Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba kowa, duk 'yan aikin gidan sun shi cikin gida, hakan yasa tana fitowa daga mota Bilya yaja hannunta da sauri ya kaita d'akin shi. Dan yasan gidan cike ya ke da magulmata.
Bilya dama tun kafin ya iso ya kira Baba lami ya yi mata bayanin ko mai, hakan yasa Bilya na isowa ya kira Baba Lami ya sanar da ita sun iso.
Baba lami na shiga d'akin Bilya.
Bilya ya kalleta ya ce, "Tom Baba kin san dai yadda gidan nan ya ke, Baba lami ga Yarinyar nan, dan Allah ta zauna gunki kafin Hajiya turai ta dawo".
Baba lami batare da taima Bilya magana ba, gudun matsala dan ba wani lokaci sosai,Baba Lami taja hannun 'Yar tsuntuwar ta yi d'akinta da ita da sauri.
Bayan sun shiga d'akine Baba Lami ta kalli Matashiyar budurwar ta ce, " 'Yan mata ya sunan ki? ". Cikin sanyin murya ta ce, "Sunana Hassana".
"Yauwa Hassana dan Allah ki yi zamanki nan, karkisake ki fita waje, muta nan gidan nan magulmata ne, dan Allah ki kula, kafin Bilya ya samarmiki gurin zama".
Sosai Baba Lami ke k'ok'arin b'oye Hassana.
Sai dai kash abinda Baba bata sani ba, aminiyarta wadda su ke aiki tare da ita da kanta ta kira Hajiya turai ta kai gulmar Lami ta kawo wata bak'uwar yarinya agidan, kuma abisa lurar da ta yi, Bilya ne zazo da Yarinyar ya ba Baba Lami ita".
Hajiya turai ko, sosai hakan yab'ata mata rai, acewar ta ba laifin Bilya ba ne, lafin Oga Habib ne, saboda shi ya ba Bilya damar shigowa kai tsaye gidan.
Hajiya turai ranta ad'an b'ace takira Habib awaya.
Habib ko lokacin yana zaune a office d'in shi na SANAT YOGHURT, kiran Mahaifiyar shi abin soyuwa a zuciyar, ya shigo wayar shi
Habib cikin kirarin da ya saba yi ma Mommy shi, ya d'aga kiran ya ce, "Sai Mommyna ni kad'ai Allah ya k'arami lafiya, lafiya dai ko wannan kira haka a wannan lokacin? ".
Hajiya turai cikin basar da zancen Habib d'in ta ce, "Habib wacece ta ke zaune a gida".
Habib cikin rashin fahimtar abinda Mahaifiyarta shi ta ce,ya ce, "Mommyna bangane maganarki ba". "Habib za kai min maganarta ka ko ta banza, tom wacece aka ce min Bilya ya kawo gidan da zama?, Habib ni fa ina tsoran abinda ya faru ne ya sake faruwa".
Habib cikin kwantar ma Mahaifiyar shi hankali, dan yaga alamar ta tsorata sosai da abinda ya faru Kwanakin baya.
Habib cikin sanyin muryar shi, ya ce, "Mommyna Allah ban san da zaman kowa ba, amma ki bari zan yi bincike yanzu".
Hajiya turai kashe wayarta ta yi.
Habib ko Mahaifiyar shi na kashe kiran, ya kira Number Bilya. Bilya na d'agawa Habib ya ce, "Bilya da kai da wadda ka kawo da kuma wadda ka ba ajiyarta, kuzo yanzu".
Cikin bilya sai da ya yi k'ara jin abinda Habib ya ce, hakan yasa da sauri ya bar SANAT YOGHURT, ya koma can gidan Habib d'in.
Bilya tun kafin ya isa yakira Baba Lami awaya ya ce su had'u wajan get harda Yarinyar da yabata ajiya.
Bilya na zuwa suka ya iske Baba da Hassana wajan get d'in suna jiranshi.
Bilya kallan Baba ya yi, ya ce, "Baba Wallahi ban tab'a ganin muna fukai ba kamar 'yan aikin gidannan ba, yanzu wai har an samu wanda ya kaima Oga Habib gulmar zaman Yarinyar nan agidannan, yanzu haka yana nai manmu mu dukanmu".
Baba lami dafe k'irji ta yi, ta ce, "Bilya kasan Allah yaron nan korarmu zai yi".
Bilya kallan Baba Lami ya yi, ya ce, "Baba ni ba abinda ke damuna ba yanzu kenan".
Bilya a motar shi ya d'auki su Baba, zuwa SANAT YOGHURT.
Koda suka shiga wajan Hassana kallan sunan da ke d'auke da tank'ameman Company ta ke, da kuma tsaruwa irin ta gurin, ko ina 'yan akine sanye da Uniform d'in su green and orange .
kasan cewar Habib ya san da zuwan su Bilya , hakan yasa kai tsaye suka shiga tank'ameman Office d'in Oga Habib.
Habib na zaune yana ta aikinsa a laptop d'in shi, yana jin su Bilya amma yaci gaba da aikinshi. Habib sai da yagama abinda ya ke yi, sannan ya d'ago kai yana kallan su d'aya bayan d'aya.
Habib mai da kallan shi ga Bilya ya yi, ya ce.......................




Labari ne mai cike da CAKWAKIYA, ku dai ku bini asannu zaku fahimce ni nan gaba kad'an๐Ÿค



DUk mai son kasan cewa a group d'in Oga Habib.Tom Comment dole ne 'Yar'uwa.


In kinkaranta daure ki Comment.

COMMENT PLEASE ๐Ÿ™
๐Ÿ“š OGA HABIB ๐Ÿ“š
๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ
*๐Ÿ…™๏ธŽARUMAI ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ WRITERS ๐Ÿ…๏ธŽSSOCIATION๐Ÿ“š๐Ÿ–Š๏ธ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa๐Ÿ’ช*_

*๐Ÿ’ซ(๐Ÿ…™๏ธŽ.๐Ÿ…ฆ๏ธŽ.๐Ÿ…๏ธŽ)๐Ÿ’ซ*

RUBUTWA DA TSARAWA
FADILA SANI BAKORI(Faddy baby).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
My Facebook group:Fadila SANI
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

Ba kowane lokaci ne mutane za su fahimce ka ba. K'aramar k'wak'walwa ba ta gane manyan kalamai. Babban kifi sai babbar gora.
Allah kasa mu dace.




Shafi na 6&7.




..... Bilya wacece wannan?, Habib ya yi maganar ba alamun fara'a a fuskar shi.
Bilya cikin girmamawa ya fara magana, kamar haka, "Oga Habib ita ce Yarinyar da muka tsinta, kace in d'akko ta ranar da muka je kano".
Habib wani banzan kallo ya yi ma Bilya, sannan ya ce,cikin fad'a-fad'a " da nace ka d'akkota sai kuma nace ka kaita gidana!? ".
Bilya cikin alamun ban hak'uri, ya ce, "ka yi hak'uri Oga Habib, na aikata kuskure, insha Allah haka bazai sake faruwa ba".
Habib banza ya yi da Bilya yaci gaba da typing d'in sakon da ya ke yi, a laptop d'in da ke gaban shi. Habib sai da yagama abinda yake yi, duk su Bilya na tsaye suna jiran sakamakonsu. Sannan ya d'ago kai ya kalli Bilya ya ce, "Bilya daga nan karku koma min gida ku dukanku".
Bilya cikin tsorata da jin kalaman Oga Habib, duk da dai yasan zai iya ai kata hakan,Bilya ya ce, "Oga Habib dan Allah k........ ".
Habib hannu ya d'agama Bilya, sannan ya nuna masu k'ofar fita".
Baba Lami da sauri ta k'araso in da Habib ya ke, ta ce, "Oga Habib dan Allah ka yi hak'uri munsa.... ".
Habib ranshi a d'an b'ace ya nuna ma Baba lami k'ofa ya ce, "Baba dan Allah ku fitarmin Office! ".
Baba lami fita tayi tana mai da nasanin amincema Bilya da ta yi ta amshi Hassana, gashi abin ja mata kurarta aiki.
Bilya ya je dai-dai k'ofar fita ya tsaya, cikin taushin murya raunanna, ya ce,"Ka yi hak'uri Oga Habib da abinda zan ce maka. Oga Habib amma da kasan bazaka taimaki yarinyar ba, da baka sani na d'akkota ba, Oga Habib sanin kankane bani da gida, ni ba d'an garinnan ba ne, yanzu da kakoreni ina ita zan kaita?, da ace mun barta a'inda muka ganta da Allah zai kawo wanda zai tai maketa, amma mu tai makon da mu kai mata ya zamana bashida amfani. Oga Habib ita fa mace ce,Idan munbarta tatafi ina zata?, Oga Habib dan Allah ina rok'onka dan Allah idan ka koreni tom ita dan Allah ka yi k'ok'ari ka ci ka aikin alkairin da ka yi niyyaryi tun farko akanta. Inda dama kai kayi niyyar taima kon....".
Habib katse Bilya ya yi, alamun ranshi ya fara b'aci da magan-ganun Bilya. Ba kamar maganar shi ta k'arshe ba, wai dama shi ya yi niyyar taimakon ta bashi ba. Habib wani banzan kallo ya yi ma Bilya sannan ya ce, d'an zafafe, "Bilya ni na ce maka zan taimaketa?, dama da nace ma ka ka d'auketa sai aka cema hakan na nufin agidana zata zauna kenan!? ". Habib ya tambayi Bilya cikin d'aga murya.
Bilya shima da yake sosai Habib ya b'ata mai rai, cikin k'ok'arin danne fushinshi, dan yasan in dai ya ce zai sa fushi tom Habib ba zai ya yi abinda ya ke so ba, gara ya yi hak'uri ya danne fushinshi. Hakan yasa Bilya cikin danne fushinshi ya ce, " Oga Habib hak'uri za kai ka tai maka mata, dan na tambayi yarinyar garinsu in kaita, ta ce min ita marainiya ce, shine ma dalilin da yasa nakaita gidanka".
Habib cikin had'e rai ya ce, "Sai aka cema kuma shi maraya bashi da 'yan'uwa, kira min yarinyar".
Bilya fita ya yi, ya iske Baba Lami da Hassana tsaye.
Baba Lami kallan Bilya ta yi, ta ce, "Bilya ya hak'ura ne? ". "Hmmm Baba wannan ne zai hak'ura da wuri haka bai wahalar da mutane ba. Ni Baba Lami dama abinda ke damuna wannan yarinyar ya nuna Hassana da ke tsaye, kuma shine yasa ni taimakonta, shine na ke son yasan yadda zai yi da ita inda shi ya yi niyyar tai makon dama bani ba, shine yanzu da nai mai complain akanta, shine ya ce in kira mai ita".
Baba lami kallan Hassana ta yi, ta ce, "Je ki kinji Allah ya tai make ki, yabarki. Baba lami mai da kallanta ta yi ga Bilya ta ce, " Bilya mufa? ".
"Baba Lami ki rabu da shi kinji, ni na san yadda zan mai, Hajiya turai ta yarda da ni sosai, kuma kinga kema ta yarda da ke, shiyasa ta zab'eki da ki rik'a yi ma Oga Habib girki, dan haka ki bari kawai nasan yadda zanyi, Allah dai yasa in nakirata ta d'aga".
Ameen Baba Lami ta ce.
Bilya kallan Hassana ya yi da har yanzu ta ke tsaye ta k'i tafiya, ya ce, "Je ki Office d'in ce inda muka fito yanzu".
Hassana ko da bata fatan k'ara ganin Habib, kallan Bilya ta yi, ta ce, "Dan Allah ni dai kutai dani inda zaku, ni bana son zuwa dan Allah ".
Bilya dariya ya yi, dan yaga alamar ta tsorata da Habib sosai. Bilya kallan Hassana ya yi, ya ce, "kinga ni yanzu haka nasan ni da Baba zai mai da mu, saboda Mahaifiyar shi tana son mu, da ma ke nake ji, inda bazasu yarda ba ki zauna agidansu, dan yanzu suna tsoran bak'o saboda abinda ya faru da su kwanakin baya, ki yi hak'uri ki je, idan Allah ya taimaka, duk da Oga Habib shegen mutum ne, k'ila ya barki".
Hassana a tsorace ta tura Office d'in Habib ta shiga, dan ita bata son wulak'anci kuma ta lura OgaHabib irin masu wula k'anta mutanan nan ne, saboda kud'insu.
Habib na zaune yana mai cigaba da typing d'in da ya ke a laptop d'in shi, kayan da za'a kawo masu ne ya ke ta aikin lissafawa. Habib na zaune ya ji anturo k'ofa anshigo ba naiman izini ba komai. Habib d'ago kai ya yi yana mata kallan baki da hankali ne, Banza Habib ya yi da ita, ya ci gaba da typing d'in shi ya barta nan tsaye.
Hassana ko magana ta ke son yi tana tsoro dan taga Bilya ma yana mai fad'a bare ita. Hassana jin ya yi banza da ita babu alamunma zai gama abinda ya ke yi bare har ya yi mata magana. Hakan yasa ta ce,cikin rawar murya, kamar yadda ta lura kowa na cewa, "Oga Habib dama Oga Bilya ne ya ce min kana kirana".
Habib ko cigaba da aikin da ya ke yi ya yi kamar bai jita ba, bamu ma wata ala da ta nuna mata yaji abinda ta ce, hakan yasa ta kuma cewa, "Oga Habib dama Oga bilya ne ya ce min inzo kana son gani n...... ".
Tsawar da Habib ya yi mata ce yasa ta yi shiru, cikin d'aga murya Habib ya nuna ta da d'an ya tsa, ya ce, "get out from my Office ".
Hassana fita ta yi jikinta na rawa, dan sosai ta tsorata da tsawar da Habib ya yi mata.
Hassana inda tabar Baba lami da Bilya ta je, amma bata gansu ba. Hassana guri ta samu ta zauna ta yi shiru kamar za tai kuka, tabbas tun yanzu da ba aje ko ina ba, ta fara da na sanin barin gida. Hassana na nan zaune tana kallan ma'aikan gurin kala-kala sai aikinsu suke, can wani d'aya daga cikin staff d'in gurin wanda tun d'azu ya lura da Lokacinda Hassana ta fito daga Office d'in Oga Habib. Inda Hassana ta ke tsugunne ya zo ya sameta, kallan Hassana ya yi, ya ce, "Bai war Allah lafiya kuwa? Nalura da ke tun d'azu keke gurinnan. Idan aiki kika zo naima aiba Office d'in Oga zaki ba, gurin manager zaki".
Hassana d'aga kai ta yi tana kallan shi, sannan ta ce, "Ni ba aiki nazo naima ba, amma inna samu aikinma zan yi".
"Ok, amma dan Allah ko zan iya sanin mekika zo naima, in ba aiki ba? ".
Hassana kallan shi ta yi, sai taji bata da zab'i kamar ta fad'a mai, inda taimo ta ke naima k'ila ya tai maketa. Hakan yasa Hassana ta kallai, ta ce, "Bansan kowa ba a nan Abuja, su Oganku suka tsinceni ahanyarsu ta tafiya kano,suka kawo ni nan, shine yanzu shi Wanda ake kira da Oga Habib, wai bazan zauna agidan shiba, shine shi Oga Bilya ya ce in je Office d'in shi ya na kirana, tom na je kuma ya Koreni".
murmushi ya yi, staff d'in nan, ya ce, "Bilya ai ba wani bane staff ne kamar kowa anan, dan dai shi yana driving d'in Oga Habib ne, kuma in dai Oga Habib ne ya ce yana kiranki a Office d'in shi zai saurareki, sai dai in da kika je ne, kin mai ba dai-dai bane. Kuma maganar gaskiya in ma komawa kikayi ki mai magana kan ya d'aukeki aiki, amma maganar gaskiya Oga Habib ba zai kaiki gidan shiba, dan gidansu akwai tsaro sosai. Idan harshi ya ce kije, ki tashi ki koma ki je zai saurareki, in da yasan da zuwanki".
Hassana tashi ta yi ta nufi office d'in Oga Habib, saboda bata da zab'in da ya wuce ta tashi ta je d'in.
Staff d'in nan kallan Hassana ya yi da tausayawa, dan mata masu ajima Oga Habib ba saurararsu ya ke ba bare ita.
Habib na zaune yana waya da Mommynshi, Hassana ta yi sallama ta shigo.
Habib kallo d'aya ya yi mata ya d'auke kanshi ya ci gaba da wayar shi. Jinai Habib na cewa, "Mommyna dan Allah ki barsu kawai, idan mutum na laifi irin haka ya kamata ai funishiment d'insa. Banajin abinda akecewa daga can b'angaran, sai dai naji Habib ya ce, "Ok, Mommy zasu dawo, amma ni idan tanine ma nafi son inyi driving d'in kaina. Abinci kuma ki rabu da Baba Lami inda ga Baba dije nan".
Mahaifiyar Habib sosai ta nuna ma Habib in dai bai dawo da su bilya ba ranshi zai b'ace. Tana kaiwa nan ta kashe wayarta.
Habib ranshi b'ace ya kira bilya awaya, kira d'aya bilya ya d'aga, yana d'agawa Habib ya ce, "Bilya kazo Office d'ina yanzu".
Habib mai da kallan shi ya yi ga, Hassana da ke gefa tsaye arakub'e.
Doguwar rigar da Likitarnan ta bata ce har yanzu ajikinta, sai wani haif hijab da tasa.
Habib d'auke kai ya yi daga kallanta, sannan bazato ba tsammani Hassana ta ji ya ce, "Ke 'yar wata jaha ce?,kuma me yarabo da ke daga gidan ku? ".
Hassana kallan Habib ta yi taga ba'ita ya ke kallo ba hankalinsama akan laptop d'in gabansa ya ke, ba akanta ba. Hassana muryarta na cracking ta ce, "Ni yar kano ce, mamana da babana duk 'yan jahar kano ne, Babana nada mata biyu. matar Babana tana da fad'a sosai, kuma macece mai son kanta da yawa. Babana tunda ya auri mamana Allah bai bata haihuwa ba, hakan yasa kakata wato Mahaifiyar Babana ta matsama Babana ya k'ara aure. Babana ya auri Umma Rabi ba dad'ewa Allah ya bata ciki ta haifi Aunty jamila, sai da Umma Rabi ta haihu uku sannan Allah ya ba Mamana cikina, tom kuma itama Umma Rabi lokacin tana da ciki, kusan tare sukayi rainon ciki ita da Mamana. Mamana ta haihu da kwana biyu Umma Rabi ma ta haifo yarinyarta mace. Hakan yasa Babana ya ce, sai dai ahad'a sunan mu.
Tom Mamana dama tunda ta haifeni bata da isassar lafiya, hakan yasa kwanana biyar aduniya Allah ya yi ma Mamana rasuwa. Babana sosai hankalinsa ya tashi da mutuwar Mamana saboda yafi jin dad'in zama da ita fiye da Umma Rabi. Tom mamana da ma ita ma ita kad'aice awajan Iyayanta kuma Allah ya yi masu rasuwa dad'ewa, hakan yasa Babana badan ya soba sai dan bashi da yarda zai yi ya d'auke ni ya ba Umma Rabi ni, ya ce ta had'amu ta shayar damu tare da 'yarta.
Da da farko Umma Rabi ta Nuna ma Babana baza amsheni ba, amma sai Babana ya nuna mata dole ta amsheni, in da bai san Wanda zai kai ma niba. Hakan yasa dole Umma Rabi ta amsheni. Ranar suna Babana ya sa mana Hassana da Usaina ni da yarinyar Umma Rabi. Nasha wahala sosai awajan Umma Rabi dan ko kuka nake sai taga dama ta ke ban nono insha. Kuma koda zan riga Usaina tashi in dai Usaina ta tashi tom Umma Rabi sai ta d'auki Usaina ta lallasheta ta yi shuru sannan koda zata kulani.
Ahaka har muka girma. Tunda nafara wayau na fahimci Umma Rabi tafi son Usaina akaina. Babana dawuri ya samu Islamiya, ita Usaina bata cika zuwa ba saini, saboda ni kona ce ba zani ba dole za'a turani. Tun ina 'yar k'arama ta na iya duk wani aikin gida, dan hatta wankinmu Nida Usaina ni ke mana, acewar Umma Rabi ni ce babba.
Babana duk lokacin da zaizo gida ya iske ina aiki sai yi ta fad'a ya ce Usaina tazo muyi tare. Wannan abinda da Babana ke yi shiya k'ara jawo min tsana sosai gurin Umma Rabi.
Ahaka rayuwa taita tafiya har muka girma , muka shiga secondary school. Tom da akwai wani teacher mu, wanda ya ke kula da duk abinda ya shafemu Nida Usaina, sai dai yana yawan yi min complain, akan wai Usaina ta fi ni tsafta, ni dai ban tab'a fad'amai wani abuba game da gidanmu, shine ya tsinto labari acikin gari. Tunda teacher Kabir ya tsinci labarin halinda nake, ya zamana yake yawan yimin kyautar kud'i. Sosai teacher Kabir ke min hidima hakan yasa har Babana ya sanshi.
Muna gama j. S. E. Babana ya ce, bazamu cigaba da karatuba aure zai mana. Tom dama ita Usaina akwai wini dake zuwa gunta harma ya yi ma Babana magana, ni kuma dama teacher Kabir shike Sona shima ya naimi izini gurin Mahaifina ya kuma bashi. Lokacin da Babana ya je ma da teacher Kabir maganar ya turo manyasa gidanmu ai maganar aurena da teacher Kabir . Teacher Kabir rok'on Babana ya yi akan dan Allah ya barni in kamma secondary school sannan. Kasan cewar Babana na son tarayyata sosai da teacher Kabir yasa ya yarda da abinda teacher Kabir ya ce. Koda Babana ya kaima Umma Rabi maganar saina kamma secondary school sannan za ai aurena, cewa ta yi itama Usaina abarsa sai ta kammala sai ayi duka tare. Aiko haka akayi. Muna S. S. S 3 first term, Babana ya sa ranar aure na da Teacher Kabir. Ita kuma Usaina da wani Jamilu d'an layinmu. Umma Rabi bata son tarayyar Jamilu da Usaina ko ka d'an bakamarma da taga teacher Kabir na min hidimaba sosai, ita kuma Usaina babu abinda ke shiga tsakaninta da Jamilu na kyauta. Da akwai wata rana teacher Kabir ya kawo min waya. Wannan kyautar da ya yi min tab'ata ma Umma Rabi rai sosai,hakan yasa tace sai dai in maida mai wai in ya auran ya sai min agidansa. Babana koda yazo yaji abinda Umma Rabi ta ce hanawa ya yi in maida ma teacher Kabir wayar shi". Hassana shiru ta yi, tana goge hawayanta saboda wani kuka da ke son k'wace mata, saboda tunowar rabuwarta da teacher Kabir ta k'arshe da ta yi.
Hassana cikin murya mai kama da ta kuka taci gaba da magana kamar haka, "Ranar da bazan mantataba arayuwata, ita ce ranar wata laraba, Iyayan teacher Kabir suka zo gidan mu wai d'ansu Kabir ya janye maganar auran shi dani ya mai da ta kan Usaina. Bani ba har Babana ya girgiza da jin haka, mamaki da al'ajabi suka cika shi, saboda shi kanshi asanin kanshi Kabir bama sa wani jutuwa da Usaina, sai yau rana tsaka wai ace Kabir ya janye maganar auran shi da Hassana ya maida kan Usaina. Babana cema Iyayan teacher Kabir ya yi tom su bari zaiji daga bakin Kabir d'in sannan. Aiko haka akayi Babana kiran teacher Kabir ya yi ya tambayai ya akan maganar da Iyayanshi suka zo da ita".
Bud'ar bakin teacher Kabir sai cewa ya yi, "Eh hakane shi Usaina ya ke so".
Wannan maganar sosai ta d'aga hankalin Babana. Washe gari da safe Babana ranshi b'ace ya je d'akin Umma Rabi. Babana nazuwa ya kalli Umma Rabi, ya ce, "Rabi ina son kisan wani abu duk k'ula-k'ular da kika yi, ki ka maida auran Hassana ya koma kan 'yarki tom tun wurima ki warware shi, dan ni bazan tab'a aura auran Usaina da Kabir ba, garama kisani tun wuri.
Haka Babana ya gama fad'anshi Baba Rabi bata tanka mai ba.
Abu kamar wasa yazo ya zamana gaske, dan teacher Kabir idan yazo gidanmu sai inga Usaina taje suna hira, ni ko ko gaisuwata baya amsawa. Abin ya daman Sosai, hakan yasa na kaima Babana k'arar teacher Kabir. Babana kallona ya yi cikin alamun tausaya min, dan ya lura ina son teacher Kabir sosai. Hakan yasa Babana cikin lallashi, ya ce, "Hassana kinsan dai wani baya aurar matar wani ko?, haka kuma wata bata auran mijin wani, inji hausawa sunce matar mutum kabarinsa. Tom Hassana dan Allah karki tambayan dalili dan nima ban sani ba, amma ina so ki hak'ura da Kabir ".
Wannan magana da Babana ya fad'a ji nai kamar ya lumamin wuk'a azuciya, dan Allah ya sani ina son teacher Kabir sosai, kodan shine saurayina na farko.
Kuka na fashema Babana da shi jin abinda ya ce.
Babana duk wata magana mai dad'i da zai fad'amin wadda zata sa in yi shiru ya fad'amin, amma ina na kasa. Sosai kukana ya d'agama Babana hankali. Ni ko kafin kace me sai ciwan kai tsabar kukan da nayi haka kaina ya yi ta min ciwo. Aranar dai da ciwan kai na kwana.
Iyayan Kabir ko sun yi ake kamar me akan Babana ya maida auran Hassana da Kabir kan Usaina ya k'i.
Umma Rabi ko ganin Babana yak'i amsar maganar Usaina da Kabir, yasa taturasu wajan k'aninta. Tom da ya ke shima k'anin nata gashi ga irin shi. Hakan yasa batare da binciken komai ba, ya amshi maganar, nan dai ya yi jagoranci aka tsaida ranar auran Usaina da Kabir, wata biyu masu zuwa.
Wannan ranar nayi kuka kamar raina zai fita. Wannan kukan da nayi sosai ya tadama Babana hankali. Kafin kace me hawan jinin Babana ya tashi. Washe gari da safe shiri-shiru Babana be ne meniba. Hakan yasa na lallab'a na tashi dan kaina sosai ya ke min ciwo. Ina tashi d'akin Babana natura nashiga. Ganin Babana kwance kuma harna tura d'akin bai tashi ba, yasa na k'arasa gun shi ad'an tsorace. kiran sunan Babana nayi ina bubbuga k'afarshi amma shiru. Kuka na fasha dan duk da ban san Mutuwa ba jikina ya bani kamar babu rai ajikinsa. Babana ya tafi yabarni yatafi in da bazan sake ganinsa ba. Haka akai zana'izar Babana.
Nayi kuka sosai dan Babana shine abokin shawara, shine abokin firata idan yana gida, shine wanda abu in yasaman nake fad'amawa sai ko teacher Kabir, tom shima anrabani da shi.
Bayan wata d'aya da rasuwar Babama, abubuwa sun cakud'e min, ga aiki na gidan duk ni ke yi, wanke-wanke, shara, girki, wankin kayan mu.
Ana

Please Login or Register in order to submit comment