Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki je bedroom d'inki ki kwanta kakki bacci anan". Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib yau ba zan yi bacci ba, kaina kamar zai cire". "Tom ba ke bace kika kama kuka akan abinda bai kai ya kawo ba". Cewar Habib ".


"Tom ai kaine kai min alk'awari ka fasa, Wallahi na tsani manager nan, shi dan yaga Billy budurwar shi ce shine zai wani anshe matsayina ya bata, ita kuma sai wani jin dad'i take hadda min gwalo, ni Wallahi na tsaneta ma, naga yadda za tai gobe idan taji an ban min matsayina". "Nifa wasa nake miki, ki tsaya a supervisor d'in da manager ya baki.... ". Ai Habib bai rufe baki ba, Hassana ta fad'o daga kan caution d'in, tana bubbuga k'afarta kamar sabuwar 'yar bori, tana bubbuga k'afarta tana kuka". Habib da sauri ya d'ago Hassana da ga k'asan ya maida ta kan caution d'in ya ce, " Wasa fa nake miki". "Wallahi babu wani wasa nasan daga manager yazo zaka ce mai abar ma Supervisor , ai gashi nan kama fad'a ". Hassana haka ta dage sai kuka take, dan ita fa gani take tabbas Habib da gaske ya ke wasa yake mata, ai rannan ma haka ya yi mata, ya ce ya bata matsayi ashe bai ba ta ba, inda bai bi tsarin da aka ba Supervisor ba".


Babu yadda Habib bai yi da Hassana ta yi shiru ba wasa ya ke mata amma tak'i, daga k'arshe d'au karta ya yi ya nufi bedroom d'in shi da ita, Habib aje Hassana ya yi gefan ga don shi shima ya zauna, ya ce, "Kin ga kan ki ciwo yake ki yi shiru, ni wasa nake miki, na baki mataimakiyar manager, kamar yadda nace miki gobe zan sanarda manager, yanzu ki kwanta ki yi bacci ko zaki samu sau k'in kan".


"Hassana shiru ta yi, ta kwanta kamar yadda Habib ya umar ceta, dan kukan nan da ta sake yi yasa kan ya sake mata wani sabon ciwan. Ahaka dai bacci ya kwashe Hassana, inda Habib shi kuma ya tashi ganin Hassana tai bacci ya watsa ruwa, sanan ya kwanta shima d'an nesa da Hassana".


Washe gari Habib sai da ya yi sallah sannan ya tada Hassana, tana tashi side d'in ta ta nufa. Hassana da wuri ta yi abinda za tai ta yi shirin ta na fiya aiki. Hassana na fitowa taci karo da Habib shima zai tafi. Hassana da sauri ta k'arasa gurin Habib ta ce, "Ina kwana Oga Habib ". 'Lafiya".Habib ya amsa ma Hassana. Hassana da sauri ta k'arasa gurin Habib, ta ce, "Oga Habib in zo mu tafi tare? ". "Kai Habib ya d'aga ma Hassana".


A mota Hassana tai ta rok'on Habib, akan dan Allah karya amshe matsayinta, ahaka dai suka isa Habib bai amsa ma Hassana ba".


Can b'angaran Billy ma ita ma yau da wuri ta je Sanat, tana zuwa ta shiga Office d'in manager. Bayan sun gaisa ne, Billy ta kalli manager ta ce, "manager wai baka ce komai ba, game da maganar da yarinyar nan ta yi jiya ba? ". "Eh ina so yau zan ma M, d magana , idan yazo, karki ji komai matsayinki na nan". Billy cikin jin dad'in abinda manager ya ce, ta ce, "Manager idan har kai min haka ni kuma nai maka albishir d'in tsaida auran mu cikin watan nan ".
"Aiko ki shirya zama amarya , dan ina mai tabbatar miki M, d, zai amshi maganata, nina san ta yadda zan b'llloma mai".


Habib na zuwa babu dad'e wa manager ya Shigo Office d'in shi. Bayan sun gaisa ne, manager ya ce, "M, d dama akan maganar da Hassana ta yi jiya, kan matsayin Supervisor da ta ce bata yarda ba. Tom M, d idan zaka duba Hassana bata da Experience d'in da za abata matsayin mataimakiyata, Aganina matsayin Supervisor zai fi da cewa da ita,shine nake so ka ban dama a sake had'a wani meeting d'in, ka sanar da Hassana da kanka za tafi yarda ta yi hak'uri". Habib kallan manager ya yi yace, "Babu damawa".


Yauma kamar jiya manager da kanshi ya sanar da kowa ne staff's a kwai meeting yanzu. Cikin k'ank'anin lokaci kowa ya hallata meeting d'in".


Manager ne ya tashi ya ce, "Jiya munyi meeting inda muka tabbatar da matsayin Supervisor a mataimakiyata, tom amma kuma sai aka d'an samu matsala, inda Hassana ta tashi ta ce, bata yarda ba, ita M, d, ya ba matsayin. dan haka yau M, d zai tabbatar da matsayin kowa da kanshi, M, d, mismilah".


Habib yana a zau ne ya fara magana kamar haka" Nina ba Hassana matsayi kamar yadda ta ce jiya, dan haka matsayinta na nan na mataimakiyar manager, ita kuma Supervisor zata zauna a matsayin..............โœ๏ธ



Idan kin karanta daure ki Comment sister ๐Ÿค.



Share
&
Comment please๐Ÿ™.

๐Ÿ“š OGA HABIB ๐Ÿ“š
๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ
*๐Ÿ…™๏ธŽARUMAI ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ WRITERS ๐Ÿ…๏ธŽSSOCIATION๐Ÿ“š๐Ÿ–Š๏ธ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa๐Ÿ’ช*_

*๐Ÿ’ซ(๐Ÿ…™๏ธŽ.๐Ÿ…ฆ๏ธŽ.๐Ÿ…๏ธŽ)๐Ÿ’ซ*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).


https://chaveryt.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7


https://www.facebook.com/groups/301023561618950/

Update d'in d'iya nayi mistake, zan sa shafi na 74&75.Sai nasa 74&74. Dan haka yau zamu tashi a Shafi na 76&78.

Albishirin ku masu bibiyar littafin Fadila Sani Bakori.
Yau gani da da daddad'an albishir gare ku, insha Allah daga na kamma Oga Habib, zan nisha d'an tar da ku da sabon littafina wanda na baje basirata acikin shi. Anyi amfani da salo na birgewa acikin littafin. Labari ne wanda ya ke d'auke da madarar Soyayya, mai d'auke da ban al'ajabi. Inda ta wani b'angaran labarin ke d'auke da ban tausayi mai tsayawa a zuciyar makaranci. Duk yadda zan sanar daku ba zaku fahimta ba, ke dai karki bari abaki labari.
Zaki samu littafin akan farashi mai sauk'i da rahusa๐Ÿ‘Œ๐Ÿ‘Œ.
Summary.
Abba tin ina yaro kana yawan fad'a min, duk abinda ya yi tsanani yana tare da sauk'i.Shin ni sai yau she sauk'i na zai zo! ?. Abba me yasa muta ne basa ganina, maganata kawai su ke ji!?.Abba me yasa muke rayuwa a daji mai makon cikin gari cikin mutane !?.
Abba kana gani Husna zata aure ni, duk da halin da nake ci!?.
Abba me yasa Husna ta kasan ce ita kad'ai ke ganina!?. Abba kace kai ba Mahaifinsa bane, tom waye Mahaifina, kuma me yasa muke rayuwa a jeji!?, Sannan me yasa Abdussalam kad'ai ke zuwa gurin mu, sannan Abba waye Abdussalam ?.
Haidar duk banda amso shin tambayoyin ka, nima ban san kai na ba Haidar, ban san waye ni ba, bare kuma kai!.
Labari mai tab'a zuciyar mai karatu.

RAYUWAR HAIDAR
Paid book

Akan farashi mai sauk'i da rahusa ๐Ÿ‘Œ
Dan nai man k'arin bayani zaki iya managa ta wannan Number๐Ÿ‘‰ 08063830828



Shafi na 76&78.




Habib Yana a zau ne ya fara magana Kamar haka"Nina ba Hassana matsayi Kamar yadda ta ce jiya, dan haka matsayin ta na Nan na mataimakiyar manager. Ita Kuma supervisor zata zauna a matsayinta na Supervisor".Habib na kai wa nan ya yi shiru. Manager sosai hankalin shi da ranshi ya b'ace Jin abinda M. D , ya ce. Manager da kyar cikin b'oye yanayin b'acin ran da ya ke ciki, ya tashi ya ce, "Tom Masha Allah da fatan ko wa yaji matsayinta, dan haka kowa ya tsaya ya yi aiki sosai, dan zamu rik'a bincika aikin kowa, idan Muna samun mutum da rashin kula da aiki tom zamu d'au ma taki akan shi".


Nan taran ya tashi, inda aka bar daga Farida Sai Billy, Billy kallan Farida ta yi, ta CE,"Yau zan aje aiki, dan ba zan yarda ba, inyi aiki a k'ark'ashin yarunyar Nan, danni gaskiya Sai dai mu yi ta fad'a da ita, Kuma ina ga ya tabbata Oga Habib ya fara son yarinyar Nan,tunda ake meeting kin tab'a ganin ya tashi ya yi magana,Amma Yau da kanshi ya tashi Yana tsara yadda za'ai, gaskiya ni Yau zan bar aikin nan! ".Farida kallan Supervisor ta yi, cikin damuwa ta ce," Supervisor idan Kika bar aiki dan yarinyar nan ai wallahi kin fad'o , zama zaki yi mu had'e mata Kai, kinga ke manager ma na jin maganarki, ai idan ki ka ce yanzu kin aje aiki Wallahi ta San dan ita kika aje, ta san tsoro Kika ji, ke dai ka wai ki yi hak'uri aiki ma ai yanzu aka fara , ai Sai mun ga bayan yarinyar nan agurin nan, kina nu fin duk abinda tai Mana zata ci banza ne?, Yanzu abinda nake so da ke, ki aje maganar barin aiki mu fuskanci ta ina zamu fara, Kuma kin ga abin zai zo mana da sauk'i, inda in tana ta k'amar saman ki ta ke, tom ita ma manager ai samanta ya ke, kuma kin ga manager yana jin maganarki, yanzu ki je ki samu manager ki sanar da shi Zaki bar aiki, muji me zai ce".


Billy shawarar Farida ta bi, Manager na zaune a Office d'in shi yana tunanin yadda zai b'ulloma Billy , Sai ga Billy ta shigo , Billy kallan Manager ta yi, daga ganin kwayar idon Billy ka san tana cikin damuwa. Manager kallan Billy ya yi, ya fara magana Kamar haka, "Tabbas na San ranki zai b'ace da abinda ya faru, ki yi hakuri.... ". Billy da da katar da manager ta yi ta ce," Manager maganar hak'uri ta k'are dan ni Yau zan bar aiki a Company'nan dan ba zan iya aiki ak'ark'ashin yarinyar nan ba". Manager cikin damuwa da barin aikin da Billy ta ce zata yi,ya ce,"Billy na san zaki bar aiki ne saboda matsinki da M.D yaba yarinyar'nan ,ki yi hak'uri nai miki alk'awarin zan dawo miki da matsayin ki ka fin nan da k'ar shen watan nan ".


Billy kallan manager ta yi, ta ce, "ka tabbata dearie? ".murmushin magana ya yi, sannan ya d'aga ma Billy kai, Billy cikin jin dad'i ta tashi ta fita".


B'angaran Habib ko yana zaune a Office d'in shi Hassana ta shigo da fara'arta tana zuwa ta idasa inda Habib ya ke zau ne. Babu zato babu tsammani sai dai Habib ya ji Hassana ta rungume shi, ta ce, "Oga Habib nagode, naji dad'in matsayina da ka bayyana agaban staff's, nagode dear.. ". Hassana saurin rufe bakinta ta yi, ta saki Habib zata gudu, dan sukubutar bakin da ta yi".


Habib jawo Hassana ya yi, ta dawo ya rik'e ta ya ce, "Mai-mai ta abinda kika ce". Habib ya fad'i maganar yana kallan Hassana. Hassana hannu tasa ta rufe idanta, ta ce, "Nifa babu abinda nace".Habib hannu Hassana ya rik'e yana burzawa. Hassana ihu ta fara, tana cewa , "Wayyo Oga Habib da zafi Allah! ". "Tom mai-mai ta abinda kika ce". Cewar Habib ".


"Tom naji sakar ni in mai-mai ta". Habib sakin Hassana ya yi, aiko yana sakin ta ta ta gudu".

Habib jin kina ya yi da chair d'in da ya ke zaune kanta, idon shi rufe, ya na mai-mata abinda Hassana ta ce,ya yi murmushi, sannan ya ci gaba da abinda ya ke".


Hassana tana fita Office d'in Habib ta wuce wajan koyan girkinta, ba ita ta dawo ba sai la'asar, tana dawowa ta je kan rubber chair ta sauna tana kallan staff's d'in sai aikin su suke, Hassana na nan zaune taga fitowar Farida daga Office d'in Billy. Farida ta zo dai-dai inda Hassana ta ke zata wuce, Hassana ta ce, "Farida me ya shigar da ke Office d'in ca muna tsakiyar aiki? ". Farida da mamaki ta kalli Hassana, sai tai murmushi ta ce, "Zan shiga duk inda nake so a Company nan a duk lokacin da naso, gargad'i na k'arshe kar ki kuma shiga safgata, idan ba haka ba, zan b'atar da ke da ta rihinki, acikin Company'nan". Hassana ta shi tai tsaye, tana kallan Farida dan ta bar shakkarta, ta ce, "Ni kuma ina miki albishirin zanyi amfani da da mata na koreki a Sanat company, ko kin san dan ke na amshi matsayin nan, ba zan tab'a barin Sanat ba sai naga bayanki, mu zuba ni da ke! ".Farida dariya ta yi, jin abinda Hassana ta ce, ta ce, "Aiko in dai danni kika amshi matsayin nan, ina mai tabbatar miki kinyi aikin banza, dama kin tsaya a share-sharanki da wankin toilet da yafi miki, dan ni Farida nafi k'arfin ko ruwa a gurin mutum k'askantaciya irinki, wadda bata da asali!, ni ba Sanat kad'ai zan kore ki ba, har gidan Oga Habib sai nayi amfani da basira na koreki". Sakarya mai aiki a titi babu Office! ". Farida na fad'in haka, ta bar gun kafin taji abinda Hassana zata kuma cewa".


Hassana ko zama tai agun tana mai-mai ta maganganun Farida azuciyarta, tabbas sai nayi amfani da matsayina agun nan na mataimakiyar manager Farida na koreki gurin nan. Hassana ta dad'e zaune agun, sannan ta ta shi ta shiga office d'in manager ".

Magan-ganun da Hassana ta ji anayi ne a Office d'in manager ya hana ta shiga, manager ne taji yana cewa, "Farida naji duk abinda kika ce, wato ta amshi matsayi ne dan ta kore ki aiki a Company, kar ku damu ku dai ku ban nan da lokaci kad'an, sai tabar Sanat yughurt da k'afafunta, na san yadda zan mata.... ". Hassana ji tai baza ta iya jure sauraro ba kawai ta banka Office d'in ta shiga. Hassana tsayawa ta yi tana kallan su d'aya bayan d'aya, sannan ta kalli manager ta ce, "Manager ada ina maka kallan adali, amma kuma a yau ina maka wani rin kkallo wanda ban san ya zan kira shi ba, sai dai ina mai mu ku albishir daga kai har su buku isa kusa in bar Sanat ba, sai dai ni in barta alokacin da naso". Hassana shiru ta yi, sannan ta ce, "Manager nazo ne ka ban Office ". "M, d bai fad'i a baki Office ba alokacin da ya baki matsayi". Cewar manager ".


Hassana juya wa tai zata tafi, Farida ta rik'o hannun ta ta ce, "Ji mana, kina tunanin zaki iya karawa da mutum uku ko?, Yaro man kaza bai san wuta ba sai ya taka tabbas haka abin yake, zaki iya tafiya". Farida ta idasa maganar tana sakin hannu Hassana da k'arfi, Hassana kallan manager ta yi, ta ce, "Manager idan har haka zaka ci gaba da tafiyar da aikin ka, tom ba wai su ba, hatta kai zaka iya barin Sanat cikin k'ank'anin lokaci, kabar ta k'amar kana da power agun Oga Habib, ni zan rugaza power taka". Hassana na fad'in haka taja Office d'in da k'arfi ta fita".


Manager da su Billy kallan juna sukai, manager ya ce, "kar ku ji komai zuwa gobe aikin zai fara, ai yarinyar nan sai ta bar gurin nan cikin satin nan, zan yi amfani da barinta gurinnan da ta ke yi, kullum ai ko yau sai da taje inda zata ta dawo taci gaba da aiki, dan haka karku ji komai, cikin satin nan nan komai zai zo k'arshe". Su Farida cikin jin dad'i suka kashe da juna ita da Billy ".

Hassana ko gu d'aya ta samu ita ma ta zauna tana tunanin ta ina zata fara b'illo musu, wani tunani yazo ma Hassana ya sa ta tashi ta nufi Office d'in Habib".


Hassana zama ta yi tana kallan Habib, sannan ta ce, "Oga Habib ina da tambaya? ". Habib d'agowa ya yi yana kallan Hassana, sanna ya ce ina ji? ". "Oga Habib atsa rin masana'antar nan manager zai iya hakana wasu aiki kawai su keb'e suna hira? ".Habib kai ya girgiza ma Hassana. Hassana kuma ta ci gaba da cewa, " Ni zan iya tsawatarwa akan abinda naga anayi ba dai-dai ba? ". Kai Habib ya kuma d'aga ma Hassana".


Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "shikenan Oga Habib ni zan wuce gida, akwai abinda zanyi". "Ki bari mu wuce tare". Cewar Habib ".



Hassana hak'ura ta yi har lokacin da Habib ya tashi suka wuce tare".


Washe gari Hassana ta gama shirinta na fiya aiki Habib ya ce mata yau ba zata ba, Hajiya na kiranta. Habib da kan shi ya d'au ki Hassana ya kai ta gidansu".


Yau sati d'aya kenan raban Hassana da zuwa Sanat saboda kullum gidan Hajiya Turai ta ke wuni. Can b'angaran su Manager ko acewar shi sun samu damar dakatar da Hassana aiki, in da bata sanar ba. Aiko haka akayi yau Hassana tazo aiki saboda Hajiya Turai yau taje unguwa bata gida. Hassana na zuwa ta samu gu ta zauna inda ta ke zama, Hassana na nan zaune manager yazo da ta wata takarda ya mik'a ma Hassana ya ce, " mun baki suspection na sati d'aya, saka ma kon rashin zuwa ki na sati d'aya da biki ba, kuma ba bu wata sanarwa ko dalilin hakan".


Hassana amsar ta kardar ta yi, ta kalli manager ta ce, "Zan tafi ne kawai dan uzirin kaina, Hassana na kaiwa nan ta tashi ta tafi. kamar yadda manager ya ce mata".

Tun daga wannan rana Hassana ta fara zuwa koyan girkinta kullum har na tsawan sati d'aya kamar yadda manager ya bata. Habib ko koda ya tambayi Hassana lafiya ta bar zuwa aiki , fad'a mai ta yi manager ne ya bata suspection, Habib bai cema Hassana ko mai ba. Ahaka dai har Hassana ta yi sati d'aya".


Zaman Hassana da Habib ko masha Allah, dan ahanki ahankali shak'uwa keta k'ara shiga tsakanin Hassana da Habib sosai".


Yau Hassana da wuri ta tashi tai shirin zuwa aiki, tana zuwa ta samugu inda ta saba zama ta zauna".


Billy ko da ke cikin karanta ba babbaka k'arfe biyu tazo aiki. Abin sosai ya yi ma Hassana da d'i, ganin Billy yanzu tazo aiki. Hassana tashi ta yi tana kallan Billy ta ce, " 'Yan matan manager ki ce yadda kika ga dama kike zuwa aiki, tom ki koma gida sai nan da sati biyu ki dawo! ". Billy dariya ta yi, ta ce, "Banda lokacin ki amma ga manager nan bari yazo ya baki amsa. Manager k'arasowa gun ya yi yana kallan Billy irin lafiya? ". Murmushi Billy ta yi, sannan ta ce, " dearie wai ta ban Suspection na two week's ". "Muje ". Manager ya cema Farida". Hassana kuma kallan manager ta yi, ta ce, "Ai wallahi sai ta yi zaman gida na sati biyun da na anbata". Billy kallan manager ta yi, ta ce, " dearie muje ka rabu da karyar". Hassana ranta b'ace ta ce, "Shine kare, shida ke binki kamar. ..... ". Marinda manager ya yi ma Hassana ne yasa bata k'arasa fad'in abinda tai niyya ba, manager hannu yasa zai kuma wanka ma Hassana mari... ".


Yaji an ce, "Managereeeeeeeee..... โœ๏ธ



Idan kin karanta daure ki Comment sister ๐Ÿค




Share
&
Comment please ๐Ÿ™
๐Ÿ“š OGA HABIB ๐Ÿ“š
๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ
*๐Ÿ…™๏ธŽARUMAI ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ WRITERS ๐Ÿ…๏ธŽSSOCIATION๐Ÿ“š๐Ÿ–Š๏ธ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa๐Ÿ’ช*_

*๐Ÿ’ซ(๐Ÿ…™๏ธŽ.๐Ÿ…ฆ๏ธŽ.๐Ÿ…๏ธŽ)๐Ÿ’ซ*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).


https://chaveryt.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7


https://www.facebook.com/groups/301023561618950/

Albishirin ku masu bibiyar littafin Fadila Sani Bakori.
Yau gani da daddad'an albishir gare ku, insha Allah daga na kammala Oga Habib, zan nisha d'an tar da ku da sabon littafina wanda na baje basirata acikin shi. Anyi amfani da salo na birgewa acikin littafin. Labari ne wanda ya ke d'auke da madarar Soyayya, mai d'auke da ban al'ajabi. Inda ta wani b'angaran labarin ke d'auke da ban tausayi mai tsayawa a zuciyar makaranci. Duk yadda zan sanar daku ba zaku fahimta ba, ke dai karki bari abaki labari.
Zaki samu littafin akan farashi mai sauk'i da rahusa๐Ÿ‘Œ๐Ÿ‘Œ.
Summary.
Abba tin ina yaro kana yawan fad'a min, duk abinda ya yi tsanani yana tare da sauk'i. Shin ni sai yau she sauk'i na zai zo! ?. Abba me yasa muta ne basa ganina, maganata kawai su ke ji!?.Abba me yasa muke rayuwa a daji mai makon cikin gari cikin mutane !?.
Abba kana gani Husna zata aure ni, duk da halin da nake ci!?.
Abba me yasa Husna ta kasan ce ita kad'ai ke ganina!?. Abba kace kai ba Mahaifinsa bane, tom waye Mahaifina, kuma me yasa muke rayuwa a jeji!?, Sannan me yasa Abdussalam kad'ai ke zuwa gurin mu, sannan Abba waye Abdussalam ?.
Haidar duk banda amso shin tambayoyin ka, nima ban san kai na ba Haidar, ban san waye ni ba, bare kuma kai!.
Labari mai tab'a zuciyar mai karatu.

Paid book

Akan farashi mai sauk'i da rahusa ๐Ÿ‘Œ๐Ÿ‘Œ

Dan nai man k'arin bayani zaki iya managa ta wannan Number๐Ÿ‘‰ 08063830828.



Shafi na 79&80.




Managerrrrrrrrrrrrr.... ". Habib da fitowar shi ke nan daga Office d'in shi, ya ci karo da marin da Manager ya yi ma Hassana, manager ya kuma d'aga hannu zai k'ara mata ne Habib ya yi mai wannan kiran. Habib ranshi b'ace ya k'ara so gun, yana zuwa ya d'aga hannu sai da ya yi ma manager mari kwarara guda uku, sannan Habib ya nuna shi da hannu ya ce, "Manager ashe baka da tunani ban sani ba, yau fa ta dawo aiki daga Suspection d'in da ka bata, haka bai yi ma ba yanzu ta dawo zaka d'aga hannu ka mareta a company'na kuma!, ba komai ba laifinka ba... ". Maganar Hajiya Turai da Habib ya ji ce, ya yi saurin juyowa. Hajiya Turai zuwan ta kenan, ta hango Hassana zuk'un ne agun tana kuka, Hajiya Turai ita duk tunaninta ma Habib ne ya mari Hassana, hakan yasa, tana zuwa ta kamo hanun Hassana da ke zuk'unne agun ta ce, "Yi hak'uri daughter tashi muje gida". Daga ganin yadda Hajiya Turai ke magana kasan ranta a matuk'ar b'ace ya ke".


Habib ko da kallo ya bi Hajiya Turai, dan yama rasa ya zai ce mata, Habib bin Hajiya Turai ya yi, dai-dai zasu shiga mota, ya ce, "Mommy ki.... ". "Bana son magana a condition d'in da nake! ". Habib jin abinda Mahaifiyarsa ta ce ne yasa ya ja bakinsa ya yi shiru".


Habib Office d'in shi ya koma, ga ba d'aya ya rasa abinda ya ke mai dad'i, ana cikin haka ne, manager ya shigo, manager cikin hikima ya fara magana kamar haka"M'd ka yi hak'uri na kasa control d'in fushina, dan Allah ka yi hak'uri, ta kira ni da sunan da nakasa control d'in kaina ne... ". Tsawar da Habib ya yi ma manager ce tasa ya yi shiru. Habib kallan manager ya yi, ya ce, "Manager wai hak'uri zaka ban!?, kasan abinda ka aikata kuwa? , mari fa!?, tom bari kaji naji haushin korarta aiki da kayi, amma ban nuna ma ba, amma haka bai ma ba..., manager bana son yawan magana dan Allah ka fita kawai! ". Manager kallan Habib ya yi, ya ce, "M. D, dan Allah ka saurare n.. ". "Kafita nace ko!? ". Habib ya fad'i maganar da k'arfi".


Manage fita ya yi. B'anga ran Hajiya Turai ko, bayan sunje gida kallan Hassana ta yi ga sawun marin da manager ya yi mata nan kwance a fuskarta, Hajiya Turai kallanta ta yi, ta ce, "Habib d'in ne ya mareki haka daughter? ". Kai Hassana ta girgiza ma Hajiya Turai ta ce, "A, a Mommy ba shi bane manager ne". Hajiya Turai da mamaki ta ce, "Manager kuma?, yanzu har Habib ya ba su manager damar da zai d'aga hannu ya mareki!?, dama da nace ma Habib kar ya sake kije Sanat aiki, da ya ke yaga na tafi shine sai da ya tura

Please Login or Register in order to submit comment