Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Frnd dina nan idan zaki aureshi yana sonki,yaushe zakiyi aure ? Shukura kunya ta kamata ta tace da dai Inna tana da rai ne sai aje a tambayeta yaushe zasu yi min aure,ta furta tare da rufe ido tana murmushi,Ahleef ma murmushi ya saki yace to idan kin shirya aure ga abokina yace kina da kyau kin masa,idan zai dinga siya min kayan dadi to zan aureshi ta Mike ta bar wajen da sauri ta koma Bedroom dinta wai kunya.

Farhan ransa idan yayi dubu to ya baci abinda Ahleef yayi masa a gaban yarinya,a ransa yace amma tunda yayi masa haka shi kuma yanzu zai karbi soyayyar nan da gaske kuma wlh indai tana sonsa auranta zaiyi tunda yayi masa haka,a fili yace Good for u, ni zaka yiwa haka a gaban yarinya zaka zubar min da mutunci,ko sonta nakeyi haka zan fada mata direct? Idan kaine zanyi maka haka? Fine ni kuma da gaske zan fara soyayya da ita ka jira gobe ta shirya zanzo zance,Ahleef ya kalleshi yana murmushi yace kaifa kace kana sonta ni kuma na hadaku shine nayi laifi dama dan ka sota ka aureta na hadaku,tunda kace kana sonta gida bai koshi ba za a kaiwa dawa ba,Kullum ma kazo zance kuma zan kai maka ita gidan Momee ta rike maka ita ka aura,Farhan yace to dan Uwarka ka kaita ka gani kuma ina nan zaka zo kasameni banza dan iska, Ahleef yace kaine dan Iska daga ganin fara me kyau shike nan mayen mata,ni kasan yanzu ba abinda zanyi da mace ko a kafa aka daura min ita sai dai na kaita bola,Girgiza kai Farhan yayi yana dariya dan abin dariya ya bashi,Ahleef da baya surutu sosai amma shine daga zance daya akan yar magana ya hakikice haka lallai zai koya masa hankali.
tashi ka tafi malam dare yayi,korata kakeyi ma yau kenan to dama kwana zanyi ina kallon Matata tana zirga zirga, dariya Ahleef yayi yace ga bedrooms ka zaba Wanda kake so me mata na Shukura ikon Allah, Kallonsa Farhan yayi kawai ya Mike ya fita bako sallama ya bar gidan.











AsmaBaffa
[7/22, 1:12 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO







9







Official








By
AsmaBaffa










Pls Wanda sukayi Sharhi suka ga banyi reply ba SMS nasu waiting yasa min ayi min hakuri da Uzuri kuma aci Gaba da Sharhi dan Allah fans.


ZAINAB ATIKU SALAMA, AUTA and MAMAN MEENAL this page is for u Sabo da Jin dadin Sharhinku.

KHADIJA A HAMZA da JANNAT jinjina da godiya me yawa.











Washe gari da safe Sunday Ahleef yana gida,Shukura taki yarda ta fito karma ya ganta wai kunya take ji akan maganar Aure da yayi mata tun jiya,tana so ta fito amma ta kasa gashi yana Palon,Leko da kanta takeyi sai ta koma da sauri tana yarfe hannu ita ya za ayi yau ta kalli Ahleef, yau ji take baza ta iya yini a gidan ba, gwara ta fice yawonta har sai dare ta dawo, fuskarta ta rufe da gyale yana Palon sai gani yayi Shukura ta fice da gudu tayi waje,ya tsorata domin kamar wacce Aljanu suka tasar mata,tana fita kamar yanda take yawonta da haka ta dinga yawo a kafa tana hutawa har Dare yayi,ta dauki hanyar komawa,tana kusa da layin sai ga Farhan ya shararo motarsa zaije wajen Ahleef, kallo daya yayi mata ya gane itace,slow yayi tare da sauke glass ya danna mata Horn ta juyo,sai da ta kalleshi ta gane kuwa shine kawai sai ta rufe fuska, yace tazo ta shiga mota taki yarda sai ma sauri data kara tana tafiya yana binta a mota,babu rokon da baiyi mata ba amma taki shiga sai da kyar ya samu ta Shiga, Ahleef kuma yana gida hankalinsa ya tashi yaga tun safe ta fice da gudu kuma har dare babu labarinta karfa Ko wani abu ya sameta,yana samansa jikin window kawai compound yake kallo, Farhan aka budewa gate ya shararo motarsa ciki,Shukura ya fara gani ta fito daga motar, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya fito zai tarbi abokinsa, Ahleef yasan dole a hanya Farhan zai hadu da Shukura,Farhan kuma abinda yasa ya nace sai ya dauki Shukura Sabo da ya batawa Ahleef rai dole sai ya gano gaskiyar Ahleef ko son Shukura yakeyi yasan halinsa da zurfin ciki,cike da kunya ta shigo Farhan yana gabanta kamar Saurayi da budurwa, Shakura da Ahleef suka hada ido dake Ahleef maye ne da ido ya mata magana ina taje dake itama yar duniyace ba wuya ta gane sai ta mayar masa da ido Cikin kankanin lokaci,Farhan bai san me akeyi ba,bai taba tunanin zasuyi haka ba da idonsu zai kalla, sai yaga kawai Shukura ta wuce abinta,Farhan ne ya dameshi shi ya bashi abinci yunwa yake ji,so yake wai yaga Ko Shukura ke masa girki, idan itace yasan dole zai sata tayi yau fa sai ya kuresu,Ahleef yace sai dai kasan kaci Indomie,to kasa Babyna tayi mana me dadi mana, Ahleef dariya yake a ransa Sabo da ya harbo jirgin Farhan,Sai ya shiga kitchen da kansa ya iske Shukura ciki tana dafawa kanta abinci wai tuwo zatayi miyar taushe,Ta yanka kabewa kawai ta cika tukunya da ita ruwan cikin katuwar tukunya har baki, har tayi hadinta gaba daya komai ta zuba har Allayyahu du a ciki kuma tukunyar ko tafasa batayi ba, Gashi sai yanzu ma ake gyara nama za a zuba, naman ne karshe,Ahleef kallonta kawai yakeyi duk tayi kaca kaca da kitchen din,ko ina kwanikan aikinta ne ake ta yi,duk ta firgita kanta Bata gane me Ahleef yakeyi ta cikinta takeyi tun safe Bata ci komai ba, Ahleef gefe guda yake nasa,duk kamshin jikinsa ya kara gigita Shukura,Tukunyarta katuwa data dora ya bude kamar Wanda yaji kamshi ya wani lumshe ido tare da cewa uhmmmm... Kaji irin na manyan mata,mata fa suna girki anan yanzu naga girki anan Amma dai za a sammana wannan kamshi haka,Dadi Shukura taji an yabi girkinta ta Washe dan bakinta tace zan San muku ka daina budewa kar miyar ta lalace,Dariya ta cikawa Ahleef ciki,yace lallai zaiyi dadi kam ayi sauri a gama muna jira,me kake dafawa kai? Yace uhmm Indomie da kwai zamu ci kafin ki gama naki,kawai sai yaga ta kashe gas tace ni bana son girkina naku zanci ga me kwai ai yafi dadi wa zai hada abinda aka dafa da kwai da kuma tuwo,Ahleef yace sai kin mana tuwon sannan ki San mana nima na baki namu,baki ta turo tana kunkuni ta kunna gas taci gaba da girki,kawo na tayaki nima sai na koya Ko,tace to zo ka tayani wanke kwanikan nan,suka fara wanke wanke Shima ya fuskanci Bata iya sosai ba, sai labari ta fara bashi,Sai ga Farhan ya shigo shima ganin kwakwaf,Shukura ta fara labarinta tace Sanda Inna da Baffa suna da rai ko, Farhan yace uhmm muna ji,tace kai baka tsayawa kaji lbr sai surutu ka bari mana kaji abin tausayi sai kayi kuka,Inna ce dai Inna ce watarana da karanbaninta wai ta danawa bera tarko a karkashin gado zata kamashi Sabo da yana dauke mata soyayyen namanta, kwana daya biyu ta manta ashe tasawa bera tarko sai ta tura hannunta kasan gado wai zata ebo naman sai tarko ya saki ji kake bas ya danewa Inna Hannu ya kamota, ta fito dashi...tun wajen Suka fara tuntsira dariya Bama kamar Farhan,tace wai ku ance ku tsaya mana kuji to,Ahleef yana dariya yace muna ji, taci Gaba Inna dai da tarkonta a hannu ta kasa cirewa gashi ni na tafi yawo na,Baffa kuma yana kiwo gashi ba mayafi a jikinta baza ta iya fita haka ba,sai ta tsaya jikin katanga ta fara kwalawa mutane kira babu Wanda yaji dama muryarta kamar ta tsuntsu haka take idan tana magana Volume baya daduwa baya raguwa,kuma wai sai dai tace mutane...mutane kuzo baza tace jama'a a taimaka ba,Baffa ne ya shigo ya Cire mata Allah sarki hannunta ya kumbura Inna babba ce fa amma ta kama kuka,kaiiiii ta bani tausayi, Farhan suka dinga dariya,karshe ya tabe baki yace to shine me ? Shike nan labarin ? Ahleef yace kai amma akwai tausayi gaskiya,Allah sarki Inna,Shukura tace Kaji me Imani amma banda kai ta nuna Farhan Wanda ya fice daga kitchen,Tukunyarta har yau Bata tafasa ba, Amma ta bude sai juyawa take tana dandanawa,Ahleef yace muna jira fa, zuciya tayi wai tukunyar ta bata haushi akan me Bata tafasa ba, shine ta kwala murfin da kasa tace na gaji wlh ni bazanyi ba, Kin girma da iyayenki me yasa du baki iya girki ba,gyaran gida kawai kika iya taya zaki rike mijinki idan kinyi aure,kicin kicin tayi da fuska tace kai in dai ba me kiba bane tsab zan iya rikeshi wlh ina da karfi fa kalli damtse na ta dago hannu, Ahleef ya dinga dariya,tace yar gata ce ni fa a gida bana komai ko zanyi Iyayena hanawa sukeyi,gyaran gida nafi iyawa Sabo da kullum idan Bata nan inayi,Kai ya jinjina tare da cewa to gashi yanzu Sun rasu Sun barki ya za ayi ke nan, to ba sai ka koyamin ba tunda ka iya, Bani da time ni kinma kusa bar min gida kiyi shiri Next wk,gabanta ne ya fadi tace dan Allah kayi hakuri ka kara min ko wata goma ne ina yin kudi zan tafi kuma na kusa saura kadan.

Indomie ya juye a plate Uku kowanne da kwai biyu ciki dafaffe,plate guda ya mika mata,ya dauki nasa dana Farhan yayi waje,a kitchen din ta cinye nata sannan ta gyara kitchen din tas ta zubar da miyarta da takeyi ta wanke tukunyar sannan ta wuce palon wajen su Ahleef, Inner wears ta gani sababbi latest an kawo na maza da yawan gaske Ahleef ya zaba Farhan ma ya kwashi nasa,Shukura ta koma kusa da Ahleef ta zauna tana ta kallon kayan, Farhan yana kallonsu yanda Ahleef ya Bata rai sosai dan kar ma Shukura tace zata taba kayan,mikewa Farhan yayi tare da cewa saida safe ya,ka fasa kwanan ? Ahleef ya tambaya,Ae Bazan kwana ba a cika min ciki da Indomie Budurwata sai da safe,Shukura Kunya ta rufeta da kyar tace Allah tashe mu lfy,Ka gaida Mama zan shugo gobe cewar Ahleef.
Shukura ta kalli Ahleef a hankali tace tace Dan Allah bani guda biyu ina so Harara ya watsa mata,bata kara cewa komai ba ta Mike tayi Dakinta.

Shukura an gama Shiri ana murna taji cewar Ahleef gidan Momee zai kaita ta zauna can wurin Inna Saudatu,cikin Shiri ya fito yana zuba kamshi yasha wani yadi me tsada da kyau, Kayanta suna leda tabi bayansa har mota sanye take cikin doguwar rigarta Pink, yauma Driving zaiyi da kansa,tana shiga yaja motar,Sai gani tayi ya tsaya a wani katon gida Farhan ya fito da trolley har biyu manya ya saka musu a bayan mota,Ahleef yace bazan shiga ba ka gaisar da Mama,gidan su Farhan kenan,Shukura a ranta tace dole kuyi wulakanci wannan irin kudi haka,Shagon dinki suka tsaya na mata taga nan ma an sa musu katuwar Ghana Must go a bayan mota,Ahleef ya ja mota suka tafi,bai tsaya ko ina ba sai wata schl me Arabic da boko ba nisa da gidan Momee ya shiga yayi mata registration da komai,makaranta ce me tsada Sabo da a kauye tayi makaranta yace a sata a ss1 a dawo da ita baya.
Bayan ya gama yace ga makarantar da zaki dinga zuwa an gama komai Uniform dinki yana Cikin kayanki akwai komai a ciki,Shukura Bata kaunar zuwa schl dama tun asali Gata da basira amma tun iyayenta na da rai sai da kyar take zuwa, wata waya me kyau da tsada amma yar Nokia ce Bata WhatsApp kawai ta kira ce yace gashi akwai number ta a ciki ko me ya faru ki sanar dani,kuka ta fara yi yanzu kullum sai taje makaranta,mene kike kuka? Tace ni tsoron yan birni nakeyi kuma kullum sai naje makaranta,kin fi so a barki cikin jahilci kina yiwa mutane kauyanci baki iya komai ba? Shuru tayi a mota tana shesheka har suka je gidan,ta fito Cikin yan aiki wasu suka shigar mata da kayanta kaf na Boot part din Saudatu,Tana mamaki ashe duk kayanta ne haka aka zuba,Ahleef yace jeki ciki zan wuce Office Sauri nakeyi,Murmushi tayi tace na gode Allah kara arziki sai kuma ta fara hawaye,lfy ? Tace shike nan na daina ganinka kullum kullum waye zai siyo min kayan dadi? Dan Allah ka maidani gidanka mu zauna tare ni nafi sonka yanzu akan Saudatu,dariya ta bashi yace indai akan kayan dadine Saudatu ma zata baki kici,ai ita tsohuwa ce irin naku na yan boko nake So,to jeki idan kina so ki kira wayata,yanzu baza ka dinga zuwa ba shike nan ? Yace da Momee tana nan kullum sai kin ganni,Amma to ai ga Inna Saudatu ko,a'a akanta ni bazan zo ba kullum to budurwarka fa wacce nake zanewa ? Ko dan ita kazo mana, yace a'a ba haka nake soyayyata ba ni kullum sai naga budurwata,to yanzu idan ta dukeni fa ko ta zagi Inna ? Ahleef yace na baki wuka da nama ki mata duk abinda kikaga dama, Shukura da kuri tace Allah ballata zanyi ba ruwana,mota ya shiga tana daga masa hannu ya bar gidan yana dariya, duk abinda sukeyi kan idon Niima,tace Alhmdllh dama tazo har gida da zan kassara rayuwar yarinya matsiyaciya.

Shukura da gudu ta shiga part dinsu wajen Inna Saudatu tare da rungumeta ta baya,ba Zato Saudatu taji Shukura ta fada a jikinta tana murna,Saudatu dama tasan da dawowar Shukura Ahleef ya sanar dasu,kallon part din Shukura tayi komai me kyau ne daki biyu da toilet ko Wanne da palo sai kitchen kamar bangaren Amarya haka wajen yake, Bayan Sun gaisa suna hira Saudatu ta yarda lallai Shukura yar uwar Ahleef ce tunda ba Momee ce ta haifi Ahleef ba, sannan taji yan aiki suna cewa Ahleef dan uwan Momee ne ta raineshi.
Trolley Shukura ta bude kayan sawa ne na mata babu kalar da Babu ciki, har Bra duk ya siya mata kamar yasan size dinta,komai dai dai ita,haka dinkuna dake Ghana mustgo laces ne Atampopi,Shadda dasu materials iri iri masu tsada da kyau dinkin kuma dai dai ita kamar an aunata na zamani iri iri, sai mayafai takalma da jakankuna, Uniform dinta kala hudu Har Sandals da schl bags kala uku da littatafai komai an hada ba abinda zata nema.

Inna tace Mashaallah gaskiya Dan uwanki yana ji dake wannan kaya haka kamar lefe,murmushi Shukura tayi ta kwanta tana latsa wayarta,sabo da Baffanta yana da waya tun tuni tana dauka shi yasa bata Bata wahala ba ta gano kanta,Tana Kwance Inna tace tashi mu kara gyara gidan nan sai muyi girki,Shukura ba musu ta Mike Sabo da tuntuni tasan Fadan Inna idan tace ayi ka zauna wasa masifa zaka sha Bata daukan raini kuma Bata bada kofar da zaa rainata sai irin su Hafcy da Niima marasa Tarbiya.
Shukura ta zage akayi gyaran duk inda baiyi dai dai ba sai Umma Saudatu tasa ta tisa wajen ta iya dole,Duk ta gaji likis,Umma Bata bari ta huta ba tace girki zasu yi yanzu, suna girki Umma taga Shukura Bata iya ba, haka ta dinga fada sai da ta koya mata dole sannan tace tayi girkin a gabanta tana Guiding nata,tanayi Umma na koya mata,ta kusa gamawa ta dauki waya ta latso Number Ahleef,tayi Ringing me tatsawo sannan ya dauka Sabo da yayi saving Number din nata,yana dagawa ta kwalla da karfi tace girki nake ta yi kai tun dazu,dariya ta bashi sosai da kyar ya danne yace Dan Allah fa? Na rantse baka ji kamshin bala'i ba Allah ta furta cike da murna, murmushi ya saki yana rubutu a Office dinsa yace to ya da dadi? Ban Sani ba Umma ta hanani dandanawa tace ba a dandanawa wai sai anjima,yace wow Har miyau na ya tsinke ya zubo,dariya ta kyalkyale da ita tare da cewa yau ga Babana wajen kwadayi,Bari idan Umma ta barni na Dandana to zan kiraka na fada ma irin dadinsa Ko kasa Driver yazo na zuba ma ya kawo maka Office ai dai ni ba kazama bace zaka ci,to yace kawai ta dinga Murna zaici girkinta karshe tace ka fadawa Abokinka na manta sunansa me suna kamar za ace Fari,Oh Farhan ? yawwa ae shi kace na iya girki ina ta yi,Dariya Ahleef ya saki ba tare da ya shirya ba yace Ok zan fada masa yazo yaci girkin Amaryarsa,cike da Shagwaba tace kaifa ka iya sa mutum kunya Allah ai tunda Baffa ya rasu to ni wa zai daura min aure,yace danginki mana,baki ta tabe Auren dole zasu min fa na tsere ka bari watarana zan baka lbr kaci dariyar kawunmu yanda na siyar masa da Akuya naci dadi da Kudin.to Allah kaimu yanzu jeki wajen girkin idan ya kone bazan ci ba,kashe wayar tayi,Umma tace keda Yayan naki ne ? tace ae mana lbr na bashi na iya girki,Dariya Umma tayi sosai,Shukura ta kafeta da Ido tare da cewa Umma wlh kama kukeyi da Yaya sosai,Umma tace rufa min asiri Tsohuwa da ni kina hadani da me kyau haka,Baba ne ya dawo daga Office ya gama aikinsa har Ahleef ya sallameshi ya dawo gida ya Iske Shukura da Saudatu suna girkinsu,Umma tace gafa Shukura yar Uwar Alhaji Ahleef ce wacce nake baka lbr ashe yarinyar nan yar uwarsa ce amma take zuwa muna soya doya a titi,Baba yayi dariya Shukura ta tsura masa ido tace yeee... Baba ma Irin yaya Ahleef ne kalli wlh Dimple dinku iri daya har hancin kamar wa da kani,Baba yace haka ake ta fada a Office kuma kama haka take yanzu idan za aje Turai sai kikaga mai kama dake Shukura ai duk Dan Adam ne yan uwane shi yasa ake samun wani yayi kama da wani, suna ma wani iri daya,Shukura tace hakane nima sanda muka je makka naga me kama dani Balarabiya,Baba yace gaskiya yayanki mutumin kirki ne,Shukura tasan karya tayi tace uhmm kawai tare da canja zancen tace Baba harfa Muryarka da tasa wlh iri daya,Umma cikin wasa tace ke kin damemu da kama kama fa, Sun dade suna Hira har suka gama girkinsu.
Lafiyayyar Fried rice tasha kayan hadi iri iri, ga hadin Couslow sai soyayyar kaji,kunun Aya sukayi da lafiyayyan zobo, duk Umma yau ta koyawa Shukura su sunyi tare.

Umma tace to Shukura kinga yanzu mun gama girki sai Yayanki kije bangaren su Momee Ki karbo foodflask da za a zuba masa kinga mu flask dinmu duk da masu kyau ne amma irin nasu na daban ne,kije ko yan aiki, ko Niima ko kuma Latifa su baki kizo a hada a bawa Driver ya kai masa.
Tsoro ya shigi Shukura yanzu fa ta dawo gidansu da zama,gashi ta daki Latifa watarana ga abinda tayiwa Niima rannan wai wai Yau ya zatayi.Shukura ta kware wajen satar Hanya ta shiga waje ba tare da kowa ya ganta ba ko Bata San hanyar shiga ba sai ta nemo ta da kanta,haka tabi ta barauniyar hanya ta hanyar Garden har ta samu nasarar shiga cikin Palon ba kowa,ta lalubi kitchen ta shige da sauri ta tarkato duk abinda take so,har zata fita ta bude fridge dinsu na kayan sha,ta dauki wani hadin lemo da Niima ta zauna ta Bata lokaci wurin hadashi Sabo da zatayi bako,yayi masifar dadi kuwa cikin wani juck na roba me kyau, Shukura ta bude juck din robar karami dashi ta kurba taji dadi,kawai ta kafa kai ta shanyeshi tas ta Ebo ruwa ta cika juck din ta mayar inda ta dauka, wani flask ta gani hadadde karami an shirya abubuwa kusa dashi a saman tire,sai ta bude a hankali tayi arba da farfesun Hanta da Koda kawai sai ta fara ci taji dadi ta dinga ci tana cewa nasan na wannan yan iskan ne,da Momee tana gidan bazan ci ba tare da na fada mata ba, amma tunda su Niima ne kadan zan rage,dama Shukura Bata ci komai ba,jira take sai tayi sallah sai taci Wanda suka dafa da Umma to yanzu ta fasa cin nasu sai zuwa dare yau Allah ya ciyar da ita nasu Latifa,baifi Guda Shida ta rage hantar ba duk tacinye,romon ma bata barshi ba sai da ta yagi bread a kitchen taci dashi kadan ta maida komai inda yake ta dauki kwanikanta ta kara bi ta barauniyar hanya ta koma Part dinsu,Niima tana daki sai kwalliya take zubawa,taji motsi tunaninta yan aiki ne suke zirga zirga, Latifa ma yau Sunday tana gida tana jin karar kwanika a kitchen amma tayi tunanin Niima ce.

Bakon Niima yazo taci uban wanka kamar zata je Dinner, sai da taje ta shigar dashi palon baki sannan ta dawo kitchen domin kai masa abinci,bata duba flask din da hantar ke ciki ba kawai ta dauki katon tire din data jera komai a kai,juck din kuma Shukura ta cikashi da ruwa nan ma Bata duba ba ta daura saman tire komai da komai taje wajen babban bako tare da ajiye masa a gabansa tana karairaya, saurayi yace yau zanci dai girkin Amaryata da ake ta fada min a waya za ayi min. Murmushi ta saki tace yau gaka gashi sai ka manta hularka, yayi dariya baki da dama Amarya ta shi yasa yau ba yanda Mama batayi dani ba kan naci abinci wlh naki ci Sabo da nasan me Amaryata zata shirya min.
Niima tayi wani fari sannan ta dauki plate da spoon bari na zuba maka kar yunwa ta illata min kai,tana Bude flask wayam sai yanka shida rak a ciki roman kuwa babu ma,Rudewa Niima tayi kunya ta kamata ta rude gumi ya fara feso mata ta shiga tunani,yace Lfy Sweetyna? Da Ina ina tace kaga wlh nayi na....a... Jiye..amma kalli babu a ciki to ko Aljanune? Dariya yayi yace wanne Aljanu ko dai bakiyi ba karya kikayi nasan yan matan yanzu da karya Ko kuma yan gidanku Sun cinye ? Wlh daga ni sai Latifa masu aikin ma basu taba yi mana haka ba kuma yanzu babu wacce ke shigar mana kitchen Momee ta hana tace sai dai muyi girki da kanmu,tace bari na zuba ma lemon kasha kayi hakuri idan ka dawo next zan sake maka, yace Ok ba damuwa,ta fara tiltilo lemo tsiiiiiii sai farin ruwa shaaaaa ya cika cup,dariya ya kwashe da ita tare da cewa amma Kin iya rainin hankali wannan ne girkin da kike ta yi min kuri ? Kin hanani cin na uwata,haushi Niima taji ya kasa fahimtarta,tace karfa ka raina min hankali kasan dai nan gidan munfi karfin karya idan kudine gidansa kazo ya zaka zo ka dinga fada min magana,kune Matsiyata wlh ba mu ba,Saurayi ya saki baki tare da cewa ashe baki da tarbiya dabba Ce ke? Fada ya kaure sukayi kaca kaca yaja motarsa ya bar gidan yana godewa Allah da ya gano Niima Bata da tarbiya.
Sabo da bakin ciki sai da Niima tayi kuka tana bawa Latifa labari,latifa ta dinga salati tace naji motsin kwanika dazu tunanina yan aiki ne,nima haka cewar Niima,Suna ta tunani to waye yayi musu haka,kaf yan aikin gidan sai da suka tara su aka tambayi kowa,amma suka rantse basu dauka ba,Niima tace duk ranar da na kama Wanda yayi wlh sai ya bar gidan.

Shukura kuwa tana komawa tace Umma yau kamshin girki ya cika min ciki sai dare zanci nawa,Umma tace to zubawa yayan naki, nan Shukura ta shirya komai daban daban kalar yan gayu,aka

1 Comments On JIN DADI SABO
avatar
mahamane-noura

2 years ago

Reply

Asalama alaikum, dan Allah yane ake sauke littafin akan waya

Please Login or Register in order to submit comment