Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

gida.

Tunda Shukura taga Ahleef ya bar gidan ta fito ta gyara gidan Neat har samansa yana ta kamshi ko ina ta canja tsarin gidan yayi Masifar kyau, tayi girkinta taci ta koshi ta dauki remote tana ta danne danne har Allah ya taimaketa ta kunna TV ta kamo tashar American film tana ta kallo har ta gaji ta mike ta shige bedroom din Ahleef toilet dinsa ta shiga tace dole na dana,ta fesa wankanta da kayan wankansa,ta fito ta shafa Body lotion dinsa,kayan gyara gashinsa da su ta gyara nata yana kamshi, Cikin sip dinsa ta bude ta duba cikin wankakkun shaddojinsa ta zabi wata ruwan toka ta dauki iya rigarsa wata yar fitted hannun links ne ta sa abarta shar tayi kyau kuwa,bata sa da wandon ba, turarensa iri iri ta fesa sannan ta kara gyara masa komai na dakin ta fito ta baje a palo tana kallon film tana shan lemo abinta,Ahleef har ya dawo Bata Sani ba, sai ji tayi ana kokarin bude kofa da gudu ta kashe TV ta arce inda ta saba buya,tun daga waje Ahleef ke Jin karar TV amma abin mamaki yana shugowa yaga TV a kashe,sai kwalin lemo,gashi shi yasan bai sa a gyara masa gida ba amma yaga gida sai kyalli yakeyi da sabon kamshi,tsoro ya kamashi ya haura sama yasha mamaki kalar gyaran dakin na musamman har Bedsheet an sake masa,Ya fito ya duba gidan kaf ko ina yasha gyara, ya tambayi security ko wani ya shigo ? Yace shi ba Wanda ya shigo,ya dawo ciki a fili yace wlh idan na kara ganin abin Tsoro guduwa zanyi na bar gidan.

Kwana uku tsakani kullum sai Shukura taje wajen da suke soya doya amma ba Saudatu ba labarinta,ta tambaya amma babu Wanda ya San inda Suke,har gidan Da Saudatu ke aiki taje amma akace an koresu daga aiki har kuka Shukura tayi sannan ta dawo gidan Ahleef taci Gaga da buyanta.
Yau Misalin 12 na dare Ahleef yana gida,Shukura ta sa rigar Shaddarsa wata Milk color Garin labe labenta ta daki wani karfen motsa jiki ta fadi Tim a kasa,kafarta ta dauje Jini yana fita,Kuka ta fashe dashi sosai ta manta Sam da za a kamata Bata kaunar ganin jini na fita sai ta fara kuka,kuka ta shiga rerawa,Ahleef Tsoro kamar ya sume,ya dauki katuwar kujerar Mirror yana lallabawa da niyyar duk Wanda ya gani ko aljanine fasa masa kai zaiyi,yana lallabawa a tsorace har ya bude kofar inda yake Jin kukan na fitowa a hankali ya Shiga,Yaga Gashin mace ai ba shiri ya jefar da kujera zai gudu regarsa ta makale a kujera ya fasa kara,Shukura kuka ya dauke dif tasan asirinta ya tonu shike nan korarta zaiyi kwanan kan titi ya ganta,Fuskarta ta dago suka hada ido da Ahleef yana kokarin guduwa rigarsa ta makale,Cak ya tsaya da yaga kamar yarinyar da suka kwanta a Hospital da Momee,kuma wacce ya gani sanye da Jallabiya irin tasa,tabbas itace ashe dama Kusan 2wks kenan tana gidansa ashe itace take sawa yana tunanin Aljanunee,wani bakin ciki ya kamashi,tana jira taji saukar duka sai taji cikin fushi yace Amma kin zalunceni kin cutar dani,all ths While ashe kece,why baza ki fada min ba ki rokeni na baki inda ya dace dake,hawaye ya kwararo mata na tsoro cikin rawar murya tace uhmm..tsoro...tsoro naji karka koreni wlh zan baka labarina ni marainiya ce,Hey...u better stop tht nonsense ina ruwana da maraicinki Who even care,Mikewa tayi ya kare mata kallo wato kayana ma kike sawa Sabo da kin rainani,ashe duk abincin nan kece kike cinyewa,shuru tayi ta wani turo lips Gaba,tace Allah baka hakuri, dan Allah kayi hakuri bari na bar ma gidanka,ta kwaso kayansa sunkai kala bakwai da take ta sawa tace ga kayanka,mamaki ya cikashi ashe barnar har ta kai haka ji yake kamar ya kasheta,rokonsa tayi dan Allah ka taima kamin da wajen kwana kafin na samu kudi,Kin San da haka me yasa baki rokeni ba tun wuri,har Ya juya zai tafi ya dawo yace sai kiyi ta zama Mayya,ya Leka lungun da take boyewa tana bacci yace hmmm tare da bude Bedroom din da take shiga toilet din ciki tana wanka yace ga daki nan kuma wlh kina min shirme sai kin bar gidan nan tunda bana ubanki bane,Murna ta kamata ashe haka yake da mutunci, bata taba zato ba gashi ya bata daki ma tsantsarere, kallonsa tayi baki a washe tace ashe mutunci ne da kai haka na gode,Allah yaji kan magabata,Allah kara budi da arziki ya biyama bukatunka na alkhairi yasa Aljanna makoma,Baki ya tabe tare da cewa yar Maula,Shuru tayi murna ta isheta Bata ma ta ciwon da taji tace ba dadewa zanyi ba ina samun wasu kudi zan bar ma gidan,ina sa rai da wasu kudade naji a jikina zanyi kudi kwanan nan sai na barma gidanka karka damu saura kadan.tsaki yaja yayi gaba abinsa yana cewa sai kinyi kudi ma zaki barmin gida? Ba rana kenan ya barta a wajen tana murna harda tsalle.














AsmaBaffa
[7/22, 1:12 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO











7










Official








By
AsmaBaffa











ZAMA NA AMANA 2 FACEBOOK wannan page naku ne,na gode Allah ya bar kauna.

FLOWER jinjina gareki wajen Sharhi ba daga kafa tnx alot.



Fans bana son tnx fa Sharhi nake bukata ni.








Bedroom din daya Bata ta fada ciki tare da kwanciya saman Bed tana faman murna,yau ba wani tsoron Aljanu yayi bacci sosai shi kanshi washe gari yayi mamakin baccin daya kwasa ya nisa tare da cewa amma yarinyar nan ta cuceni wlh yaushe rabon da nayi bacci haka,ko gidansu zai maidata wajen Momee ina shi ina kwana gida daya daga shi sai budurwa ina bazai iya ba, wani tunani ne ya fado masa sai kuma yace no Momee zata kwasheta tace zata zauna a wajenta har abada shi kuma bai Son kwashe kwashe kawai ta gama kwanakinta ta bar masa gida shike nan,Saudatu ce ta fado masa a rai yace dama dawo dasu yayi gidan suka fara aikinsu kawai yace da yamma zai tura Driver ya dauko masa su.

Saudatu kuwa tunda aka koresu basu da wajen zama sai can karkashin gada suka koma suna kwana ita da Alhaji Amadu,ruwa,iska komai a kansu yake karewa suna Cikin yan cirani suna fadi tashi,Babu wurin kwana ina wata sana'a idan ma Sun bar gari to basu da wajen zuwa, Ahleef yana ranta Sabo da yace zai daukesu aiki dan haka Kullum Saudatu da mijinta sai sunzo kofar gidan Alhaji Dauda Sun yini Ko zasu ga Ahleef yazo daukansu,Saudatu da ta gaji da wahala Duk dauriyarta Yanzu kuka takeyi sosai wai su me yasa tuntuni rayuwarsu a wahala suke ne,yau ma suna nesa da gidan Alhaji Dauda ta tsuguna a kasa Bata San sanda ta fara hawaye ba, shi kuwa Alhj Amadu kusa da ita ya zauna yana tausaya wa kansu matarsa balarabiya talaucinsa yasa duk ta tsufa, da yasan hakane da bazai aure ta ba, tunda yasan talauci a jininsu yake gashi har yau ya jawowa masoyiyarsa ma, Lallashinta ya fara suka samu wurin inuwa suka zauna Kafadarsa ya miko mata tare da cewa kwanta Saudat ki huta,ita kuwa dama dake balarabiyace ko a jikinta ba ruwanta da mutane ta lafe a kafadar Alhj Amadunta.
Haka yauma suka karaci zamansu har dare ba Ahleef ba alamarsa suka hakura suka koma Karkashin gadarsu inda yan cirani ke taruwa su kwana mata da maza babu iya shegen da ba ayi a wajen sai dai ka sharesu kawai.

Yau da safe da wuri sai ga Shukura da shishigi har kitchen din Ahleef anan ta soya doyarta da kwai Irin yanda Saudatu keyi,ta dafa tea yasha kayan kamshi ta ajiye a Dining ta wuce dakinta domin yin Wanka, Ahleef ya fito cikin Shirinsa na fita Office yaga an shirya abu a Dining,budewa yayi yaga doya ta soya yanka biyar ta cikin mutum daya,wato kanta kadai ta Sani, sai ya zauna yasha tea dinsa tare da cinye doyar tata tas bai bar ko kwallo ba
Ya Mike ya koma Bedroom dinsa yana amfani da System Kafin ya fita,Shukura Ansa jallabiyar Ahleef Milk ta fito zata kwashi girki ta bude plate wayam ba komai,tace to ko shine ya cinye min? Bari naje na tambayeshi naji aiko idan me gadi ne wlh sai ya gane kurensa kuji karfin hali,Saman Ahleef ta nufa sai taji tsoro tasan baya daukan raini,sai da ya fito cikin shirinsa tana palo lokaci da saura ta tsuguna har kasa jikinta na rawa tace ina kwana, baki kawai ya tabe,ta maza tayi tace uhm...Kawu na kaine ka matsar min da abincin dana dafa,wai wayo tayi masa ya matsar mata kar tace ya cinye mata, Shuru yayi mata tace Kawu dan Allah nace Ko kaine ka boye min wata doya a plate? Na sanka da kirki shi yasa nace ko kaine ka boye min ita, ya ganeta tsab, sai yace ban gane ba au har girki kikeyi dama? Au ba kai ka cinye ba ? harara ya zuba mata yayi gaba tare da cewa ni gidana tare da Aljanu nake rayuwa maybe sune.sai yaga ita ko a jikinta Bata wani Jin tsoron Aljanu Mamaki ya kamashi yar yarinya karama da ita Amma Bata Tsoro lallai girman kauye ce.

Sabon shiri ya sake kamar baza a mutu ba, ya fito ya iske Shukura sanye da Jallabiyarsa Milk sabuwa dal ta saka masa ta wani jera girkinta a gabanta harda Fruits cikin karin safenta hhh kuma abinda ya bashi dariya da yaga danwake a gefe da safe haka,ita Bata iya girke girke ba sai na gargajiya sai doyar da ta koya wajen Saudatu shike nan,suma na gargajiyar kadan ta iya,duk Bata San illar zama daga ita sai namiji a gida daya ba,sabo da iyayenta basu nuna mata komai ba kawai abinda taga dama shi takeyi. iyaye Irin wannan ke jawowa kaga yaran wasu kamar dabbobi haka suke a cikin alumma.
Tsawa ya mata kadan keee...tayi mugun tsorata ita Bata saba ba,ba a yi mata tsawa, sai tagigice kawai ta fashe da kuka, Kuka take kamar ana mata azaba,lallai zaki bar gidan nan kuwa dan iskanci daga miki magana,kayan maza kike sawa baki da ilmi babu kyau mace nasa kayan da Akayi su domin Maza haka ma maza,Allah ya tsinewa mace me kamanceceniya da da Namiji, haka Namiji ma,sai kina shigar min Bedroom baki da hankali kina ebo min kaya.
Shukura wacce tayi mukus taji ance zata bar gidan,Ta turo baki cike da shagwaba kamar zata narke tace to ai lalurace tasa,kayana suna Hotel na gudu kudina ya kare,kuma bani da kaya shine na ranci naka ka daina masifa pls kudi Sun kusa zauna min kwana nan zasu zo zan biyaka abinka, kuma sai na siye gidan nan idan nayi kudi ya zama nawa gaskiya yayi min.

Dariya ma ta bashi daga taimako shine zata siye masa gida idan tayi kudi,mazewa yayi yace to karki kara taba min kayan sawa ta ya isheki haka,in ba haka ba wlh bulala zan siyo a gidan nan,Dariya tayi ya kalleta suka hada ido ya bata rai Irin karfa a rainashi,wayarsa ce tayi kara ya dauka Hello Momee gani nan Airport din zan zo yanzu,da sauri ya dauki hanyar barin Palon yace ke taso muje na siya miki kaya karki kara taba min kaya,da Karfi tace Allah da gaske kake? Kace wallahi tallahi? taga bazai kulata ba kuma yayi Gaba abinsa,Da gudu ta kwashe kayan abincinta ta kai Kitchen ta figi dan gyalenta ta yafa a saman kanta sanye da jallabiyarsa ta fito da gudunta,Jallabiya ta tadeta ta fadi tasan jiranta yakeyi amma sai ta fara kuka a wajen yanda ta saba yi a gidansu gaban iyayenta,ko kulata baiyi ba da Alama ba driver zai tafi shine a mazaunin Driver,da sauri ta kara mikewa a rude ta bude Bayan mota ta zauna maimakon ta zauna yanda ake zaman mota duk ta rude sai ta zauna takalli bayan motar saitin Boot kamar biri,kafafunta ta lankwashesu ta zubawa bayan titi ido ba gabansa ba,Ahleef bai san sanda dariya ta kamashi ba kawai bai kulata ba dan mugunta yaja mota a haka,sai dariya akeyi Sabo da duk motar daya wuce to sai Sun kalli fuskar Shukura ana ta dariya,Yana Sani ya fisgi motar tayo luuu ji kake guf ta bige keyarta da bayan kujerar gaba me zaman banza tunda dama baya take kallo.

Har airport yaje yayi parking sannan ya fito ya Shiga bayan motar kusa da Shukura,wata Igiya doguwa ya dauko,yace oya kwanta,a tsorace ta kwanta tunaninta saceta zaiyi ko dan yankan kaine dama Bata Sani ba ta kawo kanta.
Hannayenta ya hada biyu ya daure tam,Kamshinsa duk ya cika mata hanci Har hanci take kara budewa,Kafafunta suma ya hade ya daure sannan ya fita ya kulle motar yayi gaba wajen su momee.

Suhail su zasu koma Us schl,sunyi shirin barin kasar,Momee kuwa Abba yayi fushi matarsa tayi jinya an boye masa shi yasa yace da ita zai tafi yanzu yafi kula da abarsa sai nan da 2mnths zasu dawo kasar, Latifa da Niima kawai za a bari,sai Ahleef dake can gidansa,Sallama sukayi da juna a gurguje an fara screening ma, Shukura tana mota da kyar ta Samu ta Mike Zaune tana hango Momee suna magana Ahleef Sun kebe,wayyo taso Ace Ahleef bai daureta ba da sai taje wajen Momee ta gaisheta Amma ba damar hakan, Niima tana Airport din can gefe tare da sabon saurayinta Yazo wai zai yiwa iyayenta a dawo lfy, kishi ya kama Ahleef yasan dan ta kona masa rai ne yasa ta kira saurayinta,kuma kishinsa ya motsa da kyar ya danne Har su Momee suka tashi sannan ya bar wajen a fusace,yana zuwa fuska ba Rahma ya kwance daurin da ya yiwa Shukura yace fito ki koma gaba, lokacin da Shukura ta fito har zata shiga gaban mota akan idon Niima,kamar kiftawar ido sai ga Niima taja rigar Shukura da karfi ta fisgota baya,Shukura ga saurin zuciya da daukan Hukunci Bata tsaya sanin wace ko waye ba yar karama da ita amma ji kake Tasss ta kwashe Niima da mari me mugun Zafi Wanda saida marin ya jawo hankalin kowa aka fara kallonsu,Ashar Niima ta dura kafin tayi wani motsi tuni Shukura ta shige mota ta rufe tare da sauke Glass tana cewa ki kiyayi ranar da zamu kara haduwa wlh sai na miki Illa ba irina akewa wannan a kwana lfy ba ba a takani duk inda muke da mutum, kaf Abuja birnin tarayya kinga Wanda ya Isa dani ta furta tana Nuna Ahleef,shi kadai ne zai iya Sani ya hanani,shine me fada aji shi kadai zan iya kyalewa sai wasu Dattijai mata su biyu,(momee da Saudatu) Amma bayan wannan to babu Wanda ya Isa ya min na kyaleshi bare ke banza a banza gaja,kazama,yar Kauye dake ana birni amma an kasa wayewa ban hakura ba duk ranar da muka kara Huduwa wlh sai kin fada,me kai kamar murhu.Niima ta Sandare a jikin motar tana mamakin wannan yar yarinyar da Bata fi mate din Latifa ba Amma take ci mata mutunci haka ta window cikin mota take aiko mata da zagi haka,Shukura ta tsinke mata tunani da cewa da Allah ki dinga sallah akan lokaci ko kyayi kwarjinin musulunci gashi Sabo da baki da kwarjini kamata na kare miki zagi da gani addininki bai cika ba, kinga kawu Ahleef shi ko kallon banza ban Isa na iya yi masa ba,ke kuwa har mari kika sha to ki kiyayeni yarinya dan ba sanda a kusa ne da wlh sai na sumar dake da ita,wani farin ciki ya lullube Ahleef yau Shukura ta gama masa komai a duniya bai san sanda ma ya fara dariya ba dama yana neman wanda zai goge Niima shi idan yayi mata girmansa ya zube kuma ko Sabo da Momee tare da Abba baici ace yayiwa jininsu wani abu ba.
Niima ta girgiza da ganin me mugun kyau haka,dama ana samun irin wannan a kasar nan, To a ina Ahleef ya samota kyau irin na Ahleef Amma yarinyar kamar ma ta Fishi ita bata taba ganin me kyawun Shukura ba a duniya sai ko Ahleef,nan take Haushin Shukura ya kamata taji ta tsaneta Sabo da ta fita komai da komai,ita Niima Allah ya zuba mata Hassada Bata kauna wani ya fita,a ranta tace sai na gano yarinyar nan yar uban wace,kuma tana bakin ciki Ahleef ya samu me kyau irin wannan tafi so taga ya auri mummuna dan kawai kar ya ji dadin duniya,bata so ta Ganshi yana farin ciki shi yasa ma Bata damu sosai ba akan cin mutuncin da Shukura tayi mata,.

Ahleef ganin Niima ta koma wajen saurayinta cike da kunyar marin da Shukura tayi mata,sai ta tsaya tana nade borin kunya da hauka tana zubawa Saurayin Murmushi tare da rike hannunsa suna soyayya, Ahleef yaji haushi a kan titi ba mijinta ba saurayi kawai Amma Niima ta tsaya a bainar mutane yana tattabata harda su kiss,yana kallo yar Momeensa guda Zata lalace ba damar magana kawai yaja motarsa bai tsaya ko ina ba Sai wani Mall kato inda Saudatu ke Soya doya da kwai har wasu Sun fara siyar da Fruits a wajen, Shukura sai kallon wajen takeyi,Ahleef duk ransa ya jagule bama ya Jin zai iya komai,kawai Kudi masu yawa ya mikawa Shukura tare da cewa shiga nan ki siyo kayan sawa, Shukura ta fita dukkan mutanen data Sani saida ta fara tsayawa suna ta gaisawa ana wasa da dariya sama sama,Ahleef yana cikin mota yana kallonta yanda take Faran faran da mutane yana mamaki duk ina ta sansu haka,Sai tambayarta akeyi ina Saudatu? Shukura tace ta canja unguwa ne, Haka ta shiga Mall din abin haushin tana yin layin kayan ci da sha da kayan girki sai ta manta da kayan sawa yace ta siyo, chocolate,Biscuits su snacks iri iri kayan zaki ta kwaso,tayi layin kayan dafawa Ko Bata sanshi ba indai ya birgeta sai ta siya,ko idan taga Hoton tukunya a jikin ledar, Ice Cream iri iri, taga yogourt tace laaa bamu da irin wannan a fridge dinmu nan ma ta kwasa,harda su markadaddiyar gyadar gongoni tace wannan da gani zatayi dadi da Bread, side din Drinks taje nan ma taga wata katuwar kwalaba tunaninta lemo ne ashe giya ce duk tsadarta Sabo da kwadayi da son dadi saida ta siya,karshe taga wani wajen Shawurma da ake yi a ciki ta siyo abinta,sai data kashe kudin wajen kayan ciye ciye sannan taje side na kayan kwalliya ta kwaso iri iri babu duhun kai duk abinda Bata gane ba sai ta tambaya an wayar mata da Kai,Sai data gama sannan ta tuna me akace ta siya,a fili tace ai wlh gwara kayan dadi abinda zanji dadi akan wasu kayan sawa,ai da ragowar kudin bari na siyi kala biyu sun isheni kafin nayi kudi ai na kusa zama me kudi.
doguwar Riga ta dauka da Riga da skert Engliish wears sai panties guda biyar,da wani 3qutr tight legins,sai flat shoe kala biyu tace Sun isheni zaman duniya bana kiyama ba taja kayanta takai ta biya Kudin sai dubu uku ce ta ragu change,tace kai bani abin dadi na sauran Canjin babu Awara da kwai a nan ne wai ? Dariya me auna kaya yayi sosai yace babu Hajiya,tace to Kantu me sugar fa ko na gwangwani babu ? Yace sai Snail da frog na gwangwani abincin yan China ne,ido ta zaro tace kwado da dodon kodi ? yace ae,musulmi suna ci ? Ya halatta ? Yace sosai ma ai abin ruwa ya halatta,tace da dadi ? Yace sosai ma, tace to bani Snail kawai banda kwado bana sonsa,yace kin San dadi yafi dadi musamman kika hada shi da vegetables yasha miya me kyau,tace ka hado da ganyan miyar,Mutumi dai ya bata snail da wani ganye kala uku na turawa da suke girki dashi,Ahleef yaga ana ta fito da ledoji kawai boot ya bude aka zuba komai sannan ta zaga ta shiga suka tafi sai murna takeyi kamar zata tashi sama.

tsoro ne ya shigeta ganin yanda yake tuki ransa a bace kamar an aiko masa da mutuwa sai tsaki yake ja,shuru tayi itama Bata ce komai ba,tunaninta ma ko ita tayi masa laifi a hankali tace ko Budurwarka ce na mareta ban Sani ba ? Shuru bai kulata ba,to ko kanwarka ce ? Da kyar yace Budurwa tace,baki ta bude tace Allahhhhh.... Sarki yi hakuri ungo kumatuna rama mata marinta,Dariya ta bashi sosai,tace ka rama mata mutum yana ci da kai ya baka wajen kwana,Sutura ka Isa ka Bata masa maza dalle ni da mari,dariya ya shiga yi nan take Ya koma normal cikin farin cikin da ya dade rabon da ya samu,tace gaskiya Budurwarka Bata Sonka kana gani sai kula wani takeyi yana yi mata abin cikin Film din turawa amma kayi shuru gaskiya mijin tace ne kai,mijin Hajiya ka bada maza, murmushi yayi kawai, Kallonsa takeyi yanda yake me mugun kyau kamar Saudatu musamman idan yayi dariya, yee...wlh irinku daya da wata Tsohuwa me saida doya,juyowa yayi ya dan kalleta ta kwalla da karfi Yeee wlh Saudatu ce kai, Dan kara yin dariya mu gani ? Yaki yi,Shagwaba ta fara dan Allah kayi kaji Kawu Ahleef,har kwakwalwarsa saida tayi wani dumm yanda tayi shagwabar, Yana tuki ta bigi kafadarsa kadan ya sake juyowa suka hada ido ta kyalkyale da dariya tace Saudatu ce wlh, baki ya tabe tare da cewa ki daina hadani da wata yar tasha me doya kinma rainani ki rasa wacce zaki ce muna kama sai me soya doya a titi,Kai wlh ba yar tasha bace mutuniyar kirki ce mace ta gari kuma kyakyawa balarabiya baka ji larabcin da takeyi ba, Ahleef yace koma me takeyi ina ruwana,Dan Allah karka ciwa Inna Saudatu mutunci wlh yanzu nafi sonta a duniya bani da kamarta,ina ma zan ganta da a gidan dadi take wajenta zan koma ta rikeni,Oh sai gidan dadi ke kike so ? Wlh kuwa to bakina ya saba da dandano taya zan so wahala ai sai dole.uhmm kawai yace Jin yanda yar karama da ita ta iya zance haka.suna zuwa gida yayi parking yace to Saudatu muje,Dariya tayi tace suna na yafi na Saudatu dadi wannan na tsofaffi ne, Saida ta kwashe komai ta shigar dashi zata boye yace kawo sai naga me kika siyo nan fa kuma tayi miki miki tana zare ido tace ni dan Allah tunda Sabo da Allah ka taimakeni basai ka gani ba, U are Crazy dalla miko na gani a tsawace ya furta,da Sauri ta dauko komai ta jera a gabansa ya shiga Dubawa,mamaki ya cika shi ganin kayan da suke cikin ko wacce leda,bai San sanda ya kama kunnenta ya murde ba cike da bacin rai kara ta saki sosai ya murde da karfi,ya zuba mata rankwashi yafi biyar masu zafi sannan ya saketa tare da tureta gefe saida ta fadi kasa,Kuka ta zauna tana ta yi a wajen tana ni nafi son kayan dadi kawai kace kayan sawa zan siya, kuma ai kala biyu Sun isheni,Kwalbar giyar ya dauke yace wannan fa Alcohol ce kika siyo,Shuru tayi tana kallo tace to meyasa suke siyarwa idan ba tsinannu ba ni na Zata abin dadi ne ma,giyar kawai ya dauke yace kwashe tarkacenki ki bar min palo,tace nima ai yar gidance palonmu zaka ce abinda na kusa siye gidan ma baki daya,ki cire wannan hakorin makkah naki na karya,wlh bana karya bane kuma ba Makkah zaka ce ba Makoki zaka ce Sabo da zuwana makkah sau bakwai ba daya ba kaga ya wuce Makkah sai makoki, nifa yar me kudi ce ka daina ganin kai wani me kudi ne, Babu me kudin babana a garinmu.Harara ya
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On JIN DADI SABO
avatar
mahamane-noura

11 months ago

Reply

Asalama alaikum, dan Allah yane ake sauke littafin akan waya

Please Login or Register in order to submit comment