Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gobe d'aurin auran teacher Kabir da Usaina na gudu saboda zuciyata bazata iya jure ganin auran teacher Kabir da wata ba, ba ni ba............




idan dai kin karanta daure ki yi Comment 'yar'u.



More comment more typing 🖊
📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

Abokai na gaskiya suna da wuyar samu, suna da wuyar bari, suna da wuyar mantawa. Allah ka had'amu da abokai na gaskiya.


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

My Facebook group Fadila Sani.
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/


Shafi na 8&9.




Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, Oga Habib, wannan shine dalilin da ya sa, nahad'a kayana dadaddare na gudu, batare da kowa na gidanmu ya sani ba. Koda na fita gida lokacin duhu ya yi sosai. Tafiya nake amma ban san ina zani ba, ga duhun dare ya farayi, gashi tsakaninmu da titi akwai nisa sosai, haka na kama hanya ina tafiya ina sauri ga damuwa da tayi min yawa, ga yunwa rabona da abinci harna manta, sai dai in naji yunwa ta daman in dama kunu insha. Damuwa da yunwa da gajiyar da na yi ce, tasa na yanke jiki na fad'i ban sani ba, shine kuka tsinceni ainda kuka gani". Hassana kallan Habib ta yi, ganin har yanzu bai fasa typing d'in da ya ke yi ba. Ita fa gani ta ke kamarma duk surutannan tana yin shine kawai amma bajinta ya ke ba. Hassana kallan Habib ta kuma yi, cikin fargaba ta ce, "Oga Habib Wannan shine da lilin barina gidanmu". Hassana ta yi maganar da dad'ewa , dan hattacire ran Habib zai bata amsa ma.Sannan zuwa can ya d'ago kai yana kallanta, sai da Habib ya gama yima Hassana kallan cin mutunci sannan ya ce, "ya sunan ki ma kika ce? ". Hassana bakinta harrawa ya ke wajan ba Oga Habib amsa da cewa, "Hassana".
Habib Kallanta ya yi, ya ce, "Hassana ke ba abin tausai ba ce, idan ke abin tausai cema tom ni ban tausaya miki ba, kuma ni bazan tai makeki ba. Duk wadda ta gudu daga gidan Iyayanta tom yawan bariki ta fito, dan haka fitar min daga office ". Habib ya fad'i maganar cikin d'aga murya. Jikin Hassana rawa ya farayi dan sosai ta tsorata da Habib.
Hassana kuka ta farayi, cikin muryar kuka ta ce, "Oga Habib dan Allah ka yi hak'uri, Wallahi bayawan bariki na fito yi ba, kona zauna gidan b........ ". Tsawar da Habib ya yi ma Hassana ce tasa ta yi shiru.
Habib nuna mata hanyar fita ya yi da hannu, ya ce, "fitar min daga Office na ce, stupid kawai! ".
Hassana da saurin ta har tana d'an tintib'e ta fita daga office d'in. Saura kad'an Hassana su yi karo da Bilya shi kuma lokacin yazo shigowa.
Bilya da d'an damuwa ya bita da kallo dan duk da bai san labarin yarinyar ba, sosai ta ke bashi tausai, acewar shi yarinya k'arama haka ace bata san ina zata ba. Bilya cikin tausan Hassana ya k'arasa office d'in Oga Habib.Bilya cikin girmawa, ya ce, "Barka da hutawa Oga Habib, ka yi hak'uri dan Allah ka kirani banzo da wuri ba, bana kusa ne".
Habib kallan Bilya ya yi, sannan ya ce,fuskar shi a d'aure, alamun ranshi ab'ace ya ke. "Bilya me yasa ka kai k'arata wajan Momyna". Habib ya yi maganar cikin d'aga murya, dan shi aganinshi bai kamata ace yaron shiba, wanda ya ke ci ak'ark'ashin shi ya zartar da hukunci akanshi ace ya kai k'ararsa wajan mahaifiyarsa ba.
Bilya cikin kame-kame ya ce, "Oga Habib ba...... ". Habib d'agama Bilya hannu ya yi, ya ce, "ka adana kala manka, amma kabar kama k'afa da son da Mahaifita kema, dan kar hakan yasa kaji zaka iya yin koma, wannan shine last worning da zanma, duk sanda ka sake ma hajiya complain akaina, daga ranar Bilya kabar aike a k'ark'ashin Sanat yoghurt". Habib na fad'in haka ya kalli Bilya, ya ce, " Bilya da kai da Baba Lami na baku, suspension na one month". Bilya da alamun tsoro ya d'ago kai yana kallan Habib, jin wai ya da katar da shi har wata d'aya.Bilya magana zai yi Habib ya nuna mai hanyar fita.
Fita Bilya ya yi, batare da yace ko mai ba. Bilya na fita ya iske Hassana can bakin get d'in wajan tsaye, ta yi shiru ita kad'ai. Bilya gurinta ya k'arasa, kallanta ya yi sannan ya ce, "korarki ya yi ko? ". Hassana kai ta d'agama Bilya.
Bilya shiru ya yi sannan, ya ce, " Ni Wallahi duk namarasa abinda zance miki, ni kaina yanzu haka ya dakatar dani aiki harna tsawan wata d'aya, ga aurena saura wata biyu masu zuwa, ni kaina yanzu kinga in da munyi haka dashi ba damar in kwana gidansu sai dai in koma d'akin abokina da kwana. Tom kuma itama Baba Lami bata san kowa ba a Abuja, kuma kinga ya dakatar da ita aiki itama, yanzu na san sai dai ta koma garinsu. Bilya shiru ya yi, yana tunanin yadda zai yi da Hassana amma bai sani ba,hakan yasa, ya ce, "Hassana ni yanzu ma kaduna zan tafi, ki zauna nan anjima kad'an zaki ga manager ya fito, zaki ganshi da red d'in shirt da black jeans. Ki mai magana, in dai ya amince ya d'auke ki aiki shikenan, Oga Habib babu ruwansa da d'aukar ma aikata".
Hassana kallan Bilya ta yi, ta ce, "Tom Oga Bilya, wajan kwana fa?, in ya d'aukeni aikin? ".
Shiru Bilya ya yi dan shi yama manta da wajan kwana sai yanzu ya tuna. Bilya kallan Hassana ya yi, ya ce, "Hassana ki ci gaba da zama nan, idan kika ga Oga Habib ya fito, ki je ki sa ke rok'anshi, k'ila ya amince". Bilya na kaiwa nan, ya yi ma Hassana fatan alkairi ya tafi.
Hassana cigaba da zama ta yi kamar yadda Bilya ya ce mata, tana jiran fitowar Oga Habib. Hassana har 8:00pm tana gun zaune, tana jiran taga fitowar Oga Habib amma shiru, Hassana tunini ta rik'ayi k'ilama ya tafi bata sani ba, inda ta je sallah. Wata zuciyar ta ce mata, tom idan ko haka ne ina zata kwana,uhm tom wai in ma naganshi lallene ya taimakan d'in. Hassana na cikin wannan tunanin taga motar Oga Habib ta fito. Hassana da saurinta har tana tuntub'e ta matsa wajan motar Habib d'in, shikuma lokacin ya tsaya yana ma mai gadin gun magana.
Hassana ko kafin tak'arasa Habib ya yi ma motar shi key. Hassana tsabar furgici da rashin sanin yadda za tayi, kawai sai ta zauna gun tana kuka.
Hassana na nan zaune tana kuka kamar wata ta b'abb'a, manager gun ya fito domin tafiya gida. Tsayawa ya yi ganin mutum a zaune, kuma bisa ga alama kamar kuka ya ke ji. Tsayawa manager ya yi ya fito daga motarshi, inda Hassana ta ke zaune tana kuka ya k'arasa. Tsananin hasken gun yasa tun kafin ya k'arasa ya k'are mata kallo. Kallanta ya yi da kyau sannan cikin siririyar muryar shi ya ce, "ke lafiya?, zaki zo nan ki zauna da daddarannan? ". Hassana da sauri ta d'ago kanta tana kallan manager. Manager ko jin Hassana ta yi shiru tana kallan shi, ya sa ya k'ara cewa, ", ke bakya ji ne! ? ". Ad'an tsawace ya yi maganar.
Hassana kallan Manager ta yi, cikin muryar kuka ta ce, "Bansan ina zani ba ne". Manager da mamaki ya kalli Hassana, ya ce, "kamar ya baki san ina zaki ba?, tom waya kawoki nan? ".
Hassana kai tsaye batare da tunanin komai ba, ta ce, "Oga Habib ne ya tsinceni shida Oga Bilya, shine ya kawo ni nan, ni kuma bansan kowa ba a Abuja, kuma ya hana in sake zuwa mai gida". Hassana ta idasa maganar cikin kuka.
Manager shiru ya yi yana mai ci gaba da kallan Hassana, dan shi gaba d'aya bai gane takan maganarta ba. Manager waya ya ciro ya kira Oga Habib.
Kira d'aya Habib ya d'aga yana tambayar manager lafiya, dan manager bai cika kiran shi airin wannan lokacin ba.
Manager ko Habib na d'agawa ya ce, "M. D. Dama wata Yarinya ce nan na gani wajan get zaune tana kuka, shine dana tambayeta ta ce min wai kaika kawota, ni dai gata nan bama wai gane kan zancan nata nayi ba".
Habib ba tare da tunani wata yarinya ba ce, dan in yaga dama yanada girki. Habib shiru ya yi sannan ya ce, "Manager kawo ta nan gida". Habib na cewa haka ya kashe wayarshi.
Manager ko kallan Hassana ya yi, ya ce, "zo mu je". Hassana motar manager ta shiga. Manager gidan Habib ya kai Hassana kamar yadda Habib ya ce mai, ya kawo ta.Daya ke duk masu gadin gidan sun san Manager hakan yasa suna ganin shi suka bud'e mai get d'in ya shiga. Manager direct falon Oga Habib ya nufa, Hassana na biye da shi, sai kalle-kalle ta ke. Hassana azuciyarta ta ce, "Tabbas dole Oga Habib ya yi wulak'anci, ga kyau, ga kud'i, ga ilimi". Manager ko da ya je bakin k'ofar Habib nocking ya yi.
Kasan cewar Habib ya san manager ne ya sa, ya ce, "yashigo".
Manager shiga ya yi, da Hassana da ke biye da shi.
Hassana sosai ta rud'e da had'uwa irin ta falon Oga Habib. Ko mai na falon milk & Orange ne.
Habib ko kallo d'aya ya yi ma Hassana ya gane ta. Hakan yasa cikin d'an fad'a ya ce, "Manage dama wannan yarinyar ce? ". Manager cikin girmamawa ya ce, "M. D, ita ce".
Habib kallan manager ya yi ya ce, "Manager me za ayi mata? ". "Tom M. D, nima dai ban sani ba, amma idan na fahimce ta kamar bata da wajan zama ne". Manager kallan Hassana ya yi, ya ce, "Dame za a tai maka miki? ". Hassana cikin sanyin muryarta mai cike da rauni ta ce, "Dan Allah aiki nake so kuban, sai kuma gurin da zan rik'a kwana". Manager kallan Oga Habib ya yi, sai yaga Habib ya d'auke idon shi akan shi. Hakan yasa manager ya ce, "Shikenan za ki rik'a mana swapping & mopping, morning &evening , zaki iya?" Manager ya kalli Hassana yana tambayarta.
"Eh zan iya ". Cewar Hassana.
Manager batare da tambayar Habib ba dan yasan in dai ya ce Habib zai tambaya, tom ba abin cewa zai yi ba, amma in ko ya riga ya yanke hukunci ya san sai dai ya yi mai tsiya daga baya. Hakan yasa manager ya ce, "Shikenan wajan kwana kuma sai ki rik'a kwana site d'in 'yan aikin gidan nan". Hassana cikin jin dad'in abin Manager ya ce, ta ce, "Nagode sosai, Allah ya saka maka da alkairi ". "Ameen". cewar manager. Manager Kallan Habib ya yi jin bai ce komai ba, hakan yasa manager Kallan Hassana ya ce, "Biyo ni in nuna miki site d'in worker's d'in gidan.
Shi dai Habib na jin manager bai ce mai ko mai ba. Haka manager da kan shi ya kai Hassana b'angaran masu aikin gidan. Bayan ya kaita ne, ya koma yima Oga Habib sallama.
Habib kallan manager ya yi, ya ce, "Manager ya zama First and last, ban hanaka d'aukar staff ba a company, amma ba dai zama nan ba, dan duk wata worker da ka gani agidan nan, Hajiya kawai suke ma aiki, amma ba Company ba". Manager hak'uri ya ba Habib, sannan ya ce, "Insha Allah, M. D, haka ba zai kuma faruwa ba, wannan ma tausai ta ban, ganinta mace bahaushiya da nayi, kuma daga ganinta tana buk'atar tai mako, amma ka yi hak'uri ". Banza Habib ya yi da shi.
Manager tafi ya yi, dan ya san fushin kafin gobe ne, Oga Habib akwai saurin fushi, amma kuma baida wuyar sauka.
Hassana ko da ta k'arasa b'angaran masu aikin, cikin girmawa ta gaida su, sai dai duk kansu wani irin kallo suke ma Hassana.Hassana cikin tsarguwa da kallan da suke mata ta gaidasu,.
D'aya daga cikin su ce, ta ce, ma Hassana, "Baiwar Allah daga ina? ". "Nima ma aika ciyace kamar ku, sai dai ni ba acikin gidan nan zan rik'a aiki ba, a Sanat yoghurt zan rik'a aikina". Da mamaki dukkan su suka kalli Hassana, dan su aiya saninsu 'yan aikin gidannan ne kawai Hajiya turai ta yadda da su zauna anan. Wata wadda ake kira Jimmai daga cikin su, kallan Hassana ta yi, ta ce, "Baiwar Allah waye ya kawo ki gidannan? ". "Oga Habib". Hassana ta basu amsa kai tsaye , dan ta gaji da tambayoyin da su ke mata. Hassana guri ta samu d'an nesa da su ta kwanta, dan ta gaji sosai dan ma Allah ya tai maketa ta yi sallarta.
Hassana kallan ma'aikatan gidan ta ke tana mamakin tom aikin me sukeyi haka, suke da yawa. Hassana kwanciya ta yi, tana kwanciya bacci ya d'auketa. Ma'aikatan gidan Hajiya turai sun sabo tun k'arfe shida na safe kowa ke tashi ya yi aikin da ya ke mazaunin nata. Hassana ko saboda gajiya kasa tashi ta yi.
Jimmai wadda ta ke kusan sa'a da Hassana zuwa ta yi, ta bubbuga Hasana da ke kwance tana baccin gajiya. Hassana bud'e ido ta yi tana kallan jimmai.
Jimmai ma kallan Hassana ta yi, ta ce, Baiwar Allah ki tashi hakanan, ki yi sallah mana.
Hassana tashi ta yi tana kallan jimmai, ta ce, "Dan Allah ina make wayinku? ". Jimmai hannun Hassana ta kama ta ce, "muje in kai ki.
Jimmai har toilet d'in su na ma'aikatan gidan ta kai Hassana sannan ta juyo ta dawo. Hassana da sauri ta yi sallah sannan ta kalli jimmai ta ce, "Dan Allah idan zani Sanat yoghurt, idan zan hau keke napep ina zan ce? ". Jimmai kallan Hassana ta yi, ta ce, "amma dai ke ba 'yar garinnan ba ce ko? ". "Eh ni ba 'yar nan ba ce ". "Ok, in kin samu keke napep ki ce zone, e nepar Sanat yoghurt duk wanda ya ke garin Abuja ai yasan sanat yughurt, za akaiki, har Sanat yoghurt. Hassana godiya ta yi ma Jimmai sannan ta kalli jimmai ta ce, "Dan Allah ko zaki ranta min kud'in keke napep d'in zan bi yaki, wallahi banda ko sisi". Jimmai kallan Hassana ta yi da tausayawa ta ce, "Nawa zan baki? ". "Nawa su ke kaiwa? ". Hassana ta tambayi jimmai.
Jimmai d'ari biyu ta ba Hassana ta ce, "Gashi D'ari biyu ne ai ba nisa". Hassana amsa ta yi taima Jimmai godiya. Hassana har ta juya zata tafi Jimmai ta kirata ta ce, "Ba dai da kayan jikinki zaki tafi ba ko? ". Jimmai ta tambayi Hassana ganin kamar da kayan jikinta zata tafi.Hassana kallan Jimmai ta yi, ta ce, "Banda kaya haka nazo ni kad'ai ". Jimmai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Ya su nan ki ne?, kuma dan Allah ko zan iya sanin labarinki". Hassana ji tai zuciyarta ta aminta da Jimmai hakan yasa ta ce, "Sunana Hassana, kallo d'aya nai miki sai naji zuciyata ta aminta da ke, dan haka zan baki labarina amma ba yanzu ba, yanzu ina sauri zan tafi". Hassana na kaiwa haka ta juya zata tafi. Da sauri Jimmai ta kamo hannun Hassana ta ce, "Duk da baki ne mi sanin Sunana ba, Sunana Jimmai, idan ba zaki damuba kirik'a sa kayana kafin ki samu naki". Hassana sosai ta ji dad'in abinda jimmai tai mata, dama sosai ta ke jin kunyar fita da kayan jikinta dan sunyi datti sosai.
Jimmai ko ta kurama Hassana ta yi tai wanka ta yi break fast sannan tata fi.
Lokacin da Hassana ta isa sanart yoghurt, lokacin k'arfe goma na safe, ita da aikinta sharane da goge-goge su da ake buk'atar su je da wuri kafin kowa ya je dan su yi aikinsu. Hassana na shiga gurin ta na cin karo da manager. Sosai Manager ya yi ma Hassana fad'a akan zuwanta lale da ta yi, bayan yagama yi mata fad'ane ya mik'ama mata file d'in hannun shi, ya ce, ta kai Office d'in Oga Habib.
Hassana tsayawa ta yi, tana kallan file d'in, sannan manager ad'an tsawace ganin bata amsa ba, ya ce, "Ki amsa mana ki kaima Oga Habib, ki ce mai ya yi marking d'in abubun da muke buk'ata ". Hassana amsa ta yi dan bata da yadda zata yi, amma bata so har ta gama aiki agurinba ta kuma shiga office d'in Oga Habib. Hassana cikin sanyinta ta tura k'ofar office d'in Habib ta shiga.
Habib ko alokacin ya na kishingid'e kan sit, ya ji anturo k'ofar Office d'in shi an shigo.... ............











PLEASE
COMMENT &
SHARE.
📚OGA HABIB📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

Mak'iyanka mutane uku ne:Mai k'in ka, da mai k'in masoyinka, da mai son mak'iyinka. Mai son uwa dole ne ya so d'anta. Allah ka had'amu da masu son mu fisabilillahi.

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK'R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D'AN TARKU DA HAZIK'AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD'UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K'AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK'E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K'OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN 👇🏻
K'ABILA CE! K'ABILA CE!! K'ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K'ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA ZA A FARA POSTING.
KI GARZA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D'AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K'ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT 👇🏻
08142904255.



Shafi na 10&11




Habib da kallo ya bi Hassana da shi.
Hassana ko cikin da burcewa da kallan da ya ke mata, ya sa ta mik'a mai file d'in hannunta, ta ce, "Oga Habib ga shi inji manager ya ce ka yi marking d'in abubun da ake buk'ata". Hassana ta idasa maganar muryarta na rawa.
Habib amsar file d'in ya yi, batare da ya kalli ko inda ta ke. Habib na amsar file d'in Hassana ta juya da saurinta tafita office d'in.
Hassana na fita office d'in Habib ta had'u da wata staff itama agun ta ke aiki, amma ita tana cin masu programme d'in sanat yoghurt. Hassana da sauri ta k'arasa gunta ta ce, "Baiwar Allah dan Allah tambaya na ke? ". Wadda Hassana ta kira da ke, juyowa ta yi tana ma Hassana wani kallan lafiya.
Hassana itama kallanta ta yi, azuciyarta ta ce, kai gaskiya 'yan aikin gunnan suncika ji da kai, sai kace wasu masu aikin banking. Ita ko staff d'in nan jin Hassana ba ta ce mata ko mai ba, ya sa juya ta cigaba da tafiyarya zuwa inda zata. Hassana ganin ta tafi ta barta gun tsaye da sauri tasha gabanta, ta ce, "Yi hak'uri dan Allah office d'in manager na ke nema? ". Wani irin kallo ta ke ma Hassana dan ita bata tab'a ganin Hassana ba a ma'aikatar nan ba. Hakan yasa ta kalli Hassana ta ce, "Wacece ke? ". Hassana batare da tadamu da irin kallan da ta ke mata ba, ta ce, "Ni new worker ce a factory nan". Da hannu ta nuna mata office d'in manager ta juya tayi tafiyarya. Hassana ko kanta a k'asa ta juya ta nufi office d'in manager. Hassana na zuwa cikin girmamawa ta gaida manager dan tana ganin girmansa sosai, tai makon da ya yi mata. Hassana kallan manager ta yi, ta ce, "Oga Manager dama bansan site d'in da zan rik'a mopping bane". Manager kallan Hassana ya yi, ya ce, " supervisor zaki ma magana. Ki ji Office d'in kusa da nawa ita zata fad'a miki site d'in da zaki rik'a morpping d'in". Hassana fita ta yi daga Office d'in manager ta shiga office d'in ku sa da na shi.
KyKkyawar budurwa ce, a ganinda nai mata baza ta wuce twenty five years ba. Zaune ta ke tana ta aikin dan na laptop d'in da ke gabanta. Hassana cikin girmamawa ta ce, "Barka da aiki Aunty". Da sauri Billy ta d'ago tana kallan Hassana jin sunan da ta kirata da shi. Cikin b'acin rai Billy ta ce, dan ita jin kanta ta ke kamar wata 'yar seventeen years. Hakan yasa cikin d'aga murya Billy ta ce, "Uwar ki ce Aunty ".dan ita aganinta Hassana kallan girma tai mata shiyasa ta kirata da Aunty.
Ita ko Hassana girmamata ta yi.
Hassana cikin girmawa ta ce, "Yi hak'uri dan Allah, ban sanda sunan da zan kiraki da shi bane, shiyasa". Billy kallan Hassana ta yi, ta ce, "me ki ki so? ". "Ni sabuwar ma aikaciyarku ce, Oga manager ne ya d'aukan aiki zan rik'a shara da goge-goge, shine Manager ya ce inzo Office d'in ki, ke ce zaki fad'amin b'angaran da zan rik'a sharewa da gogewa".Billy kallan Hassana ta yi, ta ce, "Ai muna da 'yan mopping da yawa, amma inda ya riga ya d'auke ki, ki rik'a mopping d'in site d'in da engine su ke, amma fa dole zaki rik'a zuwa da wuri". Hassana kallan ta ta yi, ta ce, "Aunty ai bansan site d'in ba". "Ki samu wata staff d'in ki tambayeta zata nuna miki". Hassana godiya ta yi mata ta juya zata tafi.Hassana ta na fitowa daga Office d'in supervisor ta had'u da wani staff da suka had'u jiya. Cikin zakin fuska da washema Hassana baki, yak'araso inda Hassana ta ke. Kallan Hassana ya yi, ya ce, " 'Yan mata ina fatan dai kin samu aiki". Hassana cikin sakin fuska itama ta bashi amsa, ta ce, "Eh Wallahi na samu". "Kai amma nai miki murna, kina cikin masu programme d'in sanat yoghurt ko? ". Hassana kai ta girgiza mai ta ce, "Ni aikina sharane da goge- goge". "Ok, karki damu wata rana zaki zamama d'aya daga cikinmu, wasinmu duk daga haka suka fara, kin san dai aikin Company sai nada hak'uri, dan haka ki yi hak'uri ba kamar da supervisor d'in mu ba".Hassana kallan shi ta yi, ta ce, "Dan Allah inane site d'in ku d'in can ne b'angaran da ta ban aikin". Staff d'in nan da mamaki ya kalli Hassana, ya ce, "Kai, kin sanfa da yake batada hankali taba masu sharar gun suspension, gaskiya gun ya yi miki yawa ke kad'ai. Amma kinga yanzu ke new worker ce be kamata ki fara kai complain tun yanzu ba, amma daga kin yi one week ina yi bata dawo da wa inda ta ba suspension ba, tom ki kai ma manager complain akan haka". Hassana godiya ta yi, mai sannan suka jera ya je ya nuna mata inda zata rik'a sharewa da gogewa, duk Hassana ta saba aikin wahala agida amma tasan wannan gun yafi k'arfin sharar mutum d'aya. Hakan yasa Hassana ta kalli staff d'in da ya rakora gun ta ce, mai"gaskiya gunnan ya yi min girma, bazan iya shareshi da goge shi ba ni kad'ai ba". Kallan Hassana wannan staff d'in ya yi sannan ya ce, "Gaskiya sai dai ki yi hak'urin kwana ko biyu ne tukun nan, dan kinga wa inda ta dakatarma jiya su biyu daga sun mata magana akan tak'aro masu wasu gun ya yi masu yawa su kad'ai, shikenan wai su je gida su huta na

Please Login or Register in order to submit comment