Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Bayan sati biyu tuni dangi sun Gama komai za a daurawa Shukura aure da megari, zance ya baza gari,ance kar a fada mata sai an daura ta ji daga baya, Ana saura kwana Uku a daura aure Shukura taje gidan Aishalle,Aishalle tace ke kuma da kike auren me kyau a birni ya naji za a daura Miki aure da Megari,Shukura tace aure kuma? Ban gane ba kefa kin cika hauka,Dariya Aishalle tayi tace to wlh boye Miki akeyi kaf garin da Yan uwanki sun sani Amma ance kar a fada miki yau saura kwana Uku ki zama Amaryar me gari,gashi can Talliya Matarsa tayi yaji ta bar gidan ma,idan Baki yarda ki tambaya kiji,Yafendo tasan komai,har an Kai kudin aure wajen Kawu,idan kin San kina da auren wani wlh ki San abinyi tun wuri.

Ai Shukura ko Gama ji batayi ba ta fito sai gida wajen Yafendo ta fado da gudu tana Hawaye tace Yafendo me nake ji wai za ayi min aure da Megari? Yafendo tace yo tsayawa zamuyi mu kalleki ko me,kinzo sai karya kike Mijinki zaizo Yana Ina?Baki da sheda,Wanda suka kawoki sunce karuwanci kike Zaki likawa wani Dan ya aureki Kinga sun tabbatar Mana Baki da aure kuma aure kamar anyi.

Ga Dubu goma Megari ya kawo sune kudin lefenki, da Sauri Shukura ta karbi Kudin lefen dubu goma,har Yafendo tana dariya tunaninta ta yarda da auren,Sai taga Shukura ta tattara kayanta a akwatuna tas ta fito ta kalli Yafendo tace wannan dubu goman ki fadawa Megari na ranceta zanzo tare da Mijina na biyashi kudin Lefensa,da sadaki ya kawo bazan ranta ba Amma tunda kudin Lefe ne na ranta na bar muku garinku wlh Akan na auri Megari gwara na koma ga Allah banyi aure ba.
Tasa Kai ta fice sanye da hijab tana Jan akwatunanta tana tunanin Ina zata je inda Ahleef zai San tana nan.

Tana cikin tafiya sai ga Megari a saman wani tsurar machine dinsa da ciyawar tumaki a bayansa ya dawo daga gona,kallo daya ya gane barin gari zatayi,ai da sauri yaci uban birki ya dirgo daga Machine ya rike hannun Shukura Kam,tunawa da tayi tana da aure wani bakin ciki ya kamata ta dage iya karfinta ta warware Megari da Mari,idonta cike da kwalla tace Ina da igiyar wani a kaina baku da hankali ko jahilci na damunku.

Megari yaja baya dafe da kumatu Yana mamaki,tace kaja mutuncinka Ina ganin mutuncinka,ta ja kayanta taci gaba da tafiya abinta ta bar Megari da jimami duk girmansa da mutuncinsa ga mulki babu Wanda ya taba ko Masa magana marar dadi Amma wannan so ya jawo Masa yasha Mari,Allah ya taimakeshi ba a gaban talakawansa bane da yaji kunya.

Shukura Machine ta hau Bata tsaya ko Ina ba sai wani Kauye me Dan Nisa gaban kauyensu,Suma Yan Fulani ne wai Dan kar tayi Nisa da garinsu sabo da zuwan Ahleef.

Rashin sani Shi kuma Ahleef yace Umma ta bawa Farhan Address din kauyen su Shukura su Shirya tare da Baba da Umma Farhan ya kaisu garin su dauko Masa Matarsa a dawo da ita kafin ya dawo, washe gari da Sassafe suka dauki wanka musamman Farhan daya ke ji da kansa,Umma kuwa kowa ya ganta yasan Balarabiyace Tasha lace tayi Masifar kyau gashi dama tayi kiba haskenta ya Kara fitowa,Baba ma yasha Shadda me tsada yayi kyau,Farhan a wata arniyar motarsa yazo driver na jansa,Umma suka shiga suma,Sai wata dalleliyar mota da escort din Ahleef a motoci biyu suna binsu a baya suka dau hanyar Jos.

Sunje garin Jos suka tsaya Suka ci abinci da sallah sannan suka dauki Hanyar Kauyen su Shukura,sun Sha tafiya me nisa kafin sannan suka Isa garin,tun a farkon garin Yara ke bin motar suna motoci ne motocine,sulluwa ce wlh har guda uku,Farhan ne ya sauke Glass yace gidan su Shukura yake nema,Suka ce Shukura Maji dadi ai jiya ta gudu ta bar gari Akan za a ayi Mata aure da Megari,Farhan gabansa ya Fadi yace to a wanne gida ta zauna? suka nuna musu gidan Yafendo.

Bayan sunyi parking Nan fa gari ya dauka Mijin Shukura bature yazo daga birni Ashe gaskiya Shukura ta fada,Mata har da masu leke ta katanga kallon Mijin Shukura,kafin kace me kofar gidan Yafendo ya cika dam da Yara da manya maza da Mata harda matan aure za aga Ahleef.

Farhan Yana fitowa kamshi ya turare wajen,Samari suka fara Kaine Ahleef Mijin Shukura? Farhan yayi Murmushi yace Ashe kun San Ahleef kuma? Nan suka dinga bashi labarin Ahleef yanda Shukura ta fada musu har dinkinsa da ake yayi a garin,Farhan yasha mamaki yau,yace bani bane Ahleef ni abokinsa ne,Ahleef Yana America,zuwa mukayi muga Shukura mu dauketa wannan sune iyayen Ahleef.

Yafendo ce tace babbar magana Ashe yarinyar da gaskiyarta to ku shugo ayi maganar a nutse,Yafendo tayi musu saukar mutunci sannan ta Kira manya cikin dangin uban Shukura da kuma manya cikin na Inna aka zauna,bayan an gaisa da addua,Baba ya zube musu zance tiryan tiryan ya Basu labari haka Umma ma ta bada Wanda Baba ya manta,
Yafendo tace to Wanda suka kawo Shukura kuma su waye? Nan Umma ta Basu tarihinsu,Dana Ahleef harda na Momee ta Basu kaf sannan tace wannan kuma Dan sabani aka samu shi yasa ta dawo da Shukura har ta furta munana Nan kalamai a kanta.

Nan fa kowa ya shiga zare Ido kunya ta kamashi yanda suka dinga wulakanta Shukura,Suma sai suka Basu labari yanda Shukura Tasha wahala a garin kowa ya gujeta,da auren da za ayi mata da Megari har ta gudu ta bar garin yanzu ba a San Ina take ba,Baba da Farhan tausayin Shukura ya kamasu,Umma har da kuka tace shi yasa ake son bincike Akan abu,gaskiya baku kyauta ba,Shukura yarinyar kirki ce wlh me yasa kuka kasa ganewa kuna Yan uwanta, Farhan waje ya fita can gefe ya Kira Ahleef, ring daya Ahleef ya daga tare da cewa dalla Malam bawa matata waya naji muryarta na lallasheta, Farhan kansa Ahleef ya bashi tausayin Amma Haka ya daure ya bashi labarin komai.

Son Shukura ne sabo ya Kara sukan Ahleef hawayen tausayinta ya zubo Masa duk a kan aurensa Shukura ta Sha wahala haka, Ahleef yace Farhan Amma Allah ya tsinewa Megari shi ya cuceni ya jawo min masifa matata ta bace wlh idan na dawo kasar Nan ba a ganta ba wlh sai yayi prison,Farhan Yana ta bashi hakuri Yana Lallabashi tare da kwantar Masa da hankali.
Umma tace ku tashi mu tafi to me zamu jira,Farhan yace Addua zamu ci gaba da Yi Ana bincikenta Allah ya bayyana Mana ita.

Farhan ya yiwa mutanen garin kyauta da yawan gaske sai murna akeyi har suka musu sallama suka bar garin, Koda suka koma gida tuni Ahleef ya bada sanarwa a kafafen gidan radio da tv anyi ko Ina idan Shukura taji ko wani da ya santa a sanar Mata ta koma Abuja da Address din gidan su Umma Amma Shuru tana can wani Kauye Wanda yafi nasu ma harkar shanu kawai akeyi na Kiwo a garin.

a garin kuma Shukura tunda ta sauka Allah ya hadata da wani Dattijo da Matarsa su kadai a gidansu Basu da yaro ko daya suka ce Shukura ta zauna tare dasu ba damuwa abinda Shukura Bata sani ba tsofaffin mugayen Yan fashi ne dasu ake hada Baki Ana tare hanya,su suke yiwa Yan fashi waya,Shukura tsakar dare sai taji sun fita suna ta waya, ita Bata San me sukeyi ba,Bata da burin da ya wuce ganin Ahleef yanzu yakai kullum aikin kuka take ba dare ba rannan har ta kwashe sati biyu tare da wannan tsofaffin, wata ranar asabar katsam sai taga Yan sanda sun cika gidan tab sunzo mota mota tare da damke Dattijo da Matarsa an gane cewar yan fashi ne,Zasu hada da Shukura ta fashe da kuka tace Wlh ni bakuwa ce sati na biyu da zuwa garin,Yan sanda suka tambayi Yan gari aka tabbatar musu sannan suka kyaleta,sai gashi an samu bindigu sunfi ashirin a dakin dattijo Nan akayi gaba dasu.
Shukura Tasha mamaki tace Lallai mutum mugun ice Ina ta bacci dasu da gudu ta kwaso akwatunanta ta hau Machine tayi hanyar kauyensu da ta gudu, dai dai lokacin kuma Ahleef yazo Nigeria ba tare da sanin kowa ba,escort dinsa kawai yayiwa waya suka sameshi da sababbin motocinsa sunfi goma a Hotel din da yake ya fito cikin shiri yace a kaishi kauyen su Shukura tunda wasu daga ciki Farhan yaje dasu.
Wanka iya wanka yasha kamar baza a mutu ba,sanye yake cikin wata dakakkiyar Shadda Yar gasken gaske light blue,fitted dinkinsa links,sumar Nan ta Kara yawa an kwashe gefe da gefe kadan taci kudi sai kyalli take hade da Dan sajensa zuwa Dan gemunsa na matasa yasha gyara luf luf sai ya Kara kawata fuskar tasa abinka da farar fata ba a cewa komai,Agogonsa Gucci me tsananin tsada,ga wani takalminsa kalar shaddar irin na sarakai flat half shoe sai kamshi take ta ko Ina,cikin tafiyarsa ta kasaita ya shiga mota suka Ware wuta sai Jos,duk inda suka wulga sai anbi motocin da kallo sabo da kyawunsu.

cikin garin Jos suka ci abinci da sallah kana suka dauki Hanyar Kauyen suma, suna shigowa hanyar, Machine da Shukura ke Kai ya yanko Shima fiiiii Hijab dinta na tashi Yana gefen motocin sun jera suna tafiya, Ahleef Sam bai kula dasu ba sabo da motarsa tana tsakiya,Shukura kuma Bata taba zato ba tunaninta bazai zoba sabo da ta cire Rai da ganin Ahleef,kuma wannan kalar motocin Bata sansu ba Sam,tunaninta ma ko Gomna zasu Kai ziyara kauye,kamar suna tsere da motocin,ga akwatunanta a gaban me Machine filfila wuta kawai suke Suma.

sunzo garin dai dai Yar kasuwar kauyen karama dai dai jikin wani container me charji suka tsaya Machine ya lalace,Shukura tace nazo gida ni bari na sallameka na karasa a kafa,ta sauke kayanta tana lalubo kudi ga rugugin kidan da me chaji ke sawa ya cika kasuwar Baki daya,Sai da su Ahleef suka shugo garin ya bude Ido ya fara kallon gefensa dai dai inda kida ke tashi kamar ance ya kalla itama Shukura ta bawa me Machine kudi kenan ta juyo sukayi Ido biyu ta glass dinsa na mota,ai da sauri ya sauke Glass don ya tabbatar, itama ta kafeshi da kallo wai kuwa shine Anya? Motocin ya bawa Umarni su tsaya, Shukura tayi Masa zuru da Ido har ya bude mota da sauri ya fito a nutse kamshi ya cika wajen kaf, Shukura ta tabbatar shine Bata San sanda ta washe Baki ba kawai sai da ta bi kidan me chaji tayi girgiza da rawa duk mutanen da suke kasuwar da wajen suna kallo hankalinsu ya Kara dawowa wajen sunga Shukura tana rawa,Ahleef ya harde hannaye a kirji Yana zuba Murmushi Yana kallo Shukura tasa kafa ta daki akwatunanta suka watse tace kun zama old version, Ahleef ya Kara sakin dariya ba shiri tare da takowa wajenta itama ta taho da gudu kamar wata yar basketball Haka ta daka tsalle ta makalkaleshi, da badan me karfi bane da sai sun zube a kasa,Kara kankameta yayi Yana manna Mata kiss a ko Ina na jikinta,mutane kuwa sun taru kamar Ana kallon wasan dambe kowa ya zura Ido Ana mamakin ina Shukura tasan wannan Baturen me kudin?ko shine Mijin nata?ko kuma kwartonta ne,wasu kuma suna jinjina rashin kunya da bariki irin na Shukura da wannan saurayi,wasu ma sai rufe Ido sukayi wai baza su iya gani ba kunya suke ji.

Sun dauki Lokaci me tsawo kafi su rabu da juna,Shukura taja gefe tace uhmm kayi kiba da kyau kafi da kana can ka manta Dani,ke kuma kin Kara girma kalli yanda kikayi tsayi let's go muyi magana later.

Mutanen wajen Shukura ta kalla tace wannan ne Mijina Ahleef ku sanar duk me Bina bashi yazo kofar gidan Yafendo ya karbi kudinsa,Ahleef ya dinga dariya wato bashi aka ci Masa haka,da kansa ya bude Mata mota ta shiga Shima ya shiga guard ya rude suka karasa cikin garin kofar gidan Yafendo,kafin kace Me mutane kowa har matan aure an fito ganin Ahleef,masu bin bashi sun cika damkan suma,Iro da Yahaya ne suka fara arba da Ahleef,Shukura tace to ga Mijin,Iro yayi dariya tace bayan kin bar gari abokinsa da iyayensa sunzo,Nan Iro ya Bata labarin zuwan Farhan dasu Baba tare da alkhairin da sukayi musu.
Shukura tace ikon Allah kenan, Ahleef ya rike hannun Shukuransa kakam.
Yafendo tuni an tattaro kan Yan uwa harda kalan dangi sunzo ganin Ahleef me kudi kamar Dan Shugaban kasa shine Mijin Shukura,ga kyau kamar aljani,Kawu saida ya firgita,dangi suka fara Nadama harda bawa Shukura hakuri,Shukura a fili tace yanzu ba da aka ga Naira,da kuwa ai Mahaukaci ya fini mutunci,me zaku Gaya min,wlh kawai kuna Yan uwana Amma bazan ga mutuncinku ba dama dama Yafendo da yaranta.
Ahleef ne ya Dan matse hannunta wai tayi Shuru,tace baka San wacce wahala Nasha ba kawai ka kyaleni,Yanzu kowa ya yarda Ina da aure,kuma ga Mijina,sannan zan iya siye garin Nan kaf,zan iya maida wasu Bayi,Ba danginta ba har Yan garin sai suka fara bawa Shukura hakuri kar ta siye garin,Ahleef ne ya kwantar musu hankali da wasa take muku fa,Yafendo ta gabatar da kowa wajen Ahleef haka kawu sai waazi da Nasiha yake musu,cikin masu ganin Ahleef harda Megari da Liman, Megari a ransa sai Allah ya Isa da tsunuwa yake jawa Ahleef tafi dubu.

Bayan an Gama gaisawa Ahleef yayi musu ruwan kudi, Shukura Bata so ya bawa danginta ko kwandala ba irin abinda suka yi Mata,
Sai fushi takeyi,karshe tace Ina masu bashi,Nan suka cunkuso ciki Suma aka fara da Megari dubu goma,Ahleef ya bada,tace Ina me tsire dubu biyu ne nasa,Ahleef yace nasan za a Rina,tace me balangu da me kifi dubu daya daya,Aishalle adari biyu Amma Bata dubu goma kyauta,Me chemist kudin paracetamol da pad,Ahleef ya bude mota kawai kudi yake irgawa Yana mikowa Ana ta biyan bashi mutane masu yawan gaske,da ya gaji ma kawai wajen kudin ya bude Mata ta karasa da kanta,Wanda zata yiwa kyauta tayi Masu bashi a biyasu har ta Gama kaf,dariya ta bashi sosai yanda ta kware wajen cin bashi sabo da tana da shi tasan zai biya.

Ahleef yanaji Ana Zancen Dinki Ahleef style dama Farhan ya bashi lbr kawai dariya yake a ransa abinsa,har ta Gama tace kazo muje ko zaka ga garin?Ni pls ki shigo mu tafi Abuja dare fa zaiyi Bae ya furta cike da Shagwaba, Murmushi tayi Shagwabar tayi Masa kyau, tace to Dan jira Ni pls ta shiga gidan Yafendo,Bata tsaya jiran komai ba ta fada wanka,bayan tayi wanka ta fito ta canja atamfa cikin kayanta wata sabuwa sau daya ta sata tunda tazo da kayan garin,wata black and blue ce dinkin Riga da skert sun kamata das ba karamin kyau tayi ba,mayafi Baki ta dauka da wani flat shoe baki me tsada duk dama ta sako su cikin kayanta Amma Bata Sa ba sai yau,kamar ka sace ta,yau wankan da kwalliyarta ta dabance,sai gashi ta fito a Yan matan Abuja masu ji da kansu, Yafendo anji kudi Har ta fita ta harhadowa Shukura magungunan tsumi iri iri ta karanta Mata yanda ake amfani dasu ta Bata Leda guda, Shukura sukayi sallama tace watarana zata zo ta daukesu suga gidanta.
Duk ta Dan yiwa dangi sallama an yafi juna,Kawu ma an biyashi kudin kazarsa da ta cinye musu.

Ahleef yaga yanda Shukura ta dau kyau gaba daya ta Kara wani kyau gashi ta sake girma komai ya Kara cikowa sosai sabo da Shan madarar shanu kullum tayi wani fresh kamar ba a kauye take ba.
Bodyspray din Yafendo ta fesa me dadin kamshi,Ahleef ji yake kamar yayi tsuntsu ya gansu a Abuja masau kinsa Hotel,suna tafiya a mota kasa kyale Shukura yayi sai da ya fara kissing din lips dinta Yana lasar Mata wuya,ita kuma tana hanashi wai kunyar Driver pls ka Bari,wani wuri ya Danna kawai sai ga labile masu kyau sun sakko suuuu kasa ya raba tsakaninsu da driver.

Ko Ina ya rufe saisu kadai a bayan mota,jikinsa ya jawota ta kwanta,Shukura tace wai har yau Yaya baka canja halinka na lashe lashe ba?,Murmushi yayi tare da cewa ai ke za a tambaya har yau Baki canja halinki ba kin San mene aure me akeyi,wai ma Ina ciki na Dana yi Miki? Kunya ce ta kama Shukura tace ai yanzu fa watansa biyu da sati Uku bai Isa fitowa ba ,bakiyi period ba? Nayi Mana ai matar Iro tace wasu idan suna da ciki basa daina period itama haka takeyi idan tana da ciki,kaga maybe nima Haka ne.

Ahleef yace uhm gaskiya ne to ki lallaba min Babyna Allah yasa ki haifo min mace,Shukura ta boye fuskarta a kirjinsa tana dariya kasa kasa tace nima nafi so na haifo Mace ta,Sabo da me kike son mace ya tambaya yana kallon fuskarta cike da zallan so,tace Sabo da na dinga yi Mata kitso,Ina shafa Mata Jan Baki, Ahleef yace to ki dage ki haifo ta tunda har nayi Miki cikin,Shukura tayi Murmushi tace tam,wannan kuruciyar ta Shukura nishadi take bashi.

Dankwali ta ya zame ya shiga Shafa gashinta me ssantsi yace Farhan ya bani labarin yanayin da kika shiga I'm really sorry ban sani ba,Bakinsa ta rufe Masa da tafin hannunta tace never mind nasani shi yasa na jiraka a kauye nasan zaka zo,Nan ta bashi labarin abinda bai sani ba harda rayuwarta a gidan Yan fashi, suna ta dariya Shukura na matashi da bindiga a cikin pillow Bata sani ba.

Sai wurin Magrib suka Isa Abuja Hotel din daya sauka suka tsaya,Shukura tace ban gane ba Ummafa da Baba Ni nake son gani Dan Allah a kaini wajensu Kai sai ka zauna a Nan pls, u are not serious yaja hannunta suka shiga ciki bayan yayi musu order abinci, Room din suka shiga Shukura taga akwatunansa guda Hudu manya a ciki tace nifa bani da kayan sawa na bayar da nawa a kauye,na ba matar Iro data Yahaya kyauta.
Akwai kayanki a Nan karki damu.








Asmabaffa
[7/22, 1:13 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO








46-50








Official







By
AsmaBaffa










Baki Shukura ta turo Masa tana wata Shagwaba me gigita hankalin me gida ni dai Umma nake son gani, ran Ahleef ne ya baci shi Bata sonsa Bata son ganinsa sai su Umma,yazo tun daga wata kasar sabo da ita,yaje ya dakko ta amma tana maganar wai su Umma take son gani,it a ya kaita can shi ya zauna a Nan, a fusace ya kalleta,kallo daya ta tsorata tasan Lallai ransa ya baci da kalamanta,sai yanzu taga ita ma fa Bata kyauta ba, batayi Masa adalci ba, Baki ta bude da niyyar magana kafin tace komai ya shige Toilet abinsa.

Fushin nasa har mamaki ya Bata, tana Nan tsaye ya Dade ya fito daga wanka ya isketa bai ko kalleta ba, itama kasa magana tayi sabo da tsoro taji kar ya masge ta,toilet din ta shiga itama tayi wanka,kasa daura towel tayi sai skert dinta ta maida tare da jawo shi sama kamar tayi daura kirji ta yafa Mayafinta sannan ta fito lokacin ya Gama shirinsa cikin kayan bacci ya daura jallabiya ya tayar da sallah abinsa.
lotion dinsa ta shafa me kamshi ,gashinta ta busar tayi amfani da wasu mayukan gashin nasa ta gyarashi sosai,sannan ta dakko powder dinta da ta shiga mota da ita ta Dan shafa sama sama ta shafa lipgloss sannan ta maida kayanta itama ta fara sallolinta, bayan ya idar tare da adduoinsa abinci ya fita ya karbo Wanda yayi order, fuskarsa ba rahma ya dawo lokacin ta idar da sallah kawai ya ajiye Mata nata ledar abincin ba tare da yace komai ba.

Shukura kamar zatayi kuka ta kalleshi Amma bai ko bi ta kanta ba,tana gani ya zare jallabiyarsa kayan baccinsa masu kyau suka bayyana 3qtr wando da Riga armless farare ba karamin kyau yayi ba,sai kamshi yake fesarwa.
Laptop dinsa ya kunna ya fara aiki a ciki Yana cin abincinsa hankalinsa kwance Amma hankalinsa Yana kanta kawai dai fuskewa yakeyi Dan ya nuna Mata kuskurenta.

Shukura taki taba ko ledar abincin duk kwadayinta,tana zaune bisa sallaya tayi Shuru,Yana kallonta ta gefen Ido har ta gaji ta bude abincin duk dadinsa Bata iya ci da yawa ba,ta mayar ledar ta mike tayi brush ta fito ta koma inda ta Bari ta ci gaba da zama tanaso tace ya Bata Kaya ta canja tana Jin tsoronsa, tana kallo ya Gama Shima yayi brush ya dawo da niyyar kashe light zai kwanta.

a hankali Shukura ta iya furta Dan Allah Ina kayan nawa zan canja,da yatsa ba tare da yayi magana ba ya nuna Mata wasu akwatuna har uku,mamaki da murna ya kasheta Bata San sanda ta saki Murmushi ba,wato tsarabarta ce tunda daga kasar waje ya dawo,kamar tayi tsalle ta rungumeshi Amma ba hali idan ma tayi yanzu zai ce saboda kayan daya Bata ne, sai kawai ta share ta jawo karamar ta bude taci sa'a inner wears ne da kayan bacci a ciki, tunawa tayi ta taba ji Yan schl dinsu Mata suna hirar idan anyi aure kayan bacci na Jan hankali ake sawa,masu kalar nuna tsiraici ko fushi me gida yakeyi da Kai sai ya daina,yau ga Mijinta na fushi da ita ya kamata ta gwada ta gani.

Wata light pink ta zabo da kadan ta Dan sauka tudun mazaunanta shara shara, hannunta siriri kamar net Haka take tana wani sheki da kyalkyali Wal Wal ta hadu karshe me tsada ce ta gaske.
Ahleef bai kashe light ba da yaji ta tambayeshi Kaya zata canja sai ya bar Mata hasken ya koma saman bed yana zaune ya jingina da fuskar gadon Yana Shan Jinger tea Yana latsa waya ta wani bangaren Yana satar kallon Amarya.

Mayafinta ta daura a jikinta ta cire atamfar tare da linkewa sai kuma ta saci kallon Angon nata sai ta ka kalli rigar tana so ta samu wajen da zata buya ta sa kayan, Yana kallonta kawai sai ya kwanta tare da kashe wayarsa ya lumshe Ido kamar bacci ne ya kwashe shi,a hankali tazo jikin gadon Dan ta tabbatar yayi bacci sai ta ja yatsan kafarsa a hankali taga ko motsi baiyi ba,har zata rufa Masa bargo sai taji tsoro kar ya farka ya zaneta dama cikin fushi yake.
Zip din rigar ta zuge ta saka abarta saman gyalen data daura sannan ta janye gyalen ta gyara zaman rigar a jikinta,subhannallah kamar a jikinta aka Dinka,ba karamin kyau tayi ba kamar wata baturiya,hips din Nan kamar zai Fado,Haka kirjinta a cike taf,cinyoyin lukuta lukuta suna sheki, lallabawa tayi zuwa jikin Mirror ta kalli kanta ita kanta sai da ta kalli kanta ta Kara tare da godewa Allah sannan ta saki gashinta ta Kara tajeshi wai yau sai ta koma Baturiya, sai ta tsaya a mudubi tayi ta kallon kanta tana juye juye, kirjinta ta kalla a fili tace kuci gaba da jiran jariri a haifo shi,Ahleef Wanda ke kallonta Yana jinta bai San sanda ya danne Bakinsa ba sabo da

1 Comments On JIN DADI SABO
avatar
mahamane-noura

2 years ago

Reply

Asalama alaikum, dan Allah yane ake sauke littafin akan waya

Please Login or Register in order to submit comment