsaya a kawo min abinci sai kici,ba a fi 5mnt ba sai ga Driver me aikin Momee ta aiko da abinci iri iri.

Momee tace taso ki iba, Tana daga kwance tace dan gidan Gwaggo dan zubo min naci dama ta saba bawa iyayenta Umarni,ko kallonta baiyi ba waya yake latsawa,ba shiri ta mike har gaban Momee sannan tace sannu da jiki,Momee tace yawwa ebi ki tafi,nan fa ta fara kici kicin bude Flasks kowanne ta kasa budewa har nishi takeyi Momee tana ta dariya,sai da tayi ta gaji sannan tace kai ni na gaji gaskiya,Momee tasan Ahleef bazai bude mata ba sai tace bari na bude miki,jin Momee zata bawa kanta aiki kawai sai yace kwanta Momee ya fisgi flask daya ya bude,ya bude sauran ma wani kamshi ya daki hancinta,Shukura tace zanci wlh na gode,ta dauki plate ta ebi farfesu,ta ebi naman cikin miyar,sai ta ebi chips duk wani abin dadi shi ta iba, karshe ta kalli shinkafar fara ta zaro mata ido tare da cewa ke yar gidan kowa ce me za aci da ke in banda kisa mutum basir Bazan taba ibanki ba,Macaroni ma ta kalleshi tace ga kayan dadi wa yake ta kai me za aci da kai da wasu kofofinka kamar na hancin mutum.

Momee ta fara dariya, Ahleef a ransa yace wannan kawai yar iskar kauyece yana dariya a ransa, ita kuwa ko rufe flaks din batayi ba ta koma gefen gadonta ta fara ci, Ahleef cikin Isa yace wa zai rufe miki Flasks din ? Dan mitsitsin lips dinta ta turo zata yi kuka tsawa ya buga mata Idan kika Sani magana...kafin ya karasa har ta diro gaban kayan ta fara rufewa daya bayan daya da kyar, Momee tace Bata da lfy fa kana takura mata Son,Momee bari naje na dawo,ok kaini bakin toilet sai ka tafi,bayan ya kai momee tayi fitsari ya kara riketa ya kwantar da ita Saman Bed sannan ya fice abinsa.Shukura tana gama cin abincinta ta kwanta sai bacci ya kwasheta me karfi.
Bata tashi ba sai Cikin dare karfe 11pm tana bude ido Momee ta hango tana sallah saman sallaya Ahleef yana gefe saman Bed yaci uban wanka Cikin 3qtr da yar armless yana karanta jarida ya harde kafa daya kan daya,Shukura a ranta cewa take gaskiya ya hadu Ban taba ganin irinsa ba a duniya,a hankali ta Mike Bata Sani ba garin bacci pad ta goce ta Bata kayanta kadan Ahleef yana gani ya runtse idonsa yana Jan tsaki an kawo musu kazama daki a haka gata kamar me tsafta,sai da ta shiga toilet ta fara takaici Allah yasa dai dan Gwaggo bai gani ba, sai da ta gyara kanta tsaf ta fito tare da cewa Gwaggo dan san min turarenki,murmushi momee tayi ta mika mata kala uku ta shafa,Mikewa Ahleef yayi tare da cewa bari naje na kawo miki abincin zan aiko a kawo miki,Momee tace ga Shukura taji sauki tunda siyo min zakayi kuje tare Idan kun dawo sai ka Bata ta kawo, da sauri yace no Momee pls wannan kazamar ? Bata rai Momee tayi kawai da sauri yace am sorry Momee ke zo mu tafi,Shukura ta tsaya kallonsu suna birgeta yace kazama i'm talking to u da sauri ya fita cike da gadara,tabi bayansa da gudu gudu sauri sauri,jikin wata rantsatsiyar mota ta hangoshi ya bude side din Driver yashiga yau ba Escort da sauri cike da kauyanci ta zaga itama ta rasa ina zata bude kawai ta finciki murfin mota kamar zata balle shi, da kyar da kokawa ta bude gaban motar ta shige shima ya shiga yana dariyar kauyancinta a ransa yace mace har mace haka.

kalle kalle takeyi Ko gyale dama Bata dashi dan siririn dankwalin doguwar rigarta ta daura a kanta tare da zamge kanta da mayafin.

gudu yake sharawa a titi kamar zai tashi sama da ita,gidansa da yafi zama yanzu ciki ya fara zuwa ko kallonta baiyi ba taga ya fice ya barta a motar,tana ta karanta Address din gidan dake Manne a jiki har sai da ta haddace su tas,sai gashi ya fito da Latifa tana rike a hannunsa,ta shiga Baya sannan yaja motar suka tafi,Latifa akwai raina yan kauye,tace Yaya wannan budurwarka ce ? Tana da kyau sosai sai dai yar kauyece,bakin ciki ya kama Shukura,Latifa tace ai yarinyace ma wlh da kadan zata girmeni,daga wanne kauyen kike ? Shukura bata San Sanda ta juya da sauri ta zubawa Latifa rankwashi a kai tare da cewa dan uwarki sa'arki ce ni ? Latifa zafin rankwashi yasa ta shako Shukura ta baya,Shukura ta juya sosai suka fara kokawa suna doke doke da zage zage,Wani uban birki Ahleef ya taka kuuuu sai da suka tsorata ya buga musu tsawa sannan suka dawo normal,Shukura tace wlh duk ranar dana kamaki sai na lakada miki duka. Tsaki yaja yaci Gaga da Driving da sauri yayi parking a wani katafaren wurin cin abinci yayi take away,har cikin asibitin ya kaisu sannan ya mikawa Shukura ledojin Yana zuba mata uwar harara,karba tayi kawai zata kaiwa Momee,Latifa tana so taje ta duba jikin Momee amma ba yanda ta iya ya hanata wai gida zai maidata tunda Bata Jin magana tana ji tana gani sai hakura tayi,lokacin tuni Shukura ta wuce cikin Hospital din amma ta manta Hanyar da zata mayar da ita dakinsu,sai zaga Hospital takeyi tana duru duru sai faman bude rooms takeyi na mutane sai da Allah ya kawo wata nurse sannan ta dinga masifa marar lafiya da fita yawo ba tare da an sallameta ba haka dai ta nuna mata dakin nasu ta shige tana kunkuni.






AsmaBaffa
[7/22, 1:11 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO








5







Official









By
AsmaBaffa








AsmaBaffa fans club Page dinku ne.









Da sallama Shukura ta shiga tace mun dawo tare da ajiyewa Momee ledojin a gabanta da Ladabi,Momee tana kallonta dauke da murmushi a fuskar ta,ta mikawa Shukura nata itama ta fara cin nata,Shukura dadin girki yasa ta fara surutu iri iri tana yiwa Momee tana shan dariya har suka gama ci amma momee na mamaki dangin Shukura basu zo ba kuma Igbo ne ya kawota sannan taga yarinyar ko a jikinta harkokinta takeyi, tayi niyyar tambayarta ina danginta sai ta fasa kawai ta share komai.Shukura i tace yau ta dinga taimakawa Momee idan zata je toilet momee tana sa mata albarka da godiya.
Washe gari da safe 8am sai ga Ahleef tare da Latifa wacce take sanye cikin Uniform da alama schl zata je, yau Ahleef ba karamin kyau yayi ba cikin shadda Grey sai sheki yakeyi ko kallon side din shukura baiyi ba ya gaisar da momee sannan ya ajiye mata abinci iri iri, Momee tace Allah yayi maka albarka Ahleef,Shukura a ranta tace Ahleef wannan sunan yan gayu ne, Latifa sai yanzu ta kula da Shukura hararar juna sukayi ko wanne ya dauke kai,Ahleef Jan Hannun Latifa yayi kinyi fa late lets go malama,Momee suka yiwa sallama suka wuce,yau kwanan Shukura Uku yau ne kuma za a sallameta maimakon murna sai ta fara bakin ciki yanzu Idan ta bar asibitin a ina zata ci abinci har ta samu wurin kwana,Lulluba tayi kawai take ta faman kuka a hankali ba tare da kowa ya gane ba,idonta yayi jajir tana dana sanin barin kauyensu yanzu ga halin da take ci,
abincin ma ta kasa ci, momee tayi mata magana har ta gaji Nurses ma sunzo Sam taki fitowa a Cikin blanket din sai gajiya akayi aka kyaleta, Igbo dai daya kade ta har yau bai zo ba Sabo da aiki ya rikeshi sai waya yayiwa Doctor cewar kawai tunda ya biya komai su sallameta a Bata 5k ta shiga taxi ta tafi gidansu tunda yaga zata iya komai,dama kuma Doctor din Abokin Igbo man ne, yanda yace haka Doctor ya aikata 5pm ya shigo still taki bude idonta,Ahleef yazo wajen Momee yana shan kallon ikon Allah, Da mutum ya kai Hannu zai cire bargon sai ta danne ko ina da kyar Doctor ya faki idonta ya cireshi tare da wulli dashi gefe,Da sauri ta mike zaune idonta Jajir dashi kamar me fuska takumbura ga Hawaye suna kwarara mata, tunanin kowa dama so take a sallameta zaman asibitin ne ya dameta shi yasa take kuka,Momee tace yi hakuri yata yanzu zai sallameki ki tafi gida Ko ? Ai sai aka ga ta kara volume din kukanta,Doctor yayi murmushi tare da leka fuskarta ya nuna mata takarda kinga da gaske takeyi ga takardar ma sallamar taki na gama komai inye yau zata ga Daddy dinta da Umma, yau zata ci abincin Mamanta kaga yan mata inyeeeeee....Shukura kuwa sai ta kara rafsewa da kuka tana tuna kayan dadin da take ci wajen Momee a banza har wani shidewa takeyi tana kuka,wani farfesu da kayan ciki da take ci kullum suka fado mata a rai,sai ta zamo kasa daga kan bed ta dinga rera kuka,Gasashiyar hanta take tunowa kullum a asibitin sai an raba musu sunci ga dadi Hawaye sababbi suka tawo sharrrrrr,Tunowa tayi Bata da wajen kwana tare da tunowa yanda kullum take karyawa da dankalin turawa,hannayenta biyu ta daura saman kai tana shesheka tana shidewa,Momee sai hakuri take Bata,Doctor ma na lallashi da kyar aka samu ta daina Kukan,likita ya Bata sallama da 5k,Momee tace gaskiya bai dace a Barta ta tafi gida ita kadai ba haka,Igbo ya kadeta bazai iya zuwa ya kaita gidansu ba, Ahleef dai danna wayarsa yake yi bai ce kala ba,Har Shukura ta mike zata tafi sai ta dawo taje gaban kayan abincin momee ta ebi duk Wanda take so taci ta koshi kamar zatayi amai haka ta cika cikinta wai taci na karshe,Gwaggo...Momee tace na hanaki kirana da wani gwaggo fa kin Sani, murmushi tayi kadan tace na manta ne Momee zan tafi ni Allah baki lfy, Momee tace ga number ta ko watarana zaki kawo min ziyara, karbar card din tayi ta fice Abinta kamar kwai ya fashe mata a ciki haka take tafiya har tayiwa asibitin nisa sosai.

sai data yi nisa sannan ta samu wata bishiya ta zauna tana hutawa,ko 2mnt batayi ba sai ga wasu mutane Sun koreta wai ba a zama a wajen,Shukura tace da a kauyene wa zai koreka ko a filin tsakar gidan Me unguwa ne sai yanda kaga dama zakayi,a hankali take tafiya ragowar 2k dinta Cikin Wanda Igbo yace nurse ta Bata suka zube a hanya,baya ta koma tana dubawa amma Bata gansu ba gashi kafafunta Sun gaji kawai sai ta fashe da kuka tana ci gaba da tafiya tana goge hawaye tare da cewa na Kawo kaina gashi ni dama ban iya komai ba zuciyata ta gama mutuwa Iyayena gata suka nuna min,ita kadai take maganarta har tazo dai dai inda Haj Saudatu take soya doya da kwanta me dan karen dadi, har ta wuce sai ta dawo Baya ta kafe Saudatu da mugun kallo a fili tace wlh tana kama da dan gidan Gwaggo Momee, Haj Saudatu ta kalli Shukura itama tana murmushi tace yan mata lfy ? Shukura tace wlh Inna kamarku daya da wani dan gayu baki ganshi ba idan kikayi dariya komai naku iri daya ne,Murmushi kawai Saudatu tayi tare da cewa ni kinga bani da yaro a zuci kuma tunanin danta abin sonta ya fado mata,Shukura tace Inna da zaki bani aiki sai na dinga tayaki ina miki wanke wanke kina bani dan Ladan aiki mu daga kauye muka dawo nan Abuja bamu samu aiki ba,Saudatu taji dadi dama tana neman me tayata aikin tana biyan lada, yarinya a ina iyayenki suke,Shukura gani takeyi idan ta fadi gaskiya za a hanata aikin sai tace daga kauyen Jos muke yankin Fulani,muka dawo nan neman aiki iyayena suna can Nyanya a nan Abuja gidanmu yake,Saudatu kuma ta tace muma yan Niger ne a Kaduna muka fara zama, sai muka dawo Abuja,mijina gadi yake a wani gida,nan muke Zaune hakan ma da kyar masu gidan suka barmu muke dan rabawa a gidansu basu da kirki.

Shukura a ranta tana Sa rai ko Saudatu Zata dauketa ta koma gidanta da zama ta samu wajen kwana sai taji Gaba daya ba harka, Shukura cikin karfin hali tace Inna idan zan kawo miki ziyara watarana fa ? Saudatu ta rike baki tare da cewa wuuuu yar nan rufa min asiri ai Ko baki basu bari muyi idan ma zaki zo sai jefi jefi kuma babu dadewa mu gaisa ki tafi gidanku in ba haka ba ki jawo mana masifa,Shukura taji ba wajen zama kawai tana tunani ga dare nayi to ina zata je ta kwana,jiki a sanyaye tace to Inna yaushe zan fara zuwa ina tayaki aikin ? Saudatu tace banda yau tunda kinga na kusa tashi dare yayi ki bari sai gobe kizo,yanzu maza ki tafi gida kar a nemeki,Shukura tace da na tayaki daukan kayan sai na rakaki gida,Saudatu tace na gode Allah miki albarka baza ki jawo min ba yar nan kiyi hakuri dan Allah ki barshi,Shukura Badan taso ba ta juya tana cewa sai goben zanzo, 3pm cewar Saudatu har ta zubawa Shukura doya da yawa a leda ta Bata kyauta.

Shukura ta rasa ina zata je har 8 na dare kawai sai ta tuna da Address din gidan Ahleef Wanda yanzu yafi rayuwa a cikinsa kawai taxi ta shiga ta bashi Address din gidan Ahleef,bayan me taxi ya kaita sai da ta tabbatar da gidan ne sai ta tsaya can farkon layin dan kar a ganta,ta juya wajen me taxi tace ita wlh kudinta Sun fadi yayi hakuri Bata da ko sisi amma yana binta bashi nan da 3days su hadu a wajen Saudatu me doya inda ya daukota,Me taxi ya dinga masifa har ya gaji karshe yace zaizo wajen Sauden nan da 3days din in dai ba a bashi kudinsa ba to wlh Ko Sauden ce kamata zaiyi,Godiya tayiwa Allah sannan ta fara dube dube sai da ta tabbatar ba Wanda ke ganinta sai tayi sauri ta zaga ta bayan katangar Ahleef inda babu security,Dalaf ta kama wata bishiya dake jikin katangar ta dane bishiyar ta gama kwalkoleta sannan ta lallaba ta taka dalaf ta dane saman katangar gidan Ahleef,Tayi sa'a a saitin garden ne sai ta kara tsalle kamar biri ta hau Saman wata bishiyar goba dake cikin garden din Sabo da katangar tayi stayi haurawa sai da dabara,ta kan bishiyar ta dirga a katafaren gidan nasa sannan ta fara tafiya cikin Sanda dan kar a ganta,ta kofar baya tabi sai gata a kitchen ta tura kofar a hankali,ta bi ta wuce ta fito ta wani katafaren palo tana son tayi kallo ba hali,da sauri tabi ta wasu wuraren har ta samu ta ga Steps taga wata Hanya ta kasan Benan da gudu ta shige tabi ta nan sai gata a wani part din guda ba abinda babu,wani katon wuri ta shiga Gaba daya kayan motsa kiki ne, ta wuce sai gata a wani kitchen din ba abinda babu, cikin inda kayan motsa jiki Suke a nan ta samu wani lungu Wanda idan mutum ya shiga ciki babu me iya ganinka a nan ta samu ta shimfida dankwalinta a kasa harda kashe Light ta kwanta sai bacci ya kwasheta.

Shukura Bata iya bacci lfy ba sai tayi birgima da shure shure taji gida me dadi sai juyi take tana bige bige har ta bige wani karfen motsa jiki kadan, Lokacin Ahleef ya dawo yayi shirin bacci cikin Fararen kayan baccinsa tunda ya shigo yau yake Jin kamar ana motsi a gidansa,kamar ba shi kadai bane,idan kuma ya kasa kunne sai yaji shuru,Yana Saman Bed yana latsa system sai yaji kamar abu yayi motsi,tsoro ya kamashi kawai dai ya dan daure ya Mike ya fara lallabawa yana sanda kamar sabon barawo,a haka ya duba ko ina na gidan sai yaga ba kowa,kawai sai yace ko kunne na ne ? Baki ya tabe tare da kashe Light na ko ina ya koma ya kwanta bacci.
Washe gari da safe ta lallaba ta fada wani bedroom wanda yasha kayan alatu masu kyau, Da sauri ta shige toilet din ciki,ta samu sabon brush da toothpaste tayi brush tare da wanka ta daura Alwala ta shirya cikin kayanta tsab sannan ta kara lallabawa ta fito inda take boyewa anan tayi sallar asuba tare da adduointa, sai 10am taji motsin Ahleef ya fito dakin da take zai motsa kiji,kara boyewa tayi sosai tare da leko da kanta tana kallonsa daga shi sai Boxers yana motsa jiki,shiko bai san da mutum ba,Yana ta motsa jiki,itako mamakin kyawu nasa takeyi ga kyan sura kasa dauke ido tayi a kansa kamar zata lasheshi,tana kallo ya hada zufa har ya gama sannan yayi wata mika sosai,Dariya ya Bata yanda yayi mikar saida ta murmusa,tana kallo ya juyo kamar yana facing nata da dan tight boxers din dake jikinsa Kamar tsirara haka yake Sabo da shape din komai ana gani,Shukura ta firgita ganin kato haka Bata San sanda tace kai..tab

1 Comments On JIN DADI SABO
avatar
mahamane-noura

2 years ago

Reply

Asalama alaikum, dan Allah yane ake sauke littafin akan waya

Please Login or Register in order to submit comment