Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Farkanki a kan sauran to ki sanar min wlh naje har can na kwade shege da sanda mene amfaninsa.
Shukura kallon Me gari ta fara ba shiri ko dai ya haukace ne?ita Bata Fahimci me yake nufi ba Sam, amma duk da haka tace nufina nayi kewarsa,shi nake jira yazo gareni ya daukeni mu tafi,Me gari yace uban wa? Mijina Mana.

Talliya ce ta fado gidan gabanta ya yanke ya Fadi ganin Me gari gaban Shukura kamar me rokon Gafara,Salati ta saki tare da cewa da mutuncinka?wlh tashi maza kafin na Tara muku jama'ar gari ki bar min gida,har abada Baki Kara ko 1hr a gidan Nan,Megari zaiyi magana Amma Talliya tace na rantse da sarkin dake busa min numfashi kayi magana ko ka hanata tafiya sai na Tara ma jama'ar gari kaf nayi Maka sharrin da baka zato, Tabarya Talliya ta dauka a Haukace tayi kan Shukura da gudu Shukura ta fada dakin da take kwana,ta fito da kayanta dake akwatuna fit tayi waje Hawaye Suna shararo mata yanzu Ina ta nufa,Talliya kuwa cewa take daga sati daya har an fara zagayowa Nan ta ingiza keyar Megari ta kulleshi a daki Dan karma ya fita ya taimaki Shukura.

Shukura kuwa hadiye kukanta tayi ta ta fara bugar kirjinta tace Shukura Hadiye kukanki ki zama me zuciya,kinje birnin tarayya ma kinyi abinda kika ga dama bare kauye gidan kwana ya gagareki?kamar bake ce kika iya satar shiga gida ba komai kyansa da lalacewarsa, a fili ta furta kalamanta a ranta tana cewa zan iya canja gari ko state ma Amma Nan garin kadai Ahleef zai San Ina Nan,Nan zai zo ya daukeni mu tafi muji dadinmu.da murna har tana rera wakarta ta ja akwatunanta sai Gidan Aishalle wacce akayi mata aure tun suna Yara basa shiri da Shukura Amma Shukura yau ta yarda Aishalle tafi Yan uwanta kawai ta kwada sallama a gidan,Mijin Aishalle ya ganeta to shi Allah ya bashi hakuri shi yasa ya kasa korarta akwai Kara da alkunya a tare dashi,Shukura ta gaisheshi tare da cewa dan Allah kar gabanka ya Fadi ba wajen kwana na zo nema ba,yar Iskar matarka zaka Kira min na Bata ajiya,Sai ga Aishalle ta fito daga Bayi ta kalli Shukura sannan tayi Murmushi tare da cewa kina Nan dai da halinki to Dan Uwarki kawo ajiyar ki tafi kin San dai ko sanda kina garin Nan zaneki nakeyi,Mijin Aishalle ya kallesu yayi dariya ya tabbata kaf dinsu kuruciya ce ke taba su basuyi hankali ba tunda Yara ne har yanzu.

Kafin ya gama tunaninsa Shukura tace ke ja can da muninki Amma ni Baki ga Mijina ba wlh duk ranar da yazo garin Nan na tabbata sai kun sume inda kika San aljani kin San bana karya zaku gani kuma kyau ne ya auri kyau ba irinki ba Muni ya auri kyau,Mijin dai dariya yake suna ta zagin juna karshe Shukura ta bada ajiyar akwatunanta tayi gaba,tana fitowa sai da ta zage gidajen danginta kaf Bata kuma yiwa kowa magana zata fito abinta, ko ma ka kulata baza ta kulaka ba,gidan Kawu ne na karshe Matar sa ta gama miyar ta tare da tsame Naman kaza ta ajiye kazar a gefe tana gyara miyarta,Shukura ta shigo idonta ya sauka kan kwanon da kazar guda take ci har murfin kwanon ba ya iya rufe kwanon sabo da kazar ta tokare ko Ina, Alhmdllh Shukura ta furta tare da cewa an Dade ba a hadu ba, Kawu na gefe a zaune Yana jira a kawo kaza, Shukura ta tuno rashin mutuncin da Kawu ya mata kawai ta dauke kwanon kazar ta koma kofar gida abinta ta zauna gefe ta rike kazar Nan da hannu biyu tana yaga a nutse tana ci,sai da taci tafi rabi,Kawu da Matarsa tare da yaran gida duk Baki bude suke jira suga Shukura ko zata dawo da Kazar Amma shuru,har Kawu ya kasa Hakuri ya zari katuwar sandarsa ya fita neman Shukura sabo da kazar ma Bata da lafiya da kyar ya bari aka yankata Dan yaga zata mutu ne Amma shine tazo a banza to wlh sai ta biyashi kudin kazar indai taci.yana fita ya iske Shukura tana yagar kaza,tana ganin Kawu ta mike tsaye kuma tana ci gaba da yaga tana uhmmmm dadi wlh Kawu gaskiya nagodewa Allah da Kaine Dan uwan Babana na jini,kayan wa mutum ya Isa ya taba idan bana Dan uwansa ba,shi yasa nake Alfahari da samun Uba kamarka.

JIN DADI SABO
Complete Hausa Novel Document


Kawu ji yake kamar ya hadiya zuciya har wani cije Hakora yake Sabo da masifa,Ki nemi ubanki,ni ba ubanki bane bana fatan ki zama yata ko wata yar uwata,kuma wlh tunda kika Ci kazar Nan ban yafe Miki ba ko yanzu kika mutu sai munyi sharia dake a gaban Allah sabo da Baki da gadona, Shukura ta fara yar dariya tana ja da baya gudun kar Kawu ya kamata tasan kawai ta mutu,ta yagi kaza tace ka Fadi kudinta naci bashi idan Mijina yazo zai biya,ba kunya Kawu ya dinga tsine tsine akan kaza sabo da son abin duniyarsa, Shukura tace za a biyaka Kawu relax calm down Ok,Kawu yace kin zagi Uwarki ta kabari ba ni ba,kuma tunda kika zageni da turanci wlh sai Naga bayanki a garin Nan,sai na tabbatar Miki barikin naki bai je ko Ina ba,yaja kwafa ya shige gida,Amma Shukura sai ta tabe Baki ta mayar da ragowar cikin kwanon ta rufe ta shiga har gaban Matar Kawu ta ajiya da sauri tace a rabawa Yara su maida yawu ni kuci na baku kyauta,ku Yan uwan nane na siyi kazar wurin Kawu, wata yar Budurwa wacce Kawu yace zai fara Bata rubutu Tasha, tace talaka Ina kika ga sisi? Me kikayiwa kanki bare wani,Shukura tace na tabbatar Miki ki bani lokaci kadan sai na siye garin kaf na bar muku kyauta ku zauna Zaki gani, Da ace ke ba yar uwata bace to siyenki zanyi ki koma baiwata Amma kinci darajar zumunci,Kawu ta kalla tace da sannu duk mutanen garin Nan sai sunyi nadama indai Allah ya bamu Rai da Lfy tana gama fadin haka ta Kara gaba abinta.

Gidan yar Uwar Innarta Yafendo take kallo daga nesa tana tsara yanda zata dinga shiga gidan ba tare da an gane ba, masifaffiya ce ta gaske gashi komai ita ta iya wani bai iya ba,tana da zaratan samarinta guda biyu suna zamansu a gida daya tare da matayensu,Yafendo akwai Tsafta da komai ita ta sani wani bai iya ba. Shukura ta zabi zama a gidan sabo da gidan Kato ne baza a gano ta ba, har dare tana can bakin Rafi tayi sallar Isha sannan ta karaso gidan dama su katangar Kara ce kawai ta Buda yar kofa dai dai ita ta baya ta shige gidan ta gyara musu katangarsu yanda take ta bi ta jikin rumbu ta buya a bayansa tana kallonsu suka Gama hirarsu da cin tuwonsu kowa ya tafi ya kwanta gida yayi Shuru, Yafendo tuni tayi bacci a kan Dan gadonta,Shukura cikin duhu ta lallaba sabo da ganganci ta shiga dakin Yafendo ta sadada ta shige karkashin gadonta dake gadon karfe ne me rumfa tun irin na zamanin da,Ko Ina a Tsaftace Shukura ta shaki baccinta har gari ya waye, Yafendo ta fita tana shararta da ta Saba har kofar gida take Sharewa Shukura ta fito a sace ta ebi ruwa a botiki da buta ta shige Bayin Tsohuwa da sabulunta tayi wanka da Alwala tare da maida kayanta da sauri ta koma dakin,tayi sallar asuba Yafendo Ana can Ana share share sarakan Tsafta,Surukar Yafendo Indo ita ta shigo dakin lokacin tuni Shukura ta koma karkashin gadon tana gani ta ajiye Koko da fanke me sugar,sai ga daya Surukar ma Gaje ta ajiye kosai da Kunun tsamiya yasha Nono lafiyayye a samansa,suna fita Shukura ta janyo Kunun da kosai sai ta dakko sabon ludanyin Yafendo Tasha dashi yanda take so ta mayar ta rufe komai ka rantse ba a taba komai ba haka aka kawo yanda taci da dabara ta mayar ta ajiye komai yanda aka kawo,haka ta jawo fanke ma taci guda uku ta mayar,Ludayin Yafendo kuma ta boyeshi can gefe cikin kasan gado...

Duk mai son cigaban labarin sai ya DANNA HOTON DAKE NAN KASA DON CIGABA DA KARANTA LITTAFIN KO KUMA KU DOWNLOADING NASHI
👇👇👇👇😂😂
https://t.co/luSBCx2QT7

Yafendo kuwa tana gama aikinta tayi wanka sannan ta dawo dakin tana masifa mata Basu iya abin duniya ba haba Ina rayuwa zata tafi a haka,ba tare da ta kalli kasan gadon ba ta zura hannu ta jawo kwandon kayan kwalliyarta ta shafa Mai ta shirya ta mayar ta tura,ta Kara zura hannu ta jawo a kwati ta sa kayanta ta tura ta mayar, Shukura na gefe can a kwance tana kallonta.

Yafendo ta bude kunu da kosai tace A'a yau kuma rowarce ta motsa aka kawo Dan wannan ba a ciko kwano ba,Baki ta tabe tare da kurba tace hmmm ai da akayi kunu ba irin na yaran yanzu ba,idan Dane wa zai Sha wannan kunu,Kosai ta bude da sauri ta bude Baki ta dafe kirji na shigesu sai kace jariri ne zaici Lallai Gaje ta fara canja hali Amma zata ci ubanta sai na yi maganinta a gidan Nan.

Shukura tana ji tana kunshe dariyarta,haka dai Yafendo ta Sha Kunu,ta Bude Koko taga Koko da yawa tace Allah sarki Indo mutuniyar kirki matsalarta daya ita kuma Koko Babu kauri a tsinka Masa ruwa yanzu mu a zamaninmu ka kaiwa me gida wannan ba sai kayi kwanan gidan ubanka ba ranar,Amma Allah sarki Iro na Yana hakuri,ludayi tasa ta ebo Koko ta sakeshi a kwanon tsiiiiiii tace ashasha kalli harda burbushin tokar Kara a ciki sabo da kazanta duk sai na gyara muku zama.Shukura a ranta tace Yafendo ba a iya mata Allah kyauta.

Shukura tana so ta fita Amma ba dama sabo da Yafendo ta share dakinta ta kwanta tana Jin radio su Gaje kuma suna wajensu suna girki,mazajensu Iro da Yahaya suna kiwo,wani yaro ya shigo da katon buhun mangoro a kansa jajaye nunannu Wanda yanzu aka tsinko su a sama,gaban Yafendo ya ajiye yace gashi inji Yahaya can wajen Kiwo ya bani na kawo miki, Godiya Yafendo tayi tace Kai yaro ka dinga sa takalmi a kafarka gashi Nan kazanta tasa duk ta tsatsatsage ina uwarka take da zata barka Haka,yaro dai yayi waje Yana Jin haushi,tsaki taja sannan ta raba ta bawa su Indo tasu ta ebi wata ta wanke ta zauna tana Sha sauran kuma a buhun ta tura kasan gado.

Dama Shukura yunwa ta fara cinta Yafendo ta fita wanke Mangwaro tayi sauri ta bude buhun ta ebo kusan guda goma,ta fito ta bude randar dakin ta kamfaci ruwa a wata roba me Fadi ta koma kasan gado,dake kusan komai har kayan kwanikan Yafendo suna kasan gado a wanke a shirye,a hankali Shukura take wanke magoronta tana Sha a hankali,idan Yafendo ta fita sai tayi taunarta yanda take so idan ta dawo kuma sai tayi a hankali,Yafendo taso taji kamar motsi a kasan gadon Amma sai tace Kai wannan bera da naci yake ya dameni tun rannan a kasan gado kwana Nan zan kawo Mage gidan Nan kowa ya huta.

Da Rana Shukura Bata samu taci abinci ba sabo da a tsakar gida Yafendo ta fita ci,Sai yamma ta samu ta fito daga gidan Baki daya,gidan Aishalle taje ta dauki toothpaste da brush dinta tayi sannan ta karbi rancen dari biyu wajen Aishalle wai sai Mijinta Ahleef yazo zata biya ta fice abinta da su ta siya danwake da dafaffen kwai guda biyu taci a garin sannan ta tafi can lambu inda ta Saba zuwa hutawa sai dare ta dawo gidan Yafendo,sai da ta shiga kitchen dinsu taci tuwo da Miya sannan ta shige dakin Yafendo kasan gado, sai da su Indo suka zo zasuyi Dumamen tuwo suka ga ba malmala daya,Gaje tace watakil almajirai suka sata kin San yanzu Haka sukeyi,da sunga baka kusa sai su sace ma abinci.

Kullum Shukura haka takeyi har ta kwashe sati biyu a haka Allah bai sa an kamata ba,bashi kuwa yanzu ta karfi take kwatar kudi tace ta ranta sai Mijinta yazo zata biya,haka masu shaguna ma duk taci bashin sabulan wanka da wanki da wasu abubuwa duk tace sai Mijinta yazo,Haka bangaren masu abincin siyarwa,masu tsire da kifi,har chemist taci bashin paracetamol da maganin ciwon ciki,bashin always pad ma haka,kuma ba roka take a Bata bashi ba kawai shiga zatayi ta faki Ido ta kwashi abin ta fice tace kana Bina bashi sai Mijina yazo,idan kayi magana tace zata siyeka ka koma bawanta ko kuma ta siye shagon naka.

Kwana daya tsakani Yafendo da sassafe tace yau Kwalimar karkashin gadon ta zatayi ta gaji da Jin beraye na motsi gwara taga ko mene a ciki,Katuwar sandarta ta dakko da nufin idan taga bera ta buge shi,ta bude gado sukayi Ido biyu da Shukura,Yafendo tayi mugun tsorata tunaninta gamo da aljana tayi ta fito da gudu tana Kiran Iro da Yahaya,suka raho da gudu da saddunansu,tana nuna musu kasan gado suka dage har katifar da komai sai ga Shukura Shar Shar dake tayi wata kiba da kyau sabo da ciye ciye kuma Bata aikin komai sai tunanin Ahleef dake damunta.

Yahaya yace Yafendo ai Shukura ce,zo kuga masifa wajen Yafendo kamar zata ari Baki,zagi kuwa ba Wanda Bata yiwa Shukura ba sannan tace fada min tun yaushe kike a dakin Nan,Shukura ta zauna sosai ta Basu labari kaf kan gidan Megari da dalilin da yasa har take shugowa tana kwana,Iro yaji tausayin Shukura ko ba komai yar uwarsu ce ai Amma duk gari da dangi an ki ta an kyamaceta bayan Bata da kowa sai su,Nan Iro ya roki Yafendo a barta taci gaba da zama a gidan kafin Nan gaba aga me Allah zaiyi, Duk Masifar Yafendo tana tunawa da yar uwarta Inna tace to ta yarda Shukura ta zauna a gidan su dinga kwana tare Amma sai dai ta kwana a kasa kan karamar katifarta dake gefe.

Dadi ya kama Shukura ta dinga zuba Godiya sannan taje ta kwaso kayanta na wajen Aishalle ta dawo dasu gidan Yafendo, ta fara Taya Yafendo sukayi kwalimar tare Yafendo na Masifa ta Bata mata kasan gado da kazanta duk kwallon magoro,ga ludaya duk ansha Koko da fura a zube, duk aikin da Shukura keyi Yafendo cewa take Bata iya ba ita tafi kowa iyawa.

Da dare Tare da Shukura su Indo sukayi girki a gidan na dare,Ana tsakar gida Ana ci sai Yafendo tace sanata Elrufai an bashi zaben Gomna yanzu a kaduna ko? Shukura tace ai ba Senator bane Yafendo dama Gomna ne ya Kara ci,Nan Yafendo ta ce to yar karya wa Zaki gayawa to sanata ne yanzu yaci Gomna, da shine shugaban majalisar dattijai a Abuja,Shukura tace bafa haka bane,Nan Musu yakacame tsakanin Yafendo da Shukura,Duk su Iro suka ce Zancen Shukura ne gaskiya,Yafendo kuma ba a Isa ance an fita sani ba Nan ta fusata tace to ai na Dade da sanin Gwamna ne har za a Gaya min shi Gomna ne,Ganduje na Kano ma ba ya koma ba ta dole bai ci ba aka kwace dole,kasar Nan ba wani me gaskiya duk karya sukeyi sai yanzu nake nadamar guri'a ta Dana sawa Buhari.

Baki Shukura ta tabe tace tab ni kuwa Ina Buhari sabo da shi Mijina yake so,Ahleef shi yake so,Yafendo ta durma mata dundu a baya Dan ubanki Ina kika ga auren?a Ina Mijin yake Nan aka ce ciki kikayi aka dawo dake shine Zaki ishemu dama Kawu yace Alfahari kike tayi da Kwarton ki na birni kina sonsa tir da halinki,Iro yace Haba Yafendo kufa daina Zurfafawa wlh baku sani ba ni Ina gani kamar tana da gaskiya,Yahaya ma yace a dai bi a hankali lokaci Dole zai nuna.

Megari ya Dade Yana fama da ciwon son Shukura har yanzu bai hakura ba sai ya auri Shukura indai Yana Raye liman sai zuga shi yakeyi,yayin da Shukura ta kame kanta yanzu kullum tana gida ko fita Bata yi a garin sabo da ko Ina taci bashi,kuma gashi tana tsarewa Ahleef igiyoyinsa ko ba komai ita da auranta tasan idan Ahleef Yana Nan bazai bari a dinga kalle Masa mata ba shi yasa take tayashi.
Labarin Ahleef kuwa su Yafendo har sun gaji daji a bakin Shukura Kai kaf garin Babu Wanda bai San labarin Ahleef ba Mijin Shukura na bariki,manya da Yara sun sani har dattijai in kaji yanda ake tsara kyawunsa Ana dariya suna ganin Shukura karya take, akwai wani da yazo daga Birni garin yasha dinkin Shadda Shukura tana gani cikin bainar mutane tace irin style din Ahleef na wata farar shaddarsa,tana Nan a cikin kayana nazo da ita,,shike Nan samarin garin suke layin karbar aronta wajen Shukura Ana yi musu irin dinki kusan kowa a garin kana cewa Ayi Maka dinkin Ahleef kowa yasan mene har telolin wasu kauyukan kana ce musu ayi min dinkin Ahleef style to za ayi Maka,yanzu dinkin shi ke tashe a kauyukan, Shukura ita kanta tana mamaki kowa yasan Ahleef a Baki,Ahleef style.

Kuma abinda yasa suka Kara yarda cewa Shukura da gaske take Ahleef ko dai Mijinta ko farkanta ne yanda suka ga tana sa dinkunan maza iri iri har jallabiya tabbas na Namiji ne kuma da gani mutumin me kudi ne shi yasa hankalinsu ya kwanta suna ganin Shukura zata biya su bashin da taci da gaske take.
Shukura zaman hakuri kawai take da Yafendo sabo da fadanta kuma komai baka iya ba Babu abinda zakayi ka birgeta bare ta yaba.

Ahleef kuwa tun bayan tafiyarsa yake fama da son kasancewa da Shukuransa,ya kasa komai sai tunaninta,gashi ko a waya ba ita ba labarinta kuma harda Umma sun kasa fada Masa gaskiya,Idan ya gama wa Momee komai zai dawo sai Momee ta Kara tura shi wata kasar ba tare da ta bari ya tako Nigeria ba,gaba daya ya fita daga tunaninsa ya kasa gane wa Momee,Matarsa yake son kasancewa da ita,yanzu ya tabbatar tsananin son Shukura yake ba kadan ba,Momee kam tuni ta sanarwa Abba cewar Ahleef ya tafi wani aiki kasashe,Amma Matarsa ta zabi tafiya garinsu ta zauna da Yan uwanta kafin ya dawo sabo da ta gudu ta Bata musu rai Dole zata wanke kanta wajensu,Abba yace ahlmdllh yarinyar tayi tunani,Momee tayi Murmushi tare da cewa ai tana da tunani da kaina muka je na kaita sannan akayi musu bayanin aurenta nace Nan gaba ma zakuje dasu Baba shi mahaifin Mijin nata,wlh masu mutunci sun karramamu,Abba dadi ya kamashi yace sai Ahleef ya dawo kasar idan za a dakkota sai mu taru muje gaba daya aga juna ayi abinda ya dace Allah yayi Miki albarka kema,Momee ta waya tace na gode mijina,Abba hankali ya kwanta tunaninsa abinda Momee tace gaskiya ne kuma da sanin Ahleef.

Saudatu da Baba yanzu sunga Momee ta daina musu magana Sam tsakaninta dasu sai Harara da kallon banza,ganin haka suka yanke sanarwa Ahleef zasu bar musu gida,tunda Matar gidan da alama Bata kaunar zamansu yanzu.











AsmaBaffa
[7/22, 1:13 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO







41-45







Official







By
Asmabaffa










Saudatu da Baba da kansu suka sanarwa Ahleef sufa sun gode da taimakonsa Amma zasu bar gida ga abinda Momee ke Musu sannan suka bashi labarin abinda ya faru na tafiyar Shukura,Ran Ahleef idan yayi dubu to ya baci kamar zaiyi hauka,Farhan ya Kira a waya ya bashi Umarnin ya kwashe su Umma da kayansu ya kaisu can Wani sabon gidansa daya siya kwana Nan me shegen kyau ba abinda Babu a gidan na rayuwa. Farhan ba Bata lokaci yaje ya kwashe kayan sawarsu ya Kai can gidan,ya zuba kayan abinci da komai sannan ya kawo masu aiki mata su biyar da maza sabo da su Umma suji dadin rayuwa a gidan girki kawai Umma zatayi ba abinda zatayi.

Sun Sha mamaki da murna suna sawa dansu albarka Babu adadi,Momee kuwa tunda taga Farhan ne ya dauke su tasan Umarnin Ahleef ne tace Umma ta gaida aisha Haka kawai tsofaffi sunzo sun rikita min gida baku San wahalar yaro ba kuce zaku Sha dadinsa.

Mubaraq yayan su Hafcy ya nacewa Niima har sai da ta fara kulashi ta karfi,tun Bata damu dashi ba har ta fara sonsa,Mama tafi kowa Murna zasu ci kudin su Momee tace saura ku Hafcy ko ke ko Zahra ku dage Ahleef ya auri daya ko zamu samu kudin da yawa sabo da shine me kudin, ko mata dari yayiwa ciki suka haife Babu ruwanmu ku aureshi kudi muke nema ba wani tarbiya ba.
Hafcy tace nima Dana yi tunani Haka na gani kawai ayi asan abin yi, tunda mun sallami shegiyar matar tasa.

Ahleef ne ya Kira Momee yace ya gama komai da Company din nasu dake kasar Japan gida zai dawo gobe, Momee cikin fada tace idan baka son aikin Nan Dana ke saka Ahleef ka fada min,gaba daya ka damu ka dawo Nigeria uban me zakayi a kasar ga aiki a Nan kaca kaca,Dan kaga bani da manyan Yara irinka shine kake min Haka, Allah sarki Ahleef baya son yaga Momee tayi fushi dashi ko ace shi ya Bata mata Rai sai kawai ya rude ya shiga Bata hakuri Yana lallaba ta sabo da halaccin rikeshi ta raineshi fiye da yaranta data haifa, Afwan Momeena what Next kuma? Wasu Kaya zaka je north Korea ka turo minsu zan bude shagon butique, da mamaki yace Momee sai na kwashe more than 2mnth a garin kin sani kuma yanzu akwai nauyi da hakkin Shukura a kaina, Salati Momee ta saki yanzu Shukura ta fini?akanta kake so dama ka dawo?

Momee Bata San Umma ta sanarwa Ahleef komai ba sai tace yarinyar kana tafiya ta tattara kayanta ta shiga duniya ba a San inda take ba,ai Abba yace kin fada Masa kin maidata kauyensu kafin na dawo,Momee tace Kai da kanta ta gudu kawai fada Masa nayi Dan hankalinsa ya kwanta,Kai wai me zaka yi da wannan yarinyar ne?Ahleef tuni ya gane Momee Bata da gaskiya ransa yayi Mummu Nan baci daba Dan kar tace ya hada ta fada da Abba ba da sai ya sanarwa Abba komai,a fili yace Momee wlh I do really love my wife,Dan Allah na dawo ko 2wks nayi sai na koma nayi Miki aikin? Momee tace Sam baka Isa ba ta datse Kiran ma Baki daya.
Baba da Umma dai suna can hankalinsu kwance Farhan ke musu komai da Umarnin Ahleef.

Shukura yau ta kwashe wata daya kenan a kauyensu kullum cikin sa Rai take zata ga Ahleef yazo Amma Shuru ,Nan kuma Megari ya samu Dangin Shukura ciki harda Kawu da Yafendo zai auri Shukura karya take Bata da wani Miji a birni,Kawu haushi ya kamashi ganinsa idan Shukura ta auri Megari taci gaba kaf garin ta ciri tuta,shi ga yarsa zata auri talaka Amma Shukura me gari Guda me fada aji me mulki, sai yace Kai Megari da girmanka da hankalinka zaka auri Karuwa? Megari yace ko a gidan Karuwai take na ganta zan aure ta Haka,Yafendo kuwa Murna takeyi ai Shukura ta ci gaba Megari Guda, Kawu yace to ya zakayi da yaron cikinta?Megari yace karya ce ba wani ciki,tana da ciki zaka ganta haka?kawai maganar mutam kauyece, Yafendo tace Bata da wani ciki Shukura fa shirmenta kawai takeyi sabo da kuruciya ko rannan tayi alada.
Megari ya washe hakoransa na cin goro.



1 Comments On JIN DADI SABO
avatar
mahamane-noura

2 years ago

Reply

Asalama alaikum, dan Allah yane ake sauke littafin akan waya

Please Login or Register in order to submit comment