Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Amma sautin kadan ya fita baza ka gane maganace ko ba magana bace,a tsorace Ahleef ya fara waige waige yaga ba kowa,tsoro ne ya kamashi ya fita da gudu ya banke kofar,Abin dariya ya bawa Shakura namiji haka amma sai tsoro.

Sai da ya daina Jin tsoron sannan Kitchen dinsa ya shiga domin dafawa kansa Breakfast shi bai son girkin yan aiki,Chips and egg ya hada sai tea daya hada lafiyayye a cup,ya shirya komai a Dining,Shukura yunwa ta addabeta,ga kamshin girkin ya cika mata ciki,tana kallo Ahleef ya tafi bedroom din sa domun shiryawa sannan ya fito ya karya,da sauri ta fito tare da dauke Shayin ta balli Bread,Chips and egg duka ta dauke ta cinye tas da sauri ta ajiye masa empty komai sannan tabi ta inda ta shigo jiya gidan ta kara bi ta sama ta dirga ta waje can tayi sauri ta bar layin,Ahleef ya dau wanka yana zuba kamshi yazo dining ido ya zaro cike da tsoro jikinsa ya fara mazari ya ajiye komai ya shirya abinci amma yaga ba komai a wajen sai plate da cup,a tsorace ya fice da sauri tare da Umartar Driver dinsa ya kaishi Hospital wurin Momee,ganinsa da driver yayi a firgice tunaninsa Ko jikin Momee ne ya tashi Da sauri Driver yaja zukekiyar motar zuwa asibitin,Momee ma ta kasa gane kan Ahleef taga kamar a firgice yake ta tambayeshi ko lfy yace normal Sabo da abin kunya ne ya fada cewar kamarsa yana Tsoron Aljanun gidansa.

Shukura kuwa kowa ya kalleta yasan tana Cikin Nishadi yau tayi kwanan dadi,idan ta tuna yanda Ahleef ke firgita sai ta kwashe da dariya haka ta yini tana gantali a gari Bata da wajen zama,gashi kayanta Gaba daya suna Hotel ta barsu Bata da abinda zata canja kaya doguwar rigarce kullum a jikinta ko wanki Bata samu ba duk tayi dirty,lokaci yana cika 3pm ta wuce wajen Saudatu me Doya Zata fara aiki,gashi tunda ta cinyewa Ahleef abinci Bata kara cin komai ba, yunwa ta gama kwakwuleta.

Da murna ta karasa wajen Saudatu wacce ke hada kaskon suyarta,Sallama tayi tare da gaishe ta cike da ladabi,Saudatu tace yata Kinzo Akan lokaci kuwa haka nake so,Inna ai Bazan Bata lokaci ba bari na fere miki doyar,Nan Saudatu ta shiga koya mata yanda ake komai tana yi ba laifi ta iya duk da cewa Bata saba da aikin ba amma tayi kokari,sabo da kyan Shukura yau cinikinsu yafi na kullum,doya taci ta koshi har ta gode Allah,bayan 6pm suka siyar da komai,Saudatu ta bata Dubu daya kudin aikinta tace gashi ki shiga taxi da dari biyar,biyar kuma ladanki na aiki,Shukura murna kamar tayi Hauka tana ta godiya ta raka Saudatu bakin gate din gidan da suke aiki sannan ta tafi gidan Ahleef itama kamar gidan ubanta, a hanya taga wani wajen shan Ice cream tace yee wlh yau sai na sha,nayi niyyar tara Kudin amma dadina kawai zanci, ubanwa wahala ta kashe ? ,Allah ya hore, kawai ta shiga ciki taji ice cream tsada babu na kudinta,daga na 2k sai sama,Wani matashin me kudi ta gani yana ta jidarsu da yawa,tace sannu malam,dan Allah kaga kudina dari biyar gareni dan Allah cika min dubu daya da dari biyar zan sha ina so,yawuna ya tsinke,raina ya biya,kaga kuma ido guba ne,Matashin saida ta bashi dariya ya dauki roba guda ya bata,ta shiga gode masa ba adadi.

maimakon ta boye kudinta tana fitowa taga wajen da ake siyarda Shawurma taji Kudin sunyi yawa amma sai da ta siyi wata Samosa da akeyi a wajen guda biyu dari biyar, dari biyar din kuma ta shiga taxi drop babu ko neman sauki,yau ma ta sama tabi ta dirga cikin gidan Ahleef kamar jiya har zuwa makwancinta,ta cire kayan jikinka sai dankwalin rigar ta daura ta shige toilet ta wanke tas ta shanyata a toilet din cike da tsoro kar me gidan ya kamata,Ice cream dinta tasha da samosa dinta har lumshe ido takeyi.
Ahleef yana bacci amma sai ya dinga ji kamar motsin mutum yau ma haka ya duba ko ina baiga komai ba.sai da safe rigarta da inner wears dinta suka bushe, bayan tayi wanka fes tare da brush harda wanke gashi tana kamshi ta ko ina ta samu soap me tsada,Bayan ta saka kayanta Da suka bushe sai ta wanke gyalen shima ta shanya shi ta fito tare da kara boyewa, tana kallonsa yau ma ya motsa jikinsa, yau indomie ya dafa da kwai bai tafi wanka ba ya cinye abarsa sannan ya Haura samansa,yana tafiya ta fada kitchen din da sauri ta shiga dube dube nan taga ruwan zafi a flask ta hada tea me shegen kauri har yayi yawa ma, ta kwashi snacks a fridge ta fito da sauri ta koma wajenta na boyo,tana fita yana saukowa kasa yana latsa waya sanye Cikin fitted jallabiya fara yana kamshi kamar balarabe,Cikin palon ya zauna tare da daukan remote ya kunna TV tashar kwallon kafa yana kora lemo lafiyayye da Alama yau sunday ba inda zai fita,Shukura kuwa taci ta koshi,garin labe laben ganin ko yana palo ta fadi a kasa,ta mike da sauri tare da kwashewa da gudu ta koma wajen boyonta,Ahleef yaji kamar abu ya fadi harda yar kara,wani tsalle ya buga a tsorace ya haura sama da gudu ya buya a bedroom dinsa shima yana tunanin to mene a gidansa haka,ko dai barin gidan zaiyi ? Ko bakin aljanine a gidan.
Shukura kuwa yau itama ba inda zata sai 3pm zata je aikinta Sabo da haka ma ta lallaba ta shige daya kitchen din na daya bangarenta, duk wani abin ci da sha idan ta gani sai da ta dandana shi taji irinsa.
Kullum haka Shakura takeyi a gidan Har ta kwashe sati daya a gidan Ahleef tana buya ba tare da ya Sani ba,idan baya gida ma har girke girke takeyi ta wanke komai ta mayar inda yake yanda bazai gane ba, kudin aikinta kuwa kullum Saudatu zata Bata dubu daya ko dari takwas amma kafin taje gida ta siyi kayan ciye ciye da Kudin, watarana ko Na taxi Bata bari sai dai tayi ta rokon me taxi ko ta dinga tare lift, ta kara wani uban kyau da haske tare da kiba Sabo da yanda take ciye ciye a gidan Ahleef,har yau bai Ankara cewar kayan abinci suna ta karewa ba kuma bashi yaci ba, wasu abin ma ko farka kwalin baiyi ba amma Shukura duk ta farke su tana ta kwaba girkinta tana ci. Wani abin ma bata san mene ba,dama kuma ba wani iya girki tayi ba, dama dama na gargajiya ma.yanzu babu girkin da tayi mugun iyawa sama da doya da kwai,ta koya wajen Saudatu,sai Dambu,danwake,tuwo,fate,da sauran abincin kauye ta iya kadan tun iyayenta suna da rai.
yau ma Saturday Ahleef ba inda zai fita,haka Shukura ma Saudatu tace yau da gobe baza suyi abin siyarwa ba me gidansu zai yi baki zata taya masu aikin girke girke etc.
Tun safe Ahleef yake Jin kamshin girki a gidansa na musamman yana tashi,ya rasa a ina yake jinsa,ya duba baiga komai ba, yasan kuma shi kadai ne a gidansa,tunani ya shiga yi jimm Kadan ya tuna wani abu, a fili yayi dariya yace Oh makwafta ne, kaiii... amma Sun iya girki sai kawai ya koma palo yaci Gaga da kallon ball dinsa,ita kuwa Shukura tana ta suyar doya da kwai a daya kitchen din wanda Ahleef baya shiga, Sabo da Shirmen ta bata taba tunanin za aji kamshin girkin ba ai nan wai buya tayi tana girkinta a boye,chanel ya canja ya tare da kure Vol na kidan turawa me dadi,Shukura ta jiyo dadin kida bata ma san sanda ta fara rawa tana juya doya a kasko ba.















AsmaBaffa
[7/22, 1:12 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO







6







Official







By
AsmaBaffa








JIN DADI SABO FANS GROUP ga page naku aci Gaba Sharhi.











Soye soyenta takeyi har ta gama tare da gyara kitchen fes ta dauki abincinta ta koma inda ta saba boyewa taci ta koshi abinta ta kawo ragowar Doyar ta ajiye a Kitchen ta koma da sauri kar me gidan ya kamata, Gaba daya Ahleef a tsorace yake a gidan shi yasa yake Jin kamar motsi,a hankali yabi inda yake jin motsin har kitchen din da tayi girkin ya shiga yaji kamshin girkin dazu ya bigi hancinsa Gaga daya kamshim ba a makwafta Bane,tsoro ne ya kamashi bai gama firgita ba saida ya hango ragowar Doya soyayya a plate, Kara ya saki tare da dauko wani Dogon Spoon idan ya taba plate din sai yayi tsalle ya kwalla kara yana ja da baya,Shikura tana labe tana kallonsa sai dariya takeyi a boye,Tana kallo ya leka dustbin ya kara suman tsaye ganin kwalaye da ledoji iri iri a ciki harda robobin Ice Cream,mopper ya gani a jike alamar anyi amfani da ita,da sauri ya fita tare da daukan key din mota ya bar gidan a firgice, Shukura Saida ta tabbatar ya fita sannan ta fito karo na farko da ta fara yiwa gidan kallon tsab,ta dinga yawo tana shan kallon haduwa har ta shiga Bedroom dinsa na Alfarma kamar me ya hadu komai White.

Har toilet ta leka a fili tace ba ruwansu da tunanin mutuwa,Saman Bed din ne ya birgeta kawai ta haye Sannan ta dinga tsalle tsalle wai dadi ta kara kwanciya tare da bajewa Bata ma san sanda bacci ya kwashe ta ba sai da ta kwashe fiye da Hour daya sannan ta farka a gurguje ta sace Wasu Boxers dinsa,Dogon jean pencil kala biyu, ta kara bude wasu bangaren ta kwashi Singlet kala biyu wai zata dinga bacci dasu,Jallabiya kala Uku fitted har kala uku ta dauke masa,har Zata fita taga wasu biscuits manya masu tsada dasu chewgum iri iri ta ebo wasu da yawa ta fito tare da komawa wajenta na boyo,Tana fita Shi kuma Ahleef ya shigo tare da manyan Malamai har su goma kowanne rike da katon Qurani,babu Bata lokaci suka dinga zuba karatu ana korar shedanu har suka gama ya basu kudi masu yawa suka tafi tare da tabbatar masa an kori Aljanu dama rashin addua ne yasa suka mai da gidansa kamar dakinsu,Babban malamin yace Ahleef wato Allah ya taimakeka ka fada mana da wuri,da tuni Sun nakasa ka,ido ya zaro,Malam yace ae fa ai gidanka kasuwar Aljanu ce guda ta duniya,a nan kasa kasa suke zuwa siye da siyarwa amma yanzu mun koresu,Ahleef yace malam ka tabbata babu ko jaririnsu basu tafi Sun bari ba ? Malam ya karkace gemu tare da cewa ko tsinke basu bari ba ka godewa Allah,Godiya Ahleef yayi yana murna har ya rakasu ya dawo gidansa ya kara bajewa saman kujera shi a dole an kori aljanu,Lokacin Shukura har tayi wanka ta saka Jean dinsa fari tare dafarar Jallabiyarsa fitted duk da cewa Sun mata yawa sai tayi masifar kyau tare da yafa gyalenta na doguwar rigarta tayi Rolling sannan tace bari ta fita yawo ganin gari,ta Saman bishiya zuwa katanga tabi ta fita abinta,Shima Ahleef ya kira escort dinsa zasu kaishi wurin Momee yau za a sallameta,kuma Abba dasu Salman sunzo duba ta suna gari,cikin motocinsa na Alfarma suka jero kamar Gomna motar da yake ciki tana tsakiya,Shukura kuwa wahalalliya tana tafiya a gefen titin da jallabiyarsa a jikinta tayi kyau, white color,Jallabiyar Ahleef Unique ce yana ganinsu yasan nasa ne,sabo da kalarsu daban ake dinka masa a turkysh har wasu tambari ne dasu Wanda shi kadai ya zabi abinsa ake masa.
Motarsa tazo wucewa ta saitin Shukura dake tafiya ko layin Bata bari ba, Tunda Ahleef yaga irin tambarin Jallabiyar a jikin mace ya cika da mamaki gashi Ko wace tayi kyau kuma da gani ta maza ce amma sai yaga kamar ya santa ma,kuma wannan ai tafi waccen kyau da kiba tare da gogewa,ta window din motarsa yake ta faman kallonta ya kasa gano ta, Baki ya tabe a fili yace dama a duniya dole sai ka samu abu me irin Naka.

Yana Shiga Hospital yayi arba da Niima tazo itama yau,kirjinsa ne ya buga ganin yanda ta kara wani kyau da kiba gashi ta sha kyau,Nan take Tsohon ciwonsa ya motsa ji yake kamar ya rungumeta,ita kuwa Niima wani kallo ma take masa na wulakanci ita tunaninta kyau shine so,ganin tana da kyau yasa sai yanda taga damar juya maza,sai kallonta yakeyi kamar ya hadiyeta zuciyarsa tayi rauni Hawaye ke shirin zubo masa shi kadai yasan azabar da yakeji a kirjinsa.Momee ta gano hakan ranta ya kara jagulewa tana son Ahleef fiye da kowa,Abba ma bakin cikin Niima yake ta gama Bata masa rai,haka su Suhail,Abba ne yayi magana Ahleef an sallameta fa muje gida,Momee Hannunsa ta riko Cikin kasa da murya tace My Dear Son ya akayi ne ? Kayi hakuri kaci gaba da addua kaji,ka daina damun kanka zaka sa ciwona ya dawo,murmushin karfin Hali yayi kawai yace to Momee ba damuwa lets Go, har Abba sai da ya murmusa ganin yanda Momee da Ahleef suke magana a hankali babu me jinsu,Suhail yace Bro ko sannu da zuwa baka yi mana ba, Salman yace nayi fushi ni suna ta dariya Gaba daya banda Niima dake taunar chewgum ta wani hade rai,Ahleef ya kalleta dan kar Momee taga kamar ya tsani yarta yace yan mata ba magana ? Kamar gimbiya da kyar tace sannu ya kk ? Yace Hmm Kawai ya shareta,ba karya Niima satar kallonsa takeyi yanda ya gaji da haduwa ga kyansa ba a magana kullum karuwa yake,tabe baki tayi tare da cewa can da matsalarsa.

Momee tasan idan tace Ahleef sai ya dawo gida da zama ta shiga hakkinsa Sabo da Niima ce bai son ta zauna a ransa shi yasa yayi dan nesa dasu gwara ta kyaleshi ya samu Nutsuwa,suna Komawa gida tace Son tashi ka tafi gidanka ka huta naga ka gaji jeka gobe ka dawo jeka huta,dama Kadan yake jira Sabo da Niima tana ta faman shige da fice hankalinsa yana tashi soyayya tana matsa masa,sallama yayiwa kowa ya wuce zuwa gidansa zuciyarsa a jagule,lokacin Shukura ta dade da dawowa gidan tuni.sai yanzu Yaga Bedroom dinsa an lalata masa shi kamar wani ya kwanta,kayansa kuma kamar an taba su, sai yayi tunanin idonsa ne ke masa gizo Amma gobe zai fadawa masu gyara gidan su kara gyara gidan,kudinsa ya duba ya gansu yanda suke ba a taba ba, shakira halayenta ba sata a ciki,ko nawa zata gani komai talaucinta baza ta dauki abinda ba nata ba bare kudi.

Bayan yayi shirin bacci sai ya fito zai duba gidansa tare da kashe Light lokacin Shukura ta shiga kitchen dinsa ta kwaso su Apple da sauran kayan Fruits tana wucewa shi kuma ya fito yaji kamar an rufe kofa da gudu yabi bayanta amma kafin ya kamata tuni ta boye shi kuma gani yakeyi kamar mutum kamar ya gani,a hankali yace lallai aljanu ne a gidan nan masu yawan gaske,amma akan na koma gida da zama gwara nayi rayuwa da Aljanu Sabo da Niima ta dawo gida yanzu,bazai iya canja gida ba Sabo da yafi son gidan da yake ciki, to ko Security camera zansa koma mene ai zan gani,to ai aljanu ne kuma ba a ganinsu idan kuma ya gansu zai tsorata,motsi yaji kamar an bigi wani karfe da sauri ya juya baya fara gudu gudu sauri sauri ya kulle kansa a Bedroom tare da kudundunewa cikin bargo yana addua iri iri har bacci ya kwashe shi,Shukura tana kallonsa tana ta dariya kasa kasa lallai wannan matsoraci ne na gaske.

Saudatu yau Alhajin da suke aiki a gidansa zaiyi baki zasuyi Meeting na business Ogansa me gidansa tare da Dansa zai kawo masa ziyara gidansa a nan zasuyi Meeting Sabo da Alhaji Dauda abokin Abba ne kuma suna Business da Ahleef yana ta musu mitar sunki zuwa gidansa,gaba daya gidan yan mata da samari tare da iyayen duk Sun rude Sun gigice sai kwalliya Suke zubawa kamar zasu je ganin sarki Sabo da Dan Abba yace yana sonsu,Mama Cewa take yawwa yan matana kuyi kyau sosai so nake Ahleef ya zabi daya a cikinku ya aureku burina ku auri me kudi irin babanku Wanda zai dinga kaini Makkah da kasashen turawa,wanda zai dinga siyo min super England ba wanda zai siya min Nichem ba,gidan da zaku huta gidan Naira,Ko Abban ne yace yana Son daya dole na bashi komai tsufansa,Yan mata suna dariya tare da cewa ai sai Mama Allah bar mana ke, Wani Saurayi zai kai shekarun Ahleef Mubaraq yace ni kaina da Abban yana da budurwa lallabawa zanyi nayi Auren jari da ita,Karaf Mama tace tana nan sunanta Niima har Company gareta ban San me yasa aka fasa aurenta da wani ba ban San kan lbr ba Amma tana nan batayi aure ba kaje kayi duk yanda zakayi ta soka dama gaka kyakyawa da kai duk yarana babu me kyanka,duk abinda suke fada Saudatu tana goge goge tana jinsu sai da gabanta ya fadi da taji an ambaci Ahleef me sunan jaririnta Amma tasan shekaru 31 ba wasa ba, tuni ta hakura tasan danta yan mafiya Sun yankashi tuni,Har so take a duniya ta ga waye wannan me sunan danta daya bace gashi sai rubibinsa akeyi Sabo da yana da kyau da kudi.aranta tace ai kuwa sai ta labe ta ga waye wannan baza tayi nisa ba.

tsawa taji wata budurwa ta buga mata me suna Hafsy,Hafsy itace budurwa Babba a gidan kuma tana da dan kyau kadan shi yasa Momee tace lallai ta makalewa Ahleef har ya aureta,gashi kuma duk gidan ita ke wulakanta Saudatu fiye da kowa, watarana har marin Saudatu ta taba yi, tafi kowa fitsara,daga ita sai Mubaraq a rashin mutunci,sai kanwarta Zahra sauran suma ba tarbiya amma mutum uku sune kan gaba, Mama kuwa itama haka take har Alhaji Dauda amma bai fiye wulakanci ba shi sai kadan kadan.Hafsy ce ta watsawa Saudatu Harara dalla malama wuce inda kika fito sai sa ido,Mama tace hmm kuma dai kwa fada suka sheke da dariya gaba daya,Saudatu ta riga ta saba kawai sai ta wuce abinta a ranta tace duniya ce, tazo zata wuce ta kofa Zahra ta bangajeta ta wuce abinta.

Yamma 5pm kowanne dake gidan yaci kwalliya yana jiran manyan baki suzo,Hafsy sai kwarkwasa akeyi,5:30pm motoci laba laba Sun kai 6 ne sukayi parking a cikin gidan,Yan mata fa ansha kyau,Guards ne suka fara Budewa Abba ya fito sai Salman da Suhail Sun dau wanka suna zuba Kamshi,Wata rantsatsiyar mota suka sake budewa sai ga Ahleef yaci uwar uban Wanka kamar baza a mutu ba,cikin manyan kaya farar Shadda kal tasha dinki fitted ta samarin Abuja, sai kyalli da sheki yakeyi,Yana uban taku kamar Sarki yana basarwa ga kyau kamar wankin Engine,kamshinsa duk ya cika gidan,yan mata sai leke suke ta Window,Hafsy tace wai...wai... Zahra na riga ki wannan me farar shaddar nake so,Zahra ta hayayyako da masifa wlh na rigaki shine nawa,ai wlh baki Isa ba,Babba sai babba,yaro kuwa na yaro ne, Jamila wacce suke kira Jamcy itama tace Ahleef take so suna leke ta window,Nan fa fada ya kaure a tsakaninsu sai da Mama ta raba su da kyar, Mama tace ku nuna min akan Wanda kuke fada naga kyan nasa da kuke fada,Zahra tace leka ki gani Mama gashi can da Farar Shadda tunda muke bamu taba ganin me kyau irinsa ba a duniya,Mama ta leka nan take ta hangame baki tare da cewa ina ma ana tariyo baya nima na dawo yarinya Akan wannan wlh sai nayi kisan kai,Dama sun San Mama akwai budurwar zuciya duk harkar charting baya wuceta,Mama ta wuce tace na tafi tarbar baki anjima kuzo ku gaisheshi.

Alhaji Dauda yana tare dasu a katafaren Palonsa suna ta Hira daga nan suka fada harkar Business,Mama ce itama ansha wanka taje suka gaisa taci kitson attach kamar arniya tana zaune a palon kusa da mijinta,bayan 30mt sai ga su Hafsy suna ta layin gaishesu suna karairaya,daga nan Mama tace suzo aci abinci,Ahleef kawai waya yake dannawa Ko kallo basu isheshi ba,babu wacce ya amsawa gaisuwa sai Mama kawai,su Salman kuwa harkar gabansu sukeyi suma,Jikin yan matan yayi sanyi amma basu hakura ba.
Bayan nan Ahaji Dauda yasa aka kawo musu abinci a nan Palon ba sai anje Dining ba,duk Sun zagaye ciki harda Zahra da Hafsy, Mubaraq yana ciki sai Mama da Jamcy.
Yan aiki aka bawa Umarnin kawo abinci ciki harda Saudatu sabo sunfi yarda da tsabtarta,Saudatu ta kawo katon Flask ta ajiye a saitin Ahleef cikin Nutsuwa tana Tsoro karta yi ba dai dai ba, tsaki Hafsy taja tare da cewa dan Allah madam ki ajiye ki tafi ke kullum baki San aikinki ba,Zahra ta kara Jan dogon tsaki uwar kinibibi tsohuwa dake,Mama maimakon tayi fada sai tace hmm Saudatu kenan Uwar Iya,Alhaji Dauda ne yace ku fa bakwa kyautawa Allah kyauta abinda yace kenan,Mubaraq ya shekawa Saudatu harara.
Abba dama shi ya dade da sanin gidan abokinsa ba tarbiya baiyi mamaki ba, yana Allah wadai da halayensu,Salman suma mamaki ya kamasu dattijuwa kamar wannan ana zaginta,Ahleef kam da sauri ya kalli matar da akayiwa tsaki dattijuwa sosai irin wannan ita kuwa ta bar aikin mana idan ba son kudi ba, ana zaginka kana zaune,Su Hafsy yaji ya kara tsanarsu yanzu sosai,Saudatu ya gani ta kawo wasu cups,Mama ta daka mata tsawa zubawa baki abinci mana,su duk ganinsu birgewa sukeyi su masu kudi.

Saudatu jiki na bari ta fara zubawa Su Abba,zata zubawa su Salman yace no na koshi ni,Suhail ma yace bazai ci ba ruwa zai sha kawai,Saudatu da fara'a ta kalli Ahleef tare da cewa kai fa Alhaji me za a zuba maka ? Ahleef ya kalleta aiko sai ya saki murmushi kamar ya santa yace Umma wanne kika dafa da hannunki ? Ta nuna masa kala uku harda Zobo Drink me dadi tace wannan nayi da kaina,yace zuba min su zan ci ni,Ita dai Saudatu sai tana ganin kamar ta San Ahleef amma ta kasa ganewa,Mama kuma da Su Hafsy sai kallon Ahleef sukeyi suna kallon Saudatu sai suka ga kamarsu daya har tayi yawa ma, komai nasu har hakoran kusan iri daya,Bayan ta zuba masa ya karba da kansa, har zata bar wajen Ahleef yace zauna mana Umma idan na gama sai mu tafi na jirasu a waje,Tsoro ya kama Saudatu tasan yau tata ta kare a gidan,tana zaune ya gama cin abincinta me shegen dadi sannan ya Mike Saudatu tabi bayansa suka fita har waje,yace Umma haka kuke rayuwa ke yar aiki ce ? Saudatu tace ae wlh rayuwa kenan,Ahleef yace ke da mijinki duk nan kuke aiki Saudatu tace ae a takaice ta bashi labarin irin zaman da suke a gidan,da wulakancin da suke fuskanta ita da mijinta,Ahleef ya tausaya musu yace watarana idan na samu time zan daukeki ki dinga dafa min abinci ina biyanki albashi Kin yarda? Murna ta kama Saudatu ta dinga godiya harda durkusawa har kasa,yace mijinki kuma sai na kaishi Office dina yana min goge goge ina biyansa,Zan baku wajen zama a gidana zan dawo na daukeki nan da 3wks.
Godiya kawai Saudatu keyi masa,yace haba Umma ki daina godiya haka ya zaro 10k ya Bata.

Abba ya fito tare da yan gidan suka rakasu suka tafi,Mama lokacin suka rufarwa Saudatu da balai da masifa iri iri suka ce gobe sai Sun bar musu gida,Asiri take wa bakinsu kowa yana sonta,tana mallake musu masu kudi,sai kace wata budurwa ita me zatayi da wasu maza masu kudi Saudatu ta furta a ranta, Babu hakurin da Bata basu ba har mijinta da suka sa masa dan dako Sam suka ce dole gobe su bar musu

1 Comments On JIN DADI SABO
avatar
mahamane-noura

2 years ago

Reply

Asalama alaikum, dan Allah yane ake sauke littafin akan waya

Please Login or Register in order to submit comment