Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce, "bud'e bakin". Hassana bud'e bakin ta ta yi Habib ya tsiyaya mata tea d'in, haka dai suka gama shan tea d'in Habib na sha yana ba Hassana ".


Bayan sun gama shan tea d'in ne Habib ya tashi dan yau yana son yaje Company ya gani, Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Sanat zan je aiki yau". "Tom sai ka dawo". Hasssana na fad'in haka ta juya zata tafi, Habib jawo hannun ta ya yi ya ce, " Ban wani abu mana, da zan tuna da ke in naje". Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Wani abu kamar me? ". Hannun Hassana Habib ya ja wo ya yi mata Uhhmm muahh lips d'in ta. Hassana da babu zato babu tsammani ta ji sauk'ar kiss aleb'anta. Habib ya ce, "Kamar irin haka nake nufi". Hassana fusge hannun ta ta yi ta gudu tabar Habib tsaye agun, Hassana kusa da Hajiya Turai ta Fad'a ta zau na, tana sauke ajiyar zuciya, Hajiya Turai wai gowa kawai ta yi ta kalli Hassana ta girgiza kai. Hassana ko sai yan zu ta lura da Hajiya Turai".


Habib sallama Ya yi ma Hajiya Turai ya tafi. Habib ko da ya je Company, Alhamdulillah ya iske kumai na tafiya yadda ya kamata, dan yan zu Bilya da Billy suke jan ragamar komai. manager ko dama ya ce ma Billy daga ta ga M. D, ya zo ta kira shi ta fad'i mai. Aiko Billy tana ganim Habib ya zo ta kira manager a waya ta sanar da shi".


Habib na zau ne a Office d'in shi Manager ya yi nocking, Habib izinin shiga ya ba shi, manager cikin sanyi ya gaida Habib sannan ya ce, "M. D, hak'ik'a na san nayi kuskure kuma tabbas nayi nadamar abin da ya faru, dan Allah ka yi hak'uri". Shiru Habib ya yi yana kallan manager , sai zuwa can ya d'aga kai yana kallan manager ya ce, "Manager abu d'aya zai sa in yafe ma kuma abun d'aya ya hana ban d'au ma taki akan ka ba, saboda ayan zu kai kamar sirikina ne, zan ma hak'uri ne sabo da haka, Sannan kai ka shige gaba wajan aure na da Sanat, zan ya fema dan haka,amma duk da haka sai da yaddar Sanat, dan haka ka saurare ni zuwa gobe". Manager godiya ya yi ma Habib ya tafi, dan yadda ya ke samun kud'i a Sanat ba zai yarda ba aikin ya sukub'uce mai ba".



Habib gaf da magriba ya tashi aiki ya koma gida. Side d'in shi ya shiga sai da ya watsa ruwa ya yi sallah sannan ya nufi b'angaran Hajiya Turai. Habib Hajiya Turai kad'ai ya iske a Falon, zama Habib ya yi gefan Hajiyarsa ya gaida ta. Shiru-shiru Habib bai ga Hassana ba, Habib Hajiya Turai ya kallah ya ce, "Mommy ina yarinyar nan? ". Hajiya Turai kallan Habib ta yi, ta ce, "Wata yarinyar? ". Kai Habib ya sosa ya ce, "Mommy Sanat fa nake nufi". "Ok, tana ciki... ". Hajiya Turai bata rufe baki ba Hassana ta fito, Hassana gefan Hajiya Turai ta zau na. Hassana na zama Hajiya Murja na yin sallah ma ta shigo, Hajiya Murja na zuwa ta je ta rik'e k'afafun Hajiya Turai tana kuka, ta ce, "Hajiya dan Allah ki bar Habib ya rufa min asiri ya ceto rayuwar yarinyar nan ya aure ta, Wallahi yan zu haka Hajiya Turai na barota sai aman jini take,Habib dan Allah ku tai maka". Habib da tausan Hajiya Murja ya kama shi, gyaran murya ya yi, ya ce, "Mommy ki yi hak'uri ni nai miki alk'awari kuma zan cika miki insha Allah". Habib mai da kallan shi ga Hajiya Turai ya yi ya ce, "Mommy ku yi hak'uri dan Allah ke da Sanat zan auri Farida ne ba dan soyayya ba, zan aure ta ne dan ceto rayuwarta, dan Allah Mommy ku yi hak'uri ". Hajiya Murja kallan Habib ta yi, ta ce, "Habib in dai ka yarda zaka ceto rayuwar Farida tom kazo mu je yan zu ga waliyin Farida nan cikin mota, kai kuma sai ka samu naka, yan zu ad'aura auran idan an idar da Sallar issha'i ". Habib kallan Hajiyarsa ya yi da fata furta koma ba, ya mai da kallan shi ga Hassana da ita ma shi ta ke kallo, Habib jin du kan su babu wanda ya yi magana, kallan Hajiya Murja ya yi, ya ce, "ki je gida kawai zan nai mi wanda kika ce kuna tare yan zu mu yi magana". Hajiya Murja godiya ta yi ma Habib sannan ta tashi ta tafi, Hajiya Murja ta tafi bai fi da minti goma ba Habib ma ya tashi jin kiran Sallah zai tafi. Hassana ko da ta san Habib daga wajan Sallar za'a d'aura auran shi da Farida, Hassana ta shi ta yi da sauri ta rik'o hannun Habib, Hassana cikin kuka ta ce, "Wallahi Oga Habib Allah baza ka fita ba sai ka sakan ai tun jiya haka mu kai da kai, ka sakan sai kaje ka aure ta in da tausan ta ka ke ji! "Habib tsayawa ka wai ya yi yana kallan Hassana yama rasa me zai ce mata, Hassana kuma ta kama Habib kata kam ta rik'e ta k'i saki. Hajiya Turai ko da ita kanta bata san mai zata cema ba,tashi tai ta ba su gu".


Habib kallan Hassana ya yi cikin sanyin murya ya ce, "Haba Sanat wai ke biki san abin da kike fad'a babu kyau ba, dan Allah me yasa kike yin haka ne, ki zauna in je Sallah in dawo sai mu yi magana". "Ai ina ji kace idan kaje sallah za'a d'aura auran acan, ni dai kawai ka ban sannan ka tafi, amma ni bazan tab'a zama da Farida ba!". Duk maganar da Hassana ta ke yi cikin kuka ta ke yin ta".


Habib hannun Hassana ya kama suka zauna, hannu Habib ya sa ya goge ma Hassana hawayan ta, ya ce, "Sanat ki yi shiru tom muyi magana". Hassana shiru ta yi tana kallan Habib alamun ina jinka. Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Yan zu me ye damuwar ki da auran Faridar? ". "Ni ban iya zama da ita ba ne". Hassana ta ba Habib amsa. Magana Habib zai k'ara yi ringing d'in wayar shi ya hana. Habib d'aga wa ya yi, daga can b'angaran Hajiya Murja ta ce, "Habib dan Allah naji shiru ga waliyin Farida ya kirani wai yaji ka shiru"."Ok, gani nan zuwa". Habib ya ba Hajiya Murja amsa".


Habib tashi ya yi zai tafi, Hassana ta rik'e Habib tai tana kuka, tana cewa, "Dan Allah Oga Habib karka je, dan Allah, Allah in ka aure ta ba zan ji dad'i ba, dan Allah ". Haka Hassana ta rik'e Habib tana kuka tana rok'an shi. Dan tai mai ma kurarin sakin amma bai ji ba".


Habib jikin shi sosai ya yi sanyi da yadda yaga Hassana tana kuka, ga Hajiya Murja na jiran shi. Habib rasa yadda zai yi ya yi, komawa ya yi ya zauna dan Hassana ta k'udin-dine shi ta hana shi fita, ga kukanta na da mun shi sosai, dan ya lura in dai tai kuka bata da wuyar ciwan kai".


Habib rungume Hassana ya yi yana lallashin ta, ya ce, "Shikenan na fasa, tom ki share hawayan ki". "Ai jiya ma haka kace min"
Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Kina son in fasa auran Farida? ". Kai Hassana ta d'aga ma Habib".


Habib kallan Hassana ya yi, yana na zari, dama yana son Hassana ta koma gidan shi da zama tom yasan Mommy ba zata bari ba, ba kamar yan zu ba da yasan ya k'ara b'ata ma ta rai ba, hakan yasa Habib cema Hassana, "Sanat na fasa auran Farida, amma in dai kin yarda sai dai yau ki koma gidanki ki bar gidan Mommy, kuma karki bari Mommy ta sani, tom in dai kin yarda da haka ni kuma na fasa auran ta". Hassana ba tare da tunanin ko mai ba, ta ce, "Eh na yarda". Habib cikin jin dad'in abin da Hassana ta ce, ya tashi ya ce, "Tom tashi mu tafi kafin Mommy ta fito ".


Hassana ta shi ta yi tana kama hannun Habib suka bar falon Hajiya Turai, suna zuwa Habib ya hangi wanda Hajiya Murja ta ce yana jiranta acikin mota. Shi ko mai jiran Habib ya na ganin Habib ya yo inda ya ke da sauri, hannu ya ba Habib suka gaisa, sannan ya ce, "Tun d'azu nake jiranka, gashi har nai ma limamin magana, yan zu haka kai suke jira". Habib kallan shi ya yi, ya ce, "sai zuwa gobe ma yi magana". Habib na fad'in haka ya shiga motar shi ya ja suka tafi suka bar Waliyin Farida tsaye".


Habib na isa gida direct falon shi ya yi da Hassana suna zuwa Habib ya shiga wanka, ya yi alwallah. Habib bayan ya fito sanye da farar jallahbiya aji kin shi, kwance Habib ya iske Hassana, Habib hannun ya mik'a ma Hassana ya ce"Sanat zo in cud'aki". Hassana dariya ta yi, ta ce, "Bana so kai ma kai kai ma kanka, ni ma ni zanma kai na". "Ok, kina sha'awar yi min ne? ". Habib ya tambayi Hassana ".


Hassana ta shi ta yi tana ba Habib amsa ta ce, "Uhm lokacin da baka da lafiya dai nai m.... ". Habib bud'e baki ya yi yana kallan Hassana ya ce, "Kin me? ". Hassana da sauri ta nufi hanayar Toilet, Habib ya ja wo ta ya yi yana kallan ta, ya ce, "Serious kin tab'a min wanka? ". Hassana kai ta juya ta ce, "Ni dai ka sakan in je in yi wanka na". "Nak'i d'in sai kin ban amsa, kin tab'a? ". Habib ya tambayi Hassana".



Shiru Hassana ta yi, sannan ta ce, "Ni fa bani kema ba, kai ne ke shiga da kanka idan ina wanka, duk yadda nayi ka yi da kanka kake ma kanka". Habib kallan Hassana ya yi ganin ta fad'i maganar tana b'oye dariya , ya ce, "Da kaya jikina ko ko? ". "Tom ni dai na ma manta kamar akwai kamar babu". Hassana ta ba Habib amsa still tana son yin dariya ".



Habib jan hanun Hassana ya yi juwa toilet d'in ya ce, "Muje nima yau ni zan miki ". Hassana k'ara ta yi, ta ce, "Tsaya in fad'ama gaskiya, Allah da kaya jikin ki". "Uhm nima muje in miki da kaya jikinki". Habib ya ce ma Hassana ".


Hassana tsayawa ta yi tana kallan Habib ta ce, "Tom inda haka ne ma na fasa wankan". Murmushi Habib ya yi, ya ce, "Aiko yau dole ki wanka". Habib da k'arfi yaja Hasssana ya kai ta toilet d'in". Hassana cikin sakin k'ara da ya ke ita mai katsaniya ce, ta ce, "Tom Oga Habib tsaya, Allah da kaya nake ma, nima ba sai na cire ba". Habib ko sauraran Hassana bai ba, ya zage zip d'in doguwar rigar jikinta. A haka akai wankan daga ita sai bra sai pant d'in jikinta. Hassana ganin wankan ya k'i k'arewa jawo towel ta yi ta d'aura tana turo baki, ta fita tana cewa, "Duk an bi an wani kalle mutum".


Habib dai murmushi kawai ya yi ma Hassana. Hassana na zaune tana shafa lotion d'in Habib, wayar Habib ta yi, ringing, Habib ganin number Hajiya Turai sai da gaban shi ya fad'i, aiko yana d'agawa Hajiya Turai ta ce, "Habib ina Hassana!? ". Habib kallan Hassana ya yi da ke zau ne tana shafa, sannan ya ce, "Mommy ga ta nan muna tare". daga can b'angaran Hajiya Turai ta ce, "Duk abin da ka ke ka bari ina son inga Daughter yan zun nan!? ". Hajiya Turai na fad'in haka ta kashe wayarta, tana mai ganin sakarcin Hassana ".



Habib ko tashi ya yi ya tada sallah, yana idarwa ya kalli Hassana ya ce, "kin yi Sallah ne? ". Kai Hassana ta d'aga ma Habib".



Habib ko gudin kar Hajiyarsa ta sake kira kashe wayar shi ya yi, acewar shi gobe ya mai da mata Hassanar. Habib kwanciya ya yi yana tunanin yadda zai yi da Mahaifiyar Farida, Hassana ko bayan ta gama shafarta da d'an k'aramin towel d'in da ke jikinta ta nufo wajan Habib, dan Hassana ta kan manta sabon da su kai da Habib kafin ya samu lafiya ne. Habib na kwance Hassana ta zo ta kwanta gefan shi. Habib juyo wa ya yi yana kallan Hassana, Habib jawo Hassana ya yi kusa da shi ya ce, "Mommy na nai manki, gashi ni kuma ba zan iya komawa yan zu ba sai dai gobe"."A'a ni dai ka tashi ka kai ni yan zu". Habib kuma jan Hassana ya yi ya ce kwanta mu yi bacci da sassafe zan kai ki".


Hassana da dama bacci ta ke ji tana kwanciya bacci ya kwasheta, Habib kuma ga ba d'aya ya kasa bacci, d'an k'aramin lips d'in Hassana ya k'ura ma ido, can dai ya kama lips d'in yana kissing. Hassana cikin bacci taji an rik'e bakin ta. Ta shi ta yi da sauri zata zauna, Habib ya yi saurin rik'ota ya ce, "Sanat please ki yarda yau mu zama d'aya mana ". Hassana ciku-cikun kwace kanta ta ke, amma ina abun ya ci tura".


Atak'aice
acikin daran Habib ya mai da Hassana ci kakar mace".



Asubar fari Habib ya tashi ya watsa ruwa, ya yi alwallah ya yi sallah, yana nan zau ne har aka kira Sallah, sai da gari ya yi haske sannan Habib ya tada Hassana, da kan shi ya tai maka mata ta kin tsa kanta".


Hassana na yin Sallah ta koma ta kwanta in da Habib ma ya kwanta rungume da Hassana suka koma wani baccin".


Kiran wayar Habib ce ta sa Habib ya tashi, Habib na d'agawa Hajiya Murja ta ce, "Habib kazo yan zu dan Allah ". Hajiya Murja ta fad'i maganar tana kuka". Habib ta shi ya yi ya shirya yana cikin shirin Hassana ta tashi tana son yi ma Habib magana ta kasa, dan ta ji wayar da ya yi da Hajiya Murja. Hassana ta shi ta yi ta nufi side d'in ta, tana zuwa da sauri ta shirya ta zauna Falo tana jiran Habib".


Habib zau ne ya iske Hassana a falo, Hassana ta shi ta yi ta rik'e hannun Habib tana mai kauda idonta, da kallan shi, dan sosai ta ji tana jin nau yin had'a ido da Habib d'in".


Habib kallan Hassana ya yi ya ce, "Sanat zaki bi ni ne? ". Hassana kai ta d'aga ma Habib". Habib kama hannun Hassana ya yi suka nufi asibitin da aka kwantar da Farida...... โœ๏ธ



Idan kin karanta daure ki Comment Sister ๐Ÿค



Share
&
Comment please ๐Ÿ™.


๐Ÿ“š OGA HABIB ๐Ÿ“š
๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ
*๐Ÿ…™๏ธŽARUMAI ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ WRITERS ๐Ÿ…๏ธŽSSOCIATION๐Ÿ“š๐Ÿ–Š๏ธ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa๐Ÿ’ช*_

*๐Ÿ’ซ(๐Ÿ…™๏ธŽ.๐Ÿ…ฆ๏ธŽ.๐Ÿ…๏ธŽ)๐Ÿ’ซ*

TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).



Albishirin ku masu bibiyar littafin Fadila Sani Bakori.
Yau gani da daddad'an albishir gare ku, insha Allah daga na kammala Oga Habib, zan nisha d'an tar da ku da sabon littafina wanda na baje basirata acikin shi. Anyi amfani da salo na birgewa acikin littafin. Labari ne wanda ya ke d'auke da madarar Soyayya, mai d'auke da ban al'ajabi. Inda ta wani b'angaran labarin ke d'auke da ban tausayi mai tsayawa a zuciyar makaranci. Duk yadda zan sanar daku ba zaku fahimta ba, ke dai karki bari abaki labari.
Zaki samu littafin akan farashi mai sauk'i da rahusa๐Ÿ‘Œ๐Ÿ‘Œ.
Summary.
Abba tin ina yaro kana yawan fad'a min, duk abinda ya yi tsanani yana tare da sauk'i. Shin ni sai yau she sauk'i na zai zo! ?. Abba me yasa muta ne basa ganina, maganata kawai su ke ji!?.Abba me yasa muke rayuwa a daji mai makon cikin gari cikin mutane !?.
Abba kana gani Husna zata aure ni, duk da halin da nake ci!?.
Abba me yasa Husna ta kasan ce ita kad'ai ke ganina!?. Abba kace kai ba Mahaifinsa bane, tom waye Mahaifina, kuma me yasa muke rayuwa a jeji!?, Sannan me yasa Abdussalam kad'ai ke zuwa gurin mu, sannan Abba waye Abdussalam ?.
Haidar duk banda amso shin tambayoyin ka, nima ban san kai na ba Haidar, ban san waye ni ba, bare kuma kai!.
Labari mai tab'a zuciyar mai karatu.

Paid book

Akan farashi mai sauk'i da rahusa ๐Ÿ‘Œ๐Ÿ‘Œ

VIP group 300 Only๐Ÿ‘Œ , normal kuma 200 ne, zaki yi transfer ta account d'in nan 2111619333.
Account name Fadila Sani.
Bank Name Zenith bank.
Dan nai man k'arin bayani zaki iya managa ta wannan Number๐Ÿ‘‰ 08063830828


Shafi na 90&91.



Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Sanat za ki bi ni ne? ". Hassana kai ta d'aga ma Habib. Habib kama hannun Hassana ya yi suka nufi asibitin da aka kwantar da Farida".


Habib na rik'e da hannun Hassana su shiga d'akin da aka kwantar da Farida. Lokacin Hajiya Turai bata nan ta ta fi kiran likita ya duba Farida ganin yadda ta ke ta aman jini, Habib da Hassana da sauri suka k'arasa in da Farida ta ke. Habib cikin tausayin Farida ya ce, "Sannu Farida". Farida ko da ta ji Muryar Habib kamar a mafarki, cikin rauni irin na marasa lafiya Farida ta rik'a lalibar Habib. Hassana ganin haka da sauri ta rik'o hannun Farida. Farida ko a tunaninta Habib ne ya rik'e ma ta hannu".



Farida cikin dauriya da jarumta ta fara magana kamar haka, "Oga Habib ko da Mommy'na ta ce min zaka auran ban yarda ba, duk da ka fad'a aga bana, tabbas kai d'in raban Hassana ce, Hassana ta kasan ce mai sa'a arayuwa, Oga Habib ina ji ajikina mutuwa zan yi sonka shi zai zama sanadin ajalina, zan sanar da kai abin da baka sani ba ayau. Oga Habib ni ce nai silar auran ka da Hassana, na yi abubuwa da dama dan ganin ka zama miji agareni, amma ina abin bai yuwu ba". Farida shiru ta yi sabo da yadda taji numfashinta na fusgar mata, Farida sai da ta share wasu hawaye masu d'imi da ke zubar mata, sannan ta dafe gefan zuciyarta ta ci gaba da magana cikin kuka-kuka kamar haka, "Oga Habib ni ce sanadin haukarka, na yi haka ne ko zaka zama miji a wajena, amma da ya ke kai d'in ba rabo na bane, sai abin ya fad'a ma Hassana, mai makon karik'a yaddar da ni ni ka d'ai kamar yadda naso, sai ya zama mana da Hassana ka d'ai ka ke yadda,
Inda tunanina ya bani, idan ya kasan ce dani ka d'ai ka ke yarda na san kowa zai yi tunanin had'a ni aure da kai, tom abin sai ya fad'a akan Hassana". Nan ma Farida shiru ta yi sannan ta ci gaba da cewa, "Oga Habib duk da Mommy ta had'a auranka da Hassana ban yi hak'uri ba nayi abubuwa da yawa ganin na raba auranka da Hassana, shima bai yuwu ba, na tura b'arayi akan su d'auke Hassana shima bai yuwu ba. Shi ne nayi tunanin fara aiki a Sanat ko zan ja hankalinka".kukan da ya k'wace ma Farida ne ya sa tai shiru, sai da tai kukanta ta gama sannan, ta ci gaba da cewa, nayi k'ok'ari sosai ganin na ta kurama Hassana".


Farida kuma rik'e hannun Hassana ta yi d'ayan kuma ta dafe saitin zuciyar ta, da ta ke tunanin hannun Habib ne ta ci gaba da cewa, " Oga Habib kai da Hassana ku yafe min dan.....". Tarin da Farida ke yi ne, mai tattare da aman jini ya hana ta fad'in abin da ta ke so".


Allah sarki Hassana da tausan Farida ya kamata kuka ta kama, dai-dai lokacin kuma Hajiya Murja ta shigo da likita".

Wata doguwar Hajiyar zuciya Farida ta ja, daga nan tarin ya lafa. Likitan duba Farida ya yi, sannan ya kalli Hajiya Murja ya ce, "Hajiya Allah ya yi ma mata rasuwa!? Ihu d'aya Hajiya Murja ta yi ta yanke jiki ta fad'i".


Ita kanta Hassana kuka ta fasa,cikin rud'ewa ta ke "Innalilahi'wa inna ilaihirraju'un! ". Habib rasa yadda zai yi da Hassana ya yi, ganin ta rud'e da yawa, ga kuma Hajiya Murja a sume".


Habib waya ya ciro ya kira Hajiya Turai, tana d'agawa Habib ya sanar da ita mutuwar Farida yan zu haka suna asibitin. Ai Hajiya Turai bata gama saurara ba ta kashe wayar".


Cikin minti goma Hajiya Turai ta iso asibitin, tana zuwa lokacin kuma dai-dai za atai da gawar Farida gida, haka aka tafi da gawar Farida gida, da Hajiya Murja keta rusa kuka tana kiran ta bani ta shiga uku, wa'iyazubiiya, Innalmaiyata layu'azibi bibika'ilhai, lallai mamaci ina masa azaba da kukan Wanda ya ke da rai. Allah ka ki ya ye mu kasa mu dace".



Haka akai zana'idar Farida aka kaita gidan ta na gaskiya. Sai da aka gama komai sannan Habib ya d'auki Hajiya Turai da Hassana suka koma gidan Hajiya Turai ".


Hassana da zazzab'i ke damunta tun acan daurewa ka wai ta ke, suna zuwa ta kwanta kan Three seater Falon Hajiya Turai, Habib kallan Hajiya Turai ya yi, ya ce, "Mommy Sanat fa bata ci komai ba".Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Daughter me zaki ci? "."Mommy tea ". Hajiya Turai Maimuna tasa ta had'ama Hassana tea ta kawo mata. Habib buga k'afar Hassana ya yi kad'an ya ce, "Tashi ki sha tea d'in ". Hassana tashi tai dama kuma yunwa ta ke ji, dan ma d'azu Habib ya kaita wani restaurant ta ci abinci. Hassana amsar tea d'in ta yi ahankaki-ahankali ta samu ta shanye tea d'in".



Hajiya Turai kallan Habib ta yi, ta ce, "Habib ina son ka yafe ma Farida dan ta aikaita abubuwa masu girma gareka, ban yi niyyar sanar da kai ba, amma zan fad'a maka sabo da nai man mata yafiya da zan yi". Habib kallan Hajiya Turai ya yi ya ce, "Mommy duk abin da kike son sanar da ni Farida ta sanar da ni da kan ta, shine ma maganar ta ta k'arshe. Tabbas alokacin da take sanar da ni abin da tai min raina ya b'ace sosai, amma kuma bayan mutuwar ta sai naji tausan ta, na yafe mata Mommy Allah ya yafe mana baki d'aya ". 'Ameen". Hajiya Turai ta ce".


Hajiya Turai ta shi ta yi ta nufi ciki ta watsa ruwa. Habib ko naganin Hajiya Turai ta tashi ya bubbuga Hassana ya ce, "Sanat tashi mu tafi kafin Mommy tazo please ". Hassana kafad'a ta mak'ema Habib ta ce, "Naki d'in, Habib tada Hassana ya yi zau ne, ya ce, "Sanat dan Allah kin san tun jiya Mommy ta so in dawo da ke, tom yan zu idan ta fito ta kangi Allah na san ba zata bari ba mu tafi". Hassana kwanciya ta yi kan kafad'ar Habib ta ce, " Ni kam yau ba zan bika ba". Habib da ke jin tsoran kar Hajiya Turai ta fito, tashi ya yi yana tada Hassana ya ce, "Sanat ki tashi mana, kar Mommy ta zo".Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Ni fa ba zan bika ba". Habib da fe kai ya yi, ya ce, "Sanat kizo muje ina son muyi maganar tafiyar ki garin ku ne". Hassana cikin jin dad'i ta kalli Habib ta ce, "Allah da gaske kake? ". Kai Habib ya d'aga ma Hassana.
Hassana tashi tai suka tafi".


Bayan su Hassana sun tafi ne Hajiya Turai ta fito falon tan bayar Habib shi mai zai ci. Amma abin mamaki Hajiya Turai bata ga kowa ba.

Please Login or Register in order to submit comment