Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta hakane kad'ai zamu samu biyan buk'ata, dole sai yaron ya kusanci yarinyar, tom kinga idan akai auran ai zasu kasance tare, tom alokacinne ke kuma zaki basu maganin". Ya mik'ama Farida maganin, ya ce, "Ki yi hak'uri za ayi aure amma auran ko sati ba zai yi ba, dan dama maganin zaifi tasiri idan yarinyar tana kusanci da shi sosai. Yanzu ki yi k'ok'ari ki basu maganin abinci ko abinsha, ki kwantar da hankalinki ni Malma mai biyan buk'ata dole nai miki alk'awari sai naraba tsakanin Yarinyar nan da yaron, ke kuma aure da shi babu fashi". Farida godiya taima Malam mai biyan buk'ata dole , sannan suka tashi suka tafi jikin Farida ba wani k'wari dan bata so haka ba, taso ace kar a d'aura auran nan kwata-kwata amma yaza ta yi inda Malam ya ce ta yi hak'uri ta bari ayi, aikinsu zaifi ci tahaka".
Haka su Farida suka tafi bama mai kowa magana tsakaninta da Hajiya Murja, kowa da tunanin da ya ke yi".

Can ko b'angaran Hajiya Turai, tana zaune ta ji sallamar manager. Bayan sun gaisane, Hajiya Turai ta kalli manager ta ce, "Manager kasan Habib tunda ya fara rashin lafiyar nan, baya yadda da kowa sai Hassana da ke aiki wajanku, tom shine na yanke shawarar had'asu aure, tana bashi magani da kula dashi kafin yaji sauk'i, shine nakiraka dan Allah ka zamarma Hassana waliyi zanma musa magana shi kuma sai ya zama waliyin Habib". Manager kallan Hajiya Turai ya yi, ya ce, "Kai Hajiya amma hakan ya yi sosai, amma bakya tsoran ranar da M, d, sai ji sauk'i yaga Hassana a matsayin matar shi? ". "Eh nasan wannan, dama daga yaji sauk'i shikenan zan warware abun cikin sauk'i, insha Allah badamuwa shiyasama nake son auran yazamana nasirri".

Hajiya Turai Baba Lami tasa ta kira mata Hassana. Bayan Hassana tazo ne, Hajiya Turai ta d'akko kud'i kimanin dubu d'ari, ta mik'ama Hassana , ta ce, "My daughter amsa". Hassana amsa ta yi, bayan Hassana ta amsa ne, Hajiya Turai ta kalli Hassana ta ce, "My daughter wannan sadakinki ne, kiba Manager su, shi ne waliyinki". Hassana gabanta ne yafara fad'uwa, cikin rawar hannu ta mik'ama manager sadakin. Hajiya Turai kallan manager ta yi, ta ce, "shikenan maganar zaka iya tafiya, dan Allah daga kunshiga sallah nake son ad'aura auran, kaga yanzu 12:39pm, yanzu za a kira Sallah, dan Allah ka hanzarta "..

Manager tashi ya yi ya tafi yana mamakin had'in nan da Hajiya zata yi".

Hajiya ko kallan Hassana ta yi, ta ce, "My daughter kije kiyi duk wani shiri da zaki yi, anjima zan ne me ki".

Hassana tashi ta yi ta tafi tana mai jinta wata iri kamar mara lafiya".

B'angaran manager ko ana idar da Sallar azahar dama ya yi ma Liman bayani. Ana idarwa aka d'aura auran Hassana da Habib, abisa saki dubu d'ari. Inda manager ya zamana waliyin Hassana , Liman d'in masallacin kuma ya zama waliyin Habib, dan sun jira musa baizo ba".

Bayan and'aura auran ne manager ya taho tan sanar da Hajiya Turai an d'aura aure...........





Idan kin karanta daure ki yi Comment sister 🀝




Share
&
Comment please πŸ™

πŸ“š OGA HABIB πŸ“š
πŸ’«πŸ’«
*πŸ…™οΈŽARUMAI πŸ…¦οΈŽ WRITERS πŸ…οΈŽSSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausaπŸ’ͺ*_

*πŸ’«(πŸ…™οΈŽ.πŸ…¦οΈŽ.πŸ…οΈŽ)πŸ’«*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

Gaisuwar ban girma gareki sister Hafsat Yahaya Bakori, Alkairin Allah ya isarmiki aduk inda kike, rashin network ya hanani jin muryarki, nayi missing d'inki da kyau Wallahi 😭😭😭😭.

*ISTIGHFARI TANA SANYA NUTSUWA A ZUCIYA TANA KAWO BIYAN BUKATU WAJEN UBANGIJI UWA UBA KUMA ISTIGHFARI TANA BADA TICKET NA ALJANNA DIRECT😭*

Shafi na 36&37.



Hajiya Turai na zaune a falo, Manager ya yi sallama ya shigo.Hajiya Turai amsa Sallamar manager ta yi, sannan ta ce, "Bismillah manager ka zauna mana! ". Bayan manager ya zauna ne, ya kallai Hajiya Turai cikin nuna jin dad'insa ya ce, "Hajiya an d'aura auran". Hajiya Turai hawaye cike da idonta ta kalli manager ta ce, "Nagode manager". Can kuma sai kuka, manager cikin damuwa da ganin Hajiya Turai na kuka, cikin sanyin murya ya ce, "Hajiya dan Allah ki yi hak'uri, nasan maganar auran nan ce tasaki kuka, tom ya za'ayi haka Allah ya hukunta, addu'ar zakima m, d, Allah ya bashi lafiya". Hajiya Turai cikin muryar kuka ta ce, " Manager Wallahi ayanzu ba ciwan Habib nakema kuka ba, yanayin rayuwa nakema kuka, nagode maka manager Allah ya sakamama da alkairi nagode ". Manager sai da ya kwantarma Hajiya Turai da hankali sosai sannan ya tafi".

Hajiya Turai na zaune har kusan magriba amma shiru Hassana bata shigoba. Hajiya Turai jin shirun ya yi yawa aikawata yi aka kira mata Hassana".

Hassana ko wunin yau haka take yinshi duk bata jin dad'in jikinta, daga ta tuno wai za'a d'aura mata aure yau, gabanta sosai yake fad'uwa bakamar in ta tuno wanda za'a had'ata auran dashi ba, har wani d'an zazzab'i ke jin ya rufe ta. Hassana na zaune ita kad'ai ta yi ta gumi, d'aya daga cikin worker's d'in gidan ta zo kiranta. Hassana sai da gabanta ya fad'i jin Hajiya Turai nakiranta. Tashi ta yi kamar mara lafiya tabi bayan mai kirannata".

Hajiya Turai na zaune,Hassana ta yi sallama cikin sanyin muryarta mai tattare da rauni. Hassana guri ta samu d'annesa da Hajiya Turai ta zauna, sannan cikin girmama ta gaida Hajiya Turai, ta ce, "Hajiya gani". Hajiya Turai kallan Hassana ta yi da kyau, sannan ta ce, "Zoki zauna kusa dani, kinji my daughter". Hassana tashi ta yi ta zauna inda Hajiya Turai ta nuna mata".

Hajiya Turai kud'in dake hannunta ta sama Hassana su a hannu, ta ce, "My daughter kirik'e da kyau, kud'in sadakinki ne ki yi wani abun da su".

Gaban Hassana har wani fat-fat, ya ke saboda fad'uwa. Ita kuma Hajiya Turai ta ci gaba da cewa"My daughter d'azu da Sallar azahar aka d'aura auranki da Habib". Shiru Hajiya Turai ta yi nad'an wani lakaci, sannan ta ci gaba da cewa, "My daughter dan Allah karki sama kanki damuwa kod'aya akan auran nan, Kamar yadda na fad'amiki indai Habib kikeji tom ki saki ranki, dan bazaima sanda maganar auran ba, kamar yadda na yi shi bai saniba, haka zan warware shi bai sani ba, dan Allah daughter ki saki ranki, babu abinda zai faru insha Allah ".

Hassana goge hawanda ke zubar mata ta yi, sannan ta kalli Hajiya Turai ta ce, "Babu komai Hajiya, insha Allah babu damuwar da zansa maraina". "Yauwa daughterna, amma daga yau karki kuma cemin Hajiya, kirik'a cemin Mommy kinji?".kai Hassana ta d'agama Hajiya Turai ".

Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "daughter daga yau zaki koma site d'in Habib da kwana, saboda rubutunda aka bashi, kinga ya kamata afara bashi rubutun, yanzu kije ki d'akko komai naki dake site d'in ku ki kai sie d'in Habib ki aje". Hassana da tom ta amsa ma Hajiya Turai, sannan ta tashi ta fita zuwa b'angaran su".

Hassana na zuwa ta iske Jimmai tana alwallar magriba, Hassana kud'in hannunta ta mik'ama Jimmai".

Jimmai kallan Hassana ta yi ta ce, "Hassana wa innan kud'infa?, ina kika samosu? ". Hassana bud'e baki ta yi za tai ma Jimmai magana kuka ya kub'uce mata".

Jimmai cikin tashin hankali ta ke tambayar Hassana ta ce, "Dan Allah Hassana kimin bayani mana, kin kawomin kud'i dayawa haka kin tasani kina kuka, kud'in waye? ". Hassana sai da tagama kukanta sannan ta kalli Jimmai ta ce, "Kud'in sadakina ke". "Kud'in sadakinki kuma!? ". "Eh, yanzu haka maganar da nake miki Hajiya ta sanar dani and'aura aur... ". Kukwane ya hana Hassana k'arasa abinda ta ke fad'i".

Jimmai ko cikin jin dad'i, ta ce, "Dan Allah and'aura auran? ". Hassana da kai ta ba Jimmai amsa".

Jimmai kallan Hassana ta yi gala-la, ta ce, "Haba Hassana yanzu wannan shine abin kuka, dan Allah meye abin kuka aciki ?, nidai indai zakiji nasihata tom kibar kukannan, ni Wallahi dani nasamu damar nan taki Hassana inajin saina yi party, dan Allah ni dai in dai kina son tarayyata da ke ta d'ore tom kibar kukan nan muyi magana! ".

Hassana share hawayanta ta yi, tana kallan Jimmai. Jimmai ma kallan Hassana ta yi, ta ce, "Yanzu ke me ki kaga zakiyi da kud'in nan? ". Shiru Hassana ta yi, sannan ta ce, "Zan barsu agunki ki ajemin".
"A'a, ba haka za ai ba, nishawar da zan baki kisai kayan sawa, kinga dai baki da wasu kaya, kinaji Hausawa nacewa sutura itace mutum, dan haka ki samu dogayan riguna guda Shida (6) ki saya".
Hassana kallanta ta yi, sannan ta ce, "Tom taya zan siya, nida bansan ko inaba? ". "Nizan siyo maki gobe a wuse market ". Shiru Hassana ta yi, Sannan ta ce, "Shikenan ki rik'e kud'in awajanki goban sai ki yi amfani da su". Hassana kallan Jimmai ta yi, ta ce, "Sister Jimmai zan tafi, Hajiya na jirana".

Hassana kayanta ta d'akko sannan ta tafi".

Jimmai ko har kusan part d'in Hajiya Turai ta raka Hassana tana k'ara kwantar mata da hankali, tana cewa"Wallahi Hassana ki saki ranki kici arzik'i kibar arzik'i". Nan dai Jimmai ta tafi tabar Hassana".


Hassana kan abin Sallah ta iske Hajiya Turai. Hassana zama ta yi tana jiran Hajiya Turai ta idar. Hajiya Turai ko na idarwa ta kalli Hassana ta ce, "kin yi Sallah? ". "A'a, banyi ba". Hassana taba Hajiya Turai amsa".

Hajiya Turai kallan Hassana ta yi ta ce, "Shiga bedroom d'ina ki yi alwallah kizo ki yi".

Hassana tashi ta yi tashiga bedroom d'in Hajiya Turai tashiga toilet d'in ta. Hassana ta dad'e tsaye tana yaba tsaruwa da had'uwa na toilet d'in Hajiya Turai, dan sai yafi burgeta fiye da na Habib. Hassana alwallah ta yi tazo bayan HajiyaTurai ta tada sallarta".

Bayan Hassana ta idar da sallar ne tana nan zaune har ake sallar isha'i ta tashi ta yi. Bayan duk sunyi sallah ne, Hajiya Turai ta kalli Hassana, ta ce, "Hassana ki d'auki kayanki sai ki kai site d'in Habib d'in, zan aiko miki da abinci da maganin shi. Rubutun farar roba shine nadare d'ayan kuma na safe da rana sai dare". Hassana tom ta ce ta tashi ta tafi tana jinta duk ba dad'i".


B'angaran Farida ko cema Mahaifiyarta ta yi, bazata dawo gidansu Habib ba sai zuciyarta ta lafa, dan hankalinta atashe ya ke game da maganar auran Habib da Hassana. Duk da mahaifiyarta tana ta yi mata kalamai masu sanyin akan auran, acewarta bazai je ko ina ba, dashi da babu duk d'aya ne, dan hakakama karma ta d'aura makanta damuwa".


B'angaran Hassana cikin sanyi ta bud'e k'ofar Falon Habib tashiga. Allah sarki Habib zaune yake yana jin alamun shigowar mutum ya tashi da sauri, dan wannan ita ce d'abi arshi. Shiyasa kusan duk lokacinda Hassana zata shiga sai gabanta ya fad'i, dan in yayo kanta sai ta ga kamar itama wujijjigata Zai yi irin yadda ya ke ma mutane. Hakan yasa indai ya taho jikin k'ofar ta ke jingina da d'an alamar tsoro. Habib na k'arasowa inda Hassana ta ke, Kamar yadda ya saba ya rik'o hannunta ya k'arasa da ita cikin Falon. Habib kan caution ya zauna ya zaunar da Hassana kusa da shi kamar yadda ya saba".


Hassana ko kanta ak'asa ta kasa kallan Habib, dan gaba d'aya yau ta kasa sakewa da Habib kamar yadda ta ke yi kullum. Hassana na nan zaune Baba Lami tai mata nocking , tana kiranta.Hassan da saurinta ta tashi ta nufi wajan k'ofar. Nan fa shima gogannata ya tashi da sauri ya bita. Hassana bud'e k'ofar ta yi da niyyar amsar abincin. Habib ya yi kan Baba Lami. Hassana da sauri ta irik'e Habib, Baba Lami kuma ta yi saurin aje abincin da rubutun hannunta ta ce, "Kai Hassana Sannu da k'ok'ari dama haka yakema mutane aini bansani ba". Hassana cikin sanyi ta ce ma Baba Lami "Eh Baba haka yake yi". Hassana rufe k'ofar ta yi sannan ta kalli Habib da ke rik'e da hannunta ta ce, kamar za tai kuka"Oga Habib kasa kar min hannu dan Allah in d'auki abincin in shigar da shi ciki". Habib kafad'a ya mak'ema Hassan. Alamun bazai saki ba. Hassana bakin k'ofar Falon ta zauna ta ce, "Tom sai kaci abincin anan inda kak'i sakina in shigar da shi ciki".

Habib na ganin Hassana ta zauna shima ya zauna. A gurin Hassana ta zubama Habib tuwan shinkafa da miyar a gushi. Habib sosai Ya ci abincin, sannan sauran da yarage Hassana ta d'auka itama taci dan tun kusan safe bataci komai ba".


Bayan Hassana ta gama cin abincin ne ta ta ta shi takoma kan caution d'in Falon ta zauna, Habib ma zama ya yi kusa da ita yana mai rik'e da hannunta. Nan dai Hassana ta fara gyan-gyad'i , dan jiya kusan bata yi bacci ba. Hassana ganin zata fad'i yasa ta kwanta kan caution d'in da yake 3 seater ce".

Habib ma ganin Hassana ta kwanta, shima bin bayan Hassana ya yi ya kwanta, akan caution d'in kusan kan Hassana, inda gurin ya yi masu kad'an. Hassana da sauri ta ta shi tana kallan Habib, ta ce, "Oga Habib ka tafi bedroom d'in ka ka kwanta". Habib mak'ema Hassana kafad'a ya yi, irin nak'i d'in. Hassana tashi ta yi ta kai Habib bedroom d'in shi, ta zauna bakin bed d'in ta ce, "Tom kakwanta". Habib kallan Hassana ya yi, yana zaune kusa da ita dan shima zama ya yi kamar yadda yaga ta zauna".

Hassana hawa ta yi kad'an kan gadon ta kwanta, inda taga sai abinda ta yi ya ke yi. Aiko take shima ya kwanta bayanta. Hassana tashi ta yi da sauri ta ce, " tom ka kwanta ka yi bacci ". Tanu falon. Tana tashi Habib ma ya tashi yabi bayanta". Hassana na zuwa ta kwanta kan caution d'in duk ta tattare yadda babu yadda Habib zai yi ya kwanta, dan bata bar guba, duk ta babbake caution d'in. Habib ko nazuwa yabi kan Hassana ya kwanta".


Hassana cikin tsabar nauyin shi da taji ta ture shi ta milmilo k'asa da sauri tana nishi ta kwanta. Habib d'in ma k'asan ya biyota ya kwanta shima. Hassana juyowa ta yi tana kallan Habib, dariya ma ya bata, aiko ta haudariyarta. Damamaki sai taga Habib d'in shima yana murmushi. Hassana kallan shi ta yi ta girgiza kai. Dan baccinma sai taji ya wuce. Hassana cigaba da kwanciyarta a k'asa ta yi, ahankaki-ahankali ta ji bacci na son d'auketa. Tashi ta yi ta zauna dan tasan indai ta yi bacci tom bazata iya tashi ba taba Habib maganin shi, hakan yasa tana tashi ta d'akko wayar Habib da ta ke gani a Falon ta duba taga. 11:57Am. Hassana maganin Habib ta tashi zata d'akko da mamaki tabi Habib da kallo ganin ya tashi ya biyota dan duk atunaninta bacci ya ke. Hassana rubutun ta d'akko ta tsiyaya a cup. 12:00Am nacika ta mik'ama Habib maganin. Habib k'in amsa ya yi. Hassana ta san dalili dan ya k'oshine, dan ta lura indai ya k'oshi kome zata bashi baya amsa. Hakan yasa Hassana ta kai Cup d'in bakinshi ta ce, "Tom sha". Habib bud'e baki ya yi yana sha. Nan ya shanye wanda ta zuba mai".

Hassana nagama ba Habib maganin ta ci gaba da kwanciyarta ak'asa Habib ma k'asan ya bita ya kwanta. Hassana duk yadda zatai ma Habib ya tafi bedroom d'in shi ya kwanta ta yi mai amma yak'i. Hassana kwanciyarta ta yi tana jan tsaki, dan duk sai taji badad'i yadda Habib duk ya kanannad'eta, gashi yasa hannu d'aya ya rik'o k'ugunta, hakan yasa ta kuma jinta wani iri ba dad'i. Hassana hannu Habib ta kama ta rik'e dan ba tajin dad'in yadda ya rungumota ta baya. Shiko Habib hannun shima da ta rik'e ya isai, dan dama gani ya ke kamar zata gudu ne, yana ko jin ta kama mai hannu shikenan".


Hassana cikin dare ta tashi domin yin fitsari dan ita tana da tashin fitsarin dare. Abin mamaki tana tashi Habib ma ya tashi".


Hassana da kallo tabi Habib, sannan tanufi bedroom d'in shi dan acan ne toilet d'in shi ya ke. Hassana na tafiya Habib ya bi bayanta. Hassana ta bud'e k'ofar toilet d'in ta shiga, kusan tare da Habib suka shiga. Hassana kallan Habib kawai ta ke, sannan ta ce, "Oga Habib kafita mana, baka ganin nan toilet ne". Shidai Habib da ido ya bi Hassana da kallo. Hassana ganin Habib ba fita zai yi ba, kuma fitsari ya matseta ya sa ta zuk'unna ta yi fitsarinta".

Hassana na zuk'unnawa Habib ma ya zuk'unna bayanta shima yana fitsarin. Hassana na gamawa ta fito shima Habib ya tashi ya fito. Wato so dadama idan Habib ya yi wani abun, Hassana sai taga kamar mai hankali, sai dai in yayi wani abunne zaka tabbatar da k'wak'walwar ta tab'u".


Hassana komawa kan bed d'in Habib ta yi ta kwanta, d'an ak'asan sanyi gashi ana sanyi-sanyi". Habib bayan Hassana yabi ya kwanta, Hassana ko kojuyowa bata yi ba, jin ankwanta bayanta dan tasan kowaye".


Kiran sallar asuba, Hassana ta farka ta ga Habib kamar wanda ke shirin shigewa cikinta, yadda ya kanannad'eta ga hannu d'aya yasa ya rik'e k'ugunta da shi. Hassana cire habnun Habib ta yi daga jikinta, sannan ta d'an ture shi daga jikinta ta tashi. Tana tashi yana tashi yabi bayanta. Atare kusan sukai alwallar dan duk abinda ta yi sai ya yi. Sallarma tana ta dawa shima yazo kusa da ita ya tsaya yana yin duk yadda ta yi, ahaka dai suka idar da sallar. Sai da ka gari ya yi haske sannan Hassana ta tashi. Ta koma kan caution zata kwanta sai ta tuno daga ta kwanta mutuninta shima zai ce zai kwanta kuma gurin ba isarsu zai ba, hakan yasa ta fasa ta koma kan sallayar ta kwanta. Aiko shima kusa da ita ya kwanta".

Bacci mai nauyi ya d'auke Hassana, dan bugun da akema k'ofar ne ya sa ta tashi a furgice ...............



Idan kin karanta d'aure ki yi Comment sister 🀝


Share
&
Comment please πŸ™.

πŸ“š OGA HABIB πŸ“š
πŸ’«πŸ’«
*πŸ…™οΈŽARUMAI πŸ…¦οΈŽ WRITERS πŸ…οΈŽSSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausaπŸ’ͺ*_

*πŸ’«(πŸ…™οΈŽ.πŸ…¦οΈŽ.πŸ…οΈŽ)πŸ’«*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

*YAN UWA KULLUM KARA KUSANTAR KABARI MUKE KWANAKINMU SUNA KAREWA AJALINMU YANA KUSANTOMU AMMA BAMA FARGA DA HAKA😭😭!*ALLAH KASA MU CIKA DA IMANIπŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘.


Shafi na 38&39.



Hassana cikin furgici ta tashi tsabar yadda ake buga k'ofar. Hassana tashi ta yi da saurinta dan zuwa ganin mai bugun k'ofar. Baba Lami ta gani tsaye da abin breakfast d'in su a hannunta. Hassana kallan Baba Lami ta yi tana murza ido ta ce, "Baba dama ke ce, Wallahi har naji tsoro! ". Dariya Baba Lami ta yi, ta ce, "Haba wannan wana irin bacci ne, tun d'azu fa nake tsaye nake buga k'ofar nan, amma shiru". Hassana mutsitsika ido ta k'arayi ta ce, "Ina kwana Baba ". "Lafiya k'alau Hassanan, ya mai jikin? ". Hassana cikin alamun kunya tace ma Baba Lami, "Da sauk'i ". Baba Lami kallan Habib ta yi dake tsaye kusa da Hassana ta ce, "Hassana ki matsar da mutumin naki sai in shigo in kawo muku abin k'arin,". Hassana bud'e ma Baba Lami k'ofar ta yi ta matsa da Habib daga jikin k'ofar. Amma duk da haka bai hana Habib yunk'urowa ba ya ce zai kamo Baba Lami. Baba Lami ko da saurinta ta aje abin breakfast d'in ta gudu".

Hassana zuwa tai ta rufe k'ofar, sannan ta je cikin kayanta da tazo da su, ta d'akko brush d'inta tashiga toilet d'in Habib ta yi brush. Habib ko tsaye ya ke cikin toilet d'in shima yana kallan Hassana, Hassana kallan Habib ta yi bayan ta gama brush d'in, ta ce, "Oga Habib kaima za kai? ". Habib dai da ido yabi Hassana da kallo. Hassana d'aya daga cikin tooth brush d'in da ta gani a toilet d'in ne ta matsama Habib toothpaste ta mik'amai. Habib amsa ya yi yana kallan Hassana. Hassana hannu Habib ta gama ta kai brush d'in bakin shi ta ce, "Yauwa tom wanke bakinka ko? ". Habib kafad'a ya mak'ema Hassana alamun bazai wanke ba. Hassana amsar brushi d'in ta yi daga hannun shi ta ce, "Tom bani ni in wankema". Habib sakarma Hassana brush d'in ya yi. Hassana ta ce, "Yauwa tom bud'e bakin". Habib bud'e bakin ya yi. Hassana ta tura brush d'in cikin bakinshi tana wankema. Sai dai fa mai makon ya zubar shanyewa ya ke. Hassana kallan shi ta yi, ta ce, "Kai Oga Habib ba fa shanyewa ake ba, karik'a zubarwa kaji?, yauwa tom zubar haka". Hassana ta tofar da miyau abakinta, tana gwadama Habib shima yadda zaiyi ".

Nan dai ashiririce aka dama wanke bakin. Hassana break fast d'in da Baba Lami ta kawo masu ta d'akko tana bud'ewa, kunun gyad'a ne ya yi haske sosai sai k'amshin kunun ya bid'e falon. Sai soyayyar doya da akai ma miyar k'wai. Hassana tsiyayama Habib kunun ta yi, tana bashi ko ya amsa ya fara sha. Hassana soyayyar doyar taba Habib amma ya k'i ci. Rubutunshi ta d'akko ta bashi, sannan itama ta zubama kanta kunun tasha, bayan ta gama shanyewa ne ta ci doyar. Habib shima ganin Hassana na cin doyar d'auka ya yi yana ci. Hassama sosai ta ci doyar. Bayan Hassana sun gama break fast d'in ne, taji tana son yin kwanka inda dama ta saba wankan safe ta ke, amma kuma bata san yadda zatai da Habib ba. Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib ka zauna nan zanyi wanka, indai kuma ka biyoni tom zan b'ata da kai zan tafi in barka, kaji? ". Habib shi dai kallan Hassana ya yi da ido".

Hassana ko, tashi ta yi ta nufi bedroom d'in Habib.abin dariya kusan tare suka shiga bedroom d'in. Hassana tsayawa ta yi tana kallan Habib ta ce, "Oga Habib Allah yau zan b'ata da kai indai baka zauna ba kajirani nayi wanka, ka zauna nan kaji rani". Habib mak'ema Hassana kafad'a ya yi alamun yak'i d'in".

"Hassana ta ce, "Na shiga uku, tom wai kai komai zanyi sai ka bini". Hassana hannun Habib ta kama ta zaunar da shi bakin gado, ta ce, "Yauwa, tom zauna anan in yi wanka ". Habib kallan Hassana ya yi. Hassana ko ganin Habib bai mak'e mata kafad'a ba, sai ta yi tunanin bazai bita ba, ya hak'ura zai zauna, hakan ya sa,Hassana tashi ta nufi toilet d'in. Aiko tana shiga kusan atare suka shiga".


Hassana cikin jin haushin Habib d'in ta d'aure fuska ta ce, " Oga Habib fita".Hassana ta fad'i maganar tana nunama Habib hanyar fita. Habib ko da ido ya bi Hassana da kallo. Hassana ko ganin haka sai tafara tura Habib. Sai dai ko motsi Habib bai ba. Hassana duk yadda za tai da Habib ya fita yak'i dole ta rabu da shi ta fasa yin wankan ta fito, ta zauna bakin bed d'in Habib cikin jin haushin Habib ya k'ifita yabarta ta yi wanka".

Habib ko zama ya yi kusa da Hassana zai kama hannunta. Hassana cikin jin haushi ta fusge hannunta ta ce, "Da Allah ni sakarmin hannu, aina b'ata da kai tunda kak'i barina inyi wanka. Habib ko kallan Hassana kawai ya yi. Hassana na nan zaune taji yo nocking d'in k'ofa. Tashi ta yi da sauri, mutumin tama ya mara mata baya".

Hassana tana zuwa abin mamaki Hajiya Turai ta gani tsaye jikin k'ofar. Hassana

Please Login or Register in order to submit comment