Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ce ma, Mahaifiyarta, indai Farida ta tabbata ta ba Habib ruwan tea d'in yasha shikenan, Hajiya Turai azuciyarta ta ce, "Tom ko dai had'a kai su kai harda Bilyan ma?, nan dai Hajiya Turai da taga bata da mai amsa mata, maida kallanta ga Bilya ta yi, ta ce, "Bilya waya ce ka kaima Habib ruwan tea bacin kasan daga nan ake kai mai? ".Bilya cikin natsuwa ya ce, "Hajiya shi yace in kaime, nima bansan dalilinshi ba nahakan". Hajiya Turai kallan tuhuwa taima Bilya sannan ta ce, "Tom meyasa baka kaime da kanka ba kaba Hassana? ". Bilya cikin full Confidence, ya ce, dan yaga kamar Hajiya Turai yau zarkin shi ta ke yi, hakan yasa ya ce, "Hajiya tun kafin in Tashi bacci Farida ta matsamin da kira akan sai dai in kaita Sanat yughurt, amma nace mata sai nayi wanka, rok'ona ta yi akan dan Allah in kaita, alabashi idan na dawo sai in yi wankan, tom ni kuma bazan iya musa mata ba, hakan yasa sai nace mata ganinnan zuwa, tom shine fa bayan takatse kiran ni kuma na yi sauri nashiga wanka. Tom ina fitowa daga wanka Oga Habib ya kirani akan in siyo mai tea in kai mai yanzu. Tom nasan idan Oga Habib ya na son Abu yadda yake, hakan yasa ina fitowa na manta da Farida na jirana na tafi, sai da nashiga Sanat company sannan natuna da tun d'azu Farida ke jirana. Tom nasan Oga Habib idan nashiga dakyar idan zai barni in fito yanzu zai iya sani wani abun, hakan yasa da naga Hassana na bata tea d'in nace ta kaime, ni kuma na dawo da niyyar d'aukar Farida, tom ahanyama muka had'u ta gaji da jirana ta taho a napep,na tsaida napep d'in na d'auketa. Shine fa muna shiga cikin Company muka ji wata irin razanannar k'ara Oga Habib ya yi".
Bilya kallan Hajiya Turai ya yi ya ce, "wannan shine abinda nasani Hajiya, amma ga Hassana nan sai ta idasa miki bayani".

Shiru Hajiya Turai ta yi dan tabbas a kwai alamun gaskiya a magan-ganun Bilya, hakan yasa Hajiya Turai ta kalli Hassana ta ce, "Hassana bayan shigarki Office d'in Habib me yafaru, alokacin? ". Hassana cikin sanyin murya ta ce, " Hajiya Duk da Oga Habib nada idan mutum ya yi nocking ya dad'e bai amsa mai ba, amma gaskiya a Jiya da zan shiga office d'in shi, naji shirun ya yi yawa, dan har saida nafara tunanin ko dai baya office d'in ne, sannan zuwa can yace in shigo, koda nashiga jug d'in hannuna na mik'a mai na ce inji Oga Bilya ya ce zai dawo yanzu". Shiru Hassana ta yi ta d'an numfasa, sannan ta ci gaba da cewa, " gaskiya tunda nashiga Office d'in Oga Habib zan ita cewa babu lafiya atattare da yadda naga yana yin shi, dan koda na bashi sak'on Oga Bilya, bai amsamin ba bai kuma kallan ba, sai dai ya tashi tsaye ayanayin yadda naga jikinshi kamar rawa yake, hakan yasa sai naji tsoro naja baya, sai ji nai ya mik'on hannun shi ya ce, dan Allah in rik'e mai. Tom ni dama gaskiya ko ayanayin yadda naji maganarsa nasan ba lafiyar shi k'alau ba, hakan ya sa naruga zan bud'e k'ofa in fita, amma kafin in fita har yarik'omin hannu, dan su Oga Bilya ne ma suka k'watan daga hannun shi".
Shiru Hassana ta yi sannan ta ce, "wannan shine abinda ya faru, Hajiya da nashiga office d'in Oga Habib kai mai tea d'in ".
Shiru Hajiya Turai ta yi tana kallan Hassana, dan akwai alamun gaskiya a maganar Hassana d'in, dan yanzu ta san abinda kunnan ta yaji mata hakane, Farida ce ta ba Habib wani tea d'in kenan, wato idan ta fahimta farida taso zuwa office d'in Habib kafin abinda ya sa mai ya sa mai.
Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana je ki abinki". Bayan Hassana ta tafi ne, Hajiya Turai ta kalli Bilya ta ce, Bilya kaje Zaria yau d'in nan ka tahomin da Baba lami, dan ina buk'atarta sosai, amma dan Allah kafin munje akaima Habib abin break fast, nasan tunjiya baici komai ba, inda bacikin hankalinshi ya ke ba.Bilya tashi ya yi Hajiya Turai, tafi bayansu suka tafi ganin halinda Habib ya kwana, tare da kai mai abin break fast. Bilya tsayawa ya yi daga k'ofar d'akin ya ce, "Hajiya ko za ki yi gaba? ". Hajiya Turai gaba ta yi batare da ta tankama Bilya ba.Hajiya Turai zaune ta iske Habib, sai dai kafin ta k'arasa inda ya ke Habib ya yo kan Hajiya Turai".

Wani irin rik'o Habib ya yi ma Hajiya Turai, yana wujijjigata. Hajiya Turai tun tana daurewa tana cewa, "Habib ni ce fa, Habib mahaifiyarka ce fa ni, Habib kamanta ni ne ?, sakanni Habib da zafi! ". Haka Hajiya Turai ta idasa maganar cikin tashin hankali. Daga k'arshe da taga Habib tabbas bacikin hankalinshi ya ke ba, hakan yasa ta fasa k'ara ta ce, "Wayyo Bilya kana ina zo ka tai makamin! ".

Bilya da saurinsa ya shiga, kan Habib ya yo, Habib ko na ganin Bilya ya saki Hajiya Turai ya yi kan Bilya, sai dai Bilya na ganin haka ya fita da gudu. Hajiya Turai ko ta k'ofar baya ta fita itama. Hajiya Turai falon bedroom d'in da Habib ya ke ta zauna tana, kuka. Bilya zagayawa ya yi ta baya yashiga falon Habib d'in, zaune Bilya ya iske Hajiya Turai tana kuka ".

Bilya k'arasawa inda Hajiya Turai ta ke ya yi. Bilya cikin lallashi ya ce, "ki yi hak'uri Hajiya shi kuka da kika gani babu wani abunda zai miki sai dai ya samiki wani ciwan, yanzu abinda ya kamata muyi musan abinda ke damun Oga Habib". Hajiya Turai d'aga kai tayi tana kallan Bilya ta ce, "Bilya na san meke damun Habib, shi yasa nake son ganin Baba lami da sauri, ka tafi Zaria yanzu dan Allah Bilya ka tahomin da Baba Lami". "Shikenan Hajiya babu damuwa insha Allah yau d'innan zaki ga Baba Lami. Bilya na fad'in haka ya yi ma Hajiya Turai sallama ya kama hanyar Zaria.
Hajiya Turai ko na nan zaune tana tunanin, magan-ganun Farida na d'azu, ta ce, "wato idan nagane maganar Farida tana nufin wadda Habib ya tashi ya farka a halinda ya ke yagani, zai iya yadda da ita kenan.kai wai tom meye niyyar Farida ne akan Habib?, ya Allah ka kawo min Baba Lami yau". Hajiya Turai fitowa daga falon Habib ta yi, tana fitowa ta had'u da Farida ita kuma da shirinta na barin gidan".

Farida cikin mamaki ta kalli Hajiya Turai ta ce, "Kai Mommy ashe kin dawo?, yaushe kika dawo? ". Hajiya Turai ji tai kamar tai banza da Farida, sai da bata son ta nuna ma Farida komai, akwai lokaci acewarta. Hakan yasa Hajiya Turai ta ce, "Jiya da daddare lokacin kinyi bacci, Ina zaki ne haka? ". Hajiya Turai ta tambayi Farida."Sak'o Mommyna ta aikan in amso mata, yanzu zan dawo". "Ok". Hajiya Turai ta ce mata sannan ta juya ta tafi. Hajiya Turai Bilya ta kira awaya, Bilya na d'agawa tace, "Hello Bilya kana jina ko? ". "Eh Hajiya Ina ji". "Yauwa, Bilya idan baka riga katafi ba, ka je Sanat company yanzu dan Allah, ga Farida nan zata je yanzu, kayi k'okari ina son sanin abinda ya kaita". "Shikenan babu damuwa, bari inje kafin ta isa". Bilya na fad'in haka, ya juya yakama hanyar Sanat company".

Hajiya Turai nagama wayar sai ga wata binta da ke mata wanki, Hajiya Turai kiranta ta yi, ta ce, "Binta kiramin yarinyar da ke aiki a Sanat yughurt". Binta da saurinta ta juya ta tafi dan ida sak'on Hajiya Turai".

Hassana na zaune ita kad'ai dan soran worker's d'in Kowa ya kama gabanshi dan yin aikin da ya ke amazaunin nashi, binta tazo ta ce, "Ke Hajiya na kiranki, ta ce ki sameta a falonta". Gaban Hassana fad'uwa ya yi jin wai Hajiya na kiranta. Azuciyarta ta ce, "Tom bayanzu ta kirani ba ba dad'ewa, Allah dai kasa lafiya". Hassana tashi ta yi tanufi site d'in Hajiya Turai. Hassana zaune ta iske Hajiya Turai a falonta. Hassana cikin sanyin muryarta ta yi sallama, d'annesa da Hajiya Turai Hassana ta zauna, bayan Hassana ta zauna ne, ta kalli Hajiya Turai ta ce, "Hajiya gani ance kina kirana". Hajiya Turai abin break fast d'in da suka kaima Habib suka dawo dashi ta mik'ama Hassana ta ce, "Kin san site d'in Habib? ". "Eh na sani". "Yauwa, Hassana dan Allah me ba Habib abinci ne baya nan, na aikai Zaria, shine dan Allah nake son ki kai mai".
Hassana cikin girmamawa ta ce"Tom". D'aukar abin break fast d'in Hassana tayi ta tafi.Hajiya Turai tashi ta yi ta yi bedroom d'in ta fita tashiga Falon Habib ta na jiran zuwan Hassana taga ikon Allah, ta ga maganar da Farida ta fad'a gaskiya ne kok'aya".

Hassana ko,
tambayr kanta ita kad'ai ta yi, ta ce, "Tom oga Habib ya warkene? ".Nan dai bata da mai bata amsa, haka Hassana ta nufi site d'in Habib da abincin gabanta na fad'uwa. kasan cewar Hassana ba taji labarin Habib na dukaba, hakan yasa ba wata fargabar hakan, ta bud'e k'ofar ta shiga kai tsaye.........




COMMENT
&
SHERE
PLEASE πŸ™

πŸ“š OGA HABIB πŸ“š
πŸ’«πŸ’«
*πŸ…™οΈŽARUMAI πŸ…¦οΈŽ WRITERS πŸ…οΈŽSSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausaπŸ’ͺ*_

*πŸ’«(πŸ…™οΈŽ.πŸ…¦οΈŽ.πŸ…οΈŽ)πŸ’«*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK'R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D'AN TARKU DA HAZIK'AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD'UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K'AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK'E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K'OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN πŸ‘‡πŸ»
K'ABILA CE! K'ABILA CE!! K'ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K'ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA AKE POSTING.
KI GARZAYA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D'AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K'ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT πŸ‘‡πŸ»
08142904255.



Shafi na 22&23.



Habib na kwance ya juya baya, motsin bud'e k'ofar da yaji yasa ya juyo da sauri. Habib batare da yasan ko waye ba ya tashi da sauri ya yo kan Hassana. Hassana ko ganin yadda Habib yayo kanta da sauri sai abin ya bata tsoro, duk da bata san yana duka ba, Hassana gefe d'aya ta takure da break fast d'in dake hannunta.
Hajiya Turai da ke lekyan Hassana ta window, dafe kai tayi dan a tunaninta Habib zai rufe Hassana da duka ne, amma sai taga akasin hakan.
Habib na zuwa inda Hassana ta ke da sauri ya kamo hannunta yana janta cikin d'akin, Hassana da mamaki tabi Habib da kallo.
Habib ko kan lover chair d'in shi ya zaunar da Hassana shima ya zauna kusa da ita, ba baki sai dai kallanta kawai da yake yi. Hassana ko koda ganin yadda Habib yake kallanta da yanayin yadda yake acting ta kuma tabbatar da Habib bacikin hankalinshi ya ke ba. Hassana so ta ke ta kwace hannunta daga na Habib amma ta kasa, gashi duk cikin tsoro ta ke. Cikin jarumta da rawar murya Hassana ta ce, "Oga Habib ga abin break fast d'in ka, Hajiya ta ce in kawo ma". Hassana ta nuna ma Habib abin break fast d'in. ruwan Lipton ne sai gwangwanin madara da na Nescafe da milo, Sai wainar k'wai. Habib kalla kawai ya yi batare da yace ma Hassana ko mai ba.
Hassana ko ganin Habib bai ce mata ko mai ba, sai ta kuma cewa, muryarta na rawa, "Oga Habib ka sakanmin hannuna in had'ama tea d'in ". Habib sakin hannun Hassana ya yi. Hassana kuma da sauri tatashi ta had'ama Habib tea d'in, bayan tagama had'a mai, kallan shi ta yi cikin rawar murya ta ce, "Oga Habib ga tea d'in? ". Habib hannu ya mik'ama Hassana ta mik'amai tea d'in. Hassana ko ganin ta yi abinda ya kawota tashi ta yi daniyyarta ta tafi. Habib ya yi saurin rik'o hannunta. Hassana cikin tsoro ta kalli Habib dan ita yanzu tsoro ma ya ke bata, dan daga ganin shi kasan bacikin hankalinshi ya ke ba, Hassana kamar zata yi kuka, ta ce, "Oga Habib Hajiya ke jirana dan Allah ka sakanmin hannu".Habib kafad'a ya mak'alema Hassana alamun nak'i d'in. Babu yadda Hassana batayi ba Habib ya sakar mata hannu amma yak'i, Hassana kamar zata yi kuka ta kalli Habib ta ce, "Oga Habib dan Allah katai maka kasanmin hannuna dan Allah". Hassana ta fad'i maganar kamar zatayi kuka. Habib sake mak'ema Hassana kafad'a ya yi.
Hajiya Turai ko tananan tsaye jikin window tana kallan duk abinda ke faruwa tsakanin Habib da Hassana. Hajiya Turai ganin Hassana ta fara kuka akan Habib ya saketa shi kuma yak'i yasa ta fita da sauri ta zagaya ta shiga bedroom d'in Habib d'in . Habib ko naganin Hajiya Turai ya saki Hassana ya yi kan Hajiya Turai. Habib na isa yarik'e Hajiya Turai yana jijjigata. Hajiya Turai bata san sanda ta fasa kuka ba, bawai jijjigar da Habib ya ke mata bace tasata kuka ba, a'a, bak'in cikin yadda aka rabata da d'anta guda ne yake sata kuka, ace wai ita ce yau Habib bai son gani in har yaganta sai dai yayi ta jijjigata, hakan yasa Hajiya Turai tai ta kuka, Habib kuma na ci gaba da jijjigata".


Hassana ko ganin yadda Hajiya Turai ke kuka, yasa cikin tsoro ta nufi gurin da ta ke dan itama tsoro ta ke kar Habib ya yi mata yadda ya ke ma Hajiya Turai. Hassana na zuwa cikin tsoro da fargabar kar Habib itama ya yi mata abinda ya ke ma Mahaifiyar shi. Hassana tana kuka ta rik'e hanun Habib tana cewa,cikin kuka" Oga Habib dan Allah ka saketa, Mahaifiyarka ce fa, ka barta ". Hassana anshe Hajiya Turai ta yi daga hannun Habib. Hassana kama hannun Hajiya Turai ta yi tazaunar ta ita bakin gadon Habib tana cewa, "Hajiya dan Allah kiyi hak'uri kibar kuka, kinsan Oga Habib bazai miki hakaba cikin hankalin shi ba, ki yi hak'uri dan Allah kibar kukan Hajiya ". Hajiya Turai da katawa ta yi da kukan ta d'aga kai tana kallan Hassana, Hajiya Turai batare Da ta ce ma Hassana ko mai ba tashi ta fita daga d'akin".

Hassana da kallo tabi Hajiya Turai, sannan itama ta tashi tabi bayan Hajiya Turai, sai dai kafin ta fita Habib ya yi saurin dawo da ita ta hanyar rik'o hannunta. Hassana kamar zata yi kuka ta kalli Habib, ta ce, "Oga Habib kasa kan min hannu dan Allah ina so zan tafi ne". Habib mak'ema Hassana kafad'a ya yi. Duk yadda Hassana taso Habib ya saki hannunta k'i ya yi, k'arshe ta fashe da kuka.Haka Hassana ta yi kukanta ta gaji daga k'arshe ta yi shiru".

Shiko Habib koda yaga Hassana na kuka kallanta kawai ya ke, kuma har yanzu yana rik'e da hannunta.
Hajiya Turai bayan ta koma falonta kuka ta yi sosai sai da ta gaji dan kanta sannan ta yi shiru. Hajiya Turai tashi ta yi ta koma falon Habib, ta window ta lek'a ta hango Hassana zaune da Habib kusa da ita yana rik'e da hannun Hassana kamar wata wadda tai mai laifi. Hajiya Turai kiran Hassana, ta yi,ta ce, Hassana kizo yanzu". Hassana kallan Hajiya Turai ta yi, dake magana jikin window ta ce, "Hajiya tun d'azu nake son tashi Oga Habib ya hanani". Hassana ta fad'i maganar kamar zata yi kuka.
Hajiya Turai cikin sanyin murya mai cike da rauni ta ce, "Hassana ki yi hak'uri kin ji dan Allah nasan yanzu Bilya zai shigo". Hajiya Turai na fad'in haka tabar gun tana share hawayanta, dan sosai halinda Habib ya ke ciki ya ke damunta, uwa-uba kuma ganin yadda ya ke mata in tashiga wajan shi, wannan abin shike k'ara d'agama Hajiya Turai hankali".

Bilya bashi ya dawo daga Zaria ba sai 3:13Pm. Haka Bilya da Baba Lami suka jera suka shiga falon Hajiya Turai. Zaune suka isketa kan caution ta yi ta gumi.
Bilya cikin tausayama halinda Hajiya Turai ta ke ciki ya yi sallama falon Hajiya Turai. Hajiya Turai d'aga kai ta yi tana kallan Bilya, sannan cikin sanyin murya ta amsa mai sallamar. Bilya da Baba lami shigowa sukai cikin falon suka zauna da nesa tsakaninsu da Hajiya Turai".

Bilya Kallan Hajiya Turai ya yi ya ce, "Hajiya ga Baba lamin nan, bari inje inyi sallah ahanya ta saman". Bilya na fad'in haka yatshi zai fita.
Hajiya Turai Kallan Bilya ta yi, cikin sanyin murya ta ce, "Bilya tun safe yarinyar nan na gurin Habib ya hanata fitowa, dan Allah ko za kai ma su musa magana ku shiga ku fito da ita? ". Bilya cikin damuwa da fad'uwar gaba ya kalli Hajiya Turai ya ce, "Ok, bar in yi sauri muje". Bilya na fad'in haka ya juya ya fita daga falon. Bilya cikin tashin hankali ya nufi k'ofar da zata sada ka da falon Habib, ta window Bilya ya lek'a, dan a tunanin shima yanzu Habib ya yi ma Hassana illa, dan har yanzu Bai manta wujijjigawar da Habib ya yi ma Hajiya Turai ba, tom ita da ta ke mahaifiyarshima bare Kuma wata Hassana da tun lokacinda abin yasa meta da kyar aka kwaceta awajanshi. Bilya na maganganun zuci ya isa k'ofar, ta window Bilya ya lek'a da yake window abud'e ya ke".

Zaune Bilya ya hangi Hassana da Habib da ke rik'e da hanbuta kata kam kamar irin yana tsoran za a kwace ta . Ajiyar zuciya Bilya ya yi ganin Hassana lafiya klau.
Hassana ko zaune ta ke sai zazzare ido ta ke kamar wadda tai k'arya asirinta yatonu.
Bilya komawa ya yi ya je bakin get yakira Musa. Musa yana d'aya daga cikin masu gadin gidan".

Bilya na zuwa kusan mamayar Habib su kayi, amma dakyar suka iya k'wace Hassana daga hannun Habib. Hassana ko naganin Allah ya taimaketa ta kubuta daga hanun Habib da saurinta har tana tuntub'e wajan rugawa site d'in su.
Bilya ko suna kwace Hassana suka yi sauri suka rufe k'ofar suka bar Habib shi kad'ai".

Hajiya Turai ko bayan fitar Bilya Kallan Baba Lami ta yi, ta ce, "Baba barka da zuwa, ya hanya, ki yi hak'uri Baba zaki ce ban ne mekiba lokacinda Habib ya koreki sai yau da buk'atata ta tashi, Baba dan Allah taimako zaki min kamar yadda ki kaimin kafin mutuwar Mahaifin Habib? ". Baba Lami Kallan Hajiya Turai ta yi, dan duk bata gane takan zancan ba ta ce, "Hajiya ina ji, wana irin tai mako zan baki? ". Shiru Hajiya Turai ta yi, tana tunanin ta inda zata fara yima Baba Lami bayani, sannan zuwa can ta ce, "Baba Habib ne baida lafiya, kuma ciwannashi kamar hauka, dan Baba Lami yanzu ko ni ban isa inje d'akin Habib ba, sai yarinya d'aya agidannan dan yauma ita akaba abin break fast d'in shi ta kai me, amma cikin ikon Allah ita Bai mata komai". Baba Lami Kallan Hajiya Turai ta yi ta ce, "Hajiya to aiko idan haka ne akwai alamar tambaya ajikin yarinyar nan, wata yarinyar ce? ". Hajiya Turai Kallan Baba Lami ta yi ta ce, "Yarinyar da ya koreki keda Bilya akanta". Shiru Baba Lami ta yi, Sannan ta ce, "Hajiya wai meye musabbabin ciwanne?, koko sai dai kuka wayi gari kuka ganshi ahaka?". "Eh Tom Baba Lami, maganar ce nada mamaki da kuma d'aure kai, wato Baba Lami naje d'akin Farida sai naji tana waya da Hajiya Murja tana cewa ita yanzu abinda ke damunta yarinyar da ciwan ya riski Habib da tana wajan yanzu da ita zai rik'a yarda ba ita ba, ita abinda ke damunta kenan, tom da yake a speaker wayar ta ke, sai naji ita Hajiya Murja na cewa, Farida kuma kin tabbata kin bashi tea d'in ya sha, Farida ta bata amsa da Eh, tom shine fa ta ce wai ta binciko mata sunan yarinyar da ciwan yamu Habib agabanta". Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta ci gaba da cewa, "tom Baba Lami kinjin abinda ke faruwa, dan Allah ki taimakamin kamar yadda ki kaimin lokacinda Mahaifin Habib na da rai! "? "Karki damu Hajiya insha Allah, mu bari sai gobe inda yanzu yamma ta yi". "Tom Allah ya kaimu goban Lafiya". Cewar Hajiya Turai ".
B'angaran Hassana ko yanzu haka kwance ta ke tana mamakin da Oga Habib Bai yadda da kowa ya shiga inda ya ke sai ita, abinda ya k'ara d'aurema Hassana kai har Mahaifiyar shi ma taga bata isaba tashiga inda ya ke ba, nan dai Hassana ta na tunane-tunananta ta bacci ya kwasheta inda dama ba sallah zata yi ba".

Bilya bashi ya k'ara shiga part d'in Hajiya Turai ba sai da ya yi Sallar magriba sannan. Zaune Bilya ya isketa kan sallaya ta yi ta gumi. Hajiya Turai na ganin Bilya ta ce, yauwa Bilya dama maganarka na keyi azuci yanzu haka,kamar kasan san ganinka nake yi. D'azu da nace ma kabimin bayan Farida, ya akayi? ". "Hajiya kamar yadda ki kayi tunani Sanat yughurt taje, tana zuwa suka had'u da supervisor gun, bayan sun gaisane da yake sunsan juna tom shine Farida ke tambayar supervisor sunan wadda Habib ya rik'ema hannu lokacin da lallurar ta sameta, dan acewarta ga supervisor ke kika aikota wai kina zargin Hassana, tom nan dai ta fad'a mata sunan Hassana". Shiru Hajiya Turai ta yi Sannan ta ce, "Bilya dan Allah ka mik'ama Habib abinci kota window ne, dan ni Wallahi tsabar rud'ewa na manta kona rana ban bashi ba".

Bilya amsar abinci ya yi ya je ya jira ma Habib shi ta window kamar yadda Hajiya Turai ta ce.
Sai dai abinda basu saniba Habib ko Kallan abinci bai yiba".

Washe gari Hajiya Turai da Baba Lami da wuri suka yi sammakon zuwa zaria, inda Bilya ne zai kaisu.
Bayan sun fitone Hajiya Turai ta lek'a ta window tana kallan Habib zaune yake inda yasaba zama. Hajiya Turai ganin abinci jiya ta yi yadda aka kaishi yana nan ahaka. Hajiya Turai Bilya ta kira ta nunamawa ta ce, "Bilya kaga abincin jiya ko Habib bai ciba? ". "Eh Wallahi Hajiya nima haka nagani". Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta kalli Bilya ta ce, "Bilya ku jirani amota kaida Baba Lami ina zuwa".

Hajiya Turai site d'in worker's d'in gidanta ta je, wata daga cikin masu yima Hajiya Turai aiki, Hajiya Turai ta aika takiramata Hassana.
Hassana ko lokacin tana kwance tana baccin safe,Binta ta shigo ta tada Hassanan, ta ce, "Hassana ki tashi Hajiyar Oga Habib na waje tana jiranki! ". Binta na fad'in haka ta juya ta tafi badare da ta tsaya taji amsar Hassana ba".

Hassana ko tashi ta yi ta tafita tana mai addu'ar Allah yasa Hajiya Turai ba abinci zata kuma cewa ta kaima Habib ba. Hassana na wannan tunanin ta isa inda Hajiya Turai ke tsaye tana jiran fitowar Hassana".

Hassana har k'asa ta juk'unna ta gaida Hajiya Turai tare da tambayarta ya mai jiki.
Hajiya Turai cikin sanyin murya ta ce, "Lafiya klau, Hassana dan Allah taimako zaki min na k'arshe? ". Hassana cikin girmamawa ta ce, "InajI Hajiya". "Hassana dan Allah abinci zaki taimakamin ki kaima Habib, tun abincin jiya da kika kai

Please Login or Register in order to submit comment