Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a Hankali karki kone,Harshenta ta zaro waje tare da cewa yaji Inna fifita min Harshena,Inna tana murmushi tana kallon yarta abar kaunarta gashi tana fifita Harshe, Innaa.... Ruwa ki bani nasha, a randa ta ebo mata me sanyi,Inna bani abaki,ai kuwa ta Bata a baki ta sha,Dankwalinta ta cire ta jefar dashi,gashinta baki me santsi ya zubo a kafadarta Bata da tsayin gashi me yawa amma baza a kirata marar gashi ba, Bayan Inna ta gama mata komai ta koma tana aikinta sai ko Shukura tace Innaa... Zanyi wanka ruwan wankan ki dafa min, katuwar Budurwa amma kome sai an mata lafiyayya kuma,Baffanta ne ya dawo daga kiwon shanu,Da Shukura yayi arba nan ya fadada fara'arsa yace Autata ta kaina banga kin cakare ba ga Yamma lis tayi,tana Shagwaba tace Baffa sannu da zuwa,Inna nake jira ta kai min ruwan wankan, Da Sauri Baffa yace a kyale tuwon daren nan dan Allah azo a kula da yata yaran gari fes banda Yata,Inna ta fito ta hada ruwan wanka ta kai mata bayi,Bayan ta fito daga wanka ta shirya fes,tuwon dare ma tana ci ana mata fifita ko Inna ta Bata a baki taci Bata fiye cin abinci da kanta ba, Ko tsinke Bata daukewa a gidan kuma ta iya ko zata yi sai Inna tace a'a zata Bata jikinta,Idan Baffa yaga tana aiki to sai ya kwana ya yini yana masifa.

yau ma shukura ce ta nace sai ta dakawa Inna kayan miya,ta fara tana ta yi Sai Baffa ya kwada sallama,ganin Shukura na daka da masifa ya karasa shugowa haba Haba kashinta kike so ya karye ko kashi kike so ki buda mata, yarinya kamar Shukura nawa take da za a barta tayi daka,Inna tace nima bana son takeyi nayi nayi taki yarda,Shukura tace Inna na gaji zo ki karasa abinki dama idan da Sun kyaleta ma indai Shukurace sau biyu ma zata daka tace baza ta iya ba.

wacece Shukura ?labarin Auren Iyayen Shukura yayi kama dana Iyayen Ahleef nan gaba za muji.









AsmaBaffa
[7/22, 1:08 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO







2







Official







By
AsmaBaffa










Dan Jin dadin AsmaBaffa fans club and Duk Inda ta Fadi Fans.








Washe gari da safe Shukura tana ganin Innarta tana aiki amma ko tsinke baza ta tayata daukewa ba sai dai komai ma ayi mata,sai lallaba ta akeyi ta shirya ta tafi makaranta amma taki sai wasa takeyi gata da kokari amma bata maida hankali,Baffanta yana da burin tayi karatu amma taki yarda sam,har coper yake dauko mata tana mata lesson ana biyansu kudi har ta fara jin dan turancinta ta koreta tace zarnin fitsari arniyar takeyi bata tsarki,tana ss3 ta kusa gama secondary schl dinta duk makarantar babu me kokarinta amma babu me wasa kamarta da tsokana ga Kuka da shagwaba sabo da gata yayi mata yawa sabo da haka ma mutane da yawa Yar Gata suke ce mata,gata da kyau amma duk kyan nan babu wanda ya taba cewa yana Sonta a duniya ko a kauye kowa gani yake tafi karfinsa,ga shegen kyau ga Shagwaba Da tabara kowa tsoronta yake ji,yan mata kawayenta har addua suke mata Allah ya kawo sanadin da wata ko wani zata ketawa Shukura mutunci wanda zai karya duk wani abinda take ji dashi,samarin Garin ma har Meeting suke hadawa a boye za a samu wasu mazaje suyiwa Shukura fyade sabo da su kawo karshenta suna mata hassada,babanta duk garin babu me kudi da dukiyarsa gata ya daya tilo har birni ake kai Shukura tana cin kayan dadi.

Alhj Umaru shine Mahaifin Shukura,Iyayensa sun haifi yara da yawa amma cikin ikon Allah duk sai sun Zama samari da yan mata suke rasuwa,Har Iyayensu suma suka rasu tun Umaru na matashi,sai yan Uwa da yayan yan Uwa,Umaru ne kadai Allah ya rayashi har ya girma ya gaji dukiyar Iyayensa na dabbobi shanu da Tumaki,kaf rigar fulanin dake can wani daji yankin Plateu Jos,wajen tafiya kiwo a nan ya hadu da Matar da ya Aura Haj Bilkisu wacce a daji suka hadu fada ya barke tsakanin arnan Jos da musulmi an harbe kowa nata ita kuma Allah ya taimaketa ta hadu da Umaru ya kaita rigarsu wajen yan Uwansa daga nan suka fara soyayya ya auri Bilkisu,tare ya biya musu aikin Hajji suka je yafi sau biyar, daga nan Allah yasa ta samu ciki ta Haifi yarta Mace zukekiyar gaske ranar suna taci Shukura,wacce ita kadai suka Haifa a duniya ga rashin iyaye da yan uwa sabo da wannan sai suka dauki son duniya suka tattara shi kan yarsu Tilo Shukura,tun tana yarinya haka ta taso komai tace shi za ayi mata,yanzu zai siyar da shanu ayi mata abinda take so,makaranta kuwa a kauyen da ba yanda zaiyi ne amma da Birni yace zai kaita Private amma basa son yarsu tayi nisa dasu wani abu ya sameta,shi yasa ya barta a ta garin Kauye sai yake dauko mata Igbo cikin masu Nysc ana mata lesson yana biya yana so yarsa ta iya turanci,aiko dake makarantar kauye ba karatu haka Shukura da taimakon lesson ta iya karatun Hausa da rubutu ta iya rubutun turanci sama sama kuma tana dan ji bada yawa ba,sai ta Zama kaf garin babu kamarta,ko baki akayi ma'aikatan Gomnati Shukura ake kira tana jagorantarsu wajen karatu da rubutu,yayin da take zuba shagwaba da tabara ga sangarta harda tayi yawa,kowa bata raga masa bata da kunya ko kadan komai girmanka ba ruwanta sabo da iyayenta basa mata fada sai abinda take so,iyakaci suce bari Shukura ko Allah ya kiyaye gaba,ko Allah kyauta,bata cas bata as,sai umarni ma da take bawa iyayenta kamar ita ta haifosu komai direct zatace Inna tashi ki min kaza,Baffa yi kaza kuma ba musu jiki na rawa zasuyi mata sabo da kaunarta da sukeyi,Shukura tana da kirki idan taga dama sai ka dauka wata me hankali ce,gata da fara'a yanzu ta wangale baki,indai ba shagwabar ce ta motsa mata ba to bata fushi a duniya,zai wahala ka gane fushinta ko ranta ya baci,duk aikin da Inna keyi Shukura tana gani kuma duk ta iya kawai yi ne baza tayi ba ta saba da hutu,Haka ga son jin dadi,bata fiye cin abincin gidan ba sai Nama,kifi,yogourt da sauran kayan dadi su take ci ko nawa ne iyayenta bata sukeyi wasa take da kudi a kauyen,gata da kyauta yanzu idan kuna mutunci zata baka kudi ko kayan sawa,Sabo da Babanta Sutura sosai suke mata kusan kayanta ma duk na Saudiyya ne sabo da iyayenta kusan duk shekara sai sunje Makkah kuma da Shukura ake tafiya tun tana shekara 10 ake zuwa Makkah da ita,gashi ta cika 18 zuwanta Makkah sau 7,shi yasa ta dan waye ba laifi baza kace daga kauye take ba,bata fiye sa Atamfa ba duk kayanta na kasar waje ne kana na da dogayen riguna masu kyau ,yanzu idan Shukura taga dama sai tace Baffa a kaini Birni zanyi Kallo kallo da gudu zai ajiye duk abinda yakeyi su tafi cikin garin Jos har Mall yake kaita iri iri sabo da Umaru ba bagidaje bane shi sam yasan ta duniya,Haka suke shiga Mall suyi kauyancinsu su fito,idan taga dama tace Aje Kano,katsina,kaduna kusan da yawa state din Nigeria Shukura taje ta cikin birni yawon bude ido Abuja ce yanzu burinta,so take Baffa ya kaita yace sai babbar Sallah tazo zasu je tana ta murna bata da buri sama da taje Abuja shine next target nata,A birni idan taga abu bata San sunanshi ba sai taga dan gayu na gaske ko yar gayu ta karshe sai ta tambayesu dan Allah ya sunan wannan?idan an fada mata tace mene Amfaninsa?a fada mata tace da turanci fa? Nan ma a fada mata haka takeyi a birni bata shuru da bakinta komai sai ta tambaya amma indai kai ba dan gayu bane to ko kallonka baza tayi ba kawai ita baka waye ba kuma ba dan birni bane,idan kuwa ka sake ta tambayeka baka Fada ba zaka ci masifa da jaraba ga gori kayi magana ta tara mutane sabo Da Kuka zata sa ta fara shure shure shi kanshi Baffa da kyar yake lallashinta,Baffa ma Har mall idan zasu shiga da sandarsa yake shiga ta kiwon shanu ayi ta musu dariya amma ko a jikinsu, wannan kenan.

Baffa ne zaune kusa da Inna yace Inna ya kamata kema ki shirya Wannan lokacin mu tafi dake sabo da tafiya ta taso min zuwa birni cikin Kano zan tafi da Shukura tayi kallo Kallo kema ya dace ki bude idonki,Tsalle Shukura ta shiga bugawa tana Murna zata je Kano wannan zai Zama zuwanta na biyu kenan Kano,tace Baffa zamu je Shopirayit wai (ShopRite) take nufi,Baffa yayi dariya yana jin dadi Shukuransa tana farin ciki yace Yar Shopirayit din bantan uba Saura muje ki damu mutanen birni,dariya sukayi gaba daya tace Ai Allah sai na tambayi yan gayu sun fada min Sunan jakin Baban gida da turanci,dama na dade ina so na tambayi sunan Jakin Baban gida da turanci ban sani ba aiko wlh wannan lokacin sai na tambayi yan Birni,Baffa yana dariya yace ai da kin bari sai munje Abuja birnin tarayya sai ki tambaya a nan ai sunfi yan gayu,sunfi ilmi ga boko,da sauri tayi tafi ai wlh Kano ma sai sun sani, kuturin uba kai kaga wasu yan gayu Inna baki gani ba yanda suke tafiya kwas kwas,baku ga wani Namiji ba Allah dana ganshi fatarsa santsinta yasin kamar na Gansa kuka sulub sulub.
Dariya sukayi gaba daya Shukura tace cab Inna kinga wani da muka gani yana cin Nama a bakin titi suna Shan lemo a tasha cikin tashar Unguwa Uku ai kadanba Sumarsu tayi Ukun takan Baba Sumar nan da kake tarawa kaima ashe Baffa kaima dan gayu ne hhh sukayi dariya,Shukura tunaninta Sumar Baffa ma ta yan gayu yake tarawa bata San irin kauyencin yan Fulani bane wacce suke tarawa duguzum ba gyara,haka kuma da taga wasu a birni a tasha yan iskan tasha ne masu sa mutane a mota amma dake na kauye daban da taga na birni sai ta gansu yan gayu ne ma bata San yan jagaliya bane hh,yan Wiwi ma kuwa,wanda kuma take cewa me santsin fata Wani ne kawai fari amma ba wani dan gayu bane kawai dai yayi dan wankansa.

Yau asabar yau tun safe suka shirya tafiya Kano Baffa an siyar da shanu za aje birni harda Kudin dan karamin Hotel da zasu kama daki daya su Uku dama haka yakeyi Su Baffa an waye.
Baffa anci rawani kamar dagaci ga Sanda katuwa,Inna kuwa duk Wanda ya ganta zai rantse mahaukaciya ce sabon Kamu a haka kuma taci gayu,Ita kuwa Shukura ansa doguwar riga Baka ta makkah katuwa da ita amma ko gyale bata yafa ba dankwali kawai ta daura a kanta sai faman kalle kalle takeyi,ana mota tuni Inna bacci ya kwasheta,Baffa ma haka,Shukura kuwa taki bacci wai kallon Hanya takeyi har aka zo kano sai da ta bawa mutanen motar dariya yanda ta zura hannunta ta window tana nuna Abu da yatsa,Inna tana bacci taji Shukura ta daketa a baya tas Inna tashi...tashi...ki Sha kallo,kin gani ...laaaa....Baffa...kalli...wan can zuwan Wallahi babu wannan,na rantse da Allah ba wannan abin,ikon Allah...laaaaaaaa...kaga Baffa.... Inna...kalli katon gida,Baffa yace Shashasha Banki ne wajen ajiyar kudi,Kudine a ciki mu shiga Baffa muyi kallo,ana jin Shukura ta rafka Salati kunga tallan Sabulu,Fati Muhammad ce yar Film gata a sabulu shi yasa ta kara fari nima sai na siyi irinsa,nan ma ta kalli katon Symbol Wallahi ga Sani Danja ta karanta tace An rubuta Glo yeeee tallan layi yakeyi na waya yasin na gane.

Driver da conductor ana ta dariya har suka sauka ta cika motar ita kadai, kyan Shukura yasa duk inda suka ratsa sai hankalin alumma ya dawo kansu ana kallon kyawunta. Shukura ta gigice,ana sauka a tasha sai taga wani Zabiya fari marar kyau,duk kuda na binsa,jikinsa yayi wani rodi rodi,ga Hakoransa yellow,hanci kato muni iya muni,ta kalli Zabiya (albino) ta kara kalonsa ta sheke da dariya kowa ya fara kallonta a tashar,hankalin kowa ya dawo kanta amma ko a jikinta,tana ta dariya sai kuma ta kalli Zabiya ta rufe idonta tare da cewa wayyo...Allah ni bazan so wannan ba,Baffa ai wlh gwara a yoni baka kamar bayan tukunyar Inna akan na Zama irin wannan,ashe farin ma akwai na muni,me za aci da kai ta furta tana kallon Zabiya,jikinka kamar nama ga kuda sai Binka yakeyi,Inna tace Allah kyauta miki,yo Allah na tuba ko Aishalle karshen muni a garinmu me zatayi da kai,zabiya dai bai kulata ba,tace anji kunya ana birni ba a goge baki da Brush,kalli hakora na farare wulluuuuuu...ta ware masa hakora,ai ko aka dinga dariya ana Shan kallo sai Baffa ne ya fisgi Hannunta suka tafi tare da hawa Napep,tana shiga Napep tace ko ni sai na iya tuka wannan yar motar,jibeta yar karama,me Napep ya tsaya daukan wata katuwar mata nan Shukura ta saka rigima ita ba wanda zai shigar musu wannan katuwar ta dannemu a ciki,Baffa da Inna sabo da sai abinda Shukura tace aiko suka ce baza a dauki wata ba Shukura bata so,Me napep yace sai kun kara min kudi fa,Shukura karaf tace kaine matsiyaci kaje ruga kaga shanunmu da awaki ehe.Mai Napep ya mata banza har suka isa Hotel ya saukesu,Baffa ya shiga da kansa ya kama musu daki daya tal su Uku,Baffa yace su shigo dama Shukura ta saba tun a Hanya ta cire takalminta sabo da karta bata musu Hotel gani takeyi kamar gida Ne,Inna ma ganin Shukura tayi haka itama sai ta zare takalmanta suka fara tafiya sadaf Sadaf kamar Barayi ka rantse wani Glass suke takawa a hankali.

Inna ta Rafka magana ganin alhazawa da mata masu kudi suna Hutawa tace gafaranku dai bayin Allah, Shukura wayayya tace ke Inna nan fa Kamar Makkah ne bakya ganin wajen me kyau, nan Inna ta kwala sallama da takalminsu a hannu,shuru ba Wanda ya kulasu,Shukura tace sai kinyi kalkala Inna irin na larabawa yan gayu, Shukura ta makale murya tayi Sallama aiko mutanen wajen suka sheke da Dariya tunaninsu almajirai ne suka zo bara har Hotel, Baffa yazo ya Fara Fada haba Haba Bilki kamar baki waye ba Ashe zuwa Makkah da kuke na banza Ne,Nan suka bishi har dakin da aka Kama, Shukura tace wlh kamar a Madina Baffa ta furta tare da fadawa gado tana shan AC.
Shukura ta fara shagwaba wanka Inna Baffa wanka zanyi,Haka suka rude suna lallashinta kowa ya shiga yayi wanka tare da Sallah.

Baffa yace to Alhmdllh amma baza muci abincin nan ba yayi tsada, Karaf Shukura tace ni kosai zanci da doya da kwai, Inna tace a siyomin Biredi da fanke me sugar.
Baffa ya fita ya siyo musu shi Kuma ya siyo gurasa da kuli, Bayan sunci sun koshi sai suka bazama kallon gari,wannan haske kamar a Makkah Cewar Inna,sai cikin dare suka koma masaukinsu,Inna da Baffa a kasa sukayi shimfida,Shukura kuma ita kadai a saman Bed sabo da gata.

washe gari Baffa yaje inda zai ga mutanen da zai gani dama shine dalilin zuwansa kano,Bayan ya dawo suka kuma bazama cikin gari yawo sune har countryMall,Shukura taga kofa wacce ake turawa ta Glass sai ta fara knocking Kwan... Kwan... Salamuakaikum a bude,ku bude min,a bude.sai da Ma'aikatan suka zo suka bude Mata,bayan sun gama yawonsu kaf tare da siyayya sai kawai Baffa ya Manta sunan Hotel da Address,suna ta shan wahala a cikin napep sai Baffa yace Shukura Dan ubanki baki rike Sunan ba?ke da kike yar Boko, Inna tace wlh kuwa kai mun gaji,baki Shukura ta turo yo Kai Baffa ni ina zan sani,kaine fa ka kawo mu,me Napep yace ya gaji shi tafiya zaiyi,nan ya saukesu ya kara gaba,Su Baffa dai bakinsu Kamar zai cire sabo da tambayar Hotel, Shukura ta zabura ta tare wani me Taxi yana tsayawa tace Dan Allah tambaya nake,yace ina ji,dan Allah malam kasan wani Otel me kyau jikinsa duk fulawoyi? Da bene sannan ga kamshi,yana ta kyalli...shuru tsagal Inna tace yaro da Kwan lantarki a ciki,harda Tv,Me taxi ya fara dariya ya gansu daga daji suke yayi mamaki ma da suke zancen Hotel shi bai gane ba yayi tafiyarsa.

Su Baffa sai a gindin wata bishiya suka kwana, Gari na wayewa sai Baffa ya tuna Sunan Hotel din,nan suka shiga Napep suka Koma suna zuwa sukayi wanka suka shirya suka fito da kayansu sai Tasha, Suka shiga mota sai kauyensu suna ta murna sunzo birni sunga Gari cikin mota sai ciye ciye suke.Shukura ta damu mutane da surutu har suka isa kauyensu lfy.

Kwance yake saman cinyar Momee shima Ahleef kusan irin Shukura ne yana son sa wani aiki yana kwance yana hutawa amma shi sai dai kannensa ba Manya ko iyayensa ba, in banda tunanin masoyiyarsa Niima ba abinda yakeyi son da yakewa Niima ko rabinsa Niima bata son Ahleef haka,sabo da shakuwa da kyau ga kudi shine yasa take son Ahleef sosai ba wai tayi zurfi bane, Shi kuwa Bashi da wacce ta fita a duniya.
Niima ce ta shigo daga aiki ta Dawo ido suka hada da Ahleef masoyinta ya kashe mata ido daya tare da furta sannu kamar bazaiyi magana ba,hannu ta daga masa tana zuba masa murmushinta me tafiya da zuciyarsa,sai kallonsa takeyi a ranta Tana jinjina kyau,kyan diri da kyan sura irin na Ahleef,a ranta ta ayyana dadin da zaiyi on bed take duk da cewa bata taba bin maza ba amma Tana kwadayin Ahleef wanda shi kuwa Son Niima yake tsakani da Allah ba Dan komai nata ba.
Muryarsa taji a nutse yace 5pm ki shirya zaki rakani gidan su Farhan,ok tace Tana fari da ido.
Misalin 5 na yamma taci uban wanka kamar a saceta cikin wani lace maroon color,
Hannunsa ta rike yasha azabar kyau kamar wankin engine haka yake tafiyarsa kamar wani Gomna,hannunsu rike cike da so kamar a sace su,Bayan sunje gidansu Farhan yawo suka wuce na shakatawa,Suna zaune suna shan Ice-cream sai ga wani frnd dinsa yazo zai wuce nan Ahleef ya Mike ya tafi wajensa suna tafawa suna Hira,Niima tana latsa waya sai ga motocin Gomna zuga guda sun shigo da Alama Meeting suka zo yi Abuja,Niima ta gigice kamar bakuwar kudi bayan gidansu ma sunfi Gomna kudi, sai gyara Riga takeyi tana karairaya,Ido hudu sukayi da Gomna tare da Manyan masu kudi da suke kusa da Gomna,tasan Gomna ne amma bata San Gomnan wanne state bane,Gomna shima yaga me Kyau yawunsa ya tsinke,ba bata lokaci yayiwa yaronsa magana,sai gashi Cikin Guard wani ya kawo mata card na Gomna yace gashi Inji me Girma Gomnan Taraba State Exelency Muhammad Aliyos,fit Niima ta cafke Card tare da jefawa a jaka tare da furta tnx, guard da sauri ya koma cikin tawagar Gomna,Niima kuwa wani Farin ciki da girman kai ne ya mamayeta lallai ta cika me kyau da farin jini har Gomna guda binta sukeyi, tace ahaf har wani kudi ne damu,ai kudin yan siyasa sune kudi kullum shigowa suke ta ko ina kamar banza,duk da Babana shima yana siyasa ai ba kamar Gomna ba kai zan yashi dollars fa zanyi abinda naga dama,tana wannan maganganun zucin kawai Ahleef ya dawo cikin takunsa ko ina ka duba kallonsa akeyi maza da mata,ita Kanta Niima a ranta tace Allah ya zuba baiwa a nan.
Ahleef kashe mata ido daya yayi yana murmushi sai wani lallaba ta yake yana mata shagwaba sai ta fara biye masa sai ta tuno samarinta yan siyasa masu kudi ciki harda Gomna Aliyos.













AsmaBaffa
[7/22, 1:09 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO







3








Official










By
AsmaBaffa









Naku ne Fans na ko ina.











Hannun Niima ya kamo yana kare mata kallo,wani yarr taji a jikinta shima haka a hankali yace I love u Niima dan Allah ki rikeni amana karki barni duk da nasan bani da wani Asali iyayenku sune gata na dan Allah karki kyaleni ki taimaka min ta wannan hanyar kadai zan iya sakawa da Momee da alkhairi tare da Abba shine na aureki ina matukar Sonki Niima,hankalin Niima ne ya Tashi gaskiya ita yanzu bata son auren nan idan tayi aure shike nan Namiji daya tal zata dinga kulawa mijinta,ba samari duk masu kudin nan baza ta kula kowa ba, a hankali tace ina sonka nima ai baka da matsala Dani,Murna ta kamashi yace yanzu dai na fadawa Abba a sa mana Rana ko? Uhm Kawai tace tana wasi wasi a ranta,sai kallonsa takeyi kamar mayya ,Kalli mijinki da kyau Babyna,kunya ce ta kamata ta mike tsaye tare da cewa tashi mu tafi Hearty.
Soyayya sosai take nunawa Ahleef bata nuna masa akwai matsala,shi kuma ya gama sakin jiki da ita sai kashe mata kudi yakeyi sosai,so iya so tare da kulawa yake nuna mata,ita kuwa bata wani caring dinsa amma tana nuna tana sonsa,sai wahala yake a kanta,Har Abba ya dawo sukayi shawara da Momee suka yanke hukunci,nan Abba ya nemo danginsa Maza da mata,tare dana Momee suka yanke ranar aure nan da 4mnths,Wasu a dangi suna ta gulma za a aurawa Niima Marar asali Dan gidan raino dan tsuntuwa,Niima munafuka a gaban dangi sai ta zauna tare dasu a dasa gulmar Ahleef da ita, tace sam ita bata sonsa Abba da Momee ne suke so nanfa Zance ya zaga dangi ai auren dole za ayi mata Ahleef kadai ke sonta sabo da yaci dukiyarsu sabo da yasan bashi da gado,Haka Niima tabi itama kawayenta tana fada musu sai tsinewa Ahleef akeyi shi kuma bawan Allah bai san komai ba murna kawai yakeyi kamar me, Momee da Abba ma murna Sukeyi Sosai.

Shukura zaune take gefen Inna dake dama fura,Shukura tace Inna Sosa min bayana,Inna ta jawota tare da kwantar da ita a cinyarta kamar jaririya ta fara sosa mata baya,ita kuma tana Inna nan nan,Tana kwance tace Inna miko min Plate din can na cinye awarata,Inna ta dauko mata,sai da ta cinye sannan tace Bari nayi wanki Inna, Inna tace wanki? A'a kwanta ki huta zan wanke miki su,Shukura tace Allah bar min ke Inna, Tana kwance Inna taje ta wanke mata kaya tas, da yamma Inna na aikin tuwo Shukura tace kawo nayi miki tankade Inna, a'a Shukura zaki bata kayanki zauna ki Huta abinki,Shukura kuwa ta fice yawonta cikin kauyen.
Tun safe Shukura yau da period ta tashi tana shan wahalar ciwon Mara Dama idan tanayi Sai kuka takeyi harda shagwaba ma abin nata,Inna kuwa harda kuka tana tausayin yarta,Baffa kam yau ko kiwon shanu bai fita ba sha lele ba lfy,sun rufu a kanta sai addua suke mata har ta samu bacci ya kwasheta,da yamma kuwa ta tashi sosai taji sauki har ta fito Tana wanke kayan da Jinin ya bata tare da panties dinta,bayan ta wanke tace Inna...zo ki karba ki shanya minsu,da sauri ta karba ta shanya mata Kuwa,Baffa ne ya shigo da sauri ya manta ma da wata Sallama so yake yaji jikin Shukuransa.

Shukura tana so ta fadawa Baffa Pad dinta ta kare dama ita take zuwa cikin gari can jikin wani asibiti ta siyo abarta Sabo da kauye ma basu wani santa sosai ba Da tsumma suke kunzugu,sai tace Baffa kaje bakin asibiti kace a baka Biredin mata,Baffa ya washe baki ahh lallai sauki ya samu Shukurere ta har Biredi zaki ci,wanne kala?,murmushi Shukura tayi tace Baffa a bakin asibitin Ishu kawai ake samo shi,kace biredin mata zasu

1 Comments On JIN DADI SABO
avatar
mahamane-noura

2 years ago

Reply

Asalama alaikum, dan Allah yane ake sauke littafin akan waya

Please Login or Register in order to submit comment